Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia Wakokin Zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.

ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

NA

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA

SATUMBA, 2024

BABI NA UKU

ZUGA A WAƘOƘIN SIYASAR MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

3.1 Gabatarwa

Mawaƙan siyasa suna amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu domin su kambama wanda suke yi wa waƙa ya aikata wani abu na bajinta ko alheri. Wato, zuga wata magana ce wadda mawaƙa ke furtawa mai ƙunshe da kalmomin yabo da kirari a cikinta. Ana danganta kalmomin yabon ne da ayyukan bajinta ko ƙwazo da iyaye da kakanni suka aikata a lokacin rayuwarsu da wanda ake yi wa waƙa. ‘Faɗar waɗannan kalmomi na yabo za su zaburar da wanda ake faɗa wa ya aikata wani abu da ba zai iya aikata wa idan yana cikin hankalinsa’. Zuga tana da alaƙa makusanciya da kirari da yabo, domin zuga shi ke ta da kirari ta hanyar amfani da kalmomin yabo dangane da ayyukan alheri da iyaye da kakanni suka taɓa aikatawa a lokacin rayuwarsu. Idan zuga ya haɗu sosai ba ka rasa jin amon kirari a cikinsa ba.Wato dai zuga da kirari ɗan juma ne da ɗan jumai, domin dukkansu ana amfani da kalmomin yabo domin a zaburar da wanda ake yi wa, ya ji cewa, babu wani mutum da ya fi shi a fagen jaruntaka.

Ana amfani da zuga a waƙoƙin sarauta da waƙoƙin maza, irin na dambe da tauri da kokawa da sauransu. Haka kuma ana amfani da zuga a mu’amalar jama’a ta yau da kullum, musamman a lokacin da wata taƙaddama ta shiga tsakanin abokan gaba, sai a riƙa zuga su, su yi faɗa da juna domin su warware renin da ya shiga tsakaninsu. Bugu da ƙari, a fagen siyasa mawaƙan Hausa sun taka rawa wajen amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu domin su kambama shugabanni ko yan takara ko kuma jamaa magoya bayan jam’iyyun siyasa daban-daban su jajirce wajen ganin jam’iyyunsu sun cimma nasara.

Dangane da irin waɗannan bayanai ya sa (Dunfawa, 2004) ya yi ƙoƙarin rarrabe zuga har zuwa gida uku kamar haka; Zuga kumburau da zuga kambamau ko kariyau da kuma zuga ingizau; domin ya fayyace abubuwan da ke sa a yi amfani da zuga cikin waƙoƙin Hausa musamman na siyasa.

Ana zaburar da shugaba ko kambama shi ya aikata wasu muhimman ayyukan raya ƙasa ko ya yi wata kyauta ta fitar hankali wadda da ba don an zuga shi ba da ba zai yi ta ba. Ta hanyar amfani da zuga ne mawaƙan siyasa ke zaburar da shugabanni su aiwatar da ayyukan alheri ga jama’a, musamman a ɓangarori da al’umma suke buƙatar a agaza masu.Misali, akwai ɓangaren samar da ilimi, da agazawa talakawa da takin zamani don bunƙasa noman damina da na rani. Haka kuma akwai ɓangaren kiwon lafiya da samar da magunguna kyauta ga marasa lafiya,da samar da wadataccen ruwansha ga mutanen ƙauyuka da birane. Haka kuma, uwa-uba a samar da ingantattun hanyoyin sufuri don cigaba da bunƙasa kasuwanci,da haɓɓaka tattalin arzikin al’ummar ƙasa.

Mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari sun yi amfani da zuga a lokacin da suke ƙoƙarin jawo hankalinsa ya kula da halin da‘yan Nijeriya suke ciki na matsin tattalin arziki da yunwa da rashin tsaro.Wannan yunƙuri da mawaƙan suka yi, ya yi matuƙar tasirin gaske ga al’umma domin kuwa Muhammadu Buhari ya amsa kiran ‘yan Nijeriya ta hanyar amincewa da ya tsaya takarar shugabancin ƙasa.Manufar Buhari ita ce, ya ƙwato wa ‘yan Nijeriya haƙƙoƙansu da azzaluman shugabanni suka danne masu. Sannan ya yi ayyukan da za su yi wa al’umma amfani ta hanyar samar da ayyukan yi ga matasa don magance zaman banza da ke haifar da ayyukan ta’addanci da sace-sace, da rashin tsaro a Nijeriya. An yi nazari a kan zuga a matsayin dabarar isar da saƙo, wato salon jawo hankali da zuga a matsayin salon sarrafa harshe, da tasirin zuga a zukatan al’umma, da zuga a matsayin tubalin gina waƙa, da zuga a matsayin tubalin gina ayyukakan fasaha da sauransu.

3.2 Zuga a Matsayin salon Jawo Hankali

A tsarin waƙoƙin Hausa, zuga tana taka rawa a matsayinta na salon jan hankali da mawaƙa kan yi amfani da shi wurin isar da saƙo ga jamaa. A duk lokacin da mawaƙi ya yi nufin tsara waƙa, akwai manufar da yake son ya cimma. Wannan manufa ita ce jigon waƙarsa, Saboda haka, wani lokaci mawaƙi kan ƙirƙiri dabaru yadda zai warware jigonsa ya isar da saƙon buƙatunsa ta ƙashin kansa, ko kuma ta wani mutum ya ba su wata buƙata, ko hukuma ta ba su abin da take so a isar ga jamaa. Sarakuna da masu hannu-da shuni da yan siyasa sukan buƙaci mawaƙa su rera masu waƙa domin su faɗakar da al’umma game da wani abu da ya ɓullo domin su fahimtar da su muhimmancinsa gare su.Yahya, (1997, P 13-14) ya bayyana cewa, akan nemi mawaƙa su wayar wa mutane kai idan buƙatar wani abu da ake son su sani ta taso dangane da shirinbunƙasa kiwon lafiya, ko ilimi,ko siyasa. A siyasance, mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari sun yi amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu a matsayin salon isar da saƙo ga jamaa domin su kambama shi ta fuskar kyawawan ɗabi’u na gaskiya da riƙon amanarsa.A lokaci ɗaya kuma, su jawo hankalin masu saurare su fahimci abin da mawakan suke ƙoƙarin isarwa gare su na manufarsa ta hana cin hanci da rashawa, da hana maguɗin zaɓe, da hana ha’inci da zalunci, da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma tsaro, da sauransu idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasar Nijeriya.Misali:-

3.2.1 Zuga ta Fuskar Shugabanci

Shugabanci wani jagoranci ne na al’umma da ake ɗora wa wani mutum ko wasu mutane a gargaiyance ko a siyasance kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Misali; a wannan jamhuriya ta huɗu da muke ciki, mawaƙa da dama sun yi wa Buhari waƙa domin su ingiza shi ya nemi kujerar shugaban ƙasa.

Misali a jumhuriya ta huɗu, wato wannan jumhuriya da muke ciki; mawaƙa daban-daban sun yi waMuhammaduBuhariwaƙa.Sun yi amfani da dabarun zuga don su jawo hankalinsa ya karɓi kiran al’umma na neman sa yatsaya takararshugaban ƙasa.Waɗannanmawaƙa sun ba da gagarumar gudummawa wajen harzuƙa Mhammadu Buhari ya sami ƙarfin guiwar fuskantar abokan adawarsa na wasu jam’iyyoyi, ciki har da jam’iyyar PDP mai mulkin ƙasa.Misali, da yake zuga gwarzonsa,Aminu Alan waƙa ya zuga Muhammadu Buhari, inda yake kiransa “Sarki.” Alan waƙa ya yi haka ne don ya nuna wa jama’a irin kwarjinin da Muhammadu Buhari yake da shi kamar yadda sarakunan ƙasar Hausa suke da shi. Wato, shi mutum ne mai ƙarfin iko a tsarin shugabanci kamar yadda sarki yake da ƙarfin iko a tsarin sarautun gargajiya. Sarki shugaba ne mai martaba a idon al’umma, kuma yana iya sawa a yi, ko a bari.Kamar yadda talakawa ke jin tsoron sarki, haka shi ma Buhari ake jin tsoron sa,sabodayatsare gaskiya da amana cikin al’amurran shugabancinsa.A al’adance duk mutumen da ya kiyaye tsare gaskiya da riƙon amana, doleneajitsoronsa.Kuma yanaiya zartar da hukunci ga marasa gaskiya ko ha’inci.Aminu Alan waƙa,yana cewa:

Ka zama sarki Buhari kai dai sa ai maka,

SNa so a ba ni tamburra in ta buga maka,

Na tabbata da kana mugunta da ba ka haka,

Zamani mai tafi da kowa ba a dari,

Gwanina ba zan wuce ba ni dai sai na faɗi.

  (Aminu Alan waƙa: waƙar APC 2014/2015)

Kalmar sarki tana nufin shugaba wanda aka ɗora wa shugabancin al’umma bisa tsarin sarautar gargajiya.Wannan kalma ta sarki tasamo asali daga macijiyar da aka samu a cikin rijiyar kusugu a lokacin mulkin sarauniya Daurama a Daura.Afolabi, (1969, P. 47),da Hogben, (1967, P. 73), sun tabbatar da samuwar wannan suna daga asalin wannan maciya, bayan zuwan Bayajida a Daura. Sun bayyana cewa, sarki shi ne mafi ƙarfin iko a ƙasar Hausa, wanda ke iya sawa a yi ko a bari. Wannan baiti yana ƙunshe da jigon kambamawa ne;domin mawaƙin ya nuna wa jamaa cewa, Buhari shugaba ne da ke ɗaukar matakin ladabtar da mai laifi kamar yadda sarki ke hukunta duk wanda ya saɓa wa dokar tsarin sarautar gargajiya.

Mawaƙin ya yi amfani da kalmar sarki domin ya yi wa Muhammadu Buhari kwaliyya, ta hanyar amfani da zuga kumburau ta yadda zai jawo hankalin masu sauraro su fahimci saƙon da yake isarwa gare su. Mawaƙin ya bai wa Buhari matsayin da ba nasa ba, inda ya kira shi da suna ‘sarki’ alhali shi ba sarki ba.Wannan wata dabara ce ta isar da saƙo cikin sauƙi ga mutane don su fahimci irin ƙarfin iko da yake da shi kamar na sarki a masarautarsa. Har wa yau, ya yi amfani da wannan salon zuga ne domin ya ƙara kumbura Muhammadu Buhari ya ji cewa babu wani ɗan siyasa da ya kai shi ɗaukaka da daraja a idon duniya. Bugu da ƙari, ya kira shi da suna “sarki”, duk da kasancewa shi ba sarki ba ne. Amma yanayin aikin da sarki ke yi, shi ne ya bai wa Buhari; domin ya zaburar da shi, ya yi koyi da sarakunan gargajiya wajen zartar da hukunci ga masu laifi don ya zama izna ga na baya. Kalmar sarki wani salon kambamawa ce ga Muhammadu Buhari domin ya zuga shi, ya ɗauki girma irin na sarakunan ƙasar Hausa.. Ya ce, dole ne ya buga masa tamburra don ya tada shi daga bacci, kamar yadda ake buga wa sarki tamburra don a ta da shi daga barci,wato ya tsima shi ya aikata hukunci a kan marasa gaskiya kamar yadda sarakunan gargajiya suke yi a lokacin mulkinsu.

A lokacin da aka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa a Nijeriya, ya taras da matsaloli da dama dangane da taɓarɓarewar harkokin ilimi da tsaro da tattalin arziki. An fara samun tsaro da zaman lafiya, musamman a yankunan da ‘yan ta’addar boko haram da ɓarayin shanu suka addaba.Wannan dalili ne ya sa mawaƙin ya ba shi darajar sarki domin ya kambama shi a idon jama’a. Mawaƙin ya kambama Buhari domin ya ƙara himma wajen kawar da duk wani aikin ta’addanci da rashin tausayi da shugabannin jam’iyya mai mulki suka haddasa.Mawaƙin ya sifanta Muhammadu Buhari da “zamani mai tafiya da kowa ba nuna bambanci”,domin ya zuga gwaninsa ta hanyar faɗar wasu ayyuka na raya ƙasa da shugaban ya yi a lokacin da ya riƙa muƙamai daban daban a baya lokacin da ya yi mulkin soja da sauransu. Saboda haka, ya ce, dole ne ya zuga gwaninsa dangane da ayyukan alhairi da ya yi wa talakawansa da kuma farfaɗo da zaman lafiya da tsaro a wasu yankuna na Nijeriya.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kwalliyar ne don ya ƙara ɗaukaka darajarsa da kuma jawo hankalin masu saurare su ɗauki Muhammadu Buhari a matsayin mutumen daya dace ya riƙa Nijeriya. Haka kuma, ya ambace shi da gwarzo kuma jarumi domin ya ɗaukaka darajarsa a idon mutane. Dalilin kiran sa da gwarzo jarumi, musamman saboda da kasancewarsa tsohon soja wanda ya yi gwagwarmayar yaƙe-yaƙe da dama don kare martabar ƙasarsa da sauran jama’ar Nijeriya. Wannan salon isar da saƙo ya yi matuƙar tasirin gaske wajen kumbura ko harzuƙa Muhammadu Buhari domin ya ƙara samun ƙwarin guiwar tsayawa takarar shugaban ƙasa daga jama’ar Nijeriya da suka tabbatar masa cewa, za su kasa, su tsare, su kuma raka duk ƙuri’un da aka jefa don kada a yi masu murɗiya.

Kasancewar Muhammadu Buhari jarumi kuma mai gaskiya da riƙon amana ya sa Alan waƙa ya ba shi matsayin sarki a fagen siyasa. Dalilin da ya sa mawaƙin ya bai wa Buhari muƙamin sarki saboda mutum ne jajirtacce mai hukunta maras gaskiya; saboda shi ya tsare gaskiya da adalci. Kuma yana da haƙuri da tausayin talakawansa.

Idan aka yi la’akari da muƙamai daban-daban da ya taɓa riƙawa a baya, kama daga Gwamnan mulkin soja a jihar Arewa maso gabas (Borno), har zuwa ga muƙamin Minista da kuma shugaban hukumar amintattu ta rarar kuɗin man fetur a lokacin gwamnatin Sani Abacha; sai a ga cewa, Buhari shi ya fi cancanta da a zaɓe shi ya yi shugabancin ƙasa domin ya yi an ga irin takonsa. Dalilin haka ya sa mawaƙin ya kira shi da sunaye irin su sarki da gwarzo da jarumi don ya ƙara zaburar da shi ya aikata ayyukan alheri da ya taɓa aikatawa a baya, idan ya zama shugaban ƙasa.

Shi kuma Ibrahim Yala Hayin banki, a cikin waƙarsa ta jam’iyyar APP a shekarar 2003,yana cewa:

Ga zakaran da Rabbana sarki yan nufa,

Dole a ƙyale maigida koko a rankwafa,

Don haka gar ku ja dashi balle ku zurfafa,

Yau Allah yana a bayan mai gaskiya.

(Ibrahim Yala: Waƙar APP, 2003).

Zakara shi ne namijin kaza, wanda Hausawa ke cewa, “mai neman suna”. Hausawa suna cewa, “Zakaran da Allah ya nufa ya yi cara, ko ana mazuru ana shaho sai ya yi”. Mawaƙin ya yi amani da karin magana ne don ya zuga Buhari a zaɓen 2003, lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar APP. Mawaƙin ya zuga Buhari don ya jawo hankalinsa ya karɓa kiran talakawan Nijeriya da ke nemansa ya zo ya yi shugaban ƙasa. Mawaƙin ya bayyana wa ‘yan adawa cewa, Buhari zaɓin Allah ne, wanda kushe da hassada ba za su hana shi ya zama shugaban ƙasa ba; matuƙar Allah ya ce, ya zama. Saboda haka duk wanda Allah ya ƙaddari ya yi mulki, to jayayya dashi ko zurfafa ƙiyayya gare shi ɓarnar lokaci ne. Hausawa na cewa,”Hassada ga mai rabo taki”, wato idan Allah ya zaɓi Buhari ya zama shugaban ƙasa, to sai ya zama.

Mawaƙin ya yi amfani da salon Zuga kariyau don ya ƙara fito da kwarjinin Muhammadu Buhari a fili ga idon jama’a da sauran ‘yan adawa. Ya harzuƙa shi ya ji ƙarfin guiwar karawa da abokan hamayyarsa ga gwagwarmayar neman shugabancin ƙasa. Wannan zuga da mawaƙin ya yi wa Buhari ya taimaka masa wajen ƙara dogaro ga Allah mai bada mulki ga wanda ya so. Idan Allah ya nufi ka zamo, sai ka zamo, ba wata barazanar ‘yan adawa daza ta hana ka zamowa. Buhari ya zama zakaran da Allah ya nufa ya yi mulkin Nijeriya, saboda gaskiyarsa da riƙon amanarsa ya sa kowa ke kwaɗayin ya zo ya zama shugaban ƙasa.Wato shi kaɗai ne daga cikin ‘yan takara ake sa ran zai kawo sauyin rayuwa ga jama’a, a sami zaman lafiya da tsaro da adalci.

Mawaƙin ya yi amfani da salon zuga kariyau ne inda ya yi wa waƙarsa kwalliya,tare da tsora ta ‘yan adawa domin kada su sake su yi jayayya da Buhari saboda shi Allah ya zaɓo, wato zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Buhari mutum ne kamar sauran mutane, sai dai mawaƙin ya sifanta shi da zakara don ya nuna wa mutane cewa, koyaushe zakara yana ƙoƙarin ya kyautata wana ƙasa gare shi. Saboda haka, yaharzuƙa shi ya jajirce ga neman mulkin Nijeriya domin ya ƙwato wa talakawa ‘yancinsu. Kalmar zakara tana nufin, ”Namijin kaza” wanda ke jure wa duk wata wahala da zai fuskanta wajen kare martaba da mutncin iyalansa. Wannan wani salo ne da mawaƙin ya yi amfani da shi na dabbantarwa don ya yi wa waƙarsa kwalliya, duk da cewa Buhari mutum ne ba zakara ba. Amma saboda ɗabi’ar zakara ta juriya ga kare mutuncin iyalinsa ya sa mawaƙin ya sifanta shi da zakara. Wannan wata dabara ce, ko hanyar jawo hankalinsa ya cire fargaba a zuciyarsa wajen neman shugabancin ƙasa.Domindukwanda ya dogara ga Allah, to ya riƙa babbar igiyar da zai kai ga samun nasara.Saboda haka, Buhari shi ne zaɓin da Allah ya yi wa ‘yan Nijeriya.

Aminu Alan waƙa yayi amfani da zuga ingizau, inda ya nuna wa Buharicewa talakawan Nijeriya a shirye suke su ba da jininsu da martabarsu ga mulkinsa muddin ya yarda ya tsaya takara ashekarar 2015. Wato al’ummar Nijeriya sun shirya sadaukar da rayukansu su zama fansa, idan har Buhari zai jajirce ya tsaya takara. Mawaƙin yana cewa:

Jininmu da martaba tamu

Ya zam fansa a mulkinka.

  (Aminu Alan Waƙa A.P.C.)

Sadaukar da jini da ƙimar mutane wajen ganin haƙa ta cimma ruwa ga neman wani abu da zai amfanesu, ba ƙaramin abu ba ne ga tsarin zamantakewar al’ummar Hausawa. Idan mutum ya kasance mai kyawawan ɗabi’u to jama’a za su so shi, kuma su sadaukar da komi nasu domin ganin sun kare mutuncinsa. Mawaƙin ya zuga Buhari ta hanyar nuna masa yadda mutane suka sadaukar da jininsu da komi nasu domin ya jawo hankalinsa ya sake neman a zaɓe shi ya mulkin ƙasa don ya gudanar da ayyukan alheri da yake gurin aiwatarwa a Nijeriya. Wato,mutanen Nijeriya sun yi alƙawarin sadaukar da jininsu da martabarsu ga Buhari, idan har ya amince ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa karo na biyu. Wannnan magana ta ƙara ingiza Buhari ya jajirce ga niyarsa ta neman shugabancin Nijeriya. Wannan yunƙuri da Buhari ya yina sake tsayawa takara ya sa ‘Yan Nijeriya a tafiyar 2019, suka yarda su ba da jininsu da martabarsu su zama fansa ga mulkin Buhari. Ma’ana ko da za a karkashe talakawan Nijeriya, sai sun zaɓe shi ya shugabanci Najeriya domin talakawa su sami ‘yanci da walwala.

Haka ya sa mawaƙan siyasa suka sami nasarar jawo hankalin mutane suka yarda da ingizawar da aka yi masu na su ba da jininsu da martabarsu domin ganin Buhari ya ci zaɓe. Don haka mawaƙin ya yi amfani da zuga ingizau inda ya ingiza talakawan Nijeriya cewa, su ba da jininsu ya zama fansa a mulkinsa. Zugan da mawaƙin ya yi, ya yi tasirin gaske domin kuwa talakawa da aka zuga ,sun yi ƙoƙarin jajircewa su ga ko tawane hali sun jawo ra’ayin Muhammadu Buhari ya amsa kiran talakawan Nijeriya. Allah (S.W.T.), ya ƙaddare shi da samun nasarar lashe zaɓe a shekarar 2015. Hawansa keda wuya, sai ya fara kakkaɓe zalunci da almundahana da wasu tsirarrun ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati suka yi wa dukiyar al’umma hawan ƙawara. Misali, a tashin farko ya sa aka dawo da dukiyar al’umma da wasu ‘yan tsirarun mutane suka kwashe suka kai ƙasashen waje.

Shi kuma, Ibrahim Yala Hayin banki ya zuga Buhari a zaɓen 2015, inda ya nuna wa jama’a matsayin Muhammadu Buhari uba ga ‘yan Nijeriya. Ya jawo hankalin talakawa dasu fahimci Buhari cewa, shi mutum ne mai gaskiya, wanda ya kira shi da “Gaskiya dokin ƙarfe.” Yana cewa:

Ga Buhari Uba babba,

Jarumi Gwarzo babba,

Janar Buhari mazan fama,

Kin ji gaskiya dokin ƙarfe.

  (Ibrahim Yala: Waƙar APC).

Ubawani mutum ne da ake kira baba a wani yanki na ƙasar Hausa.Wato wanda ya haifi ‘ya’ya maza da mata, ko maza kawai ko kuma akasin haka. Matsayin uba ga ‘ya’ya shi neya kula da lamurransu ta hanyar ba su kariya daga kowace irin fitina. Haka kuma da ɗaukar nauyin cinsu da shansu, har su kawo ƙarfi. Ana son uba ya kasance mai tausayi da adalci da kuma gaskiya da amana tsakanin ‘ya’yansa. Idan aka sami uba mai irin waɗannan ɗabi’u, babu shakka za a sami rayuwa mai inganci a cikin gida da kuma cikin al’umma. Bugu da ƙari, shi uba ya zama mai ƙwazo da jaruntaka wajen tsayuwa ba tare da fargaba baga yaƙi da rashin gaskiya da cin amana. Samun irin wannan uba zai taimaka wajen tafiyar da shugabanci cikin adalci a cikin al’umma, da ma ƙasa baki ɗaya.

Mawaƙin ya yi amfani da zuga kumburau inda ya zaburar da Buhari ta hanyar ambaton sa da kalmomin jarumi da gwarzo da kuma mazan-fama, don ya harzuƙa shi ya cire masa shakku a niyarsa ta neman shugabancin ƙasa daya sa a gaba. Nijeriya tana buƙatar jarumi gwarzo, wanda bai da fargaba ga abin daya yi nufin aikatawa matuƙar dai abin zai amfani al’ummarsa.

A duk lokacin da aka zuga wani mutum,ko shugaba ko ɗan siyasa,zai ji a zuciyarsa cewa ba kamarsa. Don haka duk abin da zai aiwatar na kyautata wa jama’arsa zai tabbatar da bai yi ƙasa a guiwa ba. Irin wannan zuga da aka yi wa Muhammadu Buhari ya ƙara masa ƙarfin guiwar neman kujerar shugabancin Nijeriya don ya kawarda azzaluman shugabanni da suka yi wa arzikin ƙasa tu’annati.Zugayayimatuƙar amfani a cikin tafiyar siyasar Buhari domin ya sami ƙwarin guiwa ga jama’ar Nijeriya wajen zaɓen sa da aka yi a 2015, yahaye kujerar shugabancin ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kwalliya a waƙarsa, inda ya yi amfani da kalmomin zuga kumburau, ya kira Buhari da jarumi, da gwarzo da kuma mazan-fama don ya ƙara masa kwarjini da ƙwaringuiwar jajircewa ga neman kujerar da sai namijin gaske ke iya daurewa wajen neman ta. Ana danganta Kalmar jaruntaka ga barde a fagen yaƙi ko dambe ko wani aikin bajinta.

 To, shikuwa Buhari ai ya yi aikin soja, ya kuma fuskanci yaƙe-yaƙe da dama, inda har ya kai matsayin da yake ba a ga kasawarsa ba. Haka kuma ya nuna ƙwazonsa ga ayyuka daban-daban daya taɓa riƙawa a lokacin da ya yi mulkin soja da bayan ya yi murabus daga aikin soja.Duka kalmomin da mawaƙin ya yi amfani dasu a cikin waƙarsa, sunnuna zuga kumburau ne mawaƙin ya yi amfani da shi domin ya harzuƙa Muhammadu Buhari ya ji ƙwarin guiwar karawa da abokan adawarsa wajen neman kujerar shugabancin ƙasa ba tare da fargaba ba.

Buhari ya kasance abin tsoro ga azzaluman shugabanni da kuma marasa gaskiya da riƙon amana. Saboda haka sai ya sami karɓuwa ga yawancin al’ummar ƙasa da kuma girmamawa saboda tsare gaskiya da riƙon amana da ya nunaa dukkan al’amurran rayuwarsa ta yau da kullum, musamman a fagen tsare dukiyar al’ummada aka ba shi amanar kulawa da ita. Tsare gaskiyarsa da hukunta marasa gaskiya da cin amanar dukiyar ƙasa ya sa mawaƙan siyasa sukakumbura shi, suka kamanta shi da “Fiya-fiya’’ kashe ƙwari. Buhari bai shan inuwa ɗaya da mazambata, dalilin haka ya sa mawaƙa irin su Ibrahim Yala Hayin banki, yake ingiza shi ya tsaya takara domin kawo wa ƙasa cigaba, inda yake cewa:

Sannu Fiya-fiya da ba ka yin murɗiya,

Zo ka kawad da Tanko mai fuskar saniya,

Harda na Babalola mai halin ‘yan giya,

Wanda suke ta ɓata tsarin Nijeriya.

  (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

Fiya-fiya wani magani ne (Chemicals),da ake amfani dashi wajen kashe ƙwari irin su kyankyaso, da kwarkwata da gazunzumi/kuɗin-cizo da sauran ƙananan ƙwari da suke cutawa al’uma. Haka kuma ana amfani dashi wajen kashe ƙwarin da ke addabar ko lalata amfanin gona. Mawaƙin ya zuga Buhari ta hanyar amfani da wannan kalma mai nauyi wadda ta nuna wa masu saurare cewa, ba ƙananan ƙwari kawai ake kashewa da fiya-fiya ba; har ma da manya saboda guba ne.Domin kiran Buhari fiya-fiya da mawaƙin ya yi, ya tabbatar da cewa, shi mutum ne wanda baya raga wa azzalumai masu murɗedukiyar talakawa. Saboda shi baya zalunci, kuma baya ƙyale mai murɗe dukiyar al’umar ƙasa. Don haka mawaƙin ya jawo hankalinsa da ya zo ya kawar da macutan shugabanni irin su Tanko da Babalola na jam’iyyar P.D.P, mai mulki; waɗanda mawaƙin yace, suka ɓata tsarin Nijeriya.Wato cin hanci da rashawa da waɗannan shugabanni suke yi, shi ne mawaƙin yace, suka hana talakawa ‘yancin more wa arzikin ƙasarsu, da walwala. Mawaƙin ya sifanta Tanko da fuskar Saniya,wato, mutum ne mai fuskar saniya, wadda ya ce kowane lokaci ka gan shi, fuskarsa a murɗe take. Wato, mutum ne mai baƙin rai, babu fara’a a fuskarsa. Shi kuwa Babalola, mutum ne mashayin giya, koyaushe a buge yake cikin maye. Saboda haka, ta yaya irin waɗannan shugabanni za su yi abubuwan da za su amfani al’ummar ƙasa. Mawaƙin yayi amfani da zuga kambamaudomin ya harzuƙa Muhammadu Buhari ya karɓi tayin ‘yan Nijeriya domin ya kawar da waɗannan mutane da ya kira Tanko da Babalola, wato, shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo(Babalola),da mataimakinsa Atiku Abubakar (Tanko).

Waɗannan mutane su ne ya ce, sukaɓata duk tsarin da aka yi na hana cin hanci da rashawa da suka jefa ƙasa cikin halin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.A samu mutum wanda zai ceto Nijeriya daga cikin halin da take ciki sai gwarzo jarumin shugaba irin Muhammadu Buhari. Mawaƙin ya kambama Buhari ne,ya yi amfani da zuga kambamau don ya jawo ra’ayinnsa ya amince ya karɓi tayin da ‘yan Nijeriya suka yi masa na neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APP/ANPP, a shekarar 2003 -2007. Mawaƙin ya zuga Buhari don ya zo ya kawar da shugabannin da suka kasa samar da ci gaban ƙasa,sai dai sata da murɗe dukiyar ƙasa da sauran ayyukan fitsara kawai suke aikatawa. Nuna wa ‘yan Nijeriya cewa, Buhari mutum ne wanda baya murɗiya, saboda haka shi ne ya fi dacewa a zaɓa ya yi mulkin Nijeriya. Zuga Buhari ta hanyar amfani da Kalmar fiya-fiya , wato maganin kashe ƙwari don ya tsorata azzaluman shugabanni da suka hana Nijeriya ta ci gaba. Yace Buhari shi ne mai gaskiya da zai iya ceto Nijeriya saboda shi baya murɗiya ga dukiyar al’umma. Don haka ne ya yi amfani da zuga kambamau don ya kwarzanta shi ya karɓa kiran ‘yan Nijeriya;ya tsaya takarar kujerar shugabancin Nijeriya domin ya kawar dasu Tanko da Babalola mazambatan shugabanni da suka jefa ƙasa cikin halin ƙuncin rayuwa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon kwalliya ta fuskar kiran sa da suna fiya-fiya alhali shiba fiya-fiya ne ba.Amma ya yi amfani da salon abuntarwa don ya ba shi darajar abu maras rai a ɗan waƙa na farkon baiti.Wato, ya kira shi da suna ‘fiya-fiya’ don ya tsorata azzaluman shugabanni da kuma kambama shi a idon duniya.Ya nuna cewa, yadda fiya-fiya ba ya raga wa ƙwari, haka shi ma Buhari ba ya raga wa azzaluman mutane da suke satar dukiyar al’umma.Anan mawaƙin ya yi amfani da salon abuntarwa ne don ya ƙarfafawa Buhari guiwa ya yi aikin da fiya-fiya yake yi ba sani, ba sabo idan ya hau ragamar mulki. Muhammadu Buhari mutum ne kamar sauran mutane,sai dai aikinsa irin aikin da fiya-fiya ke yi na ba sani-ba-sabo idan aka fesa shi ga ƙwari.

Shi ma Yusuf Fasaha Kano ya yi irin wannan zuga ingizau ga talakawan Nijeriya na kudu da na arewa domin su amince su zaɓi Buhari a 2015, inda ya kira su da kowa a farka ya bar bacci don kada ‘yan ta’adda su mamaye su. Ya ce matuƙar suna farke ,to, ba za su ƙyale ‘yan ta’adda su zalunce su ba.Mawƙin ya jawo hankalin Buhari da ya zo, ya ceto al’ummar Nijeriya daga mawuyacin halin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki da Nijeriya ta sami kanta a ciki a sanadiyar mulkin ‘ya’yan jam’iyyar PDP a ƙasa.Mawaƙin na jam’iyyar APC yakira jama’ar Nijeriya su zo su zaɓi Buhari mai gaskiya da riƙon amana don ya ceto ƙasa da al’ummarta daga mawuyacin halin da suke ciki. Yusuf Fasaha ya zuga al’ummar kudancin Nijeriya da na arewacinta dasu tashi su bar bacci, su fito su zaɓi Buhari a jam’iyyar APC saboda a gyara ƙasa. Mawaƙin yana cewa:

Un kudu da arewa mu bar bacci,

Ba ma kyale ‘yan ta’adda ba.

Zaɓe na gaskiya dole ne a yi,

Mu dudduƙa ba mu fargaba.

  (Yusuf Fasaha: Waƙar APC jam’iyyar ƙasa,)

 

Nijeriya ƙasa ce mai ƙabilu da yawa da suka fito daga ɓangarorin kudu da arewa.Turawan mulkin mallaka su ne suka cure ta,tazama ƙasa ɗaya, al’umma ɗaya a shekarar 1914, saboda su sami damar gudanar da mulkin mutane cikin sauƙi a shekarar. Turawa sun yi ƙoƙarin haɗa kudanci da arewacin Nijeriya a ƙarƙashin tsarin da Gwamna Lugard ya yi na haɗa kan al’ummomin Nijeriya don samar da ingantaccen yanayin kasuwanci da bunƙasa tattalin arziki, da kuma samar da haɗin kai tsakanin al’ummomi daban- daban da ke Nijeriya a shekarar 1914, (Afolalu: 1969:276). Tun lokacin da aka fara mulkin farar hula a Nijeriya bayan haɗe Nijeriya ta kudu da ta arewa ake gudanar da zaɓuɓɓuka bisa ga kundin tsarin mulki na ƙasa. Kundin tsarin mulki ya ba wa kowane ɗan ƙasa damar ya fito, ya nemi duk wani muƙami da yake so a ƙarƙashin jam’iyyun siyasa. Saboda haka dukkan ɓangarorin Nijeriya, wato, kudu da arewa suna da ‘yancin su haɗa kai, su zaɓi mutumen da suke zato zai yi masu adalci a mulkinsa. Gwamnatoci da suka gabata sun yi ƙoƙarin ganin sun ƙulle igiyar haɗin kan Nijeriya da Turawa suka ƙulla ta hanyar raba daidai ga kujerin neman shugabancin ƙasa.

Da wannan niyya ce mawaƙin ya zuga al’umma dasu bar bacci, su zo a yi zaɓe na gaskiya don a zaɓi shugaba da zai kawar da ayyukan ta’addanci da cin hanci da rashaw a ƙasa. Amma haka ba zai samu ba, sai idan an zaɓi shugaba mai gaskiya da riƙon amana, wanda ba shi da fargaba.

Mawaƙin ya yi amfani da zuga ingizau, inda ya yi amfani da Kalmar “babu fargaba” don ya ƙara ingiza ɗantakarar ya nemi azaɓe shi, ya wakilci al’ummarsa. Kamar yadda mawaƙin ya bayyana, Nijeriya ƙasa ce mai yawan ƙabilu a dukkan bangarorin kudu da arewa. Saboda haka, dole ne mu kasance uwa ɗaya, uba ɗaya don mu cigabada gina ƙasarmu ba tare da nuna bambanci ba. Mawaƙin ya kira dukkan ‘Yan Nijeriya da su fito ƙwansu da kwarkwatarsu ba tare da fargaba ba; domin su zaɓi shugaba nagari mai gaskiya da riƙon amana. Zaɓen shugaba nagari shi ne kaɗai zai iya ceto ƙasarnan daga mawuyacin halin da take ciki da suka haɗa da cin hanci da rashawa da sace-sace da kuma ayyukan ta’addanci wanda ya yi sanadiyar taɓarɓarewar zaman lafiya da tsaro. Haɗin kai abu ne mai muhimmanci a tsakanin al’ummomi daban daban domin ta hanyar haɗin kai ne, ake samun cigaba a kowane fanni na rayuwa.

Dangane da haka ne, ya sa mawaƙin ya gargaɗi ‘yan Nijeriya baki ɗaya da mu haɗa kai a zaɓi mutum mai gaskiya, wato, Muhammadu Buhari. Idan aka zaɓi mutum mai gaskiya shi ne zai ƙwato wa Nijeriya ‘yanci daga hannun azzaluman shugabanni, waɗanda suka ɗaure wa cin hanci da rashawa da ‘yanta’adda gindi suna cin karensu ba babbaka.Mawaƙin ya nuna cewa, idan har ‘yan Nijeriya basu haɗa kai suka zaɓi Muhammadu Buhari ba, to fa jikinsu zai gaya masu. Yana cewa:

In Tu’o fiftin (2015) jiki magayi,

Kowa yai yi ba za mu basshi ba.

  (Yusuf Fasaha:Waƙar A.P.C.)

Abin nufi a nan, shi ne,duk wanda ya ƙi haɗa kai, a zabi Buhari, to jikinsa zai gaya masa domin zai cigaba da shan wuyar da masu mulkin waccan jam’iyya suka jefa mutanea ciki.

Mawaƙin ya yi amfani da salon aron harshen Turanci don ya ƙara burge masu saurare da kuma jawo hankalinsu su fahimci saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Don haka ba za a danne masa haƙƙi ba, yana iya gwagwarmaya ta nemar wa kansa ‘yanci da jama’arsa da kowane harshe ba wai harshen Hausa kaɗai ba.An yi amfani da Kalmar “Two’o fiftin’’,( wato,2015), kamar yadda Turawa ke kiranta.Saboda haka ya yi amfani da wannan dabara ta isar da saƙo a cikin waƙarsa don ya jawo hankalin waɗanda ba Hausawa ba, su fahimci saƙon da yake isarwa ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya dangane da zaɓen da za a yi a shekarar dubu biyu da sha biyar (2015).

3.2.2 Tallata Ɗantakara

Mawaƙan siyasa suna amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu domin su kumbura ‘yan takara tare da tallata su a idon jama’a. Talla tana nufin bayyanar da wata haja ga jama’a domin masu buƙata su saya,ko nuna ta ga jama’a domin ta samu kaɓurwa (Bagery,1934, P. 984).Wato mawaƙan siyasa suna wanke ‘yantakara, ko ‘yan siyasa su kambama su,su fito da su fili ta yadda masu sauraren waƙarsu za su yarda dasu, ba tare da kula da laifukan da suka taɓa aikatawa ba a baya ba, ko suke aikatawa a halin yanzu.Mawaƙan kan wanke ‘yantakara kuma su rangaɗa masu kwalliya tamkar sabuwar amarya;su kuma tallata su ga al’umma don su sami karɓuwa. Wannan zuga da mawaƙan kan yi wa masu neman muƙamin siyasa,wata dabara ceta jawo hankalin ‘yan siyasa su gyara ɗabi’unsu domin su sami karɓuwa ga mutane kafin a tsayar da su kowace irin takara ta siyasa.Misali, Murtala Mamsa yana cewa:

Janar Buhari ikon Allah ka zud da ƙwallukan Nijeriya,

Kun ci zaɓe an murɗe mana hayaniya za mui kai ka tsaya,

Ka hana mu mu ɗau doka a hannu al’ummar Nijeriya,

Lokaci in ya yi Uban kuturu kaɗan ya yi yai mana fariya.

(Murtala Mamsa: Waƙar A.P.C., Gaskiya ta zo).

 

Faɗar da mawaƙin ya yi na zuga Buhari cewa, ikon Allah ne ya nuna mana cewa mawaƙin ya yi amfani da zuga kariyau alayi na farko, da kuma zuga ingizau a layi na huɗudon ya bayyana wa jama’a irin martabar da yake da ita a idon al’umma. Sannan ya ingiza talakawa su jajirce wajen kare ƙuriunsu daga maguɗin zaɓe, wanda ‘ya’yan waccan jama’iyya mai mulki suka saba yi. Saboda haka da zarar aka ce mutum,‘ikon Allah ne’, ana son a nuna buwayarsa ga maƙiyansa ko abokan adawarsa.Mawaƙin ya yi wannan zuga ne tare da tunatar da Buhari cewa, ya ci gaba da riƙe Allah, wanda yin haka zai sa ya sami kariyar Ubangijinsa daga sharrin maƙiyansa da ‘yan adawa.Watoya ce, ya riƙe Allah, domin kowa ya riƙa Allah ba zai yi fargaba ba ga duk abin da yasa a gaba. Kuma riƙe Allah ga dukkan lamurra kan sa maƙiya su kasa taɓuka komi a kan abokin hamayyarsu. Yace,sun ci zaɓe aka murɗe, za su ta da hayaniya,amma Buhari ya hana su ɗauki doka a hannu. Ya ce a zaɓe mai zuwa idan suka ci zaɓe, to, ‘uban kuturu ya yi kaɗan’ ya hana a ba su, wato za su ƙwaci haƙƙinsu da ƙarfi. Kalmar ‘uban kuturu’, a nan tana nuna wa jama’a cewa mawaƙin yana ingiza talakawan Nijeriya da su tashi tsaye su ɗauki kowane irin matakin hana a yi masu maguɗi a zaɓe mai zuwa.Wato,a yi masu yaudara a danne ƙuriun da suka jefa wa Buhari. A zaɓuka da suka gabata anyi masu murɗiya, sannan aka yi masu fariya cewa an kada su .Wannan karo ba za su yarda da haka ba, balle a yi masufariya cewa an yi zaɓe na gaskiya. Mawaƙin ya zuga gwarzonsainda ya kira shi da cewa,’Janar Buhari ikon Allah’, Kalmar ikon Allah wani salo ne na zuga kariyau domin a nuna wa maƙiyansa cewa ya buwaya a fuskance shi ko ta wane hali. A al’adar Bahaushe yakan ji ƙarfi idan aka danganta shi da Mahaliccinsa cewa , Allah yana tare da shi a lokacin da ake kambama ko ingiza shi ya aikata wani abun alheri ko bajinta ko akasin haka.

A fagen siyasa, idan aka danganta mutum ga Mahaliccinsa, yakan ji ƙarfin zuciya wajen aiwatar da ayyukan alheri da aka ingiza shi ko kambama shi. A nan ana son a nuna wa jama’a cewa, shi Muhammadu Buhari mutum ne jarumi, wanda ke da ƙarfin fuskantar duk wata barazana ta ‘yan adawa. Don haka mawaƙin ya zuga Buhari da cewa, ya kau da ƙwallukan Nijeriya don ya tsorata yan adawa. Koyaushe ɗan siyasa ya kasance mai gaskiya ne da taimako wajen tallafa wa talakawa, to, babu shakka zai zama abin so ga mutanensa. Haka kuma duk wani abu da ya nema gare su a ɓangaren buƙatun siyasa ba za su ba shi baya ba. Saboda irin tausayi da gaskiyar da Buhari yake da su sun taimaka masa ga samun karɓuwa a siyasance a zukatan ‘yan Nijeriya. Mawaƙin, a madadinsa da sauran jama’ar ƙasa yake ingiza Buhari ya cire hannunsa wajen hana su ɗaukar matakin hana a yi masu maguɗin zaɓe a zaɓe mai zuwa.Wato,mutanensa su yi tsaye wajen ganin ɗan takararsu ya lashe zaɓe da za a yi a 2015.Mawaƙin ya yi amfani da wannan dabara domin ya isar da saƙonsa ga jamaa su fahimci alherin da ke tattare ga zaɓen ɗan takararsa a matsayin wanda zai shugabanci al’ummar Niijeriya a samu zaman lafiya da cigaban ƙasa. Da wannan zuga ne mawaƙin ya sami nasarar jawo hankalin mutane suka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa a 2015.

.Shi ma Yusuf Fasaha ya yi irin wannan zuga inda ya zuga jama’a don su tabbatar da sun zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jamm’iyyar A.P.C. Mawaƙin yana cewa:

Bana ko da tsiya ko da arziki,

Kan zarenku mun ƙulla gargada.

Mun hau maja motar yaƙi,

A siyasa sai mun yi ga-da-ga.

  (Yusuf Fasaha: Mu bi APC al’ummar ƙasa).

 

Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin zuga ingizau masu nuna tashin hankali ga duk wanda aka faɗa wasu. Wato, cewa da ya yi, “ko da tsiya, ko da arziki,” kalmomi ne da ke nuna wa abokan adawa cewa, babu lalama ko sassauci ga neman abun da suka yi tarayya wajen neman sa. Kuma ko da tsiya, wato tashin hankali, ko da arziki, wato cikin lumana (kwanciyar hankali) ba za su yarda ‘yan adawa su yi galaba a zaɓen da za a gudanar ba. Saboda haka sun hau motar maja,wato sun shiga jam’iyyar haɗaka ta A.P.C. domin su ceto Nijeriya daga mulkin jari-hujja na rashin adalci da jam’iyyar P.D.P mai mulkin ƙasa take yi. Wato talakawa a shiye suke su yi tashin hankali su ƙwato wa kansu yanci; domin sun fahimci ana cuta masu, ana danne masu haƙƙinsu a lokacin zaɓe. Don haka yanzu, sun shiga jam’iyyar APC, domin su kayar da jam’iyyar PDP mai mulki a zaɓe na tafe. Wannan baiti yana ɗauke da saƙon faɗakarwa ne ga jama’ar Nijeriya baki ɗaya, cewa mutane sun gaji da baƙin mulkin zalunci na jam’iyyar PDP, domin shugabanninta sun kasa kyautata wa al’ummar Nijeriya.

Salon mulkin jam’iyyar PDP, ya yi kama da mulkin kama-karya irin na ‘yan jari-hujja. A dalilin haka ya sa ‘yan Nijeriya suka ƙosa da wannan mulkin na jamiyyar PDP.Don haka ko ta wane hali, talakawa suna son canji, domin a sami farfaɗowa daga mawuyacin halin da ƙasar nan take ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin zaman lafiya, musamman a wasu yankuna na Nijeriya. Mawaƙin ya yi amfani da kalmomi na gwagwarmaya da ‘yan raɗin kawo sauyi a salon mulkin Nijeriya suke amfani da su.Kalmomin su ne, ‘ko da tsiys, ko da arzik’, babu gargagada, sai mun yi ga-da-ga. Wato, kalmomi ne da ke nuna a yi fito-na-fito da gwamnati ko wata hukuma da take yi wa talakawa rashin adalci ga mulkinta. Saboda haka amfani da waɗannan kalmomi da mawaƙin ya yi cikin waƙarsa yana harzuƙa talakawa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin su ƙwato wa kansu yanci ta hanyar jefa ƙuria.Wannan salo na zuga da mawaƙin ya yi amfani da shi, wata dabara ce ta isar da saƙo ga talakawa don su harzuƙa su shiga jam’iyyar A.P.C.,wadda Muhammadu Buhari yake takarar kujerar shugabancin ƙasa a inuwarta.

Ibrahim Yala ya zuga Muhammadu Buhari da ya fito ba tare da fargaba ba, ya nemi shugabancin ƙasa domin shi ya fi dacewa, kuma talakawan Nijeriya shi suke jira ya fito domin su nuna ƙaunar da suke yi masa a zahiri. Mawaƙin yana cewa:

Ka zama jinjirin wata kai ne ake jira,

Rana ta fito ta riga ta gagara,

Dutse ka wuce bubu koko tokara,

Har mai gatari Muhammad zai juriya,

  (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

Wannan ɗan waƙa wani saƙo ne na kambama Muhammadu Buhari da mawakin ya yi amfani da zuga kumburau domin ya zaburar da wanda yake yi wa waƙa, ya nuna wa jama’a irin kwarjininsa a fagen siyasa. Mawaƙin ya faɗakar da mutane game da kwarjinin Muhammadu Buhari,wanda ya ce, ya fi sauran ‘yan takara soyuwa ga jam’ar ƙasa.Wannan saƙo ne mai muhimmanci mawaƙin yake isarwa ga mutane domin su zaɓi Muhammadu Buhari ya yi shugabancin ƙasa.Mawaƙin yana tallata Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC,ga jama’ar Nijeriya domin su zaɓi jam’iyyar da Muhammadu Buhari ke takara a ƙarƙashin inuwarta. Ya bayyana matsayin Buhari ga ‘yan siyasa tamkar jinjirin wata ne, wanda jama’a ke murnar ganin sa.Haka kuma, ya kira shi da rana, da dutse, waɗanda ya kwatanta darajarsu da Buhari a idon jama’a. Mawaƙin ya yi amfani da zuga kumburau don ya kambama gwarzonsa ya amshi kiran ‘yan Nijeriya na tsayawa takarar shugaban ƙasa a inuwar jam\iyyar A.P.C. Ya yi amfani da salon abuntarwa ne domin ya yi wa waƙarsa kwalliya ta yadda zai jawo hankalin talakawan Nijeriya su amince su zaɓi Muhammadu Buhari.

Har wa yau,mawaƙin ya yi amfani da salailai daban-daban domin ya jawo hankalin Muhammadu Buhari ya yarda ya tsaya takarar shugaban ƙasa. Haka, su ma jama’a da sauran masu saurare su yarda su zaɓi Buhari a matsayin shugaban ƙasa. Mawaƙin ya yi amfani da salon sifantawa, a inda ya sifanta Muhammadu Buhari da jijirin watan azumi da na salla waɗanda kowa ke jira domin su fara azumin watan Ramadan ko sallah.Haka kuma ya kamanta Buhari da Rana wadda ya ce ta riga ta fito ta gagara tafin hannu ya rufe ta, kamar yadda Buhari ya gagari abokan hamayyarsa. Ya kuma kinayantar da Buhari, inda ya kira shi ‘dutse’ kai tsaye, alhali shi ba dutse ba ne, amma saboda ƙarfinshi da haƙurinsa, ya sa ya sifanta shi da ‘dutse’. Mawaƙin ya yi wannan gami ne domin ya nuna wa jamaa irin ƙarfin da Buhari yake da shi a cikin siyasa, wanda yan adawa ba za su iya jayayya da shi ba.

Amfani da waɗannan kalmomi na jinjirin wata, da Rana da Dutse duk zuga kumburau ne, mawaƙin ya yi amfani da shi, don ya jawo hankalin masu sauraro da shi kansa Muhammadu Buhari su aminta da jam’iyyar APC da manufofinta na kawo wa talakawa sauƙin rayuwa idan ta kafa gwamnati. A cikin wannan zuga akwai zuga kumburau da zuga ingizau da mawaƙin ya yi amfani da su a cikin baiti guda domin ya harzuƙa gwarzonsa ya fito takara, wanda ya ce sauran yan takara ba za su iya jayayya da shi ba. Mawaƙin ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin ya yi wa waƙarsa kwalliya yadda zai ƙayatar da waƙarsa har mutane su fahimci saƙon da yake son su sani. Wannan wata dabarar isar da saƙo ce mawaƙin ya yi amfani da ita don ya jawo hankalin jamaa su fahimci muhimmancin zaɓen Muhamadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa da zai ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da take ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro.

