Citation: Koko, H.S. (2024). Matsayi da Matsalolin Rayuwar Mata: Nazari DagaRubutattun Waƙoƙi na Mata. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 224-232. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.027.
MATSAYI DA
MATSALOLIN RAYUWAR MATA: NAZARI DAGA RUBUTATTUN WAƘOƘI NA
MATA
Hadiza Salihu Koko
Department of
Hausa
Shehu Shagari
College of Education, Sokoto
Tsakure:
Mata sun daɗe a harakar adabi, hasali
ma da su aka fara, da su aka ci gaba da yi, kuma har yanzu da su ake yi. Mata
sun fara rubutu tun lokacin Shehu Ɗanfodiyo, watau 1820, lokacin da Nana
Asma’u ‘yar Shehu take rubutu a kan
abubuwan da suka shafi addini. Daga cikin rubutunta akwai waƙa
wadda ta rubuta a cikin harsunan Larabci da Fulatanci da Ajamin Hausa. Ko a
wannan lokaci ta yi waƙe a kan abubuwa da dama, kama daga wa’azi da faɗakarwa
da bege da jan hankali zuwa ga al’ummar musulmi musamman ga mata ‘yan uwanta.
Don haka, rubutun waƙa ga mata ba sabon abu ba ne yana da daɗaɗɗen
tarihi. Bayan su Nana Asma’u, mata sun ci gaba da rubuta waƙoƙi a
kan fannonin rayuwa daban daban, kuma a ciki sukan mayar da hankalinsu a kan
matsayi da matsalolin mata da al’amurransu
tare da yin gargaɗi da
faɗakarwa ga jinsin
nasu na mata. Wannan muƙala mai taken Matsayi da Matsalolin Rayuwar Mata: Nazari Daga
Rubutattun Waƙoƙi na Mata, ta yi nazari ne a kan yadda mata masu rubuta waƙa ke
fitowa da irin matsayi da matsalolin da mata ‘yan uwansu ke fuskanta a cikin rubutattun waƙoƙin
nasu. An kawo tarihin rubutun waƙa ga mata da matsayin da suke ba jinsinsu
na mata da kuma matsalolin mata na rayuwa waɗanda
mata ne kaɗai suka san
su sosai, kuma su ke iya fito da su. Dukkan misalan da aka kawo daga rubutattun
waƙoƙin da
mata suka rubuta ne. Daga ƙarshe an gano cewa mata suna fito da mata a matsayin masu
daraja da mutunci har dai in sun kama kansu, kuma sun dage da yin sana’a da neman ilimi da neman
na kai wanda zai sa su yi mutunci ga idon mutane. An kawo shawarwari a kan
yadda za a inganta rubutun mata na waƙa, a fito da su a kuma yi nazarin su a
makarantu da wajen tarukan ƙara wa juna sani, don su samu karɓuwa kamar takwarorin su maza.
Fitilun Kalmomi: matsayi,
matsaloli, rayuwar mata, rubutattun waƙoƙi
Gabatarwa
Bayan
rubuce-rubucen da su Nana Asma’u da suka yi da Ajami, ba a samu wani rubutun
mace ba, sai bayan da Turawa suka shigo Ƙasar
Hausa suka buɗe makarantu a shekarar 1905. Ko a wannan lokaci mata sun
daɗe ba su fara rubutu waƙa da boko ba, saboda ko makarantar mata ta boko daga baya
aka buɗe ta. Al’ummar Hausawa kuwa ba su ɗauki
ilimin mata na boko a matsayin wani abu mai muhimmanci ba a wannan lokacin, sun
ajiye su a matsayin masu rauni da rashin basira da tsananin kishi da gulma,
(Jibril, 1995). Wannan naƙasu na
rashin samun ilimin boko ga mata da wuri yasa har yanzu ba su kai ga
takwarorinsu maza ba wajen yawa da ƙwarewa
ga rubuta waƙa.
Wannan rashin ilimi ga mata ya
taimaka wajen rashin jin muryarsu a fagen rubutaccen adabi, sai maza suka
mamaye wannan fage har tsawon shekaru 47, (Ibrahim, 2010).
Kasancewar maza ne suka kakace
wajen rubuce-rubuce na boko tun tashin farko, yasa suna fitar da mata a
matsayin da bai dace ba ko suka mayar da su kurame waɗanda ba za a ji muryarsu ba. Wannan ta sasai mata suka miƙe tsaye ƙem wajen fuskantar matsalolin
rayuwarsu ta hanyar jajircewa, domin ganin sun bi matakan cimma gurin rayuwa. Ɗaya daga cikin matakan shi ne ta
hanyar adabi, inda suka bijiro da rubuce-rubuce domin ceto mata ‘yan’uwansu
daga matsayin da ake ba su zuwa wani matsayi na daban da suke ganin ya dace a
ce tun tuni ana fito da mata da shi. Da haka mata suka fara nuna mace a
matsayin mai daraja da kuma muhimmanci ga al’umma. Sun gina wannan ra’ayi a
sassan adabinsu daban-daban na Hausa kama daga rubutattar waƙa da rubutattar wasan kwaikwayo
da rubutun zube da sauran rubuce-rubucensu na yau da kullum.
Wannan matsayin rayuwa da
matsaloli da mata ke fito da mata ‘yan uwansu da shi ne wannan muƙala ta duba, tare da kawo
misalai daga waƙoƙin da mata suka rubuta.
Tarihin
Rubutun Waƙa
Ga Mata
Rubutaccen adabi ko adabin
zamani, shi ne wanda aka samu bayan shigowar baƙi a ƙasar
Hausa. Asalinsa a rubuce yake, saboda sai da Hausawa suka samu ilimin addini da
boko sannan suka fara karatu da rubutu har suka san su adana wani abu cikin
rubutu. An fara ne da rubutun Ajami wato rubuta sautukan Hausa da haruffan
Larabci. Daga baya aka samu rubuta sautukan da haruffan Romanci wanda ake kira
boko. Wannan adabin ne ake kira adabin zamani saboda yana tafe ne da zamani.
Sassansa sun haɗa da rubutattar waƙa (tun kafin jihadi) da
rubutattar wasan kwaikwayo (1930s) da rubutun zube (1933). Duk wani abu da aka
gani na adabi a rubuce wanda ba waɗannan ba to, adabin baka ne aka
rubuta domin a adana shi.
Idan aka gangaro nan Afirika,
sai a ce matan da suka fara rubutu a kan matsalolin mata musamman a waƙa su ne, su Nana Asma’u ‘yar
Shehu Ɗanfodiyo
da sauran mata, su ke rubuta waƙoƙi a harshen Fulatanci da Larabci
da Hausa (ajami) waɗanda ke da ilimin rubuta waƙa tun a shekarar 1820. Waƙoƙin sun danganci matsalolin rayuwarsu, burace-buracensu da
matsayinsu a al’umma. Rubuce-rubucen Asma’u ya haɗa
da fannonin ilimi da fiƙihu
da madahu da tauhidi da yabo da bege da addu’o’i har da siyasa, (Boyd da Mack,
2013). Tun a wannan lokaci ake cin gajiyar Asma’u ‘yar Shehu ta hanyar shirin
ilimin mata na ‘Yantaru, inda take da ƙungiyoyi
na mata a birane da ƙauyuka ƙarƙashin jagorancin Jaji wadda ke zuwa gida-gida suna ilmantar
da mata addininsu da faɗakar da su a kan zamantakewa ta
hanyar waƙa, (Boyd
da Mack, 1999:9).
Nana Asma’u ta kalli mata a
cikin waƙoƙinta a matsayin masu daraja da
muhimmanci don haka ta yi kira da a ba su ilimin addini domin a ci moriyarsu.
Idan suka sami ilimin suna amfani da shi su yi wa addini aiki da al’umma. Ta yi
hakan ne ta hanyar ‘Yantaru da take koya wa karatun addini ta hanyar waƙa, su kuwa su hardace, su je
gidaje inda mata suna rerawa don su fitar da su duhun jahilci. Ta jinjina wa
irin waɗannan mata a cikin waƙarta ta Tuwassali ga Mata Masu
Albarka (1837), inda ta ambaci matan da suka taimaka wa addinin Musulunci
saboda ƙwazo da
ilimin da suka samu kamar su Joɗa Kanwuri da “Yar Hudu da Habiba
da sauransu.
Bayan rasuwar Nana Asma’u a
shekarar 1865, an samu wasu mata da suka biyo bayanta, kuma suka ci gaba da
mayar da hankali a wajen rubutunsu na waƙoƙi ga al’amurran da suka shafi
addini, kama daga wayar da kan al’umma da neman ilimin addini musamman ga mata
da yin wa’azi da fiƙihu da
siyasa da zamantakewa. Waɗannan mata, kamar yadda Modibbo
Kilo ta zayyano wasu daga cikinsu har zuwa ga ita kanta Kilon, a cikin waƙarta ta Hijira da Zaman Modibbo Kilo A Makkah inda take cewa:
Farkon nufa tabsir
ga matan Sakkwato,
Ku tsaya ku saurara fa kaziban
wuri.
Babbaɗ ɗiya ita matat Tafa,
Da Uwag-gari da Uwad-daje
yaransa shi.
Baicin su Dudu, ɗiya ta Abdullahi kau,
Mata ta Landijo fa ɗanai shahidi.
Sai Ukhitiya ‘yas
Sambo sai Janajo ji,
Ita ad ɗiya matat Tafa Mutafannini.
Bayan su
Matar-Modi bint Uwad-Daje,
Umrinta haƙƙan babu bidi’a zahiri.
Baicin su Dikko ɗiya ta Ahmadu Gwandu ta,
Haifan Basharun Ukhtiya da Aliyu shi.
Zamaninta Habsatu
tay yi gwaggo amaliya,
Haifan fa malam Mani ta Mutafannini.
Haka nan fa Hauwa ɗiya ta Abdulƙadir,
Baban fa malam Bube na mashahuri.
Bayansu Saudatu ta
Kilon Mahmudu ji,
Alƙali
Ma’aruf na kau addini.
(Mdibbo Kilo: Waƙar Hijira da Zaman Modibbo Kilo
a Makkah).
Daga waɗannan baitoci an fahimci matan da suka ci gaba da gudanar da
rubuce-rubuce na waƙoƙi, da sauran al’amurran addini
bayan gushewar Nana Asma’u. An zayyano su Khadija (matat Tafa) ƙanwar Nana Asma’u da Maryam
(Uwad-Daje) da Maryamu (Tamodi) da Dudu ɗiyar Abdullahin Gwandu da
Aishatu (Utiya) da Dikko da Habsatu da Hauwa Mammange da ita kanta Saudatu
Modibbo Kilo.
An ci gaba da samun mata masu
rubuta waƙa a cikin
Ajami har zuwa ƙarni na
20. Turawa sun shigo ƙasar
Hausa shekara 38 bayan rasuwar Nana Asma’u, kuma sun zo da tsarin karatunsu na
boko inda suka fara ba maza dama su koyi karatun kafin su ba mata. Mata ba su
samu wannan damar ba sai a shekarun 1930 zuwa 1960 lokacin aka fara kulawa da
iliminsu na zamani da bunƙasarsu,
(Mack, 2016). Kafin nan maza sun yi nisa da fara rubuta waƙa a cikin Hausar boko, don haka
su aka fi sani da buga waƙoƙinsu kafin a san na mata. Mafi
yawan matan da ke rubuta waƙa
da Hausar boko matan aure ne ko ‘yan mata da ke ƙarƙashin
iyayensu, don haka ba su samun fita zuwa wasu wurare (kamar gidajen rediyo da
talabijin) don nuna fasaharsu kamar yadda maza ke yi. Bugu-da-ƙari, ba a daɗe da bawa aikin mata muhimmanci ba, balle a yi nazarinsu ko
a fito da su duniya ta ji su ta san su. Mata ba su cika samun shawarwari daga ƙwararru game da
rubuce-rubucensu, musamman a fagen rubutattar waƙa inda har yanzu ba a jin sunayen mata marubuta waƙoƙi kamar yadda ake jin na maza irin su Aƙilu Aliyu da Aliyu Namangi da
Yusuf Kantu da Alƙali
Haliru Wurno da sauransu, (Ibrahim, 2010). Ko Nana Asma’u da ta yi suna a fagen
waƙa lokacin masu jihadi, ba a daɗe da tattaro waƙoƙinta ba aka sa cikin littafi,
kuma mata ne suka yi wannan hoɓɓasar, watau Boyd da Mack.
Duk da haka an samu wasu mata da
suka rubuta waƙoƙi a kan addini da neman ilimi
musamman na mata da wa’azi. Da yake asalin rubutattar waƙar Hausa daga addini ne, shi ya
sa mafi yawan abubuwan da ake tattaunawa ba su wuce na addini ba. Waɗannan matan sun haɗa da Maimuna ‘Yar Isma’ila wadda
ta rayu a Kano tsakanin shekarun 1895-1987, da Zainab Ahmad Sufi da Hassana
Ahmad Sufi. An kuma samu su Hauwa Gwaram da Hajiya ‘Yar Shehu da ke magana a
kan abubuwan rayuwa da na zamani waɗanda ke tusgowa a cikin waƙoƙinsu. Waɗannan mata suna kishin mata kuma
su suka gwada muna yadda rayuwar mata take a ƙasar Hausa, musamman dangane da ladabi ga miji da tsaftace
gida da kare mutunci da karɓar canjin da zamani ya zo da
shi. Watau dai suna nuna ra’ayin mata a kan halin da mata suke ciki a Arewa.
Kafin daga baya-bayan nan da aka samu mata da suka fara rubutu a kan soyayya da
zamantakewar aure (kishi) da abubuwan da suka shafi zamani da matsalolin
rayuwar mata a yanzu, kamar su Hauwa Habibu Alhassan da Zuwaira Isah Jos da
Sa’adatu Baba Ahmad da Sadiya Yusuf da sauransu.
Matsayi
da Rayuwar Mata a Rubutattun Waƙoƙi Na Mata
Hauwa Gwaram ta yi waƙar ‘Buɗe Kos a Tsohuwar Laburare Sabon Gari’ inda ta nuna yadda
mata za su inganta rayuwarsu ta hanyar koyon sana’a don su samu abin dogaro da
kai, tana cewa:
Ina so in gargaɗi matan garin nan,
Ku zan
daina yawo ku kama sana’a.
Idan dai lalura ta
sa kun fita,
Ku dawo
ku zauna ku kama sana’a.
Ku dubi abin da
ake kwanakin nan,
Ishara
da tsoro rashin yin sana’a.
(Hauwa Gwaram: Waƙar ‘Buɗe Kos)
Marubuciyar mace ce mai kishin
mata, kuma wadda ke so ta ga rayuwar mata ta inganta. A cikin waɗannan baitoci tana nuni da cewa, mata su daina zaman banza
da yawon banza su rungumi sana’a, wadda ba ta iya ba ta je ta koya. Sana’a da
ma hanya ce ta samun abin dogoro da cimma burin rayuwar yau da kullum. Duk
wadda ba ta sana’a rayuwarta ba za ta inganta ba kamar yadda Salima Auwal
Jegara ta ce a cikin shirin Mujallar Iyali a NTA Sokoto cewa: “idan mace tana
son ta san kanta, kuma ta taimaki kanta a san ko ita wace ce to, ta rungumi
sana’a, saboda garkuwa ce ga ‘ya mace”. (Jegara, 27/12/2015). Wannan haka yake,
saboda yanzu zamani ya kawo cewa dole mace ta kasance tana da wani abu da za ta
taimaka ga gida. Ko matan masu kuɗi suna da tasu irin sana’a da
suke yi cikin gida ko tsakanin ƙasa
da ƙasa domin su taimaki kansu da
iyalansu da ‘yan uwansu. Bugu-da-ƙari,
sana’a na rage tunani, tana kuma hana zaman banza da gulma da tsintse ga mata
baya ga maganin ƙananan buƙatoci na yau da kullum.
Gwaram ta sake kallon mata a
matsayin masu daraja da mutunci da ya kamata su tashi tsaye su kare wannan
mutuncin a duk inda suke. Su kuma kame kansu daga maza maɓannata ta hanyar suturta jikinsu don kada su ba su sha’awa.
Hausawa kan ce “Mutunci dai madara ne idan ya zube ba ya kwasuwa”. A cikin waƙarta ta Lulluɓi ta nuna jikin mata yana da
martaba da daraja, don haka dole su rufe shi don kare mutunci inda take cewa:
Ƙaddara in ta kira ki,
Kin fito waje za a
gan ki,
Sai a gan ki da
lulluɓinki,
Dena nunin kyawun
jikinki,
Lulluɓi na kyau da mata.
In kuna waje ko a ɗaki,
Ɗaure kai zai kyau gare ki,
Yafa ɗan gyale sai ɗiyarki,
Sam mutunci gun
zamanki,
Lulluɓi na kyau da mata.
Kun ga mataye na
sunna,
Ba su kwance zani
su zauna,
Kishiyoyi ‘yan
uwana,
Ba faɗa balle hiyana,
Lulluɓi na kyau da mata.
Mumuna mai son ta
tsira,
Ita ce ta kula da
gyara,
Ba ta yin yawo
tsirara,
Ba ta roƙon masu nera,
Lulluɓi na kyau da mata.
(Hauwa Gwaram: Waƙar Lullubi)
Idan aka dubi waɗannan baitoci da idon basira, za a fahimci cewa suture ta
jiki wajibi ce ga mata, ko suna cikin gida ko idan lalurar fita ta kama su. Ana
mutunta mace a darajanta ta ta hanyar suturar da ke jikinta wanda zai kare
mutuncinta daga mazan banza. Suturta jiki ga mace yana kuma kare ta daga iska
(jinnu), domin ta nan ne suke samu su shiga jikin mata, musmman waɗanda ba sa rufe kai ko ɗaura ɗankwali. Marubuciyar a matsayinta na mace, tana so ta ga
rayuwar mata ta inganta shi yasa ta ɗauki mata a matsayin masu
mutunci musamman idan suna kare mutuncinsu ta hanyar suturta jikinsu da yin
lulluɓi a gida ko a waje. Su kuma kama
kansu daga kwaɗayin abin duniya kamar kuɗi, musamman a hannun mazan banza wanda shi ke zubar da
mutunci, kuma yawo tsirara ke kaisu mahalaka wani lokaci har a yi musu fyaɗe. Ta kuma faɗakar da su kan zamantakewarsu da
kishiyoyi da su ɗauke su kamar ‘yan uwa ne, a
zauna lafiya don a amfani juna.
Ita kuwa Hajiya “Yar Shehu ta
kalli mata a matsayin masu kwaɗayi da son abin duniya, inda har
wasu mata ke cutar mazajensu na aure don abin duniya, suna bin mazan banza fasiƙai don su samu kuɗi ko su yi gadaje irin na wasu mata. Hausawa dai kan ce
‘idan ba ki da gashin wance, kada ki ce za ki yi kitson wance’. Wannan shi ne
kiran da ‘Yar Shehu ta yi wa mata don su masu daraja ne don haka dole su yi
kariyar mutunci da tsare amanar aure inda take cewa:
Gargaɗina ga mata masu bin sunna,
Ku tsare amana ta aure har da addini.
Ku riƙe mazanku ku daina kula da
banzaye,
Maƙiyan
Rasulu abokan nan na shaiɗani.
....................................................................
Me za su ba ku ya
amfane ku nan duniya?
Har za ku cutar da kanku ku saɓi Rabbani.
Har ma ku cuci
mazanku ku ɓata aurenku,
Kuma ran ƙiyama
ku tashi cikin su fattani.
Don Allah domin
ma’aiki na yi roƙon ku,
Mu daina kallon gadajen nan na zamani.
Mu daina kallon
kumbobi gami da kabod,
Su ne suke sa waɗansu
su bi shi shaiɗani.
(‘Yar Shehu: Waƙar Zamani).
Hajiya ‘Yar Shehu mace ce mai
son ta ga rayuwar mata da addininsu sun inganta. A waɗannan baitoci ta nuna cewa wasu mata suna da kwaɗayi da son abin duniya da gasa na wance ta yi ni ma sai na
yi ko da ba ni da shi, wanda ke kai su ga bin maza banzaye. Akwai kuma wasu
maza da ke ƙoƙarin ɓata rayuwar mata musamman waɗanda
ba su san darajar aure ba, suna ruɗin matan aure da dukiya, har su
sa su keta rigar mutuncinsu su ci amanar mazansu na aure. Wannan waƙar an yi ta da daɗewa, amma har yanzu za ta yi aiki ga mata, don har yanzu ana
samun irin waɗannan mata da maza masu halin
banza a cikin al’umma.
Sa’adatu Baba Ahmad marubuciya
ce ta waƙoƙi da ke taɓo rayuwar mata a cikin waƙoƙinta. Ta
wallafa littafi mai suna Muryoyin Zuci inda
take faɗin abin da ke ƙarƙashin zuciyarta dangane da rayuwar mata. A ganinta, a ba
mata ilimi shi ne mafita ga matsalolinsu, domin ilimi shi ne gishirin zaman
duniya. A cikin waƙarta ta
‘Mu Nemo Mafita’ tana cewa:
Mu nemo ilimi a makaranta.
Mu riƙe sana’a kar mu sangarta.
Walau a daraja mun cancanta.
Sai da ƙarin ilimi za mu ƙasaita.
..................................................
Ku taho mu mamaye aikin likita.
Don mu dinga ceto rayuwar mata.
Da aikin shari’a don ƙwato haƙƙin mata.
Kar mu tsaya muna ta yin mita.
Ilimin addini shi ne kaɗai gata.
Mai yawan iso da kyakkyawan
fata.
Rabbi temaki rayuwarmu ‘ya’ya
mata.
(Sa’adatu Baba Ahmad: Waƙar Muryoyin Zuci).
Sa’adatu Baba na kallon mata a
matsayin masu ceton ‘yan uwansu mata daga matsalolin rayuwa, musamman idan suna
da ilimi na addini da na zamani. Daga waɗannan baitoci za a fahimci cewa
duk macen da ke da ilimi ko sana’a ta cancanci a darajanta ta kuma dole ta yi ƙasaita. Don haka, samun ilimi ga
mata zai taimaka ga kiyon lafiyarsu da ƙwato
wa kansu haƙƙi a ɓangaren shari’a. Ke nan wajibi ne ga mata su nemi ilimi na
addini da na zamani domin su kyautata rayuwarsu da ta ‘yan uwansu mata.
Ita kuwa Ruƙayya Sabuwa Nasiru tun a
shekarar 1948 ne ta kalli mata a matsayin masu kishi. Ta nuna haka a cikin waƙarta ta ‘Kishi’ cewa akwai mata
masu mugun kishi wanda ba ya da amfani kuma yana lalata zamantakewa tsakanin
‘yan uwansu mata. Misali:
Ya ‘yan uwana mata
A aje kishi a huta ne.
Shi fa kishi
wahala ce,
Kuma kullum fargaba ne.
Kuma koma baya ne,
‘Yan uwa da za a gane.
(Ruƙayya Sabuwa Nasiru: Waƙoƙin Hikima)
Wannan marubuciya ta san mata
suna da kishi wanda ke wahalar da su a gidan mazajensu, saboda kodayaushe cikin
fargaba suke na me zai faru anjima ko gobe na tashin hankali daga kishiya. Shi
ya sa ta yi kira gare su da su aje kishi su huta wa rayuwarsu ko za su ci gaba.
Matsalolin
Take Haƙƙi
Da Cin Zarafin Mata
Idan aka ce take haƙƙi. ana nufin hana wa mutum wasu
haƙƙoƙi da ya kamata ya samu a rayuwa. Wahala, da wuya wadda mutum
ke sha ko yake fama da ita ta wasu aikace-aikace ko wani abu da ya fi ƙarfinsa ko yake neman ya fi ƙarfinsa wanda aka aza masa dole
sai ya yi, alhali ba haƙƙinsa
ne ya yi su ba, a nan shi ake kira take haƙƙi. Cin zarafi kuwa shi ne a keta haddin
mutum ko a ci mutuncinsa da nufin tozartawa kai shi maƙura.
Duk da yake mata a ƙasar Hausa, sun saba da ayyukan
gida da suka haɗa da daka da girki da ɗibar ruwa da shara da wani lokaci kula da dabbobi. To, amma
saboda zamani da samun ilimin addini da sanin haƙƙoƙin da
addini ya ba su, yanzu mata na ganin waɗannan ayyuka a matsayin
matsalolin da yakamata a rage musu ko suna samun sukunin yin wasu abubuwa kamar
neman ilimi da kula da yara da yin sana’o’in zamani, wanda rashin yin haka a
gare su tamkar take haƙƙi
ne. Wannan ya sa wasu marubuta mata suka fara fito da waɗannan ayyuka a cikin adabin da suke ginawa a matsayin
matsalolin da ke ci wa mata tuwo a ƙwarya,
kuma suke take musu wasu haƙƙoƙi na ci gaban rayuwarsu.
Marubuciya Sa’adatu Ahmad
(2010), ta fito da yadda ake take haƙƙin
mata a hana su sukuni a al’umma a matsayin matsalar da ke damun mata a cikin waƙarta ta ‘Mu Nemo Mafita’ a
littafin Muryoyin Zuci inda take
cewa:
Guri da yawa mun sani mata.
Muna shan wahalar bauta.
Wasu surfe da daka suna kanta.
Wata an mutu da ‘ya’ya an bar
ta.
Wata an kore ta har ita har
‘ya’yanta.
Wasu wajen haihuwa suke samun
cuta.
Ta yoyon fitsari akwai da yawan
mata.
Wasu an sake su don sun furta.
Bin tsarin gaskiya da cancanta.
Wajibi ne a kanmu mu gaggauta.
Mu nemo wa kanmu mafita.
Domin a yau lamari ya gawurta.
A na ta take haƙƙin mata.
Shin ina za mu mu nemo mafita.
(Sa’adatu Ahmad: Waƙar Muryoyin Zuci)
Lalle tabbas marubuciya Sa’adatu
Ahmad ta fito da matsalolin da mata ke fuskanta a wannan zamani, wanda dole ne
mata su tashi tsaye su ƙwato
haƙƙinsu su kuma nemo wa kansu
mafita. Ta yi magana a kan wahalhalun da mata ke fama da su na aikace-aikacen
gida duk da ba su samun kulawa ga lafiyarsu, da matsalolin cututtuka iri-iri da
mata ke fama da su a sanadiyar haihuwa ko zamantakewar aure irin su hawan jini
da cutar yoyon fitsari, ga take haƙƙinsu
da ake yi duk da Musulunci ya buƙaci
a tausaya wa mata ba a azabtar da su ba, a sauƙaƙa musu ba
a wahalar da su ba, Maƙera,
(2017:30). Ana amfani da al’ada ne kawai ana jibga musu ayyuka, kuma ana hana
su yin ƙorafi. A
ganin Maƙera idan
aka ga miji na wulaƙanta
matarsa a tabbata ya jahilci Musulunci, haka idan aka ga uba yana wulaƙanta ‘yarsa mace a tabbata ya
jahilci Musulunci.
Ita kuwa Hajiya ‘Yar Shehu ta
fito da matsalar cin zarafin mata da wasu maza ke yi musamman ga matan aure har
ma da ‘yan mata, musamman idan suka gan su a waje sun fito don yin lalura.
Wannan takurawar matsala ce ga mata wadda shugabanni da hukumomi ba su cika ɗaukar mataki a kai ba. ‘Yar Shehu na cewa:
Kan tituna kwararo
lungu da banzaye,
Ya kai shararai gumakai babu
imani.
In sun ga mata na
aure sai su dinga kira,
Ke Binta, ke Hajiya har ma da fige zani.
In an ka sami ta
kirki ba ta tankawa,
In sun ka sami shararu su saɓi Rabbani.
Allah tsare mu da
su amin ku ce jama’a,
Mata maza har da yara masu imani.
To malamai da
sarakai ga wasiƙata,
Na durƙusa
na ba ku don ku gani.
………………………………………..
Domin faɗar Rabbi na ku anka ba kiwo,
Daidai muke
da makafi waɗanda ba su gani.
Ku za ku ja mana
gora har ku kai mu gari,
Ku fitar da
mu daga sharrin nan na shaiɗani.
To shi ya sa na yi
ƙara gunku don ku sani,
Aikinku ne ku tsare haƙƙi na Rabbani.
(Hajiya ‘Yar Shehu: Waƙar Zamani)
Wannan marubuciyar na magana ne
a kan matsalar da mata ke fama da ita ta cin zarafinsu da wasu mazan banza ke
yi wa matan aure a kan hanya musamman da dare idan lalurar fita ta same su. Ana
samun maza masu cafken sunayen mata don su kula su, kuma sukan dace wani lokaci
har su samu irinsu sheɗanu. Ta fito ƙarara ta nuna cewa ƙara ce take yi ga shugabanni don
su kula, kuma su kawo musu agaji a kan wannan cin zarafi da ake yi wa mata,
saboda matsalar tana ci musu tuwo a ƙwarya.
Matsalar
Daƙushe Cigaban Mata
An daɗe ana daƙushe
cigaban mata a fannoni da yawa na rayuwar yau da kullum, saboda wasu dalilai na
daban. Don haka mata na fama da matsalar ci gaban rayuwa da wani lokaci al’umma
ke daƙushewa musamman tauye su da ake
yi wajen neman ilimin ta hanyoyi da dama. Waɗannan
hanyoyi sun haɗa da tusge su daga makaranta da
ake yi ana yi musu aure ba tare da sun ci gaba da karatu ba, da kuma hana su
samun cikakken ilimi don wata manufa da ma talla da ake sa su yi wadda ke
lalalta tarbiyyarsu da rayuwarsu gaba ɗaya. Wani lokaci kuma su ke hana
ci gaban kansu da kansu musamman ta ɓangaren sana’a, domin wasu mata
sun fi son zaman banza. Misali Sa’adatu Ahmad, a waƙarta ta ‘Mu Nemo Mafita’ a
littafin Muryoyin Zuci ta yi kawo
matsalar rashin son sana’a da wasu mata ba su son yi, sai dai su dogara ga wasu
kuma ba su son neman ilimi saboda lalaci, inda take cewa:
Waƙa
zan tsara manufata.
Wacce ta shafi rayuwarmu mata.
A yau babu zancen mu kwanta.
Ko mu tsaya wajen yin wauta.
Mu nemo ilimi a makaranta.
Mu riƙe
sana’a kar mu sangarta.
Walau a daraja muna cancanta.
Sai da ƙarin
ilimi za mu ƙasaita.
(Sa’adatu Ahmad: Muryoyin Zuci)
A nan Sa’adatu ta nuna dalilinta
na tsara waƙa shi ne,
domin ta jayo hankalin mata a kan zaman banza da suke yi ba su neman ilimi ko
yin sana’o’i don inganta rayuwarsu. Ilimi muhimmin abu ne a rayuwar ɗan Adam domin shi ne abin da ke tabbatar da mutuntakar mutum
kuma da shi ne Allah (SWT) ya fifita ɗan Adam a kan sauran halittu,
(Bugaje, 2011). Ita kuma mace mai ilimi tana samun ƙarin daraja da ƙima a idon al’umma har ta yi ƙasaita.
Marubuciyar ta ci gaba da yin
kira ga mata da cewa iliminsu zai taimaki rayuwar mata, inda take cewa:
Ku taho mu mamaye aikin likita
Don mu dinga ceto rayuwar mata
Da aikin shari’a don ƙwato haƙƙin mata
Kar mu tsaya muna ta yin mita
Ilimin addini shi ne kaɗai gata
Mai yawan iso da kyakkyawar fata
Rabbi taimaki rayuwarmu ‘ya’ya
mata.
(Sa’adatu Ahmad: Muryoyin Zuci)
A nan marubuciyar ta nuna cewa
matsalolin mata sai mata kaɗai ke iya warware su, don wani
abu sai mace kamar asibiti da sauran wurare, sannan yin ilimin shari’a ga mata
zai taimaka wajen danniyar da ake yi wa mata a fannin shari’a musamman ta gefen
aure da zamantakewa.
Hassana Sufi ma a cikin waƙarta ta ‘Ilimi’ ta kawo matsalar
talla da wasu iyaye ke jefa ‘ya’yansu a cikin masifa da yarda haƙƙinsu na ba yara ilimi musamman
mata don kwaɗayin abin da bai taka kara ya
karya ba, inda take cewa:
‘Ya’ya fa haƙƙinsu na nan kan iyayensu,
Su sa su hanyar karatu don su san ilmu.
Amma yawancin mu
ba a kula da ‘yan yara,
Tun ba a ce mata ba, sai ta girma ba ilimu.
Sai dai a ce “Zo
ki ɗau tallar, ki je ki yi man,
Mu san abin hid da kunya”, ba batun ilmu.
To” in ba kiy
talla ba, me za a sayi,
Kayan da zan kai ki ɗaki”, ki ji matanmu
Ta gantale, ta
lalace duk a kan titi,
Tallar da
ba ta ƙulla komai, sai yawan jurmu.
(Hassana Sufi: waƙarta Ilimi)
Marubuciyar na nuna yadda talla
da rashin neman ilimi ga ‘ya’ya mata ke zama babbar matsala ga ci gaban rayuwa.
Ta nuna iyaye musamman mata ke hana ‘ya’ya mata neman ilmi saboda tallar da ba
ta ƙulla masu komai in ban da sa su
su lalace su hinjire a sanadiyar talla a tituna.
Sa’adatu Ahmad, ma ta tsoma
albarkacin bakinta a kan talla inda ta ce:
Mu riƙe sana’a don samun nagarta
Kun san wasu da yawa ‘yanmata
Gun talla maza ke mu su cuta.
(Sa’adatu Ahmad: Muryoyin Zuci)
Waɗannan
mata suna cikin sahu na farko a ɓangaren rubutattar waƙa da suka fara rubuce-rubuce a
kan inganta rayuwar mata da magance matsalolinsu da kawo sauyi a kan kallon da
ake yi wa mata a duniya. Ko bayan su akwai ɗimbin
mata da ke rubuta waƙoƙi a harshen Hausa waɗanda ba a jin muryoyinsu balle a san saƙon da suke ɗauke da shi, saboda rashin kulawa da ayyukan mata da al’umma
ke nunawa.
Dukkan misalan waƙoƙin da aka kawo waɗanda mata suka rubuta ne, kuma
suna magana ne a kan matsaloli da matsayin da Allah ya ba mata. Watau dai har
yanzu ciwon mace na ‘ya mace ne domin a cikin waƙoƙin da
mata suka rubuta kaɗai ake iya samun waɗannan matsaloli suna fitowa, ko an samu a na maza sai dai
suka da wa’azi a kan su.
Shawarwari:
·
Zai yi matuƙar
kyau da amfani idan mata marubuta waƙoƙi suka haɗa kansu, suka yi ƙungiya
mai ƙarfi wadda za ta fito da ɗimbin ayyukkansu a fili duniya ta san da su, domin suna ɗauke da hikima da fasaha kila ma fiye da na takwarorin su
maza.
·
Da a ce ana saka waɗannan waƙoƙi da mata suke rubutawa a rediyo kamar yadda ake saka na
maza da kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
·
Ya kamata a fara nazarin waƙoƙin da
mata suke rubutawa a manyan makarantu domin fito da ɗimbin saƙo
da hikimar da ke cikinsu.
·
Ya kamata a samu waɗanda za su tattaro waƙoƙin da mata suka rubuta, domin a fito da su a matsayin babban
kundi ko littafi don madogara, saboda mata ba su cika mayar da waƙoƙin a matsayin littafi ba kamar yadda ake buga na maza,
saboda rashin kuɗi da shawarwari.
·
Ƙwararri da masana su riƙa
dubawa tare da yin gyara ga duk macen da ta ƙoƙarta ta
rubuta waƙa, domin
a samu ci gaba, a kuma ba su ƙwarin
guiwa.
·
A fito da gasa ta musamman ga mata ta rubuta waƙa, kuma a tallafa musu a buga a
matsayin littafi bayan sun yi gyare-gyaren da aka yi musu.
Kammalawa
Muƙalar a kan yadda mata marubuta ke fito da matsayi da
matsalolin rayuwar mata ne a cikin rubuce-rubucen da suke yi na waƙa. daga misalan da aka kawo na
wasu baitoci da wasu mata suka gabatar a cikin rubutattun waƙoƙinsu, za a iya kammalawa da cewa mata suna kallon ‘yan
uwansu mata a matsayin masu daraja da mutunci musamman idan suka kama kansu
kuma suka nemi ilimi tare da riƙa
sana’a domin dogaro da kai da kauce wa wulaƙanta.
Haka kuma muƙalar ta gano cewa mata ne suka
fi fito da matsalolin mata ‘yan uwansu a cikin waƙoƙin da
suke rubutawa don yin gargaɗi ga al’umma da su kansu matan
An kuma kawo shawarwari waɗanda
ake ganin idan an bi su ɗaya bayan ɗaya za a cimma gaci na samun ingantattun litattafai na waƙoƙin da mata suka rubuta, a kuma samu ƙarin ilimi na rayuwa musamman ta
mata da zamantakewarsu da gudummuwar da suke bayarwa ga al’umma. Lalle ruwa na ƙasa, sai da rashin tono.
Manazarta
Ahmad, S. B (2010). Muryoyin Zuci (Waƙoƙin
Hausa).Kano:
Triumph Publishing Company.
Boyd, J. & Mack, B. (1999). The Collected Works of Nana Asma’u, Daughter
of Usman Ɗanfodiyo,
(1793-1864).
Ibadan: Sam Bookman Publishers.
Boyd, J. & Mark, B. (1999). The Caliph’s Sister: Nana Asma’u
1793-1865.Teacher, Poet and Islamic Leader. London: Frank Cass.
Ibrahim, B. (2010). ‘Gudummuwar
Mata A Rubutaccen Adabi’. Kundin Digiri na Uku, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Jibril, S. (1975). ‘The Status
of Women in Hausa Literature’. M.A Thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Mack, B.B. (1981). ‘Waƙoƙin Mata: Hausa Women Poetry in Northern Nigeria’, Ph.D,
Madison: Wisconsin University.
Mack, B.B, (1983). Alƙalami
A Hannun Mata: Waƙoƙi daga Hajiya Hauwa Gwaram da
Hajiya ‘Yar Shehu.
Zaria: NNPC.
Mack, B. B. (2016). Full Circle: Muslim Women’s Education from
the Magrib to America and Back. Patricia Lercin, New York: Routledge/Taylor
and France (UK).
NNPC. (1974). Waƙoƙin Hikima. Zaria.
Omar, S. (2013). Modibbo
Kilo (1901-1976) Rayuwarta Da Ayyukanta (Ta Biyu Ga Nana Asma’u Bint Fodiyo a Ƙarni na 20). Zaria: Ahmadu Bello University Printing Press.
Omar, S. (2014). ‘Yantarun Nana Asma’u Ɗanfodiyo: Tsarinsu da Taskace Waƙoƙinsu.
(B.W) Kamfanin
Zeetma Investment Ltd.
Omar, S. (2021). ‘Fitattun
Malamai Mata na Daular Usmaniyya da Gudummuwarsu a Fannin Rubutacciyar Waƙa a Ƙarni na 19 da 20’. 25th
Inaugural Lecture. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo
University.
Sufi, H. A Cikin Bugaje (2011). Wa’azi a
Rubutattun Waƙoƙin Mata na Ƙarni Ashirin. Kundin Digiri na
Biyu, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Jarida
Maƙera, S. (2017). “Yadda Musulunci Ya ‘Yanta Mace (2),” Filin
Addinnin Musulunci, Shafi na 30. Jaridar
Aminiya. 7/7/2017.
Shirin
Talabijin
1 |
Salima Auwal Jegara |
Mujallar Mata |
NTA Sokoto, |
27/12/2015. |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.