Citation: Ibrahim, M.A. (2024). Nazarin Falsafa a Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Marigayi Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 189-200. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.024.
NAZARIN FALSAFA A
WASU ƊIYAN WAƘOƘIN MARIGAYI SA’IDU FARU
Maryam Abubakar Ibrahim
Hausa Department
FCT College of
Education Zuba-Abuja
Email: maryammashi2000@gmail.com
Tsakure
Nazarin Falsafa a waƙar baka na nufin zaƙulo wata hikima ta musamman wadda mawaƙi ya yi amfani da ita a cikin waƙoƙinsa. Kasancewar Falsafa wata taska ce matattara tataccen
tunani da hasashe ko tsinkaya wadda yawanci haziƙan mawaƙan Hausa kan yi amfani da ita domin nuna hikima da hangen
nesa a cikin waƙoƙinsu. Wannan takarda ta ƙunshi fito da falsafa kai tsaye daga cikin wasu waƙoƙin Malamin kiɗi
mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba wato makaɗa Sa’idu Faru. An bi hanyar tattara waƙoƙin tare da saurarensu ɗaya bayan ɗaya,
kana aka tace waɗanda suka ƙunshi irin kaifin tunanin mawaƙin (falsafa) daga ɗiyoyin
waƙoƙinsa, sannan kuma an tattauna da ma’abota sauraron waƙoƙinsa domin neman ƙarin bayani na wasu kalmomin cikin waƙoƙin. Wannan takarda an ɗora ta ne a kan Ra’in alfanun Sassan Al’umma wato (Functionalism
Theory) wanda ra’i ne da ya yi fice a wajen nazarin al’adu da adabin al’umma
wanda fitaccen masanin nan mai suna Charls Darwin (1809-1882) ya samar, wanda
ya yi aikin sa a kan alfanun sassan Halittu masu rai a fannin dabbobi. Daga
baya aka samu wasu Turawa masana tsarin zamantakewar al’umma suka goya wa
Charles Darwin (1809-1882) baya. Su waɗannan Turawa kamar yadda Ado (2022) ya bayyana sun yarda da
cewa kowace al’umma tana da sassa daban-daban, kuma kowane sashe yana taimakawa
wajen ginuwar a’lumma. Daga cikin waɗannan
magoya baya na Charles sun haɗa
da; Emile Durkhein (1858-1917) da Herber Spencer (1820-1903)
da Weber (1864-1920) da sauransu. Hausawa al’umma ce cikakkiya kamar kowace
al’umma ta Duniya da take da nata tsarin na falsafa da sha’anin zamantakewa,
kuma Hausawa suna da sassa daban-daban ɗaya daga ciki su ne mawaƙan baka waɗanda
suke tamkar ginshiƙi a
cikin adabin al’ummarsu. Da wannan ɗan
bayani ne ake ganin dacewar wannan bincike da wannan ra’i. Bugu da ƙari wannan takarda ta ƙunshi muhimman misalai na ɗimbin falsafar da ke cushe a cikin waƙoƙin makaɗa
Sa’idu Faru tare da cikakken sharhi da bayanan da suka sawaƙa.
1.0 Gabatarwa
Falsafa hanya ce
ta ƙoƙarin zurfafa tunani a kan bincike tare da nazarin dukkan
abin da yake kai komo a sararin Subhana tare da hikimar bayinsa ta yadda za su
tace tunaninsu wajen samun sakamakon manufarsu ta rayuwa gaba ɗaya. Su kuwa waƙoƙi wasu ginshiƙai ne na tace
hikimomi da sarrafa su ta hanyar sussuka adabi da fece shi domin adana al’adun al’umma. Lura da hakan
ne ya sa wannan aiki ya zaɓi ya yi nitso
cikin waƙoƙin mafalsafi
malamin kiɗi mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba wato makaɗa Sa’idu Faru domin zaƙulo irin falsafar da yake cusawa cikin waƙoƙinsa wadda ta
danganci tsinkaya da hasashe da hangen nesa da abin da ya shafi yabo da zuga da
kirari ga shi kansa mawaƙin ko kuma ga
iyayen gidansa. Kana wannan aiki zai kalli falsafar zamantakewar rayuwa wadda
ta danganci maƙwabtaka da abokan
sana’a da sauransu. A wannan aiki an yi ƙoƙarin fito da
misalan falsafa daga mabambantan ɗiyoyin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru tare da ingantaccen sharhi.
2.0 Ra’i
Wannan aikin an ɗora shi ne a kan Ra’in Alfanun Sassan Al’umma (Functionalism
Theory). Ra’i ne da ya yi fice a wajen nazarin al’adu da adabin al’umma. Wannan ra’i fitaccen masanin nan mai
suna Charls Darwin (1809-1882) ya samar da shi, da farko wannan masani ya yi aikinsa a kan alfanun sassan
halittu masu rai a fannin dabbobi. Daga baya an samu wasu
Turawa masana tsarin zamantakewar al’umma suka goya wa Charls Darwin, su waɗannan Turawa kamar yadda Ado (2022) bayyana sun yarda da
cewa kowane sashe yana taimakawa wajen ginuwar ai’umma.Wasu daga cikin waɗannan mabiya na charls sun haɗa da; Emile Durkheim (1858-1917) da Herber Spencer (1820-1903)
da Maweber (1864-1920) da makamantansu (Otile,1981:2, Mahuta,2000:61, Mashi 2015:28).
Kasancewar wannan ra’i yana magana a kan al’umma a matsayin dunƙulalliyar abu guda ɗaya.To amma a cikinta ta rarraba zuwa sassa ko ɓangarori daban-daban, waɗanda suke jingine da juna, kuma kowane sashe yana da alfanunsa
a cikin al’ummar da suke (Bello, 2016:22, Ado, 2019:38) Bisa madosar wannan
ra’i na kowane sashe yana da muhimmanci a cikin al’umma, domin sassan sukan yi
cuɗanya da juna ta yadda idan babu wani
sashe to ita al’ummar ma ba za ta iya wanzuwa ba a matsayin dunƙulalliya kuma cikakkiyar al’umma ba.
Duba da bayanan da suka gabata kan wannan ra’i da masana
suka zayyana, za a ga cewa ra’i ne da yake fayyace irin gudummuwar da kowane
sashe na al’umma yake bayarwa gwargwadon iyawarsa. Hausawa al’umma ce cikakkiya
kamar kowace al’umma ta duniya da take da nata tsarin na falsafa da
zamantakewa. Sannan al’ummar Hausawa suna da sassa daban- daban, ɗaya daga ciki su ne mawaƙan baka waɗanda su ke tamkar gishiri a cikin adabin al’ummar
Hausawa. Mawaƙa mafalsafa ne wajen bijiro da
tunaninsu da cusa shi cikin waƙoƙin da suke aiwatarwa.
2.1 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
Dangane da Tarihin Malamin kiɗi Sa’idu Faru kuwa, Gusau (1996:117), ya bayyana mana
cewar an haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, Ƙaramar Hukumar Talatar-Mafara a wajajen
shekara ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da “Ɗan’umma” wanda matar ƙanen ubansa ta sanya masa, saboda ba ya
faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma.
Shi
ya sa ita kuma ta dinga kiran sa da Ɗan’umma, amma wannan laƙabi bai shahara a
tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka watau Sa’idu. Shi da kansa
Sa’idu Faru yakan yi wa kansa kirari yana cewa:
Ɗan’umma Rungumi
Ɗantumba Rungumi
Sunan mahaifin
Sa’idu Faru shi ne Makaɗa Abubakar Ɗan’alu, shi kuwa Makaɗa Abdu; Alu Maikurya ya haife shi. Ashe kenan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar ɗan Abdu ɗan Alu Maikurya. Dukkan waɗannan makaɗa an yi su ne a garin
Faru. Sai dai mahaifiyar Sa’idu mutuniyar
Banga ta cikin ƙasar Ƙauran-Namoda ce,
kuma a can ne aka haife ta.
Sa’idu Faru kamar
sauran makaɗan fada, ya yi gadon kiɗa ta wajen
mahaifinsa. Kakansa na sama Makaɗa Alu makaɗin kurya ta kiɗin yaƙi ne wadda ake yi
wa kirari “kurya gangar mutuwa”. Makaɗa Alu ya yi waƙoƙi da yawa a
zamanin yaƙi, sai dai ba za a
iya kawo su a yanzu ba saboda tsawon lokaci.
Yawancin ƙuruciyarsa ya yi ta a garin banga ta Ƙauran-Namoda inda aka haifi uwarsa,
amma kafin ya girma ƙwarai sai ya koma wurin tsohonsa makaɗa Abubakar Faru. Makaɗa Sa’idu bai sami ilimim Muhammadiyya da yawa ba, sai dai
an sa shi makarantar allo inda ya yi zurfi ga karatun Alƙur’ani Maitsarki. Haka kuma ba a sa
shi makarantar boko ba, domin haka bai san komai ba game da sha’anin boko.
Alalhaƙiƙa, tun yana yaro
sha’anin kiɗa da waƙa ya ɗauke masa hankali. Za mu ga tasirin iliminsa na Muhammadiyya
a cikin waƙarsa wadda ya yi
wa Alhaji Amadu Sarkin Kiyawa na Ƙauran-Namoda mai amshi kamar haka:
G/waƙa: Gwauran giwa
jirayi gaba na Amadu,
Inda yake cewa: Da
ku masu bakandama,
Jagora: Da ku masu
jalalaini,
Ku tabbata malam
Sa’idu ya iya ishiriniya,
Ni mai ishiriniya ta waƙa,
Mamman kanen gyaɗa mai kwana kiɗi.
Y/amshi: Domin dai
in ana ba ni,
Ba gajiya ni kai
ba,
Rantsan turu ni
kai,
Hat turu ya fashe,
Mu ja attahiyatu az-zakiyatu mu sallame,
Mu ɗauko tabayyada abilahabi wa tabba ma,
Mu jawo wasshamsu
wal duhaha,
Waƙa yanzu ta ɗore,
Sai tai wata guda sai
zwaƙi ta akai,
Cakwai zad daɗin bugu.
Daga misalin wannan ɗiyan waƙa za a tabbatar da lallai malamin ba na
kiɗa ba ne kawai har ma da na karatun
addini, domin dai ga shaida nan ya faɗi da bakinsa ya iya ishiriniya kana ya
yanko tahiya da wasu ayoyin Alƙur’ani Maigirma. Ya kuma nuna mana
muhimmancin yin hakan, domin idan har ya karanta waɗannan ayoyi, to zai iya yin wata yana kiɗi bai gaji ba, kuma
shima kiɗin da waƙar za su daɗa zwaƙi cakwai. Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna
mana shi mai tauhidi ne da bin ƙa’idojin Addininsa. Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu
a shekara ta 1987, Allah Ya
gafarta masa.
3.0 Falsafa
Kalmar falsafa
kalma ce mai nisan zango domin kamar yadda Ƙamusun Englishi na Advanced Learner Ditionary, ya kawo mana
bayanin cewa, falsafa kalma ce da aka samo daga Girkawa wadda suke amfani da
ita a matsayin kalmomi biyu wato philia (so) da kuma Sophia (nazari). Ma’ana
son yin tunani ko son nazarin rayuwa. To amma daga baya sai mafalsafa suka haɗa waɗannan kalmomi biyu
zuwa kalma ɗaya mai cin gashin
kanta mai ma’anar “Ilimin sanin duniya da abin da ke cikinta”. Haɗa kalmomin ya sa
an sauya mata suna zuwa Philosophy
maimakon Philosophia. Amma akwai
mabambanta ra’ayoyi game da ma’anar (falsafa) kasancewar masanan suna da dama
kuma kowa da yadda ya ɗauke ta, kowa ma’anar da ya ba ta daban da ta ɗan’uwansa, duk da kasancewar akwai dangantaka a tsakaninsu.
Ƙamusun
Encyclopedia Britannica, ya bayyana mana cewa ana jin wanda ya fara amfani da
wannan kalma shi ne Socretes sai kuma magoya bayansa,
daga nan sai Philato da Aristotle waɗanda suka faɗaɗa kalmar. A halin yanzu wannan kalma ana danganta ta da ilimi mai zurfi na hanyoyi daban-daban.
3.1 Falsafa a Turai
Bayanai da dama sun gabata a kan asali da tushen falsafa,
amma mafi ingancin zance shi ne kalma ce ta Girkawa su ma kuma Girkawa sun samo
ta ne daga Latin, a inda su kuma Turawa suka ɗauko daga Girkawa kana Larabawa suka ɗauko daga Turawa su kuma Hausawa suka ɗauko daga Larabawa. Kuma duka waɗannan ɓangarori sun rarrabu dangane da yadda
suka ɗauki kalmar falsafa da kuma yadda suke
kallon ta da yadda suke amfani da ita a cikin hulɗoɗinsu na yau da kulum. Mun ga yadda
Girkawa suka ɗauki kalmar kuma suka ba ta ma’anar
ilimin sanin duniya da abin da ta ƙunsa. Amma a wajen
Turawa, a cikin wani littafi na Bram L.L (ed) mai suna Funks and Wagnalls New Encyclopedia; ya bayyana sunayen waɗansu mafalsafa da kuma irin ra’ayoyinsu game
da ma’anar kalmar falsafa.
Thales, wannan
bawan Allah malami ne na falsafa kuma ya nuna cewa “Dukkan wani abu in dai
halittacce ne to yana da falsafa inda ya yi misali da ruwa. Ya ce ruwa yakan
daskare ya zama ƙanƙara, a yayin da
ita ƙanƙara idan ta ji
zafi takan narke har ma ta zama zazzafan ruwa tana turiri. Ya ci gaba da cewa
“to idan kuwa har za a tsaya a nemi dalilin da ya sa sanyin nan ya zama zafi,
to sai an haɗa da tunani irin
na mafalsafa”.
Anaximander; shi ma malamin falsafa ne, ya kuma bayyana kalmar da cewa “Tunani ne a aiwace ta yadda wani abu kan zama
wani abu, da kuma yadda yanayi kan sauya wani abu”. Ya yi misali da zafi da
sanyi da rana da iska da kuma wuta, ta yadda waɗannan abubuwa ke sauyawa lokaci-lokaci. Pythagorean, shi ma
malamin falsafa da lissafi ne, kuma a nasa ra’ayin ya bayyana falsafa da cewa, “Wani mataki ne da ya haɗa da hangen nesa da halitta da lissafi da kuma yarda da
camfe-camfe. Haka kuma ya ba da misali da fatar jikin mutum wadda ya ce kamar
garkuwa ce ga gangar jikin mutum wadda ba ta rabuwa da mai ita har mutuwa.
Kamar yadda ake danganta lissafi da kimiyya, alhali kowane da irin tasa
falsafa”.
Eleatic, shi kuma
a gurinsa duk wani mafalsafi ɗan duba ne, “Domin
wai yakan yi wani abu wanda sai an daɗe sannan a ga abin
ya tabbata”.
Atomists, shi kuma
a nashi ra’ayin ya kalli falsafa da cewa “Tunani ne na aikace-aikace ta yadda
za a zayyana wani abu a ba shi saffa da kama, sannan kuma ya ƙayatar ta hanya
mafi kyau. Har ya gangaro kan bayani ga rayuwar tsirrai da dabbobi, da
bil’adama”. Ya yi bayanin ta yadda mutum zai iya amfani da ƙwaƙwalwa a kan
fannonin ilimi addini, siyasa da kuma duk wata hanya ta shari’a.
Sophists, a tasa
manufar yana ganin falsafa ba ta da wata tsayayyar manufa illa dai kawai ɗabi’u da halayyar mafalsafi ta hanyar tunani don cimma biyan
buƙata. Kaɗan kenan daga cikin mabambantan ra’ayoyin manazarta falsafa
daga nahiyar Turai.
3.2 Falsafa a Wajen Larabawa
Su ma Larabawa
asalin kalmar ba ta su ba ce, sun samo ta ne
daga Turawa a wani ƙaulin kuma an nuna
cewa sun samo ta ne daga Girkawa. Bayan Larabawa sun samo wannan kalma sai suka
riƙa kiran ta da
(falsafa) ko kuma “Ilmul Hikma” wato ilimin hikima da fasaha dangane da bunƙasar duk wani abu
da ya shafi rayuwa gaba ɗayanta har zuwa
mutuwa.
Tarihi ya nuna
cewa Larabawa sun fara amfani da wannan kalma tun lokacin daular Abbas, kuma
suka riƙi irin ra’ayoyin
Plato, wanda ke nuna ra’ayinsa na naƙaltar halittu da cewa duk wani abu da muke gani na duniyar
nan tamkar na’ura ce domin ai yadda mutum zai tsayu
a wuri ɗaya to rayuwasa ma
nan za ta tsaya har sai ya juya ita ma ta juya. To amma daga bisani malaman da
suka bi ra’ayin Aristotle, sun bunƙasa ilimi na
fannoni daban-daban inda suka kasa ilimi zuwa gida biyu na ɓangaren tunani da kuma ɓangaren da ya
shafi kimiyya. Don haka, sai wannan ɓangaren da ya
shafi tunani ya karkata zuwa wasu manyan fannoni irin su:
a. Manɗiki: Ilimin tsarin
ma’anar magana
b. Dangogin hankali: Wanda ya shafi aiki
cikin nutsuwa da kuma bincike cikin hankali.
c. Ƙa’idojin aikin falsafa: Wanda ya shafi ƙere-ƙere da
zayyane-zayyane da mayar da wani abu cikin sura mafi inganci da kuma ƙayatarwa.
d. Duba: Wato bincike don sanin abin da
zai sami wani ko wata ko kuma al’umma baki ɗaya na gaba.
Bayan Addinin
Musulunci ya wanzu a ƙasashen Larabawa,
kuma ya shiga zukatansu sosai da sosai, sai su kansu mafalsafa Musulmi suka
kasu gida biyu game da ra’ayoyin su Plato wanda ya shafi sha’anin Ubangiji da
kuma waɗanda suka shafi
halittu. Mafalsafi mai suna Imamu Gazali, a cikin littafinsa mai suna
‘Tafahatul falsafa’ ya mayar wa su Aristotle da Plato martani, inda har
ya kafirta su dangane da wannan ra’ayi na sha’anin Ubangiji. Haka kuma da inda
suka ce wai mutum shi ya yi kansa. Kuma zai iya yin komai da kansa ba tare da
Allah Ya isar da ikonsa a kan shi mutum ɗin ba. A nan ma
Imam Gazali ya ce sun kafirta. Haka kuma inda suka ce wai hankalin mutum zai
iya sa ya gane komai ba tare da wani Annabi ba. To a nan ma duk ya ce sun
kafirta. Ya jaddada Tauhidin Ubangiji ga masu iƙirarin wai sun san
abin da zai auku nan gaba, ai babu wanda ya san gaibu sai Allah, kuma sai wanda
ya so ne yake ba hikima ta irin wannan hasashe kamar na falsafa.
Ibnu Rushdi, shi
ma shahararren mafalsafi ne kuma ya yi ƙoƙarin yin sasanci
tsakanin malaman falsafa da na Larabawa Musulmai, domin a cikin wani littafinsa
mai suna ‘Tahafatul Tahafut’ ya yi bayani sosai inda ya kare malaman falsafa
irin su Alfarabi da Ibn Sina ya kuma ƙwaci shi Aristotle daga
kafirta shin da Imamu Gazali ya yi, a inda ya ce wai komai na duniya kamar wani
keke ne a inda yake juya kanshi. A nan sai Ibn Rushdi ya ce “Ai keken sai da ikon Alah yake kewayawa.” Haka kuma ya ci gaba da cewa
zatin Allah ya shafi komai da komai na dangin halitta domin halitta na da
martabobi har ya yi misali da halittar mutum da tunaninsa na mai da katako ya zama kujera. Ibn Rushdi ya yi wannan ne don ƙoƙarin kare
Aristotle daga kafirta shi da Imamu Gazali ya yi.
Su ma Larabawa an
samu malaman falsafa da dama daga cikinsu, kamar su Alfarabi da Ibn Sina da
Abubakar Muhammad bin Yahaya da Abubakar Muhammad bin Abdulmalik ibn Tonhail
Alkais da sauransu.
3.3 Falsafa a Ƙasar Hausa
A ƙasar Hausa zai yi
wuya a yanke hukunci a kan asalin tsantsar falsafa ko da za a samu wani abu a
kanta to ba zai kai na sauran al’ummomin ba kamar Turawa da Larabawa, waɗanda su sun riga sun yi zurfi a wajen ilimin karatu da
rubutu wanda ya sa aka sami manyan malamai daga cikinsu waɗanda suka naƙalci wannan fanni
na falsafa kuma har ma mafi yawancinsu sun yi rubuce-rubuce da dama a kan
falsafa. Kasancewar rubutun boko baƙon abu ne ga al’ummar Afirka, wannan ya sa Hausawa sun fi ƙarfi a kan Adabin baka. Duk da kasancewar rubutu baƙon abu ne, wannan
ba zai hana ace Bahaushe ba ya da falsafa ba, tun da da yawa daga zantuttukansa cike suke da hikima da basira. Haka kuma idan muka lura da yadda Aristotle da Plato da Ibn
Sina suka bayyana kalmar falsafa, za mu ga ya yi daidai da
yadda Bahaushe ya ɗauki matsayin
tsokaci da tunani da hasashe da kuma hangen nesa a cikin zantuttukan da suka
shafi rayuwar ɗan Adam ta yau da
kullum, musamman kamar zantukan waɗanda suka shafi
Addini ko Aƙida ko Siyasa.
A cikin al’ummar
Hausawa idan mutumin kirki ne ko mai ilimi ana ɗaukar maganarsa da muhimmanci, har ma ka ji ana cewa “Ai da
ma malam wane ya faɗa”. Ko kuma duk
abin da malam wane ya faɗi ga shi ya
tabbata. Kai idan ma muhibbar mutum ta yi gaba sai ka ji ana faɗin “malam wane waliyi ne”. domin yadda Bahaushe ya ɗauka, duk waliyyi, ya san abin da ba zai faru nan gaba.
Wannan na ɗaya daga cikin
abin da ya sa ake girmama su. Misali, a wata
waƙa mai suna “Zuwan Annasara” wadda Sarkin Musulmi Attahiru ya yi a
baiti na takwas; inda yake cewa:
Batu
na Shaihu yay yi shi ba shi tashi,
Ƙasag ga tana zama
mulkin Nasara.
Hausawa sun ɗauki Shehu Ɗanfodiyo da girma ƙwarai domin wasu ma na cewa shi waliyyi
ne, don haka duk abin da ya faɗi gaskiya ne, kuma zai tabbata. Don
haka a nan Sarkin Musulmi Attahiru Amadu ya ƙara nuna mana yadda Shehu Danfodiyo ya
taɓa faɗin cewa “Ƙasar Hausa za ta koma ƙarƙashin mulkin Nasara”. To ga shi kuwa ya tabbata, wannan ya nuna mana akwai mafalsafa a ƙasar Hausa. Bayan
waɗannan an samu
falsafa a zantuttukan manyan malamai na ƙasar Hausa. Haka kuma an samu falsafa a zantuttukan manyan Arewa irin su
Abubakar Tafawa Ɓalewa da Sir Ahmadu Bello Sardauna da Malam Aminu Kano da
Abubakar Imam da Sa’adu Zungur da Maitama Sule Ɗanmasanin Kano da dai sauransu.
4.0 Falsafa a Waƙar Baka
Waƙar baka ta Hausa
abu ce mai daɗaɗɗen tarihi, wadda aka faro tun lokaci mai nisan gaske. Masana
da manazarta da dama sun bayyana fahimtar su game da ma’anar waƙar baka kamar
haka: Ɗangambo (1982) ya
ce, “Waƙa furuci (lafazi
ko saƙo) ne cikin azanci
da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin
amfani da dabara ko salon armashi”. Shi kuwa Yahaya (1984:2) yana ganin, “Waƙa maganar hikima
ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba, wadda ke ɗauke da wani salo
da ke ƙunshe cikin wasu
kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”. Amma a ra’ayin Gusau (2008:187)
cewa ya yi, “Waƙa tana zuwa ne a
sigar gunduwowin zantuka waɗanda ake kira ɗiya kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman”.
Ita kuma falsafa
wani tataccen tunani ne kimtsattse kuma taƙaitacce, mai zurfi mai yalwa ga ma’ana, mai koyar da
hikimomin rayuwa gaba ɗaya. Saboda haka,
ita falsafa tana bayyana yadda abubuwa suke a tsarin rayuwa da fasalin aukuwar
al’amura da dalilin faruwarsu ga al’umma (Gusau, 2008:462). Duba ga ma’anar da
masana suka ba waƙa da cewa, “Lafazi, furuci ne cikin azanci”, da kuma “maganar hikima ce mai ɗauke da saƙo cikin zaɓaɓɓu kuma tsararru,
zaunannun kalmomi”. Da waɗannan siffofi da
aka danganta da waƙa za a gane cewa
lallai waƙar baka na ɗaya daga cikin tubalan ginin zuzzurfan tunanin al’umma wanda
kuma shi ne (falsafa). Don haka kenan falsafa a waƙoƙin baka ta zama
tamkar wani ginshiƙi majingina tsanin
hawan ko wane fasihin mawaƙi domin nuna
hikima da falsafarsa da gwanancewa wajen ƙulla zaren waƙoƙinsa. To amma fa
ba kowane mawaƙi ne mai falsafa
ba, sai mai amfani da hikima wajen tace tunaninsa da amfani da hasashe da hange
da tsinkaye a cikin zantuttukan waƙoƙinsa. A ƙasar Hausa muna da
mafalsafa mawaƙa da dama, irin su, Ibrahim Narambaɗa da Sa’idu Faru da
Makaɗa Maidaji da Sabon
Birni da Mamman Shata da Musa Ɗanƙwairo da Aliyu Ɗandawo da
sauransu. Ga misalan Falsafa a waƙoƙin baka kamar
haka: Alhaji Mamman Shata; waƙar da ya yi wa
Sarkin Zazzau mai amshi: (Alhaji Sarkin Zazzau Shehu)
Inda yake cewa: Na ce maku za shi zame sarki,
Kuka ce zancen giya ne na yi,
To ga zancen giyar nan ya zama,
Daidai da na Malaman birnin Zazzau.
Yawanci a al’ummar Hausawa musamman ga
mutanen da suka kwankwaɗi malunta, suna kallon mawaƙa mashiririta ne, don haka ba su cika ɗaukar maganarsu da muhimmanci ba. A lokacin da Shata
ya yi wannan zancen a cikin waƙa kowa ya ɗauka irin fadancin nan ne na mawaƙa. To, sai ga shi kuma bayan an daɗe zancen ya tabbata, jin daɗin hakan ya sa Shata ke kwatanta zancen nashi da irin na
malaman birnin Zazzau, kasancewar Zariya garin ilimi kuma mai shaƙare da malamai na kowane fanni. Daɗin daɗawa kuma Hausawa
na girmama malamansu ba sa wasa da dukkan furucin da ya fito daga bakunansu.
Haka za a ga kwatankwacin wannan misalin a waƙar makaɗa Ibrahim Narambaɗa a cikin waƙar da ya yi wa
Sardaunan Isa Abdullahi, mai amshi kamar haka:
G/waƙa: Na riƙa ka da girma,
Abdu ƙanen mai daga,
Kan da mu san kowa,
Kai munka sani
Sardauna.
A ɗiyan da ya ke cewa:
Jagora: Shigihwa in babu azara,
Kuma babu gimshiƙi,
Kai ka san sai ta tuɗe,
Mi aƙ ƙarhin shigihwa ba
su ba,
Ai ko da dai ɗan bajimi,
Shi ka zama bajimi,
Yai boboƙali yai to zo,
Ɗan akuya na kallo,
Manyan maza uban
Sule,
Na dubi gaskiya,
Hasken rana da
wata ba ɗai ba.
Duk da kasancewar yawancin ɗiyoyin waƙoƙin Narambaɗa sun fi kama da habaici ko zambo,
to amma idan aka ɗora wannan ƙauli da ya yi a
bisa faifan falsafa, zai zauna daram. Domin dai a nan yana nuna cewa duk
mutumin da ba shi da madogara to kuwa faɗuwa yake, domin
dai in kuna da majingina ko ya take, ya fi zama haka nan. Haka kuma duk ɗan Sarki shi ke zama Sarki, ɗan hakimi kuwa sai dai kurin shi ɗan sarauta ne, shi kuwa ɗan talaka sai dai kallo. Haka ma da mai akwai da wanda ba
shi da komai matsayinsu ba ɗaya ba ne, kamar
yadda ba za a taɓa haɗa hasken rana da na wata ba. Wannan waƙa cike take da
azanci da naƙaltar harshen mawaƙin, tare da
hasashe da gwaninta wajen ƙulla zaren waƙoƙinsa wanda shi ne
falsafa.
Daɗin daɗawa, za mu ƙara ganin wani
misalin a waƙar makaɗa Salihu Jankiɗi wadda ya yi wa
Ahmadu Sardauna, inda yake cewa:
G/waƙa: Alhaji Amadu
Sardauna
Girmanka ya yi babba riƙa
Jagora: kai as sinadarin ‘yan sarki
Mutan Kudu ka taushe
muna su
Komi sai ka yarda a yi.
Wannan batu kam haka yake domin kuwa tun lokacin Amadu
Sardauna har yanzu mutanen Arewa sama suke sun taushe mutanen Kudu ta ɓangaren mulki. Akwai misalai da dama na falsafa a waƙoƙin baka daga cikin
ɗiyoyin waƙoƙin mawaƙanmu mafalsafa,
irin su (Dr.) Adamu Ɗanmaraya Jos da
Shehu Ajilo da Aminu Ladan (Ala) da Nazeeru Ahmad da Malam Yahaya Makaho da dai
sauransu.
4.1 Falsafa a Waƙoƙin Sarauta
Kamar yadda Ɗangambo (1984:44) ya rarrabe mana
azuzuwan makaɗan Hausa kashi-kashi, inda yake bayanin
cewa, “Waƙoƙin makaɗa sun kasu zuwa kashi-kashi, domin
akwai makaɗa iri daban-daban. Rabe-raben waƙoƙin ya shafi nau’o’in ko irin waƙoƙin jigogin waƙoƙin da kaɗe-kaɗen da irin mutanen da ake yin waƙoƙin dominsu. Daga cikin waɗannan kashe-kashe
akwai makaɗan Fada ko makaɗan Sarauta. To su ma waɗannan rukunin mawaƙan sun kasu gida biyu, domin daga cikinsu akwai makaɗan fada waɗanda suke yi wa
sarakuna da masu mulki waƙa da duk waɗanda suka shafi gidan sarauta da Hakimmai, Alƙalai da sauransu.
Kana akwai makaɗan sarauta waɗanda su kuma ba sa yi wa kowa waƙa sai ubangidansu
ko magajin shi wato ɗan shi ko jikan
shi, ko kuma waɗanda suka nemi
izini daga ubangidan nasu. Irin waɗannan makaɗa za ka iske su jingine da iyayen gidansu domin duk wata
hidimarsu da ta iyalansu wadda ta shafi ci da sha da sutura da muhalli duk suna
rataya ne a wajen wannan ubangida nasu, kuma su irin waɗannan makaɗa koda ubangidansu
ya mutu ba su cika canza sheƙa ba. Sukan zauna da iyalan ubangidansu su ci gaba da yi wa wanda
ya gaje shi kiɗi da waƙa. Haka shi ma ta ɓangaren makaɗin idan ya rasu,
yawanci ɗansa ko ƙanensa ko ɗaya daga cikin yaransa kan ci gaba daga inda ya tsaya.
Makaɗa Sa’idu Faru daga
cikin wannan rukuni ya fito, domin kamar yadda muka gani a tarihinsa ba ya yi wa wanda ba sarki ba waƙa, don haka ma
duka waƙoƙinsa na sarauta ne kuma makaɗin Sarkin Kudu ne wato Macciɗo. To amma abin da ya shafi falsafa a waƙoƙin sarauta yawancin makaɗan sarauta suna lura ne da wata halayya ko ɗabi’a ko yanayi na ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarki sai su yi amfani
da hikimarsu ta hasashe ko tsinkaye a cikin waƙarsu su nuna ai wannan yaro shi ne
magajin Baba kuma sai zancen ya tabbata bayan shekarun da suka shuɗe. Duk da yake akwai manazartan da suka ƙalubalanci irin wannan ƙaulin da cewa, “Kawai dai hikimar roƙo ce ko salo ne na maroƙa, suna iƙirarin wai ai ko mawaƙi bai faɗi ba dama duk ɗan sarki, magajin sarki ne”. Abin lura a nan
shi ne, me ya sa a cikin ‘ya’yan sarkin sai wanda suka ambata ne yake
sarautar? Misali a cikin waƙar Sani Aliyu Ɗandawo wadda ya yi wa Gwamnan farar hula na farko a Jihar
Sakkwato, Alhaji Shehu Kangiwa,
inda yake cewa:
G/waƙa: Bajimi na
Sarkin Kudu,
Gwamnan jahar Sakkwato,
Shehu Kangiwa mai niyyar riƙon gaskiya.
Jagora: Jikan Amadu uban Amadu,
Jikan Shehu mai gaskiya,
Duk wanda kas sani,
Ya yi halin Firimiya,
Bai kai Shehu Kangiwa ba.
Kudu gagaren maza,
Jikan Shehu Sarkin Kudu,
Dud radda kay yi sarki,
Kag gadi Bubakar,
Rannan duniya sabuwa,
Ka matsa magajin gida.
Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo ya nuna Gwamnan Jihar Sakkwato Shehu Kangiwa yana
da halin Firimiya wato Ahmadu Bello Sardauna. Amma a inda
falsafar take a nan shi ne, inda ya ambaci Sarkin Kudu Shehu kakan Gwamna Shehu Kangiwa
ya nuna duk ran da ya gaji “Bubakar rannan duniya sabuwa.” Sai ga shi kuwa zancen ya tabbata,
domin kuwa Shehu Sarkin Kudu kakan Shehu Kangiwa sai da ya gaji Sarkin Musulmi
na uku. Wannan kenan dangane da misalan yadda falsafa take cushe a
cikin waƙoƙin baka na sarauta
dangane da tsinkaye da hasashe da hangen nesa da mawaƙan kan yi su
aiwatar da waƙoƙinsu masu cike da
falsafa.
4.1.1Tsinkaya
Ƙamusu na Turanci
da Hausa (1982:60) da Ƙamusun Hausa na
Bargery (1993:1038), duka sun fassara mana kalmar ‘tsinkaya/tsinkaye’ da ‘tsammanin wani abu ko zaci
wani abu, ko sa rai wani abu’. Ko kuma ‘kallo ko tsammani ko jiran wani abu ko
tabbatar zuwan wani abu daga nesa’. Irin wannan ya zamewa mawaƙan baka ɗabi’a ta tsinkayo wani abu ko janyo nesa kusa ga iyayen
gidansu ko waɗanda suke yi wa waƙa. Kuma galibi
mawaƙan baka suna
amfani da tsinkaya ta sigar yabo ko hango abin alheri ko na ci gaba ga waɗanda suke yi wa waƙar. Za mu ga misalan tsainkaye daga waƙar (Dr.) Adamu Ɗanmaraya Jos,
wadda ya yi ta ‘Duniya’, mai amshi kamar haka:
Ke duniya ba ki san gwani ba,
Jagora: Sai ka taras yau kana da hali,
Sai ka taras gobe babu hali,
To duka Allah Ya tsara wannan.
Haka ma akwai wani misali a waƙar (Dr.) Mamman Shata wadda ya yi wa (Alhaji Maude
Tabaco) inda yake cewa:
Jagora: Dan Audu mutum mugun ice,
Shi za ka dasa sai ya girma,
Kuma yai inuwa ta lib-lib-lib,
Gun shan inuwa kai tawaye.
Idan aka lura da kyau duka waɗannan misalan waɗannan ɗiyan waƙoƙi, za a ga cewa
cike suke da falsafa irin ta tsinkaye, domin dai sun daɗa jaddada mana wata halayya ne ko ɗabi’a da ɗan Adam yake
rayuwa a cikinta kuma wadda za ta iya juyawa a kowane lokaci daga daɗi zuwa rashin daɗi, ko daga wani
yanayi na murna zuwa wani yanayi na baƙin ciki. Kamar yadda Ɗanmaraya ya fasalta yadda rayuwar duniya ke juyawa. Da kuma
yadda Shata ya fasalta halayyar mutum, ya kwatanta shi da mugun icce, da yadda
za ka yi masa dare, shi kuma ya yi maka rana. Wannan kenan dangane da yadda
mawaƙa kan yi amfani da
falsafa irin ta tsikaya/tsinkaye a cikin waƙoƙinsu.
4.1.2. Hasashe
Game da hasashe kuwa, Ƙamusun Harshen Hausa na Abubakar, A.T (2014:198), ya bayyana mana
ma’anar kalamar Hasashe da cewa; “Hasashe tsammani ne na yadda wani abu zai
auku ta hanyar yaɗa yiwuwar wani abu
da aka tuna da shi, don ya auku da can”. A nan, idan mun
lura, ana so ne a nuna mana, hasashe “Tsammani” ne ko hasasowa ne na wani abu da ake
sa ran afkuwarsa ko kuma ma ya taɓa faruwa, to ana
hasasho ko ganin ƙara faruwarsa nan
gaba, wato tsammanin koman nisan jifa, ƙasa za ta faɗo. Al’ummar
Huasawa mutane ne masu taƙawa da yaƙinin Ubangijinsu
zai iya yi musu komai a duk lokacin da ya so, don haka wannan ya ƙara wa hasashen ƙaimi na tabbatar
da Allah zai yi, kuma cikin ikonsa. Sai wannan hasashe na su ya tabbata. Kuma
irin wannan hasashe, shi ake kira da falsafar hasashe daga bakin mafalsafan
mawaƙa.
Akwai misalai da dama na falsafar hasashe a cikin ɗiyoyin waƙoƙin baka, kamar a
waƙar Makaɗa Sa’iduAngo Maidaji Sabon Birni.
Inda yake cewa:
Jagora: Marafa na gane duniya zamanin yanzu,
In zama yai daɗi mutane ka ɓata shi,
Tun da ban cuci mutum ba kar a cuta min,
Y/amshi: Idan mutum ya cuce ni, Allah Ya rama min,
Tun da na tsare Allah yana ko yi min komai,
Ƙi garaje uban buba
bai ɗauki wargi ba,
Dole in yaba malam Hassan mai halin girma.
Haka kuma za a ga wani misalin irin wannan na falsafar
hasashe, a cikin waƙar Alhaji Mamman
Shata wadda ya yi wa Sarkin Bakwai na Sabon Birni, inda yake cewa:
G/waƙa: Sarki Bakwai na
Sabon Birni,
Jagora: ‘Yan yara duniya rawar ‘yanmata,
Duk wadda tas shigo tat taka,
Da ta gama ta koma baya.
Waɗannan makaɗa sun yi amfani da
hasashe ne a cikin waɗannan ɗiya na waƙoƙinsu ga ma’anar
hasashe da muka gani a baya za mu gane makaɗa Sa’idu Maidaji ya hasasho wata halayya ta ɗan Adam, wadda duk
yadda ake da shi, wata rana sai ya kawo fitina, ko cuta. Kana kuma yana da yaƙinin duk wanda ya
cuce shi, Allah zai rama masa domin ko ya tsare Allah don haka tun da ko ya
dogara ga Allah yana da tabbacin zai yi masa komai. Wani abin lura a nan shi ne, Sa’idu Maidaji mawaƙi ne kuma waƙa yake amma ayar
Alƙur’ani ce nan ya
kawo mai fadin: “Duk wanda ya dogara ga Allah, Ya isar masa.”
Wannan misalai sun nuna mana cewar mawaƙanmu malamai ne,
kuma masu amfani da hikimominsu wajen amfani da tataccen tunaninsu, wanda ba
kowa zai iya yin haka ba sai mafalsafa.
4.1.3. Hangen-Nesa
Hangen-nesa shi ma kamar hasashe yake amma a cikin Ƙamusun Abubakar A.T
(2014:193) ya kawo ma’anar hangen-nesa da cewa “Hangen-nesa shi ne hanga/hange/hangi/hangawa/hangowa. Duba ga abin da yake
nesa, tunanin abin da zai auku nan gaba. Suna da hangen nesa su ga mai ya
kamata a yi. Daga wannan ma’ana za mu fahimci cewar duk mutum mai hangen nesa
zai zama mai kaifin tunani, ko wanda ya iya ƙulla zaren tunaninsa
na hango nesa me zai je-ya-zo, ko nan gaba wato lokaci mai zuwa abu kaza zai
faru, kuma sai wannan hangen nasa ya zama gaskiya. Duk mutum mai hangen-nesa a
cikin al’umma in dai zai furta kuma ko ɗan duba-duba ne,
domin yana hangowa yana faɗi kuma zancen sa yana tabbata. Akan samu irin waɗannan misalan na falsafar hangen-nesa daga cikin waƙoƙin mawaƙan baka. Misali, a waƙar Alhaji Mamman
Shata wadda ya yi wa Abba Sirsi-sirsi inda yake cewa:
G/Waƙa: Ɗan’alhajiya Abba Sirsi-sirsi,
Jagora: A bar shi haka nan dutchi,
Ka san mutum tara yake,
ba ya cika goma.
Haka ma a cikin wata waƙar wadda ya yi ta ramin mugunta, inda
yake cewa:
G/Waƙa: Ku garkaɗi mai gina ramin
mugunta,
Jagora: To kai mai gina ramin mugunta,
Sai ka gina daidai ƙwaurinka,
Don wata ƙila kai ka fada,
Ku gargaɗi mai gina ramin mugunta.
Duba ga misalan waɗannan ɗiyan waƙoƙi, mawaƙin ya yi amfani da tunaninsa na
hangen-nesa inda yake jan hankalin mutane da su bi junansu a hankali, domin duk
ɗan Adam ba shi cika goma, babu cikakke
sai Allah, amma mutum tara yake duk girmansa, duk ƙimarsa, da mulki ko sarauta tabbas sai
an same shi da naƙasu. A ɗaya ɗan waƙar kuma ya hango
wa mai gina ramin mugunta cewa ya gina ƙarami domin zai iya faɗawa. Wato duk wani
mai shirya mugun abu ga ɗan’uwansa to Allah zai iya tsallakar da wannan
da ake ƙulla wa, shi kuma mai shirya muguntar ya fada
ciki.
Kaɗan kenan dangane
da manyan turakun falsafa waɗanda ma’anarsu kan
cuɗanya wajen bayani
wato tsinkaye da hasashe da kuma hangen-nesa waɗanda dukkaninsu ake ɗora falsafa a
kansu.
4.1.4 Yabo da Zuga
Yabo da zuga su ma a wajen mawaƙa tamkar tubalai ne na gina waƙoƙinsu domin da su suke saye zukatan waɗanda suke yi wa waƙa. Domin mawaƙa sun gaji su yabi mutum ko su zuga shi ta yadda har zai
dinga jin babu tamkarsa, kuma da wannan siga ne suke samun ɗumbin alkhairi daga taskar iyayen gidansu ko jama’ar da
suke yi wa waƙa. To abin lura a nan shi ne, wane irin tunani suke? Ya suke tace tunaninsu
wajen zaɓen kalmomi da ƙarfafa harshensu,
hadi da zaƙaƙa muryoyinsu wajen
zaɓen kalmomin daɗaɗa domin yabo ko
zuga wanda suke wa waƙa? To irin wannan
shi ne falsafa domin sai sun tsinkayo sun Hasasho sun kuma hango kafin su furta don haka amfani da ƙwaƙwalwarsu wajen
tunaninsu na aiwatar da yabo da zuga a cikin harsunan waƙoƙinsu, aiki ne na
haziƙin mafalsafi,
domin kasancewarsa yana ɗauko wancan ya haɗa da wannan ya ta
da lafazi mai daɗi ga zuciyar wanda
ake yi wa kuma mai daɗi ga kunnuwan masu
sauraro, kana mai daɗi gare su su mawaƙan.
