Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Kwanta Min A Rai Zan Iya Ce Masa Ina Son Shi

TAMBAYA (187)

Aslm malam barka da warhaka malam ina da tan baya ni macec ina son wani amma shi baisani Ba ya halata a duk lokacin da nai sallah in din Ga addu ar Allah ya mallaka min shi ?

YA KWANTA MIN A RAI ZAN IYA CE MASA INA SON SHI

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

A'a

Saboda ai baki da ilimi akan cewar alkhairi ne a gareki ko Kuma zama dashi sharri ne ga rayuwarki dakuma addininka

Wannan dalilinne yasa Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar damu addu'ar Istikhara

Ki samu lokaci kiyi Sallah (Nafila) Raka'a 2

Bayan kin sallame sai ki karanta addu'a Istikhara

Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.

Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ka fadi buwatarka) khayrun lee fee deenee wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ka fadi buqatarka) sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.

Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".

Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;

(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)

"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".

Kiyi bincike akan halayyar sa musamman akan addininsu da kuma mu'amalar sa da mutane. Idan yaci Screening to daganan sai kiyi qoqarin nuna masa alamun soyayyar yanda zai gane kuma ba laifi bane ba ma idan kikace "Inni uhibbuka fillah😍" bi ma'ana: "Ina son ka don Allaah" la'akarida Nana Khadija (Radiyallahu anha) ita da kanta ta firta tana son auren fiyayyen halitta Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) saboda amanar sa da Kuma iya mu'amalar sa da mutane

SHARHI: Da akwai wasu da suke cewa wai saidai ayiwa mutum istihara, to nidai bansan a wanne waje suka samo wannan nassi ba, domin kuwa sahihan hadisai sun tabbatatarda cewar Annabi SAW yana koyawa sahabbai Istihara kamar yanda yake koyardasu ayoyin Qur'ani. Don haka duk wani wanda yace zaiyi maka Istihara to dan damfara ne number 1. Sannan kuma ba'a nafarki ake gani ba, kamar yanda kwanaki wata yar uwa take cemin ta ga wani haske a mafarki bayan tayi Istihara wanda wai a tunaninta hakan na nufin saurayinta alkhairi ne a rayuwarta. Wannan duk rudin shaidanne. Allah yabamu ikon kiyayewa

Wallahu taala aalam

Muna muku tallar sabuwar makarantar Online mai suna: "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI". Wanda yake da ra'ayin shiga yayi magana ta Private hukumar makaranta zata turo masa tsare - tsare da dokokin shiga

(WhatsApp: 07035387476)

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments