Ticker

6/recent/ticker-posts

Nasiha Shi'iriyya

Bayan na miƙa ta (ƙanwata) i zuwa filin jirgi, kafin jirgin ya gungura na rubuta mata wannan ‘yar NASIHA.

Wannan ‘yar URJUZA ce (gajeruwar waƙa), me ɗauke da muhimman saƙwanni, hakan ne ya sa na zaɓi wannan sahar a matsayin dandalin tura wannan saƙo.

Ba-da-banza-ba, sai dan sauran manazarta su nazarci wannan waƙar, kuma sui hoɓɓasar ɗabbaƙa ta ga ‘yan uwansu a kowane lokaci.

Bismilla na gode Ta'ala Wahidun,
Me kimsa imani a sassan zuciya.

Allah kiyaye Walida ‘yan Cyprus,
Nai addu'ar Alla sa ku sauƙa a lafiya.

Kuma na yi horo na gare ki kina kula,
Ki tsaya a turbar ‘yan gidanku ta tarbiya.

Salla ibada babu wasa ko kaɗan,
Koyaushe addini da shi ki tutiya.

San nan ki sa lura karatu jumlatan,
In kin ci boko sai ki zo ki yi Arbiya.

Ƙyale Gabata, ta gabata a failure!
Ko ma su Basti ba biye wa ƙawalliya.

Komai ki sa wisdom ki yi shi a wisely,
No confusion ai da fatan kin jiya?

Sam kar ki sanya maƙon gida ki hanƙuri, 😳
No need to focus ai a kan Nostalgia.

Ki kula da Zainab to ki ƙaro ƙoƙari,
Domin zumunci wajibi ne gaskiya.

Sannan da dukkan ‘yan uwa duka ɓangare,
Ai yau zumunci na da sauƙi ga waya.

Fa hazihi URJUZATAN laki Walida,
Ki gaida Barista da kin isa Turkiya.

Wannan turaren kar ki ɓoye kai masa,
Kyauta na ba shi fa bani so yai godiya.

Nai sallama a gareki sai watarana to,
Ya Faɗima ga tau nasiha kin jiya.

Ni ne ƙanin Zainab da Sani da Salihu,
Kuma dai brother naki amma Siniya. 😆

Usmanu Nagado ɗa ga Ibrahim nake,
Ni ne na tsara ko akwai mai tambaya.

Na yo salati da sallama bisa Annabi,
Me kimsa imani a sassan zuciya.

(m) Usman Nagado (II)
20 ga Agusta, 2025.
11:58 (na safe).

Nasiha Shi'iriyya

Post a Comment

0 Comments