Ticker

6/recent/ticker-posts

Malam Ta Yaya Ka Karanta Wadannan Littattafan Da Yawa Haka

TAMBAYA (172)

Jazakallahu khairan, malam naji voice naka na littattafanda ka karanta kabamu shawaran mu karanta.

Malam kozaka fadamana yanda kasa musu lokaci ka karanta. Saboda yanayin rayuwa ga kasuwa da makaranta da sauransu

📚MALAM TA YAYA KA KARANTA WADANNAN LITTATTAFAN DA YAWA HAKA?

AMSA

Karatu Sakaine kuma kema zaki iya yar uwa maimuna. Saidai it really takes time. Ki tsara time table ta Yanda zaki dinga karanta Littattafan a tsare. Kinga iya waɗancan guda 24 din da na bada shawarar a karanta tun 2021 nake karatunsu (for almost 2yrs) sannan na ƙara 1 year Ina fahimtarsu daki daki

Ko lokacin da naje Lagos harkan kasuwanci banyi Wasa da karance karance na ba, na samu ƙarfin gwiwar yin Da’awah tun a Lagos a gefe guda Kuma ana samun Dawa (kudin business) da ace na biyewa son zuciya kuma da tuni nayi Dawa😃

Ko a lokacin da Ina Jami’ar Bayero ta Kano, gaskiya nafi fifita bangaren research dina akan Course dina na Microbiology, yan department dinmu sune shaida, wanda silar research da nake aka bani AWARDS dayawa, irinsu "BEST PERSONALITY OF THE YEAR" wanda kungiyar dalibai ta SUG suka bani a 2018/19 da Kuma "USMANNOOR MEDIA LEGEND" wanda MBBS students suka bani, sannan kuma musamman "BUKITES DIARY" sukayi launching littafi a Coronation Hall aka gayyaceni Kuma a cikin littafin naga an saka sunana a matsayin wadanda suka bawa BUK gudunmawa ta bangaren "RESEARCH" da Kuma "DA’AWAH", nayi mamaki matuƙa duk da dai nasan ban cancanta ba amman nasan daga Allaah ne, akwai kuma certificates da kungiyar daliban BUK mazauna Kano suka bani da wasu certificates khatheran katheeran da ba sai na zayyanosu gaba daya ba

Kuma a matsayina na Class Captain na Microbiology (Kamar yanda shima suka bani AWARD: Capacitated Class Captain na Faculty dinmu), ayyukan sunamin yawa kamardai yanda sukaimin yawa a lokacin da aka zabeni as Class Captain a makarantar sharar fagen shiga Jami’a wato CAS Kano. A CAS Kano ma kullum cikin research nake, kafin nanma a boarding school dinmu (Dawakin Tofa Science College) anfi sanina da Research, wanda tun muna SS1 na fara karatun haddace Dictionary (Adɓanced learner 8th edition). Harma yan set dinmu suke cemin Mai boshon ruftu😂bi Ma’ana karatun da nake bazai amfaneni ba amman Alhamdulillah a karshe na fita da kyakkyawan sakamako (both all science subjects din da Kuma English din) Kuma Naga tasirin karatun Dictionary dinnan domin kuwa nayi participating a kungiyar marubuta ta arewacin Nigeria wato ANSA (Association of Northern Nigerian Authors). Sun cireni ne sakamakon wani Poet da wani Christian ya turo wanda yaci karo da koyarwan addininmu na Islam nayi criticizing din abin da big big grammar words silar remoɓing dina kenan

Na karanta Littattafai sama da guda 200 Kuma har ynɗn akan karanta wasu nake. Kuma kullum ji nake Kamar ma ba abinda na karanta

Littattafan da nake dasu, iya softcopy (PDF) Sun zarce 400. Kuma akwai hardcopies alot. Na koyi yawan karance karance ne a wajen malami wanda na amfana da ilimin da matuƙa wato: Shaikh Hamza Yusuf Hanson (Founder Zaytuna College, California, USA) wanda duk sanda zaka ganshi Yana tafiya to da akwai Littattafan da yake nazari a ƙalla guda 6 a taredashi, he’s literally a Bookworm or Pedant. Kuma Alhamdulillah silar wannan Da’awah mun hadu da malamai da dama a taron shekara (2019 Annual Islamic Conference) da aka gabatar @The Afficient GRA, Kano, kamar irinsu Shaikh Assim Alhakim Wanda yake daukanmu darasin "SEERAH" a makarantar"ZAD ACADEMY" dake Makkah. Irinsu Dr. Muhammad Salah, Shaikh John Fountain, Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya (Wanda Yana bani Shawarwari) da dai sauran Ulama’u magada Annabawa, wasu Kuma a media platforms muka hadu Wanda ba saina zayyano sunayensu ba saboda yawansu

Tabbas karatu yana da dadi ammanfa sai an tsarkake zuciya, an dage da addu’a Kuma sai an hana Ido bacci. Rabon da nayi bacci tun 12 na dare na manta, saidai wajen 2 ko 3 na dare saboda saƙonnin tambayoyi. Musamman ma yanzu da Malam Khamis bin Yusuf yace na dinga bada gudunmawar amsoshin da hujja daga ƘUR’ANI, HADISI, ƘIYASI da IJMA’IN magabata a Zauren nan na TAMBAYA DA AMSA

Astaghfirullah, ba Ina fada bane don fariya (proud) saidai don Maza da Mata musamman iyayen da suke a wannan zaure na Tambaya da Amsa su dage da tarbiyyantar yayansu ta yanda zasu taso da bincike na ilimin addini da na Boko

Fatanmu dai Allaah yabamu ikon amfana da karatun da muke ya tabbatar damu akan ikhlasi ya rabamu da riya

Nasara, haƙuri da jajircewa a rayuwa ne yasa har Allaah ya bamu ikon bude "USMANNOOR ONLINE ACADEMY" wanda daruruwan mutane daga ƙasashe sama da 10 sukai registration ta online kuma kullum ake ci gaba da shigowa, kuma wataran inda rai da lafiya zamu tattauna sosai akan tarihin rayuwata a matsayina na dalibin ilimi, da rayuwar malamai, da ma rayuwar marubuta da sauran daliban ilimi maza da mata, maybe a USMANNOOR TƁ, Idan Allaah ya bamu ikon budewa Nan gaba. Idan Kuma Allaah ya dauki rayuwarmu to Ina roƙon Allaah yasadamu a ALJANNATIL FIRDOUS baki daya

Wallahu taala aalam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments