Ticker

6/recent/ticker-posts

A Ina Allah Yake? Gaskiya Wurin Da Allah Ubangiji Yake

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Akwai Masu Cewa Allah Yana Ko Ina, Suna Hujja Da Faɗinsa a Suratul Hadid Aya ta huɗu:

هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَىٰ عَلَى الْعَرْشِ ۚ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۖ وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

ShI ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

 Dai Wasu Ayoyin, Yaya Abun Yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Allah maɗaukakin Sarki yana Saman Al'arshi, saman dukkan halittu, a wajan Ahlussunnah Wal-jama'a, Haka dukkan manzanni sukazo da Wannan aƙidar, Allah yana Saman Al'arshi. Kamar Yanda ya faɗa a cikin Ayoyi maban-banta Masu yawa acikin Alƙur'ani mai girma.

Allah ya bayyana Ƙarara ya dai-daita a saman Al'arshinsa, dai-daituwar da ta dace da girmansa da Ɗaukakarsa, Ba Wani Abun Halitta da yai Kama dashi wajan yanda ya dai-daita. Babu Wanda yai kama da Allah, ko yake kama dashi.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya Tambayi Wata baiwa a ina Allah yake? Ta ce yana Sama, Ya ce Ni Wanene ta ce: Manzan Allah, sai ya cewa: Uban gidanta ka 'yantata tabbas Ita Muminace. Muslim ya ruwaito.

Wannan ya Nuna Allah yana Sama can Saman Bakwai Saman Al'arshi sama maɗaukakiya.

Sahabbai sun haɗu kamar yanda Manzanni Suka haɗu, akan Allah yana Sama, Saman Al'arshi. Duk Wanda ya ce Allah yana Kowanne waje, ko baya Sama, shi kafirine, Mai Ƙaryata Allah da ManzanSa, da ƙaryata Ijma'in Ahlussunnah Wal-jama'a, Kamar dariƙun bidi'a irinsu *Jahamiyyah da Mu'utazilawa, da Makamantansu, Waɗannan suna cikin Waɗanda sukafi kowa kafirci cikin Mutane, saboda Inkarin sunayen Allah da Siffofinsa.

Fadin Allah maɗaukakin Sarki acikin Suratul Mujadala aya ta 7:

أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ مَا يَكُونُ مِن نَّجْوَىٰ ثَلَاثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ وَلَا خَمْسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمْ وَلَا أَدْنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَا أَكْثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا ۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

Ashe, ba ka ga cwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ƙiyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.

Bata nufin Irin yanda ɓatattu da 'yan bidi'a suke fassara ta, da yanda suke jefa shubuha da ruɗu a zuƙatan Masu ƙaramin Sani.

Abunda Ake nufi acikin Ayar shi ne, Babu wasu mutum uku da zasu zauna suyi zance ko tattaunawa a ɓoye asirri face sai Allah ya zama Na huɗunsu, idan Su biyarne ko Ƙasa da Haka ko sama da haka face Sai Allah ya Zama yana tare dasu, da iliminsa da Buwayarsa, a duk inda Suka kasance, Babu Abunda zai ɓoyu agareshi na Al'amarinsu, Sannan ranar Alƙiyama Ya basu labari akan Abunda Suka aikata, na Alkhairi ko sharri, Sannan yai Musu sakayya dashi, Tabbas Allah Masanine Akan Komai.

Wannan shi ne Abunda ayar da Ire-irenta suke nufi, Bata cin karo da Ayoyi da Ingantattun Hadisan da suka nunar da Allah yana Sama a saman Al'arshi, babu Abunda yake ɓuya agareshi Na ayyukan bayi aduk inda suka aikata Wani abu, yana tare dasu da Ilminsa da Buwayarsa.

Duk Wanda kaji yana jidali da hayaniya akan Abunda ayoyi da Hadisan dai-duwar Allah a saman Al'arshi suka tabbatar, inma tantirin jahile wanda ya gaji bidi'a a nonon uwarsa, ko kuma zindiƙine Batacce wanda Allah ya Wulaƙantar dashi ta hanyar aukawa wannan bata.

Mai Son Ƙarin bayani saiya duba Litattafan tafsiri musamman Tafsirin ibnu kaseer ƙar-ƙashin wannan aya da Makamantanta, da Kuma litattafan Aƙida da Tauhidi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments