Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta'aziyyar Fasihi Mal. Garba Gashuwa

GWANI A ALƘUR'ANI || SHA'IRI || ƊAN GWAGWARMAYAR SIYASA || ƊAN KISHIN HAUSA

 "WAƘAR BARDEN ADABI"

 —SANNU DA HIMMA GARBA SADAUKI,

KAI HIDIMA KAN GYARA ƘASATA.

(AMSHI)

In dai kana shaƙa numfashi,

Ka ci ka sha har ma kai kashi,

Muddin mutum na kwana ya tashi,

To wataran dole ba ya tashi,

Ko ba—daɗe zai je maƙabarta.

 

Da ta iso rai ne za ta karɓe,

Kan-mai-jawabi ai ba ta zaɓe,

Ai ba a zille wa ko a saɓe,

Riƙo na tarna take ba—raɓe,

Dangi abokai har ma maƙota.

 

Ta gangaro kan Garba sadauki,

Ɗan Gashuwa sha'iri fa gwanki,

Fannin fusaha cene shi zaki,

Labarin tamkar fa a mafarki,

Fesbuk rubuce na ko karanta.

 

Waƙar "Mutum wanda ba a i mai",

"Sannu da Himma" ka bi da mai-mai,

"Allah kiyaye" waƙar da yai mai,

IBB ya tabbatar da komai,

Fannin ƙasida ya jinjina mai,

Dukkan fasihai ya ba su rata.

 

Gwagwarmayatai har ƙoƙari nai,

Ya ɓata dukkan nin shekarunai,

A ƴanta kowa yayye da ƙannai,

Dan mu ji daɗi ya sai da rainai,

Sannu da himma ka so ƙasata.

 

Barden mawaƙa an sallama ma,

Maƙogaran P.R.P bale ma,

In kun haɗe da Isah Bunguɗu ma,

Sauran Fasihai ba mai fa toma,

Idon su dan dai zai raina fata.

 

Dare da rana sanyi da zafi,

Duk mun wuya ya tsaya a kaifi,

Guda fa shi bai da wani haufi,

A kanmu ya jure duka yarfi,

Allah ya saka Barden Ƙasata.

 

Shin me ya saura a duniyar nan,

Ya ku fasihai ku san da wannan,

Ba Sambo Wali ba Garba wannan,

Ba ɗan Magoga a shekarar nan,

Mun yo rashin Sha'iranmu kwata.

 

To yanzu aikinsu ne ya wanzu,

Kamar suna nan ƙasar a yanzu,

Dan sun fa jajirce ne a ɗazu,

Me zai hana mu ma mui gumurzu,

Dan gyara addini na ƙasata.

 

Yau Garba Gashuwa ya je makwanci,

Ya za mu kwanta wai mui ta barci,

Bayan ƙasar ta zurfafa ƙunci,

Da ba ta kai hakka ba a ɓaci,

Su Garba sun kai tsaye mu huta.

 

An tafka jibgegiyar asara,

Kan ilimi yau ƙasa a tura,

Ga hikima ba dama a shura,

Ahir Fasihai mu bar gadara,

Cikinmu wai zai tsaya ku furta.

 

Kai Jalla ya mai baiwar fusaha,

Wajen yabo gun Manzanmu Ɗaha,

Ka duba littafinai Fusaha,

Tsantsar basira ya mai Ilaha,

Da kwaikwayon ma murya ta Shata.

 

Na yo kira to gurbin Hukuma,

Kar dai a mance sunansa shi ma,

Da hidimarsa ga ƴan ƙasa ma,

A SANYA SUNANSA JAMI'A MA,

Wannan fa shi ne to manufata.

 

Kan Sambo Wali muna tuni ma,

Malam Kabiru Magoga shi ma,

Da Dr. Yusuf ɗan Ali shi ma,

Ga Sheikh Muhd Ƙani fa shi ma,

Sun hidima gun gyara ƙasata.

 

Barden mawaƙa ga ƙi—garaje,

Zaki fashe ayarin mazaje,

In yai amo kai tamkar ya gwarje,

Sai nan-da-nan sun karkaɗe buje,

Sun gudu ba sa ƙaunar ƙasata.

 

Kiran da zan yi aboka dangi,

Ku dangana ba ihu da zagi,

Dan kar mu faɗa cikin fa ƙangi,

Rai na wurin Jalla babu zargi,

Shi ya ara mai ya kuma ƙwata.

 

Me zan yi wai ne yau rai ya huta,

Wai in yi kuka ko in fusata,

Ko na yi ma bai biyan buƙata,

To zai fi ma in yi addu'ata,

Ga malami Garba na ƙasata.

 

Allah kai ne Rabbi Ganiyyu,

Me sama Allah ya Alhayyu,

Dan darajar Manzonka Nabiyyu,

Gun Garba yo rahmarka Ganiyyu,

Ka haskaka mai inda ya kwanta.

 

Allah dai kai ne da sarauta,

Don haka kai ne ka yi halitta,

Don haka kai kab bani fahimta,

In shirya waƙa har in rubuta,

Kan ta'aziyyar Garba na yi ta.

 

Ka ƙara salati gun Manzo,

Ahmadu Ahmadu mai ƙwazo,

Alu Sahabbainai Manzo,

Ka sa su ciki maƙurar ƙwazo,

Ka ban ladar ta'aziyyata.

 

(m) Usman Nagado (II)
1 ga Satumba, 2025.

Post a Comment

0 Comments