Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Kallon Blue Film Ni Da Matata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Kallon Blue Film? Shin Ya Halatta Mu Rika Kalla Ni Da Matata?

ZAN IYA KALLON BLUE FILM, NI DA MATATA?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

A’A bai halatta ba ta kowacce fuska. Domin illoli da dalilai kamar haka:

1. Allah yana cewa:

قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ ۝ وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ

"(YA MUHAMMADU KA GAYA WA MUMINAI MAZA SU RINTSE IDANUWANSU (DAGA KALLON HARAM) KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU (DAGA ZINA DA DANGOGINTA) YIN HAKAN SHINE MAFI TSARKAKA AGARESU, DOMIN ALLAH MAI BADA LABARI NE AKAN ABIN DA SUKE AIKATAWA (AƁOYE KO AFILI). KUMA KA GAYA WA MUMINAI MATA SU RINTSE IDANUWANSU (DAGA KALLON HARAM) KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU...." [Suratul Nuur Aya ta 30-31]

2. kallon tsaraici haramun ne. Kuma kusantar zina ne. Allah yana cewa:

وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا

"KADA KU KUSANCI ZINA" [Suratul Isra’i aya ta 32].

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa: "ALLAH YA TSINEWA MAI KALLON TSARAICI DA KUMA WANDA AKE KALLON TSARAICIN NASA."

3. wannan kallon blue film ɗin, shima wani nau’i ne na zina. Domin Manzon Rahama (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa: "ZINAR IDANUWA SHINE KALLON (ABINDA BAI HALATTA BA).

4. Yanzu Kai Ɗan’uwana ba zakaji tsoron Allah ba! Ka rika kallon fasadi tare da iyalinka alhali kana sane da cewar yin hakan rashin jin tsoron Allah ne! Kana koyar da matarka kenan yadda ake yin ba’dala ta Zina.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yace "...mata kuma su kiyaye mutuncinsu [farjinsu, daga aikata zina] domin sunfi yawa a wuta."

WALLAHU A’ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments