Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsattsafin Bandariya a Cikin Wakar Zaura ta Sanin Baldo

Citation: Umar, R.A. (2024). Tsattsafin Bandariya a Cikin Waƙar Zaura ta Sanin Balɗo. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 536-541. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.066.

Tsattsafin Bandariya a Cikin Waƙar Zaura ta Sanin Balɗo

Rabiʼatu Abubakar Umar
C/O Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato, Nijeriya.
08033880753

Tsakure: A waɗansu lokuta, makaɗa kan ɗauki wani abu a masa waƙa a bisa son ransu. Abin da za su yi wa waƙar yana iya zama abin mamaki ko takaici a gare su. Daga cikin ire-iren abubuwan da sukan ɗauka su tsara waƙa a kansa har da abin da ya shafi zamantakewa. A kan sami wani abu da ya yi wa mutum daɗi ko akasin haka wato rashin daɗi, ta yadda da zuciya ta bayar da rinjayenta a kansa, kwatsam sai a ji waƙa ta fito. Haka abin ya kasance ga wannan waƙa da aka yi nazarinta a cikin wannan maƙala, waƙar bazawara ta Sanin Balɗo. An nazarci waƙar aka kuma yi ƙoƙarin fahimtar dangantakar Sanin Balɗo da bazawara domin sanin yadda aka yi wannan waƙa ta fito har ta zama abar sha’awa take kuma bawa mutane dariya a duk lokacin da suka saurareta. Daga cikin ire-iren dariyar da aka hango a cikin waƙar sun haɗa da dariyar ƙeta da ta mamaki da sauransu.

Fitilun Kalmomi: Tsattsafi, Bandariya, Waƙar Zaura, Sanin Balɗo

Gabatarwa

Waƙoƙin ɗarsashin zuciya, waƙoƙi ne waɗanda sukan wanzu a sakamakon wani abu da ya motsa wa mutum rai da ya danganci farin ciki ko farin rai ko akasin haka wato baƙin ciki. domin haka, waƙoƙin ɗarsashin zuciya sun ƙunshi bayyana farin ciki ko baƙin ciki bisa wani abu da ya faru ga mutum ɗaya ko a ƙungiyar mutane ko a gari ko a ƙasa. Su kuma waƙoƙin rinjayen zuciya akan yi su ne a kan abubuwan da suka danganci kauce wa ƙa’idojin zamantakewar rayuwa waɗanda sai in zuciya ta rinjaya ake faɗawa cikin yin su, kamar sata da caca da karuwanci da daudanci da sauransu. Har wa yau irin waɗannan waƙoƙi akan yi su a kan abubuwa da zuciya ba ta son su, amma su auku saboda an rinjaye ta kamar aukuwar fari da yunwa da makamantansu Gusau (2008:390).

Kowane makaɗi yana da ire-iren waƙoƙinsa masu ɗauke da mabambantan manufofi waɗanda a cikin su ne ake samun irin wadda jama’a suka fi so, ko kuwa ta fi karɓuwa ga jama’a. irin wannan son da jama’a ke yi wa waƙar makaɗi yakan sa jama’a su kirayi waƙar da sunan bakandamiya ko da shi makaɗin bai san da hakan ba.

Haka abin yake tattare da waƙar bazawara ta Sanin Balɗo. Waƙa ce da aka yi sakamakon faruwar wani abu day a jawo ɓacin zuciya, hart a sa aka sami wannan waƙar. Saboda irin karɓuwar da waƙar ta samu a wajen jama’a, ta sa ana ɗaukarta tamkar ita ce bakandamiya a cikin jerin waƙoƙin da Sanin Balɗo ya yi.

 Waƙar tana burge mutane a duk lokacin da aka saurare ta, tana saka mutane cikin nishaɗi a waɗansu lokuta har su ɗan dara ko kuma su yi dariya. Baitocin da suke ɗauke da tsattsafin daariya ko dariya kanta, su ne wannan takarda za ta sakata ta wala ta yi kiɗanta da rawarta a cikinsu domin a yi ƙoƙarin gwadawa mutane ire-iren dariyar da aka tsinkayo a cikin ɗangogin waƙar domin fahimtar da jama’a. Kaɗan daga cikin ire-iren dariyar da aka hango a cikin wannan waƙar sun haɗa da dariyar mamaki da ta ƙeta data raha da sauransu kamar yadda za a gani sannu a hankali a cikin maƙalar.

2.0 Sanin Balɗo da Bazawara

Waƙar bazawara kamar yadda makaɗin ya faɗa da bakinsa, ya fara yin ta ne a garin Nassarawar Burƙulle ta jihar Zamfara (gangaren magina). Waƙar bazawara ta Sanin Balɗo, ba waƙa ɗaya ba ce kamar yadda makaɗin ya nuna. Waƙar bazawara da ya yi tana da yawa, sai dai akwai haƙiƙanin cewa sauran waƙoƙin sun samo asali ne daga waƙarsa ta farko da ya yi wa bazawara

Daga nan ne sai abin ya ci gaba, duk inda aka gayyace shi domin ya yi waƙar bazawara sai ya sami sababbin kalmomi da azanci yana ƙarawa tare da la’akari da canjin zamani. Haka abin ya riƙa tafiya gaba-gaba har a halin yanzu.

Kasancewar komai yana da dalili, wannan waƙa ta bazawara da Sanin Balɗo ya yi, tana da dalilin yin ta. Sanadiyar wannan waƙa ta bazawara shi ne, makaɗin ya yi zawarcin wata bazawara a garin Nassarawar Burƙulle mai suna Fati. Sun yi alƙawari sh da ita cewa za su yi aure don haka shi yake ɗauke da larurorinta duka, kamar yadda yake faɗa:

“Mai guntun alƙawali,

Mai guntun keso,

Mai guntun luddai,

Daɗa kai dai ba ka lalura duk sai tata,

Sai ta koce kamar kaɗa ta tashi.”

 (Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

Bayan soyayyarsu na daɗa ci gaba, sai ta nemi da ya raka ta garin Boɗinga domin ta ziyarci ‘yan uwanta, bayan sun dawo sai a ɗaura musu aure. Kafin ranar tafiya ta zo Sanin Balɗo ya hau mashin ɗin sa (Roadmaster) ya tafi Gusau domin a yi gyare-gyare (service). Da tafiyarsa Gusau, sai Fati ta faɗawa Aminisa Abu cewa, ita fa ta faɗawa duk masu nemanta da aure cewa, mijinta na baya bai sake ta ba, don haka za a mayar da aurensu. Don haka kowa sai ya janye har da Sanin Balɗo. Amma sai ta ce, ban gaya wa Sanin Balɗo ba, saboda ina jin kunyarsa. Ashe wannan Magana ƙarya ce, alƙawari ta yi da wani cewa za ta aure shi bayan suna tare da Sanin Balɗo.

Bayan Sanin Balɗo ya dawo daga Gusau, sai aminisa ya gaya masa abin da Fati ta faɗa. Ɗan Balɗo da jin haka sai ya ce: “wanda ke bisa sa ai bai kwaɗayin tozo.” Dalilin yin wannan azanci shi ne, ko da yake neman Fati (bazawara), ashe yana shawarar komawa wajen wata yarinya (budurwa) mai suna Mutuna. Bayan wannan labarin sai Sanin Balɗo ya hau mashin ya tafi Waramu garinsu daga Nassarawar Burƙulle ya ɗauko kayan kiɗa ya waƙe bazawara amma bai ambaci suna ba. Da ya ƙare sai ya ɗakko rikodarsa ya je wajen wani mai sayar da shayi a bakin gidan su Fati ya saka kaset na waƙar bazawara ya kunna rikoda.

Da mutane suka ji waƙa, kuma aka ce ga wanda ya yi waƙar, sai suka ce lalle ba lafiya ba. Sai taubashiyar Sanin Balɗo ta ce ya faɗa mata abin da ya faru har ta kai shi ga shirya wannan waƙa. bayan ya faɗa mata abin da ya faru, sai ta tafi wajen uwar Fati ta kwashe yadda labari yake ta faɗa mata. Ko da aka kirawo Fati sai ta ce, ita ba ta faɗa wa Sanin Balɗo komai ba, amma ga yadda suka yi da Abu. A nan sai aka nuna mata rashin wayonta, aka faɗa maata cewa ai abin da ya yi Abu shi ya yi Sanin Balɗo domin aminai ne. da jin wannan Magana sai uwar Fati ta yi saƙo wajen Ɗan Balɗo cewa, don Allah idan zai yi waƙa kada ya saka sunanta a ciki. Ko da uwar Fati ta aika wannan saƙo an riga an gama waƙa, amma duk da haka Snin Balɗo bai saka sununan uwar Fati ba bai kuma saka sunan Fati a cikin waƙar ba. Ya bar waƙarsa buɗe ta zama habaici ga zaurori. Dalinlin da yasa zaurori ba su son buƙatar wannan waƙa kenan. Duk inda bazawara ta ji wannan waƙa sai ta yi sauri ta sake hanya.

3.1 Yadda Ake Yin Dariya:

Dariya wani aiki ne na fara’a, da nuna jin daɗi da sakewa, ko kore wasu abubuwa na al’ada. Mafitar ta shi ne baki, wanda zai sauyar da yanayin fuska gaba ɗaya, ta ɗauki wani yanayi na nuna rashin damuwa da wanzuwar farin ciki, ko da kuwa ba shi ake ciki ba.

Dariya wani babban aiki ne da ya shafi hankalin mutum da tunaninsu. Don haka, wani babban mudu ne na auna hankalin mai yin ta. Ga al’adar dariya, ba ta yiyuwa cikin wasu ayyukan gaɓɓai, irin gudu, ko rawa. Haka kuma, ba a yin ta da sakewa idan ana kwance. Ba ta taɓa haɗa bagire ɗaya da kuka, dole sai an daina ɗaya za a iya yin ɗaya. Ba su haɗa mazauni ɗaya da magana ba, da an fara magana ta tsaya, idan ana yin ta magana ta yanke. Idan ta zaburo, kamar kumallo ne, dole sai an yi tsaye a yi ta, domin ba a yin ta yadda ya kamata idan ana tafiya Bunza (2011:3).

3.2 Yanayin Dariya:

Gabanin fayyace dalilan da ke haddasa dariya ko rabe-raben dariya ya kyautu a san yadda ake aiwatar da dariyar, ita kanta dariya nune ne ga abin da ya haddasa ta. Yayin da Bahaushe ke aiwatar da dariya, ko wani ya gan shi yana dariya ko ya ga wani na dariya, idan zai labarta abin da ya gani za a ji wasu bayanai irin su:

·         Ya bushe da dariya

·         Ta tuntsure da dariya

·         Sun yi ta ƙyalƙyatar dariya

·         Kai! Jiya an ci dariya

·         Na fashe da dariya

·         Dariya ta kashe ni

·         Ta kasa kame dariya

Waɗannan zantuka bakwai da aka ambaci dariya da su, muhimman abubuwa ne ga mai son nazartar dariya. Wanda ya bsuhe da dariya, ya kasa ya yi ta sosai, ta koma ciki. Irin su ke cewa, sai da cikinsu ya yi ciwo. Wanda ya tuntsure da dariya, in zaune yake, ya faɗi kwance, in tsaye yake ya yi ruku’i, irin na masallata ya dafe gadon baya ko ƙirji irin na mai amai. Mai kyalƙyatar ta shi ne, wanda ya daga sautin yin ta. Waɗanda suka ci ta, sun yi ta zube ban ƙwarya, babu mai sauraron na wani. Idan aka fashe da dariya asali fuskar kame take da dariyar ta zo, ba a samu sake fuska ba bale murmushi sai kawai aka ji dariya girshi, an kasa haƙurin rashin yin ta bale a riƙe ta. Waɗanda dariya ta kashe su ne, maƙetata sun shagaltu da ita har hankalinsu ya so ya kawa. Idan wani abin ƙeta ya bayyana maƙetaci bai iya kame dariyarsa sai ya dara. Ga al’ada, ba a so a yi ta ba, amma ta rinjayi mai ita dole ya buɗe baki ta fito ka da ta yi masa aibi a zuci Bunza (2011:4).

 3.3 Rabe-raben Dariya:

Dariyar da ke fita bakin ɗan Adam, ba a kan banza yake yin ta ba. Haka kuma, ba a kan fara’a da jin daɗi da annashuwa kawai ake dariya ba, kamar yadda na bayan fage ke hange. Ga yadda na ɗan kalato rabe-raben dariya kamar yadda Bahaushe ke kallonta:

1.         Dariyar raha

2.         Dariyar haure (yaƙe)

3.         Dariyar darara

4.         Dariyar ƙeta

5.         Dariyar yarda

6.         Dariyar rashin yarda

7.         Dariyar kunya

8.         Dariyar magana

9.         Dariyar mamaki

10.     Dariyar kore

11.     Dariyar reni

12.     Dariyar hauka

13.     Dariyar ƙwaruwa

14.     Dariyar ƙarya

4.0 Tsattsafin Bandariya a Cikin waƙar Bazawara ta Sanin Balɗo

Ta la’akari da abin da ake nufi da dariya da yadda ta ked a kuma rabe-rabenta. An yi tsinkayen abin day a yi kama da haka a cikin waƙar bazawara ta Sanin Balɗo. Makaɗin ya kawo dangogin waƙa da zasu hau mizanin ire-iren dariya da ake das u kamar yadda aka bayyan a sama tun da farko. Daga cikinsu akawai:

4.1 Bandariya Ta Raha

Ita ce, dariyar da ta fi fice daga cikin rabe-raben dariya. Dariyar raha ita ce, rai ya cika da raha ta abin da ya samu, ko abin da aka ba shi labari, ko abin da ya gani na raha. Abubuwan da ke haddasa dariyar raha sun haɗa da abubuwan da suka shafi addini ko tattalin arziki ko siyasa ko zamantakewa ko al’ada da wayewar kai da ci gaban zamani irin na mai ginan rijiya.

A game da wannan nau’i na dariya, ga labarin da Sanin Balɗo yake bayarwa karonsa da bazawara. Labari ne da ya shafi zamantakewa, ta yadda duk wanda ya saurara ba shakka zai dara. Ga abin da yake cewa:

“Ni da zaura ta iske ni gida zamne na harɗe,

Na kame ga kujerata garkammu,

Tac ce min kai a Alhaji Ɗan Balɗo yaka,

Ni ce ni a Alhaji Ɗan Balɗo,

Tac ce don kai ɗai nik kasha armen ga,

In ka shirya in ba ka shirya ba,

Auren ga da kai aka ɗarma shi,

Ɗan Balɗo farar fatag gag a ruɗani dun nir ribce,

To dudda tsawon hancin ta misali nai,

Ya kai mil goma misalign dogon hancin.

Ina da near dubu ga kwatolona niz zwage,

Wada nim miƙa mata ta karɓa,

Sai ɗai tac ce na slipa na kab bbani,

Nik koma nij juya kwatolona nil lwasto,

Ina da near dubu ga kwatolo na niz zwage,

Wada nim miƙa mata ta kraɓa,

 Sai ta ce Alhaji Ɗan Balɗo,

To yanzu waɗanga na lalle na kan ba ni.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

A cikin waɗannan ɗangayen waƙa na sama, za a lura cewa, Sanin Balɗo ya kawo tarsi na salon labara. A inda ya zayyana yadda ta kwashe tsakaninsa da bazawara. Da jin wannan labara, sai mutum ya ɗauka tamkar yana nana bin ya faru a gabansa, a ƙarshe har mutum ya ɗan dara.

Haka kuma ya ci gaba da amfani da irin wancan salo, a inda ya ce:

“Zaura ‘yar Ina da Baba shiririta nomanki,

‘Yar Inna da Baba shiririta nomanki,

‘Yar Inna da Baba da Goggo ɗiyak Kawu,

Mai gutun alƙawali mai guntun keso,

Bori kike mai maganar yohi ‘yar Inna.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

A nan ya ambaci zaura a matsayin ‘yar Inna da Baba da Kawu da kuma Gwaggo, ba domin komai sai don ya nuna cewa zaura shagwaɓaɓɓiya ce. A taƙaice makaɗin ya nua cewa, duk cikin jerin iyayen nan na zaura babu mai iko da ita, ita ta ke iko da kanta. Abin da ta so yi shi za ta yi. Ko da iayen nata sun maka alƙawarin za su aurar maka da ita , to babu tabbas, hakan tasa makaɗin yake cewa “mai guntun alƙawari mai guntun keso”

A gaba kuma sai makaɗin yake cewa:

“Kura ke saba da ɓaci,

Maƙera ke saba da kuɗa,

Shegiyar gona na sha wuyar ki,

Baƙar tunkiya ke saba da gwami,

Kesa mai kwanan kesa,

Gatarin wahala ke ‘yar jidali.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

Da jin waɗannan ɗangogin waƙa ka san an sha wahala. Dubi dai yadda makaɗin ya yi amfani da salailai iri-iri da ya kama dabbantarwa da abuntarwa da suransu wajen bayyana bazawara saboda irin halin day a samu kansa a ciki. Ba wai ba inke, duk wanda ya dubi ɗangogin wannan waƙa za dara

4.2 Bandariyar Ƙeta

Ita ce, dariyar da ake yi wa mutum idan ya shiga cikin wani hali da zai cutu a jikinsa ko a rayuwarsa gaba ɗaya. Hausawa na tarbon irin wannan dariyar da faɗar, mugu ba ka dariya sai ta ɓaci. Maƙetaci da ya yi dariya, wani ya cutu.

A cikin waƙar Sanin Balɗo tabbas an hangi abin d ya ɓaci wanda zai iya saka mutane su dara har ma su yi dariya baki ɗaya. Ga dai abin da makaɗin ya faɗa:

“Shekaranjiya na ga abin tausai,

An kasa kurma ga biɗaz zaura,

Ni ran nan na ji bululluƙƙai,

Don ni han na aza gebe nay as shaƙe,

Han na sheƙa in samo aron gora in take,

Nic ce kurma in ban da karambani mik kai ka?

Ko mai ji ya yi biɗar zaura ta ƙi shi,

Bayan kurma ta ƙare lalura tai ɗan kuwwa,

Rannan mun ci dariya har mun ƙoshi.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

Masu iya Magana suna cew: “abin dariya daa yaro y tsinci haƙori” abin day a bawa yaro dariya a nan shi ne, wao yasan haƙorin nan day a tsinta bas hi da amfani a wajensa. A nan kuwa kurma ne ya sha wuyar neman bazawara ta yadda har hauka ya kusan yi saboda rashin nasara day a yi. Makaɗin da yake shi ma ba a bar shi a baya ba waje neman bazawara, tasa yake cewa mai kunne ma yaya ya ƙare da bazawara bare kurma mutumin dab a ya ji.

Da aka matsa gaba domin ƙoƙarin fahimtar dariya ta ƙeta sai aka yi karo da wani bayani a cikin waƙar wadda ya bayyana yadda wani barunje ya faɗa tarkon zaura, ga dai abin da aka kalato:

“Kwanaki ta hwasa rundawan wajjenmu,

Ɗan yaro Bello da ta ribtai tar rabke,

Ragon jikka tara ya yanka,

Ɗai wajje y agama hiɗa,

Ɗai waje bai gama hiɗa ba sai yaɗ ɗauka,

Bai cire hanji ba bale tumbi,

Sanna ba ko katse kai ba,

Ba a ebe ƙafafu kai fata ba sai yaɗ ɗauka,

Yattai yak kai saman waya yay yaɓa,

Yas sheƙa yak kwaso tukar rake ɗai ya tara,

Sai na hangi ashana ga hannu nai ya kyatta,

Yah aye dutsi yai ta kirari,

Ni na yaron sarkin fawa,

Mai gasa nama ros,

Kai ku taho maza ta soyu,

Ka san runji da hlin kara,

Su sun ka cire ma shi naman nan can gefe,

Nic ce to wanga kashin zaura ya ɓaci.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

Haka kuma, wani wuri inda mutum zai ƙyaƙyata dariya shi ne, wurin da zaura ta haukata wani barunje. Kamar yadda makaɗin ya bayyana a cikin waƙarsa, saboda zautuwa da barinjen ya yi wajen neman bazawara tasa har ya yi ƙoƙarin sayar da nama a haukace. A wannan hali barinje ya yanka rago bai gama fiɗa ba, sai ya ɗakko ragon ya ɗora a kan waya ba tare day a fitar da kayan ciki ba. Bayan nan sai gas hi ya taro tukar rake yana neman ashana zai gasa nama domin a saya. Wannan duk halin ribcewa ne da barunje ya samu a wajen bazawara.

A gaba sai karon Bafulatani da zaura, ga dai abin da faru:

“Ya’u irin zaurag ga ta Hillani,

Irin zaurag ga ta Hillani,

Kwanakki Kiruwa tar ribta yaz zwage,

Tat tai tak kungumi Harumbe tat taushe,

Shi da zaura tac ci amana tai,

Shi ya isko ni gida ran nan yake,

Ko da yaz zaka na tafi daji nan,

Yas say at tafi azure yay yi zamanshi,

Ya’u irin maganag ga ta Hilani,

Ita ka yi ma Alhaji Ɗan Balɗo,

Yac ce min kai a Alhaji ɗan Balɗo ka ganka,

Lalle kai naga kiɗan zaura ‘yak kuwwa,

Da dai yaɗ ɗakko batun zaura,

Sai in ce za mu wurin wasa Argungu,

Haba mutumniyarka ta ci amanita,

Nic ce Yawuri waƙa tam maishe mu,

Dub bai gane ba niƙ ƙyale shi,

Yag ga alaman na hita shirgi nai,

Dac can yak karumo Ɗan Balɗo,

Kai Balɗo ka ƙara kiɗin zaura kura ta,

Wajeen maraƙi huɗu nis sai kai tac canye,

Yara na sun yi kiwon rago ɗan gyarni,

Su huɗu na kai tac canye,

Ba haɗa tggo sabo nai ba.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

wani abin dariya kuwa da faru shi ne, sakamakon karon Bafulatani da bazawara. Bafulatani ya samu labarin Sanin Balɗo ya yi waƙar bazawara, don haka ya yi tunanin cewa, ai shi ma zaura ta ƙware shi , don haka bari ya kai kuka gidan makoki ko ya samu abokin tayi. Wannan tasa ya zo wajen Sanin Balɗo ya kuma gaya masa cewa, bazawara fat a cinye masa maraƙa huɗu da rago kuma bat a aure shi ba, don a ƙara waƙar zaura.

4.3 Bandariyar Mamaki

Wata dariya ta bayyanar da mamaki ce ga abin da aka gani, ko aka ji, ko aka karanta. Idan mamaki ya cika tunanin mutum ga wani abu sai a ga dariya ta fito kai tsaye.

A nan dai kan ga wani abin mamakin da bayar da dariya, domin zaura da ake nemanta da kuɗi, amma sai ga wani y ace shi ko da kuɗI da gida da mota ba ya son bazawara, ga dai abin da yake faɗa da bakinsa:

“Tsaya ka ji don tsananin ban son zaura sanƙira,

Don ni da a ce mini ga zaura am ba ni,

Tare da mota Fayib o fayif (505),

Kai, Kai

A gina gida na gilashi,

Sai an shase swal,

A kawo fameka uku a jera min,

Ɗan Balɗo a liƙa gilashin gyaran fuska,

A ban tibi da rikoda ta jibisi,

Ga janareto sabo an ban,

Ai mun murtsatse na rowan sha,

Ga firjin don sanyinsu,

A ba ni near dubu ta sayen manja,

A ban dubu biyat na sayen manja sanƙira,

Kuma ga zaura ni adda.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

A nan saboda tsananin masifar da zaura ta gwadawa Sanin Balɗo, tasa y ace duk abin da za a bas hi, a haɗa masa da bazawara bay a so. Masu iya Magana suna cewa “wari yake an ce da makaho ga ido”. Don haka sai mu ce, anya kuwa Ɗan Balɗo ba gani ya yi wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa ba tasa y ace ko da me da me aka haɗa aka bas hi bazawara ba ya so ba!

A gaba kuma mamakin da zai kama mai karatu har ya saka shi dariya shi ne, na yadda bazawara ta ke mayar da iyayenta rashin dattako. Kamar yadda yake cewa:

“Mai sa Dattijo a rena mai dattako,

Mai kai tsohonta ga rantsewar kaffara,

Zaura mai sa rabon gida ba a shirya ba,

Ke mai wanta zuwa cin ranin dole,

Mai sa rabon gida ba a shirya ba,

Da wa da ƙane da uwa kaka am ɓata sabad da ɗiya ga ta,

Dut ita ta tay yamutse danginta an dame.”

(Waƙar Zaura: Sanin Balɗo)

Rashin cika Magana yana daga cikin abin da yake jefar da girman mutum, ga bazawara kamar yadda makaɗin ya kawo ba wani abu bane. Hasali ma bazawara tana iya zama sanadiyar raba zumunci a tsakanin ‘yan uwa. Dalili kuwa shi ne, a duk lokacin da aka yi rashin sa’a akwai shagwaɓaɓɓiyar bazawara a cikin gidan gandu, d zarar wani ƙanin ubanta ya yi mata maganar dab a ta gamshe tab a sai ka ji ta faɗawa ubanta shi kuma idan bai kai zuciya nesa ba, yah au ya zauna ta yadda za a samu rashin jituwa. Kwana biyu sai ka ji ana cewa a raba gida, wani yana ƙorafin ana takurawa ‘ya’yansa.

5.0 Kammalawa

A wannan maƙala an yi ƙoƙarin fahimtar yadda aka dubi tsattsafin ban dariya ko kuuma a ce ita kanta daryar a cikin waƙar zaura ta Sanin Balɗo. tun da farko a cikin maƙalar an bayyana dangantakar da take tsakanin Ɗan Balɗo da bazawara da hart a saka shi yin wanan waƙa. a gaba kuma aka yi wiwayi ita kanta wannan kalma ta dariya, aka dubi yadda take da kuma yadda ake yin dariya aka ƙarƙare da ire-iren dariya. A gaba kuma aka kawo ɗanggin waƙar zaura ta Ɗan Balɗo a inda aka yi ƙoƙarin ɗora su a mizanin ire-iren dariya da ake das u, a ƙarshe an yi ƙoarin fitowa da mizani guda uku na ire-iren da ɗangayen waƙar suka hau. A ƙarshe aka rufe maƙalar da kammalawa.

Manazarta

Anka, M. N. (2001) Kiɗan Tama a Ƙasar Hausa: Bincike a Kan Alhaji Sanin Balɗo Waramu. Kundin Kammala Karatun Digiri Na Farko, Sashen Nazarin Harsuna Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Abdullahi, R. (1999) Mata a Adabin Baka: Nazari da sharhi a Kan Waƙar Bazawara ta Balɗo Kundin Kammala Karatun Digiri Na Farko, Sashen Nazarin Harsuna Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Bunza, A. M. (2011) Dariya a Bahaushen Ma’auni. Takarda da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani, Sahen Nazari Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar aduwa. Katsina.

Gusau, S.M. (2008) Waƙoƙin baka A ƙasar Hausa. Yanaye-yanayensu da Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited, Kano-Nigeria.

Tureta, A. T. (2010) Nazari a Kan Waƙar Zaura: Bincike a Kan Alhaji Sani Balɗo Waramu. Kundin Kammala Karatun Digiri Na Farko, Sashen Nazarin Harsuna Nijeriya.  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Post a Comment

0 Comments