Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ba Ya Kula Ni, Ina Neman Shawara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum Nice ta uku amatan shi, amma bamu zauna tare ba, nazo nasamu mace ɗaya mukayi zaman shekara ɗaya suka rabu yadawo da ɗayar itama zaman shekara ɗaya suka rabu. Uwar gidan yaranta huɗu na biyu kuma yaranta biyar Amma in yakawo mana garin tuwo kwanu goma toh idan yakare in zan gaya masa sena bishi har wajan get kamin nafada masa, hakama shinkafa yakawo kwanu uku ko biyu in yakare wataran senadau komai raguwar yagani nafara lissafamai ranakunda muka dafa Hakama taliya, gashi in yadawo daga wajan aiki, in naje nakaimai abinci namai sanda zuwa, ya amsa toh Wallahi malam in zan shekara ina maimagana Wallahi banida amsa Yarana in suna son abu agunsa senagayawa karamin yaron ɗayar matar sesuje kamin nan yabasu, amma in sukaje zasu nemi abu agunsa Wallahi baze basuba Kuma Malam kuɗin chafane yabani ɗari biyar, museya mai kwata ɗari biyu da hamsin barkono maggi komai aciki in nagayamai seyace, wai shi ɗin ai ba kyauta akeba shi kuɗin ba Gashi acikin yaran akwai me shekara ashirin da huɗu akwai me da uku, mata uku maza Tara harda nawa, ya aurar da ɗaya Kuma yara nane kananu Malam narasa yadda zanyi gashi ni yanzu shekara ta talatin da ɗaya shi kuma yayi tamanin Kuma malam Wallahi semuyi wata biyu ko uku ko huɗu Wallahi be yi kwanciyar aure daniba, Yanzu da nake maganan nan Wallahi Allah rabona dashi tin azumi da kwana biyu, se shekaran jiya kuma😭 toh tin ina hakuri Wallahi malam nagaji bazan iya wayan nan watannin nan ba. Yanzu sha’awata karuwa yakeyi, kuma in na tambayeshi namishi wani abunne yayi hakuri yagaya min seya cemin bayasan surotu in natakurashi seyacemin wai banida hankali Nagayawa iyayena wai sukacemin bana koshine narasa mezan ce musu bankara gayamusu bah Nagayawa wakilina yazo yasameshi wai yacemai ina rufedakina kuma wallahi bana rufewa wataran shiyake rifewa yana kallan nawa a buɗe bazece narifeba sede yagayawa yanmatan surufe nasu amma ni seran da ya gadama zenemeni Amma in naje ɗakinsa dan kaina baze kulaniba wataran, har kuka ina masa amma ko kulani bazeyiba Nagaji malam, kuma banason tafiya nabar yarana, sune kananu, kuma wallahi manyan yaran nasa mugayene yarana zasu sha wahala agunsu in natafi Waiyo Allah nashiga uku narasa me tausayamin narasa inda zankai kukana narasa yadda zanyi nagaji Wallahi kuma ina kasuwanci Kuma ina kare mutuncina ina addu’a koda yaushe Allah yakareni malam amma wataran ina tinanin wasu abubuwanda basu kamataba araina toh kar shaiɗan yaci nasara akaina katemakeni kai malamine zakabani shawara zakatausaya wa halinda nakeciki nagaji Wallahi Allah ya zabomin abinda yafi alkhairi arayuwata.

MIJINA BA YA KULA NI, INA NEMAN SHAWARA:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa AlaikisSalaam:-

Toh Allah ya shirya Gaskiyar magana shine wannan Zalunci ne da Rashin Tausayi da Rashin Adalci, yau ko da ace wani abun ne Kika Yi Masa ai yakamata ace ya fito Fili ya Miki magana, domin ki gyara ya ci gaba da kula da ke da Yaran ki da Rayuwar ki.

Amma wallahi Ba daidai bane ace Namiji kafin ya Auri Mace Yana son Mace Kamar zai mutu Amma daga baya ya dawo Yana azabtar da ita, wannan kuskure ne wallahi shi Bai sani ba Yana Ɗaukar kansa laifin da a ranar Alkiyama zai Yi Nadamar Ayyukan sa ne wallahi. Shekarar sa 80 ko yanzu ko gobe mutuwa zata iya riskar sa Amma meyasa ba zai gyara Rayuwar sa ba? ko Yana Tsammanin Cewa Cutar da ke da yake Yi Allah ba zai tambaye shi bane? Wallahi ko Baya so sai ya amsa tambaya a gaban Allah, idan har ba ki yafe Masa na irin cutar da ke da Yake Yi da wannan Zaluncin ba, Dole Sai ya Dandani Azabar Allah wallahi.

Bai dace ba idan kin Yi Masa wani Abu ne ko akwai abun yake gani a jikin ki wadda baya so sai ya fito ya Gaya Miki ki gyara ya Gaya Miki irin abun da shi yake so yake Burge sa wannan shine Rayuwar Auren, Amma bawai Haka kawai sai dai Mace ta ga Miji ya juya Mata baya wani zai Fi Shekara ma Bai Yi Jima’i da Matar sa ba Wai Yana hora ta, wannan Zalunci ne da Rashin Tausayi wallahi.

Yanzu idan Ɗiyar sa ce Mijin ta yake Mata irin yadda yake Miki zai ji daɗin Haka ne? Shin wanne irin Mataki zai Ce zai ɗauka akan wannan Mijin, Amma meyasa ke yake cutar da ke? Bai kamata ba.

Da ace Matsalar Abinci ne kawai da Kuma bayanin da Kika Yi a sama Rashin kula da Yaran ki da ke kanki, wannan Dole ne a ba ki Hakuri ace ki Jure Halin sa domin yanayin da ake Ciki kenan a yanzu, Amma Abun da ya shafi Jima’i ayi wata 1 ko 4 namiji Bai sadu da Matar sa ba wani har Shekara 1 ba Jima’i da Matar sa, kuma Suna Gari Ɗaya shi ba matayi bane Wadda zai Ɗauki watanni baya Gari, Kuna Gari ne tare tana da Lafiiya shima Mijin Lafiyar sa Ƙalau Amma babu Jima’i.

Toh wannan kwata-kwata Babu Tausayi da Imani kuma wallahi wannan Zalunci ne Kai Tsaye da cutarwa, Kuma Addinin Musulunci Bai yarda a cutar da wani ba.

A Shari’ar Musulunci ma wata 4 da 10 kaɗai aka bawa namiji a duk inda yake ya dawo domin kula da Matar sa da Jima’i da Sauran bukatar ki, wannan Wadda baya Gari kenan Amma shi Kuma ga shi Kuna tare Gari Ɗaya gida Ɗaya ya Ƙi yin Jima’i da ke Kuma Lafiyar sa Ƙalau, maganar gaskiya akwai Cutarwa a ciki wallahi Kuma sai Allah ya Tambaye shi.

Ai wallahi idan ba ki tsare kanki ba a Irin hakan ne wallahi Muna samun Matan Aure a yanzu dayawa suna fita suyi Zina da Maza waje, ko Kuma su Rika Biyawa Kansu bukatar su Suna Jin daɗin su, Zamanin Babbar waya maza Suna bin Mata a WhatsApp Matar Aure tun Bata so har ta amsa su ruka yin komai, kana tambayar ta zata ce Mijin ta ne Bai kula da ita ko Kuma Baya Zama ga Sha’awa na damun ta abun yafi Karfin ta, maza Kun San ba za ku iya rike Matan ku ba meyasa zakuyi Auren? irin wannan Babu kyau Bai dace ba Kuma Babu Adalci ko Tausayi a wannan Lamarin. Sai Allah tambaye ku idan Babu amsa akwai Azabar Allah wallahi.

Idan laifi Kika Yi Masa ko Kuma akwai abun da yake damun sa ko an Yi gulmar ki a gurin sa, ko shi ɗin Bai da Lafiya sai ya fito ya Miki bayani Amma bawai ya Rika azabtar da ke a irn wannan ba.

Sabida Haka, abun da zakiyi a yanzu shine ki sake neman Waliyyin ki ko Waliyyin Mijin naki, ki same su ki karanta musu Bayanin ki, ki Gaya musu idan ma ba su yarda abun da Kika ce ba, toh su saka ayi musu bincike idan hakane a karɓa Miki Yancin ki idan ba Haka bane ke kin yarda kin Yi Masa Karya Amma ki Gaya musu kin gaji ke ba za ki iya ba.

Sabida Haka ki same su ki Gaya musu ki ce Gaskiya ke kin gaji kiyi musu barazanar Cewa idan ba zai iya ba kawai ya sake ki kowa ya je Allah ya haɗa da Rabon sa.

Idan sun neme shi ya Ƙi ki zuwa ko ya Ƙi Sauraron su ko an Gaya Masa ya Ƙi ya koma yin Jima’i da ke baya kula ki, toh kina da Damar Kai shi gaban Alkali Masanin Shari’ar Musulunci ki je kiyi Masa bayani, Alkali zai tambaye shi Bai da lafiiya ne? Idan yace Eh Alkali zai ba shi damar ya je ya nemi magani ke Kuma kiyi Hakuri, Za’a Yanka Masa lokaci idan Lokacin ya Cika za ku dawo gaban kotu a tambaye ki Yana Jima’i da ke Yana kula da ke? idan kin ce Eh shikenan sai a Sallame ku, idan kin A’a har yanzu babu Abun da ya chanja baya Yi, toh Alkali zai sa ya sake ki ko Kuma shi Alkalin ya rubuta Takardan Saki ya ba ki. Wannan shine ka’idar Shari’a.

Kada ki damu da Cewa Yaran ki za su wahala ko wanin sa, Allah ne Mai tsare su ko kina Nan ko ba ki Nan Suna tare da kariyar Allah. Akan ki koma aikata Saɓon na Zina ko ki Rika bin Maza na WhatsApp ko Facebook ko ki rika Biyawa kanki bukata kina ji daɗin ki, wallahi gara Auren ki ya Mutu, ai ko da ace akwai ci da Sha ne Yana Miki, Amma babu Jima’i ba kowacce Mace ce zata iya jure wannan ba su ɗin ma Iyayen ai sun San da hakan.

Don Haka akan ki Saɓawa Allah kiyi Zina da Auren ki ko ki rika Biyawa kanki bukata ko wanin sa Saɓon Allah, toh gara Auren ki ya Mutu kowa ya je Allah ya haɗa shi da Rabon sa, wani rabuwar ma matukar an Yi sa akan tsarin Shari’ar Allah toh In Sha Allah Alkawarin Allah ne wannan Za’a ga Alkhairin rabuwar.

Ai Irin hakane wallahi dayawa a yanzu Matan Aure suke fita su yi Zina iya son ran su da bin maza na WhatsApp, duk Irin Zaluncin Mazan ne ya kawo hakan. Allah ya shirya, Fatan kin Gane bayanin??

WALLAHU A’ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments