Citation: Bunguɗu, A.I., Rabi'u, S.A. & Abdulmalik, S. (2024). Salon Kambamawa a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 201-206. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.025.
SALON KAMBAMAWA A
WASU WAƘOƘIN MAKAƊA
SA’IDU FARU
Aminu Ibrahim Bunguɗu
Sashen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Maru, Jihar Zamfara
aibaminu054@gmail.com
08066357569
Da
Sani Alhaji Rabi’u
Sashen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Maru, Jihar Zamfara
sanirabiu424@gmail.com
09067586878
Da
Sulaiman Abdulmalik
Sashen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Maru, jihar Zamfara
Sabdulmalik327@gmail.com
08060292700
Tsakure
Kambamawa wata
dabara ce ta mawaƙa inda suke faɗin wata magana fiye da yadda abin yake
a rayuwa ta zahiri, domin su isar da wasu saƙonni. Manufar wannan takarda ita ce fito da wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru waɗanda suke ƙunshe da salon kambamawa tare da yin sharhi gwargwadon
fahimta. An ɗora wannan aiki a bisa ra’in mazhabar
Waƙar Baka Bahaushiya wadda Gusau (2003 da
2015) ya assasa. An tattaro wasu matanonin waƙoƙin Sa’idu Faru ta hanyar amfani da
Diwanin Waƙoƙin Baka na Gusau (2009), da kuma sauraron wasu waƙoƙin tare da rubuta matanoninsu a
takarda. An gano cewa Sa’idu Faru yana amfani da salon kambamawa domin ya isar
da wasu saƙonni, da kuma ƙara wa waƙa armashi domin jawo hankalin jama’a.
Daga cikin saƙonni da Sa’idu Faru yake isarwa ta
hanyar amfani da kambamawa akwai muhimmancin wasu kyawawan halaye kamar faɗin gaskiya da haƙuri da kyauta. Sannan kuma yana nuna matsayin wasu sarakuna
da kuma nuna iyakoki da faɗin wasu masarautu na ƙasar Hausa.
Muhimman
Kalmomi: Waƙa,
salo, kambamawa, faruwar wani abu, faɗin ƙasa,
kyawawan halaye.
Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin
hikima da yake zuwa gaɓa-gaɓa
bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rere
cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi
(Gusau, 2003: xiii). Makaɗan
baka suna amfani da salo daban-daban a cikin waƙoƙinsu
domin isar da wasu muhimman saƙonni. Yahya (2001: 3) ya nuna cewa salo na nufin duk wata dabara
ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi
domin isar da saƙo. Ya ƙara da cewa, ita
wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta
yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko mai karatu. Gusau (2003: 54)
ya karkasa salo zuwa gidaje guda biyu: adon harshe da kuma aiwatar da harshe.
Adon harshe wata dabara ce wadda ake yi wa harshen waƙa
kwalliya. Akan zaɓo
wasu kalmomi a zayyana waƙa da su, a ƙawata
ta sosai yadda za a burge mai sauraro a kuma jawo hankalinsa. Kambame yana ɗaya
daga cikin nau’o’in adon harshe kamar yadda Yahya (2001: 2) da Gusau (2015: 25)
suka nuna. Ana samun wannan salo na kambamawa a cikin wasu waƙoƙin
Makaɗan
baka na Hausa. Wannan takarda ta
yi magana ne a kan salon kambamawa a cikin wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗa Sa’idu faru, kuma an yi sharhi a kan ɗiyan waƙoƙin gwargwadon fahimta.
2.0 Taƙaitaccen Tarihin
Makaɗa Sa’idu Faru
An haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru da ke cikin ƙasar Maradun da ke
jihar Zamfara, a wajejen shekarar 1932. Sunan mahaifinsa makaɗa Abubakar ɗan Abdu. Sa’idu
Faru ya yi yawancin ƙurciyarsa a garin Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda inda
aka haifi mahaifiyarsa, amma daga baya ya koma wajen mahaifinsa a Faru. Ya
yi karatun addinin Musulunci, amma bai yi karatun boko ba. Makaɗa
Sa’idu Faru ya koyi waƙa a wurin mahaifinsa makaɗa
Abubakar. Tun yana da shekara
goma aka fara zuwa yawon kiɗi
da shi gari-gari. Waƙar farko da Sa’idu Faru ya fara yi ita
ce waƙar Sarkin Yamman Faru Ibrahim (Gusau,
1996: 117-119). Makaɗa
Sa’idu Faru ya rasu a shekarar 1987.
3.0 Hanyoyin Tattaro Bayanai
Domin
samun nasarar wannan aiki, an yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen tattaro
bayanai waɗanda
suka haɗa
da sauraron kaset-kaset na CD waɗanda
suke ɗauke
da waƙoƙin
makaɗa
Sa’idu Faru, tare da rubuta matanoninsu a kan takarda. Sannan an duba Diwanin
Gusau (2009) inda aka samu wasu waƙoƙin
Sa’idu Faru. Bayan haka, an yi amfani da dabarar tattaunawa inda aka tattauna
da Alhaji Ibrahim Ɗanmadamin Birnin Magaji da Dr Muhammad
Ammani domin samun wasu muhimman bayanai. Haka Kuma, an yi nazarin wasu littattafai
da kundayen bincike da maƙalu masu alaƙa
da wannan takarda.
4.0 Ma’anar Kambamawa
Ɗangambo (2007: 47)
ya bayyana cewa ‘kambame[1] wani lafazi ne ko furuci da mawaƙa kan yi wanda sai
a ga abu ne mai wuya haka ta auku a rayuwa ta zahiri. Sukan faɗi abin da ba zai yiwu ba, su nuna ya auku ko zai auku; ko
kuma su ce in ma ya auku to ba zai hana haddasa wani abu ba.’ Shi ma Yahya (2001:
95) ya nuna cewa, ‘kambamawa na nufin mawaƙi ya yi zuƙu a cikin magana, wato ya ƙara mata gishiri
ko ya bayyana abu fiye da yadda yake a haƙiƙanin gaskiya. Haka
kuma, Abba da Zulyadaini (2000: 122) sun nuna cewa kambamawa wata hanya ce da
mawaƙan baka kan nuna aukuwar wani abu a cikin waƙoƙinsu wanda a
zahiri idan aka duba abin da suka faɗa ɗin sai a ga cewa
haƙiƙa, ba zai faru ba. Shi ma
Sarɓi
(2007: 179) ya bayyana cewa akan yi amfani da wannan dabara ta kambamawa domin
yin yabo. Ana nuna cewa mutum ya yi wani abu wanda a zahiri ba zai yiwu ba, ko
ya mallaki wani abu da ba zai iya mallaka ba.
A taƙaice ana iya cewa kambamawa dabara ce ta mawaƙa inda suke ayyana
faruwar wani abu, ko su ce zai faru, wanda hankali da tunani ba za su taɓa ɗauka ba, amma sai
su yi amfani da hikima su nuna cewa abin ya faru, ko zai faru.
5.0 Kambamawa a
Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru
Mawaƙa suna amfani da
wannan salo na kambamawa a cikin wasu waƙoƙinsu daban-daban,
domin isar da wasu muhimman saƙonni. Sa’idu Faru
yana amfani da wannan salo na kambamawa a cikin wasu waƙoƙinsa. Haka kuma ya
yi amfani da hikimomi daban-daban wajen amfani da wannan salo na kambamawa kuma
an tattauna su tare da misalai a cikin wannan muƙala ɗaya bayan ɗaya.
5.1
Kambamawa ta Faruwar Wani Abu
Makaɗa
suna bayar da labarin wani abu da ya faru a cikin wasu ɗiyan
waƙoƙinsu.
Sai dai a wasu lokuta makaɗan
suna kambama labarin ta hanyar ƙara masa gishiri, ko kuma su ƙirƙiro
wani labarin su nuna ya faru domin su isar da wasu saƙonni.
Makaɗa
Sa’idu faru ya yi amfani da irin wannan salo na kambamawa a cikin wasu waƙoƙinsa.
Ga wasu misalai kamar haka:
A waƙar
Sarkin Yaƙin Banga, Sa’idu Faru na cewa:
Jagora:
Ga Sarkin
Kano gami da Sarkin Ikko,
: Sun
kammale ɗiya,
: Ga Sarkin
Funtuwa da Sarkin Bauchi,
: Sun
kammale ɗiya,
: Ga
kuma Sarkin
Ƙayan Maradun,
: Maikudu
ɗan
Shehu ya iso,
: Ga Sarkin
Yawuri da Sarkin Gwandu,
: Sun
kammale ɗiya,
: Ga Sarkin
Yamai gami da Ardon Shuni,
‘Y/Amshi: Suna gaisuwa,
: Su
duka sun taru ba a yin magana,
: Sai
Sale ya iso,
: Sarkin
ya lura ba ka yin magana,
: Duk
sai da gaskiya.
(Gusau, 2009: 147)
A
wannan ɗan
waƙa, Sa’idu Faru ya bayar da labarin wani
taro da aka yi a fadar Sarkin Musulmi Abubakar III. Sarakunan Kano da Ikko wato
Legas da Funtuwa da Bauchi da Maradun da Yawuri da Gwandu da Yamai da Shuni duk
sun taru a fadar Sarkin Musulmi, amma ba a ba su damar yin magana ba, sai da Sarkin
Yaƙin Banga Sale (1934-1963) ya iso a
wurin taron, saboda Sarkin Musulmi ya fahimci cewa Sarkin Yaƙin
Banga mutum ne mai faɗin
gaskiya.
Idan
aka dubi wannan labari za a ga cewa Sa’idu Faru ya yi amfani da salon kambamawa
ne, domin da wuya a ce wannan abu ya faru. Wasu daga cikin sarakunan da Sa’idu Faru
ya kawo a ɗan
waƙar manyan sarakuna ne a ƙasar
Hausa, kamar sarkin Kano da sarkin Gwandu da sarkin Yawuri da sarkin Bauchi.
Shi kuma sarkin Yaƙin Banga Sale hakimi ne a ƙarƙashin
masarautar Ƙaura Namoda.
Sa’idu
Faru ya yi amfani da wannan salo ne domin ya nuna cewa Sarkin Yaƙin
Banga mutum ne mai faɗin
gaskiya. Haka kuma, wannan ɗan
waƙa na nuna muhimmancin faɗin
gaskiya da kuma tsare gaskiya.
A waƙar
Kana shirye Baban ‘Yanruwa, Sa’idu Faru yana cewa:
Jagora:
Alhaji baba Muhammadu Macciɗo,
‘Y/Amshi: Baba barka da hayewa Maliya,
Jagora:
Waƙag ga
da nim maka Muhammadu,
: Na
ji daɗin ta
Mamman Sarkin Kudu,
: Tun
dak Kabi hak Kano ham Masar,
: Hab
birnin Legas hab Bichi,
‘Y/Amshi: Kowa ya ji waƙar
Sarkin Kudu.
(Gusau, 2009: 153)
A
wannan ɗan
waƙa, Sa’idu Faru ya bayyana yadda aka ji waƙar
da ya yi wa Sarkin Kudu, wato Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
a wurare daban-daban waɗanda
suka haɗa
da Kebbi da Kano da Masar da Legas da Bichi, inda ya nuna kowa ya ji waƙar
a waɗannan
wurare. Idan aka dubi wannan magana za a ga cewa mawaƙin
ya yi amfani ne da salon kambamawa ta hanyar yin ƙarin
gishiri, domin da wuya a ce kowa ya ji wannan waƙa
a waɗannan
wurare musamman a ƙasar Masar da kuma garin Legas. Ya yi
amfani da wannan salo ne domin ya nuna muhimmancin wanda ya yi wa waƙar
da kuma yadda waƙar ta samu karɓuwa
da farin jini ga mutane a wurare daban-daban.
A
wani ɗan
waƙa na waƙar
Kana shirye Baban ‘Yanruwa, Sa’idu Faru ya ci gaba da cewa:
Jagora:
……………………………
: Can
na taɓa ‘yat
tafiya kaɗan,
: Ni
kai bakin bahar Maliya,
: Sai
ni ishe Larabawa wurin,
: Suna
ta waƙas Sarkin Kudu,
: Rainai
ya daɗe
Sarkin Kudu,
: Ala
sabbinani ɗan
Amadu,
: Allah
shi ƙara ma
nasara,
: Ɗan mai
daraja Sarkin Kudu,
: Jikan
mai daraja ɗan
Amadu,
: Sannan
mai daraja shi yay yi shi,
: Shina
gida zanne a Sakkwato,
: In ya
yi salla yai tazbaha,
‘Y/Amshi: Hasken nashi han nan kallo mukai,
(Gusau, 2009: 156)
A
wannan ɗan
waƙa, Sa’idu Faru ya nuna cewa ya ga wasu Larabawa
a bakin Bahar Maliya suna yin waƙar Sarkin Kudu, wato Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo.
Sannan kuma ya nuna cewa idan Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
ya yi sallah ya ja tazbaha a Sakkwato, suna ganin shi daga inda suke. Idan aka
dubi waɗannan
bayanai za a ga da wuya haka ta faru. Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan salo
na kambamawa ne domin ya nuna yadda waƙar
ta samu karɓuwa
da kuma matsayi da darajar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo,
da ta iyayensa da kakanninsa.
A waƙar
Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba, Sa’idu Faru
na cewa:
Jagora:
Abu
tafiya wadda kay yi Garba ta taro Hausa,
‘Y/Amshi: Gusau tariya sunka zo tasha duk baki ɗai,
: Da munka zo Maru sai ga Banaga da gudu ya
kawo,
: Don
kada ka wuce Abubakar ba ku gama hannu ba,
: Waɗan
Mahwara sunka taru gareji da ‘yan sanda hatta Yarbawa,
: Mai
Kudu yai tariya yadda duk a kai Mai Kudu duk ka yi.
(Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar, MP3)
A
wannan ɗan
waƙa Sa’idu Faru ya nuna cewa a lokacin da
Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba (1952-1960),
ya yi wata tafiya zuwa Sakkwato, mutanen Gusau baki ɗaya
sun zo tasha sun tarbe shi. A garin Maru, Banagan Maru ya zo da gudu ya tarbe
shi. A garin Mafara mutane sun fito sun tarbe shi.
Idan
aka dubi wannan labari za a ga cewa da wuya haka ya faru, domin waɗannan
garuruwa ba a ƙarƙashin
Ƙaura Namoda suke ba. A lokacin da Sarkin
Kiyawa Abubakar (1952-1960) ya yi mulki, garuruwan Ƙaura
Namoda da Gusau da Maru da Talata Mafara duk gundumomi ne a yankin Sakkwato ta Gabas,
kuma hedikwatarsu tana Gusau.
Sa’idu
Faru ya yi amfani da wannan salo ne domin ya nuna cewa Sarkin Kiyawan Ƙaura
Abubakar babban sarki ne wanda mutane ke girmamawa.
5.2
Kambamawa ta Faɗin Ƙasa
Kasancewar Sa’idu Faru mawaƙin
fada, a cikin wasu waƙoƙinsa
yana magana a kan faɗin
ƙasar wasu masarautu inda yake bayyana
iyakokinsu ko kuma garuruwan da ke ƙarƙashinsu.
Sai dai a wasu lokuta yana amfani da salon kambamawa ya yi ƙarin
gishiri. Ga wasu misalai kamar haka:
A waƙar
Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba, Sa’idu Faru
yana cewa:
Jagora:
Ni kiɗin yaƙi niy
yi ma Abu na Isau,
‘Y/Amashi: Ba ni son kana zannawa banza,
: Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakunkuna,
: Ka
sa sirdi,
: Ba
mu sansani sai bakin Tsabre,
: Kano
da Katcina da Kwantagora hab Borno,
: Riƙon
Namoda shi na ac can,
: Garba
ka amshe riƙon dud da Ummaru, Ummaru yab bam ma,
Jagora:
Garba ka hizge,
: Riƙon dud
da Ummarun Ummaru yab bar ma.
(Waƙar Sarkin Kiyawa Abubakar, Mp3)
A wannan ɗan
waƙa Sa’idu Faru ya nuna cewa Kano da
Katsina da Kwantagora da kuma Borno duk suna a ƙarƙashin
riƙon Muhammadu Namoda (1807-1810). Idan
aka dubi wannan magana za a ga cewa Sa’idu Faru ya yi amfani da salon kambamawa
ne domin ya nuna irin ƙoƙari
da jaruntar da Muhammadu Namoda ya yi a lokacin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
Domin kamar yadda Yahaya (1988: 51) ya nuna, Kano da Katsina da Borno suna
cikin garuruwan da Shehu Usmanu ya ba sarakunansu tuta. Haka kuma Ƙaura
(2020: 142) ya nuna cewa Muhammadu Namoda ya taimaka wa Ummarun Dallaji na
Katsina a wurin yaƙi.
A waƙar
Sarkin Fulanin Bunguɗu
Shehu, Sa’idu Faru yana cewa:
Jagora:
Shehu ya yi iyaka Ƙaura
: Shehu
ya yi iyaka Ƙaura,
: Ya
yi iyaka ƙasar Maradun,
: Nan
kudu bai da,
‘Y/Amshi: Iyaka, Baciri dan nan har Tabkin Chadi.
(Gusau, 2009: 160)
A
wannan ɗan
waƙa, Sa’idu Faru ya bayyana cewa a
lokacin mulkin Sarkin Fulanin Bunguɗu Shehu
(1974-1979) ƙasar Bunguɗu
ta yi iyaka da Ƙaura Namoda da Maradun. Sannan kuma ta
yi iyaka har da Tafkin Chadi. Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa tabbas ƙasar
Bunguɗu
ta yi iyaka da ƙasar Ƙaura
Namoda da kuma ƙasar Maradun, amma sai Sa’idu Faru ya
yi amfani da salon kambamawa ya yi ƙarin
gishiri ya nuna cewa ƙasar Bunguɗu
ta yi iyaka da Tabkin Chadi. Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan salo ne domin
ya jawo hankalin mai saurare, kuma ya nuna yadda ƙasar
Bunguɗu
ke da faɗin
ƙasa.
5.3
Kambamawa ta Kyawawan Halaye
Sa’idu Faru yana bayyana kyawawan
halayen wasu mutane a cikin zubin waƙoƙinsa.
Sai dai a wasu lokuta yana amfani da salon kambamawa ta hanyar ƙarin
gishiri ya nuna cewa a ƙasar Hausa ko a wani yanki babu mai
irin wannan kyakkyawan hali, sai wanda yake yi wa waƙa.
Ga wasu misalai kamar haka:
A waƙar
Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, Sa’idu Faru yana cewa:
Jagora: Bai gadi sake ba Mamman na Baura,
‘Y/Amshi: Toron giwa
uban Bello Mato,
: Duk Hausa ba mai irin hanƙurinai.
(Waƙar
Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, MP3)
A
wannan ɗan
waƙa Sa’idu Faru ya nuna cewa duk Hausa,
wato Sakkwato babu mai haƙuri irin na Sarkin Musulmi Muhammadu
Macciɗo.
Wannan salo ne na kambamawa, domin abu ne mai wuya a gano wanda ya fi kowa haƙuri
a Sakkwato. Ya yi amfani da wannan salo ne domin ya nuna cewa Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo
mutum ne mai haƙuri da juriya ƙwarai
da gaske.
A waƙar
Mai Babban Rabo Ginshiƙin Sarkin Shariffai, Sa’idu Faru yana
cewa:
Jagora:
Ba
mai kyauta irin mamman duk ƙasar Hausa,
‘Y/Amshi: Ɗan jemage
shi yah hwaɗa man
babu wasa,
: Cika
ni aza ni Mamman ya kai in za ya kyauta,
: In
ya ba mutum fam tamanin sai da riga,
: In
ya ba mutum fam talatin sai da riga,
: In
ya ba mutum fam bakwai ya mai garaje,
: Shina
iya ba ka doki na fam metin da sirdi da kayanai haɗaɗɗi,
: Kuma
ya haɗa da
yaron da zai ja ma kinami.
(Waƙar Mai
Babban Rabo Ginshiin Sarkin Shariffai, MP3)
A
wannan ɗan
waƙa Sa’idu Faru ya nuna cewa duk ƙasar
Hausa babu mai yin kyauta irin wadda Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
yake yi. Wannan salo ne na kambamawa, domin ƙasar
Hausa tana da yawa, da wuya a iya gano wanda ya fi kowa kyauta a ƙasar
Hausa. Ya yi amfani da salon kambamawa ne domin ya nuna cewa Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo
mutum ne mai yi wa mutane kyauta ta ban mamaki.
Haka
kuma, Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan salo na kambamawa a waƙar
Turakin Argungu da kuma waƙar Turakin Kano. Ga abin da yake cewa:
Jagora:
In kana biɗar
riga wadda at ta tcishi,
‘Y/Amshi: Ka zo gun Turakin Argungu,
Jagora:
In kana biɗar
doki wanda an na tcishi,
‘Y/Amshi: Ka je gun Turakin Argungu,
Jagora:
In
kana biɗab bawa
wanda an na kirki,
‘Y/Amshi: Ka zo gun Turakin Argungu.
(Waƙar
Turakin Argungu, Mp 3)
Mu’azu: Ɗan sarkin da ka kyautaj jikka,
‘Y/Amshi: Ɗan Hashin
Kano ɗai a
haka,
Mu’azu: Ɗan sarkin da ka kyautar riga,
‘Y/Amshi: Ɗan Hashin
Kano ɗai a
haka,
Mu’azu: Ɗan sarkin da ka kyautar bawa,
‘Y/Amshi: Ɗan Hashin
Kano ɗai a haka,
Mu’azu: Ɗan sarkin da ka kyautam mota,
‘Y/Amshi: Ɗan Hashin
Kano ɗai a
haka,
: Duk
wanda yaz zam irin haka,
: Ko
badaɗe
shina Sarkin Kano.
(Waƙar Turakin Kano, Gusau, 2009: 163)
A
waɗannan
waƙoƙi
Sa’idu Faru ya lissafo wasu abubuwa waɗanda
ya nuna cewa Turakin Argungu wato Muammadu Shehu Kangiwa tsohon gwamnan jihar
Sakkwato da kuma Turakin Kano Alhaji Tijjani Hashim suna iya bayar da kyautar
su. Sai ya yi amfani da salon kambamawa inda ya nuna cewa waɗannan
mutane suna yin kyautar bawa. A lokacin da ya yi waɗannan
waƙoƙi
zuwa yanzu da wuya a samu wanda ya mallaki bawa a garuruwan ƙasar
Hausa da ke yankin arewacin Nijeriya. Saboda haka waɗannan
mutane wato Turakin Argungu Alhaji Shehu Kangiwa da kuma Turakin Kano Alhaji
Tijjani Hashim ba su da bayin da za su bayar kyauta. Sa’idu Faru ya yi amfani
da wannan salo na kambamawa ne domin ya nuna cewa waɗanda
ya yi wa waƙa sun shahara wajen bayar da kyautar abubuwa
daban-daban.
6.0 Kammalawa
A
wannan takarda an dubi yadda makaɗa
Sa’idu Faru yake amfani da salon kambamawa a cikin wasu waƙoƙinsa.
An kawo taƙaitaccen tarihin Sa’idu Faru, da
ma’anar kambamawa, da kuma hanyoyin da aka bi wajen tattaro bayanai. An gano
cewa Sa’idu Faru yana amfani da salon kambamawa ta hanyoyi daban-daban. An
fahimci cewa Sa’idu Faru yana amfani da salon kambamawa domin ya isar da wasu
saƙonni, da kuma ƙara
wa waƙarsa armashi domin jawo hankalin
jama’a. Daga cikin saƙonnin da Sa’idu Faru ya isar ta hanyar
amfani da kambamawa akwai bayar da labarin wani abu da bai faru ba sam ko kuma
ba a haka ya faru ba, domin koyar da wani darasi, da jaddada muhimmancin wasu
kyawawan halaye kamar faɗin
gaskiya da haƙuri da kyauta. Sannan kuma ya azazzala matsayin
wasu sarakuna da kuma iyakoki da faɗin
wasu masarautu na ƙasar Hausa.
Manazarta
Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan Waƙar Baka ta Hausa.
Zaria: Gaskiya Corporation.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Ɗangambo,
A (2007). Ɗaurayar
Gadon Feɗe
Waƙa.
Kaduna: Baraka Press and Publishers.
Gusau, S.M (1996).
Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Gusau, S.M (2003).
Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S.M (2008).
Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa
Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark
Publishers.
Gusau (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano:
Century Research and Publishing Limited.
Gusau, B.M & Gusau, S.M (2012). Gusau ta Malam Sambo. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau, S.M (2015).
Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da
Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing
Limited.
Ƙaura, H.S (2020) “The Emergence of Ƙauran
Namoda Emirates in Zamfara State”. In Maishanu, I.M, Ƙaura, J.M and Abbas, N.I (eds.) in Zamfara and the Challenges of
Socio-Political Transformation From 1764 to 2019 Conference Proceedings.
Sarɓi,
S.A (2007). Nazarin Waƙen Hausa. Kano:
Samarib Publishers.
Yahya, A.B (2001). Salo Asirin Waƙa.
Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahaya, I.Y (1988). Hausa A Rubuce: Tarihin
Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zariya: NNPC.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.