Ticker

6/recent/ticker-posts

Za Ta Karbi Addinin Musulunci

TAMBAYA (177)

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakaatuh dan Allah wane matakai zanbi idan ina so na musulumtar da wanda ba musulma ba?

Plc ataimakamin tambayane na gaggawa sabida wacce tayi tambayan tana makaranta ne yanzu aka tasamu wata da zata musulmta hmm Bata San ta wanne hanya zata sabida tafadamata addinin islam ba

Za Ta Karbi Addinin Musulunci

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Da farko dai za’a tambayeta shin tirsasa miki akai ki musulunta ?

Domin kuwa a addini Musulunci babu tirsasawa kamar yanda (Allaah Subhanahu wata’ala) yace:

( لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ ۖ

البقرة (256) Al-Baƙara

Bãbu tĩlastãwa a cikin addini,

Daganan sai ace ta maimaita kalmar Shahada kamar haka:

Ash-hadu, anla ilaha, illallahu, wa ash hadu, anna, Muhammadan, abduhu, warasuluhu

Ma’ana:

Na shaida, Babu abin bautawa da Gaskiya, sai Allaah, Kuma na shaida Annabi Muhammadu, bawanSa ne, kuma ManzonSa ne

Shikenan ta zamo musuluma, dukkan zunubbanta Allaah zai kankare mata su, idan ya ga dama kuma ya maidasu lada

Sai ace ta zabi suna daga cikin sunayen Musulunci. Daganan Kuma sai tayi wankan Shiga Musulunci sannan a hadata da Mata (Ahlus Sunnah) wadanda zata koyi addini cikin sauƙi a wajensu kuma a sakata a makaranta. Domin kuwa idan kuka hadata da yan Bidi’ah to tabbas bazasu dorata akan Minhajin da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya dora al’ummar sa akai ba wato Kitabu was Sunnah (Ƙur’ani da Sunnah)

Muna roƙon Allaah ya karbi shahadarta ya tabbatar da ita da mu akan Addinin Islam domin kuwa Allaah yace:

( إِنَّ الدِّينَ عِندَ اللَّهِ الْإِسْلَامُ ۗ

آل عمران (19) Aal-Imran

Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci.

Wallahu taala aalam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments