Ticker

6/recent/ticker-posts

Taslisin Wakar Ka'ida Da Fa'ida

Rubutawar Asali
M. SALIHU KONTAGORA

***

TASLISI (Ukuntawa)
USMAN NAGADO (II)

01.

Wa bi hamdu zan fara za'ida,

Wanda duk ka san iske fa'ida,

Sai shi zo shi hau bisa ga ƙa'ida.

02.

Fas salatu shi za na nazzama,

Fa'ida ruwan sha kamar zuma,

Babu wanda bai san ta fa'ida.

03.

Ka ga Salihu shi ya ce maka,

Ka yi tambaya zan faɗa maka,

Me ake nufi ne da fa'ida.

04.

Ƙaruwa ta suna da ko biki,

Ƙaruwa ga hanya ta arziki,

Ko wajen sani ka ji fa'ida.

05.

Ka yi kyautar kaza ka sam kaza,

Ka saya kaza ka sayar kaza,

In ka ƙaru ka sami fa'ida.

06.

Ko ka je ga likita na magani,

Ko ka je ga malam biɗan sani,

In ya ba ka ya ba ka fa'ida.

07.

Take na biyo ta kan fa'ida,

Tambaya da ke bin ta fa'ida,

Wadda zan yiwo sai ta fa'ida.

08.

Ya Shaihu ɗan Kontagora da,

Yadda kai bayani ga fa'ida,

Mun fahimta sauran ka ƙa'ida.

09.

Ƙara ba ni dama in ɗan cika,

Ƙa'ida ina kau gaya maka,

Bi ni sannu ka sami fa'ida.

10.

Wane ƙetare nan tsaya a nan,

Wanda duk ka san shi zam haka,

Dan gudun kaza ka ji ƙa'ida.

11.

In ka hangi zaki ka saɓule,

In ka iske kogi male male,

Za ka ƙetare sai ka hau gada.

12.

In ka zo ka daidaici lokaci,

In ka hau gada don isa gaci,

Babu gardama ka bi ƙa'ida.

13.

Naka Usman Nagado na daɗa,

Na yi ma misali ga fa'ida,

Ka fahimta ka gane ƙa'ida.

14.

Baba ga MUSALLASA nai daɗi,

Ba abinda yas saura in faɗi,

Sai mu roƙi Allahu fa'ida.

15.

Ƴan gari da baƙi ku dai jiya,

Ƴan'uwa mu koma ga gaskiya,

Dan mu samu yalwa da fa'ida.

16.

Mun ɗagauta komanmu fariya,

Mun ɗimauta mun kama kishiya,

Gaskiya ina kag ga fa'ida.

17.

Mu da wai muke san musa'ida,

Mun ƙi bin tafarki ta ƙa'ida,

Mu da ke biɗan kai ga fa'ida.

18.

Ba ga Jinnu yau ba ga Bil-Adam,

Ba abinda ke tauye ɗan Adam,

In ka ɗebe ƙeta da hassada.

19.

Me fa binciken rayuwar wani,

Me gare shi me wane yas sani,

Ka ji ɗan Adam ya yi hassada.

20.

Duk ku san da wannan fa ƴan Adam,

Duk abinda ke maida ɗan Adam,

Baya ka ga babban su hassada.

21.

Har da ƙyashi ƙeta fa har da ma,

Hassada ɓata babu gardama,

Ba ɓata da yak kai ya hassada.

22.

Wane zuciyartai ya kyankyasai,

Wanda duk ya zam bai da tsirfa sai,

Ratsa ƴan'uwanai da hassada.

23.

Mai haɗo musulmi su yo faɗa,

Mai ƙwafa da gaba kaza faɗa,

Kaico ya ɓace babu fa'ida.

24.

Ƙulle-ƙulle dan ɓata ƴan'uwa,

Ƙulla rai da ɓarna ga ƴan'uwa,

Shi ake nufi duk da hassada.

25.

Wane yarda Allah ka magani,

Wanda duk ya zam ba shi san ganin,

Ɗan'uwa da ni'ima ya ɗan biɗa.

26.

Dan ya durƙusar ɗan'uwa kawai,

Dan saboda ƙeta kawai kawai,

Yar riƙe shi ya yi mashi hassada.

27.

Wa ka yarda wai du da ɗan'uwan,

Wanda ya yi murna da aukuwan,

Faɗuwanka ya yi maka hassada.

28.

Wane ya fa taɓe a nan da can,

Wanda duk ya san ba a bin ta can,

Ko cikin ruwa in akwai kada.

29.

Ya sani sarai bai sanar da kai,

Yag ga za ka bi sai ya kau da kai,

Dan ka cutu ya yi maka hassada.

30.

In ya cutu shi bai da juriya,

In ka cutu shi ya yi dariya,

Babu ja-in-ja ya yi hassada.

31.

Ko ya so ni'imarka tat tuƙe,

Ko ka ƙaru shi sai ya murtuƙe,

Duk halinsu ne masu hassada.

32.

Ka ga ja'iri mai baƙin ciki,

Ka ji gafili mai wutar ciki,

Bai da hus idan banda hassada.

33.

Mai harin ina wane wai ya kai,

Mai faɗin ina wane za shi kai,

Sa shi can cikin masu hassada.

34.

Ƙera sharri ƙarya a zantuka,

Ƙeta hassada ce haɗa duka,

Allah sauwaƙe mana da hassada.

35.

Shi maƙetaci da mutakabbiri,

Shi munafiki duk da kafiri,

Anka ɗauki sunansu aka gwada.

36.

Da mai butulci da munkiri,

Da azzalumi duk da fajiri,

An haɗa su daidai da hassada.

37.

Kun ga ZAMTASHUN na ƙara ku ji,

Kun sani fa Allah Ubangiji,

Shi ya yo mu to ya ƙi hassada.

38.

Ran da nay yi TASLISI ne na ce,

Rabbana da ikonsa shi ya ce,

Ba shi san ganin masu hassada.

Lit, 28, Satumba, 2025.

Post a Comment

0 Comments