Ticker

6/recent/ticker-posts

Ganin Maniyi (Sperm) A Waje Bayan Mu’amalar Aure

TAMBAYA (176)

Snnn kuma Maye matsalar Idan nagana Tarawa da Iyalina, sai naga Sperm din a waje?. Ma’ana ya zuba a kan Gado?. Kodai Baya shiga ciki?. Sbd ni abin Yana Bai tsoro. Ko Idan na kawo gaban ne yake fitowa wajen ya zubar da maniyyin a waje?. Shine Abinda na kasa Ganewa. Wnnn itace tanbayata ya Sheikh.👍🏻

AMSA

Alhamdulillah

Wannan ba matsala bane ai, dan uwa

Saboda a duk digo 1 na sperm akwai at least 3 zuwa 5 milliliters na semen, wanda kowannen milliliter 1 yake dauke da ƙwayoyin halittu masu rai (sperm cell) daga Miliyan 20 har zuwa Miliyan 300

Kaga kenan digo 1 na maniyyi (one drop) kadai zai zama silar samun juna biyu. Sai ka tuno da hadisin da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yacewa Sahabbansa ko da kunyi azalo (coitus interruptus) ma’ana fitarda maniyyi a waje (outside the ɓagina) don tsawaita haihuwa, idan Allaah ya ƙaddara samun haihuwa a tsakaninku to ba shakka sai an samu ciki

Kenan ba wai dole ne sai gaba dayan sperm din ya shige gaban macen ba kamar yanda kake thinking

Wannan ikon Allaah ne Mai yanda ya so don ya nuna ikonSa akan yanda yake halittar Dan Adam daga ƙwayar halittar sperm cell wadda mutum bazai iya gani da idanunsa ba saida taimakon Microscope

Allaah buwayi gagara Misali

Sannan kuma idan mutum yana fama da matsalar ƙarancin Maniyyi to a shawarce ya dinga shan Lemo (orange) ko kuma grapefruit juice

Idan mutum yana son cikakkun bayanai da suke da alaƙa da issue na aure to Albishirinku domin kuwa mun bude makarantar "MU’AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI", kuma karatunmu yayi nisa. Don haka duk wanda yake da ra’ayin shiga wannan makaranta sai yayimin magana ta Priɓate chat

Wallahu taala aalam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

FITAR MANIYYI SILAR KARATU

TAMBAYA (180)

Assalamu alaikum waharahmatullah mlm barka da sfy ya kokari ya kuma ɗalibai.

Mlm ina da tambaya, mutum ne yake sauraran abu buwa wanda suka shafi ma'amala ta aurataiyya dan yasami wani ilimi akai amma kuma bashi da aure to sai Saura ran abin yasa yana tadamashi da sha'awa har yafitar da maniyyi ko maziyyi amma baiyi wasa da gaban saba (istimna'i) meye hukuncin hakan mlm.

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Idan Maniyyi ya fita ko a bacci ko a farke to wanka ya wajaba, fitar maziyyi da wadiyyi kuma basa wajabta wanka, wanke gaba daya al'aurar ya wadatar

Sannan kuma idan yana sauraro ne don ya biya buqatarshi ta sha'awah to anan yana da laifi amman idan don ya ilimantu ne ko kuma ya ilimantar to shima akwai sharadi ya zamana bawai Video bane ba irin wanda masu koyarda karatun zaka ga suna wasu abubuwa da zasu dinga tada sha'awar mai kallon da saurarensu

La'akarida yanzu yanzu muna wani zamani wanda zakaga abubuwan alfasha sun yawaita a media platforms kamar yanda CEO din WIKIHAUSA yake fada min cewar rubuce rubucen mu sune suke daqile wasu mutanen da suke fadawa tarkon shaidan, a maimakon mace ta hau internet da niyyar koyon mu'amalar auratayya sai ta bige da koyon yanda ake Madigo (Lesbian)

Wannan dalilin ne yasa muka ga dacewar saka karatun littafin: "Guidelines To Intimacy In Islam" ma'ana: "Mu'amalar Auratayya A Musulunci" wallafar Shaikh Muhammad Adam Alkauthary. Wanda a yanzu haka mutane dayawa sunyi Registration a qarqashin sabuwar makarantar: "USMANNOOR ONLINE ACADEMY"

Manufar mu itace mu tunatar da mutane cewar ga hanyar da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi mu'amalar aure da matansa ta yanda zaa yi koyi da Sunnah: ga ilimantuwa ga kuma tarin lada. Kuma karatun namu ba na Video bane ba, na Audio ne, muna karanta abinda yake a rubuce mu fassarawa masu saurare

Wanda yake da niyyar Registration (musamman wadanda akaiwa Engagement) sai ayimin magana ta Private, hukumar makaranta zata turo maka dokokin shiga sannan kuma za'a iya turowa mutum karatuttukan da suka wuce shi

(WhatsApp: 07035387476)

Wallahu taala aalam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments