Citation: Yakasai, S.A. (2024). Matsayin Waƙa a Adabin Sinawa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 47-53. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.006.
Matsayin Waƙa a Adabin Sinawa
Salisu Ahmad Yakasai, FLAN
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto
(+234) 08035073537
syakasai2013@gmail.com
Tsakure: Confucius masanin falsafar nan na ƙasar Sin, shi ne ya bayyana adabi a matsayin rumbu na hikima. Ya faɗi haka ne a lokacin da yake nazarin irin dangantakar da take tsakanin
adabi da hikima da kuma ƙumshiyar kowanne domin ci gaban al’umma. Wen tana nufin ƙirƙirarrun ayyukan adabi, a yayin da dao take nufin hikimomin da suke
ƙumshe a cikin irin waɗannan ayyuka. Marubutan ƙasar Sin sun yi ittifaƙi cewa adabi rumbu ne na hikima, tamkar mota ce mai ɗauke da kaya. Wato hikima ita ce kayan da babu mai ɗaukarsu face adabi. Ƙumshiyar wannan maƙala ita ce tsokaci a kan matsayin waƙa a adabin Sinawa. Domin cimma wannan manufa, an karkasa maƙalar gida biyar. Kashi na farko da na ƙarshe, shimfiɗa ce da naɗewa. A kashi na biyu an waiwayi ma’anar waƙa da karin waƙa da zubi da tsari cikin yabo da zambo da kuma matsayin waƙoƙi gama-gari. Kashi na uku kuwa ya taɓo ƙa’idojin rubutun zube ne da waƙa, wato fasaha a cikin manufofin waƙa da kuma amfani da adon harshe a waƙa. Kashi na huɗu misalai
ne na yanaye-yanaye da waƙoƙi sukan bijiro kamar saƙon zuci da kaɗaici da baƙin ciki da kishin zuci da kuma tarihin al’umma.
Fitilun
Kalmomi: adabi, Sinawa, hikimomi, waƙoƙi,
ƙa’idojin
rubutun
Gabatarwa
Sinawa kamar Hausawa sun aminta da maganar hikimar nan da ke
cewa waiwaiye adon tafiya ne. Saboda haka, bari mu fara waiwayar shin ina ne ƙasar Sin, sannan daga baya mu ɗora
da sanin al’adar Sinawa a matsayin sharar fage. Zhongguo wato ƙasar
Sin, ana amfani da wannan kalma ne domin bayyana wuraren da suke daura da
tsakiya da kuma ƙasan Rawayen Kogi,
inda al’ummar Huaxia ta dauri ko
kuma al’ummar Han suka zauna. Tun
farko dai wannan kalma tana nufin dukkan wannan yankin da kuma al’adun al’ummar
da suke zaune a wurin. Su al’ummar Huaxia
sun zauna ne a daura da wannan Rawayen Kogi. A tunaninsu wannan wurin da suka
zauna shi ne tsakiyar duniya, kuma shi ne dalilin da ya sa suka kira wurin da
Zhongguo (wato tsakiyar ƙasa ba kamar waɗanda suke kewaye da ita ba). Daga baya kuma sai aka koma ana
amfani da Kalmar da nufin sararin ƙasa na tsakiyar arewacin ƙasar Sin da kuma al’ummar da suka zauna a wurin. Tun daga
zamanin Daular Qing, ana amfani da kalmar Zhonggou
ne da nufin dukkan iyakacin ƙasar
Sin da ikonta. A yanzu ana amfani ne da kalmar a matsayin taƙaitaccen sunan tarayyar al’ummar Sin.
Ta ɗaya haujin kuma
suna amfani da kalmar Zhongua (wato
al’ummar Sinawa da al’adarsu). Shi wannan suna taƙaitacciyar ma’anar gamaɗen kalmar da
aka ƙirƙira ce daga Zhongguo
da kuma Huaxia. A nan kalmar hua tana nufin fure ko fulawa, wadda
aka yi amfani da ita cikin adon harshe domin bayyana kyakkyawar al’ada.
Kakannin al’ummar Huaxia su ne suka zauna a daura da Rawayen Kogi, wanda suka ɗauka cewa nan ne tsakiyar duniya (zhong), kuma wurin yana ƙumshe da
kyawawan al’adu (hua) don haka suka
kira shi da zhongua. Wannan wuri
cike yake da ƙabilu daban-daban, waɗanda kuma al’ummar Huaxia suka mamaye. Daga baya ne yankin da suka faɗaɗa ya zamo cikin zhonghua, wanda a zamanin yanzu ake wa laƙabi da al’ummar Sinawa da al’adunsu. Al’ummar Sinawa
suna da karamci (wato zhongyong).
