Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Suka Halatta A Tsakanin Saurayi Da Budurwa

TAMBAYA (191)

Assalamu alaikum maln barka da dare, maln dan Allah inada tambaya, uhm maln anzo min da zancen aure ne to ban bashi amsaba, nayi istikhara to maln wa yafi cancanta ya bashi amsa kasancewar niya fara yiwa magana ba iyaye na ba Idan nice tawace siga zan bashi, sannan maln inaso kamin bayani akan abubuwan da suka  halatta tsakanin saurayi da budurwa

Kamar irinsu hira, saka sutura, kyauta tawa da sauransu da sauran abubuwan da addininmu ya shar'nta. Jazakallahu khayr Allah ya kareka daga makiya da mahassada ya karama lafiya, Amiin.

ABUBUWAN DA SUKA HALATTA A TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Da farko dai indai da gaske yake yanason ya aureki to iyayenki ya kamata ya tunkara akan maganar

Shawarar da Zan baki anan itace ki ci gaba da Addu'ar Istikhara ko da ana gobe Daurin auren kuwa la'akarida Allaah kike bawa zabi. Idan shine alkhairi sai kiga an shafa fatiha dashi akasin hakan Kuma sai kiga Allaah ya baki Wanda ya fi shi

Sannan Kuma kinada damar da Zaki bashi Amsa Kai tsaye la'akarida da ke yake da qudirin zai zauna har tsufa

SIGA:

Zaki iya ce masa kin aminta da soyayyar sa Amman da sharadin zai so ki domin Allaah Kuma don addininki ba don wata Manufar ba

Domin kuwa idan don kyaune to kyau yana qarewa saboda idan babu Larura akwai tsufa Mai gushe kyau Amman shi Addinin ko an tsufa yananan baya canzawa har zuwa a shiga Aljannah (In sha Allaah)

FIRA:

Ya zamana firar da zaku dinga yi kaso 85 cikin 100 ta Addini ce kubar kaso 15 akan abubuwan da suka shafi al'amura na yau da gobe kamar tattaunawa akan dalilan da sike sa saki yake yawaita musamman a rayuwar auratayya ta Bahaushe ku tattauna sosai akan hanyar da za'a bi don a magance hakan don gudun Kuma kada ku fada tarkon da Shaidan yake danawa Ma'auratan

SUTURA:

Kada ki saka suturar da zata fitina imaninsa

Ki dinga lullube jikinki idan kuwa ba Haka ba to Yau da gobe Shaidan zai Yi tasiri domin kuwa idan kuna kasancewa tare ku biyu to Shaidan shine na ukun Ku

Wannan dalilin ne ma yasa ake son a samu Yaro Mai Dan wayau a cikin qannen Budurwa ya zauna a tsakanin saurayin da ita Budurwan dukdai don a bawa shaidan Kunya

KYAUTATAWA:

Ita zuciya tana buqatar Mai kulawa Kuma tana son Mai kyautatawa

Ba saurayi ne kadai zai dinga hidimtawa Budurwa ba, a'a itama ana son ta dinga kyautata Masa

Maqurar kyautatawa juna da zasu yi shine su dinga yiwa juna nasiha akan zamantakewar Rayuwar Addini da Kuma ta Mu'amalar Yau da gobe. Idan sun kammala zance su karanta addu'ar da Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam ya koyar ta tashi daga majalisi (Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu anla ilaha illa anta Astaghfiruka wa atubi ilayka)

Mafi qarancin kyautatawa Kuma shine kyautar bazata

Yazamana baa tambayi juna wata buqata ba Kai tsaye saidai idan ya tashi kawai ki ga yace ga wannan ba yawa domin kuwa ta hakanne Zaki gane cewar idan ya aureki ba Mr. Qanqamo baneba. Kema Kuma ki dinga Yi masa hidima Kamar irinsu snacks haka ko kuma ki hada Masa wani special abinci domin kuwa kowa Yana son a kyautata Masa

Kuma zanso ki qware a fannin girki domin kuwa majority din Maza indai mace ta iya girki to ko da ta Bata musu Rai idan akai auren wannan girkin nata Yana daidaita tareda gusar da fushinsa

Ina roqon Idan akwai alkhairi a zamanku, Allaah ya tabbatar akasin hakan Kuma Allaah ya hada kowa da qaddararsa

Sannan Kuma Ina son amfani da wannan damar don tallata muku sabuwar makarantar da muka bude online Mai suna: MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI

Wallahu taala aalam

Zaku iya bibiyar karatuttukan mu Kai tsaye ta Nan:

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments