Ticker

6/recent/ticker-posts

Macen Da Ta Yi Zina Kwana Nawa Ne Istibra’i Dinta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa me ISTIBRA’I ɗin ta?

Macen Da Ta Yi Zina, Kwana Nawa Me Istibra’i Ɗin Ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaikumus salam, To ‘yar’uwa Allah ya haramta zina kuma ya sanyata daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba. Idan mazinaciya ta tuba, malamai sun yi saɓani game da iddarta.

1. Akwai waɗanda suka tafi akan cewa za ta yı jini uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya wajaba ayı abin da zai tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita da kuskure za ta yi, da kuma wacce aka şaka.

2. Za ta yi jini ɗaya kawai, saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam "Ba’a saduwa da mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma sai ta yi haila ɗaya" Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito.

Don neman Karin bayani duba Almausu’a Alfikhiyya Alkuwaitiyya 30/341.

Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana tabbata da jini ɗaya, sannan iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya, saboda iddarta ana tsawaitata ne don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa babu shi a iddar zina.

Allah shine mafi Sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

HUKUNCIN YIN AURE KAFIN A YI ISTIBRA’I

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam nayi zina saura sati ɗaya a ɗaura mana aure, kuma ya kamata a ce na yi istibra’i kafin na yi aure, amma ban yi ba, har na yi aure, yanzu haka ina jini na farko ban yi tsarki ba, amma ba da wanda na aikata laifin na yi aure ba. Ya ingancin aure na? Gani nake kamar babu auren.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:- Toh farko dai ina miki wasici da jin tsoron Allah saboda zunubin da kika aikata, amma game da aure, to aurenki ya yi, saidai yinsa bayan istibra’i shi ne ya fi, sannan ya wajaba mutukar kin san kina da ciki to bai halatta ki bawa sabon mijinki dama ya take ki ba, saboda faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” Abu-dawud : 1847.

Don haka ya wajaba a gare ki ki yi stibra’i kafin mijinki ya sadu da ke, sannan istibra’i jini ɗaya ne, idan kuma har kin ɗauki ciki, kafin ki yi istibra’i, in kin haihu kafin wata shida (6), to ba ɗan sa ba ne, amma in har kin haihu bayan wata shida (6) daga fara saduwar ku, to ɗan sa ne, mutukar ba’a samu shaidar da take nuna kina da ciki ba, tun kafin ku fara saduwa .

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu kudaamah 8\79.

ALLAH NE MAFI SANI

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments