Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia waƙoƙin zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.
ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A
KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU
NA
ALIYU RABI’U ƊANGULBI
A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA
SATUMBA, 2024
BABI NA BIYAR
NAƊEWA
5.1 Kammalawa
Kamar yadda aka gani, sunan wannan aiki, ‘Zuga da Habaici
a waƙoƙin zamani: Nazari
a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhamadu Buhari’. A babi na farko, an kawo
gabatarwa,da bayani a kan manufar bincike, wato manufar da ake son a cimma da
wannan nazari. Wannan shi ya kai mu ga tambayoyin da aka yi a kan gudanar da
wannan aiki. Bayan haka sai aka yi bayani a kan dalilin bincike da muhimmancin
bincike da farfajiyar bincike, da kuma hujjar cigaba da wannan bincike. Akwai
hanyoyin gudanar da bincike da suka haɗa da Ginshiƙan hanyoyi da Tattara bayanai da sauransu.An kawo bayani
a kan hanyoyin da aka bi aka samo waƙoƙin da aka yi nazari da lokacin da aka aiwatar da su. A ƙarshe an kawo
bayani a kan Tarihin mawaƙan da aka yi nazarin waƙoƙinsu da kuma Tarihin Muhahammadu Buhar da kuma ra’in
bincike, wato, ra’in da aka ɗora wannan aiki a
kansa.
A babi na biyu, an nazarci abubuwan da masana da
manazarta da masu ruwa-da-tsaki suka kawo waɗanda suke da
nasaba da wannan bincike, da kuma ma’anonin waɗansu muhimman
batatuwa , domin fayyacewa. An nazarci Littafai da maƙaloli da kundayen kammala karatun digiri na uku da na biyu da na farko daga
jami’o’i da kuma cibiyoyin bincike da ɗakunan karatu daban-daban.Kamar yadda
aka samu wasu bayanan suna da alaƙa da binciken kai
tsaye,waɗansu kuma alaƙar ta nesa ce. Da farko an fara kawo
gabatarwa, da ma’anar zuga da asalinta, da nau’o’in zuga
da zuga a matsayin turke, da kuma zuga a matsayin salon sarrafa harshe da zuga
a matsayin dabarar jan hankalin al’umma da kuma tasirin zuga a zukatan al’umma.
Duk a wannan babi an nazarci Habaici da ma’anarsa daga fahimtar masana da
manazarta , da habaici a matsayin jigo da habaici a matsayin salon sarrafa
harshe da kuma habaici a matsayin salon jan hankali ko dabarar isar da saƙo ga al’umma. Akwai tasirin habaici a zukatan al’umma, da nau’o’in habaici guda tara da suka haɗa da;
Habaici-Gargaɗau da Habaici -Shaguɓau da Habaici- Miƙau da Habaici Sakayau da Habaici-Nunau da Habaici Gama-gari da Habaici-Ƙasƙantau da
Habaici-Kaikaitau.
Har wa yau, an nazarci ma’anar waƙa a fahimtar masana da manazarta da tasirin waƙa ga isar da saƙo ga al’umma, da bambancin waƙa da sauran kafofin isar da saƙo. An nazarci
siyasa a fahimtar masana da manazarta da rabe-rabenta: Siyasar gargajiya da
siyasar zamani (Dimokuraɗiyya), da siyasar jumhuriya ta huɗu da kuma naɗewa.
Babi na uku an yi cikakken bayani akan gudummawar da zuga
ta bayar wajen zuga siyasar Muhammadu Buhari. An nazarci zuga ta fuskar
shugabanci da shugabanni da zuga ta fuskar tallata ɗan takara, da zuga
ta fuskar tallata jam’iyya da zuga ta fuskar zaɓe, da zuga ta
fuskar hana maguɗin zaɓe. Haka kuma akwai zuga ta fuskar hana ha’inci da zuga ta fuskar hana zalunci
da zuga ta fuskar bunƙasa tattalin arziki da zuga ta fuskar
adawa da kuma zuga ta fuskar tsaro da kuma naɗewa.
Babi na huɗu ya tattauna a kan gudummuwar da
habaici ya bayar wajen faɗakarwa kamar haka; habaici ta fuskar
salon isar da saƙo da suka haɗa da gabatarwa, da
habaici ta fuskar mulkin siyasa da habaici ta fuskar kushe shugaba da
shugabanci da habaici ta fuskar kambama jam’iyya, da habaici ta fuskar nagartar
ɗantakara. Akwai habaici ta fuskar adalci, da habaici ta fuskar zalunci da
habaici ta fuskar ha’inci da kuma habaici ta fuskar rashin cika alƙawari, da habaici ta fuskar adawa, da habaici ta fuskar
rashin kishin ƙasa da ya haɗa da bunƙasa aikin gona, da haɓɓaka ilimi da kiwon
lafiya da bunƙasa hanyoyin sufuri da tattalin arzikin
ƙasa. An tattauna a kan habaici ta
fuskar tsaro da habaici ta fuskar yaudara da addin, sannan da naɗewa.
Babi na biyar ya yi bayanin kammalawa ne da sakamakon
bincike da shawarwari da manazarta da kuma ratayen wasu waƙoƙin da aka yi nazarinsu.
5.2. Sakamakon Bincike
An gano cewa zuga da habaici sun yi matuƙar tasirin gaske a cikin siyasar Muhammadu Buhari,
musamman wajen fito da hoton kyawawan ɗabi’unsa da halayensa nagari a fili; waɗanda su ne, suka
jawo hankalin al’ummar Nijeriya har suka zaɓe shi a matsayin
shugaban ƙasar Nijeriya.Waƙoƙin siyasa, waƙoƙi ne da ke ƙunshe da hikimomi da dabarun jawo hankalin al’umma su fahimci saƙon da ake son
isarwa gare su. An gano cewa zuga da habaici sun ba da gudummawa wajen faɗakarwa da jawo
hankalin al’umma suka aminta da zaɓen Muhammadu Buhari, a matsayin mutumin
kirki wanda aka kamanta shi da mutum mai gaskiya da riƙon amana.An yi haka ne domin a cimma manufar da ake son a cimma ta samun
shugaba mai adalci, wanda zai yi mulki da gaskiya da riƙon amana ya bai wa talakawa haƙƙoƙinsu cikin adalci.
Daga cikin nasarorin da wannan bincike ya samu akwai gano
tasirin da zuga da habaici suka yi wajen ƙara fito da kwarjinin
Muhammadu Buhari ta fusakar bayyana wa talakawa kyawawan halaye da ɗabi’unsa na
gaskiya da tausayin al’umma.Wannan ya ƙara cusa soyayyar
Buhari a zukatan mutane har suka kasa ganin laifinsa ko kurakuransa a lokacin mulkinsa,
duk da kasancewar al’umma ba su ji daɗin abubuwan da suka faru na rufe kan
iyakokin Nijeriya da wasu kasashe maƙwabtanta ba.Wannan
mataki da Buhari ya ɗauka ya yi sanadiyar ƙara jefa talakawa cikin mawuyacin hali da ya fi na
gwamnatin da ta gabata kafin gwamnatinsa.
Har wa yau, binciken ya gano nau’ukan zuga uku, nau’o’in
habaici guda tara, waɗanda suka taimaka wajen kambama
Muhammadu Buhari ya samu damar aka zaɓe shi ya yi shugabancin ƙasa. Waɗannan nau’ukan zuga uku da habaici guda
tara da binciken ya yi amfani da su wajen ɗora nazarin wakoƙin siyasa da aka yi wa Buhari sun taimaka wajen ɗaukaka darajar
Muhammadu Buhari da kuma daƙushe karsashin jam’iyyun adawa da su kansu ‘yan adawa.
Haka kuma bisa ga la’akari da fahimtar ma’anonin da
masana daban-daban suka kawo na habaici, ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin ƙirƙiro nau’ukan habaici guda tara waɗanda aka yi amfani
da su wajen nazarin wakokin siyasa da aka rera ma Buhari kamar haka: Habaic-
gargaɗau, da habaici-shaguɓau da habaici-nunau da habaici-miƙau da habaici-sakayau da habaici-ƙasƙantau da habaici- gama-gari da habaici-keɓantau da kuma habaici-kaikaitau.
Wannan bincike ya gano cewa zuga da kirari suna da
dangantaka makusanciya wajen zaburar da wanda ake yi wa waƙa ya aikata ayyukan alheri ga talakawa da kuma karya manufar ‘yan adawa ko
abokan hamayya.Wato zuga da kirari dukkansu suna ɗauke da kalmomin
yabo dangane da kyawawan ayyuka da wasu magabata suka taɓa aikatawa a
lokacin rayuwarsu sai a danganta su ga wanda ake yi wa waƙa domin ya yi koyi da irin waɗannan halaye na kyautatawa ko
jaruntaka.
Dalilin faɗakarwa da gargaɗi da ilmantarwa da
nishaɗantarwa da zuga da habaici suka yi, ya sa ‘yan Nijeriya suka jajirce wajen
zaɓen Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa, sai dai daga
bisani mutane suka riƙa korafe-ƙorafe dangane da yadda Buhari ya nuna gazawarsa ga shawo kan matsalolin da
‘yan Nijeriya suka shiga a sanadiyar mulkin jam’iyyar PDP. A zaton jama’a idan Buhari
ya hau mulki, zai kawo ƙarshen matsalolin da ‘yan Nijeriya suke
ciki. Amma har ya sauka bai iya kawo ƙarshen su ba. Saboda
son da talakawa da wasu ‘yan Nijeriya suke yi masa ya sa ba su ga illarsa ba,
sai dai irin soyayyar da suke nuna masa ta zahiri ta ragu a zukatansu.Wannan ya
harzuka zukatan ‘yan Nijeriya har suna ganin cewa ba Buharin da suka sani ba
ne, musamman a lokacin da suke sauraren waƙoƙin siyasar da mawaƙan siyasa suka rera masa suna kambama shi dangane da kyawawan ɗabi’unsa da
halayensa na gaskiya da riƙon amana.
Wannan bincike ya gano cewa, mawaƙan siyasar zamani suna amfani da zuga da habaici a cikin wakoƙinsu domin su yi gargaɗi ga shugabanni da
‘yan siyasa su gyara miyagun halaye da ɗabi’u marasa kyau domin su kasance
cikin shugabannin da za a iya alfahari da su a fagen mulkin adalci da rikon
amana. A dalilin haka ya sa jama’a suka jajirce wajen jefa ƙuri’unsu suka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa domin ya kawo cigaba ta fuskar bunƙasa zaman lafiya da tsaro da tattalin arziki a Nijeriya. An kuma ga yadda
zuga da habaici suka yi tasirin gaske a zukatan al’umma wajen ƙara ɗaukaka daraja da kwarjinin da Buhari
yake da shi na halitta a zukatan al’mmar Nijeriya, har ma da na ƙasashe masu maƙwabtaka da
Nijeriya. Wato mawaƙa sun kumbura shi suka wanke shi ya
zama fari sal a idon ‘Yan Nijeriya, wanda hakan ya sa mutane suka yi tururuwa
wajen jefa masa ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a 2015.
Saboda tasirin da zuga da habaici suka yi a zukatan ‘yan
Nijeriya ya sa mutane suka sha wuya a lokacin da suka bi dogayen layuka domin
su tabbatar sun zaɓi Buhari. Mawaƙa sun kambama shi har ya kai wasu na ganin Muhammadu Buhari a matsayin
waliyi, wanda shi kaɗai zai iya riƙa Nijeriya ta gyaru, talakawa su samu walwala da wadatar arzikin ƙasa da zaman lafiya.
Binciken ya gano cewa, zuga da habaici sun ƙara fito da darajar mawaƙan siyasar Buhari a fili, har mutane suka san su, kuma suna girmama su saboda
irin hazaka da hikimomin da suka nuna wajen amfani da zuga da habaici cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin mutane su
zaɓi mutum nagari ya jagorance su a shugabancin ƙasa. Da irin wannan dubaru na jawo hankalin masu sauraro ya sa mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka taka muhimmiyar rawa
wajen ƙara cusa ƙaunarsu da sauraren waƙoƙinsu a duk lokacin da suke son nishaɗi. Wato,ta hanyar
amfani da zuga da habaici da mawaƙan siyasar
Muhammadu Buhari suka yi, ya sa suka ƙara samun ɗaukaka da shiga cikin
zukatan ‘yan Nijeriya.
Binciken ya gano mawaƙan syasa suna amfani da zuga da habaici domin su ƙara ɗaukaka darajar wanda suke yi wa waƙa ya ji babu kamarsa
a fagen siyasa.Sanna kuma a wani ɓangaren su ƙasƙanta abokan hamayyar wanda suke yi waƙa domin su tallata ɗankararsu ga jama’a har ya samu
karbuwa.
Wata babbar illar da zaɓen Muhammadu
Buhari ta yi wa al’ummar Nijeriya, kamar yadda binciken ya gano ita ce; na
farko a sanadiyar soyayyar da al’ummar Nijeriya suka nuna wa Buhari, ya sa
jama’a suka yi tururuwa a lokacin zaɓe suka jefa masa ƙuri’unsu ya zamo shugaban ƙasa. Hawan mulkinsa
ke da wuya sai ya fara rufe kan iyakokin Nijeriya da maƙwabtanta domin hana shigowa da abinci da sauran kayan masarufi da mutane
suke amfani da su a yau da kullum. Wannan rufe kan iyakoki ya yi wa al’ummar ƙasar nan
zafi,domin tashin goron zaɓo da farashen kayan abinci da sauran
kayayyaki da ake shigowa da su,suka yi. A sanadiyar haka rayuwa ta yi tsada,
talakawa suka shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi fiye da lokacin mulkin jam’iyyar P.D.P. Abu na biyu shi ne, ƙara farashen man Fetur da Buhari ya yi ya sa zirga-zirga da sufurin kayan
da ake sarrafawa a cikin gida suka tsauwala; rayuwa ta shiga wani hali, wanda
ke cin abinci sau uku a yini ya koma sau biyu ko sau ɗaya a yini. Bugu
da ƙari, tattalin arzikin al’umma ya taɓarɓare jarin ‘yan
kasuwa ya yi ƙasa.Duk waɗannan abubuwa da
aka ambata sun faru a sakamakon zuga da habaici da mawaƙan Muhammadu Buhari suka yi masa, ya sa shi Buharin ya aiwatar da haka, a tunanensamataki
ne na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ya ɗauka.Wannan mataki
da ya ɗauka ya sa aka samu‘ci gaban mai ginar rijiya’, wato, kullum sai ƙara yin ƙasa yake yi, amma ya
ce ya cigaba.
Wata babbar illa da wannan binciken ya ƙara ganowa ita ce, ta ɓangaren ilimi da
tsaro waɗanda suka zama ƙadangaren-bakin- tulu a Nijeriya. Rashin
kula da karatun jami’o’i ya sa ilimi ya fara taɓarɓarewa, ba a
kyautata wa malaman jami’o’i da sauran malaman Firamare da na makarantun gaba
da Firamare. Matsalolin ilmin ‘ya’yan talakawa da abincinsu yana neman ya
buwayi talakawa har wasu suna kasa biya ma ‘ya’yansu kuɗin makaranta
saboda tsadar rayuwa da aka shiga a dalin rufe kan iyakokin ƙasa da ƙara farashin man
Fetur da sauransu. Amma abin ban haushi saboda so da ƙaunar da jama’a sukeyi wa Buhari har ya sauka daga
gadon mulki masoyansa ba su ganin laifinsa, sai dai na maƙarrabansa. Haka su ma iyayen yara ba su ganin laifin Muhammadu Buhari
saboda tsananin son da suke yi masa.Hakan ya kawo wa ilimin ‘ya’yan talakawan Nijeriya
naƙasu; domin an wayi gari uwaye ba su iya
biya wa ‘ya’yansu kuɗin karatu a jam’o’i da sauran makarantu
masu zaman kansu a Nijeriya.
Zuga da habaici a mawaƙan Buhari suka yi amfani da su cikin wakoƙinsu domin tallata shi, sun taka rawa wajen haifar da rashin aikin yi ga
matasa wanda ya haifar da ayyukan ta’adddanci da rashin tsaro a wasu sassan
Nijeriya, musamman yankunan Arewa maso gabas da kuma yankin Arewa maso
yamma.Saboda tasirin da zuga da habaici da mawaƙan siyasar Buhari suka yi amfani da su ya sa talakawa suka yi nadama a ƙarshen mulkinsa domin sun fahimci cewa tsananin kaunar da
suka nuna wa Buhari ita ce sanadiyar faɗawarsu cikin mawuyacin halin tsadar
rayuwar da ba a san iyakarta ba. Sai dai, Allah kaɗai ya bar wa kansa
sani.
Daga ƙarshe binciken ya
gano cewa waƙoƙin siyasa, waƙoƙi ne da ke ƙunshe da hikimomi da dabarun jawo hankalin al’umma su fahimci saƙon da ake isarwa
gare su. Mawaƙan siyasa suna amfani da hikimarsu
wajen jawo hankalin al’umma su fahimci muhimman saƙonni da suke ƙoƙarin isarwa ga
masu saurarensu,domin su jawo hankalin masu jefa ƙuri’a su zaɓi mutum mai kyawawan
ɗabi’u da halaye nagari. Anfahimci cewa,zuga da habaici suna ba da gudummawa
wajen jawo hankalin al’umma su aminta da zaɓen mutum nagari domin
a cimma manufar da ake son a cimma na samun shugabanni masu gaskiya da adalci.
Dalilin haka ya sa ‘yan siyasa suke amfani da mawaƙa wajen faɗakarwa da gargaɗi da kuma ilmantar
da al’umma ta amfani da zuga domin su zaburar da su wajen neman matsayi na
siyasa. Haka kuma suna amfani da habaici domin su samu nasarar jawo hankalin
‘yan Nijeriya su ƙyamaci duk wani mutum da yake neman a
zaɓe shi ya jagoranci al’umma, amma halayensa da ɗabi’unsa ba su ba
da damar a zaɓe shi ba. Wannan dabara ta amfani da habaici wata hanya ce ta tacewa da
rairaye ɓaigurbi daga cikin ‘yan siyasa domin fitar da mutane da suka cancanta su riƙa al’umma a siyasance. Saboda haka ‘yan siyasa su gyara kurakuransu da halayensu
kafin su yi tunanin shigowa fagen siyasa. Idan aka samu haka a fagen siyasa za
a samu siyasa mai tsafta da shugabanci nagari. Wannan binciken ya gano cewa mawaƙan siyasar Muhammadu Bihari sun taka rawar gani wajen faɗakar da al’umma
game da amfanin zaɓen mutum mai gaskiya da riƙon amana, kamar Muhammadu Buhari a 2015.
5.3.Shawarwari
Wannan bincike yana ba da shawara ga ‘yan siyasa su dage
su rungumi mawaƙan Hausa su ba su muhimmanci,domin yin
haka zai taimaka masu su koyi darasi mai muhimmanci dangane da al’amuransu na siyasa,ta
hanyar gyara kurakuransu da ɗabi’unsu. Su zama mutane nagari kafin
su tsaya takarar kowane irin muƙami na siyasa a wannan
ƙasa tamu. Bugu da ƙari su kansu mawaƙan siyasa su ci gaba da amfani da zuga
da habaici domin kambama mutane nagari su tsaya takarar kujerun mulkin ƙasa a matakai daban-daban. Haka kuma su dage wajen jawo
hankalin mutane su fahimci amfanin zaɓen mutum nagari domin a samar da
kyakkyawan mulkin adalci da gaskiya da riƙon amana tsakanin
masu mulki da waɗanda ake mulka cikin sauƙi.Sannan su cigaba
da amfani da habaici a cikin wakokin su domin su naƙasa mutanen da ke adawa da shugabanni masu ɗabi’u nagari domin
su jawo hanklain al’umma su kaurace wa zaɓen ruɓaɓɓun ‘ya siyasa daga
cikin al’umma. Zuga da habaici da mawaƙan suka yi amfani
da su don faɗakar da al’umma da ‘yan siyasa yana taimakawa wajen garzaya ko kambama mutane
su aminta da jam’iyyada ɗan takarar da ake tallatawa gare su
idan ya kasance mai kyawawan halaye ne da ake alfari da su ga kowane irin
shugaba da aka zaɓa.
Haka kuma, ya dace manazarta da ke tafe, su ƙara zurfafa tunani wajen haɓɓaka bincike su samo
wasu hanyoyin da za su taimaka wajen bunƙasa dabarun jawo
hankalin jama’a ta hanyar amfani da zuga da habaici
da mawaƙan siyasasuke yi cikin waƙoƙinsu. Wannan bincike yana ba da shawara
ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkokin siyasa da su tashi
tsaye su ga sun kafa kyakkyawan tubalin gina siyasa mai ɗorewa ta hanyar
amfani da zuga da habaici da mawaƙan siyasa suke yi a
matsayin makamin gyaran ɗabi’un ‘yan siyasa kafin su nemi wata
kujere ta siyasa. Yin haka zai taimaka a sami shugabanni nagari waɗanda za su kawo wa
ƙasa cigaba a siyasance. Ana kira ga
al’umma su ba wa mawaƙan siyasa muhimmanci kasancewar su
malamai ne masu ilmantar da al’umma su fahimci alfanun da ke ƙunshe a cikin harkokin siyasada mulkin siyasa wanda ke
bai wa ‘yan ƙasa dama su shiga a dama da su a gudanar da salon mulki mai bai wa kowa ‘yancin faɗar albarkacin bakinsa. Sannan a ƙara faɗaɗa bincike a kan amfani da zuga da
habaici a cikin waƙoƙin siyasa a
matsayin wasu makamai na yaƙi da ruɓaɓɓun ‘yan siyasa
masu manufar a fasa-kowa –ya rasa a cikin siyasar Nijeriya.Wato, masu mummunar
manufa ta rushe tsarin siyasar Nijeriya da mutane masu gaskiya da riƙon amana irin su Tafawa Ɓalewa da sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakwato suka aza tubalin gininta.A ɓangaren masana
tariri, ya dace su ƙara ƙoƙarin ɗaukar wannan
bincike ya zama abin adanawa domin amfanin na baya, da kuma adana adabin Hausa.
Saboda haka sai an adana wannan bincike za a iya gano cewa, mawaƙan siyasar zamani suna da muhimmanci ta fuskar amfani da zuga
da habaici a cikin wakoƙinsu wajen faɗakar da al’umma da
jawo hankalin ‘ya siyasa su mai da hankali wajen kyautata ɗabi’unsu da
halayensu muddin suna son jama’a su aminta da su. wato, ‘yan siyasa su fahimci
saƙon da zuga da habaicin suke isarwa gare
su domin su gyara kurakuransu. Shugabanci nagari ya dogara ga samun mtane
nagari masu gaskiya da riƙon amana.
1 Comments
Aslm Alkm da fatan alheri ina rokon arziki a taimakeni da wannan aiki na zuga da habaici a wakokin Muhammad buhari zan nazarce shi in saka shi a literature review na ameenumusa12@gmail.com
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.