Wadanda suka saba da Ahlus Sunna a babin Siffofin Allah bangarori biyu ne
(1) Masu
kamanta Allah da halitta, su ake kira da "Mushabbiha" ko
"Mujassima". Kusan a yanzu babu wannar Mazhaba.
(2) Masu kore Siffofin Allah da sunan tsarkake shi daga yin kamannni da halitta, su ake kira da "Mua'ddila" ko "Jahamiyya". Wannan bangare ya tattara dukkan 'yan bidi'a wadanda suke a yau. Su ne Mu'utazila da Asha'ira da Maturidiyya, da Ibadhiyya da kuma Shi'a, duka wadannan 'Yan Jahamiyya ne a babin Siffofin Allah, sun hadu a asalin Bidi'ar Jaham ta kore hakikanin Siffofin Allah.
Wannan bangare na biyu ya gina Akidarsa ne a babin
Siffofin Allah bisa cewa; ba a sanin Allah da komai sai da hankali. Su suka
ayyana wasu abubuwa guda hudu, suka ce: ba a saninsu sai ta hanyar hankali
kadai. Su ne
1. Sanin faruwar Duniya.
2. Sanin samuwar Allah da rashin faruwarsa.
3. Sanin Siffofinsa.
4. Sanin gaskiyar Manzo.
Suka ce: wadannan abubuwa guda hudu su ne abubuwa
na farko da za a fara tabbatarwa a Addini, kuma a sansu ta hanyar nazarin
hankali. Shi ya sa suke cewa: farkon wajibi a kan bawa shi ne Nazari. Wato
Nazari a cikin dalilin faruwar Duniya "دليل الحدوث".
Alhali sanin Allah ba ya bukatar wani nazari,
saboda Allah ya kimtsa ma kowa saninsa a cikin Fidirarsa. Don haka farko kowa
ya san samuwar Allah ne ta hanyar Fidira.
Bayan haka kuma farkon wajibi shi ne: Shaidawa
babu abin bauta da gaskiya sai Allah, da shaidawa Annabi Muhammad Manzon Allah
ne.
Wannan shi ne farkon wajibi. Shi ya sa Kalmar
Shahada ita ce farkon abin da Annabi (saw) ya kira Quraishawa gare ta.
To saboda 'yan Bidi'a sun ce ta hanyar hankali
kadai ake sanin samuwar Allah da Siffofinsa, wannan ya sa suke daukar hankali a
matsayin shi ne hujja mafi girma, don haka hujjar hankali ita ce gaba da
maganar Allah da Manzonsa. Wannan ya sa za ka ga suna ajiye Nassi idan ya saba
wa hankalinsu.
Asali a babin Siffofin Allah 'Yan Bidi'a ba sa
kafa hujja da Aya ko Hadisi, idan ka ga sun yi haka to Ayar ta dace da hujjarsu
ta hankali ne, sai su kafa hujja da ita, don ta kara ma hujjarsu ta hankali
karfi.
Su kuma Ahlus Sunna sai suka ce: a'a, ana sanin
Allah ne ta hanyar Fidira. Kowane mutum Allah ya sanya masa sanin Ubangiji
Mahaliccinsa a cikin Fidirarsa. Kowa a cikin ransa yana jin cewa; dole akwai
Mahaliccin da ya samar da shi, kuma wanda ya cancanci a kaskantar da kai gare
shi, a risina masa. Wannan a dunkule kenan, amma hanyar sanin Siffofin wannan
Mahalicci wanda suka fara saninsa ta hanyar Fidira ita ce: Maganarsa da ya
saukar a Littafinsa da kuma ta harshen Manzonsa, wato Alkur'ani da Hadisi. Saboda
shi Allah gaibi ne, hankali ba zai iya riskan hakikaninsa ba, saboda shi
hankali bai taba ganin Allah ba, kuma Allah ba shi da makamanci balle hankali
ya iya ganin makamancin nasa, sai ya san Allah ta hanyar Makamancin nasa. Don
haka dole ya zama cewa; babu yadda za mu san Allah a fayyace sai ta hanyar abin
da ya sanar da mu a cikin Littafinsa, ta hanun Manzonsa.
Wannan ya sa Ahlus Sunna suke daukar Ilimin Sanin
Allah da Siffofinsa ta hanyar Manzon Allah (saw); a cikin Alkur'ani da Sunna.
Wannan ya sa ake kiransu da sunan "Ahlus Sunna", saboda sun bi abin
da Annabi (saw) ya zo da shi a babukan Addini, musamman manyan Mas'alolin
Addini, wato babin Sanin Allah da Siffofinsa.
To su wadancan 'Yan Bidi'a da suke Sanin Allah da
hankulansu, yaya za su yi da Ayoyi da Hadisai da suka zo suna bayanin Siffofin
Allah karara a fili, Allah yana da fiska, hanaye, ido… d.s?
Sai suka ce: Ai Ayoyi da Hadisan
"Mutashabihai" ne, kuma Allah ya ce: A mayar da ilimin
"Mutashabihai" zuwa ga Allah, Allah ya ce
{هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ
هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ
زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ
وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ
آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو الْأَلْبَابِ}
[آل عمران: 7]
To amma sai dai Ahlus Sunna ba su yarda da wannar
hujja ba, shi ya sa suka yi tambaya suka ce: Ya ku 'Yan Bidi'a, musamman
Asha'ira, wa ya ce muku Ayoyin Siffofin Allah suna cikin
"Mutashabihat"?!
Mu dai mun duba littatafan Tafsirai, amma ba mu ga
wani cikin Salaf ya ce: Ayoyin Siffofin Allah suna cikin
"Mutashabihat" ba!
Ga irin fassarar da Salaf suka yi ga
"Mutashabihat" kamar haka
1) Ayoyin da aka soke su "Mansukhai".
2) Ayoyin da babu wanda ya san hakikaninsu sai
Allah, kamar abin da ya shafi lokacin tashin Kiyama.
3) Su ne harufan da suke farkon surori, "Alif
Laam Meem".
4) Ayoyin da suka yi kama a ma'anoni amma
lafuzansu daban-daban.
5) Ayoyin da lafuzansu suka maimaitu.
6) Ayoyin da suke daukar fiskoki da yawa.
7) Ayoyin da suka yi kama da juna, na kissoshin
al'umomi da suka gabata, wasu sun yi ittifaki a lafazi, amma sun saba a ma'ana,
wasu kuma sun yi ittifaqi a ma'ana, sun saba a lafazi.
Shi ya sa Ibnu al-Jauziy ya ce
((وفي المتشابه سبعة أقوال
أحدها: أنه المنسوخ، قاله ابن مسعود، وابن عباس، وقتادة، والسدي
في آخرين.
والثاني: أنه ما لم يكن للعلماء إلى معرفته سبيل، كقيام الساعة،
روي عن جابر بن عبد الله.
والثالث: أنه الحروف المقطعة كقوله: «ألم» ونحو ذلك، قاله ابن
عباس.
والرابع: أنه ما اشتبهت معانيه، قاله مجاهد.
والخامس: أنه ما تكررت ألفاظه، قاله ابن زيد.
والسادس: أنه ما احتاج إلى بيان، ذكره القاضي أبو يعلى عن أحمد.
وقال الشافعي: ما احتمل من التأويل وجوها. وقال ابن الأنباري: المحكم ما لا يحتمل التأويلات،
ولا يخفى على مميز، والمتشابه: الذي تعتوره تأويلات.
والسابع: أنه القصص والأمثال، ذكره القاضي أبو يعلى)).
زاد المسير في علم التفسير (1/ 259)
To a nan ka ga duka wadannan babu kauli daya da
aka ce "Mutashabihat" su ne Ayoyi da Hadisan Siffofin Allah?
Saboda haka, tambayarmu tana nan; Ya ku Asha'ira,
a ina kuka samo fassarar "Mutashabihat" cewa su ne Siffofin Allah?
Daga Sahabbai da Tabi'ai kuka samo, ko daga wasu
na bayansu?
Saboda haka Ahlus Sunna ba su yarda Siffofin Allah
suna cikin "Mutashabihat" ba, sai kun kawo dalili karbabbe.
Dr Aliyu Muh'd Sani (H)
27 August 2022
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.