3.2.3. Tallata Buhari da Jam’iyyarsa

Mawaƙan siyasa na zamani, Allah (S.W.A.) ya albarkace su da baiwa wajen iya tallata jam’iyya da ɗan takara su nuna ma jama’a cewa, tasu ita ta fi kowace jam’iyya dacewa da a karɓe ta hannu-bi-biyu.Irin wannan zuga da suke yi wa jam’iyyarsu, shi ke sanya ƙaunar jamiyyar a cikin zukatan masu saurare ko‘yan siyasa. Misali, Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cikin mawaƙan zamani da suka kambamajam’iyyar A.P.C,har ta samu karɓuwa ga‘yan Nijeriya suka goya mata baya har ta kai gaci.Mawaƙin yana cewa:

 

Karen bana maganin zomo,

Bana tabbas lokaci ya yi,

A.P.C. ta riga ta bayyana,

don ta yi maganin ɓera,

Mu bi maja duka talakawa.

Gaba dai gaba dai mu je sat ɗaya,

APC babu gaggawa.

(Kamilu: Waƙar APC,Karen bana maganin zomo).

Wannan baiti yana ɗauke da saƙon tallata jamyyar A.P.C. ga talakawan Nijeriya, waɗanda suke neman sauyin gwamnati mai adalci. Mawaƙin ya yi amfani da zuga ingizau don ya kambama jam’iyyar A.P.C. ta tafi sat, ta shiga kwane lungu da saƙo na ƙasa ta nemi goyan bayan jama’a. Saboda lokaci ya yi da ya kamata su bar tafiyar kowace jam’iyya, su zo su shiga jam’iyyar A.P.C., don su sami sauyin da suke nema. Idan Allah ya nufi bayinsa da rahama, sai ya yi masu mafita ga irin halin da suka samu kansu na tsanani. Saboda haka a yanzu lokacin da talakawa ke jira na canjin gwamnati ya yi; domin ga wata sabuwar jam’iyya ta ɓullo domin ta yi maganin azzaluman shugabannin jam’iyyar P.D.P. masu mulkiirin na jari-hujja a ƙasa.Mawaƙin ya yi amfani da karin magana mai nuna wa mutane matsayin jam’iyyar A.P.C. a cikin jam’iyyu, kamar matsayin kare ne ga zomo. Sai dai mawaƙin ya yi amfani da wannan karin magana domin ya nuna wa mutane cewa, idan sauran jam’iyyu ko jam’iyya mai mulki ta zama zomo mai cutarwa, to yanzu an samu kare wanda zai yi maganinsa. Saboda haka, a yanzu duk abin da Jam’iyyar P.D.P. take yi na rashin tausayin talakawa, to ga jam’iyyar A.P.C. za ta yi maganin ta. Saboda haka mawaƙin ya yi amfani da zuga ingizau domin ya zaburar da jam’iyyar A.P.C. da magoya bayanta su tafi sannu a hankali su nemi shugabancin ƙasa domin jamaar Nijeriya suna bayansu.

Mawaƙin ya zaburar da jam’iyyar A.P.C. ne, domin ya cusa wa jama’a son jam’iyyar a zukatansu ta hanyar kambama ta da ya yi. Mawaƙin ya ce, ‘A.P.C. ta riga ta bayyana’, don ta yi maganin ɓera’.Wato, a nan mawaƙin yana zuga jamiyyar ne dangane da ƙarfin da ta fito da shi. Ta shiga ko’ina da zimmar kawar da azzaluman shugabanni, waɗanda ya kira da ɓera. Bisa ga wannan bayani da mawaƙin ya yi na matsayin A.P.C, ya sa mutane suka fahimci manufar jam’iyyar na kawo sauyi ga tafiyar mulkin Nijeriya. Saboda haka, sai ya ƙara zaburar da jam’iyyar da cewa, ‘ta tafi gaba gaba da niyyarta ba tare da gaggawa ba, domin ta kawo sauyin mulki wanda jama’a za su amfana da shi. Wannan zuga da mawaƙin ya yi wa jamiyyar A.P.C., wani salon kambamawa neda ya yi amfani da shi domin ya faɗakar da al’umma game da shirin da jam’iyyar ta yi na kawo sauƙin rayuwa ga talakawa idan aka zaɓe ta ta kafa gwamnati.

A nan mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen fifiko a layi na farko na baitin, inda ya kamanta kare da zomo. Irin wannan kamance shi ne ake cewa kamancen fifiko, inda kare ya fi zomo ƙarfi. Don haka duk ɓarnar da zomo yake yi, idan ya ga kare, dole ya kauce masa saboda ya fi ƙarfinsa.Wannan dabara da mawaƙin ya yi amfani da ita wajen kambama ko harzuƙa jam’iyyar APC, wani salo ne na jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon jamiyyar APC zuwa ga tallatawa al’ummar Nijeriya. Mawaƙan siyasa suna amfani da karin magana a matsayin dabarar jawo hankalin masu sauraro su ji sha’awa da nishaɗi a cikin zukatansu har su ji a zuciyarsu suna son jam’iyyar.

Kamar yadda ya nuna cikin karin magana da ya ce ‘karen bana maganin zomo’,ya nuna cewa, karin maganar tana jawo hankalin masu saurare su fahimci cewa, duk yadda wani ya kai ga hatsabibanci, to akwai wanda ya fi shi.Don haka hatsabibin zomo, maganinsa hatsabibin kare.Da wannan dabara ce mawaƙin ya yi amfani wajen jawo hankalin jamaa su yarda da jamiyyar APC, cewa ta fi ƙarfin jam’iyyar P.D.P. mai mulki.Wannan dabarar isar da saƙo ta yi tasiri wajen tallata jamiyyar A.P.C., har ta samu karɓuwa ga talakawan Nijeriya suka zaɓi Muhammadu Buhari ya kafa gwamnati a shekarar 2015, a Nijeriya.

Har wa yau Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa a cikin waƙarsa mai suna ‘Runhu an yi furen banza, akuya ba ta je dawa don shi ba’. Mawaƙin ya kumbura ko zaburar da jam’iyyar A.P.C, inda ya nuna wa jama’a cewa, matsayin da jam’iyyar take da shi a yanzu ta wuce a yi mata zagon ƙasa. Yana cewa;

Na san bautar gizo sai boka,

A.P.C ta fi gaban wawa.

(Kamilu:Waƙar APC,runhu an yi furen banza).

 

A wannan baiti mawaƙin yana faɗakar da jama’a cewa, jam’iyyar APC tana da karƙin da ko masu hankali ba za su yi jayayya da ita ba, balle wawaye,(shashasha) maras wayo.Saƙon da wannan baiti yake ɗauke da shi yanafaɗakar da al’umma ne game da matsayin jam’iyyar APC ,wanda mawaƙin ya ce, ta fi gaban wawa ya yi jayayya da ita. Ya yi amfani da zuga kariyau ya kambama jam’iyyar ta hanyar amfani da karin magana don ya kafa hujjar cewa, hassada da kushe ba za su yi wa jam’iyyar komai ba, domin ta riga ta yi ƙarfi wanda ko wawa (shashasha) ta fi ƙarfin ya yi mata zagon ƙasa ko jayayya da ita.Saboda haka sauran jam’iyyu su tsaya matsayinsu,kamar yadda mawaƙin ya ce, ya san ‘bautar gizo sai boka’, wato APC, sai mutanen kirki ke shigar ta ba mutanen banza ba.

Wannan faɗakarwa ce mawaƙin yake yi wa mutane game da amfanin shiga jamiyyar APC, wadda Muhammadu Buhari ke neman muƙamin shugaban ƙasa a inuwarta.Idan aka zaɓi jam’iyyar, to, Buhari aka zaɓa. Saboda haka, mawaƙin yana kira ga jamaa su zo su shiga jamiyyar APC don a kawar da mulkin wawaye marasa kishin ƙasa.

Mawaƙin ya yi amfani da karin magana don ya isar da saƙonsa ga jamaa.Wannan salon amfani da karin magan yana nuna irin matsayin da mawaƙin yake da shi, da ƙwarewarsa ga harshen Hausa.Saboda haka, ba ƙaramar hikima ba ce, a sami mawaƙi yana amfani da karin magana a cikin waƙarsa domin wata dabara ce ta isar da saƙo ga jamaa tare da samar da nishaɗi gare su.Sannan ya yi amfani da kalmar wawa domin ya nuna wa jama’a cewa,hana wa jam’iyyar APC ta kafa gwamnati sai Allah, amma ba wawaye ba.

Yusuf Fasaha Kano,shi ma ya zuga jama’a su shigo jam’iyyar APC, domin a kawar da ‘yan ta’addar da suka addabi ‘yan Nijeriya.Yana cewa:

Malam ya zo salla ta zo,

Canji ya zo al’ummar ƙasa.

‘Yan Nijeriya mu bi APC,

Ba ma ƙyale yan taadda ba.

(Yusuf Fasaha: Waƙar APC).

Wannan baiti da ke sama yuna isar da saƙon faɗakarwa ne ga jama’a a kan manufar jam’iyyar APC mai alamar tsintsiyar share dattin da jam’iyya mai mulki ta samar.Don haka mawaƙin yafaɗakar da al’umma cewa APC ta zo da ƙudurin kawar da duk wata ƙazanta da wasu masu mulki suka kawo a Nijeriya.Ƙazanta da mawaƙin yake nufi ita ce, ayyukan ta’addanci da satar mutane ana yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa da cin hanci da rashawa da sauransu.Mawaƙin yazuga jamiyyar APC da cewa ka da ta yi ƙasa a guiwa wajen kakkaɓe duk wani nau’in ta’addanci da ‘ya’yan jam’iyyar PDP,suka bari ya yi ƙarfi a Nijeriya.

A tunanen mawaƙin shigowar Buhari a cikin jamiyyar APC, wata dama ce da ‘yan Nijeriya suka samuna sauya gwamnati domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa.Saboda haka yana jawo hankalin talakawan Nijeriya su ba da goyon baya su zaɓiBuhari domin a fatattaki ‘yan ta’adda da kawar da cin hanci da rashawa a Nijeriya.Wannan dalili ne ya sa mawakin yake harzuƙa jam’iyyar da magoya bayanta su yi harama domin , ‘malam ya zo salla ta zo, wato,ga jam’iyya ta zo da ‘yan takarar da ya dace, sai tayar da sallah.Ya yi amfani da zuga ingizau domin ya ƙarfafawa yan Nijeriya zukatansu su shigo tafiyar jam’iyyar A.P.C.Mawaƙin yana faɗakar da al’umma don ya tallata manufofin jam’iyyar APC, na kawar da ayyukan ta’addanci da suka ƙi ci, suka ƙi cinyewa a Nijeriya.Saboda haka, abu na farko da wannan jam’iyya za ta yi idan aka zaɓe ta ,shi ne ta kawo zaman lafiya da hana cin hanci da rashawa, sannan ta ci gaba da aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa.

Murtala Mamsa Jos, ya zuga jam’iyyar APC domin ya jawo hankalin magoya bayanta su karɓe ta hannu biyusaboda ita ce, jam’iyyar da za ta ƙwato wa talakawa yancinsu kamar yadda yake cewa:

Ba batu na zuga ba, mai son karo ya zo ga rago a kara,

Ka ji giwa bukkar daji, kin wuce harbi koko tokara,

Sannu maliya ba ki ƙafewa dukkan ruwa a cikinki ya tattara,

Jam’iyyar talakawa APC mun amince ‘yan Nijeriya.

   (Murtala Mamsa: Gaskiya ta zo,APC).

 

A wannan baitin mawaƙin ya yi amfani da hikima wajen isar da saƙonsa na tallata jamiyyar APC, inda ya yi amfani da zuga kumburau don ya nuna wa mutane cewa,jam’iyyar A.P.C.ta yi girman da sauran jam’iyyu ba za su iya karawa da ita ba.Idan akwai mai iyawa, to a bar ya zo su kara a gano wanda zai sha-ƙasa. Saboda Jam’iyyar APC ta zama hamshaƙiya a fagen tara jamaa magoya baya masu faɗaa ji a Nijeriya.Saboda haka, ta wuce a ja da ita.Idan har akwai mai jayayya, to ya zo ga fili-ga- mai-doki a kara a ga wanda zai ji kunya.Mawaƙin ya yi amfani da zuga kumburau inda ya sifanta jamiyyar da Giwa, alokaciɗaya kuma ya kamanta jam’iyyar da Tekun maliya Wannan salon zuga kumburau da mawaƙin ya yi amfani da shi wata kwalliya ce ya yi wa jamiyyar domin ya harzuƙa ta ta ji babu wata jamiyya da za ta iya jayayya da ita. Haka kuma, idan akwai mai son karo, to ya zo ga rago a kara. Mawaƙin ya kambama jamiyyar ne cikin hikima domin ya faɗakar da al’ummar Nijeriya cewa ƙarfin da jamiyyar take da shi ya fi na sauran jamiyyun da ake da su a Nijeriya.Wato ta zama maliya wadda ya ce,ba ta ƙafewa,duk mai son ruwa ya je ya ɗiba ya bar su nan.

Har wa yau, ya kumbura jam’iyyar da cewa, tana da ƙarfi irin na giwa da ya sifanta ta da bukkar daji, wadda ya ce, takan rufe ko danne duk wani abu mai ƙaramin ƙarfi a cikin daji.Saboda haka, a fagen karo sai rago, ɗan akuya ba za ya iya ba.Don haka, duk wata jam’iyya mai jayayya da jam’iyyar APC, ta kama kanta,tun da ta riga ta mamayedukkan sassan ƙasa, kamar yadda giwa ke rufe daji. Kuma dukmai son karo da ita, to ya zo a kara da shi.A nan mawaƙin ya faɗakar da mutane cewa, jam’iyyar ta wuce a kara da ita; domin ko an kara da ita, ba a yi nasara ba. Saboda haka talakawan Nijeriya su rugumi jam’iyyar APC baki ɗaya domin ita ce wadda ta fi dacewa ta mulki Nijeriya.Ya sifanta jam’iyyar da maliya, wato, Teku wadda ruwanta ba ya ƙafewa,sai dai a ɗiba a bari. Wannan kambamawarita ce ake cewa zuga kumburau (Dumfawa,2004, P. 225). Shi kuwa (Dangambo, 2008, P 43) ya kira wannan zuga da kambamawar zulaƙe ce mawaƙin ya yi wa jam’iyyar APC, domin ya yi mata kwalliya ya harzuƙa ta yadda za ta ƙara kwarjini ga ‘yan Nijeriya. A sanadiyar wannan zuga ko kambama jam’iyyar da mawaƙin ya yi,ya sa ta samu karɓuwa ga talakawa suka goya mata baya a zaɓen Muhammadu Buhari a 2015.

Irin ƙarfin da jam’iyyar A.P.C. take da shi, wadda mawaƙin yake faɗakar da al’umma da shi,bai wuce na cewa, jam’iyyar APC, haɗakar wasu jam’iyyu ne masu tarin magoya baya suka amince su cure wuri ɗaya su zama jam’iyya ɗaya domin su yaƙi jamiyyar PDP, mai mulki. Wannan haɗa ƙarfi-da-ƙarfe wuri ɗaya su yaƙi jamiyyar PDP mai mulkin ƙasa, ya yi matuƙar tasiri a tarihin siyasar Nijeriya, inda wasu jam’iyyu suka haɗu suka ka da jam’iyya da ke riƙe da kujerar mulkin ƙasa.Shi ya sa mawaƙin ya kambama ta da cewa, APC jam’iyyar talakawa ce, don haka sun amince su goya mata baya domin a kawar da mulkin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP.Mawaƙin ya yi amfani da salon dabbantarwa,inda ya sifanta jam’iyyar APC, da giwa da rago daga cikin dabbobi. Haka kuma ya yi amfani da salon abuntarwa, a inda ya sifanta ta da Tekun Maliya.

Duk waɗannan dabarun jawo hankali da ya yi amfani da su a cikin baiti ɗaya, sun taimaka wajen jawo hankalin ‘yan Nijeriya su yarda da manufar jam’iyyar APC. Wannan wata dabara ce ta isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita,domin ya jawo hankalin talakawa da ‘yan siyasa da sauran masu sauraro su fahimta da abun da yake so ya isar gare su game da bambancin da ke tsakanin jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun siyasa a Nijeriya.

Murtala ya yi wa jam’iyyar APC kwalliya ta hanyar ba ta darajar Maliya duk da kasancewarta jam’iyya ce, ba Tekun Maliya ba. Ita dai Maliya teku ce matattara ruwa da Allah ya halitta. Tana cikin manyan tekunan duniya da take ɗauke da ruwa, waɗanda ba su da iyakar gani da zurfi. Saboda haka, duk mai son ya ɗebi ruwa ya sha, ko ya yi wani aiki da su, to ya tafi maliya ya ɗebo ya bar su ba tare da ya rage su da komi ba.Mawaƙin ya siffanta jamiyyar APC da maliya don ya kumbura ta bisa ga sauran jam’iyyun siyasa da ake da su a Nijeriya.Wannan salon kwalliya da mawaƙin ya yi wa jamiyyar ya sa mutane suka yi tururuwa suka ba ta goyaon baya har ta amshe mulki ga hannun jamiyyar PDP, a shekarar 2015, ta hanyarr ruwan ƙuriu da mutane suka zuba mata. Wannan dabara ta amfani da salon siffantawa da abuntarwa da dabbantarwa da mawaƙin ya yi amfani da ita wajen isar da saƙo, ta taimaka wa yan Nijeriya cimma biyan buƙatunsu na sauya gwamnati; wadda suka zata za ta fitar da su ƙangin da jamiyya mai mulki a wancan lokaci ta jefa su ciki.Bugu da ƙari mawaƙin ya ƙara zuga jamiyyar da yake yi wa waƙa don ya tallata ta ga alumma.Yana cewa:

Sannu maliya ba ki ƙafewa duk jamaa sun ɗiba sun bari,

Shi manomin ƙauye shi za ya ba mu labarin ɓarnar biri,

Wai ina sunan mugun da yas sai ashana yab bai wa biri,

Mun shiga uku‘yan Nijeriya, ɗan Neja kai ka dafa mana taliya.

(Murtala Mamsa:Waƙar APC, sabuwa ta zo)

 

Wannan baiti yana ɗauke da saƙon gargaɗi ne, domin ya nuna wa talakawa cewa, ya kamata su koyi darasi daga halin da gwamnatin ɗan Neja ta jefa su ciki shekarun da suka gabata.Saboda haka wannan ya zama izna gare su, su sani cewa rashin zaɓen shugabanni nagari, shi ne, ke jefa mutane cikin mawuyacin halin matsin tattalin arziki da rashin tsaro.Yanzu lokaci ya yi da za su kaucewa shiga irin wancan hali da waccan gwamnati ta ɗan Neja, wato gwamnatin mulkin soja ta janar Ibrahim Babangida da kuma gwamnatin jam’iyyar P.D.P, ta Olusegun Obasanjo ta saka su ciki. Saboda haka su zo, su zaɓi Muhammadu Buhari domin ya ceto al’umma daga halin ni-‘yasu da suke ciki.

Mawaƙin ya gargaɗi al’umma ta hanyar amfani da karin magana da yake cewa,’manomin ƙauye shi za ya ba da labarin ɓarnar biri’. Wato, duk irin halin da mutane suka shiga na wahala, ba sai an ce masu su canza gwamnati ba;domin a gare su halin da suke ciki na rashin abinci da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa ya zama jiki magayi. Saboda haka, su ne za su gaya wa sauran mutanen duniya irin ƙuncin rayuwa da suka shiga.Yanzu ya zama cilas su shigo jamiyyar A.P.C. mai manufar taimaka wa mutane ta hanyar samar masu da wadataccen abinci da walwala da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da zaman lafiya.Jamiyyar APC ta zama maliya (Teku),wadda ruwanta ba ya ƙafewa.Mawaƙin ya siffanta jamiyyar APC da wannan Teku don ya jawo hanklin mutane su mara mata baya ta kafa gwamnati,domin a wadata da abubuwan more rayuwa da walwala da tsaro a cikin ƙasa.

Muhimmin saƙon da wannan baiti yake ɗauke da shi, shi ne mawaƙin yana gargaɗin ‘yan Nijeriya su yi wa kansu ƙiyamul laili wajen zaɓen Muhammadu Buhari,wanda zai yi adalci ga al’umma da kuma samar da kwanciyar hali da zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin ƙasa. Saboda haka,yazuga mutane da cewa, yanzu ga mafita ta zo gare su,wato su mara wa jam’iyyar APC baya ta kafa gwamnati don a ceto al’umma daga mawuyacin yanayin rayuwa da wasu shugabanni suka jefa su ciki.Mawaƙin ya yi amfani da salon kinaya domin ya yi wa jamiyyarsa kwalliya ta yadda za ta samu karɓuwa ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya.Ya ba wa jam’iyyar APC darajar maliya kai tsaye domin ya jawo hankalin mutane su shiga jam’iyyar, wadda ya ce maliya ce da ba ta ƙafewa. Ya nuna wa jamaa cewa, ita maliya teku ce wadda ta tara ruwa da kowa zai sha ya kuma yi duk ayyukan tsabtace-tsabtace na muhalli da jiki ba tare da ya rage ruwan da ko tsinin allura ba.Wannan salon kinaya da mawaƙin ya yi amfani da shi, wata dabara ce ta jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da ake so su sani na matsayin jamiyyar A.P.C. a ƙasa.Da wannan salon kwalliya da mawaƙin ya yi wa A.P.C., ya sa ta samu karɓuwa ga al’ummar Nijeriya har ta samu nasarar lashe zaɓe, aka zaɓi Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2015.

3.2.4 Zuga ta Fuskar Gudanar da Zaɓe

Ta hanyar zaɓe ne ake samun damar kafa gwamnati da kowa ke so a lokacin mulkin siyasa, wanda ke halatta wa shugabanni su gudanar da mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada. Talakawa su ne ƙashin bayan kowace tafiyar siyasa, domin su ne masu jefa ƙuria su zaɓi mutanen da suka fi cancanta su jagoranci jama’a. A sanadiyar haka ne, ya sa mawaƙan siyasa suke jajircewa su faɗakar da al’umma muhimancin ƙuriunsu domin ta hanyarsu ne ake zaɓen wanda zai ba wa talakawa ‘yancinsu da kawo cigaba a ƙasa.Kowace jamiyyatana ƙoƙarin ta ga ta sami nasara, talakawa su zaɓe ta.Saboda haka, sai ta nemi mawaƙa su faɗakar da al’umma su yi rijistar katin jefa ƙuria domin ta hanyar katin jefa ƙuri’a ne talakawa za su san alfanun ƙuriunsu wajen zaɓen jam’iyya mai manufar kawo wa ƙasa da al’ummarta cigaba.Waɗannan mawaƙa su ne suka tashi tsaye sunazuga talakawa don su fito ƙwansu-da-kwarkwatarsu su jefa ƙuri’unsu su zaɓi mutumin da suke so don a sami nasarar kafa gwamnati mai tausayin talakawa. Misali, Murtala Mamsa ya yi amfani da zuga ingizau don ya harzuƙa talakawa su fito su jefa ƙuria domin ta hanyar ta ne ake samun yanci,kuma a samu cigaban ƙasa, idan aka zaɓi mutumin da ya cancanta.Malamin yana cewa:

Dole ne mai tarkon tsuntsu ya kau da kai ya bi sa da lalama,

In ya ci da zucci tsuntsu ya gan shi tashi za sui sama,

Dole ne in ya da maɗaci na je na ɗauko mai ƙwaryar zuma,

Jam’iyyar A.P.C, Allah ya ba mu mui kishin Nijeriya.

   (Murtala Mamsa: Waƙar APC,sabuwa ta zo).

A wannan baiti, mawaƙin yana faɗakar da al’umma game da abin da ya faru a wancan zaɓe da aka yi a 2011, inda ake zaton Buhari shi ne ya ci zaɓe, amma aka murɗe. ‘Yan Nijeriya sun yi barazanar su ta da husuma, amma sai Janar Buhari ya hana. Saboda haka a wannan lokaci da za a gudanar da zaɓen 2015, mawaƙin yana zuga talakawa su kula da yadda tafiyar siyasar Nijeriya take, don haka sai sun bi a hankali ba da garaje ba wajen tabbatar da sun fito sun jefa ƙuriunsu ga jamiyyar APC domin su zaɓi Muhammadu Buhari. A wannan lokaci idan sun ci zɓe, to babu wanda ya isa ya hana. Mawaƙin yana cewa, ya gaji da mulkin jam’iyyar P.D.P, saboda haka lokaci ya yi da zai yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. Wato ya zaɓi jam’iyyar A.P.C. domin Allah ne ya kawo ta don a yi kishin ƙasa ta hanyar zaɓen mutumen kirki.An yi amfani da karin magana mai nuna cewa duk abin da mutum yake so, to ya bi shi a hankali har ya cimma nasara.Tashin hankali ko rigima wajen neman haƙƙi bai sa a sami nasara,sai an bi a hankali.An nuna cewa idan mutum ya yi gaggawa wajen neman haƙƙinsa, to komi na iya faruwa abin da ake nema a rasa shi.Saboda haka ya zuga mutane su shiga jam’iyyar A.P.C, wadda Allah ya ba su domin su zaɓi Buhari mai kishin ƙasa da talakawa. Wannan faɗakarwa ta yi tasirin gaske ga zaɓen 2015, wanda a sanadiyar zuga talakawa da mawaƙin ya yi, ya sa mutane suka cire tsoro da fargaba a ransu; suka jajirce suka zaɓi Muhammadu Buhari. Wanna zuga da mawakin ya yi amfani da shi shi ne ake kira zuga ingizau, wanda mawaƙi ke harzuƙa wanda yake yi wa shi ya aikata wani abu da zai amfane shi ko ya amfani alumma ba tare dawani tashin hankali ba.

Mawaƙin ya yi amfani da salon karin magana a cikin wannan baiti mai nuna rashin tsoro da kuma juriya ga gwagwarmayar neman haƙƙi. Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo domin ya ƙarfafa wa alumma zuciya su fito su jefa ƙuria ba tare da fargabar cewa ko sun ci zaɓe ba za a ba su ba.Wannan dabara da mawaƙin ya yi amfani da ita wajen isar da saƙo ta yi tasirin gaske a zaɓen 2015; inda talakawa suka yi tsayin gwamin jaki don su tabbatar da ba a yi masu sakkiyar da ba ruwa ba a zaɓen da suka yi.Shi kuwa Yusuf Fasaha a cikin waƙarsa da ya yi wa APC, don zaɓen 2015, ya gargaɗi ‘yan siyasa da cewa duk wanda ya yi son kai ko abin da zai kawo cikas ga zaɓe, to ba za su bar shi ba.Yana cewa:

In two thausand fifteen, jiki magayi,

Kowa yai yi ba za mu bas shi ba.

Zaɓe na gaskiya dole ne a yi,

Mu dud duka ba mu fargaba.

‘Yan Nijeriya mu bi APC,

Ba ma ƙyale yan taadda ba.

(Yusuf Fasaha: Waƙar APC).

A wannan baiti da ke sama, mawaƙin ya faɗakar da al’umma cewa, akwai zaɓe da za a gudanar a sherar 2015. Saboda haka, kafin a kai ga wancan lokaci ya dace mutane su san jam’iyyar da ta kamata su goya wa baya. An gargaɗi ‘yan siyasa da su tabbatar da an yi zaɓe na gaskiya.Sannan ya gargaɗi ‘ya’yan waccan jam’iyya da kada su yarda su yi wata barazanar hana a yi zaɓe na gaskiya. Idan har suka yi wani yunƙurin tada hankali don kada a yi zaɓe,to mawaƙin ya ce ba za su bas shi ba.An zuga ‘yan Nijeriya ta hanyar yi masu gargaɗi da su bi APC domin ita kaɗai ce jam’iyyar da ta dace ‘yan Nijeriya su zaɓa; wadda za ta yi maganin ‘yan ta’adda da ta’addanci.Saboda haka, yake zuga mutane su bi APC,jam’iyyar mutane masu mutunci.

Mawaƙin yana isar da saƙon faɗakarwa ne game da ‘yan siyasa masu ra’ayin ‘in ba mu muka ci zaɓe ba, tokowa ma ya rasa’.Saboda haka yake faɗakar da al’umma su kula su sa ido ga irin waɗannan mutane, muamman a zaɓe mai zuwa a 2015. An yi haka domin ya zugamutane su yi amfani da ƙuriunsu su nema wa kansu yanci domin a kawar da ayyukan taaddanci a Nijeriya.Mawaƙin ya yi amfani da salon aron kalmomi,inda ya aro kalmomi daga harshen Turanci ya gina cikakkiyar jimla mai ɗauke da muhimmin saƙo zuwa ga alummar Hausawa da sauran mutane da ba su jin harshen Hausa.Saƙon kuwa shi ne faɗakarwa game da zaɓen 2015, da ke tafe a wancan lokaci.Wannan dabara da mawaƙin ya yi amfani da ita ya isar da saƙonsa ga ‘yan Nijeriya su aminta da jam’iyyar APC ya yi matuƙar tasiri a zaɓuka daban daban da aka gabatar a shekarar 2015.

Ibrahim Yala hayin banki ya zuga mutane su fito su yi zaɓe na gaskiya, domin wannan karo ba su yarda a yi masu rinto ba, wato a yi maguɗi ta hanyar zuba ƙuriu ba bisa ƙaida ba..Yana cewa:

Ku zo mu ƙara faɗa masu dai,

Yau ƙasarmu APC muka yi,

In za ai zaɓe a yi gaskiya,

Ba za mu yarda da runto ba,

Nijeriya sai baba Buhari,

Gaskiya dokin ƙarfe.

  (Ibrahim Yala: Waƙar APC 2015).

Wannan baiti da ke sama yana ɗauke da saƙon zuga ingizau inda mawaƙin yake harzuƙa talakawa dangane da zaɓe da za a yi a 2015,wanda ake sa ran wasu jam’iyyu za su yi maƙuɗi.Saboda haka, sai ya yi kira ga talakawa su zo su shiga APC, wadda ya ce duk ita ake yi a Nijeriya.An gargaɗi ‘yan siyasa su yi zaɓe na gaskiya don kada a sami matsalar zaɓen ruɓaɓɓun mutane.Wannan zuga da mawaƙin ya yi wa mutane da su bi jamiyyar APC, wani abu ne da ya nuna cewa, mawaƙin ya damu da cigaban al’ummarsa da ƙasarsa baki ɗaya. A dalilin haka ne yake gargaɗin talakawa su yi watsi da ra’ayin duk wata jam’iyyar da ba ta nufin alheriga jama’a da ƙasa baki ɗaya.Ya hazuƙa su, su shiga APC don a samar da shugaba mai gaskiya da riƙon amana. Ya tabbatar wa talakawa cewa, Nijeriya sai baba Buhari, wanda ya yi wa laƙani da gaskiya dokin ƙarfe.

Mawaƙin ya yi amfani da kalmar runto, wadda ke nufin ƙarin adadin abin da ya wuce abin da aka zata, ko zurewa ga adadin da ake tsammani a samu. Kamusun Hausa bugu na farko (2016, p. 376 ), ya bayyana runto da cewa, rikici ko rashin gaskiya ga harkar kuɗi ko abin da ya shafi zaɓe na siyasa.Haka kuma amfani da wannan kalma ya nuna cewa, mawaƙin ya san harshen Hausa; domin kalmar da ya yi amfani da ita,tana cikin kalmomin da daidaitacciyar Hausa ta yarda da ita..Daga ƙarshe ya yi amfani da salon alantarwa ta haryar ambaton gaskiya da ‘dokin ƙarfe, wanda Hausawa ke cewa, hawan ta sai an shirya’.Kiran Buhari da gaskiya dokin ƙarfe, wata kwalliyar magana ce da mawaƙin ya yi amfani da ita domin ya kwarzanta ko kambama shi ko harzuƙa Buhari a idon mutane. Hausawa sun fassara gasiya da dokin ƙarfe. Wannan yana nuna muna cewa, Muhammadu Buhari dokin ƙarfe ne, wanda hawan sa sai an shirya, wato, mai wuyar hawa idan mutum bai shirya ba. Mawaƙin ya yi amfani da wannan salo don ya jawo hankalin masu sauraro su zaɓi MuhammaduBuhari a zaɓen 2015, domin a samu waraka daga halin da Nijeriya take ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arzikin ƙasa.

Shi Mudassiru Ƙasimu Kano ya zuga jamaa su zaɓi Buhari,yana cewa:

Ranar zaɓe mu zaɓi Buhari.

Koko da za ce sai an biya kuɗi,

Za mu biya mu zaɓi Buhari.

  (Mudassiru: Waƙar mu amshi ruwa).

Wannan baiti da ke sama yana ɗauke da saƙon faɗakarwa ne ta hanyar amfani da zuga talakawa a kan zaɓe, inda mawaƙin ya zaburar da su da cewa, ko da za a sayi ƙuria ne, to a shirye suke su ba da kuɗi su zaɓi Buhari. Saboda haka mawaƙin ya zuga talakawa su yi maguɗi ta hanyar biyan kuɗi ko sadaukar da dukiyarsu domin su zaɓi Buhari. Wannan zuga ya ƙara wa talakawa ƙarfi a zaɓen 2015,domin sun nuna juriya da haƙurin ɓata lokacinsu wajen tsayawa su jefa ƙuriunsu ga Muhammadu Buhari. Wannan zuga ya ƙara faɗakar da mutane su fahimci muhimmancin zaɓen mutum nagari, wanda zai kawo wa ƙasa zaman lafiya da cigaban tallalin arziki.

Har wa yau, wannan baiti ya jawo hankalin masu jefa ƙuri’a su mai da hankalinsu, su sa ido ga yadda ake gudanar da zaɓe domin su hana a yi maguɗin zaɓe.Da yake kira ga talakawa, mawaƙin ya jaddada wa yan siyasa cewa a can baya an yi masu barazana aka kore su daga runfunan kaɗa ko jefa ƙuria. A wannan lokaci kuwa, ko an kore su, ba za su bar wurin ba. Haka kuma ko da kuɗi za a biya a jefa ƙuria, sai sun biya domin su jefa ƙuriunsu ga mutumen da suke so.Wannan wata harzuƙawa ce ko ingiza talakawa su tashi tsaye su ga sun hana a yi maguɗin zaɓe. Wato, ka da su yi ƙasa a guiwa wajen kare ‘yancinsu da daure wa kowane irin yanayi da za su shiga, har sai sun jefa ƙuriunsu ga mutumen da suke so.

Mawaƙin ya yi amfani da salon zuga ingizau domin ya cusa aƙidar soyayyar Buhari a zukatan talakawa cewa, ko da kuɗi za a kashe a yi zaɓe, to sai sun biya domin su zaɓi shugaban da suke so, mai gaskiya da adalci.Wannan salon ƙarfafa zuciya wata dabara ce ta jawo hankalin masu jefa ƙuria da su cire fargaba a zukatansu,don su zaɓi mutumen da ya dace ya shugabanci Nijeriya. Wato Muhammadu Buhari mai gaskiya da ake yi wa laƙabi da dokin ƙarfe.

3.2.5 Zuga ta Fuskar Hana Maguɗin Zaɓe

Maguɗin zaɓe yana nufin yin aringizo ko saka ƙuri’u fiye da yadda ake buƙata a akwatunan zaɓe (Begery,1934). Sannan kuma ana yin maguɗi ta hanyar kange mai haƙƙin jefa ƙuria daga yin abin da sauran jama’a suka aikata, wato a hana wani mutum ya jefa ƙuria domin ka da ƙuriarsa ta taimaka wa jamiyyar adawa ko ɗan takara na jam’iyyar adawa samun nasara. Haka kuma ba da kuɗi domin a zaɓi wanda bai cancanta ba da sace akwatin zaɓe, yin haka, shi ma maguɗin zaɓe ne. Bisa ga waɗannan dalilai ne ya sa mawaƙan siyasa suke amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu domin su zaburar da talakawa su ɗauki matakin hana yin maguɗin zaɓe a lokacin jefa ƙuria. Misali Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana gargaɗin ‘yan siyasa da su yi gaskiya a lokacin jefa ƙuria domin ita gaskiya ta fi ƙarya. Wato mutane su kauce wa yin maguɗin zaɓe, domin rashin gaskiya ga zaɓe shi ke kawo rashin adalci idan aka hau mulki. Mawaƙin yana cewa:

Gaskiya zancenta ya fi wuƙa,

Duk yankawa akwai kaifi.

Adalci maganin ƙarya,

Mun gane duka talakawa.

 (Kamilu: Waƙar APC, karen bana maganin zomo).

 

Misalan da aka kawo a sama dukkansu suna zuga masu zaɓe da su yi tsaye su ga an yi gaskiya wurin jefa ƙuria. Domin ita ce, ke sa a yi adalci ga gudanar da sha’anin mulki. Saboda haka, yake gargaɗin talakawa ta hanyar zaburar da su, su tabbatar da sun hana a yi maguɗin zaɓe a lokacin jefa ƙuria, wanda shi ne ke haifar da mulkin zalunci da rashin adalci ga waɗanda ake mulka. Mawaƙin ya ƙara ingiza talakawa da cewa yanzu talakawa sun gane cutar da ake yi masu a wajen jefa ƙuria ana yin aringizo da taushe masu haƙƙi na hana su jefa ƙuriunsu su zaɓi wanda suke so.Saboda haka yake gargaɗin masu jefa ƙuria da shugabanni da su riƙi gaskiya domin kaifinta ya fi na wuƙa a wajen yanka. Yin gaskiya ga zaɓe, shi zai sa a zaɓi shugaba da ya dace,wanda zai yi wa talakwa adalci da haɓɓaka tsaro da zaman lafiya a ƙasa.

Waɗannan baitoci suna gargaɗi tare da jawo hankalin talakawa da shugabanni cewa su saka gaskiya da tsoron Allah a zukatansu wajen zaɓe domin su zaɓimutum nagarimai gaskiya da riƙon amana ba tare da yin maguɗi ba.Yin maguɗi ga zaɓe yana kawo rashin adalci ga shugabanni a lokacin da suke gudanar da mulki.Idan shugabanni suka yi adalci, to za su yi maganin duk wata rashin gaskiya a tsakanin al’umma, ko tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka.Mawaƙin ya yi amfani da salon kamantawa, inda ya kamanta matsayin gaskiya da ƙarya da adalci wanda ya ce shi ke maganin ƙarya.Ya kuma siffanta kaifin wuƙa da gaskiya,wadda ya ce gaskiya kamar kaifin wuƙa take, duk inda aka yanka za a ji zafinta.Wato, ita gaskiya zafi gare ta kamar kaifin wuƙa. Saboda haka, mawaƙin ya yi amfani da wannan salon kamance ne na fifiko domin ya jawo hankalin masu sauraro, ko masu jefa ƙuria da su tabbatar da sun tsare gaskiya a lokacin da suka je jefa ƙuria. Wannan wata dabara ce ta isar da saƙo ga talakawa ko mutane domin su fahimci irin illar da ke akwai ga yin maguɗin zaɓe.

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da hana maguɗin zaɓe, Ibrahim Yala, a cikin waƙar CPC, da ya yi wa Muhammadu Buhari yana cewa:

Zan yi kiran ku dukkanin ‘yan Nijeriya,

Kar mu bari a sake cutar mai gaskiya,

Ku zo mu tsaya muna da ƙarfin Allah ɗaya,

Kar da mu sake ƙyale PDP tai murɗiya.

   (Ibrahim Yala: Waƙar CPC).

 

Baitin yana ɗauke da saƙon zuga ingizau zuwa ga talakawan Nijeriya baki ɗaya.Mawaƙin ya harzuƙa ‘yan Nijeriya cewa, su jajirce su hana a sake maguɗin zaɓen da aka yi a shekarar 2003 da 2011, inda ANPP da CPC suka ci zaɓe, amma aka murɗe aka ba wa Jm’iyyar P.D.P. To, yanzu zaɓen da za a yi nan gaba, talakawa su yi tsaye su hana a murɗe zaɓe, idan Muhammadu Buhari ya ci, a miƙa masa saboda yin haka shi zai kawo zaman lafiya a ƙasada kuma ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da shugabnnin PDP suka jefa ta ciki.Mawaƙin ya zuga talakawa domin su ɗauki matakin hana a yi murɗiya ga zaɓen da aka saba yi a zaɓuɓɓukan da suka gabata a 2003 da 2011, inda jam’iyyar P.D.P. ta yi wa Muhammadu Buhari na jama’iyyar ANPP da CPC murɗiya.

Mawaƙin ya bayyana wa jamaa cewa, yanzu sun waye, kuma sun dogara ga Allah; wanda shi zai yi masu taimako su lashe zaɓe domin yanzu suna da imanin cewa Allah da suka dogara gare shi, shi ne zai taimake su ba za a yi masu murɗiya ba.Ya kumbura ‘ya’yan jama’iyyar C.P.C.a 2011, da ma jama’ar ƙasa masu raayin kawo sauyi ga mulkin P.D.P, su tsaya su hana a yi murɗiyar zaɓe ta hanyar tsare akwati da sa ido, da kuma su raka akwati zuwa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa don kai sakamako. Ya ce muddin talakawa suka kasa, suka tsare, kuma suka raka,to babu ta yadda za a murɗe masu zaɓe idan sun ci. Mawaƙin ya zuga mutane ne domin su jajirce su ga cewa Muhammadu Buhari mai gaskiya ya kai ga samun nasarar zama shugaban ƙasar Nijeriya.Wato, idan a wancan zaɓe, sun yi sakaci aka murɗe zaɓen da aka wa Muhammadu Buhari, to, a wannan karo sai inda ƙarfinsu ya ƙare.Amma ba za su sake bari a yi masu murɗiya ba. Mwaƙin ya ci gaba da kawo wani baiti inda ya nuna ɓacin ransa ga wancan murɗe zaɓe da aka yi masu,ya ce bana kowa ya ce zai murɗe masu zaɓe, to, ya kuka da kansa; domin za su ɗauki mataki kamar haka:

Bana kowa ya ƙwace zaɓenmu ya tabbabta,

Zai rashin uwa, uba ‘ya’ya har mata,

Har shi kanshi har da mai sa shi ya yo cuta,

Za mu gama da jahili ba ma kauciya.

  (Ibrahim Yala: Waƙar CPC 2011).

 

Mawaƙin ya yi amfani da zuga kumburau don ya harzuƙa talakawa su ɗauki matakin ta’addancin kisan gilla ga duk wanda ya yi barazanar ƙwace akwatin zaɓe da za a gudanar. Idan har aka sake aka ƙwace masu akwatin zaɓe, ko murɗe masu zaɓe, to za su nuna wa ‘yan adawa cewa su ma ba kanwar lasa ba ne.Ya siffanta mai ɗaure wa ‘yan bangar siyasa gindi da jahili; domin ya nuna wa mutane cewa,koyaushe mai ilimi ba ya aiki da son rai, kuma ba ya ɗaure ma ‘yan ta’ada gindi su yi ta’addanci. Saboda haka, duk mai ilimi ba zai iya cuta wa mutane ba ta hanyar danne masu haƙƙi. Jahili kamar yadda mawaƙin ya nuna, shi ne wanda yake bin son zuciyarsa, ya sa a yi abin da zai cuta wa jama’a domin neman biyan buƙatar ransa.Wannan salo ko dabara ta isar da saƙo da mawaƙin ya yi amfani da ita ta taimaka wa talakawan Nijeriya wajen ganin sun ɗauki matakin tsayawa su jefa ƙuriunsu su zaɓi wanda suke so ba tare da an takura masu ba. Har wa yau, Yala ya ƙara da cewa:

Mu bi APC dai al’umma,

ita ce mafutar ‘yan Nijeriya,

2015 mu kasa, mu tsare, mu raka,

INEC babu murɗiya.

  (Yala: Mu bi APC al’ummar ƙasa).

 

Mawaƙin ya zaburar da ‘yan Nijeriya su ɗauki matakin tsare runfunan zaɓe domin su hana a yi murɗiyar ƙuriu ko zaɓen da aka yi, a canza shi a ba jam’iyyar da ba ta ci ba. Saboda haka mawaƙin ya faɗakar da al’umma tare da ingiza su, su ɗauki matakin hana a yi murɗiya ga zaɓen 2015. Wannan ɗabi’a ta yin murɗiyar zaɓe ta samo asali daga jam’iyyun da suka riƙa mulkin Nijeriya a shekarun baya da suka wuce, waɗanda suka kasa aiwatar da ayyukan gina al’umma da ƙasa baki ɗaya, sannan suka so su zarce da mulki ko ta halin ƙaƙa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon aron harshe, inda ya yi amfani da harshen Turanci don ya jawo hankalin waɗanda ba su jin harshe Hausa, su fahimci saƙon da yake son isarwa gare su.Ya yi amfani da kalmar INEC, wato (Independent National Electoral Commission) , domin ya nuna wa jamaa yana da ilimin harshen Turanci, kuma yana iya magana da shi. Wannan dabara ta aron kalmar Turanci cikin waƙarsa ta taimaka wajen jawo hankalin waɗanda ba Hausawa ba, su fahimci saƙon da waƙar take ɗauke da shi.

Mawaƙin ya ci gaba da kawo wani misali dangane da hana maguɗin zaɓe, inda yake kiran matasan Nijeriya cewa kada su sake su bari a yi musu murɗiya a zaɓe mai zuwa. A wannan saƙo mai ɗauke da zaburar da ‘yan Nijeriya, mawaƙin ya ƙara faɗakar da mutane cewa mafi yawan shugabanni da suka kasa aiwatar da ayyukan cigaban ƙasa a lokacin da suke mulki, su ne suka fi aiwatar da murɗiya ko maguɗin zaɓe domin su cigaba da mulki. Mawaƙin ya zuga yan Nijeriya domin a sami mafita ga matsalar maguɗin zaɓe a Nijeriya. Misali Ibrahim Yala yana zuga matasan Nijeriya da su tashi tsaye su ƙwato yancinsu da aka danne masu ta hanyar hana masu aikin yi bayan sun kammala karatunsu. Yana cewa:

Ina kuke rundunar matasan Nijeriya,

Mu tashi mu ƙwaci yanci Nijeriya,

Mata kar ku yarda yau a yi muku murɗiya,

Sai mu zage, mu kai Buhari mai gaskiya.

   (Ibrahim Yala: Waƙar CPC).

 

Wannan baiti yana ɗauke da zuga ingizau don a zaburar da matasan Nijeriya maza da mata su tashi tsaye wajen neman ‘yanci ta hanyar jajircewa su jefa ƙuriunsu a lokacin zaɓe,wanda shi ne zai taimaka a zaɓi shugaba nagari. Kalmomin,‘mu tashi’, ‘mu ƙwaci yanci,mu zage a nan suna nuna cewa, mawaƙin yana ingiza matasa ne su yi yunƙuri su jefa ƙuriunsu ga mutumen da ya dace. Wannan shi ne neman yanci da mawaƙin yake kambama matasa su yi, ba wai su yi taaddanci ba don nema wa kansu yanci. Wannan zuga ya nuna saƙo ne mawaƙin yake isarwa ga yan Nijeriya baki ɗaya, musamman matasa da su tashi su fito su jefa ƙuria, domin da ita ake ƙwatar yanci a lokacin mulkin siyasa. Duk yadda mutane ke fafataka a sami yanci, idan ba a jefa ƙuria aka zaɓi mutumin kirki ba, to ba yadda za a sami ‘yancin da ake nema na walwala da tsaro da zaman lafiya a ƙasa.

Mawaƙin ya zaburar da matasa da su yi rijistar katin zaɓe, wanda zai ba su dama su zaɓi wanda suke so. Idan babu katin zaɓe, to babu yadda za a jefa ƙuria, domin ƙuriarka ita ce yancinka.Saboda haka duk yadda ake son a ƙwaci yanci, idan ba a yi rijista ba, to kuwa an zubar da wannan dama ta ƙwatar yanci a siyasance.Mawaƙin ya zuga matasa maza da mata su zage damtse su ga cewa sun zaɓi Buhari, wanda shi zai ƙwato wa talakawa haƙƙinsu da aka danne, a lokutan baya da masu mulki na jamiyyar PDP,a Nijeriya suka yi.

Mawaƙin ya yi amfani da salon zuga ingizau ne, inda ya zuga ƙungiyoyin matasa, wato, rundunar matasa su tashi su nemi yancinsu ta hanyar zaɓen mutane masu gaskiya da riƙon amana..Runduna tana nufin rukunin jarumai da suka haɗu don su yi wa al’umma ko ƙasarsu aiki ta hanyar yaƙi ko ba da kaririya daga wata barazanar abokan hamayya (Bergery, 1934, P.868). Mawaƙin ya yi amfani da wannan kalma domin ya ingiza matasa ko ya tashe su daga barci su fuskanci gwagwarmayar neman yancin ƙasarsu daga hannun yan kama-karya.Wannan wata dabara ce ta isar da saƙo zuwa ga alumma domin su farka daga barci su tashi su je su yanki katin zaɓe da zai ba su dama su zaɓi wanda suke so ba tare da an tauye masu haƙƙinsu ba.

3.2.6 Zuga ta Fuskar Hana ha’inci

Ha’inci yana nufin tauye haƙƙin mai haƙƙi ko cin hanci da rashawa ko wawure dukiyar al’umma da aka ba wa shugabanni amana. Bargery,(1934,P.436), ya bayyana cewa, ha’inci yana nufin yaudara ce ta kowane fanni na rayuwa da ya shafi tauye haƙƙin wani ko hana masa abin da ya kamata a ba shi. Mawaƙan siyasa sukan yi amfani da damarsu su zuga yan siyasa ko alumma su nemi haƙƙinsu da aka haince su daga shugabanni ko wasu mutane da hulɗa ta haɗa su. A fannin siyasa mawaƙan siyasa kan zuga talakawa domin su yaƙi azzaluman shugabanni, ko masu riƙe da wani muƙami da aka ɗora haƙƙin talakawa a kansu. Misali;

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da ha’inci da shugabanni suke yi, Dauda Kahutu Rarara yana cewa:

Tattali za a yi ba cuwa-cuwa,

Sai kai baba.

Baba ka ƙara ƙwazo,

Kana daɗa kauda cutawa.

  (Dauda Rarara: Waƙar Buhari APC).

Wannan baiti ya zuga shugaba Muhammadu Buhari ne don ya ƙara mai da hankalinsa wajen ganin ya cimma gurinsa na zarcewa ga mulkin shugaban ƙasa a shekarar 2019 karo na biyu.Wannan zuga kumburau ya ƙara wa Buhari ƙwarin guiwar ɗaukar matakin lashe zaɓe domin ya cimma manufarsa ga ceto Nijeriya daga hannun macuta. Mawaƙin yana faɗakar da al’umma a kan manufar Buhari ta zarcewa ga shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin jamiyyar APC, domin ya cika alƙawarin da ya ɗauka na samar da zaman lafiya da tsaro da bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.

Mawaƙin ya harzuƙaBuhari dangane da halayensa na gaskiya da riƙon amana, wadda ya bayyana cewa, shi mutum ne mai gaskiya, wanda ba ya ha’inci,kuma ba ya satar dukiyar al’umma ko cin hanci da rashawa. Saboda haka yaharzuƙa shi ya ƙara ƙwazo ya lashe zaɓe domin ya kau da ‘yan cuwa-cuwa, masu ha’intar al’umma suna wawushe dukiyar ƙasa suna gina kansu da ita.

Dauda Rarara ya yi amfani da salon kamance, inda ya kamanta Buhari da mutanen kirki, masu gaskiya da riƙon amana. Ya nuna cewa Buhari bai yi kama da mutane marasa amana ba. Saboda haka, yana kira ga talakawa su fahimci aƙidar Buhari ta son gaskiya domin su yarda da shi ya cigaba da mulkin shugabancin Nijeriya karo na biyu. Wannan zuga wata dabara ce da mawaƙin ya yi amfani da ita domin ya isar da saƙo ga jamaar Nijeriya baki ɗaya game da kyawawan aƙidodin gaskiya da riƙon amana da sauran kyawawan ɗabi’un Muhammadu Buhari.

Shi ma da yake tofa albarkacin baknsa,Yusuf Fasaha ya zuga ‘yan Nijeriya da su tashi tsaye su zaɓi jam’iyyar A.P.C., domin a kawar da cin hanci da rashawa a Nijeriya.Yana cewa:

Za mu kauda rashawa , cin hanci,

Har zamba ba ma ƙyale yin ta ba.

Yan ƙasarmu sai mun tashi tsaye,

A kudun Arewa sannan mu kai gaci

Mu bi APC, sak ba canji,

‘yan ƙasarmu mun samu lokaci.

  (Yusuf Fasaha: Waƙar mu bi APC,alummar ƙasa).

A baitin da ya gabata a sama mawaƙin ya faɗakar da al’umma game da halin da cin hanci da rashawa da zamba suka jefa ƙasa da alumma cikin wani mawuyacin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Wato, cin hanci da rashawa suna da ma’ana kusan ɗaya, kuma sun kasance tamkar ruwan –dare-game –duniya a Nijeriya. Waɗannan ɗabi’u na shugabanni da sauran masu riƙe da muƙamai aban-aban su ne, suka hana ƙasa ta cigaba ta fannoni da dama.Haka kuma ya zuga, tare da gargaɗin ‘yan Nijeriya, inda yake neman su da su tashi tsaye su yi gwagwarmaya matuƙar suna son su cimma nasara a kawar da muyagun ɗabi’u na cin hanci da rashawa da kuma zambatar dukiyar al’ummar ƙasa. Samun nasara kuma ya dogara ne ga shiga jam’iyyar A.P.C, wadda Muhammadu Buhari ke takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin inuwarta.

Mawaƙin ya faɗakar da al’ummar Nijeriya game da illar da cin hanci da rashawa suka haifar wajen jefa ƙasa cikin mawuyacin halin taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin aikin yi ga matasa da ayyukan ta’addanci. Amma yanzu mawaƙin ya kawo wa Yan Nijeriya mafita, inda yake zuga su da su shiga jam’iyyar A.P.C. su zaɓi Buhari; domin a sami gwamnati mai aalci da riƙon amana. Ya ce, yanzu lokaci ya yi da talakwa za su zaɓi jam’iyya da mutumin da suke so. Haka kuma ya kira ‘yan Nijeriya da su zaɓi Muhammadu Buhari, wanda ake kyautata zaton zai ceto Ƙasa daga halin cin hanci da rashawa da take ciki.

Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin jawo hankali da ke nuna zuga ingizau da ke ingiza mutane su fita jam’iyyar PDP, mai mulki, su shiga jam’iyyar APC; inda ya ce, ‘yan ƙasarmu mu ‘tashi tsaye’. Tashi tsaye a nan yana nufin mutane su ɗauki matakin da duk ya kamata domin a kawar da jam’iyyar da ta kusa halatta ha’inci da cin hanci da rashawaa Nijeriya. Dabarar amfani da kalmar ‘tashi tsaye’, wani salo ne harzuƙa mutane su cire tsoro da fargaba wajen nema wa kansu mafita daga halin da suke ciki. Wanan dabara da mawaƙin ya yi amfani da ita, ta taimaka wajen jawo hankalin ‘yan Nijeriya su fahimci kyakkyawawanaƙidun Muhammadu Buhari na gaskiya da riƙon amana. Haka ya sa jamaa suka jajirce wajen ganin sun sake zaɓen Muhammadu Buhari ya cigaba da mulki daga shekarar 2015 zuwa 2019.

3.2.7. Zuga ta Fuskar Hana Zalunci

Zalunci kishiyar adalci ne.Wato, zalunci shi ne ɗora wani abu ba bisa bagiren da ya dace ba (Ƙamusun Hausa, 2016, P. 1125). A nan idan aka ɗora wani abu ba a bagiren a ya dace ba, alhali kuwa akwai in ya dace, to an yi zalunci.

Mawaƙa suna amfani da baiwar da Allah ya yi masu wajen jawo hankalin masu sauraro su fahimci saƙon da ake isarwa gare su a kan Muhammadu Buhari. A dalilin haka ya sa mawaƙan siyasa, musamman waɗanda suka yi wa Muhammadu Buhari waƙa suke ƙoƙarin yin amfani da zuga domin su zaburar da talakawa ko shi kansa ya ɗauki matakin kawar da zalunci da wasu shugabanni suka aikata a Nijeriya. Misali, Ibrahim Yala yana cewa:

 Don haka zo ka ja mu don kai ne jagaba,

 Mu a ƙasarmu kai muke so yau shugaba,

 In ka riƙa Buhari mu ba ma fargaba,

 Zo ka riƙe mu gar mu kauce daga gaskiya.

  (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya)

 

Ibrahim Yala ya zaburar da Muhammadu B uhari domin ya yi mulkin Nijeriya don a kawar a azalumai da hana ci gaban zalunci a Nijeriya. Mawaƙin ya zuga jam’iyyar A.P.C, da al’ummar ƙasa su ɗauki matakin kawar da mulkin jam’iyyar P.D.P., mai mulkin ƙasa ta hanyar jefa wa Muhammadu Buhari ƙuriunsu. Haka kuma ya ƙalubalanci jam’iyyar da cewa, shin mulkin siyasa suke, koko na soja; domin a tunanin mawaƙin mulkin farar hula yana bai wa kowa ‘yancin walwala. To, amma ga shi salon mulkin da jam’iyyar P.D.P. ta ɗauko ba ya da bambanci da na soja.

Wannan baiti yana ɗauke da saƙon faɗakarwa ne zuwa ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya. Saƙon yana jawo hankalin ‘yan Nijeriya su fahimci cewa salon mulkin da jam’iyyar P.D.P, take yi, ya saɓa wa salon mulkin dimokuraɗiyya, domin shugabannin sun kasa bai wa al’umma haƙƙinsu na dukiyar ƙasa da samar masu da wadataccen abinci da muhalli da kuma tsaro. Sabod haka, mutane su fahimci cewa, wannan hali da suke ciki, Muhammadu Buhari kaɗai zai iya magance matsalar da mutane suke ciki a Nijeriya a sanadiyar zaluncin da masu mulki ke yi.

Mawaƙin yana isar da saƙon jamiyyar A.P.C. ne ga talakawa su zaɓe ta ta kawar da salon mulki irin na soja a cikin rigar dimokuraɗiyya. Wannan faɗakarwa da mawaƙin ya yi wa yan Nijeriya ya taimaka wajen karɓar jam’iyyar A.P.C. da Buhari a Nijeriya domin a sami sauyin salon mulki irin na gaskiya ba mulkin zalunci ba.

Shi ma Kamilu ya zuga mawaƙa yan uwansa da su shigo fagen rera wa Janar Buhari waƙa wadda za ta sa ya ƙara kwarjini ga alumma har a zaɓe shi ya yi shugabancin ƙasa, yadda su ma za su fita daga ƙuncin rayuwa da suke ciki, kamar sauran ‘yan Nijeriya.Yana cewa:

Ku mawaƙan nan ku mu waƙe janar,

In Allah ya yi mu bar ƙunci.

(Kamilu: Runhu an yi furen banza APC).

 

Wannan baiti yana ɗauke da saƙon zuga ingizau tare da gargaɗin mawaƙan siyasa su rera wa Muhammadu Buhari waƙa domin idan ya samu karɓuwa ga jama’a suka zaɓe shi, to su ma za su fita daga mawuyacin halin da jam’iyyar P.D.P. ta jefa ƙasar nan ciki.Mawaƙin yana zuga mawaƙa yan uwansa da sauran mutane ne domin su yi watsi da ra’ayinsu ga jam’iyyar P.D.P, su dawo su shiga jam’iyyar A.P.C., wadda Janar Buhari ke takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin inuwarta. Ya nuna wa jama’a cewa, kowa yana da ‘yanci ya shiga A.P.C., muddin dai yana son a kawar da azzaluman shugabanni da zalunci a Nijeriya.

3.2.8. Zuga ta Fuskar Bunƙasa Tattalin Arziki

Tatttalin arzikin ƙasa yana bunƙasa ta hanyar samar da ,ko inganta hanyoyin kasuwanci a ƙasa. Kowane lokaci aka yi maganar arziki,sai a dubi irin hanyoyin da aka tanada domin bunƙasa shi. Noma da kiwo da suna daga cikin hanyoyi na farko, wato na gargajiya na bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, musamman a ƙasar Hausa, kafin zuwan hanyoyin kasuwanci na zamani. Yan siyasa suna ɗora buƙatunsu na neman shugabanci bisa ga alƙawurran bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar samar da wadatattun kayan aikin gona da kiwo na zamani ga alumma idan sun zaɓe su.Waɗannan alƙawurra ne mawaƙan siyasa ke riƙewa su riƙa tunatar da yan siyasa, alƙawurran da suka ɗauka. Idan jam’iyyar da aka zaɓa ta kasa cika alƙawurran, sai mawaƙan su riƙa zuga wata jamiyya ko yayan

jam’iyyar da suke goya wa baya su shigo su karɓi gwamnati. Haka ya yi matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya musamman a ɓangaren bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Misali, Ibrahim Yala a cikin waƙarsa mai take, Mu bi APC alummar ƙasa, yana zuga jamaar ƙasa su bar yin jamiyyar PDP don babu cigaba, su zo su yi APC ko za a kai ga ci. Yana cewa:

I,’yan ƙasa mu bar yin PDP,

Kowa ya bar ta don babu ci gaba.

2015 mun yi gangami,

Na kashe ta ba za mu bar ta ba.

  (Ibrahim Yala; Mu bi APC al’ummar ƙasa).

 

Ibrahim Yala ya yi amfani da damar da Allah ya ba shi ya faɗakar da al’umma game da manufofin jam’iyyar APC na dawowa da martabar tattalin arziƙin ƙasa idan har aka zaɓi Muhammadu Buhari ya hau mulki. Dalilin haka ya sa ya zuga dukkan ‘yan Nijeriya da su fita daga jam’iyyar PDP domin ba ta nufin mutane da alheri ta hanyar karya tattalin arzikin ƙasa. Ya ce, alumma su fice daga PDP, su shiga APC domin ta farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ta hanyar bunƙasa aikin gona da kamfunna da msanaantu da sauran hayoyin samar da kuɗaɗen shiga.

Mawaƙin ya gargaɗitare da zuga talakawan Nijeriya ne su shiga jam’iyyar APC domin a zaɓi Muhammadu Buhari ya ceto Nijeriya daga halin lahaula walaƙuwwata da ta sami kanta na taɓarɓarewar tattalin arziki. Wato, ya tallata jam’iyyarsa ta hanyar zuga ‘yan Nijeriya su shigo a dama da su domin a kawar da mulkin zalunci na ‘ya’yan jam’iyyar PDP a ƙasa.

3.2.9.Zuga ta Fuskar Rashin Tsaro

Zaman lafiya shi ne tushen ci gaban ƙasa da bunƙasatattalin arzikinta.Duk ƙasar da babu zaman lafiya,arzikinta ragagge ne.Saboda haka yana da kyau a sami shugabanni masu gaskiya da adalci, domin su bai wa al’umma haƙƙoƙansu.Rashin adalcin shugabanni shi ne ke kawo rashin zama lafiya. A kan haka ne mawaƙan siyasa suke zuga yan ƙasa da masu neman a zaɓe su su kafa gwamnati.Misali, Ibrahin Yala yana zuga ‘yan Nijeriya da su tashi su nema wa kansu ‘yanci ta hanyar shiga jam’iyyar majar ta APC. Yana cewa:

A mu bi APC al’ummar ƙasa,

Ma’anar maja ‘yan Nijeriya,

Neman ‘yanci ba a son raggo,

Ba ma ƙyale yan taadda ba

(Ibrahim Yala: Waƙar APC, maja)

Wannan baiti yana ɗauke umurni tare da zuga ‘yan Nijeriya su shiga jam’iyyar maja domin su ƙwato wa kansu yanci ta hanyar zaɓen Muhammadu Buhari.Mawaƙin ya faɗakar da ‘yan Nijeriya cewa su sani neman ‘yanci ba a son raggo.Wato, cewa da ya yi, ba a son raggo, shi ne zuga da mawaƙin ya yi wa al’umma domin ya zaburar da su, su miƙe tsaye su zaɓi Buhari domin a kawar da ta’adanci don a sami tsaro a Nijeriya. Ba a neman ‘yanci a siyasance, sai an yi rijistar katin zaɓe. Saboda haka su yi rijista domin su sami damar zaɓen mutumin da suke so, wanda zai kawo wa ƙasa zaman lafiya da tsaro. A cikin gwagwarmayar neman yanci raggo ba ya da bagire, domin ba ya iya jure wa tashin hankali saboda tsoro da yake da shi.

Saƙon da ke ƙunshe a wannan baiti ya shafi faɗakar da ‘yan Nijeriya ne game da sabuwar jam’iyyar APC, wadda ta tsayar da Muhammadu Buhari takarar shugaban ƙasa. Don haka yake zuga duk alumma baki ɗaya da su bar jam’iyya mai mulki da ta kasa samar da tsaro, ta jefa mutane cikin ƙuncin yunwa da taɓarɓarewar tattalin arziki da tsoro da rashin tabbas ga rayuwarsu. Ya nuna cewa manufar APC ta nema wa ‘yan ƙasa yancinsu daga hannun ‘yan mulkin jari-hujja na jam’iyyar PDP.

Mawaƙin ya yi amfani da salon isar da saƙo cikin harshe mai sauƙi yadda ko maras jin Hausa zai iya fahimtar abin da waƙarsa ke nufi. Sai dai ya yi amfani da kalmar aro ta ‘Marger,’ wato,maja tana nufin a haɗa ko a gwama abu biyu ko fiye su cure wuri ɗaya, su zama abu guda. Wannan dabara da mawaƙin ya yi amfani da ita don ya jawo hankalin yan Nijeriya ta taimaka wajen ilmantar da mutane akan muhimmancin shiga jamiyyar APC da kuma zaɓen Muhammadu Buhari, musamman ga waɗanda ba su jin harshen Hausa sosai. ‘Mai tsoro ba ya zama gwani’, wato babu nasara ga mutumen da ke da tsoro, (raggo). Ya ƙara da cewa:

Komi ya faru kar mui fushi,

Mu ɗau haƙuri mun ci moriya.

  (Ibrahim Yala: A.P.C.)

 

Wato, dangane da zuga ‘yan Nijeriya da ya yi, ya fahimci akwai matuƙar wahala a yi jayayya da gwamnati mai mulki, amma ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri ga duk wata matsin lamba da za su fuskanta ta ƙuntatawadaga jam’iyya mai mulki domin su jaye daga ra’ayinsu na shiga jam’iyyar maja. Su yi haƙuri domin mai haƙuri yakan dafa dutse, idan suka yi haka za su ci moriyar haƙurinsu.Wannan wani salonzuga ne tare da gargaɗin talakawa su yi haƙuri, saboda mai haƙuri shi ke cin moriya. Idan aka yi haƙuri aka jajirce aka zaɓi shugaba mai adalci kamar Buhari, to za a sami zaman lafiya da tsaro da cigaban tattalin arziki a Nijeriya.

Ibrahim Yala ya zuga Janar Muhammadu Buhari ta hanyar faɗa masa irin halin da ƙasa da mutane suke ciki da cewa, ya zo ya ceci jama’ar Nijeriya daga mawuyacin halin da suke ciki na yunwa da fatara da rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki a sanadiyar wawushe ko satar dukiyar ƙasa da shugabanni suka yi, wanda ya haddasa yawaitar ayyukan taaddanci da sauransu. Yana cewa:

Ka zo ka fitar da mu a ƙuncin da muke ciki,

Yau mun sha wuya a kullum sai farmaki,

Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki,

Ka ji halin da mu muke ciki Nijeriya.

  (Ibrahim Yala: Waƙar APC 2015).

 

Mawaƙin ya faɗakar da Muhammadu Buhari game da halin fatara da yunwa da ayyukan ta’addanci da ƙasarmu take ciki. Ya nuna wa Buhari da ‘yan Nijeriya cewa, wannan hali da muke ciki ya faru nea sanadiyar rashin mulkin adalci da jam’iyyar PDP take yi ya sa jama’a suka samu kansu cikin mawuyacin halin da suke ciki a yau. Ya nuna wa jama’a cewa, a halin yanzu ga jam’iyyar APC ta fito wadda ya ce, ita za ta fitar da al’umma daga mawuyacin halin yunwa da fatara da rashin tsaro da muke ciki idan aka zaɓe ta ta kafa gwamnati. Saboda haka ya faɗakar da mutane irin halin da suke ciki na kai masu farmaki inji ‘yan ta’adda da ‘yan bangar siyasa da kuma masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa. Wannan yaanayi ya jefa mutane cikin halin rashin tabbas na rayuwa a duk faɗin ƙasar nan. Da wannan faɗakarwa ce yake harzuƙa MuhammaduBuhari ya fito takara domin ya kuɓutar da al’umma daga ƙangin rashin tsaro da suke ciki a Nijeriya.

Wannan baiti yana ɗauke da saƙon harzuƙa Muhammadu Buhari da ya yi wa Allah ya fito takarar shugabancin Nijeriya saboda shi kaɗai talakawa ke ra’ayi domin suna sa ran ya ceto ƙasar nan daga halin da take ciki na barazanar yan taadda da ɓarayin shanu da masu garkuwa da mutane, da kuma bangar siyasa. Mawaƙin ya jaddada aniyar talkawa na ba da goyon bayansu ga tafiyar siyasar Muhammadu Buhari mai gaskiya da ba ya fargaba wajen nema wa talakawa haƙƙinsu.

Mawaƙin ya yi amfani da dabarar jawo hankalin talakaw da shi kanshi Buhari ta hanyar bayyana wa Buhari halin da yan Nijeriya suke ciki ta hanyar kawo irin nauin ayyukan taaddanci na kai wa mutane farmaki a gidajensu da wurin kasuwancinsu da ake yi kowane lokaci a Nijeriya. Ya jawo hankalin Muhammadu Buhari ya sa ido ya gani irin satar kuɗin al’umma da masu mulki suke yi , wanda ya ƙara jefa talakawa cikin mawuyacin halin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa da rashin aikin yi ga matasa.Wannan shi ya ƙara jefa matasa halin zaman banza da ayyukan taaddanci.Wannan dabara da mawaƙin ya yi amfani da ita ta isar da saƙo ta taimaka ƙwarai da gaske a bangaren samar da tsaro bayan da aka zabi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa.

3.2.10 Zuga ta Fusksr Adawa

Adawa tana nufin jiye wa wani saboa wata baiwa ko arziki ko muƙami da ya samu. Wato, dai mutum ya nuna rashin gamsuwa ga wani abu da wani mutum ko shugaba ke aikatawa. Mawaƙan siyasar zamani suna amfani da zuga wajen zaburar da wani shugaba ko ɗan siyasa ya ɗauki matakin ramuwar gayya a kan wani ko wasu ‘yan adawa ko abokan hamayya. Misali Dauda Kahutu Rarara yana cewa:

 Kai ku ba ni kiɗan janaral a sama,

 Masu gudu, su gudu.

 Mun san kanwa ku ke da gami,

Masu gudu su gudu

Bana baba Buhari ake magana

Masu gudu su gudu

  (Dauda Rarara: Waƙar sai baba Buhari)

 

Waɗannan ɗiyan waƙa suna nuna cewa mawaƙin yana zaburar da Buhari da shi kansa wajen gogayya da yan adawa. Haka kuma ya zaburar da makaɗansa da su ba shi kiɗa ya zuga Buhari domin ya tsoratar da ‘yan adawa da azzalumai su gudu daga ƙasa. Har wa yau, yana ƙara jan kunnen yan adawa da cewa idan har ka san kai sata ka gudu, saboda Buhari ya ci zaɓe zai fatattaki marasa gaskiya.

3.3 Zuga a Matsayin Salon Sarrafa Harshe

Salon sarrafa harshe wata dabara ce da ke da dangantaka da yadda mawaƙi ke sarrafa harshen waƙarsa domin ya jawo hankalin masu sauraren waƙarsa. Mawaƙi Kan yi amfani da basirarsa ya ƙulla zirin tunanensa bisa ga fahimtarsa ga harshen da yake rera waƙa da shi. Wato, yadda mawaƙi ya zaɓi kalmomi, da yadda ya sarrafa su cikin waƙa (Ɗangambo 2007:34). Wannan dalili ne ya sa harshen waƙa ya bambanta da harshen maganar yau da kullum ta fuskar saɓa wasu ƙaidojin karya dokar nahawun harshe, matuƙar bai saɓa ko gurɓace saƙon da ake son isarwa ba (Yahya 2001). Haka kuma da amfani da karin magana da aron kalmomi daga wani harshe. Mawaƙan siyasa suna amfani da salon sarrafa harshe wajen zuga wanda suke yi wa waƙa. Suna amfani da kalmomin aro da karin magana da kuma yanke wani abu daga cikin wata kalma a cikin waƙoƙinsu domin su isar da saƙonsu cikin sauƙi. Misali,

3.3.1 Aron Kalmomi

Ana amfani da zuga a matsayin salon sarrafa harshe a cikin waƙa a yayin da mawaƙi ya yi amfani da kalmomin hikima da na aro daga wani harshe, kamar Turanci ko Larabci ko ma wasu harsuna da ake magana da su a Nijeriya wajen gina zuga domin isar da saƙonni ga jamaa. Wato, mawaƙi ya yi amfani da salon aron kalmomi ya sassarƙa su cikin waƙa ko da sun karya ƙaidar nahawun Hausa, matuƙar dai ba su gurbace saƙon da ake son isarwa ba. (Yahya 2001). Misali, Yusuf Fasaha yana cewa:

‘ In two thausand fifteen, jiki magayi,

Kowa yai yi ba za mu bassi ba.

   (Yusuf Fasaha: Waƙar A.P.C., mu bi A.P.C.).

 

A wannan baiti da ya gabata, mawaƙin ya yi amfani da salon aron kalmomi daga harshen Turanci domin ya isar da saƙonsa ga dukkan yan Nijeriya masu jin harshen Hausa da mawaɗanda ba su jin Hausa.Wannan salo ya taimaka wa mawaƙan siyasa wajen isar da saƙonsu cikin hanzari.Amfani da kalmomin Turanci da mawaƙin ya yi,ko kaɗan bai gurɓata sautin muryar waƙar ba, haka kuma bai gurɓata saƙon ba.Sannan karin maganar da ya liƙa ga kalmomin aron sun bi tsarin saƙon da mawaƙin yake son isarwa ga alumma tamkar da ma Turanci aka shiya waƙar.A nan mawaƙin ya yi amfani da salon ingausa, wato haɗa Turaranci da Hausa a cikin waƙa lokaci ɗaya ba tare da saƙo ya gurgunta ba. ‘Two thousand fifteen’, tana nufin dubu biyu da goma sha biyar. Mawakin ya aro wannan kalma ce domin ya isar da saƙo ga waɗanda ba su jin harshe Hausa.

Mawaƙin ya yi amfani da salon sarrafa harshe ta hanyar aron kalmomi daga harshen Turanci inda ya aro kalmomin Turanci ya gina jumla da su a layin farko na baitin..Haka kuma ya yi amfani da karin magana domin ya ƙarasa cikasa jumlar

da ya yi amfani Turanci da Hausa duk a layin farko na waƙar. Wannan salo da mawaƙin ya yi amfani da shi ya nuna wa mutane ya laƙanci harshensa da kuma wanda ya yi aro daga gare shi. Har wa yau ya yi amfani da karin magana domin ya burge masu saurare da kuma jawo hankalinsu su fahimci saƙon waƙarsa cikin sauƙi.

3.3.2 Karin Magana

Mawaƙan siyasa sukan yi amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu domin su nuna ƙwarewarsu ga harshen da suke shirya waƙoƙinsu a cikinsa da kuma gargaɗin ‘yan siyasa ko shugabanni su yi taka-tsan-tsan ga tafiyarsu ta siyasa.Karin magana wata gajeruwar magana ce mai ƙunshe da dogon bayani idan aka warware ta (Koko, 2011, P.1-2).Mawaƙan siyasa suna amfani da zuga a matsarin salon sarrafa harsne a cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da suke isarwa gare su ba tare da wata matsala ba.Misali,Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa:

Karen bana maganin zomo,

Bana tabbas lokaci ya yi,

A.P.C. ta riga ta bayyana,

don ta yi maganin bera,

Mu bi maja duka talakawa.

Gaba dai gaba dai mu je sat ɗaya,

A.P.C. babu gaggawa.

(Kamilu:Waƙar A.P.C. mu bi maja).

 

Da farkon baitin mawaƙin ya fara buɗe waƙarsa da karin magana a matsayinsa na ƙwararre ga harshen Hausa. Karin maganar yana ɗauke da zuga, inda ya nuna cewa, jam’iyyar A.P.C. ta riga ta bayyana. Mawaƙin ya kambama A.P.C. da cewa, tabbas lokaci ya yi da talakawa za su dawo daga rakiyar jamiyya mai mulki ta P.D.P; domin a cewarsa jam’iyar A.P.C. ta riga ta bayyan.Mawaƙin ya kamanta jam’iyyar A.P.C da karen bana, yayin da ya kamanta jam’iyyar P.D.P. da zomo, wanda ya nuna fifikon kare a kan zomo. Saboda haka, ya ce, lokaci ya yi da talakawa za su sauya gwamnati a sami mai adalci, wadda za ta ceto talakawa daga ƙangin bauta da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa idan suka zaɓi jam’iyyar A.P.C. da Muhammadu Buhari.

Shi ma Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana zuga ‘yan Nijeriya, inda ya nuna wa jama’a cewa lokaci ya yi da za su nema wa kansu ‘yanci ta hanyar zaɓen Muhammadu Buhari na jam’iyar A.P.C.Mawakin yana cewa:

Kowa ya ƙi A.P.C. jamaa,

Gaskiya kam ya zuba ganganci,

Jiki magayi ne baba Janar,

Mun gane mu duka talakaw.

(Kamilu: A.P.C., Runhu an yi furen banza)

Mawaƙin ya yi amfani da karin maganar ‘Jki magayi’ domin ya isar da saƙonsa cikin hikima da samar da nishaɗi ga masu sauraren waƙarsa. Wannan karin maganar: “Jiki magayi” tana nufin duk wanda ya bi son zuciyarsa ya aikata abin da yake so, zai yi nadamar abin da ya aikata. Wannan dabara tana daga ckin salon da mawaƙan siyasa suke amfani da ita domin su jawo hankalin ‘yan siyasa da masu saurarensu su fahimci amfanin zaɓen Muhammadu Buhari ya shugabanci al’umma. Hakan na nuna cewa wata faɗakarwa ce dangane da matayin Buhari a zaman sa mutum mai gaskiya a fannin gudanar da shugabanci.

Mawaƙan Hausa, musamman na siyasa sukan so su yi amfani da basirarsu su kutsa kansu cikin harshen da suke rera waƙa, su zaɓo kalmomi masu jawo hankalin mutane a lokacin da suke ƙoƙarin isar da wani saƙo zuwa gare su. Yin amfani da karin magana da wasu kalaman hikima ko na barkwanci domin su jawo hankalin masu sauraren waƙoƙinsu, wata dabara ce ta isar da saƙo ga alumma cikin nishaɗi da raha..Misali,Yusuf Fasaha ya zuga al’ummar Nijeriya domin su tashi tsaye a dama da su cikin harkokin siyasa a Nijeriya; yana cewa:

A hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.

Mui kama-kama mu kai gaci,

  (Yusuf Fasaha: Waƙar A.P.C.),

 

Mawaƙin ya yi amfani da karin magana a matsayin wata dabara ta jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da yake ƙoƙarin isarwa gare su cikin raha da nishaɗi. Ma’anar wannan karin magana da mawaƙin ya yi amfani da ita ita ce komin ƙarfin mutum ɗaya ba zai taɓa iya ɗaukar jinka ba. ‘Jinka’, a al’adar Bahaushe tana nufin wani dabi ne na itace da ake haƙawa a ƙasa, sai a yi masa rufi da shifci (busasshen haki) wanda za ɗora wa ɗaki da aka gina da ƙasa. Idan aka gama baibaye itacen da shifci sai a nemi jamaa su ɗauki jinkar su ɗora a ɗakin da aka gina.Kasancewar jinkar mai nauyi ce, shi ya sa mutum ɗaya ba ya iya ɗaukar ta shi kaɗai ya ɗora a ɗakin. Wannan dalili ne ya sa Hausawa suka ƙirƙiro da karin magana, ‘hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka’; domin su nuna wa jama’a amfanin haɗin kai a duk lokacin da za a aiwatar da wani aiki. Mawaƙin ya yi amfani a wannan karin magana a cikin waƙarsa domin ya jawo hankalin yan Nijeriya su haɗa kai su zaɓi Buhari domin a ceto ƙasa da alummar ƙasa daga halin ni-yasu da suka tsinci kansu a ciki. Wato, ta hanyar amfani da karin magana a cikin waƙoƙin siyasa ne ake jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da ake isarwa gare su..

3.3.3 Saɓa Ƙa’idar Harshe

Mawaƙi na iya saɓa wa ƙa’idar harshe domin karin waƙarsa ya fito daidai domin saƙonsa ya isa ga waɗanda aka yi dominsu ba tare da wata matsala ba . Wannan wata dabara ce da mawaƙan Hausa suke amfani da ita wajen isar dasaƙo ga masu sauraren su. Yahya (1997), ya bayyana cewa, mawaƙi kan gutsure wata gaɓar kalma, ko ya cire wata kalma ko kuma ya cire wasali a ƙarshen kalma ko a tsakiyar kalma a yankin suna ko na aikatau domin karin muryar waƙarsa ya tafi bai ɗaya ba tare da saƙo ya gurgunta ko gurɓata ba. Haka kuma mawaƙi yakan tsara jimlarsa tare da saɓa wa ƙaidar nahawu a farkon jimla ko tsakiyar ta ko ƙarshen ta domin ya fito da saƙonsa a fili. Wani lokaci kuma a sami akasin haka a cikin baiti. Misali, Aminu Alan waƙa yana cewa:

Baƙar malfa, baƙar jarfa,

mai shanye jinin jikin talaka,

Allah kaɗa guguwar sauyi,

Buhari Janar karab da gari.

  (Alan waƙa: A.P.C.).

Wannan baiti yana ƙunshe da zuga ingizau inda ya roƙi Allah da ya kaɗa guguwar sauyi, ‘’Buhari Janar karab da gari’.Kalmar ‘karab’ tana nufin ‘karɓa’.Mawaƙin ya cire wasalin a a ƙarshen kalmar, sannan ya saka wasalin a a tsakiyar kalmar, sannan kuma ya canja harafin ɓ’ da ‘b’. Wannan canjin ya sa kalmar ta tashi daga karɓa, ta koma ‘karab’ maimakon karɓa. Yin haka a tsarin nahawun harshen Hausa ya saɓa wa tsarin ginin kalma, domin a tsarin jimla idan aka cire wani abu na ƙwayar maana daga cikin kalmar suna ko aikatau, to nan take jumlar za ta canja ma’ana ko ta sami tangarɗa. Amma a harshen waƙa mawaƙi kan iya canja wani abu daga cikin kalma ko jumla amma jumlar ba ta sauya ma’an ko sauya karin muryar waƙar ba. Misali inda Alan waƙa yake cewa; Allah kaɗa’, da kuma ‘karab’ maimakon Allah ya kaɗa da kuma karɓa. A tsarin ginin jumla, mawaƙi ya ƙi saka zagin aikatau na ya kafin kalmar kaɗa, wanda ya saɓa wa nahawun maganar yau da kullum. Misali, maimakon ya ce ‘ya karɓi gari’ sai ya ce ‘karab da gari. Wannan wani salo ne na sarrafa harshe da mawaƙan Hausa ke amfani da shi domin su nuna ƙwarewarsu a harshen da suke rera waƙa a cikinsa. Yin haka ya taimaka ma masu sauraren waƙoƙin siyasa ƙara fahimtar saƙonnin da mawaƙan Hausa ke isarwa gare su, tare ƙara ɗaukaka darajar mawaƙan da suke amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu na siyasa da kuma sauran harkokin yau da kullum.

3. 4 Tasirin Zuga a Zukatan Al’umma

Zuga yana da matuƙar tasiri a zukatan alumma, ta ɓangarori daban daban; domin mutane sukan fa’idantu da zuga a matsayin wata hanya da mawaƙan siyasa ke amfani da ita wajen faɗakar da su da kuma ilmantar da su game da wani matsayi ko kwarjinin wanda suke yi wa waƙa.Babu shakka zuga ya yi matuƙar tasiri wajen faɗakarwa da ilmantarwa da kuma samar da nishaɗi ga al’umma a duk lokacin da mawaƙa suka yi amfani da shi cikin waƙoƙinsu.Ta hanyar zuga ne mutane ke iya rarrabewa tsakanin jaruman ƙarya da na gaskiya. Haka kuma ta hanyar zuga ne jamaa suke amfana da roman dimokuraɗiyya wajen samun kyaututtuka da tallafin jarin kasuwanci da abubuwan hawa daga ‘yan siyasa da kuma gwamnati.Haka kuma zuga ya yi tasiri ta hanyar samar wa talakawa da matasa ayyukan yi, da saur