A baya mun kawo wa mai karatu wurare daban - daban da aka hakaito Ijma'in Malaman Mazhabar Salaf Ahlus Sunna a kan haramcin tawaye wa azzalumin shugaba fasiki. Mun kawo hatta daga "al-A'immatul Arba'a", Imamu Abu Hanifa, Imamu Malik, da Imamu Ahmad, Mazhabarsu ita ce Haramcin tawaye wa shugaba fasiki azzalumi, saboda Hadisai masu yawa a kan haka, da kuma saboda sharri mai girma da tawayen yake haifarwa. Sai wannan mas'ala ta zama cikin ginshikan Akidar Ahlus Sunna, sai sabani a kanta ya koma sabani tsakanin Ahlus Sunna da 'yan bidi'a; Khawarijawa, Mu'utazila da Shi'a da makamantansu, wanda idan mutum ya saba, ya fito ya dauki makami, ya yi tawaye wa shugaba fasiki, to ya fita daga da'irar Sunna, za a jefa shi cikin 'yan bidi'a.
Daga cikin Malaman da suka hakaito Ijma'in Malaman
Salaf a kan haka akwai Imamul Bukhari, da Abu Hatim al-Raziy da Abu Zur'ah
al-Raziy.
Imamul Bukhari ya ce
"لقيت أكثر من ألف رجل من أهل العلم، أهل الحجاز ومكة والمدينة
والكوفة والبصرة، وواسط وبغداد والشام ومصر، لقيتهم كرات قرنا بعد قرن، ثم قرنا بعد
قرن، أدركتهم وهم متوافرون منذ أكثر من ست وأربعين سنة، أهل الشام ومصر والجزيرة مرتين،
والبصرة أربع مرات في سنين ذوي عدد، بالحجاز ستة أعوام، ولا أحصي كم دخلت الكوفة وبغداد
مع محدثي أهل خراسان، منهم...".
“Na hadu da Malamai fiye da mutum dubu (1000), mutanen Hijaz; Makka da
Madina, da Kufa, da Basra, da Wasid, da Bagdaza, da Sham da Misra, na hadu da
su ba sau daya ba, zamani bayan zamani, na hadu da su suna cike makil, tun fiye
da shekara 46. Malaman Sham da Misra da Jazira sau biyu, Malaman Basra sau
hudu, a adadin shekaru, a Hijaz kuma shekara shida, ba zan iya kirga sau nawa
na shiga Kufa da Bagdaza tare da Malaman Hadisin Khurasan ba. Daga cikinsu….”.
Sai ya ambaci sunayen Malaman kowane gari…
A Madina sai ya ce
وبالمدينة: إسماعيل بن أبي أويس، ومطرف بن عبد الله، وعبد الله
بن نافع الزبيري، وأحمد بن أبي بكر أبا مصعب الزهري، وإبراهيم بن حمزة الزبيري، وإبراهيم
بن المنذر الحزامي
Idan ka duba za ka ga duka wadannan almajiran
Imamu Malik ne.
A Bagdaza kuma ya ce
وببغداد: أحمد بن حنبل، ويحيى بن معين، وأبا معمر، وأبا خيثمة،
وأبا عبيد القاسم بن سلام
Sai da ya ambaci Malaman Hadisi a biranen Muslunci
daban daban sai ya ce
"واكتفينا بتسمية هؤلاء كي يكون مختصرا وأن لا يطول ذلك , فما
رأيت واحدا منهم يختلف في هذه الأشياء:...".
“Za mu wadata da ambaton sunayen wadannan, don ya zama a takaice, kar ya yi
tsawo. Ban ga wani daga cikinsu da ya saba a wadannan abubuwa ba…:”.
Sai ya ambaci ginshikan Akidar Ahlus Sunna “Usul”,
a ciki ya ce
"وأن لا ننازع الأمر أهله...، وأن لا يرى السيف على أمة محمد
صلى الله عليه وسلم...".
شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (1/ 194
- 197)
Haka Ibnu Abi Hatim ya ruwaito daga Babansa da Abu
Zur’a ya ce
"سألت أبي وأبا زرعة عن مذاهب أهل السنة في أصول الدين، وما أدركا
عليه العلماء في جميع الأمصار، وما يعتقدان من ذلك، فقالا
"أدركنا العلماء في جميع الأمصار، حجازا وعراقا وشاما ويمنا،
فكان من مذهبهم:...
ولا نرى الخروج على الأئمة ولا القتال في الفتنة، ونسمع ونطيع
لمن ولاه الله عز وجل أمرنا، ولا ننزع يدا من طاعة، ونتبع السنة والجماعة، ونجتنب الشذوذ
والخلاف والفرقة".
شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (1/ 198
- 199)
“Na tambayi Babana da Abu Zur’a game da Mazhabobin Ahlus Sunna a Ginshikan
Addini, da abin da suka riski Malamai a kansa a dukkan Birane, da abin da suke
kudurcewa na Ginshikan Addini. Sai suka ce
“Mun riski Malamai a dukkan Birane, Hijaz, Iraq, Sham da Yaman, ya kasance
daga cikin Mazhabarsu akwai:…
Ba ma ganin yin tawaye wa shugabanni, da yaki a
cikin fitina. Kuma muna saurara wa duk wanda Allah ya ba shi mulkinmu, muna yi
masa da’a, ba ma cire hanu daga yi masa biyayya. Muna bin Sunna da Jama’a, muna
nisantar warewa da sabani da rabuwa”.
Wannan shi ne Ijma'i da aka yi a zamanin wadannan
A'imma. Ga shi sun ambato Malaman da suka yi Ijma'in har da sunayensu.
Wannan shi ne Ijma'in da Abul Hassan al-Ash'ariy
ya hakaito, ya nassanta Ijma'i a kansa, inda ya ce
"وأجمعوا على السمع والطاعة لأئمة المسلمين، وعلى أن كل من ولي
شيئا من أمورهم عن رضى أو غلبة، وامتدت طاعته، من بر وفاجر لا يلزم الخروج عليهم بالسيف،
جار أو عدل".
رسالة إلى أهل الثغر للأشعري (ص: ٢٩٦ - ٢٩٧)
"Ahlus Sunna sun yi Ijma'i a kan saurara wa
shugabannin Musulmai da yi musu da'a. Kuma dukkan wanda ya shugabanci Musulmai
bisa yardarsu ko da karfi, kuma aka zarce, ana yi masa da'a, mutumin kirki ne
ko fajiri, ba za a yi masa tawaye da makami ba, ya yi zalunci ko ya yi
adalci".
Babbar shubuhar masu jayayya a wannar mas'ala ita
ce: suna sukar wannan Ijma'i da cewa: -wai- ai an samu wasu cikin Sahabbai da
Tabi'ai sun saba a wannar mas'ala, don haka Ijma'in bai tabbata ba.
Jawabi a kan wannar shubuha shi ne: Aikin wadancan
ba zai taba zama abin suka ga wannan Ijma'i ba, saboda abubuwa guda biyu
1- Tawayen wadannan magabata aiki ne wanda an yi
musu inkarinsa, don haka bai halasta a yi koyi da shi ba, har ya zama kaulin da
zai zama Mazhaba abin koyi.
Ibnu Qudama ya ce
"وإذا اختلف الصحابة على قولين لم يجز للمجتهد الأخذ بقول بعضهم
من غير دليل، خلافا لبعض الحنفية وبعض المتكلمين: أنه يجوز ذلك، ما لم ينكر على القائل
قوله".
روضة الناظر وجنة المناظر (1/ 470 - 471)
Sai wannan ya nuna cewa; wadanda aka yi musu
inkari cikin masu sabani ra’ayinsu ba zai zama abin lura ba.
2- Ko da an sallama ya zama zance abin lura, to
gaskiyar zance shi ne; Ijma'i a bayan sabani yana goge sabanin, kamar yadda ya
tabbata a Ilimin "Usulul Fiqh".
Abul Waleed al-Bajiy ya ce
"إذا اختلفت الصحابة - رضي الله عنهم - على قولين، وأجمع التابعون
على أحدهما فإن ذلك يكون إجماعا، تثبت به الحجة".
إحكام الفصول (١/ ٤٩٨)
Tajuddeen al-Subkiy yana daga cikin wadanda suka
hakaito hakan daga Jumhurin Malaman "Usul" inda ya ce
"المسألة الثانية: إذا اختلفوا على قولين ومضوا على ذلك، فهل
يتصور انعقاد إجماع العصر الثاني بعدهم على أحدهما، حتى يمتنع المصير إلى القول الآخر؟
ذهب الشيخ أبو الحسن الأشعري، وأحمد بن حنبل، والصيرفي، وإمام
الحرمين والغزالي إلى امتناعه، واختاره الآمدي.
وذهب الجمهور إلى الجواز، وتبعهم ابن الحاجب".
الإبهاج في شرح المنهاج ط دبي (5/ 2093)
A nan sai al-Subkiy ya bayyana cewa; Jumhurin
Malaman “Usulul Fiqh” sun tabbatar da cewa; idan aka samu an yi sabani a kan
mas’ala, sai kuma daga baya aka yi Ijma’i, to Ijma’in nan ya kullu, ya zama
hujja, bai halasta wani ya saba masa ba, duk wanda ya saba za a yi masa
hukuncin wanda ya saba Ijma’i.
Don haka bayan wannan Ijma'i babu wanda ya isa ya
zo ya ce akwai sabani a kan mas'alar, sai dai wanda bai san da Ijma'in ba, ko
mai son zuciya, mai bin ra'ayoyin 'yan bidi'a.
A baya mun kawo misali a kan Ijma'i bayan sabani,
na mas'alar sabanin Malamai Ahlus Sunna a kan fifita tsakanin Sayyidina Usman
(ra) da Sayyidina Aliyu (ra) da gabatar da daya a kan daya, amma daga baya sai
aka yi Ijma'i a kan fifita Sayyidina Usman (ra) a kan Sayyidina Aliyu (ra).
Haka Malamai suna misali da haramcin auren Mut'a,
wanda aka yi sabani a farkon lamari, Ibnu Abbas (ra) ya saba, yake ganin
halascin auren Mutu'a, amma daga baya aka yi Ijma'i a kan Haramci.
Haka suna misali da sayar da bayi mata da suka
haifa wa iyayengijinsu 'ya'ya, da farko akwai sabani, amma daga baya sai aka yi
Ijma'i a kan haramci.
Da sauran misalai da suke kawowa a mas'alar.
Saboda haka babu abin da zai soki Ijma'in da
Malaman Mazhabar Salaf suka yi a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki sai idan
an samu wasu A'imma a wancan zamanin da aka yi Ijma'in sun saba. Amma tun da ba
a samu Imamin da ya saba ba, to ya zama Ijma'i tabbatacce. Don haka duk wanda
ya saba daga baya ya zama mai saba Ijma'i, ya fita daga cikin Ahlus Sunna, ya
hau motar 'yan bidi'a.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.