TAMBAYA❓
Assalamualaiku mlm Ina wuni ya aiki ALLAH yabada sa’a ameen dan ALLAH mlm tambaya ce zan yi akan magada wasu ne baban su yarasu a kabar musu kudi dubu dari shida toh yaya za, araba masu su Mata guda 5, maza 3 sai uwa 1
AMSAH❗
Awa’alaikumus salamu wa rahmatullah
Yan da ya rabon gadon zai kasance shine za a bawa
mahaifiyar sa daya cikin shidan abun da ya bari, sai kuma sauran abun da ya
ragi na kudin sai ƴaƴan sa su raba a tsakanin
su maza suna da rabun mace biyu,
masali
500,000 ne yai saura sai mu dauka yaran nasa guda goma sha daya ne dukkan su
mata ne tun da namiji ya na ɗaukar kaso biyu
na mace sai mazan su dawo amtsayin mace Shida to kin ga in aka raba dubu dari
biyar kaso goma sha daya sai matan kowacce ta dauki kaso daya su kuma mazan su
dauki kaso biyu-biyu, haka ne yan da rabon gadon zai kasance, hujjar hakan tana
cikin suratun nisa’i aya ta shida.
ALLAH SHINE MAFI SANI
{AMSA WA ABU ABDULLAH}
*Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.