Daga
Jabir Mahmood
Sashen Hausa, Jami'ar
Jihar Bauchi
28/12/2019
MATASHIYA
Al’ummar Hausa dai, al’umma ce dake zaune a arewa maso yammacin Tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin Jamhuriyyar Nijar. Al’umma ce mai dimbin yawa, sun bazu a cikin kasashen Afirka da kasashen Larabawa, kuma a al’adance masu matukar hazaka, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin wadanda harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A tarihi, Hausawa na tattare a salsalar birane. Hausawa dai sun samu kafa Daularsu tun daga shekarun 1300, lokacin da suka samu nasarori da dauloli kamar daular Mali, Songhai, Borno da kuma Fulani.
A farko-farkon shekaru na 1900, a lokacin da Hausawa ke
yukurin kawar da mulkin aringizo na Fulani, sai Turawan Mulkin Mallaka na
Birtaniya suka mamaye Arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan
gida, a bisa karkashin mulkin Birtaniya,’yan mulkin mallaka sai suka marawa
Fulani baya na ci gaba da manufofin aringizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin
gamin-gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne ya yi kane-kane a arewacin
Nijeriya .
Koda yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da zuwan
Addinin Musulunci da kuma karbarsa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha
bamban.
Ginshikan al’adun Hausawa na da mutukar jarumta, kwarewa da
sanayya fiye da sauran al’ummar dake kewayenta. Sana’ar noma ita ce babbar
sana’ar Hausawa, saboda ingancin noma; Hausawa ke wa sana’ar noma kirari da
cewa, “Na duke tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Akan samu
kimanin watanni shida babu ruwan sama.
To wannan yanayi ne ya ba wa Hausawa damar rinka fita daga
wurarensu zuwa wasu wuraren domin yin wasu sana’o’i da ayyuka na musamman, irin
wannan fita ce Hausawa suke ambata da cirani. Ana yin wannan fita ce don a
cinye tsayi na rani, sai ka ga ba za a dawo gida ba sai alamun damina sun fara
bayyana (Gusau, 2008: 5 – 6).
Akwai kuma wani nau’i na tafiya da Hausawa suke yi wanda kai
tsaye ya shafi fatauci inda suke daukar kaya da jakuna daga wani wuri zuwa
kasuwanni daban – daban. Masu wannan fatauci su ne ake kira fatake (Falke:
tilo). Shugaban fatake kuwa shi ne Madugu (Madugai: jam’i). haka kuma a irin
wannan tafiya akwai ‘yankoli. (Gusau, 2008:6).
A takaice, za a iya cewa akwai Hausawa mazauna kasar Hausa
daban – daban wadanda suka hada da manoma da mafarauta da mayaka da madugai da
fatake da masunta da masaka da makera da majema da maharba da madinka da
malamai da masarauta da makada da mabusa da dillalai da kuma ‘ya’ya da bayi da
sauransu. (Gusau, 2008:6).
Harshen Hausa shi ne mafi girma da sanayya a nahiyar Afirka,
harshe ne da ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman Larabci sannan kuma
harshen na tafiya tare da yanayi na zamani bisa al’adar cude-ni in-cude-ka.
Harshen Hausa ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin
jama’a da ba Hausawa ba ne a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, akwai cinciridon al’ummar Hausawa a manyan
biranen yammacin Afirka da arewacin Afirka da kuma yankunan cinikayyar al’ummar
Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar su ta zuwa aikin
Hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce
a rubutun Ajami da aka buga tun kafin zuwan Turawa ‘yan mulkin mallaka na
Birtaniya.
Hausawa sun yadu a kasashe da yawa a cikin Afirka da
kasashen Larabawa, cikin wadannan kasashe akwai: Sudan, Saudiya, Libya,
Aljeriya, Burkina faso, Kameru, Aljeriya, Benin, Cadi, Gambiya, Ghana, Togo,
Gine-Bisau, Mali, Sierra Leone, Gabon, afirka ta tsakiya, Libya, Ethiopia,
Kwango.
ASALIN KASAR HAUSAWA
Masana tarihi sun ambaci cewa, akwai mutane tun lokaci mai
tsawo da ya shude a wadannan garuruwa na Kasar Hausa, kuma babu wanda zai bugi
kirji ya ambaci daga inda suke, koda yake dai wasu kuma sun ambaci cewa ana
kyautata zaton asalin Hausawa barbarar yanyawa ne tsakanin mazauna kasar da
baki da suka yiwo kaura daga kasashen Asiya zuwa kasashen Afirka.
Dalilin wannan kaurar kuwa, an ce wai juyin mulkin da ya
faru ne a tsakanin Banu Abbas da Banu Umayyah a Bagadaza, shi ya sanya wasu
suka yiwo kaura, daga nan ne suka bazu cikin Afirka ta Yamma, musamman ta
fuskar kasuwanci. Sai dai kuma an ce, yayin da suke yin wadannan
kaurace-kauracen ne, kamanninsu da harshensu da al’adunsu suka canja saboda
auratayya da canjin yanayin rayuwa.
Har ila yau an kara da cewa, ana zaton mutanen sun fi dadewa
a Daura da Kano, ba don komai ba kuwa sai don su ne aka gwada kuma aka ga akwai
dadadden tarihinsu da yadda mutanen suka rayu a wadannan wurare. (Adamu, M.T.
1997:21 – 22).
Akwai masu ra’ayin cewa, tun asali Hausawa a garuruwansu na
kasar Hausa Allah ya yi su, ba wai sun yiwo hijira ba ne daga wani wuri suka zo
nan din. Malaman suna da hujjoji masu yawa a kan hakan, daga ciki suna kafa
hujja da maganar babban Malamin nan Sheikh Nasiru Kabara, kamar yadda yake cewa
jirgin kwale-kwalen Annabi Nuhu (AS) yayin da ruwan Dufana ya dauke ya tsaya ne
a wani gari mai suna ‘Yandoto, wanda yanzu garin yana cikin Jihar Zamfara ta
nan kasar Hausa.
A wajen masu wannan ra’ayi, wannan nahiya tun asali ana
kiran ta da shi wannan suna ne da aka santa da shi wato “Hausa”.
Yawan kare-kare a wasu shiyyoyi na Kasar Hausa, da
karancinsu a wasu wuraren shi ne babban dalilin da za a jinginu da shi. A cewar
masu wannan ra’ayin duk inda kare- karen suka tattaru a dan kankanen wuri, to a
nan aka haifi harshen. Idan kuma ka ga harshe ya yadu bai daya a kasa mai fadi,
to ba a nan aka haife shi ba ya zo ne daga wata kasa.
(T/Wazirchi, 2009:17 – 18). Bunza, yana da irin wannan
ra’ayi cewa “Hausa ba daga wani wuri ta zo ba Nahiyar Gobir nan ce mahaifar
Hausa”. (T/Wazirchi, 2009): 18). Sannan su ma mafi yawan mawakan baka, musamman
wadanda suka fito daga yankin Sakkwato, Zamfara da Kabi suna ambaton wannan
nahiya “Hausa”.
Idan muka koma ga gurbin kasar Hausa, wato taswirarta ta
faro ne daga yammacin Afirka, yankin kudancin Sahara kuma arewa da Kurmi inda
Larabawa ke kira Biladul Sudan, wato kasar bakar fata. Yanki ne da ya kunshi
kasashe da dauloli da dama a cikinsu har da kasar Hausa.
Wadda ta kafu a Yammacin Sudan, tsakanin Tafkin Cadi daga
Gabas, da guiwar Kogin Kwara daga Yamma, da hamadar Sahara daga Arewa, da kuma
dazuzzukan gabar Tekun Atilantika daga Kudu. Dangane da kasashe da kabilu da
kasar Hausa ta yi iyaka da su kuwa, a Gabas ta yi iyaka da Kanem-Borno, a
shiyyar Kudu, kuma ta yi iyaka da kwararrafa (Kasar Tibi, Nufe, Gwari, da
sauran tsirarun kabilu).
A yamma kuma ta yi iyaka da tsohuwar Daular Songhai, daga
shiyyar Arewa kuma kasar Hausa ta yi gaba da garuruwan Buzaye (Agadas) na cikin
kasar Nijar. (T/Wazirchi, 2009: 11 – 12). A yanzu haka idan muka duba taswira,
za mu ga Kasar Hausa tana Arewacin Nijeriya ne da kuma wani sashi na Jamhuriyar
Nijar (T/Wazirchi, 2009: 12).
A cikin kabilu mazauna yankin Sabannah, wato kasa mai
karancin itatuwa, ko mai itatuwa jefi-jefi, Hausawa su ne suka fi mamayar wurin
zama mai fadin gaske. Wannan wuri shi ne aka fi sani da kasar Hausa. (Gusau,
2008: 2).
ASALIN KALMAR HAUSA DA MA’ANARTA
Akwai maganganu da yawa dangane da asalin kalmar Hausa, inda
suka bayyana a matsayin ra’ayinsu. Daga cikin maganganun akwai:
Nil Skinner (1968) cewa ya yi, “Asalin kalmar Hausa, an samo
ta daga Songhai. A ganinsa, akwai dadaddiyar dangantaka tsakanin Hausawa da su
mutanen Songhai, har ta kai Hausawa suna aron kalmomin Songhai domin a nasa
binciken cewa, kalmar Hausa an samo ta ne daga ‘Assa’ sunan da suke kiran
mutanen da suke Gabas da su, su kuma Hausawa suka aro suka lakaba wa kansu.
Malam Aminu Kano kuwa, ya bayyana cewa an samo kalmar Hausa
daga kalmar Habasha, wai don a cewar sa asalin Hausawa mutanen Habasha ne, kuma
a maimakon a rinka cewa Habasha din sai ake cewa Hausa. (Adamu, M.T. 1997:19).
A nasa tsinkayen, Mr. C.R. Niben (1971) cewa ya yi, an samo
asalin kalmar Hausa ne daga Buzaye, domin kuwa haka suke kiran mutanen dake
zaune a arewacin Kogin Kwara, wato Hausa. (Adamu, M.T. 1997: 19).
Shi kuwa mai Martaba Sarkin Ningi; Alhaji Haruna Wakati,
cewa ya yi an samo kalmar Hausa ce daga labarin zuwan Bayajida garin Daura, a
lokacin, da ya isa da daddare ya sauka a gidan wata tsohuwa ‘Ayyana’ ko kuma
‘Wayre’, inda ya bukaci ruwan sha a wurinta, da cewar ba ta da ruwa ya tambaye
ta ina zai samu, ita kuma ta sanar da shi babu inda zai samu sai ya je rijiya,
kuma matsalar ba a diban ruwa sai sati-sati ake zuwa a debo ruwa; saboda wata
macijiya mai suna sarki.
Daga nan sai ya bukaci ta ba shi guga, ta nuna mai inda
rijiyar take ya je ya zura guga ya fara debo ruwan, sai wannan macijiyar ta
biyo igiyar gugar, shi kuma ya sa takobi ya sare kanta. Inda labari ya bazu a
gari har Sarauniya Daurama ta samu labarin abin da yake faruwa, ta sa a nemo
wanda ya kashe macijiyar don a yi masa kyautar bajintar da ya yi. Ana ta neman
wanda ya kashe amma ba a same shi ba.
Sai aka tambayi tsohuwa, wanda ya kashe ta ba a same shi ba.
Sai ta ce musu “Ai ya hau”. Hau-sa maimakon ta ce ya hau doki tunda ita ba ta
taba ganin doki ba. To wai wannan ‘Ya hau-sa’ ne aka hade kalmomin ne suka koma
‘Hausa’.
Haka kuma a wata fadar an ce, da can Larabawa da suka zo
harkar cinikayya Arewa zuwa Kurmi, lokacin da suka zo suka ga kalmomi da dabi’u
irin nasu, sai suka ce wadannan mutane sun so su yi kama da mu, amma sun dan
karkace. To shi ne idan za su zo sai su ce: “Za mu Hawasa”, wato za su garin
karkatattu. (T/Wazirchi, 2009:14).
Masu ra’ayin Harshe suna ganin cewa kalmar Hausa a wurin su
‘Bahaushe’ ma’anar ta “harshe”, domin idan ka yi magana da wani harshe daban,
bahaushe yakan ce ” Ya ji ana wata Hausa”, wato a nan Hausa sunan harshe ne ba
na kabila ba, kuma al’ummomin da suka taru suke magana da wannan harshe su ne
Hausawa. (T/Wazirchi, 2009: 16).
A takaice dai, Kalmar Hausa tana nufin harshe, tana kuma
nufin mutanen da suke magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa, kamar
yadda kuma take nufin kasar da su wadannan al’umma ta Hausa suke zaune. Saboda
haka ne ake kiran harshen da cewa “Harshen Hausa” a kuma ce “Bahaushen Mutum”
sannan a cewa mazauninsu “Kasar Hausa”.
SIFFOFIN BAHAUSHE DA HALAYENSA
Bahaushen mutum baki ne amma ba baki kirin ba irin wadanda
Turawa ke kiran su Negroid, domin su bakin su wankan tarwada ne. Bahaushe ba
shi da dogon gashin kai irin na mutanen Songhai, amma kirar jikinsa da
kamanninsa daidai yake da na al’ummar Aryaniyawa (Aryan), wadanda da suke zaune
a tsakanin kasashen Turai da Asiya, kafin su yi hijira su watsu wurare
daban-daban a duniya. Game da halayensa kuwa, halaye ne na nagarta wadanda ya
shahara das u, kuma yana daya daga cikin shahararrun kabilun da ake girmamawa a
Afirka. Wadannan halaye na Bahaushe su suka daga shi har ya yi fice aka san shi
a duniya ta da, da ta yanzu fiye da sauran kabilun bakar fata a Afirka ta
Yamma. (Kantoma, 2011:16-17).
SHUGABANCI A WURIN HAUSAWA
Shugabanci na nufin rikon ragamar al’umma da ba su umarni da
yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da
sasanta tsakaninsu, da makamantan wadannan. Shugaba shi ne kololuwa a tsakanin
al’umma, wato shi ne yake saman kowa, umarninsa ake bi, shi ne mai zartar da
hukunci a tsakanin al’umma. A Kasar Hausa kuwa, akan samu sarki a matsayin
shugaba, sai kuma ‘yan fadarsa wadanda su ne masu taimaka masa wajen tafiyar da
al’amuran jagorancinsa.
Shugabanci ta bangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga
tsarin zaman iyali inda maigida yake kamar sarki a gidansa, wanda shi ne babba,
daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko
fiye da haka akan zabi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi
wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jaruntaka da dauriya. Wasu dalilai
kamar halin kunci a cikin gida ko bukata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya,
kan sa maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani wuri na daban,
kamar gona ko garke. Ta haka ne iyali kan yadu su yawaita su hada wani kauye.
Saboda haka ne sai a kara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan kauye.
Wannan shi ya haifar da mukamin Mai Unguwa kuma shi zai rinka tsara musu
dokoki.
Kauye yakan bunkasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka sai
a kara zabar wani mutum a matsayin Maigari (Fagaci) domin kula da wannan gari.
Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka kara yawaita sai aka samar da mukamin
Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Maigari akalla guda biyar don ya kula da su.
Da tafiya ta yi tafiya, sai aka samar da mukamin Sarki, inda ake hada wa Sarki
masarautar Hakimai akalla biyar ko fiye domin ya shugabance su ya kuma shimfida
musu dokoki domin zaman lafiya.
DOKA A KASAR HAUSA
Game da ma’anar Doka kuwa, Neil Skinner (1980), ya bayyana
cewa “Doka wata tsararriyar hanya ce da akan gindaya ta ga mutanen gari, da
kuma horo ga duk wanda ya ketare ta don samar da tsaftatacciyar rayuwa ga
wannan al’umma”.
RABE-RABEN TSARIN DOKA A KASAR HAUSA
Dangane da rabe-raben doka kuwa, masana sun raba su zuwa
gida uku kamar haka;
Doka a bangaren cikin gidan Hausawa.
Doka a bangaren shugabanni.
Doka a bangaren masu sana’o’in gargajiya.
Wadannan su ne manyan rukunai ko azuzuwan da doka ta kasu
gare su. Ga yadda bayanansu yake.
DOKA A BANGAREN CIKIN GIDAN HAUSAWA:
A gargajiyance gidan Bahaushe yakan kunshi maigida da
matansa, da ‘yan’uwansa, da kuma ‘ya’yansa. Iyali shi ne ainihin ginshikin da
aka kafa al’ummar Hausa a kansa. Daga iyali ne jama’a kan faru, har su zama
‘yar kungiya, daga nan kuma su hadu su samar da ‘yar unguwa, wadannan unguwoyi
suke haduwa su kafa kauye, daga nan kuma sai garuruwa su samu.
A zaman iyalin Bahaushe, babba ne kan yi kokarin sadaukar da
kansa, ya kyautata wa na kasa da shi. Shi kuma karami ya yi masa biyayya, da
kauce wa duk wani abu da ka iya kawo raini ga na gaba. To akasari za ka tarar
irin wannan gida, gida ne na gado, wato wanda aka gada tun kaka da kakanni kuma
ba a raba shi ba. Sau da yawa irin wannan gida a tukunya guda ake girka abincin
da za a ba wa kowanne.
A wani bangare kuwa, Kaka na wajen uwa ko na wajen uba, shi
ne mai yin hukunci na farko a tsakanin danginsa, kuma shi ne zai fadi abin da
za su yi. Idan ka ga an jingine Kaka, to ya tsufa ne ko kuma ba shi da
cikakkiyar lafiya, ko ta Allah ta kasance a kansa (ya mutu).
A wannan bangare ana yin amfani ne da Doka ta ina gaba da
kai, don haka dole abin da na umarce ka shi za ka bi, ki da so. A lokacin da
maigida ba ya nan, wansa ko kaninsa shi zai zama a makwafinsa, kuma ko mahaifi
(Maigida) yana nan zai iya zama a makwafinsa, misali zai ce “Kai wane mun samu
labari kana neman auren ‘yar gidan wane, ba za ka aure ta ba”.
Shi kenan ba ka da ta cewa, don yana cikin masu fada a ji a
cikin danginku. Kuma sannan wadannan ‘ya’ya ba za su zama manya ba ko da kuwa
an yi musu aure, har sai sun hayayyafa. Kun ga kenan na gaba yana wucewa na
baya na maye gurbinsa, shi ma wancan kakan a da jika ne na wani, ya zama da, ya
zama uba, kana ya zama kaka. Don haka Kaka shi ne tsani na farko da za a taka
wajen bin Doka ta cikin gida.
Idan muka juya bangaren aure kuwa, Hausawa suna da al’adar
wanda duk aka ba wa yarinya ta bayu, ko tana so ko ba ta so, dole ne su zauna
tare. Haka shi ma mijin ba kasafai ake bari ya zabi wacce yake so ba, yana yin
uhn! Za a ce “Kai! Da ubannika za ka yi jayayya?.
Ko kuwa wannan ba kanin ubanka ba ne? Wato ba shi da iko a
kan ka kenan?”. Haka nan a kan dole zai zauna da wannan mata, in da rabo ma sai
ka ga sun hayayyafa. Su ma idan suka tashi aurar da ‘ya’ansu irin wancan auren
da aka yi musu (na zumunta) za su yi wa ‘ya’yansu.
DOKA A BANGAREN SHUGABANNI
Shugabanci a Kasar Hausa ya danganci rikon ragamar al’amuran
jama’a, wanda ya hada har da ba su umarni, da kafa musu doka, da sulhunta
tsakaninsu da sauran hakkokinsu na yau da kullum. A karkashin wannan aji na
bangaren masu mulki muna da Sarki da Hakimi, da Dagaci (Fagaci) da kuma mai
unguwa. Ga bayanin yadda kowanne daga cikinsu ke zartar da Doka a bangarensa.
MAI UNGUWA:
Shi ne sabon shugaban da talakawa suka zaba a yayin da suka
fuskanci sun soma yawa, dole tafiyar sai da jagora, daga baya ne abin ya zama
gado. To shi Mai unguwa yana cikin masu kafa Doka a bi dole, ko ya hana don
karfin mulkinsa, sai fa idan abin ya fi karfinsa ne zai tura shi gaba.
DAGACI (FAGACI):
Shi ne mutumin dake mulkar unguwannin dake karkashin masu
unguwanni kamar biyar ko fiye, ana kiran sa Maigari saboda yankinsa ya fi
karfin unguwa. To shi ne mai zartar da hukuncin da ya gagari masu unguwannin
dake karkashinsa.
HAKIMI:
Ya samu wannan suna ko mukami ne a yayin da aka samu ci
gaba, kuma garuruwa suka kara yawaita. Sai aka ba wa Hakimi garuruwan Fagaci
akalla guda biyar don ya kula da su. To shi ma Hakimi idan abu ya daure masa
kai, yakan tura shi kai tsaye ga shugaban kasa na gargajiya (Wato Sarki).
SARKI:
Shi ne shugaban koli ga dukkan mahukuntan da aka yi
bayaninsu a baya, shi ya sa ma wasu ke yi wa sarki kirari da “Bango madafar
bayi”
DOKA A BANGAREN MASU SANA’O’IN GARGAJIYA:
Al’umma tamkar jikin dan’adam take, wanda baya ga aikin da
tilas ne kowace gaba ta yi don tabbatar da rayuwarta cikin inganci, akwai kuma
gudunmawar da take ba da wa don kasancewar dan’adam din jiki guda. Ga kuwa
sauran aikace-aikace da suke da muhimmanci fiye da saura, wadanda in ba a yi su
ba, sai ta kai ga katsewar rayuwa. Wannan siffa ta al’umma, ta tilasta wa kowa
daga cikin jama’arta yin wani aiki, domin tabbatar da wanzuwar al’ummar, ba ya
ga wasu aikace-aikace da suka zama dole ga kowa, domin rayuwarsa shi kansa.
Sarakuna a kowanne gari, sun bai wa shugabannin sana’o’i da
manyan bokaye, da jarumai har ma da dattijan gari matsayi na musamman wajen
gudanar da mulkinsu. A hakika ma, bincike ya tabbatar da cewa wadannan
rukunonin jama’a ne suka zamo mataimakan Sarki, wajen tafiyar da mulkin
yankinsa.
Don haka a gargajiyance ana zabar dattijo da ya fi kowa
yawan shekaru da kwarewa a kan sana’ar da mazauna wurin suke yi. Irin sana’o’in
da ake da su a wancan lokaci sun hada da Noma, Kiwo, Kira, Jima, Saka, da
sauransu.
Bisa ga tsarin zama na gargajiya, Hausawa sun amince da
zaman cude-ni-in-cude-ka. Kowanne mai sana’a, yakan yi la’akari da cewa kamar
yadda yake bukatar wasu abubuwa don nasarar sana’arsa, haka ma wasu ke bukatar
wani abin daga gare shi. Wannan fahimtar tasa kowanne mai sana’a yakan yi fiye
da abin da yake bukata, ta yadda zai iya amfana daga abin da ya saura, don
mallakar wasu abubuwa da ba zai iya yi da kansa ba.
Misali, Manomin dake bukatar wuka, ko fartanya, ko lauje,
sai ya dauki hatsinsa ya kai ga Makeri. Haka shi ma makerin zai ba da garma ko
takobi don a yi masa yabbe ko jinka ko dinki. Da haka sai ka ga kowa ya samu
biyan bukatarsa kuma rayuwa ta saukaka, wannan, nau’in ciniki shi ake kira
cinikin furfure.
Amma ko ba a fada ba, irin wannan rayuwa, tana bukatar kowa
ya yi aiki tukuru, tare da nusar da mutum zuwa ga yin tsimi da tanadi na abin
da ya yi saura don gaba. Wannan ya sa tsarin tattalin arzikin Hausawa ya ginu a
kan sana’o’insu.
To idan kuma ya kasance a bangaren sana’a kamar ga Mahauta
ne, wani ya ci bashin dabbar wani ya ki biya, to shi wanda aka ci bashin nasa
ba zai ja wancan da rigima ba, a’a sai ya tafi wajen Sarkin Fawa ya yi kararsa.
Shi kuma Sarkin Fawa zai tura daya daga cikin fadawansa su yi kiran wanda ya ci
bashin, a nan za a kashe rigimar, ko Sarkin Fawa ya biya, ko a yi wa wanda ake
bi bashi lamuni ya kawo. To haka ma abin yake ga sauran masu sana’o’in
gargajiya da suke da sarakuna.
ADDINI DA BAUTA A WURIN HAUSAWA
Addini hanya ce ta bauta, wadda tilas dukkan dan’adam ya bi.
Allah (S.W.A) ya ce “Ban halicci mutum da aljani ba sai don ya bauta Mini”.
Amma kuma ya ba su na su bauta wa Allah da ya hallicce su. Ko kuma su bauta wa
waninSa. Abin da kawai dan’adam ba zai samu ba, shi ne ya zauna bai yi bauta
ba, ko ba komai ya bauta wa cikinsa, ko wani ra’ayi nasa. Allah ya tsare mu,
amin.
A matsayinsa na hanyar bauta addini shi ne yake daidaita
tunanin dan’adam da dukkan al’amuransa na rayuwa, ko da kuwa kowanne addini
mutum ya zabi ya yi, to kuwa za ka tarar addinin nasa yana da kwakkwaran tasiri
dangane da yadda yake tafi da harkokin rayuwarsa.
Idan kuwa muka koma dangane da bauta, addinin Hausawa na
gargajiya za mu tarar yana da dokoki, da tsare-tsare da mabiyansa ke bi. Misali
ga alama ‘Kan-Gida’ shi ne abin bautar kowanne iyali na Hausawa. Dodo kuwa,
abin bauta ne na jama’ar gari, kowanne gari suna da Dodon da suke bautawa, za a
iya cewa Tsunburbura ita ake bautawa a Kano. Daura kuwa, suna bauta wa
macijiya. Zariya kuwa suna bauta wa dodanni da ake kira ‘MADARA’ Da ‘KUFE’.
Shi kuwa Bori addini ne da Hausawa suke bautawa ‘ubangiji’
ta hanyar iskoki. Shi kansa addinin bori, duk da cewa ya yadu a Kasar Hausa, ba
kowa da kowa ne ya karbi addinin yake bi ba. Ma’ana ba kowane Bahaushe ne dan
bori ba, sai wanda ya yarda da addinin, kuma shugabanni addinin na bori suka
karbi yardar tasa, suka yi wasu al’adu na shigar da shi addinin nasu.
Misali, mutumin da ya zabi ya bautawa kare, za ka same shi
yana kaffa-kaffa da karen tare da yin dukkan abin da kare ke so, da kuma barin
dukkan abin da karen ba zai so ba. Haka za ka samu wannan mutum ya cika da
bakin ciki a duk lokacin da wani ya saba wa karen, ko ya sa shi fishi, sannan
ya yi farin ciki da wanda duk ya kyautata wa karen ko ya gan shi cikin koshin
lafiya da annashawa, dan haka duk wata harka da ba ta shafi karen ba bai damu
da ita ba. Karen nan ya sani, shi ya tsare aikinsa ke nan hidimar kare. Dan
haka ba ya sake da duk wata doka da ya kafa wa kansa game da karen.
TUFAFIN HAUSAWA NA GARGAJIYA
Dangane da sutura, masana da dama sun yi bayani kan suturun
Hausawa na gargajiya wato. Misali, Alhassan da Musa (1980), cewa suka yi,
“Galibi adon namiji na Hausa ba ya wuce riga gare da wando musamman tsala, da
takalmi faɗe ko
kafa-ciki da hula kube. ko ɗanƙwara,
ko dara. Idan kuwadattijo ne, yakan sa rawani. Adon mata kuwa zani ne da
gyauton yafawa, watau gyale da kallabi da taguwa da ‘yan kunne da dutsen wuya watau tsakiya”. Magaji (1986) kuwa cewa
ya yi, “Idan aka ga
mutum da babbar riga da ‘yar
ciki da wando za a sa a rai cewa Bahaushe ne, koda mutum ɗin kuwa ba Bahaushe ba ne
ba.
Bisa haka, masana suka bayyana riga Aska-Takwas,
Girken-Gwandu, Binjima, Kwaƙwata, Riga mai kwaɗo,
Sace, Riga mai barrage, ‘yar madaka, Bulla fara da baƙa dukkaninsu kaya ne na
maza. Mata kuwa kan sanya tufafi inrinsu: Zanin Gwandai, Duhun-saki, Bakurde,
Adikko da sauransu.
TASIRIN ZAMANANCI AKAN SUTURA
Dangane da tasirin baƙin al’adu kan suturar Hausawa, A’ishatu (1991) tana cewa; Hausawa sun ɗauki tsarin suturun Turawa
domin kuwa a yanzu suturun Turawa sun yi yawa a wajen Hausawa musamman matasa
waɗanda su ne
madogarar al’umma, kuma manyan gobe. Wannan shi ya sa suturun Hausawa na
gargajiya suke neman ɓacewa
wurin Hausawa matasa sai na Tarawa. Misali, yanzu in ka lura da Hausawa
musamman matasa duk inda suke, sai ka tarar ko dai tsarin suturunsu tsarin ɗinkin Turawa ne ko kuma
yadin ainihin saƙar, Turawa ne. Ɗinkin Hausawa ko yadinsu sai ƙalilan
ne ake samu wajen Hausawa. Maimakon tsarin wadatattun suturun Hausawa da aka
san su da su sai matsattsu irin na Turawa da yadinsu sun mamaye na Hausawa na
gargajiya. Mai karatu na iya duba matsayin maganin gargajiya a wurin Bahaushe.
Bayan baka, baƙin al’adu da suka shafi sutura
sun kawo tufafi irinsu kwat, shat, siket da nek tayal, waɗanda ba su dace da
al’adunmu ko yanayinmu ko addininmu ba (Zaruk, da wasu (2001). Akwai suturun maƙwabtanmu
na kusa da na nesa waɗanda
suka yi tasiri akan Hausawa. Daga cikinsu akwai tazarce, da agbada, da ashoke.
Mata ma ba a bar su a baya ba, wajen sabuwar bakin tufafi, domin su ma sun samu
tufafi iri-iri wadanda suka hada da: Sitella, Short play, Play, Follow me gayu,
Baba na isa aure, Jahannama ga fasinja, Sa hannunka masoyi, Easy to rich, Fish,
Tazarce, Kerewa, In ka isa duba, Kai ka kula, da dai sauransu.
MAGUNGUNAN GARGAJIYA NA BAHAUSHE
Maganin gargajiya shi ne yin amfani da itatuwa ko rubutu ko
addu’a ko surkulle, don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da
sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata. Wannan sana’a ta magani ta bunƙasa a ƙasar Hausa, don haka ma da wuya a sami
gari ko ƙauye
wanda ba mai magani a cikinsa. Waɗanda
suka fi shahara da wannan sana’a su ne malamai da bokaye.
Maganin gargajiya sana’a ce mai amfani don haka wasu sukan
yanke mata saƙa, kamar bokaye da ‘yar
maiganye, da ungozoma, da maharba, da malamai tsabibai. Wani lokaci, likitocin
zamani ma sukan nemi taimakon waɗannan
masu magani na gargajiya. Magungunan da suke yi kuma suna da yawa. Ga bayanin
wasu daga cikinsu.
Tsimi: Maganin da ake haɗa
itatuwa ko kaucinsu musamman ko a yi garinsu ko sassaken jikinsu, ko a tsima
su, ko a dafa su, a yi maganin cututtuka iri-iri da su kamar maganin ‘yar
maiganye.
Sassaƙe-Sassaƙe: Maganin da ake shiryawa don maganin shawara, da daji, da
maganin dafi, da na hauka, da na tauri, da na hangun, da na ciwon hakori
(haure), da ɗan
kakkarai, da ciwon mata, kamar mele, da tunjere, ko ɗan birni, da ciwon bututu, da cirar gashi, da
tunjiɓini, da
tantanau, da gumurdu, da tottojiɓo,
da sauransu.
Turare: Maganin da ake turarawa, wanda ake haɗi da wasu itatuwa da
hakukuwa, ko tsumma, ko gashi, ko sansami. Kuma ana yin turare don maganin
fitar da maciji daga kogo, ko daga gida ko daga rami. Kuma da irinsa ake
maganin hana maciji cizo, ko kunama ko munu-munu, da kamun namun daji. Kuma da
irinsa ake kau da miyagu, da sauran irinsu.
Kulle-Kulle da Tofe-Tofe: Maganin da ake yi da ƙulleƙkulle
da tofe-tofe, da zare ko da tsirkiya, ko da jijiya, ko da gashi ko da ɓawon itace, da rataya su ga
wuya, ko a kafaɗa.
Kuma akan yi ƙulle-ƙulle da tofe-tofe a kafa a cikin gona, ko a gida, ko a ɗaki, ko a kasuwa, ko a yi ɗaurin ruwa, ko daji, ko ma
mazakuta, ko wanin waɗannan.
Tofawa da Shafawa: Maganin da ake haɗawa da tambaya da tofi da shafe-shafe, kamar
maganin dori, ko ciwon kai, ko maganin haƙarƙari ko ta-ƙauye ko faɗuwar
zuciya ko haƙora
ko ƙarangashewar
wani abu ga wuya ko ma ciwon farfaɗiya.
Gashi: Maganin da ake yi da wuta ko da ƙarfe
ko da ƙasa,
kamar lalas, da ruwaye, da ƙyasƙyastu ko sakiya ko tuwon ƙasa ko kamun ta-ƙauye, da haƙarkari,
ko kafi.
Jiƙe-Jiƙe: Maganin haihuwa kamar maganin zaƙi ko faɗuwar uwa da saukin gwiwa da
na ƙarfin
jiki da na jini da maganin jinjiri saboda lafiyarsa.
Bayan haka ana yin magani gama-gari tahanyar jiƙe-jiƙe.
Misali ana jiƙa toka don ɗankanoma
da ɓacin ciki, Ana jiƙa
kanwa, ko filasko, don ciwon ciki da wanke ciki. Kuma ana jiƙa maɗaci, da tsamiya, da lemun
tsami da kayan yaji, don ƙarin mazakuta da maye, ko don ƙarin matuntaka da maganin ƙazuwa
da ‘yan rani da kirci
da ciwon hangun da sauransu.
Jifa: Maganin ɓata
wa wani rayuwarsa don son ran wani, kamar magani don a fitar da kishiya, ko don
a naƙasar
da wani, ko a karɓe
amfanin gonar wani, ko a ɓata
sarauta, ko ciniki, duka ta hanyar mugun dabo.
Ajiya da Rataya: Maganin tsaraka kamar sa fure a cikin nono
ko dawo don samun kasuwa ko a maƙala wani abu, don neman farin jini ko
bashi, ko bi-ta-zai-zai, ko gamaɗiɗi, ko ƙifit.
Siddabaru: Maganin siddabaru kamar maganin maita da ɗaukar abu mai nauyi da cika
soro, da taɓo rufin
shigifa da ƙafa,
da rikiɗa kura ko mage
ko maciji ko taiki, ko barin hannu, ko ɗora
hannun da ya karye kamar wajen wasan kwaraya.
Shashatau: Maganin shashatau, kamar ɓatar da abin noman wani, da mayar da mutum
biri, da ɓatar da kan
jinjiri, ko mazakuta; ko wanin waɗannan.
SANA’A DA MUHIMMANCINTA A WURIN BAHAUSHE
Sana’a, kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take ɗaukar ma’ana ta samar da
wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance. Misali, sana’ar ƙira .
A gargajiyance, Bahaushe yana da sana’o’in da yawansu ke da
wahalar ƙididdigewa.
Daga cikin irin waɗannan
sana’o’i akwai manya akwai kuma ƙanana. Sannan kuma masana sun kasa su
zuwa kashi uku da suka haɗa
da sana’o’in maza, sana’o’in mata da kuma sana’o’in haɗaka ko gamayya.
Sana’o’in Maza
Sana’o’in maza su ne sana’o’in da maza zalla ne suka fi
yinsu. Koda an samu mata a ciki to yawansu bai kai a misalta ba. Misali,
sana’ar ƙira,
fawa , da sauransu.
Sana’o’in Mata
Sana’o’in mata kuma su ne sana’o’in da mata ne kawai suka keɓanta da yin su. Idan aka ga
namiji a ciki irin waɗannan
sana’o’i akan kira shi da ɗan’daudu.
Daga cikin irin waɗannan
sana’o’i akwai sana’ar kitso , dafe-dafen abinci, da sauransu.
Sana’o’in Tarayya
Sana’o’in tarayya kuma su ne sana’o’in da maza da mata suka
yi tarayya a ciki. Daga cikin irin waɗannan
sana’o’i akwai kiwo , roƙon baka da sauransu.
NAU’O’IN SANA’O’I A KASAR HAUSA
1. Sana’ar Wanzanci.
2. Sana’ar Kiwo.
3. Sana’ar Gini.
4. Sana’ar Dukanci.
5. Sana’ar Sussuka.
6. Sana’ar Fawa.
7. Sana’ar Noma
8. Sana’ar Sassaƙa.
9. Sana’ar Saƙa.
10. Sana’ar
Kitso.
11. Sana’ar
Ƙira
12. Sana’ar Jima.
13. Sana’ar Rini.
14. Sana’ar Ginin Tukwane.
15. Sana’ar Arkomanci.
16. Sana’ar Farauta.
17. Sana’ar Su.
BUKUKUWAN HAUSAWA
Biki taro ne da ake yi a Kasar Hausa domin taya juna, ko
wani, ko wasu murna wanda ake gudanar da shi a nishanɗance ta hanyar kaɗe-kaɗe,
raye-raye, waƙe-waƙe, tanɗe-tanɗe, da lashe-lashe. Kenan,
duk wani taro da ya haɗe
waɗannan abubuwa guda
huɗu ko wasu daga
ciki, to kai tsaye za a iya kiransa da biki.
2 Comments
Salam alaikum, muna godiya da wannan ilimi Allah ya saka da alheri amin, dan Allah ina da tambaya, tambayar nan:
ReplyDelete"Tare da hujjoji daga al'ummar Hausawa, a yi bayanin fa'idojin da illolin amfani da Ra'i (theory) a nazarin al'adun al'umma?"
Na gode, ina jiran amsa.
Sai kuma wannan tambayar:
ReplyDelete"Nazarin sauye-sauyen al'adun aure a al'ummar Hausawa?"
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.