Bari mu dubi misalan wani yabo daga cikin waƙar Alhaji Musa Ɗanƙwairo wadda ya yi
wa Ahmadu Bello Sardauna. Inda yake cewa:
Bangon tama mai wuyar iza,
Bajimin sa Kashim uban zagi,
Bello ɗan Hassan mai martabar Ɗanhodiyo,
Mai martabar Abdullahi,
Mai martabar Moyi da Auta da Uwar Daje,
Mai martabar Isan Kware autan Shehu,
Mai martabar Ibrahimu mai ƙahon karo,
Sadauki ɗan Sadauki,
Kakanninka Waliyan Alla ne,
Ba ba’a ba ko can,
Ko lahira ma taulahinmu na nan,
Can wajen hannusa na dama.
Dubi yadda Ɗanƙwairo ya faro abin
tun daga tushe ya nuna cewa Shehu Usman Danfodiyo wanda ya jaddada Addini a ƙasar Hausa kakan
Sardauna ne. Haka kuma sauran ‘ya’yansa irin su Nana Uwar Daje da Autan Shehu waɗanda su ma sun taimaka ƙwarai wajen jaddada Addinin Musulunci, iyayensa ne. Daga nan
ya gangaro kan Sarkin Raɓah Ibrahim wanda shi ne mahaifin Sardauna.
Da ya gama lissafi a ƙarshe sai ya ce
dukkanin waɗannan kakanni nasa
waliyyan Allah ne. irin wannan yabo
muhimmi ne a wajen sarakuna domin an nuna cewa sun gaji Musulunci tun daga tushe ba da rana tsaka suka shige shi ba.
Dangane da zuga kuwa, a cewar Bunza
(2009:147) “Da kirari da zuga bori ɗaya suke yi wa tsafi. A kowane lokaci kirari ya haɗu sosai, ba a rasa zuga a cikinsa. Zuga wata dabara ce ta ɗaukaka abu sama, a iza shi, ko a tura shi a ce ya yi wani
abu ko ya saba yin wani abu, ko zai iya ganin mawuyacin abu”. Da waƙoƙin maza da waƙoƙin sarauta duk
suna da wannan jigo na zuga sosai. Zuga tana sa wanda ake yi
wa ita ya ji zai iya ɗaukar duman Magaji da nishi, ko bai iya abu ba ya ce sai ya
yi.
Dangane da zuga ga wanda makaɗi ke yi wa waƙa kuwa, za mu ga misali
a cikin waƙar da Narambaɗa ya yi wa Alƙali Abu mai amshi
kamar haka:
G/waƙa: Ya ɗau girma ya san yabo,
Ku zo mu ga Alƙali Abu.
Jagora: Da ku aka mulki duniya,
Ba don ku ba da ta yamutce,
Bilhaƙƙi amali na jan
damo,
Yara: In yai magana ta kwakkwahe.
Dubi yadda Narambaɗa ke zuga Alƙali Abu da cewar
“Ba don su ba da duniya ta yamutse”, ya kuma nuna ya fi kowa a wajen yanke
magana domin da ya yi magana an kwakkwahe; wato an gama dole a bi. Bugu da ƙari a wani ɗiyar waƙar Narambaɗa Tubali ya kawo salon zuga a gare shi da kuma ga ubangidansa a cikin ɗiyan waƙa ɗaya, inda yake cewa:
G/waƙa: Gwarzon Shamaki
na Malam Toron Giwa,
Baban Dodo ba a Tamma da batun banza.
Jagora: In an ce Isa ba ka jin an ce wani sarki,
Ni ko duk Hausa ba ka jin waƙa bayan tau.
A nan ya nuna a duk ƙasar Isa babu
kamar sarkinsa, haka ma duk ƙasar Hausa babu
mawaƙi irinsa. Abin lura a nan shi ne, a wajen amfani da salon zuga da yabo a cikin waƙa sai mafalsafin
mawaƙi mai hasashe da
hangen nesa mai tsinkaye, domin shi kansa yabon da zugar ma iyawa ne,
kasancewar ba duka mawaƙa kan yi yabo ko
zuga cikin hikima da fasaha ba. Domin a wasu waƙoƙin mawaƙan za ka ga yabon
zugar amma babu ɗarsashi da armashi
kamar na waƙoƙin mawaƙa mafalsafa.
4.2 Falsafa a
Bakin Makaɗa Sa’idu Faru
Kamar yadda Tarihi ya nuna makaɗa Sa’idu Faru shahararren mawaƙin sarauta ne kuma
haziƙi, gwani, fasihi, ƙwararre ga harshen
waƙarsa mai cike da
rumbun kalmomi, kuma ɗan gado a harkar
waƙa domin ba hayenta
ya yi ba.
Dangane da irin falsafarsa kuwa za a iya ganin misalanta a
cikin wasu ɗiyoyin waƙoƙinsa. A cikin waƙar da ya yi wa
ubangidansa Sarkin Kudu Maccido, wanda ainihin sunansa shi ne Muhammad Abubakar Macciɗo ɗan Abubakar wanda
ya rayu (20/04/1928 zuwa 29/10/2006) kuma shi ne Sarkin Musulmi na 19, ya kuma yi mulkinsa daga shekara
(1996-2006). A ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu Faru ya
nuna falsafa, inda yake cewa:
G/waƙa: Kana shire baban
‘yan ruwa,
Na Bello Mamman Sarkin Kudu.
Jagora: Duba kafak ka zuwa bisa hannuwa,
Zaman Shehu na ba wata za’ida,
Sarkin Musulmi wata ran kake,
Da imani da mu’iza na nan,
Gun Mamman Macciɗo,
Tun ga Alu Maisaje nij jiya,
Halin Bubakar yar riƙa,
Macciɗo kai ka shirin gado haka.
Jagora: Wada duk aka gadon ɗaukaka,
Wada duk aka gadon ƙasura,
Wada duk aka gadon ci gaba,
Mamman ka gaji Abubakar,
Ko da dalilin da a kai,
Baba halin da ka kai kuɗɗi su kai.
Jagora: Mamman in Allah yai nufi,
Baba gari ne da mutane nai duka,
Ɗan giwa komai yad daɗe,
Na tabbata yin giwa ya kai.
A lokacin da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo wannan waƙa, babu wanda ya
taɓa zaton cewa shi Macciɗo zai zama Sarkin Musulmi. Duk da yake shi ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III ne, amma bai yi tsammani zai
zama Sarki ba, ganin yadda al’amuran sha’anin sarauta suke tafiya. Kuma da
wannan misali za a ƙara gane lallai
makaɗa Sa’idu Faru ya
cika mafalsafin mawaƙi, dubi yadda yake
ta faɗin maganganu
tamkar yana dubawa da tabaran hangen nesa. Kodayake dama a
can baya mun ga cewa mafalsafi yana da zurfin tunani da hangen nesa, to kuwa
duk waɗannan siffofi na
mafalsafi da aka ambata a baya suna nan tare da Makaɗa Sa’idu Faru.
Duba da yadda ya dinga faɗin cewa, “Sarkin Musulmin wata ran kake, Ka
gaji Abubakar, in Allah yai nufi Macciɗo gari ne da mutane nai duka”. Ya kuma ƙara cewa “Ɗan giwa komi daɗewarsa sai ya zama
giwa”. Idan aka yi la’akari da cewa Sarkn Musulmi Abubakar III ya daɗe da mulki domin
sai da ya shekara hamsin (50), kuma sai aka ba Dasuki, amma daga baya zancen
Sa’idu ya tabbata, domin Ɗan giwa ya zama
giwa, Macciɗo ya gaji Abubakar.
Cikin ikon Allah Macciɗo bai zama Sarkin Musulmi ba sai bayan rasuwar makaɗa Sa’idu Faru, to amma ga shi duk abubuwan da ya faɗa sun tabbata.
Har ila yau a wata waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo, ya ƙara kawo mana irin
wannan misali na falsafa, inda yake cewa:
G/waƙa: Ya yi sarki dai
dai wa da mai yanzu yar riƙa,
Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai
dubun bara.
Jagora: Wada duk ɗan Sarki yaƙ ƙasura,
Bai kai ga Macciɗo,
Girma Allah yay yi ma Baba duniya.
Wannan haka yake domin dai komai girman ɗan sarki ko ɗaukakarsa ba zai yi kamar Macciɗo ba, tunda ba zai yi Sarkin Musulmi ba. Makaɗi kuma ya daɗa nuna cewa, “Allah ya yi wa Macciɗo girma a duniya tun da ga shi ya zama Sarkin Musulmin Nijeriya.
Haka ma, a cikin wata waƙar da ya yi wa shi
dai ubangidan nasa Macciɗo inda yake kira gare shi da ya ƙyale kowa ya jira lokaci, inda yake cewa:
G/waƙa: Farin cikin
Musulmi,
Mu kai muka taƙama yau,
Muhammadun Muhammadu,
Ɗan Amadu mai darajja.
Jagora: “Yan Sarki kai ta biyayya da biyayya aka sarki,
In zamaninka yaz zaka,
Ba sai an yi daga-daga ba,
Bari musu daga-daga, sai ta daga-gadassu,
Koi yarda da Allah,
Ba zai yi gada-gada ba.
Wato a nan tun daga sunan waƙar daga amshinta
za a gane lallai makaɗa Sa’idu Faru yana
cikin sahun gaba a rukunan mafalsafan mawaƙa, kasancewar yawancin duk abubuwan da ya furta suna tabbata. Domin dai Macciɗo ya zama farin cikin Musulmi, kuma jagaban da Musulmi ke taƙama da shi. Kuma
duk wannan daraja da Sa’idu Faru yake ta kira wa Macciɗo ga ta nan ta tabbata.
Malamin kiɗi Sa’idu Faru ya ci gaba da cewa: “Idan lokacin ka ya zo ba
sai ka yi gada-gada ba, don haka ka ƙyale masu
gada-gada, sui ta gada-gadarsu, tun da kai ka yarda da Allah”. To kuwa hakan ce
ta tabbata domin Sarkin Kudu Macciɗo ya hau karagar Sarautar Musulmi.
Bugu da ƙari akwai wani
misalin falsafa a wani ɗiyan waƙar Macciɗo da makaɗa Sa’idu Faru ya yi mai amshi kamar
haka;
G/waƙa Kana shire Baban ‘Yanruwa,
Na Bello jikan
Danfodiyo.
MuazuTafiyag ga da ka yi da ba ni nan,
Nib bi ka ina gudu ga
ni nan,
Nan nib bi ta Tcahe ina gudu,
Kuma nib bi ta Tcahe ina gudu,
Can na kusa kai wa Zariya,
Ɗan na Daudu ni ko sai nit tsaya,
Sai Sarkin Zazzau nig
gani,
Yac ce man Muhamman
ya tai haji,
Sai nis saki hanya
niy Gabas,
Can nan taɓa yat tafiya kaɗan,
Sai ni ishe suda na
kiwo,
Tana ta waƙar Sarkin Kudu,
Rainai ya daɗe Sarkin Kudu,
Allasabbinani ɗan Amadu,
Allah shi ƙara mai nasara,
Kana shire baban ‘yanruwa,
Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
A wannan ɗiyan waƙa malamin kiɗi Sa’idu Faru ya yi amfani da wani salo mai birgewa, wato salon mutumtarwa
inda ya ambaci tsuntsaye a siffofin mutane ya nuna su ma suna ƙaunar wannan waƙa ta Sarkin Kudu har suna raira ta suna sa masa albarka. Idan aka dubi kusan duka ɗiyan waƙar nan cike suke da falsafa kuma irin ta ƙwararren mafalsafin mawaƙi.
To wannan kenan dangane da abin da bincike ya nuna mana game
da misalan falsafar malamin kiɗi mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba Sa’idu Faru.
5.0 Kammalawa
Daga ƙarshe mun ga abubuwan da wannan takarda ta ƙunsa dangane da falsafa,
ma’anarta da kaɗan daga cikin
mabambantan ra’ayoyi daga masana fannin falsafa, sannan mun ga ma’anonin da masana
suka ba waƙa da kuma wani ɓangare na wasu ginshiƙan falsafar. Wato, Tsinkaye da Hasashe da Hangen-nesa, kana da yadda mawaƙa kan yi amfani da
salon falsafar yabo da zuga a cikin waƙoƙinsu. Sai kuma
misalan falsafa daga wasu ɗiyoyin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Sannan an dubi matsayin falsafa a waƙa tare da
ingantattun misalai kuma an kawo misalai na yadda mawaƙan baka kan yi
amfani da tataccen tunaninsu wajen cusa falsafa a cikin ɗiyan waƙoƙinsu. Kana wannan
takarda ɗauke take da
cikakken tarihin makaɗa Sa’idu Faru da
kuma irin falsafar da ya ke amfani da ita a cikin waƙoƙinsa.
Manazarta
Abubakar, M. I. (1998). Mawaƙi A matsayin
Mafalsafi (Unpublished B.A Dissertation Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.
Abubakar, A. T. (2014:). Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria N. N. P. C.
Bargery, G.P (1993). A Hausa-English Dictionary & English-Hausa Vocabulary. Zaria: ABU Press ltd.
Bunza, A.M (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria ltd
Bunza, A.M (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre ltd
Bram, L.L.(ed). Funk
and Wagnalls New Encyclopedia. Volume 19,pfitzner to punic wards New
York.
Ɗangambo, A (1984). Rabe-raben Adabin
Hausa. Kano: KDG Publishers
Ɗan Alhaji, A
(2016). Shin Ko Akwai Wata Aba Ita Falsafa a Adabin Hausa. Kaduna
Journal of Hausa studies Vol 1 No. 2. Dept of Nigerian Languages and Linguistics.
Gusau, S.M. (1996).
Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Fisbas Media Services
Gusau, S.M. (2022). Fannin Falsafa a Ilmance. Kano: Century Research and Publishing
Company ltd.
Gusau, S.M (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka Juz’i na Biyu. Century Resaerch
and Publishing ltd.
Gusau, S.M. (2020). Diwanin Waƙoƙin Baka Juz’i na Biyar. Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka. Kano: Commercial Printing and Publishing ltd.
Muhammad, Y.M
(2003). Adabin
Hausa. Ahmadu Bello University Press.
Skinner, N. (1998). Ƙamus na Turanci da Hausa. Zaria: NNPC.
Malumfashi, A.I. (2018). Lacca Ajin PhD, Hausa. Jami’ar Umaru ‘Yar’adua, Katsina.
The Encyclopedia Britannica (1911-1926) .13th edition volume 21-22 payn to polkn. The encyclopedia Britannica
Company Ltd New York.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.