Ita wannan kalma Confucius ne da almajiransa suka aminta da ita a matsayin ƙololuwar nagarta. zhong
na nufin sanin yakamata a cikin nagarta da aiki. Da yake komai yana da iyaka,
to ba a son ƙaranta ko kuma wuce gona da iri a
kowane al’amari. Yong na da ma’ana
guda biyu, ɗaya daga ciki ma’ana ce ta kara-zube, ɗayar kuma ba ta canjawa. Sanin yakamata lamari ne da
za aiya ɗabi’antuwa da shi a tsawon lokaci a zamantakewar
rayuwa. Don haka zhongyong tana
nufin ƙololuwar karamci da mutum zai nuna a
cikin mu’amalarsa da sauran mutane a rayuwa ta yau da kullum.
Mece ce Waƙa?
Waƙa tsararriyar magana
ce ta hikima. Zubinta ƙirƙira ce a cikin haɗakar tsarin adabi da kiɗa da kuma rawa.
Bambancin kiɗa da waƙa a zamanin Sinawan
dauri shi ne, a yayin da guda ana sanya kiɗa, to a ɗayar kuma babu. Wato akwai bambanci a
tsakanin waƙa mai ɗauke da da kiɗa da kuma wadda aka rera kawai. Ita wadda aka
yi kiɗa tana tafiya da hawa
da sauka na murya da aka tanada mata, amma a ɗayar babu. Ga misali kamar a waƙar Taka a Sannu ta daular Han ko kuma waƙar Chile a zamanin daulolin arewaci. Sai
dai kuma akwai waƙoƙin masana irin su Li Bang (Matsananciyar Guguwa) da
Li Bai (Waƙe-waƙen al’ummar Wu) suka rubuta. Saboda haka waƙoƙi suna daga cikin
fasahohin Sinawan dauri, waɗanda kuma ake kassafawa a matsayin yuefu na Sinawan dauri. A wannan zamanin ana ɗaukar su a matsayin
wani ɓangare na waƙa kawai.
Dangane da karin waƙa (qu) kuwa, kalma ce ta adabi da ta samu
bayan waƙa. Kalmar tana nufin salailan Karin waƙa na arewaci da kuma
kudanci da aka ƙirƙiro a daulolin Song
da kuma Jin. Asalin kare-karen waƙoƙin arewaci an yi su
ne a arewacin ƙasar Sin, kuma aka aiwatar da su a cikin karin harshen
arewa. Su kuma kare-karen waƙoƙin kudanci an yi su
ne cikin karin harshen kudanci. Tunda qu
ta samu karɓuwa a daular Yuan, sai aka ci gaba da kiranta Yuan qu ko kuma Yuan opera. Hasali ma ita qu tana da kamanni da ci a cikin zubi da tsari, amma sun
bambanta a cikin tsarin jumla da kuma amfani da harshe. Akwai qu iri biyu, wato zaju na arewaci da kuma chuanqi
na kudanci. Irin wannan qu ana
kiransu da xiqu ko kuma juqu. Ɗayan kuma shi ne sanqu ko kuma qungqu. Kamar sauran zubi da tsari na waƙa, sanqu yana bayyana yanayi ko al’amari
ko sosuwar zuciya ne a waƙe, amma babu sassa daban-daban da za a furta a magance. A
gaskiya ma dai salon da ake amfani da shi a dauri ya fi yin tasiri fiye da na sanqu. Zamanin daular Yuan an samu bunƙasar waƙoƙin Sinawa. Ga misali,
akwai marubuta fiye da tamanin a wancan lokacin. Mutane irin su Guan Hanqing da Bai Pu da Ma zhiyuan da kuma Zheng Guang sun wakilci salailai daban-daban na yin waƙoƙi a Yuan opera. Haka kuma an ɗauke su a matsayin manya-manyan gwanaye guda
huɗu da duka jagoranci
rubuce-rubuce a Yuan opera. Ita wannan Yuan opera tana da tsari
na musamman, wato ta haɗakar daulolin Tang da Song da Ming da kuma Qing, tsarin ya samar da muhimmin
tasiri a cikin bunƙasar adabin Sinawa.
Ta fuskar zubi da
tsari da suke kira gediao kuwa,
kalmar tana ɗamfare ne a cikin ƙumshiyar jigon waƙa. Haka kuma tana da
nasaba da hikima da zalaƙa a cikin tarƙen waƙa. Ge tana nufin cika ƙa’idojin da aka
tanada domin arulin (ma’aunin) waƙa, a yayin da diao take nufin hawa da sauka na murya
a cikin waƙa. Wasu masana tarƙen waƙa na daulolin Tang da Song sun ƙarfafa muhimmancin zubi da tsarin hawa da sauka na murya
a cikin waƙa, domin inganta martabar waƙa. A wasu ɗiyan waƙa, Mengyang yana cewa:
Idan kana son zama
bahari,
to ka naƙalci ƙa’idojin zubi da
tsarin waƙa,
Idan kuma kana son
dacewa,
to ka bibiyi dokokin
hawa da sauka,
na murya a waƙa.
(Li
Mengyang, 2020).
A daulolin Ming da Qing kuwa an ƙarfafa muhimmancin ra’in zubi da tsari da murya ne, a
matsayin wata hanya ta bibiyar tafarkin Confucius. Ta haka ne suke bayyanar da
hikima da zalaƙarsu cikin waƙa. Ga misali, waƙoƙin Jiang Kuis suna ɗamfare ne ga jigon
nagarta. Sai dai kuma duk da cewa a wasu lokuta ana danganta su da kaɗaici da baƙin ciki, to amma kuma
ingancinsu ya kai mizanin dacewa (Chen
Tingzhuo, 2020). Daga baya ma an yi
amfani da kalmar domin bayyana wasu nau’o’i na adabi.
Ta fuskar yabo da
zambo a cikin tarƙen waƙa (meici) kuwa, ana amfani da waɗannan kalmomin fannun adabi a cikin waƙa domin a yi yabo ko
zambo dangane da halayen sarakuna. Waɗannan halaye sun haɗa da nagarta da
tsarin shugabanci da dokoki da kuma himma da ƙwazo a wajen
jagorancin al’umma. Hususan dai, ana amfani da waƙoƙi wajen yabon
sarakuna da kuma kwarzanta ayyukansu nagari, domin su ci gaba da irin waɗannan ayyuka. Ana
kuma yi wa sarakuna zambo domin su gyara kura-kuran da suka aikata (Zheng Xuan, 2020). Confucius shi ne mutum na farko da ya fara faɗakarwa cewa, za a iya
amfani da waƙa domin gyaran hali, kamar dai yadda ya bijiro da
muhimman ayyukan waƙa a cikin littafin Diwanin
Waƙoƙin Sinawa. A wajen mabiya Confucius na daular Han, muhimman ayyukan waƙa guda biyu su ne
yabo da zambo (Cheng Tingzhuo, 2020). Ga misali, a daular Han an yi amfani da waƙa ne a wajen yabo da
kwarzanta ayyukan sarakuna. A cikin gabatarwar littafin Diwanin Waƙoƙin Sinawa da Mao ya yi, an rubuta ayyuka guda biyu a
kan ra’in waƙa, da aka yi amfani da su a daular Han wajen yabo da zambo. Daga baya kuma mawaƙa da marubuta sun yi
ta amfani da wannan salon a matsayin wata dabara ta shiga harkokin siyasa da
kuma tasiri a rayuwar al’umma. Wannan al’amari yana daga cikin muhimman ƙumshiyar ayyukan
adabin al’ummar Sinawa.
A bisa doron waɗannan ma’aunai ne
Sinawa suka yi ittifaƙi, dangane da matsayin waƙoƙi gama-gari da na
bukukuwa da kuma na bauta (fengyasong).
A ikin mashahurin littafin na Diwanin Waƙoƙin Sinawa, an karkasa
ƙumshiyarsa
zuwa manyan rukunai guda uku. Kashi na farko ya ta’allaƙa ne ga waƙoƙI gama-gari (feng), kashi na biyu ya karkata ga waƙoƙin bukukuwa (ya), wato manya (daya) da kuma ƙanana (xiaoya). Kashi na uku kuwa ya danganci waƙoƙI ne na bauta da
ibada (song), waɗanda ake ta kwarara
yabo ga ayyukan da iyaye da kakanni suka aiwatar a zamuna da suka gabata. Bugu
da ƙari
waƙoƙin bukukuwa da na
bauta, su ne suke ɗauke da babban jigo,
a yayin da waƙoƙi gama-gari suke ɗauke da ƙaramin jigo. Saboda
haka waɗannan kashe-kashe na
Diwanin Waƙoƙin Sinawa, baya ga bayanin salo da hawa da sauka na
murya, to an kuma karkasa jogon waƙoƙin zuwa manya da ƙanana. Daga baya kuma
sai aka faɗaɗa ma’anar fengya ta ƙumshe duk wani abu
mai kyau da ƙayatarwa. A taƙaice littafin yana ɗauke da muhimman
batutuwa ne guda shida, wato waƙoƙi gama-gari da na
bukukuwa da bauta da labari da sharhi da kuma dangantaka.
Manyan jigogi na
littafin, wato na labari da sharhi da kuma dangantaka su ne ƙashin bayan waƙa. Wato idan babu waɗannan batutuwa, to ba
za a kira ta da waƙa ba. Idan babu labari a cikin waƙa, to dole a yi
amfani da sharhi. Idan kuma babu sharhi to dole a yi amfani da dangantaka. Waƙoƙi gama-gari da na
bukukuwa da kuma na bauta, duk suna ƙulla zaren jigo ne a
waƙoƙi. Saboda haka, tun
da waƙoƙin suna ƙumshe da labari da sharhi da kuma
dangantaka a matsayin jigo, to shi ya sa ake kiran waƙoƙi gama-gari da na
bukukuwa da kuma na bauta a matsayin ‘yan rakiya (Zhu xi, 2020).
Ƙa’idojin
Rubutun Zube da Waƙa
Tanƙwaruwa a aikin adabi
yana nufin mutum ya girmama ƙa’idojin rubutun zube da waƙa ba tare da ɗamfarewa a gare su
ba. Wato ana so a riƙa ƙarfafa samun canji da ƙirƙira. Kishiyar tanƙwaruwa a aikin adabi
ita ce tsaurarawa a aikin adabi, wato yanayin da marubuci yakan kwaikwayi zubi
da tsari irin na tsohon alƙawari ba tare da ƙirƙira ba. Ɗaya daga cikin
hanyoyin samun tanƙwaruwa a aikin adabi ita ce ta samun izna da ƙarfin gwiwa daga
ayyukan magabata, da kuma tsotsa daga hikimarsu ba tare da ɗamfarewa ba. Wato
mutum ya kasance ya dogara ga kansa cikin ƙirƙira sababbin salailai
da dabaru na sarrafa harshe. Masana tarƙen adabi na daular Song sun tasirantu da ayyukan Chan na amfani da matsakaiciyar tanƙwaruwa, kuma daga
bisani suka ɗauke shi a matsayin
wani mizani na auna rubutun waƙa da na zube.
Waɗanda suke bukatar su
koyi yadda ake rubutun waƙa, to yakamata su naƙalci yadda ake tanƙwaruwa a aikin adabi.
Wato baya ga sanin dukkan ƙa’idojin waƙa, to kuma mawaƙi ya zurfafa wajen
samar da canje-canje a waƙoƙinsa ba tare da watsi da dokokin ba. Ƙa’idar wannan hanya
ta rubutu ita ce samuwar dokoki a matsayin jagora kawai, ba tare da ɗamfarewa ba. A yanayin
kuma da babu dokoki, to a samar da dokokin, Haka kuma mawaƙi yana iya tattauna
lamarin tanƙwaruwarsa a ayyukan adabi tare da sauran mutane, matuƙar dai sun fahimci
yadda tsarin yake (Lu Benzhong, 2020). Ta ɗaya haujin kuma, a
yayin rubutun zube akwai bukatar a tabbatar da lamarin tanƙwaruwar adabi. Idan
mutum ya ɗamfare ga tsohon alƙawari, to ba ƙirƙira sababbin ayyuka
ba, kuma wannan yanayi shi ake kira da tsaurarawa a ayyukan adabi. Wato tsaurin
yana nan tattare da kwaikwayon ayyukan waɗansu ba tare da kawo sabuwar hikima ba. A tanƙwaruwar aikin adabi
kuwa, marubuci yana da dama ta cin gashin kansa wajen ƙirƙira ba tare da ɗamfarewa ga na waɗansu ba. Gaskiyar
maganar ita ce, tsauraruwa tana kawo tawaya a ayyukan adabi (Yu Cheng,
2020).
Tambayar a nan ita
ce, idan tanƙwaruwa tana kawo tawaya a ayyukan adabi, to ina matsayin
fasaha a cikin manufofin waƙa (biecai-biequ)? Kamata ya
yi kowace waƙa ta kasance tana da manufa ta daban ƙunshe a cikin fasahar
mawaƙi. A arewacin daular Song,
Huang Tingjian ya ƙarfafa mawaƙa na makarantar Jiangxi da su ɗauki waƙa a matsayin wata
kafa ta bayyana ra’ayi dangane da al’amuran da suka shafi rayuwar al’umma. Ta
haka suna inganta amfani da salon harshen ƙarfafawa wanda ya keɓanta ga waƙa. A cikin littafinsa
na tarƙe a nazarin waƙa mai suna Canglang’s Criticism of Poetry, Yan Yu (2020) na kudancin daular Song
ya bayyana ɓacin ransa a bisa
aukuwar irin wannan al’amari. Ya jaddada cewa waƙa tana da manufa ta
daban da ta bambanta da abin da za a koya a littafi. Haka kuma tana ƙunshe da fasaha ta
musamman, don haka ba batu ne na ra’o’i ba.
A ra’ayinsa waƙa tana da maudu’i da
manufa, saboda haka ya kamata waƙa ta bayyana abin da
yake zuciyar mawaƙi, a maimakon tanadin littattafai cike da ra’o’i
daban-daban. Yakamata a isar da jigon waƙa ta irin wannan siga
Yaɗa manufar fasaha a
cikin manufofin waƙa da Yan Yu ya yi, izna ce daga kudancin daular Song cewa masu tarƙen ayyukan adabi sun
amince da salon yadda ake bayyana al’amura a waƙa. Wannan ne dalilin
da ya sa kuma suka yi kira da a koma ga amfani da salon da aka ƙirƙira a cikin rubutun
waƙa
na daular Tang. A muƙaddimar littafin Preface to A Collection of Zhuxi’s
Poems, Liu Kezhuang ya bayyana
cewa, a tsawon shekaru ɗari uku na daular Song, mutane da yawa sun wallafa ayyuka
na adabi, kuma da yawa daga ciki waƙoƙi ne da suke ƙunshe da manufofi
daban-daban. A irn waɗannan waƙoƙi, wasu maubutan sun
bayyana ra’ayoyinsu, a yayin da wasu kuma suka yi ta rarraba muhawarar da suka
gabatar a ilimance. Wasu sun wallafa waƙoƙi guda dubu, wasu
kuma dubu goma. Sai dai mafi yawansu sharhi ne kawai na ayyukan Confucius a
cikin sababbin manufohi. Gaskiyar maganar dai ita ce, ba waƙoƙi ba ne.
Ta ɗaya haujin kuma akwai
batun amfani da adon harshe a zube da waƙa (yinxiu). Adon harshe (ko kuma adon
magana), tarin kalmomi ne biyu ko iye da haka da ke da ma’ana wadda ta bambanta
da ma’anonin su kalmomin, domin samar da sahihiyar magana (Dikko da Macciɗo, 1991). Ke nan adon
harshe (ko adon magana) wata dabara ce ta yiwa magana kwalliya, domin nuna ƙwarewa da balagar
harshe domin isar da wata manufa ta wata siga da za ta wasa ƙwaƙwalwar maisauraro. A
ra’ayin Guenthener (1975) a cikin aikin Yakasai (2020), nazarin adon harshe (ko
adon magana) yana da tasiri wajen samar da cikakkiyar ma’ana a harshe. Wannan
magana ta hikima tana nufin cewa, muhimman sassan nan na zube da waƙa suna iya kasancewa ɗauke da adon harshe,
a ƙoƙarinsu na bayanin
abin da yake kyakkyawa.
A adabin Sinawa, da
farko dai wannan magana ta hikimar amfani da adon harshe a zube da waƙa, ta fara bayyana ne
a cikin babin wani littafi mai suna The
Literary Mind and the Carving of Dragons. A cikin wannan babi, ma’anar
wannan magana ta hikima tana ɗamfare da yadda za a siffanta wani wuri ko al’amari a
zuciyar mai karatu. Haka kuma adon harshe na bayyana tsabar kyau kamar yadda
aka bayyana a cikin matanin da ya fito da tushen ma’ana. Waɗannan halaye dai a
kodayaushe tare suke ba sa rabuwa, musamman a cikin ayyukan samar da adabi
nagari. Idan da so samu ne, to kamata ya yi kyakkyawan matani ya kasance yana ƙunshe da salailai na
sarrafa harshe a tsakanin jumlolinsa.
Wato matanin da aka
rubuta ya kasance mai ƙayatarwa, a ƙoƙarin bayyana jigon da
yake ɗauke da shi (Liu Xie, 2020). A wani aiki mai taken Notes on Poetry Written in the Pine and Cypress Studio, Zhang Jie (2020) yana da ra’ayin ana samun
tsaiko a lokacin da tunani da abin da zuciya take so suka ɓuya a tsakanin
jumlolin matani na ayyukan adabi. Wato tabbataccen kyau da ƙaye na bayyana ne a
lokacin da marubuci ya yi amfani da adon harshen da yake wakiltar abin da yake
cikin zuciyarsa. Duk da kasancewar irin wannan yanayi, ana kuma samun haɗakar waƙoƙi da rubutun zube (zongji). Kalmar zongji tana nufin haɗakar waƙoƙi da rbutun zube na
matubu daban-daban a wuri guda. Ita asalin wannan kalma ta bambanta da kalmar bieji wadda take nufin haɗakar ayyukan adabi na
mutum guda. Daga cikin irin ayyukan dauri masu nasaba da wannan tsari, wanda
kuma akan samu a yanzu ba shi ne na Verses
from the Odes of Chu, wanda Wang Yi (2020) na daular Han ya tattara kuma ya tace a matsayin edita.
Dangane da ƙunshiyar irin wannan aiki kuwa, masana suna ganin yana
iya kasancewa mai yawa ko kuma kaɗan. Hasali ma, kamata ya yi kowane aiki irin
wannan ya kasance na tarihi a rubuce ko kuma haɗakar abubuwan da suka faru daga wata
daula.
A cikin haɗakar irin wannan aiki
kuma ana ya kasa shit a fannoni daban-daban. Saboda haka aikin day a wakilci
irin wannan tsari shi ne Selected Literary Works, wanda gamayyar Yarima
Xiao Tong (2020) da kuma mashawartansa na daular Liang da ke kudanci suka tattara kuma suka wallafa. Ƙunshiyar aikin ayyuka
ne guda 700 da suka taɓo sassa daban-daban
na adabi tun kafin daular Qin zuwa
zamanin daular Liang. A wannan aiki
babu gudummawar jing (ayyukan
Confucius) da na shi (tarihi) ko
kuma zi (tunanin masanan dauri),
face ‘yan tarihe-tarihe da aka taɓo a gabatarwar aikin. Aikin dai ya wakilci
abubuwan da suke aukuwa a wannan zamani, kuma yana da tasiri a kan adabin
Sinawa a shekaru masu zuwa.
Galibi ana tattara
irin waɗannan ayyuka na adabi
(wato ci) da kuma na ƙirƙira (wato fu), da kuma ayyuka daban-daban da
marubuta suka wallafa. Akan tattara su wuri guda da sunan Litrary Trends and Schools daga Zhi Yu na daular Jin (The History of the Sui Dynasty). An samo tsarin irin waɗannan ayyuka ne daga cikin littattafan The Book of History da kuma na The book of Songs.
Daga nan ne kuma aka samar da wasu ayyuka da suka haɗa da Verses from the Oden of Chu da Literary Trends and Schools. Dukkansu dai Wang
Yi da Zhai Yu (2020) ne suka
tattara sannan suka wallafa su, a yayin da kuma suka biyo baya cikin manufofi
da zubi da tsari da kuma harshe gaba ɗaya. Daga bayanan da suka gabata, a fili take
cewa waƙa tana da matsayi daban-daban. Wato ana amfani da waƙa domin bayyana
halaye da yanaye-yanaye da suke bijirowa a zamantakewar al’umma.
Waƙa a Matsayin Saƙon Zuci
Asalin waƙoƙi suna bijirowa ne
daga zuciyar mawaƙi. Lu Jin na yammacin Daular Jin yana cewa: “A
fasahar rubutu, wajibi ne mawaƙi ya ji ɗarsuwar abin da yake so a zuciyarsa
kafin ya iya ƙirƙira waƙa. Wannan ra’ayi yana da nasaba da na
“kishin zuci a cikin waƙa”, kuma ya jaddada muhimmancin ayyukan adabi da bunɗasarsu a zamanin
daulolin Wei da Jin. Waɗa a matsyin saƙon zuciya, na
wakiltar wani ra’ayi a kan tsarin waƙa da adabi a ƙasar Sin ta dauri. A
ra’ayin Lu Ji (2020), kasancewarta wata kafa ta sadarwa, waƙa a matsayin saƙon zuciya tana waƙeda daɗin karantawa. Da
wannan ne kuma Liu Xie (2020) yake cewa kowane ɗan’Adam yana da
abubuwa da suke ɗarsuuwa a zuciyarsa,
kuma yana bayyanawa a waƙe a lokacin day a samu tasirin rayuwa ta yau da kullum,
kuma zuciyarsa ta ɗarsu da lamarin.
Dukkan waƙoƙi suna bijirowa ne daga yanayi da halayen da zuciya ta
sami kanta a ciki.
Idan muka ɗauki kishin zuci a
cikin waƙa (wato shi yan zhi), waƙa kafa ce ta bayyana abin da yake ƙumshe a cikin zuciya.
A nan zhi tana nufin kishin zuci da
tunanin marubuci. Batun kishin zuci a cikin waƙa, lamari ne daya
fara bayyana a littafin Confucius mai suna The
Book of History, wanda Zhu Ziqing ya yaɗa a matsayin manufar
waƙoƙin al’ummar Sinawa.
Sannu a hankali kuma, da taimakon ayyukan manazarta tarƙen waƙoƙi, sai aka ɗauki kalmar a
matsayin kalmar fannu a cikin ayyukan tarƙen adabin Sinawa.
Saboda haka, waƙoƙi suna bayyana kishin zuci daga zuciyar marubuci, a yayin
da su kuma kiɗa da waƙa ake rerawa. Hususan
dai waƙoƙi suna bijirowa ne a sanadiyar kishin zuci. Kishin zucin
da aka ji sunansa kishin zuci, amma kuma a yayin da aka bayyana kishin zuci a
rubuce cikin kalmomi, to ya zamo waƙa.
Daga abin da ya
gabata, bari mu ɗauki misalan wasu waƙoƙi a matsayin zakaran
gwajin-dafi, da suka haɗa da na ‘Rayuwar kaɗaici’ da ‘Waƙoƙin baƙin ciki’ da kuma ‘Waƙar tarihin al’umma’.
Rayuwar kaɗaici (beikai) maganar azanci ce da ke bayyana
damuwa da ake samu a cikin waƙa. Irin wannan yanayi yana ɗaya daga cikin salailai na waƙa guda ashirin da huɗu (24), da mawaƙin nan na ƙarshen daular Tang,
wato Silkong Tu ya kawo a taƙaice, Yanayi ne na damuwa cikin ƙalubalen rayuwa ko kuma ƙololuwar ɗokantuwa da wani lamari da ya auku. A lokacin da mawaƙa suka sami kansu a
cikin damuwa da baƙin ciki da fushi da kuma ɓacin rai, to sai ɗuncin yanayi ya jefa su cikin rayuwar kaɗaici da suke bayyanawa a salon rubutacciyar waƙa. Duk da cewa salon
yana yin kama da na salon ƙaddara a al’adar nazarin adabi a ƙasar Hausa, amma kuma ya fi
tasirantuwa da kaɗaici.
Dangane da waƙoƙin baƙin ciki (chenyu) kuwa, wani irin salo ne a ayyukan waƙa,
a inda ake bayyana ra’ayi a cikin hikima. Mawaƙan Sinawa na dauri waɗanda Du Fu
ya wakilta, sun fi damuwa da halin dad a al’ummarsu take ciki a kodayaushe.
Saboda haka sukan yi ƙoƙarin fahimtar dalilan da suke kawo bunƙasa da kuma faɗuwar ƙasa, sannan kuma su
tanadi shawarwarin da za su ceto ƙasa da al’amuranta
daa cikin mawuyacin halin da ta samu kanta. A yayin da irin wannan ƙoƙari nasu ya gaza
cimma burnsu, to sai sukan bayyana irin baƙin cikin da suka
shiga a waƙe. Ta hanyar amfani da zubi da tsari da kuma hawa da
sauka na murya, ayyukansu sukan samu kar`uwa ta musamman a wajen al’umma cikin
yabo da alfahari da gudummarsu wajen kishin gina ƙasarsu. A yayin da
marubuci ya kasance cikin tunani mai zurfi dangane da jigon abin da zai yi
rubutu a kansa, to da zarar ya kamala aikin nasa sai ra’ayinsa ya bayyana a
fili (Chen Tingzhu, 2020).
Idan uka juya ga waƙar tarihin al’umma (shishi) kuwa, wannan kalma tana nufin
waƙar
da jigo ko ƙumshiyata ya tattare tsarin zamantakewar al’umma da kuma
muhimman al’amuran tarihi da suka gabata. Wasu daga cikin waƙoƙin da ke cikin
littafin The Book of Songs sun shafi gaskiyar al’amuran
rayuwa na wancan ne, wanda har Confucius ya yi iƙirarin cewa littafin
jagoran fahimtar al’umma ne. Wannan yana nufin cewa ya nazarci littafin a
matsayin wanda aka yi amfani da waƙa wajen adana tarihi.
Haka kuma masana na daular Han sun jaddada muhimmancin waƙa a matsayin kafa ta
adana tarihin al’umma. Daga bisani kuma, masana ilimin nazarin waƙa na ƙasar Sin sun yi imani
da cewa yakamata waƙa ta ƙumshe zahirin rayuwa, da bayar da
nishaɗi da kuma ilimi.
Ga misali, waƙoƙin Tang Du Fu ana kiransu da waƙoƙin tarihin rayuwar
al’umma, domin suna ƙumshe da irin gwagwarmayar da ƙasar ta sha a lokacin
boren An Lushan-Shi, da kuma ɓacin ran yadda aka
bayyana halin da ƙasar ta shiga.amarin ya kuma haɗa da yadda al’ummar
suka yi fama da matsananciyar wahala, wata annoba a ƙasar. Du Fu ya yi
hijira zuwa lardin Gansu da Sichuan domin gujewa matsalolin da
boren An Lushan-Shi Siming ya haifar, sannan ya bayyana
abubuwan da suka faru das hi a cikin waƙoƙi.Da yake waƙoƙinsa sun bayar da
asalin hoton abubuwan da suku a lokacin, to sun zamo waƙoƙin tarihin al’umma.
Su kuma al’umma sun ɗauki waƙoƙin Du Fu
a matsayin waƙoƙin tarihi, musamman saboda sun bayyana gaskiyar abubuwan
da suka faru a zamaninsa, sannan kuma cike suke da yabo da kuma zambo na
al’amuran tarihi. Saboda haka kai tsaye ake kiran waƙoƙinsa da waƙoƙin tarihin al’umma (Wen Tianxiang, 2020).
Naɗewa
Abin da ya gabata a
cikin wannan maƙala tsokaci ne dangane da matsayin waƙa a adabin Sinawa. Da
farko mun yi waiwaye (wanda masu hikimar magana suke cewa adon tafiya ne)
dangane da inda ƙasar Sin take da kuma yadda al’adar zamantakewarsu ta ke.
Daga nan kuma sai bayani a kan ko mece ce waƙa da kuma sauran
muhimman batutuwa da suke ɗamfare ita. Waɗannan batutuwa sun haɗa da karin waƙa da zubi da tsari da
yabo da zambo da kuma matsayin waƙoƙi gama-gari. An kuma
kawo ƙa’idojin rubutun zube da waƙa a doron adabin
Sinawa. Ƙa’idojin sun shafi amfani da adon harshen waƙa, da kuma fasaha a
cikin manufofin waƙa. Daga nan kuma an kawo misalan waɗa a matsayin saƙon zuci da kishin
zuci a cikin waƙa da rayuwar kaɗaici da waƙoƙin baƙin-ciki da kuma waƙar tarihin al’umma.
Wani tuntuɓe daɗin gushi, waɗa a adabin Sinawa
tana kuma da wata dangantaka ta musamman da wasu al’amura na rayuwar al’umma
kamar zane (shi zhong you) da wasan
kwaikwayo (danghang). Wannan maganar
hikima tana bayyana irin dangantakar da take tsakanin zane da kuma waƙa ne, a matsayinsu na
kafafen da suke ƙirƙira al’amura a cikin ingantacciyar siga. Su Shi
ne mutum na farko da ya fara gabatar da wannan maganar hikima a cikin
littafinsa mai suna Notes to Wang
Wei’s Painting of Mist and Rain over Languan. Zane yana bayyanar da al’amura ta hanyar amfani da
kalmomi. Wato shi zane fasaha ce da ba ta ɗauke da saututtuka, a yayin da ita kuma waƙa take fasahar da ke
da saututtuka amma ba tare da zane ba. A taƙaice, haɗakar waɗannan abubuwa na
hikima guda biyu za ta samar da ingantaccen sakamako. Wannan ra’ayi na Su Shi
ya yi tasiri a kan ci gaba da kuma bunƙasar ayyukan adabi da
kuma na zane a ƙasar Sin. Ta ɗaya haujin kuma an fara amfani da kalmr danghang a cikin nazarin tarƙen waƙa, domin a bayyana
dacewa da kuma cancantar waƙa (wato a lokacin da waɗa ta cika wasu sharuɗɗa da aka tanada a
matsayin ma’aunin nagarta). Daga bisani kuma sai kalmar ta zamo ta fannu a
cikin ra’in ayyukan adabin Sinawa
Manazarta
BFLTRP (2020) Key
Concepts in Chinese Thought and Culture, Beijing: Foreign Language Press.
Chen, T (2020)
“Remarks on Lyrics from White Rain Studio” In Key Conepts in Chinese Thought
and Culture, Beijing: Foreign Language Press.
Dikko, I. & U. Macciɗo (1991) Ƙamus na Adon Maganar
Hausa, Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.
Liu, X. (2020) “The
Literary Mind and the Carving of the Dragons” In Key Concepts in Chinese
Thought and Culture, Beijing: Foreign Language Press.
Lu, J. (2020) “The
Art of Writng” In Key Concepts in Chinese Thought and Culture, Beijing: Foreign
Language Press.
Qi, M. (2020) “The
Story of Poetry” In Key Cocepts in Chinese Thought and Culture, Beijing:
Foreign Language Press.
Tianxiang, W. (2020)
“Preface to the Selected Poems of Du Fu” In Key Concepts in Chinese Thought and
Culture, Beijing: Foreign Language Press.
Tong, Y. X. (2020)
“Selected Literary Works” In Key Concepts in Chinese Thought and Culture,
Beijing: Foreign Language Press.
Wang, Y. (2020)
”Verses from the Odes of Chu” In Key Concepts in Chnese Thought and Culture,
Bejing: Foreign Language Press.
Yakasai, S. A. (2020)
Sanin Makamar Fassara, Kaduna: AMAL Pronting Press.
Yakasai, S.A. (2022)
Rayuwa da Falsafa Cikin Tunanin Al’ummar Sinawa, Kano: Gidan Dabino Publishers.
Zhang, J. (2020)
“Notes on Poetry Written in the Pine and Cypress Studio” In Key Concepts in
Chinese Thought and Culture, Beijing: Foreign Language Press.
Zheng, J. (2020) “Preface to On the Categories of the
Book of Song” In Key Concepts in Chinese Thought and Culture, Beijing: Foreign
Language Press.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.