𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Tabbas muryar mace al’aura ce mun sani. Amma yanzu sai in ga mata suna wa’azi wanda kuma muryar za ta karaɗe duniya! To don Allaah, su waɗannan muryarsu ta halatta ne sauran maza su ji, ko yaya abin ya ke ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa
Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
A fahimtar malamanmu muryar
mace ba al’aura ba ce, matuƙar
dai ba sirara muryar ko karairaya ta ta yi ba, yadda wani namiji zai yi sha’awa har kuma ya karkata gare
ta. Ubangiji Ta’aala
ya ce:
فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا
To, kar dai ku yi karairaya
da magana, sai wanda akwai cuta a cikin zuciyarsa ya yi tsammani. Ku dai faɗi
magana sananniya daidaitacciya. (Surah Al-Ahzaab: 32).
Abu ne sananne dai cewa: Tun
tuni mata suna yin magana da maza a wurare mabambanta, kamar a wurin ciniki da
yin fatawoyi da neman ƙarin
bayani a kan waɗansu al’amuran da suka shafi
addininsu da rayuwarsu. Abin da aka hana dai shi ne cakuɗa ko
keɓantuwa
a wanɗanda
ba muharramai ba a wurin da ka iya haifar da munana zato, kamar a duhu ko ɗaki
ko ofishi ko mota da sauransu.
Amma yadda mata suke fita
yanzu a cikkin taron jama’a maza da mata, ko kuma a cikin kafafen yaɗa
mabayanai na gargajiya da na zamani da sunan wa’azi ko faɗakarwa,
wannan kam ba shi daga cikin ayyukan mata a zamanin Sahabbai da Tabi’ai da
sauran magabatan wannan al’ummar waɗanda
aka yi musu shedar alkhairi. Kuma idan da wannan abin da ake neman yayata shi a
cikinmu a yau ɗin wani aikin alkhairi ne, to da kuwa
matan waɗanccan
zamunnan da suka fi namu alkhairi sun rigaye mu a kan hakan.
Muddin dai akwai mazan da za
su iya yin wannan aikin, kuma suna yin aikin yadda ya dace, kuma saƙonnin suna isa ko’ina kuma jama’a suna amfana yadda ya dace,
to a gaskiya ba sai mata sun bar muhimmin aikinsu na tarbiyya da kula da
gidajen mazajensu, sun shigo wannan filin ba. Ubangiji Ta’aala ya ce:
وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى
Kuma ku tabbata a cikin
gidajenku, kuma kar ku yi fitar gayu, irin fitar gayu na zamanin jahiliyyar
farko. (Surah Al-Ahzaab: 33).
Wato dai ita mace cikin gida
ne mazauninta, kuma tana fita ne kawai idan fitar ta kama, zuwa ga abin da ya
kama kaɗai.
Su dai waɗancan
matan salihai da suka gabata: Zama suke yi a cikin gidajen iyayensu ko na
mazajen aurensu, sai kuma ɗalibansu mata da yara su riƙa zuwa a lokutan da suka yanke musu,
domin ɗaukar
dukkan nau’uka fannonin ilimi a cikin gidajen. Su kuma manyan mazan da ba
muharramai ba, sai su riƙa
sauraro daga bayan shamaki. Kuma wannan ya isa kyakkyawan abin koyi ga
na-bayansu, in sha’al
Laah.
Amma yadda abin ya ke a yau,
akwai tsoron kar ya zama mafari ko mabuɗi
mai kai wa ga shigar da mata a cikin ayyukan da Shari’a ba ta saka su a ciki
ba, kamar shugabanci da waziranci ko alƙalancin
gari ko jiha ko ƙasa
da makamantansu. Ko kuma a shugabantar da ita a sallar jam’i da juma’a irin yadda ake ji da gani
a wadansu garuruwan ƙasashen
yamma da masu sha’awar
koyi da su. Wannan kuma duk a ƙarƙashin tsare-tsarensu ne na siyasar
dimokuraɗiyyar
zamani mai yayata maganarsu ta ƙarya
cewa: ‘WHAT A MAN CAN DO A WOMAN
CAN DO, EVEN BETTER!’
Wai: Duk wani abin da namiji ke iya yi, ita ma mace za ta iya, har ma fiye!
Wannan fahimtata kenan a kan
wannan al’amarin.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
+2348021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.