Wasu Sakonnin Da Aka Tura a Zauren WhatsApp Na Taron Kara Wa Juna Sani Na Kasa-Da-Kasa Game Rayuwa Da Wakokin Makada Sa'idu Faru

    A ranar 29/01/2024 an buɗe zaure a kafar WhatsApp domin tattauna muhimman batutuwa da tura muhimman saƙonni game da wannan taron ƙara wa juna sani na ƙasa-da-ƙasa. Malamai da manazarta da dama sun bayar da gudummawar ilimi sosai a cikin zauren. Daga ƙarshe an ɗauko wasu daga cikin bayanan, an kundace su wuri ɗaya domin ajiye tarihi da yaɗa ilimi.

    [6:48am, 31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Waƙoƙin Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba. Ya yi sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 lokacin da aka cire shi.

    [6:50am, 31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Akwai Waƙoƙin Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo Abubakar III wanda daga baya ya zama Sarkin Musulmi a cikin watan Afrilun 1996.

    [6:54am, 31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Waƙoƙin Marigayi Galadiman Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Hashim tun yana Turakin Kano da Waƙar Ɗan Alin Birnin Magaji, Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Mode Usman wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1945 zuwa rasuwarsa a shekarar 2005 da Waƙar Tudun Falale/Sarkin Tudun Falale, Muhammadu Ɗan Sarkin Mafaran Gummi Muhammadu Maidabo.

    [6:54am, 31/01/2024] Malam Dahiru Abdulkadir: Na ga ƙoƙarin gabatar da aiki mai muhimmanci da aka yi niyya. Allah sa mu dace.

    [7:05am, 31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Waƙar Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello GCON, KBE, Firimiyan Jihar Arewa ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ☝️

    [7:06am, 31/01/2024] Dr Rabiu Ba shir KASU: Allah ya gafarta wa Muhammadu Maccido, ya gafarta wa Saidu Faru.

    Sarkin Kudu ya waƙu gaya, da Allah ya sa Malamin kiɗa na da rai ya zama Sarkin Muslim Lallai kuwa ba mu san me zai gaya wa Sarki ba a waƙe.

    [7:32am, 31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Waƙoƙin Sakataren Di'on Ƙaura Namoda, Hassan Anka da S/Kano Alhaji Ado Bayero da Turakin Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Hashim da Alhaji Bello Koko Di'on Sakkwato da Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu da Ɗanmalikin Gidan Goga, Alhaji Ummaru da Sarkin Yaƙin Banga, Sale Abubakar da Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III da Sarkin Sudan Na Wurno, Alhaji Shehu Malami da Sarkin Bauran Dange, Alhaji Ummaru Faruku da Sarkin Yaƙin Binji, Alhaji Usman Abdulwahab da Kekun Gada, Alhaji Muhammadu Ɗantabawa da Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alhaji Ahmad Muhammad Asha.

    [10:35am, 31/01/2024] Alh. A. Nakawada: Sa'idu Faru is known for creating "traditional Hausa royal music. " Therefore, "traditional Hausa royal music" best describes the type of songs made by Sa'idu Faru instead of "Royal Song"

    Small karambani👏 👆

    [10:36am, 31/01/2024] Alh. A. Nakawada: Additionally, in general terms, a "song" typically refers to a musical composition with lyrics that are sung, while "music" is a broader term that encompasses any organized sound or combination of sounds. Music can include instrumental compositions, whereas a song specifically involves vocals with lyrics.

    [10:42am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: Thank you this submission.

    The LOC are following and monitoring all the chats in this group.

    Your contributions are always welcome.

    [10:49am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: The popular adopted term for the category is Hausa singers and drummers.

    [10:49am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: Singer: Singers typically focus on melody, lyrics, and vocal delivery. They may or may not accompany themselves with instruments.

    Musician: Musicians focus on playing instruments, understanding musical theory, and creating harmonies, melodies, or rhythms. They may or may not sing.

    [10:50am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: Singer: Vocal training is crucial for singers to enhance their vocal range, control, and overall performance. They often learn techniques for breath control, pitch, and expression.

    Musician: Musicians receive training in playing their chosen instruments, learning music theory, and understanding the principles of harmony, rhythm, and composition.

    [10:50am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: Singer: In a band, the singer often takes on the role of the lead vocalist, fronting the performance and delivering the lyrics. However, some singers may also play instruments.

    Musician: Musicians in a band include those playing instruments such as guitarists, bassists, drummers, keyboardists, etc. They contribute to the overall musical arrangement.

    [10:52am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: In the native English sense, while all singers are musicians, not all musicians are singers. Singers primarily use their voices as instruments, whereas musicians encompass a broader category involving individuals who play various musical instruments.

    [10:55am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: In light of the distinctions outlined above, particularly in the context of native English terminology, it is more appropriate to refer to Sa'idu Faru as a singer rather than a musician. This classification is fitting given that his talents predominantly lie in his vocal abilities and creative expression. His proficiency and artistry in singing, rather than instrumental performance, are what predominantly define his contributions to the musical domain.

    [10:56am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: This is still debatable anyways.

    [10:59am, 31/01/2024] Malam Umar Iro: Sir, kindly help us with examples of those musicians that use their voices as instruments

    [11:01am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: An instrument here does not refer to the conventional meaning of musical instruments. In Hausa for instance, you may say *muryarsa ce makaminsa. Muryarsa ce garkuwarsa. Muryarsa ce jarinsa. Maganarsa ce jarinsa. "

    [11:03am, 31/01/2024] www.amsoshi.com: However, I know of teams known as "vocals" across the world that uses their articulatory organs as musical instruments.

    A YouTube search will be great (Vocals).

    [11:08am, 31/01/2024] Malam Umar Iro: Thanks so much sir I appreciate your explanation

    [3:59pm, 31/01/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon. sir. Ina son gabatar da muƙala a kan Bakandamiyar nan

    [5:44pm, 31/01/2024] Prof. A.B. Yahya: Wadda ta ƙunshi iskewar da Faru ya yi ma suda da burtu da Labarawan bakin bahar maliya.

    [5:35pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

     

    Jagora: Ni dai bari in zaka inganai,

    Y/Amshi: Usumanu na Shamaki wan maza,

    Jagora: Ni dai bari in zaka in ganai,

    Y/Amshi: Usumanu na Shamaki wan maza,

    Biyash Shehu dut tahi bin rangama,

    Waɗan ga Sarakunan zamani,

    Yayin Gimbiya masu guntun naɗi,

    Icce da kogo ina za a kyautak kirki?

    Gindin Waƙa: Mai raba riguna na Muhamman Bello,

    Jikan Hassan ɗan Moyi.

    Ɗiyan Waƙa ne ☝️☝️☝️ daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Talata Mafara, Alhaji Shehu Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    Ya yi Sarauta a Talata Mafara daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [5:37pm, 02/02/2024] www.amsoshi.com: Don Allah, ko Makaɗa Sa'idu Faru ya yi waƙoƙin siyasa? Shin ana iya ba mu misalansu idan akwai?

    [5:44pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Makaɗa Sa'idu Faru ya yi Waƙoƙin Siyasa, musamman a Jamhuriya ta biyu. Farko ya goyi bayan Jam'iyyar NPN daga baya ya koma goyon bayan Jam'iyyar UPN.

    Ya yi wa Jam'iyyar NPN Waƙoƙi, ɗaya daga ciki ita ce mai amshi " Jam'iyyad da ba munahucci ta ɗiyan ƙwarai, jama'ag ga mu zaɓi NPN tahi gaskiya".

    Bayan ya koma UPN ya yi wa Jam'iyyar Waƙoƙi, ciki kuwa har da mai amshi "Ku zaɓi UPN Arewa, taimakon jama'a take yi, maguɗi ab bata ƙamna".

    Ba ni da waɗan nan Waƙoƙin, kuma a halin yanzu ban san a inda za a same su ba.

    [5:51pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Zama Giwa ta fito kiyo tai miƙa ta zo ta sha ruwa,

    Y/Amshi: Kuji Ɗan Zomo na hwaɗin hwaɗama su Tsari, Tsara mu tai gida

    Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,

    Jagora/Y/Amshi: Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,

    Jagora: Gurnanin Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora ɗemuwa,

    Y/Amshi: Ga wani ya yi Kokuwa da wan ƙarfi nai,

    Ya hwaɗi ya kare,

    Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,

    Jagora/Y/Amshi: Tun dai ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,

    Jagora: Ko jiya na iske Gamdayaƙi da Tuji sun iske Jinjimi,

    To sun ko murɗa gardama,

    Sun iske su Bubuƙuwa ruwa,

    Y/Amshi: Dan naan niko ina gaton gaɓa,

    Sai nik kwaɗa gaisuwa,

    Su ko sun daƙile ni dud,

    Niko niƙ ƙara gaisuwa,

    Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya amsa gaisuwa,

    Jagora: Dan nan sai Jinjimi da yad darzaza ya suntule shi dud,

    Y/Amshi: Shi ko Tuji da ad da girman baki yak kwashe Jinjimi,

    Dan nan Bubuƙuwa da tar rura tag gangame su dut,

    Jagora/Y/Amshi: Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,

    Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,

    Y/Amshi: Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,

    Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,

    Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,

    Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Dagacin Banga, Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1934 zuwa wafatinsa a shekarar 1963), Ta Makaɗa Sa'idu Faru mai taken "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi. Rubutawar Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

    Talata, 21/11/2023.

    [5:56pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Assalamu alaikum

    Don Allah zan iya samun audio na Bakandamiyar Sa'idu Faru?

    [5:56pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Wace Waƙar ce Bakandamiyarsa?

    [6:03pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Duk wadda ku masana wakokin kuka dauka a matsayin Bakandamiya. Ina so ne in kwatanta da na wasu mawaƙan tare da dora ta a wani mizanin.

    [6:04pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allah ya gafarta Malam, wa ne mu, yaji a gefen ƙosai!

    [6:06pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Watakila:

    -wadda ta fi fice

    -wadda ta fi fito da shi

    - wadda ake ganin ya fi so/sha'awa

    ..........

    [6:08pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Duk da yake ba dalibin Waƙa nake ba, ina ganin kamar waƙar da ya yi wa Maccido za ta iya zama......

    [6:10pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Don Allah ku gyara sunan sarautar Hon. Alhaji Ibrahim. Ina jin tutsun kwamfuta ne don ba ta son ta iya Hausa!

    [6:16pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allah ya gafarta Malam akwai bayanai masu karo da juna a tattaunawar da aka yi dashi kafin wafatinsa, a kafafen yaɗa labarai daban daban akan Bakandamiyarsa.

    Halifansa Alhaji Ibrahim a wata tattaunawa da na yi dashi ya kawo Waƙoƙi guda biyu yana cewa Mahaifin nasa ya fi son ɗaya daga cikin su, a gefe ɗaya kuma akasarin jama'a sun fi son ɗayar.

    Sa'idu Faru ya fi son ta Marigayi Mai girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Ƙaura Namoda, Sarkin Kiyawa Abubakar Garba wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi mai amshi "Gwabron Giwa na Shamaki baba uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kansakalin daga".

    Jama'a kuma a cewar Alhaji Ibrahim Sa'idu Faru sun fi shauƙin ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III mai amshi "Kana shire Baban Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo". Allahu Wa'alam!

    [6:28pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Shugabannin wannan dandali da ku fa nike! Yadda kwamfuta ta rubuta sarautar Hon. Alhaji Ibrahim ba daidai ba. Ta yi tutsu!! "Ɗanmadami" ne!!! Ta cire "ma"

    [6:34pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: To madalla! Bayani ya fara fitowa. Don Allah a turo mini duk biyun. Na gode

    [6:36pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: In Shaa Allah Allah ya gafarta Malam.

    [6:39pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: @ Farfesa Ibrahim Sarkin Sudan. Ta farko ce Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba ☝️

    [6:39pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Kana shire Baban Yan Ruwa ☝️

    [6:43pm, 02/02/2024] Prof. A. M. Bunza: Danyaro Ƙaramar ɗamba Koko- Besse Local Government.

    Ga mai kiɗi da baki

    Ba ki da kalangu ba

    In da akwai kalangu

    Da an tattausa min

    Kunga! Kun! Regidi

    Regekai! Kunga kun!

    Haka kuma akwai wani a ƙasar Haɗa LG mai kiɗin Wanakiri Don Kwanya

    [7:02pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Bakandamiyar waƙa ko tsakanin mawaƙa akan samu saɓani. Wani mawaƙi kan ɗauki ɗaya daga cikin waƙoƙinsa a matsayin bakandamiyarsa saboda wasu dalilai kamar ta yadda yake ji idan yana rera ta, ko saboda ya fi samun kyauta idan yana rera ta, ko kuma ya yanke hukuncin cewa ita jama'a suka fi so.

    Ta bangaren jama'a kuwa yana yiwuwa saboda dukan wadancan dalilai da na ambata ko saboda wasu dalilai na dabam. Idan aka tambaye ni wace waƙa cikin waƙoƙin Sa'idu Faru nake ganin ita ce Bakandamiya sai in ce "Kana Shire Baban 'yan ruwa" mai farawa da/Gardaye zo kai man iso/ saboda dalilai kamar haka:

    -Tun ina matashi nake jin daɗinta kuma har yanzu a ganina duk ta fi daɗi da tsaruwa.

    -Ranar da aka naɗa Muhammadu Macciɗo ita ce Rima rediyo ya saka ana ambatar shi ne Sarkin Musulmi a masallacin Muhammadu Bello. Ina saurare sai da hawaye suka zubo mini saboda jin daɗi da tausayi.

    [7:27pm, 02/02/2024] +234 812 462 9009: An nuna ma'anar meronymy kamar shi ne sashen wani abu ko a part of something. Wato akwai abinda ake kira holonym ko cikakken abu. To part of holonym shi ne meronym. Mango tree shi ne holonym ɗan mangwaro shi ne meronym na mango tree.

    [7:58pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon duk da ban son in yi sarauta amma da yake akwai jininta cikina, idan ina sauraren "Kana Shire" sai in nasarta cewa da ni aka yi wa ita da na ba Sa'idu Faru Zamfara kaf!😂😂😂

    [8:35pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Sarkin Musulmin wata ran kake,

    Da imani da mu'ujiza na nan ga Malam Macciɗo,

    Tun ga Alu mai saje nij jiya.

    Ka kai kamab Bello swasswakiya,

    Da kyauta da mulki da ban gaskiya,

    [9:27pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon. da dai ce min ka yi:

    /Ka kai kam Nana gulbin sani/

    /Bajinin Giɗaɗo hab Buhari/

    /Baban Macciɗo wan Junaidu/,

    da kuwa na ba ka FUG duka har da su Abu-Ubaidah 😂!

    [10:03pm, 02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Allah ya gafarta Malam, ina mamakin yadda 'yan galadimomi kan rikirkici idan makada sun sa su gaba!

    [10:05pm, 02/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Ban dai sani ba ko abin a kayan kiɗan yake.

    Ba 'yan Galadimomi ba, hatta' yan dambe da kokawa da ma 'yan rawa da duk wani da aka buga wa kayan kiɗa.

    [10:06pm, 02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wata kyautar sai daga baya mutun ya koma cizon yatsa!

    [10:47pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Tasirin waƙa ne. Galibi ba cikin hayyacinsu suke yin abubuwan da suke yi ba. Waƙa kamar giya take ga hankalin ɗan Adam saboda ta fi yin tasiri ga zuciya bisa ga maganar yau da kullum ko sauran ɓangarorin adabi. Kwatanta da yadda mata ke kasancewa idan suna gaban mawaƙa masu yi musu kiɗa da waƙa

    [10:39pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Sarkin Tudun Falale gogarman Magaji Ummaru,

    Y/Amshi: Ba yau ba ko mazan jiya sun san kana da martaba,

    Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu,

    Dangalin gidan mai saje

    shirin ka ya yi kyau

    Jagora: Mai fada Ɗan Iya

    Y/Amshi: Ga Sarkin Kiɗinku ya zaka,

    Na zo a bani doki

    Wani sansame abun suka,

    Ya riƙa da gaskiya

    Muhammadun Muhammadu,

    Dangalin gidan mai saje shirin ka ya yi kyau,

    Wasu ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Dagacin wani gari da ake kira Falale a gundumar Gummi ta Jihar Sakkwato (a wancan lokaci) yanzu kuma Falale hedikwatar gundumar Falale ce a Masarauta mai daraja ta ɗaya ta Gummi dake Jihar Zamfara.

    Laƙabin Sarautar yana nan bai canja/canza daga Tudun Falale ba. Sunan wanda aka yi wa wannan Waƙar shi ne Muhammadu ɗan Sarkin Gummi (laƙabin Sarautar Gummi shi ne Sarkin Mafaran Gummi da ya samo asali daga wanda ya ƙirƙiri gidan Sarautar na yau tun a cikin ƙarni na 18, Malam Muhammadu Waru ɗan Sarkin Bukkuyum/Sarkin Dankon Bukkuyum Ali Bazamfare ko Ali Jan Masari da ya fito daga gidan Sarautar Mafara/Talata Mafara).

    [10:47pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allahu Akbar! Alƙali Malam Haliru Wurno ya zauna Ƙauyenmu a cikin 1970s/80s har ma ya auri Cousin tawa, duk da yake ba su haihu ba suka rabu. Shekaranjiya ma ɗiyar Cousin ɗin tawa da ta aure shi ta zo ganin mu daga inda take aure a Kano.

    [10:54pm, 02/02/2024] +234 812 462 9009: Ni ko mun yi karantarwa da Alkali Haliru Wurno a GSS Wurno daga 1989 zuwa 1990 lokacin da na bar Wurno. A lokacin ya bar alkalanci. Sha'iri sosai. Da waƙe yake karantar da yara addinin Musulunci. Kuma yana yi wa waɗanda suka taba shi zambo a waƙoƙin sa. Allah Ya gafarta masa Ya sa aljanna firdausi ce makomar sa.

    [10:56pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Ni kuma mun fara haduwa da Birnin Magaji a rana 5/12/2022 a wani taro a Kaduna. Yadda na ji yana bayani 'yan dambe da makadan dambe to ko Dan'anace iyakar abin ke nan.

    Zan so a ce ya karasa rayuwarsa a aji. Za a amfana sosai. Allah ya ƙara lafiya da basira.

    [11:02pm, 02/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    Dogon sarki yana da ban shawa,

    Ran da an ka zo taro,

    Ya yi kyau da riguna,

    Duk wanda ag gajere,

    A aje shi gun rabon dawo,

    Shi kai ma wanga dunƙule,

    Shi kai ma wanga dunƙule,

    In wurin da mata ciki,

    Har tuman gada shi kai.

    [11:02pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Alhaji Ɗan Ali ci fansa,

    Y/Amshi: Abun biya kake ɗan Shehu,

    Alhaji Ɗan Ali ci fansa

    Jagora: Ɗaukan ni ka goya ɗan Korau,

    Y/Amshi: Kada kabab baƙauye ya wahalsan,

    Abun biya kake ɗan Shehu,

    Alhaji Ɗan Ali ci fansa

    Wasu ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Dagacin Birnin Magaji a Jihar Sakkwato ta wancan lokaci (Sokoto, Kebbi, Zamfara) yanzu garin ya zamo hedikwatar Masarautar Birnin Magaji mai daraja ta biyu a Jihar Zamfara, wato/watau Marigayi Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1945 zuwa rasuwarsa a shekarar 2005. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [11:04pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa Allah ya gafarta Malam duk da yake mun fara haɗuwa ne a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto a shekarar 2020, lokacin Taro akan Tsohuwar Daular Zamfara da Jami'ar ta gabatar. Duk da yake Allah ya gafarta Malam bazai tuna mun haɗu a lokacin ba.

    [11:08pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Jama'a a duba wadannan ko za a sami abin rubutawa a kansu:

    - Zamfarci a Wakokin Sa'idu Faru

    -Fitattun Salailai a Wakokin Sa'idu Faru

    Fasahar kulla Zaren Tunani a Wakokin Sa'idu Faru

    Lafuzzan Raha a Wakokin Sa'idu Faru

    Salon Zayyana a Wakokin Sa'idu Faru

    Kambamawa a gurbin Yabo a Wakokin Sa'idu Faru.

    [11:10pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu. Waƙoƙin Haliru yawa ne da su kuma a fannoni dabam dabam, ga su tarshe da hikimomi na harshe da lamarin rayuwa. Mawaƙi ne wanda ya yi kama da Shata ta fuskar saƙa waƙa nan take Ɗalibaina a wata shekara da na gayyato musu shi sun gwada shi da suka tambaye shi yaya waƙa ke zo masa, sai ya ce babu yadda ba ta zo masa. Suka ce masa yana iya yin waƙa nan take? Sai ya ce in sha Allahu. Matsalarsa ita ce yana buƙatar alƙami da wurin da zai rubuta ta, wato takarda. Suka ce to ya yi musu waƙa alhali ranar ce kuma lokacin ne ya taɓa dafuwa da su. Ni kuwa sai na ba shi alli, na ce ga allo nan. Haka ko aka yi. Ya yi musu waƙa mai albarka. Ɗaliban da ya yi wa waƙar na tabbata wasu suna nan da ita. Ina jin cikin shekarun 1990 aka yi haka. Ban da tabbacin ainin shekarar

    [11:11pm, 02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A gaskiya ba taɓa taron ƙara wa juna sani mai gata irin wannan ba. Allah ya saka da alheri, Ya sa a wanye lafiya.

    [11:17pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Wa da Ƙane ne. Dogon ne Ƙane kuma wanda ya yi wa Waƙar, gajeren ne ya zambata. Mahaifinsu ɗaya, Sarkin Mafaran Gummi Muhammadu Maidabo.

    Sai dai wanda ya zambata ɗin ne ya gadi gidan a cikin 1970s bayan an cire/yi wa Mahaifin nasu murabus daga sarauta.

    [11:18pm, 02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu:

    Ga manyan malamanmu sun hadu,

    Ga manazartanmu dus sun hallara,

    Suna ta begen manyan kiɗi,

    Sa'idu na Faru Uban kiɗi,

    Na ji daɗin da ankai wannan hadin.

    [11:27pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ina ba shugabannin wannan Zaure shawarar su riƙa tattara irin wannan tattaunawa su tace su mayar da ita wani kundin da za su iya sayarwa. Suna iya sa masa suna: Nazarin Waƙoƙin Hausa a Bakunan Manazarta da Masu Sha'awa Idan ko suka bar tattaunawar ta bi iska, to kada su yi mamaki idan suka ga wani ya riga su.

    [11:30pm, 02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Lallai a irin wannan tattaunawa mutane suna iya samun abin rubutawa.

    [11:34pm, 02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu:

    In dai waƙa ce ta uban kiɗi,

    Manyan mutanenmu suna shire,

    Ga Danmadaminmu yana gaba,

    Mu ga mu taronmu muna biye,

    Duk kowane tasa kawa daban,

    Can za mu taronmu a Zamfara,

    Ga shehuna sun hadu tattare,

    Muna ta waƙar Sarkin kida,

    Waƙan nan da Da'umma yai nufi

    [11:51pm, 02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Jama'a kuna lure da yadda waƙa ke tasiri ga zukatan har da manazarta! Da tattaunawar a kan zube ko wasan kwaikwayo take ban zaton a samu wani nan take ya gwada fasaharsa

    [11:55pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Gidan Malam Giɗaɗo Ɗan Lema mijin Kakarsa Malama Husaina/Hasana bn Mujaddadi (Nana Asma'u) Uwar Daje muke so ya gada In Shaa Allah.

    [12:12am, 03/02/2024] Prof. A. M. Bunza: To su turakun waƙoƙin Sa'idu Faru fa? Ai su ne kan takarda.

    [12:13am, 03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Dabirtau mai ban tsoro,

    Y/Amshi: Shehu ƙanen S/fulani Amadu,

    Gwabron Giwa kana da martaba,

    Usumanu na Bunguɗu Uban Marahwan Keku na Atto mai wuyak karo,

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai girma Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [12:13am, 03/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Makada Sa'idu Faru cewa ya yi a wata waƙar;

    Karya kot tara ta yah haye,

    Dawowa za ta yi ta wargaje,

    Ka ishe shi buku yana rabon ido!

    [12:21am, 03/02/2024] Bilya Abubakar: Assalamu alaikum, haƙiƙa ire-iren mu ƙananan almajirai muna biye kuma muna fa’idantuwa. Saboda haka ina faɗa addu'ar Allah Ya ƙaro buɗi da taimako ga abinda aka tunkara.

    Bayan haka, inda hali ina roƙon a ɗora mun waƙa "Mai babban ɗakin ƙasar Kano Alhajiya Baba Sa'idu" domin ina so ne in gunar da wani aiki kan waƙar. Ina fatar wannan r̃oƙo nawa zai samu karɓuwa ga Malamaina da shuwagabannin na. Wassalam

    [12:31am, 03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Marigayiya Mai Girma Mai Babban Ɗaki, Hajiya Hasiya/Asiya Abdullahi Bayero. Matar Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero ɗan Sarki Abbas ɗan Sarki Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarki Malam Ibrahim Dabo. Mahaifiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero ɗan Sarki Abdullahi Bayero. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [12:31am, 03/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Wani malaminka tun yana ɗan sakandare yake ƙuƙutawa ya halarci taro

    [12:34am, 03/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Allah Sarki! Ai kun taka muhimmiyar rawa a fagen ilmi, mu sai dai mu biyo baya!

    [12:37am, 03/02/2024] Mal. H.U. Maikwari

    Riƙa da gaskiya Sarkin Gobir na Bunguɗu,

    Don wanga da yab baka

    Yanzu ba wani gaba nai,

    Jikan Nana uwad Daje na,

    Kuma su aj jinin Shehu Ɗanfodiyo.

    Katsinawa sai dai su gan ka ba dai su cimma ba.

    [6:28am, 03/02/2024] Mal. B.H. Tsafe:

    Sarki sannunka da ƙoƙari,

    Wanga aiki sai fa muzakkari,

    Masana manazarta arziki

    Ma su son harshen ga ya yo ciri

    Ya yi gogayya da na 'yan gari

    Allah mun gode abin yabo

    [7:16am, 03/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wani dan waƙar Maituru Ubankiɗi yakan ba ni dariya inda ya ce;

    Wane ba yaro na ba,

    Shekara sittin yab ba ni,

    Gyara huska ka sa ana,

    Ce mai danyarro.

    Wanzame ukku ag garai,

    Wanga guda yai da sahe,

    Wanga guda yai da rana,

    Wanga guda ko yana zuwa goshin issha'i. 🤣🤣🤣🤣

    [7:17am, 03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ɗanmalikin Gabake, Ɗanmalikin Gidan Goga da Ɗanmalikin Janbaƙo duka Dagatai ne a wancan lokaci, kuma dukan su Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya yi masu Waƙa.

    Gabake a Gundumar Ƙaura Namoda, Gidan Goga da Janbaƙo a Gundumar Maradun.

    Laƙabin Sarautar Ɗanmaliki nada alaƙa da Cibiyar Daular Usmaniya, Sakkwato inda ake hasashen daga nan ne ta samo asali tun bayan tabbatarwa Malam Doshiro Bn Abdullahi Mujakka (Fulani Bororo/Bororoji ne) Sarautar Galadiman Sakkwato bayan kafa Daula.

    Galadima ne a Daular Gobir, ya yi mubayi'a ga mujahidai. Bayan an tabbatar masa da wannan sarauta a Cibiyar Daular Usmaniya sai ya naɗa ɗansa a matsayin mataimakinsa da laƙabin "Ɗanmaliki". Ya zuwa yanzu zuriyarsa ke riƙe da wannan sarauta ta Ɗanmaliki a Masarautar Sakkwato. Marigayi Alhaji Zubairu Tela ya taɓa riƙe wannan sarauta.

    A gefe ɗaya kuma Gabake (a Masarautar Ƙaura Namoda ta yanzu) wadda ta samu ne a cikin ƙarni na 18 ta hanyar ƙirƙira daga wasu jinsin Fulani da ake kira "Alwanko" dake da tushen su a wani wuri a cikin Jamhuriyar Nijar ta yanzu, laƙabin sarautarsu Ɗanmaliki duk da yake babu takamaiman dalili da lokacin da suka fara amfani da wannan laƙabi.

    Samuwar Marigayi Alhaji Mu'azu a matsayin Ɗanmalikin Gabake wanda ya yi sarauta daga cikin 1940s zuwa rasuwarsa a shekarar 1989 ya sanya wannan laƙabi na Ɗanmaliki ya yi amo sosai a mafi yawan masarautun Arewa.

    Saboda shahararsa masarautu da dama sun ɗauki wannan laƙabin sun ayyana sa a matsayin sarauta. Shi dai ne wanda Makaɗa da Mawaƙa suka yi wa Waƙoƙi da dama duk da yake wasu Waƙoƙin ba su yi fice ba kamar yadda ta Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun mai amshi "Jikan Musa Ɗanmaliki, gamda'aren Amadu (Baura jikan Baura, Mu'azu Allah sa ka gama lahiya) ta yi amo ba.

    Har ila yau akwai Ɗanmalikin Achida wanda Uban Ƙasa/Hakimi ne a Gundumar Achida, Masarautar Sakkwato da ya fito daga tsatson Muɗagel ɗan Modibbo Ummaru Mu'alkammu (suke sarautar Gundumar Mu'alkammu da kuma Magajin Rafin Sakkwato).

    Akwai kuma Ɗanmalikin Katsaura a Masarautar Ƙaura Namoda duk da yake babu takamaiman lokacin da suka fara amfani da wannan laƙabi a matsayin Dagaci.

    Gidan Goga da Janbaƙo a halin yanzu hedikwatocin Gunduma ne a Masarautar Maradun dake Jihar Zamfara. Ana iya alaƙanta samuwar laƙabin Sarautarsu ta Ɗanmaliki da samuwar ta a Cibiyar Daular Usmaniya idan aka yi la'akari da zamowar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a matsayin Sarki a Maradun a cikin 1870. Koma dai me ne ne, Sa'idu Faru ya waƙe Ɗanmalikin Gabake da na Gidan Goga da na Janbaƙo.

    [7:40am, 03/02/2024] Dr. H. Yelwa: Saidu Faru na cewa;

    "Mu Allah yaw wa gudummuwa da waƙa

    Haw wata ya kide wata. "

    Haka shi Danmadamin yake. Nazari da ra'ayin shi ga wakoki, wasu na ishe wasu.

    [7:47am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello Lalle haka. Akwai wakokin Marigayi Usmanu Dangwaggo, Danmadamin Sakkwato, Dan Sarkin Fulanin Bungudu Usman Kure, da Kuma waƙar Marigayi Alhaji Muhammad Dan Sokoto/Hakimin Gada, Keku Dantabawa.

    [7:52am, 03/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: A ƙara duba wadannan ko akwai abin da za a tsinta.

    1.       Kalmomin Fannu a Wakokin Sa'idu Faru

    2.       Fasalin Zambo da Habaici a Wakokin Sa'idu Faru

    3.       Hoton Tattalin Arzikin Hausawa a Wakokin Sa'idu Faru

    4.       Tubka da Walwala a Wakokin Sa'idu Faru.

    5.       Munanan Dabi'u a Mahangar Saidu Faru.

    6.       Zumuntar Fasahar Saidu Faru da Wasu Makadan Kasar Hausa

    7.       Koda kai a Wakokin Sa'idu Faru

    8.       Waskiya a Wakokin Sa'idu Faru

    9.       Hoton Rayuwar Sa'idu Faru a Cikin Wakokinsa

    10.    Butulci a Mahangar Saidu Faru

    11.    Alakar Sa'idu Faru da Sarakunan Kasar Hausa: Tsokaci Daga Wakokinsa

    12.    Salon Yaba Kyauta a Wakokin Sa'idu Faru.

    13.    Aron Hannu a Wakokin Sa'idu Faru

    14.    Barkwanci a Bakin Sa'idu Faru

    [7:54am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello "Yan Sarkin Bungudu akwai dubu, amma manyan gidan dabam suke" 😊

    A cikin waƙar Gwabron giwa kana da Martaba, Usmanu na Bungudu uban marahwa na Atto mai wuyar karo.

    Alhaji Attoh Bungudu, shine mahaihin Sarkin Fulanin Bungudu na yanzu, Alhaji Hassan Attahiru.

    [8:04am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello Wasu daga cikin wasiyoyin Saiɗu Faru:

    'Sarkin Musulmin watan ran kake'.

    Allah Ya kaddari Muhammad Maccido da zama Sarkin Musulmi.

    ”Dangiwa komai yad dade, ta tabbata yin giwa yakai inji Sarkin Maradun, Sarkin Kaya"

    Ishara akan cewa komai tad dade, wata ran, zuri'ar Muhammad Mualleydi Dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello zasu iya nema da yin sarautar Sarkin Musulmi.

    Bayan rasuwar Sarkin Musulmi Maccido, Sarkin Kayan Maradun na yanzu Alhaji Muhammadu Garba Tambari yana daya daga cikin wadanda suka nemi sarautar Sarkin Musulmi.

    [8:07am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello Ana iya duba:

    Salon siyasa, mulki da shugabanci a masarautun Kasar Hausa daga wakokin Marigayi Saiɗu Faru.

    [8:42am, 03/02/2024] Alh. A. Nakawada: ”Dangiwa komai yad dade, ta tabbata yin giwa yakai inji Sarkin Maradun, Sarkin Kaya"

    "Ishara akan cewa komai tad dade, wata ran, zuri'ar Muhammad Mualleydi Dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello zasu iya nema da yin sarautar Sarkin Musulmi"

    👆👆

    Ni kuma abin da na fahimta da wanga baiti na Sa'idu, ba wai ishara ko hasashe ne Sarkin Kaya ya yi a kan shi ba. Aa, hasashe ne mai kama da kirari Sarkin Ƙaya ya yi wa Sarkin Kudu Maccido

    [8:59am, 03/02/2024] Mal. M.M. Yankara:

    Manyan kaya

    Manyan ganwo

    Jakki kankambab banza garai

    Wasu kaya sai bisa raƙumi

    Bajini birni

    Bajini dawa

    Na gaisheka da ƙoƙari.

    [10:36am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello Na'am. Idan na fahimceka, baitin na isar da sakon Sarkin Kaya ne zuwa ga Sarkin Kudu Maccido na gadon Sarki Bubakar. Saboda haka, hasashen na zaman Maccido Sarkin Musulmi ne.

    [11:58am, 03/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko dai turke/jigo; turaku/jigogi

    [4:31pm, 03/02/2024] Alh. A. Nakawada: Bere gud. Na yaba maku bisa kyakkyawan tsari da kuke tafiyar da ayyukan wannan taro da za ayi na Makada Sa'idu Faru.

    Tunda ake irin wadannan hu66asa akan Makadan mu na gargajiya ban ga wanda ya kai wannan tsari da azama ba. Allah Yasa ayi nasara

    [7:37pm, 03/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ina ba da shawara da a ƙara wannan cikin batutuwan da ake iya rubuta muƙala:

    -Turke da tubali a waƙoƙin Faɗa.

    Na ba da wannan shawara ne saboda ganin ba salo ba ne kurum cikin waƙoƙin fada; kuma saboda ganin ɗalibai kan samu ruɗanin fahimta tsakanin turke/tubali da kuma salo.

    A lura: ba lalle batun da na sa ya kasance a yadda na ba da shi ba. Ana iya a yi masa kwaskwarima don ya dace da Hausar Zauren. Haka kuma yana iya ya kasance cikin kashin B da C.

    Na gode ƙwarai.

    - A B Yahya

    [9:04pm, 03/02/2024] +2348161747863: Assalamu alaikum, ina yi wa manyan Malumanmu da Shehunnai barka da dare. Ina bibiyar yadda ake baje kolin ilimai a wannan zaure tun daga shigata zuwa yanzu. Amma batun da babban Shehunmu ya kawo, ya ta6a zuciyata Kwarai da gaske., Wato ‘turke da tubali’. Da Allah zai sa Malumanmu su taimaka su 6arza mana shi, da an samu ficewar kitse daga rogo. Abubuwa ne da suke yi mana, mu dalibai shigar giza-gizai.

    Ina yi wa manyan Shehunanmu da Malamanmu adu’ar alheri, Allah ya ƙara lafiya da rakiya mai amfani.

    Mai rubutu:

    Musa labaran Muhammad,

    Dalibi a Jami’ar Bayero ta Kano, kuma mai Nazari a kan ayyukan Sa’idu Faru Rungumi Dan’Umma. 

    [10:50pm, 03/02/2024] www.amsoshi.com: Lallai an fara gabatar da takardu. 🙏👍😅

    Wannan taro dole ma kowa ya samu abin rubutawa. An ba mu topics an ba mu bayanai. 🥳

    [11:50pm, 03/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    "... Kuma ya gama da yaron,

    Da zai ja ma kinani. "

    Me kalmar ƙinani' take nufi?

    [11:51pm, 03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Shaihunan Malamanmu na kusa In Shaa Allah zamu samu ansar wannan tambayar, ni dai ban sani ba.

    [11:58pm, 03/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    "... Baba ya bamu bandir guda dun na 'lailai'... "

    "... Hula kalabus guda goma yab ban... "

    Don Allah ko za mu samu bayanin:

    a. lailai

    b. Hula Kulabus

    [12:00am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Lailai shi ne kuke kira Alwayyo/Farin yadi.

    Hula Kalabus ita ce doguwar hullar nan ja da ake sakawa ayi rawani saman ta.

    [12:13am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allah ya jiƙan Ɗan Umma Uban Kiɗi mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Rungumi Ɗan Tumba Makaɗa Sa'idu Faru, amin.

    [12:50am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Kila karin Hausar da Faru ya tashi da shi ne. Ni dai na san kinami. "na" ɗin doguwar gaɓa ce. Kinami ko ita ce fatar da ke tare da sirdin doki. Tana da lanƙwasa inda ake soka ƙarfen da ake jan (likkafar) sirdin doki. A ƙara tambayar masu hawan doki don ni ban taɓa hawan doki ba.

    [1:24am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ja mai tunani ya ce.

    Abin da hakan ke nufi wani maroki da kan tsaya tare da mawakin idan yana waƙa, wanda ke tuna masa wasu abubuwan da yake fadi a cikin waƙar.

    [1:37am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ke nan kuskuren rubuta abin da mawaƙin ya faɗa aka yi ko? Ina ba da shawarar a saurari ɗiyan waƙar na kamin da bayan layukan da kalmar ta fito. Sannan a tambai masu kiyon dawaki musamman na bargar gidan sarki. 

    [6:53am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Ai ita ce Kakanmu Farfesa A.B. YAHYA ya ba da amsa.

    A fahimtata, ai idan doki yana da wannan kinanin da aka bayyana, da shi ɗin ma ana sarrafa dokin.

    Don haka duk kuna a kan hanya, babu kuskure.

    [6:54am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Ke nan kalmar tana cikin kinin kalmomi.

    [6:55am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wato kamar yadda shi mawakin ya nuna ya ji daɗin yadda ubangidan yake yi masa. Bayan kyautar da yake ba shi har wani yaro yakan hada shi da shi wanda ke jan tunaninsa ta hanyar gaya masa wasu abubuwan kamar sunayen wasu makusantan Sarkin wadanda shi bai san su ba, sai ya ambace su a cikin waƙar. Wannan shi zai yiwu iyalan gidan ko aminansa ko kakanninsa da sauransu. 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

    [6:55am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Ban da tabbaci, amma idan fasarar da Farfesa A.B. YAHYA ya yi kin fahimce ta to lallai kalmar tana da muhalli a inda aka ɗora ta.

    [6:57am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Ban da tabbaci, amma idan fasarar da Farfesa A.B. YAHYA ya yi kin fahimce ta to lallai kalmar tana da muhalli a inda aka ɗora ta.

    [7:00am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Mai yiwuwa kuma a wata rerawar yana cewa tunani, wata kuma ya ce kinani. Kamar yadda yake cewa:

    "Ban je gidan 'ɗan giya' niy yi roƙo ba,

    Ko ya raba lafiya ba ruwana. "

    Amma da jagoran zai yi takiɗi kuma sai ya ce:

    "Ban je gidan 'ɗan bita' niy yi roƙo ba.... "

    [7:12am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Ni ma gaskiya kamar "kinani" na ji mawaƙin ya ce

    [7:12am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ai zambo/habaici ne.

    [7:14am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Dukkan ofisoshinsu ana ce masu gidan 'yan bita saboda koyaushe suna nan kuma duk inda ya lalacce sai su gyara.

    [7:22am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Mai yiwuwa dai wannan bayani na ki shi ne zai warware muna wannan hange.

    Amma kuma za a iya zurfafa bincike.

    Ban yi mamaki ba, domin idan mutum ya kwankwaɗi ilmi da yawa, yakan fasara wani abu da tunaninsa, ko ya fahimce shi daidai da tunaninsa.

    Ni da Dr. Ya ba da kalmar tunani, sai na ji kamar ita ta fi dacewa da muhallin bayanin.

    Da na saurari waƙar kuma, sai na ji kalmar da aka faɗa ta farko ta bayyana.

    Mun gode ƙwarai.

    Allah Ya biya ku.

    [7:29am, 04/02/2024] Mal. M.A. Umar "Ja mai tinani" ne, kasancewar da/t/ da/k/ sun yi tarayya a yanayin furuci da matsayin maƙwallato, ma'ana, tsayau ne marasa ziza... Sai kuma a ka samu naso, inda wasalin gaba, na sama maras kewaye/i/ ya nashe wasalin ƙurya na sama mai kewaya/u/. Kamar yadda ake da "buki" ya koma "biki"...

    [7:29am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Da yake an gama shirya doki tsaf! Cikar kyautar ita ce a ba shi yaron da zai ja masa ƙinani', wannan kalmar na iya hawa, duba da yadda aka ƙulla ɗan waƙar.

    Kamar yadda kalmar 'tunani' kan iya zama saboda muhimmancin yaron ga makaɗin shi ne ya taimake shi, ya riƙa sanar da shi wasu muhimman abubuwa da zai ƙulla ƙananan saƙonnin waƙar don nuna godiya.

    Amma fa ni kunnuwa na kalmar 'Tunani' suka ji. Mai yiwuwa kuma sanyin Kano ne, ina iya sauya ra'ayi. 😅

    [7:39am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ko dai ya take waƙa ta cika, kuma makadin ya kai don babban bambancin cikakken makadin ke nan, wanda zai wadatar da waƙarsa da kalmomin da manazarta ke iya aiki a kansu. Don dabarar mutun ta fitar da shi ko manyan masana su ƙara saita shi.

    [7:45am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Komai cikar mawakin Hausa yana jin daɗi idan ana jan tunaninsa na ambaton wasu kalamai a waƙarsa, shi ya sa ma sukan sami wani daga cikin mabobinsu mai basira su aje kusa da su don wannan aikin. Wannan ne ke sa waƙar ta yi tsawo da daɗi!

    [7:47am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Wato wasalin/i/ non- central vowel, kenan shi ya koma na tsakiya maras kewaya (high central vowel unrounded)?

    [8:18am, 04/02/2024] Mal. M.A. Umar A waƙar akwai abubuwa da suka shafi tsarin sauti kamar ganɗantawa da naso, misali inda ya ce "jan damishe" daga "damisa" me ya sa sautin/s/ ya koma/sh/? Haka kuma, "zanna", "fan talatin, fan tamanin, fam metin, fam bakwai"

    "Allah shi isam ma" da sauransu!

    [8:20am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Hwan tamaanin da hwan talatin da hwan metin.

    [8:25am, 04/02/2024] Mal. M.A. Umar A nan ya ajiye Zamfarci a gefe "fan" da "fam" ya yi amfani, ba "hwan" ko "hwam"

    [10:55am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙƙan! Wasu ma da suka aje aikin ba du je ko ina ba sai suka yi gidajensu nan cikin dajin. Na taɓa yada zango kusa da gidan irin mutanen nan.

    [11:09am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Tabbas! Manazarcin waƙa ya riƙa la'akari da cewa mawaƙan Hausa, musamman na Fada, kan sa zambo cikin waƙokinsu amma ba su ambatar suna sai dai ishara. Sannan wannan zambo, da yake kishiyar yabo, shi ma yabo ne mawaƙan kan yi ga ubangidansu a dunƙule domin daɗi yake ji idan aka nakkasa ɗan hamayya, wato ɗan sarki

    Noma
    [11:23am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Majalisaɗ ɗunkin duniya

    Majalisaɗ ɗunkin duniya

    Tayi ododi ga manoma

    A riƙa aiki ag gaskiya

    A aje abinci ag gaskiya,

    A tarda gero,

    A tarda dawa,

    A saida gujjiya,

    A saida kaɗa,

    A aje gero so nai mukai,

    Babban abun Nanjeriya,

    Kan dawo in yash sha nono,

    Ko Bature kab ba shi

    ba shi girgizawa amsa yakai,

    Ko da yash sha..

    Jagora/Y/Amshi: Sai kaji ya ɗwaɗwa Ingilishi,

    Kai nai ya hwashe da yat tamni tcakin dawo,

    Asha hura ayi wasa,

    D/Tumba shan hura ba lahani ba ne,

    Jagora/Y/Amshi: Asha hura ayi wasa,

    D/Tumba shan hura ba lahani ba ne,

    Farin cikin Musulmin Duniya,

    Mai martaba na Abubakar,

    Ci fansa Alhaji Macciɗo

    Ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Makaɗa Sa'idu Faru ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III mai gindi "Farin cikin Musulmin Duniya, Mai martaba na Abubakar, Ci fansa Alhaji Macciɗo". Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [11:37am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Shi fa mawaƙin ai abubuwa ne yake faɗa tare da abokan burminsu, fam tamanin + riga, doki + kayan doki + yaro mai jan likkafa....

    Haka kyautar wannan ubangida take. Ko gida zai ba ka sai ya gama (haɗa) ma da mata (wato sa-ɗaka ko kuyanga). A taƙaice cikakkar kyauta yakan yi ba rabi da rabi ba

    [11:45am, 04/02/2024] www.amsoshi.com: "Tsattsafin Tattalin Arziki a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru"

    [11:46am, 04/02/2024] www.amsoshi.com: "Gurbin Noma a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru"

    [11:46am, 04/02/2024] www.amsoshi.com: "Noma a Mahangar Makaɗa Sa'idu Faru"

    [12:11pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Sa'idu Faru bai kai kaiwa, gaisuwar da matafiya ko Hakimi kan kai wa basarake, ko ma mai saukar da baƙo. Shi waƙa ya iya kuma ya san ba kowa ya iya waƙa ba, balle duk mawaƙi idan ba shi ba to shirme (ƙarya ce) ne, shi Sa'idu waƙa ya iya ita zai kai kaiwa. A farko ya ce kowa a Kano, to amma da yake ya san sarakuna akan kai wa kaiwa, sai ya yi amfani da salon waskiya (M B Umar ya fito da wannan salo cikin nazarin waƙa, daga kalmar "waske") ya maimaita layin ya ce Sarkin Kano!

    [1:37pm, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Da wannan, na aminta da kalmar ƙinani'. Allah ya kyauta aikin Malam. 🙏

    [1:50pm, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Kinami dai ko?

    [1:51pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ki tuntuɓi Farfesa Sa'idu Gusau don shi ne Giwa a dajin Waƙoƙin Baka na Hausa, mu duk 'yan tsaro ne!!!

    [2:04pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Mai yiwuwa "kinani" ɗin Faru yake faɗi don kila a karin Hausar da ya tashi da ita haka ake faɗi. Ba ku ganin wasu su ce "faɗi/hwaɗi" wasu ko su ce "hiɗi"; wasu su ce "can" wasu ko su ce "in"; wasu su ce "koma" wasu su ce "dawai/dawaya". Hausa ƙwarai take da wadatar kalmomi da ma'anoni kamar Larabci

    [2:07pm, 04/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Lallai ba karamar godiya muke ba ga Malaman mu da suke ta gogoriyo da ninkaya wajen zakulo mana ilimummuka akan wannan fage, kuma suke shayar damu. Sannun ku da ƙoƙari masu girma masanan mu. Allah ya tabbatar da alkaluman ku cikin danshi a ko yaushe. Kullum ina jin daɗi yadda na yi Hausa a A-Level na kuma maida hankali akai sosai. Gashi yanzu muna ta bi muna karuwa sannan ina ganin kamar yanzu ma cikin aji nike. Muna biye Malaman mu. 🙏✊

    [10:21pm, 04/02/2024] Dr. H. Yelwa: Wato, Sarkin Bauran Dange Muhammadu Dangwaggo, Sarkin Musulmi Hassan dan Muazu da Shehu baban Sarkin Musulmi Abubakar diyan Sarkin Musulmi Mu’azu gidan Bello ne.

    [10:25pm, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Afuwan, Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Malam Usman ba ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ba ne. Jikan Sarkin Musulmi Mu'azu ne kamar yadda Sarkin Musulmi Abubakar III ya ke, kenan Malam Usman ne ya haifi Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo da Sarkin Musulmi Abubakar III 🙏🙏🙏

    [10:30pm, 04/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa. Saboda Sa’idu na ce ma Sarkin Gabas Shehu

    "Jikan Hassan dan Mamman"..

    Hassan a nan👆🏽Sarki Hassan dan Muazu wan Shehu baban Sarki Garba Na3.

    [10:31pm, 04/02/2024] Dr. I.I. Dutsinma: Slm. Wai don Allah ina ne Bauran Dange? Ko ita ce ake cewa Dange Shuni?

    [10:40pm, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa! Sarkin Baura Muhammadu Ɗangwaggo ne babban ɗa ga Malam Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu.

    [10:41pm, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Baura ko Sarkin Baura shi ne laƙabin sarautar Dange, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shuni dake Jihar Sakkwato.

    [10:45pm, 04/02/2024] Dr. I.I. Dutsinma: Na gane. To asalin waɗnada suka asasa wannan garin Katsinawa ne daga ƙabilar Fulani mai suna Dangi. Kuma sun taso ne daga ƙasar Yantumaki ta Katsina kafin yaƙin Shehu Ɗanfodiyo

    Wani ɗa ne daga cikin 'ya'yan Dangi Yusufu. Shi ne ya kafa Dange wadda ke kan hanyar Sokoto amma ban san tarihin Dange Shunin ba. Shi yasa ma ya kira garin da Dangi, daga baya ya koma Dange. Akwai wani littafi da na karanta na tarihin Fulani Dangi a jihar Katsina. Wallahu a alam

    [10:58pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Jama'a Dange/Shuni ai Ƙaramar Hukuma ce da ta haɗa ƙasar Dange da ƙasar Shuni. Wata rana mai yiwuwa ne a ƙirƙiro Ƙaramar Hukumar Dange, da Ƙaramar Hukumar Shuni.

    Wani ƙarin bayani ko tunatarwa, garin Shuni nan aka haifi mawaƙin da kuka sani mai suna Aliyu Ɗandawo mahaifin mawaƙin nan da kila matasan yau suka fi sani, wato Sani Aliyu Ɗandawo.

    [11:02pm, 04/02/2024] Dr. I.I. Dutsinma: Ok. To ni ba Shunin nake nufi ba Dangen dai wadda ke kan hanyar Sokoto. 'Swasswakiya'. Don Allah me kalmar nan take nufi?

    Tsakin tama: wannan salon baubawan burmi/ salon gambiza ne Sa'idu Faru ya yi amfani da shi domin ya kamanta Tijjani Hashim ya nuna cewa mutum ne wanda bai da daɗin gamo, ba a iya ja da shi don ba za a ji daɗi ba.

    Kafin a fahimci haka bari mu dubi kalmomin biyu: tsaki da tama.

    Tsakin da aka fi kawowa ga rai shi ne sauran dawon da bai damu ba wanda ke ƙasan ƙwarya ko kwanon fura. Tsakin nan na fura yana da daɗin tamnawa saboda nonon da ya cuɗe shi sosai. Kuma ko bai ji nono ba yana da daɗi. Saboda haka ba matsala ga wanda ya tauna shi.

    Tama kuwa dutse ne baƙi wanda ni dai a Sokoto aka fi samu kusa da gulbi. Baƙi ne mai ƙarfi sosai kuma bai jiƙa ko ka zuba mai ruwa ko ka saka shi cikin gulbi. Ina jin maƙera suna amfani da shi wurin ƙira. To ka kwatanta an samu injin ya Farfesa wannan dutse. Idan aka ba ka garin wannan dutse aka ce ka sa ga bakinka ka tauna, yaya haƙora ka za su ji? Ko za ka ji kamar kana taunar tsakin fura?

    A nazarin waƙa idan mawaƙi ya haɗa kalmomi biyu wuri guda ba yadda aka saba haɗa su ba to sai a ce ya yi amfani da salon ganin gambiza ko salon baubawan burmi. A haɗa tsaki da tama iyakar rashin gami ke nan domin shi dai tsaki na fura aka sani ba tama ko tsakuwa ba. Saboda haka Sa'idu Faru shi sai ya haɗa tsaki da tama domin ya samu ma'anar 'rashin jin daɗi' ko 'wuyar gamo' don ya siffanta Ahmad Tijjani Hashim da cewa abokan hamayya ba su iya kome da shi a kokuwar mulki ko wani abu.

    Kamanceceniya da wani ta halayya, musamman halaye na gari.

    Wani malamina Bafalasdine yana koyon Hausa sai mu ɗalibansa muka gwada shi muka nuna masa riga muka ce me ake kiran wannan da Hausa? Sai ya ce riga. Muka ce sosai haka ne. Muka nuna abubuwa da dama yana faɗin sunayensu da Hausa. Sai kuma muka nuna masa wando, ya tsaya ya noce kai yana tunani, can sai ya ce, "rigar ƙafa"!

    A nan ya yi gamin gambiza.

    Ga wasu misalan baubawan burmi:

    Bangon dutsi

    Fitilar sharri

    Rigar ƙaya

    Wandon ƙarfe

    Tsakin tsakuwa

    Madallah da wanga bayani, Allah ya gafarta Malam. 🙋🏽‍

    Akwai kuma:

    -Rijiyar lemu

    - Gadon ƙaya

    Bari dai in bari kada Kanawa su yi mini caa!

    Allah ya biya, Malam har da irinsu:?

    Hadarin kasa?

    Azumin jrmage?

    Bakan gizo?

    Duk irinsu ne?

    Jemage

    Sosai.

    Ɗanƙwairo ya ce:

    /Hadarin ƙasa maganin mai kabido/.

    Kabido shi ne rigar ruwa na Bahaushe kafin zuwan Turawa.

    Da kaba ake saƙa kabido, a yafa shi tun daga kai har zuwa guwawu. Ruwan sama ba su taɓa jikin mutum.

    To ita ce mutanen suke kwatanta da ruwa ya fito daga kasa ba daga sama ba kamar yadda aka saba, da mutun zai jike sharkaf!

    *** ***

    Bayan an cire Sarki Kabiru ɗan Sule sai aka naɗa Muhammadu Mainasara Sambo Ƙanen Sarki Sule (Mahaifinsu ɗaya da Sarki Sule Mahaifin Sarki Kabiru) a shekarar 1976.

    Sarki Muhammadu Mainasara Sambo ya rasu a farko farkon 2000s sai aka naɗa Abubakar Atiku Muhammadu Sambo, Ƙanensu Sarki Sule da Sarki Muhammadu Mainasara (Mahaifinsu ɗaya dasu).

    An cire Sarki Abubakar Atiku Muhammadu Sambo a cikin 2022, sai aka naɗa Muhammadu Bello ɗan Sarki Sule Muhammadu Sambo wanda kuma yaya ne/wa ne ga Sarki Kabiru Suleiman Muhammadu Sambo (Mahaifinsu ɗaya, Sarki Suleiman Muhammadu Sambo). Sarki Muhammadu Bello Suleiman ke sarauta a halin yanzu.

    Eh ɗan'uwansa ne. Da Mahaifinsa da Mahaifin Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Mahaifinsu ɗaya.

    Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ne ya haifi wanda aka yi wa Waƙar, wato Sarkin Gabas na Mafara Shehu. Shi kuma Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne.

    Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III ne, Sarkin Musulmi Abubakar III ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Mai girma Sarkin Gobir Na Bunguɗu kuma Shaihin Malaminmu Dr. Haruna Umar Bunguɗu barka da dare. Sannu da fama ta raya muna Zaure.

    Das rayit (That is right!), haka Mai Martaba S/M Macciɗo (Allah Ya rahamce shi) ke cewa idan abin da aka faɗi ya yi masa daidai sosai.

    Sarkin Gabas Shehu ya yi Sarauta a Talata Mafara daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969 sanadiyar gobara, Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Idan kuwa ya lura da cewa akwai 'yar matsala sai ka ji ya ce, "To daidai"😂

    Allah Ya yi masa rahma da Aljannar Firdausi amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu Ya Rabbal alamina Ya Arhamar rahimina

    Allah Sarki!!! Haƙiƙa sau da yawa ina jin wannan kalmar a bakinsa. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Ina iya tuna ranar da aka ba shi takardar tabbatar masa da sarautar Sarkin Musulmi a cikin watan Afrilun 1996, a Masallacin Bello dake Ƙofar Fadar Sarkin Musulmi a Sakkwato ta hannun Alhaji Aminu Ahmed Nahuce wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Mulkin Soja a Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto da Zamfara). Ni kuma ina ɗaukowa Gidan Rediyon Rima na Sakkwato rahotanni daga Gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato a lokacin.

    Ka san Ni Bagiɗaɗe ne, saboda haka in na je gidansa kafin ya hau sarauta, yakan ce Bagiɗade ya zo ya ci abinci. Nan na ga abin mamaki. Kwalba cike da man shanu yake bungulewa cikin kwanon abincin!

    Hakika muna godiya ga Allah SWT da Ya nufe mu da samun wannan ilimi mai albarka daga bakunan Malamanmu masu albarka a wannan babban zaure mai albarka.

    *** ***

    Don Allah ina ƙara roƙon wannan Zaure da ya gurza dukan abin da jama'a suka saka cikinsa, tun daga rana ta farko, a mayar kundi. Na fi aminta da littafi a kan na'urorin nan na zamani domin masu shuɗewa ne. Kaset-kaset na rikoda sun isa misali: Ko dai su cumuimuye har su tsinke, ko a yi ɗungum a ƙirƙiro wata na'ura da ba ta iya juyo abin da ke cikin kaset! Wa ya sani ko nan gaba a ƙirƙiro abin da ya fi 'memory carɗ ko 'hard drive' sauƙin tu'ammuli amma kuma ba zai iya juyo abin da ke cikinsu ba?!

    *** ***

    Na tambayi wani dan cikin gidan fadar sarkin Musulmi ya tabbatar man da cewa ƙumatu' jekadiya ce a gidan sarkin Musulmi. Sunanta na yanka shi ne Halima/Halimatu. Dalilin da ya sa ake mata lakabi da Kumatu, sabo da sunan matar sarkin Musulmi Abubakar III ke gare ta watau mahaifiya ce ga sarkin Musulmi Muhammadu Macido.

    To amma mece ce ma'anar sunan Kumatu cikin Hausa ko wani harshe da Hausawa suke da kusanci da shi? Misali, idan aka kira macce Tumba, to wadda aka haifa ce sakamakon auren zumunta, wato mahaifan mata da miji 'yan'uwa ne. Haka wanda ake wa laƙabi da Gambo ana nufin wanda/wadda aka haifa bayan 'yan biyu. To amma Kumatu fa?

    A nan Kumatu na nufin wadda ke da manyan kumatu. Sifa ce a nahawun Hausa

    Ke nan jekadiyar mai manyan kumatu ce ba kamar yadda ka yi bayani tun farko ba ko? An yi amfani da siffarta ne ba don tana da suna guda da mahaifiyar Sarkin Musulmi Macciɗo ba. Da ba mai manyan kumatu ba ce da an dubi wata siffarta an kira ta da ita. Misali, idan mai babban goshi ce watakila a kira ta da Goshi.

    ... Cikin tukar rukuɓu, tukuɗin Tumba yai tuɓus... Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Sauna da mai nagarta duh kama rika na Bubakar🤣🤣🤣

    ..... Wandara Allah ya taimake ka riƙon kowa da gaskiya....

    Faru mawaki ne Mai fikra da zalaka da hikma. Allah ya jikan shi da rahama.

    Sosai kuwa, ai mashahuri ne a waƙar musamman waƙar fada. Shi ne mawakin da muke misali da shi hankali kwance a matsayin makadin fada.

    .... Sa'idu Hwaru ka Waƙam mulki/iko, komi kaj jiya ƙarya akai...

    Idan kai ba ka yi Sarki ba, ko ka gadi sarauta, sai dai ya ambaci sunanka a cikin waƙar Sarkin ko mai niyyar zama Sarki.

    Don ya gode ma kyautad da Kay yi mai.

    Ina nufin da sarakina da 'Yangaladimomi yake yi wa Waƙa.

    Ai kamar shi ne babban dalilin yi wa wannan Taron laƙabi da "4 Decades Of Hausa Royal Songs...../Saboda kusan kashi Casa'in a cikin kashi Ɗari na Waƙoƙinsa na masu iko/mulki ko alaƙa da mulki ko iko ne.

    A wace shekara Sa'idu Faru ya rasu?

    A shekarar 2004.

    A shekarar 1987.

    An haifi makaɗa Saɗu Faru a shekarar 1932, a garin faru, karamar hukumar maradun.

    Da shekara 91 ya yi wafati

    Anya dai Ɗangaladima?

    Duba wannan bayani da Hon. Ɗanmadami ya yi. -1996-9 =1987

    Rankai dade, kamar na yi karanbani.

    Afuwan 🙏

    Haka nagani a sashen idon matambayi wanda suke bayar da tarihin makadan kasar hausa.

    Ranka ya daɗe barka da Jumu'a, Allah ya karɓi ibadunmu, ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin.

    A zance mafi shahara an haife shi a shekarar 1916, ya rasu a shekarar 1987. Kenan ya yi shekara 71 a duniya.

    Ƴallaɓai haka a ka rubuta a waƙoƙin da aka turo.

    "Kashi bakwai kak kwasa,

    Ƴan sarki na kallo,

    Gidan Bani,

    Kai kak kai,

    Ga irin wagga maslaha,

    Ga ka ɗan ma darijja,

    Ga ka jiƙan Usmanu, Kurɗabi na Hodiyo,

    Ga ka sarkin nasara,

    Ga ka Alhaji Macciɗo,

    Ga jikka ta yi dubu,

    Ga ka malammi kake,

    Ga ka mummuni ka ke,

    Abin da Allah duk kai wa mutum,

    Baba yai maka".

    ☝️

    Lissafin 7 ya fita. Amma a wata rerawa sai ya ƙara da:

    " Ga ka baka za'ida".

    Yabo iya yabo! Lalle Sa'idu Faru tuni ya share wa Sarkin Kudu Macciɗo hanyar zama sarkin musulmi.

    Allah ya gafarta musu.

    Sai kuma ga shi bayan shekaru 9 da wafatin Sa'idu Allah ya tabbatar da wannan fatar da addu'a tasa, Muhammadu Macciɗo ya zama Sarkin Musulmi. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    A zance mafi shahara an haifi Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III a shekarar 1926 a garin Dange, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shuni, Jihar Sakkwato.

    Ya zo Talata Mafara a matsayin Hakimi a shekarar 1953, aka mayar dashi Sakkwato a shekarar 1956.

    Ya zama Sarkin Musulmi a shekarar 1996, Allah SWT ya karɓi abinsa a shekarar 2006. 1926, 1956, 1996 da 2006. Allahu Akbar! Allah ya jiƙan sa da rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Gaskiya wannan wata Makaranta ce da ya kamata a maida hankali domin kwasar garabasar karatu. Allah ya yi muku jagora.

    Daga gidan sarautar Maradun ake tura ɗan Sarki zuwa Faru ya yi Sarauta a matsayin Dagaci/Uban Ƙasa/Hakimi da laƙabin "Sarkin Yamma".

    A cikin wannan Waƙar za a ji Sa'idu Faru yana cewa "Iro Magajin Shehu da Bello", yana nufin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio domin Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ne ya ƙirƙiri gidan Sarautar Maradun na yanzu, ya kuma yi sarauta daga shekarar 1870 zuwa rasuwarsa a shekarar 1874.

    Shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Sarkin Yamman Faru Ibrahim ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Abubakar/Bubakar ne wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1939 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi.

    Shi ma Sarkin Yamman Faru Ibrahim Abubakar an cire shi ne a farko farkon 1960s, ya rasu a cikin 1999/2000. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Don Allah ina ƙara roƙon wannan Zaure da ya gurza dukan abin da jama'a suka saka cikinsa, tun daga rana ta farko, a mayar kundi. Na fi aminta da littafi a kan na'urorin nan na zamani domin masu shuɗewa ne. Kaset-kaset na rikoda sun isa misali: Ko dai su cumuimuye har su tsinke, ko a yi ɗungum a ƙirƙiro wata na'ura da ba ta iya juyo abin da ke cikin kaset! Wa ya sani ko nan gaba a ƙirƙiro abin da ya fi 'memory carɗ ko 'hard drive' sauƙin tu'ammuli amma kuma ba zai iya juyo abin da ke cikinsu ba?!

    Tunkuda Tunku cikin tukar rukubu..... Salam!

    "Uban Kumatu uban Isa jikan Abubakar... "

    Na tambayi wani dan cikin gidan fadar sarkin Musulmi ya tabbatar man da cewa ƙumatu' jekadiya ce a gidan sarkin Musulmi. Sunanta na yanka shi ne Halima/Halimatu. Dalilin da ya sa ake mata lakabi da Kumatu, sabo da sunan matar sarkin Musulmi Abubakar III ke gare ta watau mahaifiya ce ga sarkin Musulmi Muhammadu Macido.

    To amma mece ce ma'anar sunan Kumatu cikin Hausa ko wani harshe da Hausawa suke da kusanci da shi? Misali, idan aka kira macce Tumba, to wadda aka haifa ce sakamakon auren zumunta, wato mahaifan mata da miji 'yan'uwa ne. Haka wanda ake wa laƙabi da Gambo ana nufin wanda/wadda aka haifa bayan 'yan biyu. To amma Kumatu fa?

    A nan Kumatu na nufin wadda ke da manyan kumatu. Sifa ce a nahawun Hausa

    Ke nan jekadiyar mai manyan kumatu ce ba kamar yadda ka yi bayani tun farko ba ko? An yi amfani da siffarta ne ba don tana da suna guda da mahaifiyar Sarkin Musulmi Macciɗo ba. Da ba mai manyan kumatu ba ce da an dubi wata siffarta an kira ta da ita. Misali, idan mai babban goshi ce watakila a kira ta da Goshi.

    ... Cikin tukar rukuɓu, tukuɗin Tumba yai tuɓus... Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Sauna da mai nagarta duh kama rika na Bubakar🤣🤣🤣

    ..... Wandara Allah ya taimake ka riƙon kowa da gaskiya....

    Faru mawaki ne Mai fikra da zalaka da hikma. Allah ya jikan shi da rahama.

    Sosai kuwa, ai mashahuri ne a waƙar musamman waƙar fada. Shi ne mawakin da muke misali da shi hankali kwance a matsayin makadin fada.

    .... Sa'idu Hwaru ka Waƙam mulki/iko, komi kaj jiya ƙarya akai...

    Idan kai ba ka yi Sarki ba, ko ka gadi sarauta, sai dai ya ambaci sunanka a cikin waƙar Sarkin ko mai niyyar zama Sarki.

    Don ya gode ma kyautad da Kay yi mai.

    Ina nufin da sarakina da 'Yangaladimomi yake yi wa Waƙa.

    Ai kamar shi ne babban dalilin yi wa wannan Taron laƙabi da "4 Decades Of Hausa Royal Songs...../Saboda kusan kashi Casa'in a cikin kashi Ɗari na Waƙoƙinsa na masu iko/mulki ko alaƙa da mulki ko iko ne.

    A wace shekara Sa'idu Faru ya rasu?

    A shekarar 2004.

    A shekarar 1987.

    An haifi makaɗa Saɗu Faru a shekarar 1932, a garin faru, karamar hukumar maradun.

    Da shekara 91 ya yi wafati

    Anya dai Ɗangaladima?

    Duba wannan bayani da Hon. Ɗanmadami ya yi. -1996-9 =1987

    Rankai dade, kamar na yi karanbani.

    Afuwan 🙏

    Haka nagani a sashen idon matambayi wanda suke bayar da tarihin makadan kasar hausa.

    A zance mafi shahara an haife shi a shekarar 1916, ya rasu a shekarar 1987. Kenan ya yi shekara 71 a duniya.

    [6:05pm, 09/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A nawa ɗan gajeren nazari akan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba na ci karo da waƙoƙinsa na faɗakarwa da na siyasa da kuma na wasu ɗaiɗaikun jama'a da ba su alaƙanci sarauta ko fada ba.

    Daga cikin irin waɗannan waƙoƙin na mutanen da ba su jiɓinci sarauta ko fada ba akwai na Engineer Abubakar Sahabi Sakkwato da Engineer Tori Aliyu.

    Kafin in san cewa Marigayi Alhaji Muhammadu Ɗandurgu Ƙaura Namoda banda zamansa Attajiri, hakimi ne na ɗora sa a cikin layin mutanen da ba su da alaƙa da sarauta ko fada da ya waƙe.

    Akwai kuma Alhaji Tumba Rawayya da nike yi wa kallon Attajirin da ya amfana daga fasahar waƙar Sa'idu Faru, sai daga baya na fahimci yana da alaƙa da fadar Dagacin Rawayya/Rashin Rawayya.

    Duba da rashin samun ƙarin wasu mutane irin su Engineer Abubakar Sahabi Sakkwato da Engineer Tori Aliyu Sakkwato masu waƙoƙi daga Malamin Waƙa ne ya sanya ni cimma matsayar kiransa da "Makaɗin Fada" kacokan.

    Duk kuwa da cewa babu mamaki ana iya samun su fiye da haka, amma idan muka duba cewa a cikin kashi Ɗari na Waƙoƙinsa, kashi Casa'in duka na Sarauta/Sarakuna/Masu alaƙa da sarauta ne sai nike kallon kamar hujjata na iya tsayuwa. Allahu Wa'alam!

    [6:10pm, 09/02/2024] Hon. H.A. Gusau: Allah ya ƙara lafiya da basira da hazaƙa, Honourable.  Encyclopaedia harshen Hausa, jama'ar ta da al'adunta.

    [8:40pm, 09/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ni ma a nan na rakube. Saboda kafin ka ji ya yi wata waƙar da ba ta fada ba wata dagar duniya ce, idan kuma ka debi irin wadannan wakokin ka watsa a cikin sauran sai su bace bat!

    [9:00pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa mutane da yawa suna kallon sa da mawaƙin fada/sarauta. Ina jin na taɓa karanta wata hira da aka yi da shi, ko kuma wani littafi da aka ruwaito yana cewa shi sai ɗan sarauta yake yi wa waƙa. Sai dai gaskiya na mance da tushen wannan bayani.

    [9:11pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A lura da cewa Ƙarni na 20 ya sa mawaƙan Hausa sassauya matsayinsu sakamakon tasirin Mulkin Mallaka da Turawa suka yi a ƙasar Hausa - kafin Ƙarni na 20 sarakuna ne manyan iyayen gidan mawaƙa, amma a na 20 ɗin zuwa yau sai aka samu wasu rukunan jama'a sun yi ƙarfi, wasu ma fiye da sarakuna, da mawaƙan suka sauya sheƙa, wasu kuwa suka kasance da ƙafa biyu, ba su tsaya ga sarakuna ba ba su tsaya ga wasu ba- kowa ma nasu ne kamar Sani Aliyu Ɗandawo

    [9:30pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Duk da haka ba za a rasa ɗaiɗaiku ba, da kuma wasu sabbin mawaƙa ba. Zamani tafiya yake, mutane su zo da abubuwa na ƙwarai da miyagu, masu kyawo da munana. Ƙasar Hausa ba ta tsira ba. Muna fatar Allah Ya sa mu dace da kyawawa mu kauce wa munana har da na cikin malamai ba masana ba kamar yadda Haliru Wurno ke kiran wasu malamai:

    /Karatu sunka yo ba dai Sani ba/

    /Jawabin saufa nan suke ba na'am ba/

    [9:30pm, 09/02/2024] Mal. B. Lauwali: Wannan zance na cewa an haifi malamin waƙa a shekarar 1916, ya rasu a shekarar 1987 Ina neman madogara

    [9:36pm, 09/02/2024] +234 806 666 5052: Allah gafarta malam abin tambaya anan shi ne? Mawaƙan ƙarni na 20 za a iya sanya su a jemagun mawaƙa kenan ko? Kamar Sani Aliyu Ɗandawo da makamantansu

    [9:47pm, 09/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Hira da ɗansa Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru wanda kuma a halin yanzu shi ne Halifansa a farko farkon shekarar 2018.

    Ni ne na yi hirar dashi. Sunana Ibrahim Muhammad Birnin Magaji.

    [9:53pm, 09/02/2024] Prof. A.A. Dunfawa: Tama dutsi ne da ake narkawa a fitar da karfe daga gare shi. Idan ka je makera za ka ji ana ce ma wata dauda da ke fita daga jikin karfe idan ana narka shi da suna kashin tama.

    [9:56pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ina kyautata zaton idan ka duba Sa'idu Muhammad Gusau, MAKAƊA DA MAWAƘAN HAUSA NA ƊAYA za ka samu

    [10:16pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A taƙaice tama dutsi ne mai tsananin tauri, bai fasuwa da sauƙi kamar sauran duwatsu, sai dai a narka shi da wuta. Tsakinsa kuwa bai taunuwa.

    Idan kuwa Sa'idu Faru cewa ya yi/ƙashin tama/

    To duk salon baubawan burmi ne ya yi amfani da shi, ko ma a ce tun asali Hausawa sun yi amfani da salon. Ƙashin rago ko na nagge ko na kaza da makamantansu ne aka fi sanin zamansu a tare amma ba da tama ba.

    [10:19pm, 09/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe cewa ya yi "Tsakin Tama na Abashe ana shakkah haye ma Amadu, Mai Martaba na Wambai Ɗan Hashim Ƙanen Sarkin Kano".

    [10:29pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni dai ban son in kira su jemagu domin ga kunnuwana wannan kalma ba ta dace da a liƙa wa masu hikimarmu ba.

    Yahihiya da kunkuru

    [3:38pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Yahihiya da Kunkuru, shawara guda sukai... Inji Malamin Waƙa Mai kwana Ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru a cikin Waƙarsa ta Dagacin Falale dake Masarautar Gummi, Jihar Zamfara, Alhaji Muhammadu Bala mai amshi 'Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu, Karsanin/Dangalin gidan Mai saje shirinka ya yi kyau', Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Ya ci gaba yana cewa da Hasbiya da Kurciya, shawara guda sukai har zuwa ƙarshen ɗan/ɗiyan Waƙar.

    Wannan shi ne Kunkuru, ko zamu samu hoton Yahihiya da kuma fashin baƙin abubuwan da ke ƙumshe a cikin wannan ɗan Waƙar/waɗannan ɗiyan Waƙar?

    [3:56pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Na san kunkuru amma ban san yahihiya ba. Idan aka sanar da ni yadda take ta fuskar tafiya da kuma ɗabi'arta dangane da jikinta watakila zan iya fashin baƙin ɗiyan waƙar. Na dai san wata halitta mai kama da kunkuru amma ba kunkuru ba ce. A Anka ne na sha ganin ta, kuma cikin damina na fi ganin ta, musamman idan aka yi ruwa, a wuri mai laka-laka. Ƙumbarta sumul-sumul ba kamar ta kunkururu ba. Idan yaro ya ga wannan halitta zai ce kunkuru ne.

    [3:58pm, 10/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Kunkuru shi ne karamin, yahihiya kuma in ya girma sosai. Kusa duka dabi'unsu iri daya ne.

    [4:02pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ashe! Kunkuru fa ko ƙarami ne siffarsa guda da ta wanda ya girma. A dai ƙara bincike don Allah.

    Mene ne sunan wanda na yi bayani sama

    [4:09pm, 10/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: To ni ma dai abin da na yi tsammani hakan take, amma dai in akwai wani bayanin wani ya taimaka mana.

    [4:34pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Wannan da ka bayyana ƙumbarta sumul sumul ba kamar ta Kunkuru ba ita ce Yahihiya Ranka ya daɗe.

    Kamar dai jikin Mankani da jikin Gwaza.

    [4:50pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Yanzu na fahimta. Sa'idu Faru yana nuni ne da halittun da suka so su yi kama da juna, kamar hasbiya da ƙuruciya da makamantansu. Kusan dabi'arsu guda; sukan yi kwanci a kusan wurare iri ɗaya. Watakila Sa'idu Faru kakannin Dagacin Falale ne yake kwatantawa da wannan; ko kuma wani ɗan sarki ne yake yi wa zambo. Da na saurari waƙar duka da na iya sharhin sosai

    [4:54pm, 10/02/2024] Dr. Kabiru Abdulkarim: Mashaa Allah, Alhamdulillah! Allah ya sa a yi da mu!

    Yahihiya da kunkuru

    [5:15pm, 10/02/2024] +234 812 462 9009: Yahihiya (turtle) ɗan uwan kunkuru ne amma a ruwa yake

    [5:18pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla da wannan gamsasshen bayani Mai Girma Babban Sakatare. Mun ƙaru sosai, Alhamdulillahi.

    [5:21pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A ƙarshen ɗan waƙar/ɗiyan waƙar ya bayyana cewa "Babu wanda yat tai haji babu mai nuhwaz zuwa".

    Da wannan nike tunanin da wasu 'yan Sarki ya ke, sune ya ke yi wa habaici/zambo. Allahu Wa'alam!

    [7:20pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko shakka babu! Da 'yan sarki yake. Wato babu wanda ya kama hanyar zama Dagacin Falale, ba su kyauta ba su riƙa addini ba, kai duk wani halin abin a gode ko a yaba ga mutane ko ga kansu ba su da. 

    [10:07pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A cikin ɗiyan wannan Waƙar, Malamin Waƙa ya kawo sunayen wasu Tsuntsayen da ake samu a Ruwa/Kogi, wato/watau Gamdayaƙi da Tuji da Jinjimi da Bubuƙuwa da Kulme.

    Ko zamu samu hotunansu da bayani akan abun da ɗiyan Waƙar da aka ambace su ke nufi daga masananmu domin mu ƙaru?

    [10:34pm, 10/02/2024] +234 812 462 9009: Ina nan kusa Maigirma Ɗanmadamin Birnin Magaji.

    Daga cikin abubuwan da uban kiɗi ya faɗa akwai kulme/kullume. Shi ba tsuntsu ba ne wani nau'i ne na kifi. Wato babbar tarwaɗa/cat fish.

    [10:37pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Prof. S M Gusau da ya wallafa littafinsa MAKAƊA DA MAWAƘAN HAUSA, littafi na 1 a 1996 ya kawo wata hira da ya yi da Sa'idu Faru da ya ce bai yi wa talaka waƙa saboda dalilin da ya bayar.

    To amma shekarar da aka haifi Sa'idu Faru wadda Gusau ya bayar ita ce "wajajen shekara ta 1932". Wato marubucin bai tabbatar da takamammar shekarar ba. Shafukan da marubucin ya yi cikin wannan littafi sun nuna cewa a lokacin da yake shirya shi littafin a 1987 ne kuma Sa'idu Faru yana raye. A kan wannan dalili ne marubucin bai rubuta shekarar rasuwar Sa'idu Faru ba. Hatta da tarihin ƙanen Sa'idu Faru, wato Mu'azu, da marubucin ya kawo, shi ma (Mu'azu) lokacin yana cikin 'yan amshin Sa'idu Faru.

    [10:40pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A duba shafi na 117 zuwa na 127 na littafin Prof. Sa'idu Muhammad Gusau da na ambata sama.

    Kulme

    [10:41pm, 10/02/2024] +234 812 462 9009: Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi yaa amsa gaisuwa. Mu irin wannan kifin ne mu ke kira kulme/kullume

    [10:45pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla da wannan ƙarin bayani Ranka ya daɗe.

    Ni kuma a hirar da na yi dashi a farko farkon shekarar 2018, ɗansa kuma halifansa Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru ya sheda mani cewa an haifi mahaifin nasa a shekarar 1916 a garin Faru, Ƙaramar Hukumar Mulkin Maradun a Jihar Zamfara ta yanzu. Ya kuma yi wafati a cikin shekarar 1987.

    Wannan bayanin ne da kuma wasu kalaman da shi Makaɗa Sa'idu Faru ya yi a cikin wasu hirarrakin da kafafen yaɗa labarai suka yi dashi, waɗan da na samu, na ƙumshe na kuma saka a cikin Shirinmu na Kundin Mawaƙan Hausa na Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru da muka gabatar a cikin shekarar ta 2018.

    [10:59pm, 10/02/2024] Sarkin Rafin Gobir Yayana gaskiya ne wannan shine kulme ataƙaice duk wata tarwaɗa da ta girma itamukacema kulme, shikuma Tuji tsuntsu ne na sahara ƙato ne sosai Amman baikai agululu ba Amman yahi Hankaka girma, Amman Gamdayaƙi da jinjimi da Bubuƙuwa sune tsuntsayen fadama sunfiyin ƙoto kusada Ruwa, maigirma Danmadami

    [11:02pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle shi ko Gusau da Sa'idu Faru ɗin ya yi hira ranar 3/9/1985 da wata hira da ya kawo da wakilin GTK ya yi da Sa'idu Faru a 1986. Duk wannan a littafin da na kawo.

    Ni dai na san lokacin S/M MACCIƊO ya rasu Sa'idu Faru ya dade da rasuwa domin a ranar naɗin kuma lokacin da gidan rediyon Rima yana kawo Muryar naɗin ya sa waƙar nan KANA SHIRE, sai da na tuna da Faru cikin zuciyata ina faɗin Sa'idu Faru ina ma a raye kake? Da sai Sarki ya ba ka wasu garuruwa ba ma gari ba

    [11:07pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Mu kuma muna kiran sa da ɗan ƙari, wato "kullume"

    [11:12pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla da wannan ƙarin bayani Ranka ya daɗe. Kasancewar Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru ɗan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba wanda ya yi karatun zamani har ma ya yi aikin Gwamnati irin karantarwa (inda ya kai matsayin headmaster na Primary School) da aikin Ɗan Sanda kafin daga bisani ya yi ritaya ya rungumi wannan sabgar ta gidansu gadan-gadan wanda ya yi biyar Mahaifin nasa wajen Kiɗa da Waƙa tun yana ƙaramin yaro, sai nike gani yana iya zama madogara wajen bayar da haƙiƙannin bayani akan Mahaifin nasa.

    [11:21pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle wannan bayani haka yake. Lokacin ƙuruciyata tsakanin 1959-1965 bubuƙuwa kan zo Sakkwato, kuma ta sauka kan wani iccen a Giɗaɗawa. Wani lokaci idan na bi ta wurin nakan ga kifi ƙarƙashin iccen wanda ya faɗo daga bakin tsuntsuwar.

    Na karanta cewa bubuƙuwa daga ƙasashe masu nisa kamar Turai takan taso lokacin wani yanayi ta zo nan ƙasar Hausa ta yada zango kamin ta tashi ta yi gaba ko ta koma inda ta fito. Ba a dai ganin ta sai cikin damina zuwa ƙarshen hunturu, kamar yadda shamuwa kan zo ƙasar Hausa ga damina ta kuma tafi abinta idan damina ta kusa ƙarewa. Har ma Hausawa kan ɗauka idan ka ga shamuwa to damina tana kusa; idan kuma ka daina ganin ta to damina tana kusa da wucewa.

    [11:28pm, 10/02/2024] Sarkin Rafin Gobir Hakane Ranka yadade, Shi ma jinjimi da Gamdayaƙi anfi ganinsu lokacin Damana, musamman idan Gulbi yazaka yabada Ruwa Hwadama duktashahe, Tafukka sunsha, Bayuyuka sunsha, ƙorammu sunsha

    [11:33pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Hirar da Marigayi Alhaji Aminu Balarabe Gusau, Wakilin Gaskiya Tafi Kwabo na Gusau ya yi da Makaɗa Sa'idu Faru ce a shekarar 1986.

    [11:50pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla Ranka ya daɗe. Ya rayu har bayan ƙirƙiro Jihar Zamfara. Mun yi aiki tare dashi a lokacin da nike jagorancin Ƙungiyar Yan Jaridu Ta Ƙasa Reshen Jihar Zamfara da lokacin da na yi Daraktan Hulɗa da Yan Jaridu a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da kuma lokacin da na yi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Zamfara.

    Allah ya jiƙan sa da rahama tare da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [8:11am, 11/02/2024] Dr. H. Yelwa: Ina tuna wata waƙa ta Sarkin Kudu Maccido mai amshin;

    "Hwarin cikin musulmi

    Duk kai muka takama yau

    Muhammadu Muhammadu

    Dan Audu maidarajja. "

    [8:45am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Salamun alaikum. Don ina tambaya:

    "Gurbin giwa sai ɗanta,

    Daudu zaman gurbi sai ɗan kada... "

    Zaman 'gurbi' ko 'gulbi' sai ɗan kada?

    [9:09am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Tambaya:

    "Ƙarya ba magana ba ce,

    Yanzu gidan Alu/Abu,

    Ba kamar Macciɗon Hausa,

    Girmanka ya kai,

    Muƙaminka ya kai,

    Riƙon duniya,

    Wada Bubakar yak kai. "

    Alu ko Abu (short form of Abubakar)? 🙏

    [9:11am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Alu mai saje ko Alu mai sango? Wanne Sa'idu Faru yake yawan danganta Macciɗo da shi?

    [9:13am, 11/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A tunanina kalma daya ce ta ruda ki a cikin jimlar. Wato "zaman" idan Basakkwace ya ce zaman yana nufin domin/saboda. Yanzu sai ki tayar ki ji.

    [9:16am, 11/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ki faɗi sunan waƙar don a ƙara saurarawa.

    [9:19am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Allah ya gafarta Malam, na fahimci 'zaman' abin nufi 'muhalli'.

    Gurbi kuwa na nufin 'rami maras zurfi'.

    Gulbi shi ne 'ƙaramin kogi'.

    Duka ma'anonin suna iya zama. Amma wacce Sa'idu Faru ya ambata?

    [9:20am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa: "Kana shire Baba 'Ƴanruwa...

    [9:22am, 11/02/2024] +234 807 642 1242: Tama ba dutsi ba ce. Wani nau'in ma'adani ne a karkashin kasa. Makera kan narka shi da wuta su fitar da ruwan karfe daga cikin Tamar. Sauran birbishin tarkacen da ya rage wanda shi ba karfe ba ne, shi Hausawa ke kira tsakin tama.

    Amma kofa a bude take domin samun karin bayani a kan wannan batu.

    [9:26am, 11/02/2024] Alh. A. Nakawada: "gurbi" ne. A cikin gulbi (river) ake samun "gurbi". Wani mazauni ne cikin ruwa na dabbobin ruwa

    [9:27am, 11/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi: Gurbi yake.

    [9:27am, 11/02/2024] Alh. A. Nakawada: A fahimta ta "Abu" ne. Ai kin ga a baitin ƙarshe ya bayyana "Abubakar" din.

    [9:43am, 11/02/2024] Dr. H. Yelwa: Alu Maisaje👆🏽

    Alu Maisango kuma Kano anka yi shi.

    [9:46am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Haka ne. Wasu rubuce-rubuce, sun yi kuskuren rubuta Alu Maisango. Na gode.

    A fahimtata dangane da kalmar gurbi:

     (1) gurbi - wuri mai zurfi cikin gulbi, manyan namun ruwa sun fi zama ciki kuma galibi sai idan za su ci abinci suke tasowa sama, mutumin da bai iya ruwa ba haɗari ne gare shi ya shiga cikin gurbi.

     (2) gurbi- matsayi ko muƙami ko mataki ko wuri.

    To cikin wannan ɗan waƙa abin da na fahimta shi ne:

    - gurbin giwa: Jagora yana nufin babban matsayi irin wanda magabatan Macciɗo (wato Sarkin Musulmi Abubakar 3 mahaifin Macciɗo) suka kai, babu wanda ya dace da shi sai ɗan Sarkin Musulmi Abubakar 3, (Macciɗo) domin shi ne ya gado shi ta kowace fuska - tsatsonsa ne, nagartattun halaye gare shi.

     (3) gurbi wanda ɗan amshi ya faɗi: kalmar tana da ma'anoni na (1) da (2).

    Duka layukan Jagora da na 'yan amshi kalmar "gurbi" ta dibilwa ce, wato kalmar da take da ma'ana fiye da ɗaya- ma'anar wuri mai zurfi cikin gulbi; ma'anar matsayi ko mataki ko muƙami..

    Sa'idu Faru dai yana nufin babu wanda zai gadi S/M Abubakar na 3 sai jininsa kuma Muhammadu Macciɗo, amma ba talakka ba ko wani ɗan sarki.

    Gafarta Malam ni hira na ji ya yi a Rima Rediyo yana iƙirarin cewa saraki kawai yake wa waƙa.

    Wallahi dai muna ta bautag godiya ga masananmu akan wannan ilimi da muke kwankwaɗa "banɗas" kamar dai yadda Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ke cewa a cikin wata Waƙarsa mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai', wadda/wacce ya yi wa babban ubangidansa, Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Anya! Ba 'Ramboshi' ba ne? A tambayi Dr. Musa Fadama FUGUS, ai "kulume" baƙi ne sosai.

    - Alu Maisaje - Lura da cewa Aliyu biyu suka yi sarautar Sarkin Musulmi.

    - Alu Maisango - wani ƙanen Macciɗo ne, na san shi lokacin yana ɗalibin makarantar da ake kira yanzu Nagarta College. Tare da Sarkin Sudan na Wurno Abubakar, wanda ake yi wa laƙabi da Cika, duka sun yi wannan makaranta. Duka sun riga mu Gidan Gaskiya, Allah Ya gafarta musu, amin

    Ban sa ran Sa'idu Faru yana nufin wani mutum da aka yi a Kano.

    Allah ya gafarta Malam tabbas ya sha faɗin hakan a hirarrakinsa daban daban, a kafafen yaɗa labarai a lokacin da yake raye.

    Ko a cikin Waƙarsa ta Marigayi Mai girma Turakin Kano/Galadiman Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Hashim mai amshi 'Tsakin tama na Abashe ana shakkah haye ma Amadu, mai darajja na Wambai ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano' yana cewa "Sa'idu Hwaru ka Waƙam mulki komi kaj jiya ƙarya akai".

    Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Prof. S M Gusau ma ya ruwaito wata hira makamanciyar wadda ka ji. Duba MAKAƊA DA MAWAƘAN HAUSA na 1, shafi na 120 da ɗure na 5.

    Haka ne Ranka ya daɗe. Senator Aliyu Mai Sango Abubakar III Durumbun Sakkwato kenan.

    Sarkin Musulmi Aliyu Babba ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da ya yi sarauta daga shekarar 1842 zuwa 1859 da kuma Aliyu Ƙarami ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi wanda ya yi Sarkin Musulmi daga shekarar 1866 zuwa 1867. Allah ya jiƙan su da rahama su da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

    ***

    Tabbas hakane Gurbi acikin gulbi yake hakama duk wani wuri mafi zurhi acikin Ruwa shina mukakira Gurbi, acikin gulbi akansamu gurbi dadama kila saboda tsawon gulbi da yawan Ruwan shi, Amman kaman acikin Tafki ko Baye da ƙorama mafiyawansu anfisamun Gurbi guda dai ne, zakaga mafiyawan masu wanka acikin su sukan kiyaye shiga ƙurya a-inda gurbi yake musamman ga waɗanda basuiya Ruwa ba sosai, gurbi nacikin gulbi yanada igiya gurbi nacikin Tafki ko baye da ƙorama bayada igiya saidai zurhi, too kowane daga cikinsu idan bami yahwaɗa sai ta Allah,

    Ai Allah gafarta Malam ana samun bambancin sunan kifi daga wuri zuwa wuri. Akwai buku wanda a wasu wurare ana kiran shi tambo wani wuri kuma ana kiran shi gargaza. Mu dai a fadamar Kanwa da Fadamar Rima ɗan tarwaɗa babba muke kira kulme/kullume.

    Wasu kuma suna kiran buku da "karfasa"

    Ka gani ko? Ni yau ne ma na fara jin wannan sunan.

    A Abuja naji suna kiran shi da "karfasa"

    ***

    Na gode, wannan abin ya dade yana damu na, donn ire-iren sunayen kifayen sun yi yawa har na fara tunanin bambance su zai yi wuya in ba ga Sarkawa ba.

    Haka ne. Amma bambamce bambancen sunayen yana faruwa ne daga wuri zuwa wani wuri.

    Wannan fa ya yi daidai, kuma ya katangance ni da wasu malaman daga rikirkita dalibanmu.

    @~Idris Garba Zagwalis, Malamin ne a fannin zane-zane... Yanzu haka ya fara aiki a kan wasu waƙoƙin Sa'idu Faru ta amfani da kiɗa da zane... Muna maraba da wannan fasaha ta ƙarni na ashirin da ɗaya

    Kififiya mu kan kira wagga

    Ka gani ko? Mu muna cewa yahihiya ku ko kuna cewa kififiya. Hausa ke nan. Abubuwa suna canjawa daga wuri zuwa wani wuri

    Afuwan! Don Allah Maisango yana raye ne ko?

    Mu ma a Katsina ci ƙihihiya muke cewa

    To ita kalmar yahihiya karin harshen ina ne?

    Ban sani ba ko ya auro daga Sarkin Kabin Yabo Maishanu, amma nasan ya auro daga gidan su Sarkin Sudan Shehu Malami. Da suka rabu da ita ta auri Marigayi Alhaji Sahabi Dange Immigration, yanzu haka tana gidansa dake Abuja domin tayi masa wanka.

    Ban iya tuna sunan wanda ta aura. Ko ita matar don 'yar uwa ce ga wani ɗan ajinmu na sakandaren Birnin Kabi mai suna Umaru. Bai fi shekara da rasuwa ba. Kuma yana riƙon sarautar Torankawa ya rasu. To muna sakandare ne matar ta rasu.

    To ita 'yar Sarkin Kabin Yabo ɗin tun cikin shekarun 1970 ta rasu.

    Ɗan'uwanta Umaru ɗan ajina ne a G S S Birnin Kabi, shi ya faɗa min rasuwarta kuma nurse ce. Ina jin ma a Ingila ta yi kwas ɗin

    Ina da Kaka ƴar Chiroman Kano Abdullahi Mageli, babban ɗan sarkin Kano Alu Maisango. Shi kuwa sarkin Kano Alu an ce mahaifiyarsa ƴa/jikar Shehu Usmanu ce, sunanta Saudatu (Goggon Dole).

    Mamakina, a tarihin Kano mun ji yadda Sarkin Kano Alu ya samu laƙanin Maisango, to Sakkwato fa? Ko kuwa nasaba ce ta sa aka samu sunan Maisango a Sakkwato? Sai dai ban san wanda ya tasirantu da wani ba.

    Sakkwato/Kabi/Zanhwara da wasu sassa na Arewancin Jamhuriyar Nijar.

    Daga laƙabin Sarkin Kano Alu/Aliyu Mai Sango/Maje Lokoja ne.

    Aha

    Ya yi to

    Saboda ni nazarin karin harshen ne.

    Idan naga baƙuwar kalma gare ni ina neman sanin ta

    Yes

    Aiki na na PhD da na gabatar a BUK a kan karin harshen Katsinanci da Zamfaranci ne a kan iyakar Katsina da Zamfara.

    Amma ban taɓa ganin wannan kalmar ba

    Ko da yake daga cikin kalmomin da na nazarta ban shiga sashen kalmomin da suka shafi tsuntsaye da namun daji ba sosai

    Kaga wannan ma ya ƙara bani haske wajen yinƙurin yin Post PhD research ɗi na.

    Malam a naku yankin ya kuke kiran wannan halittar?

    Ƙihihiya

    Kuma idan ka lura dama duk lokacin da sautin leɓe hanƙa na

    /f/ ya zo tare da kowane wasslin Hausa, sautin na komawa sautin ɗan maƙoshi a ganɗa na

    /h/. Misali

    A daidaita ciyar Hausa a ce

    fi

    A Katsinanci da sauran kare karen harsuna na yamma kuma a furta da

    hi

    Haƙiƙa Sarkin Kano Aliyu shi ne ya nufi Sakkwato don ya sanar game da gurgusowa Turawan Ingila (Nasara) cikin Daular Usmaniyya. Ina jin ma (ban tabbata ba) kamin ya isa ko ya koma ne Turawan suka isa Kano.

    Ni dai ni ma kunnuwana a bude suke su ji dalilin sunan Maisango daga masana, ba 'yan shaci-faɗi ba na wannan zamani. Allah sa mu dace, Amin.

    Kamar na taba karantawa a tarihi cewa Mahaifiyar Sarkin Kano Alu Mai Sango diya ce ga Sarkin Musulmi Alu Babba Dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

    An ruwaito cewa an rada mashi suna Alu ne saboda Kakanshi, Sarkin Musulmi Aliyu Babba.

    Allah Ya isar wa al'umma abin da tsinannun Turawan nan suka yi a ƙasar Hausa.

    Na rantse da Allah ban ƙaunar Nasara ko ka ɗan.

    Allah Ya gafarta Malam,

    Na taba karanta cewa shi Sarki Alu ne ya kirkiro Sango (explosive device) domin yaki da mutanen damagaram.

    Nasara azzalumai ne makissata ne macuta ne mayaudara ne maɓarnata ne mazambata ne mahilata ne makirai ne...

    ***

    Allah shi gafarta, Sarki Alu Maisango/ Maje Lokoja a lokacin tafiyar shi Sokoto ne Turawa suka shiga Kano kuma suka cita da yaki a 1903. Yazo Sokoto ne a lokacin domin ta'aziyyar rayuwar kawun shi Sarkin Musulmi Danyen Kasko. Yana kan hanyar komawa ne suka samu tabbacin an cinye Kano din.

    Lallai shi dan Saudatu ne diyar Sarkin Musulmi Alu, dalili kenan akayi mashi takwara da kakan shi.

    Shi kuma wancan na Sokoton dan Garba III lallai babu shakka zai zama yaci sunan Sarkin Kano Alu dinne. Kamar yadda a yankin Sokoto ake yawan ce ma Bello- Maiwurno ko Buhari- Maijega ko Shehu- Malami

    Madalla da wannan ƙarin bayani Mai Girma Dokajin Magajin garin Dikko Na Korau.

    Kamar shi ne ko kuma jama'arsa suka gwabza da Turawa a Ƙoramar Zorori/Mashigin Kwatarkwashi har ma Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya ya taskace wannan gwabzawar a cikin Waƙarsa mai amshi "Ga Darajja Amadu Bello da arziki na mazan jiya kay yi".

    Fata a Cikin Waƙar Fada

    Manyan malaman mu ban sani ba ko Malamin kiɗa Saidu shi ma ya yi ma wani fatan zama Sarkin Musulmi, koma bayan Sultan Maccido. Misali duk munsan Jankiɗi, in banda Sarkin Musulmi Abubakar III, mafi kusanci dashi shine Sardauna Ahmadu. To, Jankiɗi ya yi ma jama'a da yawa fatan su zama Sarkin Musulmi; irin su Maccido, Sarkin Gobir Ahmadu Bawa, Sarkin Kudun Gusau Ibrahim da sauran. To, Saidu kuwa ya rinka irin wannan fatar ga sauran yan Sarkin Musulmi, ko kawai ga Baba Commissioner kawai ya tsayar da fatanshi?

    Haka ne Mai Girma Dokaji.

    Shi ma dai Sa'idu Faru ya yi wa masu alaƙa da sarautar Sarkin Musulmi fatar su gadi/gaji gidan, sai dai ba kamar yadda ya fifita babban ubangidan nasa, Muhammadu Macciɗo ba.

    Ya yi wa Sardauna Ahmadu Bello da Sarkin Gobir Na Isa Amadu II, Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Tambari, Sarkin Yamman Faru Ibrahim (Mai abu), Sarkin Yamman Faru Salihu, Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu, Sarkin Bauran Dange Ummaru Faruku, Sarkin Sudan Na Wurno Shehu Malami, Ciroman Dange Ummaru Babuga Dange, Sarkin Tsabta Muhammadu Na Dange da sauran su.

    Allahu Akbar!

    "Ƙoramaz Zorori wurin hwaɗa,

    San Kano ya tarbi Nasara...

    Inji Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya.

    MashaAllah, Yallabai na gane. Lallai ashe shi daure bisar shi ta fata ba ga turken Sarkin Kudu Maccido ba shi kadai.

    Lallai shi ma ya yi ma yan cikin gida waƙa sosai. To, ai Yallabai kusan ba wani Hakimin cikin gida (Batoranke)da bayyi ma waƙa ba. Kila idan aka debe su Sarkin Gabas Goronyo, Sarkin Gobir Gwadabawa bangaren su Sarkin Kudun Sifawa.

    "Usumanu ka hau halifag gadon Moyi,

    Saura halifag gadon Bello ɗan Shehu,

    A kira ka S/Musulmi Usumanu,

    Da mun ci ribaz zaman duniya kenan,

    In da dut an ka juya muna tare".

    Yallabai mu a karin harshen Katsinanci mu na kiransa da KIHIHIYA, amma a kamusu sun sa KIFIFIYA, Allah ya sa mu dace

    Ai ina ganin saboda halin mu na maida 'fa' zuwa 'ha' ne ya kawo haka.

    Kamar yadda naga an yi bayani a sama. Misali mukan ce ma Funtua - Huntua (a baki amma), Fanfarmi- Hwanhwarmi, Fartanya -Hwatanya, lafiya -lahiya dss.

    Wallahi babu na ƙwarai ga iccen kabari. Sun fi kowa makirci da munafunci. Kada ka ba ɗayansu amana.

    Dubi yadda Dukansu suke bayan Isra'ila, amma suna kiran ƙasashen Musulmi da ƙawaye alhali suna ba Isra'ila makamai don su kashe Musulmi. Isra'ila fa yau shekarunsu 75 suna mulkin wariya da mallakar Falasɗinu!Wai har wasu su fito suna cewa wai Falasɗinawa su suka fara tsokana, sai ka ce a Oktoba 7, 2023 rikicin ya fara.

    Ahihiya ko ihihiya a ƙasar Kabi.

    Kunkuru dabam "Ahihiya" dabam. Ahihiya har kujerar zama matan sarkawa kan yi da ita da ranta. Yanzu haka akwai ta Gidan wani Bazabarme mai sayar da kifi a Gidajen Tarayya na Arkilla Sakkwato.

    Allah Sarki. To shi kunkuru fa? Ba a zama a kansa?

    Kihihiya muke kiran ta, a karin harshen Katsinanci. Kihihiya ita ce macen kunkuru.

    Uban kiɗi yahihiya ya ce ba ahihiya ko kuhihiya ba. Yahihiya ta sha bamban da kunkuru saboda bata zama tudu dangane da yanayin ƙafafuwan ta.

    E Malam ba a zama a kansa don ya yi ƙarami. Allah Masani.

    A'a Prof. Sai dai in ba ka taɓa ganin babban kunkuru ba. Ni kam na sha ganin babban kunkuru.

    [3:33am, 12/02/2024]: Kififiya/kihihiya, mu a yankin Katsina ba' a iya zama a kanta saboda kankantarta Amma kamarsu daya da Kunkuru saidai inka Lura akwai banbanci a halittar kofofin kokonsu daga gaba daidai kofar kafafun da Kai na Kunkuru a hade yake na kififiya kuma akwai tsakani kofar kafafun daban na Kai ma daban sannan ita kififiya tana kutsawa cikin Kada mai turbaya musamman ma a karkashin shingen Gona a lokacin da ruwa yake janyewa daga tafkin da suke chiki musamman daidai huduwar sanyin hunturu kuma haka zataci gaba da zama karkashin kasa bata fitowa har sai damina ta fadi sa tafito ta fada tafki,

    Sannan ita koda zata shekara nawa bata girman daya wuce girman kurtun dawadar malamin Zaure, karka manta ita tana yatsu da farata kamar dai na Kunkurun kuma inka Lura tana da dan wani tsigigin bindi a bayanta idan ta girma wannan ita mike cewa Kihihiya a yankinmu na Katsina

    [6:36am, 12/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Kullumen wajenmu bai da ƙaya sama. Muna da kullume, akwai ramboshi.

    [6:38am, 12/02/2024] Mal. H.U. Maikwari A wajenmu (Kulwa), wannan shi ne ragon Nagwade dangin ƙaraye/ƙaraya ne

    [7:48am, 12/02/2024]: Assalamu alaikum. Dangane da shekarar da aka haifi Makada Sa’idu Faru, na dan yi karambani wajen tattara ra’ayoyin masana a kan batun kamar haka, a Shekarar 1976 Makada Sa’idu Faru ya ayyana shekarar da aka haife shi da cewa, an haife shi a shekara ta 1937, ya rasu ke nan yana da shekara 50. Dutsin-Ma (1981) da Gusau (1988 da 2011) da Furniss (1996) sun kawo cewa, an haifi Makada Sa’idu Faru a shekar 1932. Ya rasu ke nan yana da shekara 55. A hirar da aka yi da Ibrahim Danmadami a gidan rediyon Jihar Zamfara a shekarar 2019 da dan Makada Sa’idu Faru Malam Ibrahim Sa’idu Faru a shekara ta 2020 da gidan jaridar leadership Hausa a shekarar 2020 duk sun ayyana cewa an haifi Makada Sa’idu Faru ne a shekara ta 1915/1916, ya rasu ke nan yana da shekara 71/72 a duniya. Allah ya ji kan sa da rahama.

    Idan Allah ya kaddara mini yin rubutu a wannan taro, zan ƙara bibiyar wannan batu domin samar da matsaya guda daya a takardar da za a gabatar in sha Allahu.

    Dalibinku Musa Labaran Muhammad.

    [7:51am, 12/02/2024]: Hakan kuma, a wannan zaure Honorable kuma malam Ibrahim Danmadami ya ƙara maimaita matsayarsa a kan shekarar da aka haifi Makada Sa’idu Faru, kamar yadda ya bayyana a waccar hira da aka yi da shi.

    [8:12am, 12/02/2024] Mal. B. Lauwali: Yallai sannu da ƙoƙari, wannan dan waƙar a cikin wace waƙar Sa'idu Faru zan same shi? Na gode

    [10:01am, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Ƙi garaje Uban Shamaki Shehu,

    Ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro".

    Wannan ☝️shi ne amshin Waƙar da wannan ɗan Waƙar ya fito. Waƙar Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo ce, ya yi sarauta daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    @ Allah Rufa Asiri.

    [10:59am, 12/02/2024]: Madallah da wannan kafa! Muna ta kwasar ilimi a cikin dakunammu, Allah ya saka maku da alheri kuma ya ƙara sani.

    Shin wadannan dabbobi da tsuntsayen da Sarkin waƙa ya yi amfani da su a cikin wannan waƙar, zambo/habaici ne yake yi wa wasu 'yan sarki (idan da 'yan saki yake, to suwa ne? ko yana bayanin dabi'u da halayen tsuntsayen ne. A taimaka da Karin bayani. Muna godiya.

    [11:19am, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Malam Bello Shehu Alkanci sannu da shigowa Zauren Taron Ƙasa da Ƙasa na Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ɗan Abubakar Kusu mai Kotso ɗan Makaɗa Alu Mai Kurya.

    Allah ya ƙara yi muna taimako, amin.

    [11:25am, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Dakta Sani Yahaya Mafara barka da warhaka dafatar kowa da komi lafiya. Kamar manyan Malamammu sun ansa tambayoyinka tun shekaranjiya. Idan ka bibiyi tattaunawar baya a wannan Zauren zaka samu amsoshin In Shaa Allah.

    Sarki

    [5:39pm, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Bajinin gidan Abdullahi, Mai Martaba Zaki Na Abashe Sarkin Kano jikan Alu", inji Malamin Waƙa. Marigayi Mai Martaba San Kano, Alhaji Ado Bayero kenan riƙe da Tagwayen Masu. Allah kyauta makwanci, amin.

    [5:52pm, 12/02/2024] " in sun ba ka kyauta ka da ka amsa,

    Dafi na sun ka ba ka guba Annasara." Attahirun Ahmadu. Allah Ya gafarta masa. Don gubar da Nasara suka feso mana tafi yawa a kan magani.

    [6:13pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa:

    "Dan Audu sarkin manyan sarakuna kake

    Kai ad da kammalallen iko Arewa

    Kowa kac ce kana bida sai yazo. "

    Amshi; "Ado San Kano shirarre. "

    Ina mamakin abinda Saidu ka nuhi da ƙammalallen iko' a can. 👆🏽

    [6:27pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa: Saidu na yi ma Sarkin Kudu Maccido kirari da;

    "Na Marahwa Danbaba maitura haushi

    Na Sarkin Gabas duniya hori wawa.:

    [6:32pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa: Hakanan a cikin waƙag "Gandon kasah Hausa", shi ma yana yi mai kirari da;

    Na Marahwa Danbaba maihankuri

    Kyautakka hat ta wuce godiya

    Sai dai ace kai muna gahwara

    Usumanu sarkin rikon duniya...

    [7:42pm, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Wannan Zauren tattaunawa ne akan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ɗan Makaɗa Abubakar Kusu mai Kotso ɗan Makaɗa Alu mai Kurya.

    [8:10pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa: "Ban wuce gonata da irina ba

    Inda Sarkin Kudu nits tsaya. "

    * * *

    Ba mu wuce bitam mu da nazarinmu ba nanniya

    Inda Malamin waƙa munka tsaya

    [10:47pm, 12/02/2024] Malama H.M. Kurawa: "Gaba dai ka cira,

    Baya na zuwa,

    Wani bi,

    Wata baya,

    Ta ɗara gaba".

    Amshi: Toron Giwa ɗan Abubakar,

    Maifaru na Macciɗo,

    Ma ci gari.

    [10:50pm, 12/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    "Kowacce maka sai ta kwana,

    Kai ko ce ma shi sai tai yami,

    Ya bar ce maka bai shirya ba".

    Amshi: Dodo mijin maza ɗan Shehu,

    Gagara ƙarya kana ban tsoro,

    Alhaji na Garba, Sarkin Rafi.

    [3:51am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya:/... Mai da aboki baranka./

    Haka Mallamin waƙa ya ce. Ta yaya ne mutum yake sa abokinsa ya zama baranda? Manazarta da masu sha'awar waƙa a wasa ƙwaƙwalwa don Allah!

    [3:51am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A lura da ambaton "Gada" da Sa'idu Faru ya yi cikin wannan waƙa ba garin Gada na wajjen Illela kusa da Jumhiriyar Nijer yake nufi ba. Wannan da Faru ke nufi da ya ce Gada, wani gari ne cikin ƙasar Bunguɗu. Na taɓa zuwa garin har aka nuna mini wani masallaci da aka ce Mallam Abdullahi ɗan Fodiyo ƙanen Shehu Usmanu ne ya nuna wa mutanen garin daidai inda alƙibla take. Ya isa garin ne lokacin da yake kan hanya zuwa aikin Hajji kafin ya isa Kano inda jama'ar Kano suka tsayar da shi har ya rubuta wa Sarkin Kano littafinsa mai suna Diyaul Hukkam. A nan mutanen Kano suka rarrashe shi da ya koma Sakkwato bayan shi ma ya gano cewa abin da ya sa ya baro Sakkwato shi ne cewa har nan Kano akwai shi, wato ɓarna, sai ya yanke shawarar gara ya tsaya ya ci gaba da Jihadin da suka fara. Wasu sun ce yayansa Shehu ya aika da a yi ƙoƙarin da aka rarrashi ƙanen nasa da ya dawo a ci gaba da jaddada Addinin Allah. Allah ne Masani.

    [6:23am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍😁👌🙏 Sarkin Yamman Faru Ibrahim (Mai Abu) ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Abubakar/Bubakar ɗan Sarkin Rwahin Dosara Amadu Mai Dosara ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Alhaji ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi kenan. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [6:24am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Muna ƙara yi wa Allah SWT godiya da ya dawo muna dakai lafiya cikin amincinsa. Allah ya ƙara yi muna kariya daga kowace irin musiba, amin.

    [6:31am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍😁👌🙏.... Akwai Dagatai/Hakimai masu laƙabin Sarautar "Sarkin Rwahi/Sarkin Rafi guda uku dake fittatu a yankin Sakkwato/Zamfara.

    Sarkin Rafin Dosara a Ƙasar Maradun da Sarkin Rafin Bafarawa a Ƙasar Isa da Sarkin Rafin Kuryad Dambo a Ƙasar Shinkafi.

    Wannan Sarkin Rafin Dosara ne daga zuriyar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da ya yi Sarautar Maradun daga shekarar 1870 zuwa wafatinsa a shekarar 1874. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Tambaya anan itace me Malamin Waƙa ke nufi da wannan ɗan Waƙar "Kowacce maka sha ta kwana, kai ko ce mashi sai tai yami?.

    [6:34am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ta hanyar karimci/kyautatawa/mutuntawa/ɗauke nauyin lalurorin wanda/waɗan da yake tare dasu.

    [6:47am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Muna ƙara godiya sosai da ilimin da muke ta kwasa ahaha Allah ya gafarta Malam. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    A wannan wuri ne da ake kira Gada a Ƙasar Bunguɗu ta Jihar Zamfara ta yanzu masu Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya daga Kano suka riski Jagororin Jihadin har ma aka naɗa Malam Sulaimanu a matsayin jagoran masu jihadin na Kano.

    Gada wuri ne na Ribaɗi da ya yi suna sosai, daga nan ne Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya jagoranci jama'arsu zuwa Yaƙin Yandoto.

    Laƙabin Sarautar Gada shi ne "Keku/Kekun Gada". Kekun Gada Muhammadu Ɗantabawa ne Malamin Waƙa ya yi wa wannan Waƙar. Ajinsu ɗaya da Marigayi Mai Girma Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR Turakin Sakkwato da Marigayi Mai Martaba Sarkin Yauri Alhaji Muhammadu Tukur Abdullahi a Middle School ta Sakkwato. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [7:03am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Madallah da wannan bayani. Na ƙaru sosai. Allah Ya saka ma da mafificin alheri duniya da Lahira Hon. amin.

    Abin da ya kai ni Gada shi ne, da ni da abokina muka tafi nemar wa wani abokinmu mata.

    [7:15am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Baban Mai Abu Faru na Mai'akwai,

    Ɗangiwa komi tad daɗe ta tabbata yin Giwa yakai,

    Inji S/Maradun S/Ƙaya"

    [7:53am, 13/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A gabaccin wannan masallacin akwai hubbaren wani Waliyi wanda har yanzu wasu ba su daina ziyayarsa ba, sunan Waliyin shi ne Malam Dembo. An ce daidai inda kansa yake ne wata itaciyar giginya ta fito! Kuma tana nan wurin har yanzu. Allah ya jikan magabatanmu.

    [8:01am, 13/02/2024] +234 803 397 1311: Wacce irin ɓarna ce a Kano a lokacin ? A a adabin Ka kamar an ce ya sami tarayyar ra'ayi da Abdussalam ne ?

    [8:02am, 13/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Na sami labarin cewa har daga wasu kasashen an yi zuwa don ziyarar hubbaren a garin Gada, kuma ni da na taso nikan ga irin wadannan mutanen suna wucewa ta garinmu suna zuwa Gada, ashe su ne masu zuwa Sakkwato hubbaren Shehu Usmanu Danfodiyo suke fara ziyarar a Gada kafin su wuce.

    [8:05am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne, Malam Dembo shahararre ne a Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya.

    [8:57am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Da ma Mallam Abdullahi ya yi niyyar tafiya Hajji ne saboda ya ga mutane (magoya bayan jihadin da suke yi) sun fara barin manufofin jihadi suna komawa ga abubuwan da saboda a kawar da su ne aka ƙaddamar da da jihadin kamar tara dukiya da samun ganima da jin daɗi. Abdullahi ya ga cewa 'yar gidan jiya ce za a koma wa. Saboda haka ya yi niyyar guje ma haka, alhali bai san da cewa ba can inda ya baro ba kurum wannan hali yake ba. Wannan shi nake nufi da "ɓarna". Ka kuwa san jama'ar Kano ba su zama dabam.

    Domin ƙarin bayani sai a duba littafin Mallam Abdullahi mai suna TAZYIN AL WARAƘA. Ya yi bayani dalla-dalla

    [11:36am, 13/02/2024] Prof. B.B. Usman: Malama ko cikin waƙar nan ce ambaci kalmar shege?

    [12:38pm, 13/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    Sarkin yamman Faru Salihu,

    Da isowa tai ya yi lamba wan (one)

    Wani ɗan sarki ya yi lamba tu (two).

    Ga wani Uban ƙasa ya ɓata ƙawa,

    Har na ga Makama

    Ya yi tunzuri,

    Ya ce.. su wuce da shi,

    Dubi wani shegen naɗi da yay yi,

    Mahuta kunnuwa suka biya.

    Maigirma @Mal. I.M. D/Birnin Magaji a taimaka a gyara. 👆

    [1:54pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sannu da ƙoƙari Malama.

    Kina kan hanyarki daidai. 😁😅🙏

    Makaman Doka mai yan doka kenan.

    Sarkin Yamman Faru Salihu shi ya gaji/gadi Sarkin Yamma Ibrahim wanda Sa'idu Faru ya fara Waƙarsa ta farko a wajensa.

    Dukansu daga zuriyar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne. Sarkin Yamma Ibrahim daga gidan Sarkin Ƙaya Alhaj ɗan Sarki Muhammadu Mu'alliyeɗi, shi kuma Sarkin Yamma Salihu daga gidan Sarkin Ƙaya Attahiru/Atto ɗan Muhammadu Mu'alliyeɗi.

    A can baya na ɗora wannan Waƙar akan Sarkin Yamma Ibrahim Abubakar/Bubakar (Mai Abu Faru), daga baya na ƙara fahimtar ba tasa ba ce, ta wanda ya gaje/gade sa ce, wato Sarkin Yamma Salihu Mahaifinsu Sarkin Yamman Faru Bello Ɗan Bello na yanzu. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Sardauna

    [8:18pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora:

    "Ya mirɗe maza yanzu ba mai ƙara ja mai,

    Y/Amshi: Kai ab Bello kai ah Hassan,

    Kai ad da kowa,

    Jagora: Gazagurin gidan Dange...

    Y/Amshi: Duk mai gaba da kai bai

    bakwai bai sha kunu ba,

    Ya mirɗe maza yanzu ba mai ƙara ja mai,

    Kai ab Bello kai ah Hassan,

    Kai ad da kowa,

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa na farko, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Turken Waƙa: Ya mirɗe maza yanzu ba mai ƙara ja mai,

    Kai ab Bello kai ah Hassan,

    Kai ad da kowa.

    YARO

    [8:19pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora:

    S/shaggu ka rabka kuwa,

    Kai taƙamab biri,

    Kuma saki tukkuwa ta wala,

    In na kiɗa kai ko Maba

    tadda gwarzon Sabongari nan dak kwana,

    Kai Magajin busa ka zanki busa,

    Da zamanin ana yaƙi na,

    Jagora/Y/Amshi: Maraɗi da bata kwan ukku,

    In ba aljihun Abu mai saje ba,

    Ginshimin S/fada ɗan Iro na Malan,

    Ubangijin Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Nijeriya, Abubakar Garba.

    Ya yi sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Turken Waƙa: Ginshimin Sarkin fada ɗan Iro na Malan,

    Ubangijin Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.

    [10:42pm, 13/02/2024] +234 802 687 2803: Gaskiya, muna anfana da ilmi, Allah ya saka da mafificin alheri, ya Karo basira.

    [10:44pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sannu da ƙoƙari Malama.

    Ki turo Waƙar ko za a samu waɗan da zasu gano muna abun da suke cewa.

    [10:45pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Kunnuwan Bika.../wani kalar Biri ne.

    [10:46pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka Allah ya gafarta Malam. Muna ta bautag godiya dai, muna ƙaruwa sosai.

    [11:07pm, 13/02/2024] Dr. H. Yelwa: Bika👉🏽Gorilla

    [11:08pm, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A fahimtata yana nufin duk halayen Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da na S/M Hassan duk Sardauna yana da su, saboda haka tamkar dai mulkin da Sardauna ke yi irin nasu ne. Sa'idu Faru ya yi amfani da salon kinaya ne ya ce Sardauna shi ne su, kamar a ce Sale zaki ne ko Amina damisa ce: ai ba ana nufin dabbobin ne ba, sai dai halayen da Hausawa suka san waɗannan dabbobi, zaki da damisa suna da, su ne Sale da Amina suke da > ƙarfi da sarauta; ƙin sabo da take da, da makamantan haka.

    Makamancin wannan salo na kinaya shi ne salon kamance, wanda ke cewa wane kamar wane ne. Salon kamance bai yi cikar salon kinaya ba.

    [11:09pm, 13/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    "Duk mai gaba da kai bai bakwai,

    Bai sha kunu ba".

    Wato an yi ƙasa da martabar kunu ke nan ko kuwa fushi/ɓacin rai ake nufi?

    [11:12pm, 13/02/2024] Dr. H. Yelwa: Danmadami ya amsa tambayat a sama. Kunu a nan, ana nuhin ƙunun gidan yari'. Manuhwa, maigaba dashi bai kwana 7 ba a kaishi gidan yari ba.

    [11:22pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Ya kabre ƙawaw waɗan Gusau/Ya ɗauki hayar ƙawar tawagar Gusau domin ya ƙara birgewa.

    .... Makama ya tunzuri..

    ... Ya ce Yan Nehu sun gama dashi.../kenan wannan taron an yi shi ne a lokacin mulkin Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato yana Firimiyan Jihar Arewa kuma a gabansa aka yi taron/hawan kamar yadda Malamin Waƙa ya ayyana a cikin wannan Waƙar.

    A lokacin duk wanda aka ce baya goyon bayan Jam'iyyar NPC ta Sardaunan musamman wanda ke riƙe da madafun iko irin Dagatai da Hakimai da Sarakuna a Jihar Arewa ya shiga uku, kenan Jam'iyyar Adawa ta NEPU ko AG (Action Group) ya ke goyawa baya.

    Shi wannan Dagaci da Makama ya yi wa tunzuri (Makaman Sakkwato, Alhaji Sani Dingyaɗi kenan. A lokacin Kansila ne babba a Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi) har ma ya ce "Yan NEPU/Yan NEHU sun gama dashi abu biyu ne: ko dai ya biyewa Yan NEPU dake yankinsa har ya zamo bai bi hanyar da ta dace ba (biyar NPC) gashi har ya kasa taɓuka wani abun kirki a irin wannan taron da Jagoran NPC ke halarta, ko kuma daga cikin danginsa akwai masu ra'ayin NEPU da suka yi masa makaru har ya kasance ana ganin laifinsa a hukumance daga gefen gwamnati mai ci a lokacin ta NPC. Allahu Wa'alam!

    [11:44pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Domin ya ce an yi taron ne a Giginya/Filin Wasa/Filin Sukuwa na Sakkwato da aka alaƙanta da Giginya/Iccen Giginyu/Giginyar da Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Attahiru I ya tarbi Turawan Mulkin Mallaka na Ingila a Ranar 15/03/1903.

    [11:53pm, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haka ne Hon.

    Ni da ina da iko da ba za a ƙara yin sukuwa ko wata wasa cikin wannan fili ba. Ina ganin wulakanci ne Turawan Ingila suka dasa muna, muna dirikkowa cikin filin da suka kashe kakanninmu. In su kakannin namu sun yi bisa ga tilas, mu wace hujja muke da yanzu.

    [11:58pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe kamar ba a inda filin sukuwa/sitadiyam suke ba ne filin dagar.

    Daga Dogondaji House zuwa Ƙoramar nan ta Zoolane, zuwa gidan Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa Garkuwan Sakkwato waɗan nan itacen/bishiyoyin suke.

    Kamar Giginya Barracks da Giginya Memorial Teachers College da Giginya Hotel suka ci wannan sunan, haka Filin Sukuwa da Stadium suka samu wannan laƙabi.

    [12:23am, 14/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A gaskiya ba haka na ji ba daga mutanen garin.

    La'akari da cewar akwai ƙorama a wurin da ka yi magana ban zaton a shata filin daga kusa da nan. Ai inda Gidan Gwamnati yake nan ne Turawan suka fara zama, ba su kuwa yin gida a filin da suka ci Sakkwato domin za su yi mu'amala da Sarkin Musulmi da hakimansa, ka kuwa san a kullum suka je gidan Rasdan ko D. O tilas su tuna da nan ne aka karkashe musu jama'a. Sannan ka tuna da cewa a 1903, koma a shekarun 1960, filin giginya nesa ne ƙwarai daga Sakkwato, nan ne ake iya yin yaƙi da Dawaki, yaƙin da kwatsam ya fara domin wasu daga cikin jama'a suna tattalin barin ƙasa ne sai kurum aka ji cewa abokan gaba sun iso, sai aka bar batun tattalin guzurin tafiya aka koma na makamai.

    Watakila sai idan mun kawo hujja a rubuce sannan za mu iya tabbatar da ko kore wannan hasashe. Zan duba littafin Waziri Junaidu mai suna TARIHIN FULANI la'alla in samu haske. Akwai kuma THE SULTANS OF SOKOTO

    [12:31am, 14/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Giginya Barraks da Giginya Memorial Teachers College da Giginya Hotel duk a shekarun 1970 zuwa sama aka yi su.

    Tuno da waƙar Sarkin Taushin Sarkin Katsina ta karɓar mulki ka ji abin da yake cewa.

    Sarki

    [7:52pm, 14/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dr) Rilwanu Adamu a gefen hagu yake gaisawa da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dr) Aminu Ado Bayero. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    Sarkin Musulmi

    [7:53pm, 14/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dr) Aminu Ado Bayero a gefen dama yana gaisawa da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji (Dr) Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    [8:00pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Ban je gidan dan giya niy yi roƙo ba

    Ko ya raba lahira ba ruwana😀

    [8:05pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Na tsinci wata kamanceceniyar zance a tsakanin mawaƙa a waƙar nan. Malamin kiɗa ya ce "Ruwan maliya sun wuce masu taru". Shi kuma Jankiɗi ya ce "an san ruwan da akan shiga ai iyo, kobbi ta maliya ba shi gani waje"

    [8:22pm, 14/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne, sai dai Allah ya gafarta Malam wannan ba talla ba ce.

    Hajar Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ce da ya ambata a matsayin kyautar da Ubangidansa Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya yi masa.

    Da an bi ɗiyan waƙar da ke ƙarƙashin hoton da ake yi wa kallon talla ce, za a tsinci inda yake cewa "Baba ya bamu bandur guda dun na lailai, ya bamu bandur guda dun na Yadi.... har zuwa ƙarshe, ƙila za a fahimci cewa an sako wannan ne domin a nusar damu cewa ga irin bandur nan na Yadi da yake nufin Sarkin Kudu ya ba shi.

    A daina yanke hukunci ba tare da an bibiyi saƙonnin ba.

    [8:23pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa: A cikin waƙar an yi maganar bandir na yadi, shine aka sanya don ya zama ya ƙara hasken fahimta da ƙara nishadin nazarin diyan waƙar

    [8:26pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Maigirma Danmadani da sauran malamai suna yin hakan domin ya zama haske ko dogaro wajen kawo diyan waƙa. Misali akan sanya hoton riga babba mai tsada don ayi ishara ga diyan waƙa dake maganar kyautar kaya ko kyankyandi da makamantan su.

    [8:32pm, 14/02/2024] Prof. B.B. Usman: Ni ina ganin bandir_bandir ɗin na fahimci amfaninsu a wajen gane saƙon cikin waƙar. Allah ya ƙara basira don tsarkin sunayensa.

    [8:34pm, 14/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    Ban je gidan ɗan giya,

    Niy yi riƙo ba,

    Ko ya raba lahiya,

    Ba ruwana

    Ban je gidan ɗan bita,

    [8:35pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Allah shi gafarta Malama, ina ganin ko yana maganar "yan bita" ne. Watau ma'aikatan Fidaburdi na da?

    [8:36pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Tooo, lahiya ce yake nufi a nan ba lahira ba. Angode da bayani Ma🙏😀

    [8:43pm, 14/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Haka ne, an yi bayani kwanaki, ina zaton ranar Malam bai samu gani ba.

    [9:11pm, 14/02/2024] Mal. Habibu Kaura: Assalamu alaikum. Dangade da kalmar ɗan bita. Ina tsammanin masu aikin godabe/titi/hanya na mota ko jirgin kasa.

    [9:20pm, 14/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ina ganin an walwale wannan matsala. Ɗan giya Sa'idu Faru ki nufi. Zambo ne yake yi wa wani da nufin mutumin ɗan giya ne, to me maroƙi kamar Sa'idu zai yi da zuwa roƙo gidan ɗan giya tun da giya ce kurum zai ba shi, giya kuwa haramun ce ga Musulmi

    Gari

    [11:53pm, 15/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Mu koma Ƙaura ga ɗan Isau in aza kaya na", inji Makaɗa Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Marigayi Mai Girma Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba mai amshi ' Gwabron Giwa na Shamaki baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daga'. A wannan wuri ne Malam Muhammadu Namoda ya kafa Bukkarsa dake nuna ƙirƙirar Garin Ƙauran Namoda a cikin shekarar 1807. Ya zuwa yanzu a wannan wurin ne Fadar Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda take. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Masa'udun Kauran Namoda

    [12:07am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Na zaka in gaka in yi mubayi'a, Masa'udun Ƙaura Amadu" inji Mai kwana ɗumi na Mamman da Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru a faifan da ya yi wa Marigayi Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Muhammad Asha (ya yi Sarauta daga shekarar 1960 zuwa rasuwarsa a shekarar 2004) mai amshi 'Na Magaji Ƙanen Sarkin Ƙaya, Shugaban Alibawa Amadu'. Wannan shi ne Marigayi Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Muhammad Asha, Allah ya kyauta makwanci, amin. 🤲🏾🤲🏾🤲🏾

    [12:11am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Na taɓa zuwa Ƙaurar Maida har Fadarsa na yi gaisuwa

    [12:18am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allahu Akbar!!! Akwai Hubbaren Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ummaru Ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami Ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a fadar Ƙaura Namoda.

    Anan Allah SWT ya yi masa wafati a shekarar 1891. Anan kuma aka naɗa wanda ya gaje/gade shi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abdulrahaman da aka fi sani da Ɗanyen Kasko. Allah ya jiƙan su da rahama su da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [12:20am, 16/02/2024] +234 803 639 8040: Amin ya Hayyu ya Ƙayyum.

    Takalma

    [12:28am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Ƙwahak Kuturu mutuncinta takalmi, radda dub bai dasu ba ya jin sosai" inji Malamin Waƙa a faifansa na Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar Gundumar Talata Mafara, Sarkin Gabas Alhaji Shehu Muhammadu Ɗangwaggo mai amshi 'Ƙi garaje Uban Shamaki Shehu, ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro'. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [6:48am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Za a same ta In Shaa Allah Allah ya gafarta Malam 🙏🙏🙏

    [6:49am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Ana ta tsoron ka

    kai ba ka jin tsoro,

    Baba halin Abu kay yi mai Raɓah.

    [6:49am, 16/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi: A taimaka min Hon! Shin ba ya Jin sosai yake ko ba ya Jin daidai?

    [6:51am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ma'anar ɗaya ce, wajen zaɓen kalmar ce ya nuna ƙwarewa.

    [6:52am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Gadan-gadan kay yi uban Zagi Buba,

    Usumanu ka hau halifag gadon Moyi..

    [6:58am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Allah sa wani zai fito mana da wata muƙala da ke baje falsafar Hausawa cikin waƙoƙin Mallamin Waƙa Sa'idu Faru.

    [7:01am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Karen masara daɗai ba ya yin gyamro,

    Yaushe talakka ka haihwa ɗan Sarki,

    Bunsuru ba ya yin layya ga Rago.

    [7:05am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Ƙi garaje Uban Shamaki Shehu,

    Ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro.

    [7:06am, 16/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi: *yaushe talakka ka haihuwar Sarki, kamar Karin waƙar ya kare, idan an ce "yaushe talakka ka haihuwar Dan Sarki" Prof. A. B da Prof. Dunfawa ku agaza muna.

    [7:06am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo kenan. Ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya yi sarauta daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969 sanadiyar gobara.

    Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya yi Hakimci a Talata Mafara kafin a kawo Sarkin Gabas Shehu. Shi ya zo a shekarar 1953 zuwa 1956.  Bayan ya tashi sai aka kawo Marafan Gada Aliyu, ya shekara biyu 1956 zuwa 1958.

    [7:11am, 16/02/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: ALHAMDULILLAH, rankai dade. Muna karfe 1:10 na dare.. ku yini lahiya mu kuma mu kwana lahiya

    [7:11am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A kullum ina tunanin cewa cikin karin magana ne Baushe ya sha adana falsarsa. Da kuma manazarta suna mai da hankulasu a nan da sun taimaka wa ɗalibai daidaita bincikensu, ga ɗora shi kan ra'o'i marasa dangantaka da rayuwar Hausawa, ko mu samu mu kuɓuce daga ƙangin Turawa.

    [7:13am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Daga nan sai Sarkin Gabas Shehu zuwa 1969. Sai Sarkin Gabas Mu'azu Lamiɗo ɗan Sarkin Musulmi Hassan ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio har zuwa 1975/76 lokacin da sarautar ta dawo gidan Zamfarawa/Gidan ta na asali aka naɗa Muhammadu Barmo ɗan Sarkin Mafara Aliyu. Bayan ya rasu a Shekarar 1996 sai aka naɗa ɗansa Alhaji Bello Muhammad Barmo OON, Sarki mai ci yanzu.

    [7:16am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kafin zuwan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a Mafara, Mahaifinsa Sarkin Musulmi Abubakar III ya yi Hakimci a Mafara na 'yan watanni da laƙabin Sarautarsa ta Sardaunan Sakkwato a cikin 1938 gab da ya zama Sarkin Musulmi.

    [7:18am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Bayan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ya zama Sarkin Musulmi a watan Afrilu na shekarar 1996 babban aikin da ya fara aiwatarwa shi ne naɗin Sarkin Mafara, Talata Mafara Alhaji Bello Muhammad Barmo OON da Sarkin Ɓurmin Moriki Alhaji Sama'ila Muhammad Ari II.

    [7:20am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Sannu da ƙoƙari Yallabai na fiddo tarihin da ke lunke a cikin wakokin Malamin Kida. Lallai duk idan aka bi diyan wakokin shi to, za a dace da samun bayanai na tarihi kamar yadda Maigirma Danmadani yake ƙoƙari ainun wajen fiddo su. Hakan shine gishirin fahimtar wakokin a yayin nazarin su, domin an bude ma mutum su a fili an maida su kamar film yana kallon duk yadda akayi.

    [7:24am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Malam Yusufu Yunusa da kuma Dokta Hadiza Sa'idu Koko sun tattara karin maganganu da yawa tare da bayanai masu kyawo. Ana iya zurfafa bincike a kan wannan tunani na Falsafar Mallam Bahaushe

    [7:24am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Yawancin duk garuruwan da yan Sarki ke mulkin su a Sokoto, wanda kuma kusan duk Sa'idu ya wake su, T/Mafara ce nike ganin a mayar da ita ga ainihin wanda suka fara mulkin ta. Ita Kuma sai ina zaton haka ya faru saboda ba da karfi aka amshi mulkin ba. Duk da sunyi bore a wani lokaci dab da zuwan Turawa, hakan bai sanya an dauke su ba a matsayin wanda aka sauya mulkin su ba karfin takobi.

    [7:26am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Gusau ma an mayar da sarauta a gidanta na asali a shekarar 1984 lokacin da aka naɗa Alhaji Muhammadu Kabir Ɗanbaba OFR.

    [7:27am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Haka ne Yallabai, duk da daman ita ta Mallam Sambo ce kuma shi ma duk mujahidi ne.

    [7:27am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ɗansadau ta sake komawa ruwa a cikin shekarar 2022 bayan an cire Sarkin Kudu Husaini Umar.

    [7:28am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne sai dai ba bani Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ba ne, ɗan Malam Muhammadu Ashafa ne, Bafulatanin Yandoto.

    [7:30am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Haka fa Yallabai. Ko Saidu ya yi ma su waƙa kuwa. Ina nufin irin su Muhammadu Maiakwai da Sarki Kabiru. Nasan dai Jankiɗi ya yi ma Maiakwai wakoki masu daɗi, to ban san Saidu ba.

    [7:34am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sa'idu bai shiga Fadar Gusau ba, sai ya wuce zuwa Ƙaura Namoda da Zurmi da Gabake da Birnin Magaji da Banga da Isa da Sabon Birni da Bafarawa.

    [7:35am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa: Ranka ya dade lallai Saidu yana da basirar da idan aka bibiyi wakokin shi daga janibin Falsafar Bahaushe, za a samu abubuwa da yawo. ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo irin wadannan karin magana da yin kamanceceniya wajen fidda bayanai masu dauke da ma'anoni. Misali a waƙar "Abubakar na Ahmadu baban Galadima.. " inda yake maganar namun daji da kalar su da dabi'un su.

    [1:17pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Ina cikin daji sai Gyado ka saƙƙwata ta....

    [1:50pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: In an samu waƙac can ta Dan-Alin Birnin Magaji a turo muna.

    Sarkin Sudan Na Wurno

    [8:15am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Sarkin Sudan na Wurno Zaki,

    Y/Amshi: Sarkin Sudan na Wurno Zaki,

    Gogarma Shehu na Ali

    Muzakkarin Sarki ɗan Abdu,

    Abun biya Shehu na Ali

    Jagora: Shehun gidan Hassan ɗan Mu'azu,

    Y/Amshi: Katakoron Matawalle,

    Jagora: Don kasan sai an ci Talata,

    Y/Amshi: San nan Larba ka isowa

    Muzakkarin Sarki ɗan Abdu,

    Abun biya Shehu na Ali

    Marigayi Mai Girma Sarkin Sudan Na Wurno, Alhaji Shehu Malami ɗan Sarkin Sudan Na Wurno Bello ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya zama Sarkin Sudan Na Wurno a shekarar 1973 har zuwa shekarar 1989 da ya yi murabus na ƙashin kansa. Ya rasu a ranar 20 ga watan Disambar 2022. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Doki

    [8:15am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Mu'azu kullun mahwalki ni kai sabo,

    Y/Amshi: Shehu ya ba mu doki da kaya nai,

    Jagora: Daudu kullun mahwalki ni kai sabo,

    Y/Amshi: Shehu ya bamu doki da kaya nai,

    Danda hwari biyat wanda an nan haka,

    Inda Liman ka bi zai Masallaci,

    Koma shirin daga na Muhamman Bello,

    Shehu ɗan Shehu ganɗon ƙasah hausa,

    Wannan Dokin shi ne ake kira Danda Fari biyar domin farin da ke ƙafafunsa duka guda 4 da farin dake a goshinsa. Wani kuma bayan fari a ƙafafunsa ana iya samun fari a cikinsa a maimakon fari a goshinsa.

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai girma Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo waɗannan ɗiyan Waƙar suke. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [9:20am, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: A nan Saidu Faru ya hwara da kawo tunanenai na dokin da yad dace a ba shi.

    Danwaƙad da yab biyo shi, shine na rokon dokin karara, tare da nuna cewa doki ne wanda duw wani karamin sarki bai yarda ya bayad dashi.

    "Doki nika so Baban Majidadi baban kanwa na kilisas swahe

    Shi Hakimin kauye ab bai iya kyauta

    In ya samai sai bargatai

    Hay yasa hannuwa yai ta shahwatai. "

    Dud dai don dokin ya hito, sai yat tunzura Sarkin da cewa;

    "Manyan kaya manyan ganwo

    Sarki shi aka roƙo doki

    Kyakyautani uban Majidadi

    In bada tsoro ga kauyenmu in nazo. "

    [9:25am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍😁👌🙏... Cimcintani Uban Majidadi..../kyauta asin da asin/kamalalliyar kyauta da ba abar komai a gefe ba.

    [9:35am, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: At! 'Cimcimtani'. 👆🏽😄

    Hausa ba dabo ba. Madallah da wanga gyara Onorabul.

    Da hwatab babu lauje cikin nadi ga maganatai ta Hakimin kauye bai iya kyautad doki da kuma abinda yab biyo baya cewa a cimcimtashi ya bada tsoro ga kauyensu in yazo.

    [10:23am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ai a cikin wani Version na Bakandamiya/Baba Uban Gandu ya yi nadamar fara roƙo a Ƙauye. Ya ma faɗi cewa ƙurciya ce ta ci su har suka ɓata lokacinsu can baya wajen roƙon Sarakunan Ƙauye, ga inda ake kyautar ƙasaita ba su gano ba sai daga baya.

    [10:28am, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: A waƙar Turakin dan Hashim Jikan Dabo Bangon Dutsi, Dankwairo ya ce:

    "Kowa ya kuka da arziki nai

    Da ƙauye da birni dud ɗai ne

    In Allah Ya sauwaƙa ma"🤷‍♂️😬

    [1:13pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa. Saboda, ba ga wagga waƙab ba kaɗai, Saidu ya hwa rena hakiman kauye. Ƙilan hwa da azazza. Ji nan;👇🏽

    "Maibiyas sarkin kauye wawa na

    Shi miyac ci bi zashi ba taro

    Yak kasatai kwatancin ta Garbadu. "

    [1:16pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka hwa yac ce Mai Girma Waziri.

    A cikin Waƙar Ɗan Alin Birnin Magaji Muhammadu Mode Usman kuma yana cewa "Ɗaukan ni ka goya Ɗan Korau, don kada kabab baƙauye ya wahalsan".

    [1:17pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Ina cikin daji sai Gyado ka saƙƙwata ta....

    "Daudu da duy yag ganan ya buɗek ke haƙori...

    "Abun biya kake ɗan Shehu,

    Alhaji Ɗan Ali ci fansa.

    Shi ne ☝️amshin Waƙar.

    Ya zo da ita Birnin Magaji a cikin late 1970s.

    [1:49pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa. Ka ga hasashen nan na azazza da hakimin kauye yana ta hitowa.

    [1:50pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: In an samu waƙac can ta Dan-Alin Birnin Magaji a turo muna.

    [1:54pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A keɓance Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru ya sheda mani cewa dara ce ta ci gida a wannan karon.

    Akwai wani ɗan yamutsi da Malamin waƙa ya yi da maigarin nasu sai aka taskace shi a wannan Waƙar.

    [1:56pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: Rankaidade wai me yasa bakandamiyar Sa'idu ba ta yadu sosai kamar sauran manyan wakokin shi ba?

    [2:02pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Nima na lura da hakan duk da yake na kasa sanin dalili Mai Girma Ɗanmaliki.

    [2:18pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: Mhn! Ni hwa na san 'ruwa ba su tsami banza'.

    [2:27pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: Ko ya riga yin wadancan manyan wakokin ne, kafin ya yi ta?

    [2:34pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ita ma ta daɗe domin ya yi ta tsakanin 1952 ne zuwa 1960.

    [2:35pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: Wai-wai. Lallai tsohon bugu ne.

    [2:40pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: Na samu labari ashe a cikin tawagar Sa'idu akwai wani yayan shi. Shi ba ya qarin waƙa.

    [6:16pm, 18/02/2024] +234 706 685 1000: Don Allah Sa'idu Faru yana da Diya da Jikoki a raye? Idan akwai su, suna waƙa da kida?

    [8:38pm, 18/02/2024] www.amsoshi.com: Ire-iren waɗannan tambayoyi na da matuƙar muhimmanci. Duk masu bincike kan Makaɗa Sa'idu Faru na iya turo tambaya kan wani lamari da ya shige musu duhu. Insha Allah malamai da dama da ke cikin wannan zaure a shirye suke da su ci gaba da ba da gudummawa wajen ilimantar da mu.

    Bannan burinmu shi ne, kowace takarda ta zo da cikakken inganci yayin wannan taro. Wannan gata ce gare mu.

    Samun bayanai kyauta🕺

    Samun interviewees kyauta 💃🤪

    [8:39pm, 18/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: yana da ɗiya da jikoki maza da mata suna nan raye. Wasu a Faru, wasu kuma a wasu garuruwan.

    Alhaji Ibrahim Sa'idu Faru wanda ɗansa ne mai kimanin shekaru 65/66/67 a duniya shi ke jagorantar tawagar Kiɗa da Waƙa ta gidan Marigayi Makaɗa Sa'idu Faru.

    In Shaa Allahu zai halarci wannan Taro namu da muke tattaunawa akai.

    [8:46pm, 18/02/2024] Malama H.M. Kurawa: ".. Uban Tudu,

    Sarkin ɗaukar taro". In ji Sa'idu Faru.

    In Allah ya so wannan 'take' FUG za a yi wa shi. 🙏

    [9:04pm, 18/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka hwa yac ce Allah ya gafarta Malama!

    Lalle FUGUSAU ta zama "Sarkin/Sarauniyar ɗaukar Taro😁🙏

    [9:17pm, 18/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haka ya faru ne domin, aƙalla ni dai, a ja hankalinku masu shiryawa cewa ana iya kawo muku cikas daga waɗanda ke adawa da ƙudurinku.

    [9:24pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: Akwai wani matashi a wancan lokacin da ya kan karbi waƙa in ana yi a cikin tawagat ta Saidu Faru.

    A cikin wata waƙas Sarkin Kudu Maccido yana cewa;

    "... Wani 'andizarabul elemen' (undesirable element) sai yas soke motat

    Motan nan da za a bani

    Na barma kaba ubanka. "

    Ko shine a' Ibrahim din maijagorantat tawagat a yanzu?

    [9:31pm, 18/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Shi ne fa Maigirma Waziri. A can in the background zaka ji Malamin Waƙa yana cewa "A gaishe ka Malan Ibrahim" a cikin wasu Waƙoƙinsa inda shi Alhaji Ibrahim ke ƙari.

    [9:42pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa, Onorabul Danmadami.

    Lallai ni kan jishi yana kawo kalmomin turanci;

    ".. Emiret kaunsil (Emirate Council) ta shirya babban taro

    Kuma tayi kiran 'yansarki

    Su kau sun karba kiranta

    Wani tandarkin bakauye

    Yac ce masu bai tahowa".

    Makada

    [9:46pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: 👆🏽Wasu daga cikin tawagas Saidu Faru.

    [9:47pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: Na 3 daga dama: Malamin waƙa

    Na ‘2 daga dama: Muazu

    [3:12pm, 19/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Harshen Hausa yana samun sauye-sauye saboda dalilai da dama. Wasu daga cikin waɗannan sauye-sauyen tubarkalla ne, wasu kuwa gara/... a ba dillaliya/, in ji mawaƙi Alhaji Garba Gwandu.

    Daga cikin waɗanda suke gara a ba dillaliya akwai "tawaga". Sauyin da aka samu, musamman daga 'yan jarida, shi ne na ma'ana, watakila saboda a yau an daina yaƙi da dawaki. A da da ake yaƙi a kan dawaki da takobi da masu, idan wata ƙungiyar yaƙi ta al'umma ɗaya ta tsere wa ƙungiyar abokan gaba saboda an fi ƙarfinta, wannan ita ake kira "tawaga". Wato ɓangaren rundunar yaƙi da ya fashe. To amma yau sai ma'anar tawaga ta sauya zuwa daidai da "ƙungiya". Misali, yadda aka kira mutanen nan na cikin hoto.

    [3:58pm, 19/02/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Akwai diyanshi da jikokinsa a garin faru dake karamar hukumar mulki ta maradun, jihar zamfara.

    Takanas daga nan Jihar Marland na yi waya da wani dan sa..

    Damusa

    [9:40am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim Muhammad: "Muhammadu Bello jan damishi ɗan Abdu Jatau" inji Sa'idu Faru a waƙarsa mai turke 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai ' ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun/Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III. Muhammad Bello ne sunansa na yanka, Macciɗo alkunya/laƙabi ne, Abdu Jatau Sardaunan Sakkwato kenan kafin a naɗa Sarkin Musulmi Abubakar III wannan sarauta ta Sardauna wacce shi kuma ya baiwa Sir Ahmadu Bello ita a shekarar 1938 da ya zama Sarkin Musulmi. Abdu Jatau tare suka yi neman sarautar Sarkin Musulmi da Abubakar III da Sir Ahmadu Bello da Sarkin Gobir na Isa Amadu I (Amadu Bawa)maigidan Makada Narambada da Sarkin Kudun Sifawa Muhammadu. Abdu Jatau ya riƙe sarautar Sarkin Gobir na Gwadabawa bayan ya bar sarautar Sardauna. Ya fito ne daga gidan Sarkin Musulmi Abubakar I (Abubakar Atiku/Mai Katuru) ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio.

    [9:44am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim Muhammad: *Sarkin Musulmi Abubakar III ya fito daga gidan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ne. Sir Ahmadu Bello ya fito daga gidan Sarkin Musulmi Abubakar II (Abubakar Mai Raɓah) ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio.

    Sarkin Gobir na Isa Amadu I/Amadu Bawa ya fito ne daga gidan Sarkin Musulmi Aliyu ƙarami ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio. Shi kuma Sarkin Kudun Sifawa Muhammadu ya fito ne daga gidan Malam Muhammadu Buhari ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio. Allah ya kyauta makwancinsu su da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [10:24am, 20/02/2024] +234 706 685 1000: Ko Sa'idu Faru ya yi zurfi a cikin ilimin boko dana muhammadiya?

    [10:32am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim Muhammad: Bai yi karatun boko ba, karatun muhammadiya kuma ya yi gwargwadon hali.

    [11:11am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim Muhammad: *Ya faɗa a wata hira da Malam Hamza Sanusi Funtua ya yi dashi a wani shiri mai suna "Daga bakin mai ita" a gidan rediyon gwamnatin Jihar Kaduna (KSMC na yanzu), ranar 15/8/1970 cewa tun bai fara saka bante/bance ba mahaifinsa ya fara fita dashi zuwa sabgar kiɗa da waƙa.

    Ya ce ya kan aza shi akan dokinsa idan zasu fita wajen wannan sabgar. Wasu lokutan yana amshin waƙa yana gyangyaɗi sai mahaifin nasa ya ɗan dangware shi sai ya farka ya ci gaba. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Doki

    [8:37pm, 21/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu. Yan Uwa barkanmu da warhaka, don Allah ko ya sunan wannan Dokin?

    [8:46pm, 21/02/2024]: Assalamualaikum yaa ku jama'ar wannan zaure mai albarka, Ina ƙara godiya bisa dinbin ilmoma nafede waƙaoki da kuma bayyana muna hikimomin mawaƙan Hausa.

    Bayan wannan ga wata tambaya a man fassara: minene fassarar wadannan kalmomi: 1metaphor 2 personification 3 Irony, 5Hyperbol (exerggeration)? na yi wannan tambaya be saboda na ga suna da alaka da sharhin wakoki ko rubutattu ko na baka. Ina sauraronku yaa ku Malamai na da sauran masana a cikin wanna zaure mai tare da ma'ilmanta da kuma manazarta.

    [8:56pm, 21/02/2024] Prof. B.B. Usman: 1. Siffantawa/kinaya metaphor 2. Mutuntarwa personification 3. Irony......... 4 Kambamar zulaƙe hyperbole. A yi mana gyaran fassarar.

    [9:16pm, 21/02/2024] +234 803 257 6475: Ina godiya Drs and Profs. Allah Ya karama rayuwarku albarka Mai tarin yawa.

    [10:18pm, 21/02/2024] Prof. A.B. Yahya: (3) irony > habaici/gatse.

    Wadannan kalmomi biyu su ne masana suka bayar. Sai dai ni ba da alfahari ba ne fi yarda da kalma ta biyu, wato gatse.

    A duba Bargery, sh. 372, da sh. 1188; Muhammad, sh. 27.

    Duk fassarar da Prof. B. B. Usman ya bayar ta yi muwafaƙa da ta manyan malamai, Ɗalhatu Muhammad da ɗalibinsa Abdulƙadir Ɗangambo a nazarin waƙa da ma adabi gaba ɗaya.

    Tuni "kambamar zulaƙe" ta samu takwara tsakankanin manazarta, wato "kambamawa" kai tsaye.

    [4:21am, 22/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora: Yaro in taƙamas salon

    magana kaka yi ce tsare tsara

    Y/Amshi: Tahi tsantsame tsantsara ka tsantsame tsari tsab ga tsamiya

    Jagora: Yaro in taƙamas salon magana kaka yi ce tsare tsara

    Jagora/Y/Amshi: Tahi tsantsame tsantsara ka tsantsame tsari tsab ga tsamiya

    Jagora: Tunkuɗa tunku cikin tukar rukuɓu tukuɗin Tumba yai tuɓus

    Y/Amshi: Tumba taho yau dake da Taɓo da Taɓus da 'Yat Tuɓus

    Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,

    Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi

    [3:50pm, 22/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Waƙar Makaɗa Sa'idu Faru ta farko bayan ya fara jagorancin Ƙungiyar Kiɗa da waƙa ta gidansu.

    Dagacin Ƙauyensu (Faru), Sarkin Yamman Faru Ibrahim Abubakar ne ya yi wa ita. ☝️

    [4:01pm, 22/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Alhamdulillahi wallahi na yi neman waƙar nan, har na gaji Na so ayi tsokaci, a kan salon kiɗan, don ya yi kama da bandiri/mandiri. Ya bambanta da amon kiɗansa. Ni dai har rangaji nake yi.

    [4:06pm, 22/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    "Sarkin yamma,

    Inai maka hwata,

    Ya Allah ya yi ma 'Tabaruka',

    Don girman lawalli da risala,

    Don hasken yassin da muƙama. "

    Wannan ta sa na tuna da Narambaɗa mai "Tabarukin sarki".

    [4:15pm, 22/02/2024] Malama H.M. Kurawa: To amma ma'anar Tabaruka a waƙar Narambaɗa, an ce tana nufin ƙyautar tuɓe', wato nan take sarki ya shiga ya cire tufafin dake jikinsa, ya bawa maroƙi shi kuma ya saka. Ya samu albarkar gumin sarki.

    To amma anan haka Faru yake nufi? 🙏

    [5:40pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya: "... har rangaji nake yi"

    Wannan shaida ce cewa waƙar tana a mataki na ɗaya na kyawo, aƙalla wajenki. Sa'idu Faru ya fara da ƙafar dama

    [6:33pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Salon ƙarangiya > jejjera kalmomi ko furuci cikin waƙa da ke da wuyar faɗi, kuma wani lokaci akwai ma'ana, wani lokaci babu ma'ana.

    Manufa dai ita ce mutum ya iya furtawa cikin sauri ba tare da kuskure ba ko ƙagewa ba.

    [6:35pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A lura da cewa akwai ɓangaren adabin da ake kira gagara-gwari. Shi ma akan sanya shi cikin waƙa. Ɓangare ne na Adabin Hausa

    [9:20pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Dr Bunguɗu ba haka ne ba. Ai kalmomin Larabci suna da yawa cikin Harshen Hausa. Sai kuwa in cire su za mu yi sai mu koma ga Hausa tsintsa. To kuma ka lura da cewa akwai kalmomin Ingilishi da Yarbanci da ma na wasu da ban faɗi ba da dama cikin Hausa.

    Idan kuwa har muka yi haka nan to Harshen Hausa zai mutu. Mafita ita ce a yi aiki da hankali da natsuwa.

    [11:30pm, 22/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haka ne Malam, ai na dauka saboda asalin nazarin rubutacciyar waƙar Hausa an yi amfani da salo ko hanyoyin Larabawa ne don haka tun na wakokin baka namu ne sai aka samar mana wata hanyar daban, a ciki har da yunkurin a samar mana da sunayen kamar baiti zuwa da ko baitoci zuwa diya. Amma yanzu na fahimta cewa ba hakan take ba, na karu da wannan ina godiya, Allah ya ƙara hasken makaranta.

    [7:00am, 23/02/2024]: Haka ne Allah gafarta Malam, Fannin nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa su ke6anta da kalmar ɓaiti’. Haka kuma, hanyar nazarin waƙoƙin baka su ke6anta da kalmar ‘ ɗa ’.

    Makaxan baka na Hausa ne suka fara ba da haske a kan kiran gun-gun saɗaru ko layuka a woƙoƙinsu a matsayin ɗa. Alal misali, Makaɗa Sa’idu Faru yana faɗa a cikin wani ɗan waƙa a waƙar Muhammad Tukur Sarkin Yawuri, inda yake cewa:

    Jagora: Ga waƙa nan wadda nay

    : yi maka,

    Y/Amshi: ɗa Tara ta mun bar

    : takwas gida,

    : Sai in kai murnar zakkuwanmu,

    : In aika ko yanzu su taho,

    : Mu ka kiɗi mu ak kiɗi sabod mu,

    : Allah yay yi wa gudummawa,

    : Da waƙa ga wata na ije wata.

     

    [7:48am, 23/02/2024] Malama H.M. Kurawa: @~MUSA KANO❤️❤️❤️ daga ɗan waƙar da ka kawo:

    "Ga waƙa nan,

    Wadda niy yi ma,

    Guda Tara ta,

    Mun bat takwas gida... "

    Ta nuna waƙa makaɗin yake magana ba ɗan waƙa ba. Kenan kalmar 'ɗa' a nan ba ta wakiltar saɗara ko layukan waƙa. Shi ne abin da Prof. yake so a dandaƙe. 🙏

    [8:54am, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla Malam Musa, sannu da ƙoƙari. Allah ya saka da alheri, amin.

    Kamar Malamin waƙa yana nufin waƙoƙi ne ya yi wa Marigayi mai martaba Sarkin Yawuri, Alhaji Muhammadu Tukur Abdullahi har guda tara, ya taho masa da guda ɗaya (wannan kenan inda aka ɗebo waɗan nan ɗiyan waƙar da aka bayar da wannan misali ☝️). Ya baro guda takwas (daga cikin waƙoƙin guda tara da ya ce ya yi masa a gida) idan ya ji daɗin yadda aka yi masa ta hanyar kyautatawa kuma aka yi murna da zuwan nasa sai ya aika gida sauran guda takwas ɗin su same shi a Yawuri ya zube masa su duka.

    Abin lura anan shi ne hikimarsa ce a fagen Kiɗa da waƙa ya ke so ya bayyanawa al'umma. Saboda hikimar da Allah ya yi masa yana iya yin Waƙa/Waƙoƙi masu yawan gaske a kowane lokaci ya ga damar yin haka muddin akwai yanayi mai kyau da zai sanya yin hakan. Allahu Wa'alam!

    [9:08am, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Malam Idris Garba Zaria muna godiya, a wayata wannan Waƙar ba ta yi.

    Waƙar Alhaji Umaru ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Tambari ce da aka fi sani da suna Bala/Balarabe. A lokacin bikin auren Bala/Balaraben ne aka yi wannan Waƙar.

    Alhaji Umaru Bala/Balarabe shi ne Babban Uban Ƙasar/Babban Hakimin/Senior District Head na Masarautar Maradun dake Jihar Zamfara. Laƙabin sarautarsa shi ne Sarkin Arewa/Sarkin Arewan Maradun. Ƙane ya ke ga Mai martaba Sarkin Ƙayan Maradun, Alhaji Garba Muhammad Tambari MFR na yanzu, Mahaifinsu ɗaya, Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Tambari ɗan Amadu ɗan Sarki ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Attahiru/Atto ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    Dalilin samuwar laƙabin Sarautar Sarkin Arewa a Masarautar Maradun shi ne kafin zuwan Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a wannan yanki na Maradun har ya zamo Sarki a shekarar 1870 zuwa wafatinsa a shekarar 1874, ya zauni wani yanki a cikin Ƙasar Azbin (a Jamhuriyar Nijar ta yau), ya yi sarauta a yankin da laƙabin Sarkin Arewa.

    Bayan zuwansa wannan yanki na Ƙaya/Maradun ne zuriyarsa suka ga muhimmancin taskace tarihin wancan mulki da ya yi a yankin Azbin ta hanyar farfaɗo da wannan sarauta tasa ta Sarkin Arewa da ya riƙa a can. Allahu Wa'alam!

    [9:23am, 23/02/2024] +2348161747863: Ba ina nufin kai tsaye da Sa’idu Faru yana nufin turke ba a wannan ɗan waƙa nasa, wannan ya sa na ce, makadan baka ne suka fara ba da haske. Ma’ana, Gusau ne ya kawo kalmar turke maimaikon jigo, kamar yadda Shehin Malaminmu ya fada. Gusau yakan yi amfani da wasu kalmomin da makada suke amfani da su ya kuma samar da wata ma’ana a fannin waƙar baka. Alal misali, idan aka duba Ma’anar waƙar baka da Gusau ya kawo (2003), za a ga daga kalmomin Musa Dankwairo ya curo su ya kuma samar da ma’anar waƙar baka da su. A nan, Dankwairo ne ya ba da haske ta ma’anar waƙar baka, shi kuma Gusau ya yi amfani da ilimi wajen samar da ma’anar. Allah ya sa Malama ta fahimci bayani.

    [10:35am, 23/02/2024] Malama. S.S. Labbo: Assalamu alaikum iyayena Ina muku fatan alheri. Don Allah Ina da tambaya, a cikin wakokin Sa'idu Faru akwai in da yake magana akan Mata? Ina godiya da fatan alheri ga shehunnan malamai, Allah ya ƙara muku basira da daukaka. Amin

    [11:04am, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaiki Salam Warahamatullah Wabarakatuhu Malama Shafaatu Salihu labbo. Madalla da wannan tambaya mai muhimmanci.

    Wace irin magana kike nufi?

    [3:08pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle kam. Don na san da yake mawaƙin sarauta ne sarakuna mata babu su lokacinsa da ma yanzu. Sai dai in ta kama mawaƙin bai rasa ambaton su kamar ya yaba matar sarki ko jakadiyarsa ko ya yi wa wani ɗan sarki zambo da wani hali ko ɗabi'a ta mata

    Amma dai Hon Ɗanmadamin Birnin Magaji shi ya fi cancanta da amsa tambayar domin ga shi nan har ya fara

    [3:10pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe a wajen bindiga wa ne kestu!

    [3:13pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ai kuwa akan samu garwashi a masaƙa a rasa a maƙera in ji Aliyu Ɗndawo, Hon

    [3:28pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A iya nawa ɗan gajeren nazari akan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba na samu mace ɗaya wadda ya yi wa waƙa mai zaman kanta. Ita ce Marigayiya mai girma mai babban ɗakin Kano, mahaifiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero, Hajiya Hasiya/Asiya Bayero, Allah ya jiƙan su da rahama, amin.

    Amma fa ba na ce babu wasu matan da ya yi wa Waƙa/Waƙoƙi ba ne, ni dai anan allo na ya tsaya.

    Ya ambaci mata a Waƙoƙinsa daban daban domin alheri/kyautatawa zuwa gareshi, wasu kuma saboda dangantakarsu da uwayen gidansa.

    A cikin Waƙarsa ta Marigayi Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba mai amshi " Ubangijin Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.... yana cewa " Ikka/Gwamma da kar riƙe Uban Luba.../duk da yake ban san yadda dangantakar ta take da Sarkin Kiyawa Abubakar Garba ba, anan dai ga sunan mace ya bayyana a cikin wannan Waƙar.

    ... Na gode Uwargida Dije/Maishanu kyautad da tayyi man../ da kuma abokiyar zaman ta (bani iya kawo sunan ta a halin yanzu) wadda ta ba shi atamhwa/atamfa mai kyawo yar rabka lulluɓi, a cikin Waƙar Dagacin Banga, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar mai amshi "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu Na Maigandi Kai aa Uban Zagi '. Misalai ne da nike iya tunawa inda ya ambaci mata a cikin Waƙoƙinsa.

    [3:30pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Za a samu Waƙar Mai Girma Marigayiya Mai Babban Ɗakin Ƙasar Kano, Hajiya Hasiya/Asiya Bayero. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [5:30pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A cikin wata Waƙar da ya yi wa Marigayi maigirma Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman yana ambatar uwargida Hajiya Goshi. Duk da yake ba ita ce uwargidan ba, amma dai sunan mace ya fito.

    [6:51pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Uban Kumatu Uban Isa jikan Abubakar....

    Mai Sangon daga gamda'aren babba Kwamishina....

    A cikin Waƙar babban ubangidansa, Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai amshi " Ya yi Sarki daidai wada mai yanzu yar riƙa, Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai dubun bara ". Kumatu mace ce.

    [7:05pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: *Gwamma/Ikka da kar riƙa Uban Luba/Uban Liba....

    [7:22pm, 23/02/2024] Malama. S.S. Labbo: Allah ya taimaki shehin Malama na ga ka bani abin da na ke buƙata, dama na ga shi makadan fada ne to shi ne nake tsammanin kamar ba ya ambaton mata a cikin waƙarsa, to amma Alhamdulillah ina godiya da wannan amsar. Allah ya ƙara basira. Amin

    [7:38pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon. ai mutane ke ganin malami ya kai mlami har su ba shi suna. Malaman zamani kurum kan liƙa ma kansu suna!

    Imam Abu Hamid Muhammad al - Ghazzali bai taɓa liƙa ma kansa wani laƙabin shahara ba. Mutane suka ga ya cancanta suka kira shi Hujjat al - Islam.

    Haka shi Shehu Usmanu ɗan Fodiyo bai taɓa kiran kansa Shehu ba. Ƙana'a tarbiyyarmu ce Musulmai

    [8:52pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: "... Saratu ta ban atanhwa maikyawo

    Nir rabka lullubi. "

    [9:02pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: Maibabban daki, ta dade tana jin daɗin waƙad da Saidu Faru yay yi ma Sarkin Kudu Maccido wadda yaka bayanin tahiyatai haz zuwa bakin Bahar Maliya da kammalac cewa sai ya' iske larabawa wurin.

    Wata rana Saidu ya tai Kano, sai matan hwada sunka burgutamai haka.

    Yaji daɗin abin shi ma, sai yay yi mata waƙa a matsayinta na maisarauta a hwadak Kano.

    [9:02pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: Onorabul, "Barka da hayewa maliya. "

    [9:07pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: "Manya sun ishe manya

    Inji mutanen Jidda

    Suna ziyartaj juna.. " 😄

    Allah yasa an yi karbabbiya.

    [9:24pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: A cikin ambaton mata da Saidu yay yi, akwai Nana Uwardaje a wurare da yawa.

    A waƙaw Wakilin Tsafta Mamman Nadange;👇🏽

    "Kowa ya san Nana uwad Daje

    Ya kau san jikanta na Gusau. "

    "Jikan Bello na Hodiyo

    Jikan Nana uwad Daje

    Bawan Allah jikan bawan Allah na Alu... "

    A cikin waƙas Sarkin Kudu Maccido.

    [9:26pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa!!! Sarkin Tsabta Malam Muhammadu Na Dange daga gidan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    [9:35pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa Nadange jinin ɗan Fodiyo ne, amma daga gefen Nana Asma'u Uwar Daje matar Usmanu Giɗaɗo ɗan Lema ya fito. Bagiɗaɗe ne, Allah Ya yi mai rahma, amin. 'Ya'yansa na iya zama wazirran Sarkin Musulmi

    [9:38pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla da wannan ƙarin bayani Ranka ya daɗe.

    Ya daɗe Gusau.

    [9:56pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Sosai. Ɗan'uwana ne. Kakannimmu ɗaya

    [9:59pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Yaya ne gare ni, 'ya'yansa 'ya'ya ne gare ni

    [10:14pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Na san shi saboda Mai garinmu, Ɗan Alin Birnin Magaji Muhammadu Mode Usman. Abokin shi ne sosai.

    [5:10pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Dakta Isma'il Aliyu Waziri barka da hwama, godiya mai dama da wanga aiki. Allah dai ya hi mu yabawa, amin.

    [5:45pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Yan Ruwa laƙabin sarauta ce ta fada a yankin Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara).

    Akwai ta a fadar Anka da Talata Mafara da Bunguɗu. A Moriki ta fara a fada, a halin yanzu kuma an ɗaukaka ta zuwa ta hakimci/uban ƙasa dake da gunduma mai Unguwanni/ƙauyuka da kuma jama'a.

    Ga kuma ta fadar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III tun yana Sarkin Kudun Sakkwato.

    [5:52pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Sai Sarkin Zazzau nig gani yac ce man Muhamman ya tai haji...

    Domin nuna faɗin mulkin masu iko na Cibiyar Daular Usmaniya, Malamin Waƙa ya nuna daga Mai Martaba Sarkin Zazzau (ɗaya daga cikin Tutocin Daular Usmaniya) ne ya samu labarin tafiyar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo zuwa aikin Hajji bayan ya biyo shi daga Sakkwato.

    [6:31pm, 24/02/2024] +234 806 524 0341: Salaam.....

    Akwai wadanda ba su san wadannan Tsuntsaye ba, har dani ciki, "Suda da Burtu da Jinjimi da Beguwa da Bubukuwa, a taimako da hotunansu domin mu ƙara ilimi.

    [7:30pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Na dai san Burtu: wani tsuntsu ne wanda ya kusan girman talotalo ga jiki amma ya fi talotalon tsayi, bakinsa yana da ɗan tsayi amma bai kai tsawon na bubuƙuwa ba, ƙafafunsa sun ɗan cira. Da kansa har zuwa baƙi ne mafarauta kan samu sai su liƙa wani zare ko igiya ga kan ta yadda za su iya ɗaura shi ga kai kamar yadda sukan ɗaura fitilarsu in suna cikin daji da dare don su riƙa ganin gabansu. To idan mafarauta suka shiga dajin da suka san akwai burtu ciki sai su ɗaura wannan kai na burtu, su duƙa kamar mai yin noma, da hannuwa da ƙafafu za su riƙa tafiya, suna yi suna tokarar ƙasa da bakin burtu, wato kamar yadda burtu tsuntsu yake yin kiyo. Za su yi ta yin wannan tafiya suna yin kamar burtu ne ke kiyo har su kai kusa da burtu ko taron burtu na ƙwarai da ke kiyo. Ta haka mafarauci yake ruɗin burtu mai rai ya ɗauka cewa mafaraucin irinsa ne tsuntsu. Can sai mafarauci ya yi wuf ya cafke burtu!

    Na taɓa ganin burtu cikin dajin da ke tsakanin Ɗansadau da Ɗangulbi. Tsuntsu ne mai nama

    [7:39pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa: "Ba ai wa biri burtu", Wannan na nufin ba a iya ruɗar biri ta wannan siga?

    Burtu

    [7:45pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Burtu👆🏽

    [7:45pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Tabbas na ga burtu. Ai saboda da kansa ne mafarauta kan ɗaura ga kansu su ruɗi tsuntsu su kama shi, akan ce shigar burtu. Idan mutum ya yi shigar burtu ana nufin ya ruɗu mutane ko ya yi sojan gona.

    [7:49pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa: Duk girmansa yana iya hawa kan reshe?

    Suda uwar surutu

    [7:50pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Suda uwar surutu👆🏽

    [7:52pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa: 'Suda sarkin labari', ɓaba Suda'.

    Ita kuma yaya lamarinta yake!🙏

    Jinjimi

    [8:00pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Jinjimi👆🏽

    [8:11pm, 24/02/2024] Dr. Aliyu Sambo Uny Dutse: Mai girma Dangaladima barka da sirdi. Alla ya amsa ya inganta niyya. Ni ko ko don in laqanci wakokin Malamin Waƙa, Makada Sa'idu Faru, Ina bara a bude min ajin koyon Hausar kasar Hausa. Makada Yana zuba Hausa Mai dubun hikima, ni Kuma babu Hausa. Allah ka rika mana.

    [8:12pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Barka kade Maigirma Waziri, muna ta bautag godiya dai da wanga aiki na ilmantarwa da akai muna kullun. Allah shi ƙara hasken Makaranta, amin.

    [8:15pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Malam Aliyu Sambo ɗan mutun Bauchin Yakubu barka da dare. Sannu a hankali zaka fahimci Hausah Hausa In Shaa Allahu in dai kana cikin irin waɗan ga Zaurukan da Shaihunan Mallammu kai muna zubak Kurna ta ilimi.

    [8:29pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni sai cikin maganganun Hausawa na san suda. Misali idan yaro ya cika surutu akan kira shi suda sarkin surutu/ ɗumi; idan mace ce sai a ce uwar ɗumi/ surutu

    [8:33pm, 24/02/2024] Mal. M.A. Umar Akwai wani tsoho da ake kira "Jinjimi mai ƙololo" watakila sunan na da alaƙa da wannan tsuntsun!

    Tuji

    [9:32pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Tuji👆🏽

    [9:34pm, 24/02/2024] Prof Nazir I. Abbas: Madallah da wannan ƙoƙarin kawo muna hotunan tsuntsayen

    [10:56pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa:

    Shi ko Tuji,

    Da ad da girman baki,

    Ya lanƙwasa tsara'

    Ran nan nas san,

    Duniyag ga komi na ne,

    Wani mayar wani".

    Gwabron giwa,

    Uban Galadima,

    [11:04pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle ita ake ƙira beguwa ko kayar makaya

    [11:06pm, 24/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wani mayen wani wato wani ya fi wani ko Hausawa su ce "gaba da gabanta"

    [11:09pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle ita ake kira beguwa ƙayar maƙaya

    [11:10pm, 24/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: "Kullun Sarki ya sai dawo,

    Ita kau ba ta san za'ida ba,

    Ko nono sai dai ta bungulo".

    [11:34pm, 24/02/2024] Dr. Sakina: Salam Malamaina, Magabata da Abokan karatuna.

    Barkanmu da dare.

    Sunana Sakina Adamu Ahmad manazarciya fannin kwari.

    Ina biye da wannan zauren mai ilmantarwa, kuma ina ta sauraren ko zan samu abin da zan ɗauka don gina fannin nazarina.

    Amma sai na ga ana ta baje koli da ɓarin hikima a fannin "tsuntsaye", ko canza sheƙa in dawo inda na ga an tara mini amsa?

    [12:38am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: To Dr. Sakina da yake wannan zaure a kan mawaƙi Sa'idu Faru da waƙoƙinsa aka buɗe shi, za ki iya lura da cewa wannan ɓarin ne masana da manazarta da masu sha'awa suke tofa albarkacin bakinsu. Idan kika ga ana magana a kan tsuntsaye to saboda shi mawaƙin ya ambace su ne. Idan kuma kika ga ana magana a kan dabbobi to lalle su ma ambaton su yana cikin waƙoƙinsa ne. Da yake fannin ƙwari ne fagen nazarinki kada ki ɗebe ɗammaha. Watakila wani ya kawo mana wata waƙa ko waƙoƙi da Sa'idu Faru ya ambace su. Me zai hana ki tambayi wani masani (da na roƙi masu gudanar da wannan Zaure da su ba jami'arsu shawara da ta naɗa shi Rumbun Waƙoƙin Baka na Zamfara) da ya dubo miki ko akwai waƙa ko waƙoƙin Sa'idu Faru da suka ambaci ƙwari kamar sauro da cinnaka da tarmani da zuma da rakkuwa da makamantansu. Wannan masani shi ne Hon. Ɗanmadamin Birnin Magaji. Kila ma yana nan yana burkuto irin waɗannan waƙoƙi in har akwai su. Allah Ya taimaka amin.

    [12:55am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Na dai san akwai waƙar da Sa'idu Faru yake cewa wani abu kamar/kowal kasa zuma bai koma batun maɗi/. Hon. Sir gare ka don Allah

    [5:01am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka Ranka ya daɗe.

    Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya ambaci ƙwari kamar Zuma da Zirnaƙo da Galla a cikin wasu Waƙoƙinsa.

    A Waƙar Marigayi Maigirma Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu mai amshi 'Gwabron Giwa kana da martaba, Usumanu na Bunguɗu Uban Marafan Keku na Atto mai wuyak karo' yana cewa "Zirnaƙo ƙaryaf faɗa ya kai, kowa ka biɗaf faɗa ya ja zuma, sai ya biɗi mai raba su ya rasa".

    Haka a cikin Waƙar Ɗan Uwanka, Marigayi Maigirma Wakilin Tsabta Malam Muhammadu Na Dange yana cewa "Shaye - Shayen da aka yi ma Galla, ba a yi ma Zuma shi" (duk da yake ba na rubuta daidai abun da ya faɗa ba ne).

    Ban taɓa ganin Galla ba a matsayin ƙwaro, amma ba na ce babu ƙwaron da ake kira Galla ba, amma tawa fahimta ita ce "Galla" kamar wasu ruwa ne/darɓa dake sauka daga sama/ko kuma aikin wasu ƙwarin ne dake haifar da wannan ruwan/darɓar akan tsirrai.

    Wannan ruwan/darɓar na da zaƙi, kuma saboda rashin samuwar ƙwaron/Gallar dake haifar dashi sai Bahaushe na ganin ɗibar sa a sha ba wuya, amma zuma da yake sai an yi ganinta kafin a samu a sha ta a sauƙaƙe sai Malamin Waƙa ya bayar da wannan misali. Allahu Wa'alam!

    [5:42am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: To Sa'idu Faru bai faɗi wani abu ba kamar wanda na ambata >/kowal lasa ruwan zuma bai koma batun maɗi/?

    [5:56am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe ya faɗi hakan a cikin Waƙar da ya yi wa Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo mai amshi 'Farin cikin musulmin duniya, mai martaba na Abubakar, ci fansa Alhaji Macciɗo'.

    Sai dai Maɗi ba ƙwaro ba ne. Wata cimaka/abun sha ne da ake yi daga wasu ɗiyan itace kamar su kaiwa/kanya da makamantansu.

    [6:43am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ai ni dama zumar nake son in ji. Maɗi kuma kamar wada ka ce daga rake ake yin sa. Zumar da Sa'idu ke magana kuwa ai ruwan zuma ne na ƙwaron da ake kira zuma. Ko kuwa?

    [6:45am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Madallah.

    Wai ka dawo daga Umrah? Na ga wani a Zaure yana yi ma barka da zuwa

    [7:10am, 25/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi: Watakila Hon bai yi kiwo ba, akwai kwaro da ake ce wa Galla, ana samunsa ga itacen doruwa a lokacin da yake bututun Samar da 'ya'ya, ai wannan zakin da ke darba a jikin bututun doruwa yana da alaka da kwarin gallar. Kwaron Galla ko sauro bai fi shi damuwa ba, kana korar sa yana ƙoƙarin fada ma a ido.

    [7:31am, 25/02/2024] Fugus Ba shir Abdullahi: ".... Maccido jikan Mu'azu makaye".

    Assalamu Alaikum!

    Iyayena da Malamai da sauran 'Yan uwana da Abokan Aikina da na Karatu duk ina yi maku fatan alkhairi, da fatan an an tashi lafiya.

    Ina da tambaya ne dangane da ma'anar kalmar nan ta makaye. 👌🙏🙏

    [7:59am, 25/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Sosai kuwa Dr. Ai Galla in ta fara bin Idon mutun sai ya damu don korar da yake yi mata.

    [9:36am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Gaskiya akwai buƙatar samun hotunan waɗannan ƙwarin irin su Zuma, Galla, Zirnaƙo, Rina da sauran su domin mu ƙaru.

    [11:03am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon sir, kana da gaskiya. Ina ba ka shawara da kada ka sha kunu ga azumi da sugar. Sai dai da zuma! Na leƙo inda ake kiyon zuma, babu nisa. Baitocin da ka tono muna yau kada ka bari su je haka nan!

    [11:14am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ƙarin wasu Tsuntsaye da Malamin waƙa ya ambata a cikin wasu waƙoƙinsa.

    Kaza, a cikin waƙarsa ta Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba mai amshi 'Gwabron Giwa Garba Uban Yari maci maza..

    Dale a cikin faifan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai Turke 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai' inda yake cewa "Na ishe Dale tai ƙawa ga jama'at ta ba ƙawa...

    Angulu/Ungulu/Kolo... A cikin waƙar Ɗanmadamin Sakkwato Usman Ɗangwaggo Bunguɗu mai amshi ɓajini birni bajini dawa na dai gaishe ka da ƙoƙari, ɗan mai daga na Abubakar Usman kai nik zaka in gani.

    A waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Ahmadu Muhammadu Asha mai amshi 'Sarki yai Sarki cigari ya gyado rinjaye Alu... yana cewa "Sa babba sata nig gani, tsohon ɗan Sarki Angulu... (Sa babba sata wani kalar Wake ne mai girma/ruɗu - ruɗu dake sanya mutum sha'awar ya duƙa ya cire shi a gonar da ba tashi ba).

    [11:18am, 25/02/2024] Dr. Sakina: Barka Prof. Ai tun kwanakin baya na fara tuntubarsa. Kuma ya agaza da wasu bayanai. Abin da ya burgeni, yadda naga ana ambato sunayen tsuntsayen tare da hotunansu. Wanda da yawan matasanmu ba su san tsuntsayen ba.

    [11:19am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Da ba zai zama abun ya yi yawa ba, da na turo wasu Tsuntsayen domin a ƙara muna ilimi akai.

    [11:20am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Na'am!

    A cikin Keɓɓe Local Government akwai Raha

    Akwai Raha a Kebbi can idan aka bi hanyar Bunza

    Haka ne Maigirma Babban Sakatare. Ta Tambuwal babu "n " a karshen sunan, Maradu ne ba Maradun kamar yadda ta Jihar Zamfara take ba.

    Su kuma akwai irinsu da ke da bambance -bambance kadan irinsu Kauran Namoda ta Zamfara da Kauran Wali ta Kaduna, akwai Bungudu garinmu da wani garin Bungudawa, akwai alaka sosai a tsakanin wadannan sunayen.

    Ba za a rasa alaka tsakanin garuruwan ba idan aka yi binciken. Na san akwai Kuryar Madaro da Kuryan Dembo a Zamfara. A Sakkwato akwai Kurya (ta Gandi) haka ma akwai Kurya a Kebbi.

    Mai turu yana cewa a wata waƙarsa;

    "Abin da yas sa ban hau doki ba,

    Na Bungudawa shi nika son hawa.

    A nan mutanen Bungudu yake nufi ba waccan Bungudawar ba. Ina zaton shi bai ma san da wancan garin ba.

    Haka ne Dangaladiman Shaihin Malaminmu.

    Kuryar Madaro ta Kaura Namoda kirkirar wasu Fulani ce da ake kiran jinsinsu da suna "Jallawa" domin sun fito ne daga Dutsin Jalla a cikin Jamhuriyar Nijar ta yau. Su da Rawayya wa ne da ƙane. Madaro ne ƙane kuma shi ne ya kirkiri Kuryar Madaro, Muhammadu Ɗan Na Ɓore ne ya kirkiri Rawayya.

    Kuryar Dambo dake cikin Masarautar Shinkafi a Jihar Zamfara kuma Mal. Makauru ne ya kirkire ta, ƙane ya ke ga Gatari wanda ya kirkiri garin Kware/ Kwaren Isa dake Masarautar Shinkafin Jihar Zamfara. Su kuma Fulani Alibawa ne.

    Makada Narambada yana cewa "Ai Kurya ta Dambo ta Makauru an nan, Zanhwara babu Bagare kama tai" a cikin waƙarsa ta Sarkin Rafin Kuryar Dambo Ibrahim mai amshi 'Masu gari mazan gabas tsayayye, Sarkin Rwahi ya wuce a rammai '.

    Kuryar Gandi kuma kirkirar masu jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya ce. Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ne ke kirkirar ta, amma bata haɓaka ba sai a lokacin mulkin Sarkin Musulmi Abubakar I/Abubakar Atiku/Mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio, ƙanen Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda kuma shi ne ya gaje/gade shi.

    Makada Muhammadu Dodo Mai Taushi ya tashi daga garinsu, Bakura ya koma Kurya da zama tun a farko farkon ƙarni na 21. Daga can ne zuriyarsa suka watsu zuwa garuruwan Wurno da Sakkwato da Shuni inda suke a halin yanzu.

    Shi ne ya haifi Kakan Makada Amadu Mai Launi Bakura, wato/watau wanda ya haifi mahaifiyarsa inda ta nan ne za a iya cewa ya gaji/gadi kiɗa da waƙa.

    Haka ne. Kusan abu ɗaya ne. Sau da yawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kurna kana jin yana cewa Maradu a maimakon Maradun. Ina ganin da Maradun da Maradu duk abu ɗaya ne.

    Madalla da wannan ƙarin bayani.

    Ko a Kaura Namoda akwai garin da ake kira Sakajiki, laƙabin sarautarsu shi ne Maradu.

    Rakkuwa ke yin Danko tayi Zuma Mai Zaki da Dan tsami kadan

    Gallace Mai yin Zaki ruwa-ruwa, mafi yawa a jiki bishiya ko ganyen bishiya. Ta kan Yi Zuma a kogon icce. Akan samu da yawa kama cikin garwar manja na dauri Wanda Yan garuwa ke yin doso dasua.

    Akwai Birnin Yero da Badarawa a yankin Shinkafi ta jihar Zamfara, haka Kuma akwai Birnin Yero da Badarawa a jihar Kaduna.

    Da akwai Yoro a jahar taraba babangari ne na mumuyawa l/g HQt, ce, kodayake mumuyawa sunce asalin su kanawa ne, kumanaga haryazu sunayin staga gajeruwa irin takanawa

    Tsaga

    Shaga*

    Badarawak Kaduna ainihi ba sunan unguwa ne ba. Sunan babban titin da yar ratsa cikin unguwat ne, wato Badarawa Road. Daga nan sai anka miƙe da cewa Badarawa, Badarawa, ha' abin yaz zama sunan shiyat.

    "Ko can hasken hwarin wata bai dushe rana ba" inji Makaɗa Alhaji Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba (Gwabron Giwa na Shamaki baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daga).

    "Toron Giwa yana abun da ya kai ya shigo dawa, 'yan namu suna ta gaisai sun ba da gaskiya... Inji Ɗan Umma Uban Kiɗi a faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi ' Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai... Allah ya kyauta makwanci, amin.

    "Zomo ya taho ya biya ya gaida Toro, shi ya yarda Allah kawa kowa nagarta", inji Makaɗa Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    "Ina banga - banganga mai 'yar mahuta, Alade wurin shan giya kah hi suna" inji Makaɗa Sa'idu Faru a cikin wata Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Zomo ya ce tsaya✋🏽shege lallashinta kay yi

    In karhi gaskiya ne koma ebo gabana

    Saidu na yawan ambaton giwa;

    Giwa ta sha ruwa tai mika ta taushe gurbi...

    Ga Wangara a Gezawa a ƙasar Kano. Sannan akwai Wangara a kasar Katsina.

    Wangara kuwa watakila ƙabilar da ta zo ne daga Senegal > Wangarawa

    Abin mamakin warwatsuwar al'umma shi ne a lokacin da babu abubuwan hawa na zamani sosai amma sai mu yi ta samun bayanan na wannan kasar a wata kasa ko na wata kasar a wannan kasar.

    Migration and state formation in Hausaland by Abdullahi Smith has dealt with it Dr.

    Haka ne, amma ina ganin ƙoƙarin mutanen wancan lokacin ne.

     (1) Dole ba ta rasa ɗakin kwana.

     (2) Hanyoyin da mutanen da suka bi suka kai wasu wurare ratse ne bisa ga hanyoyin zamanin yau.

     (3) Mutanen da ba sauri sukan yi ba. Sukan kwana yada zango ne don su tara guzuri sannan su ci gaba har su kai inda suka yi niyya.

     (4) Wasu kuwa yaƙi ko fatauci ko neman ilmi ko yawon buɗa ido ne ya kai su amma daga baya suka zauna ba su koma gida ba.

    A lokacin ana zaune lafiya, babu tashin hankali kamar yanzu.

    "Sai Bil'amu/Bil'amo uban dubara shi ɗai yaz zo ga Giwa, yac ce albarkacinki ni zaka in samu ruwan da nish sha, Giwa ta ba shi hili ya sha kuma ya ba ɗiyanai, ya tai ya wa dangi kirari yac ce ya ƙwato da ƙarhi, Zomo ya ce tsaya shege lallashinta kay yi, in ƙarhi gaskiya ne koma ƙwato gaba na ", inji Makaɗa Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Sarkin Zamfaran Zurmi Suleimanu Muhammadu Sambo mai amshi ' Babban bajinin gidan Sambo shirin ka daban, jikan Mamudu Sarkin nasara baban Baraya'.

    [3:31pm, 28/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Canza maganar mawaƙi ko ma kowane marubuci kasada ce domin ma'ana ko furuci ko kari na iya canzawa. Idan kari ya canza sai waƙa ta ƙare. Misali, a Sakkwatanci "ilmi" ake cewa alhali a Kananci da Zazzaganci "ilimi" ake cewa > gaɓa biyu dogaye a Sakkwatanci, gaɓa uku a Kananci da Zazzaganci, biyu na farko gajejjeru, ta karshe doguwa

    [3:40pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Salihu Jankiɗi yana cewa a wata rerawa ta wata waƙa:

    An ka da Kumama ya faɗi,

    Ya shaƙe ciki da tuwon wake,

    Ya kumbura kullum sa tusa.

    Nan take kuma sai ya maimaita ɗan ya ce:

    .........................

    Ya kumbura kullum sai rihi.

    Me za ka ce a nan?

    [3:43pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko alama! Ba haka ilimin yake ba. Su mawaƙan ne ai da kansu, suke canza kalmomin; wani lokaci ma nan take.

    Rerawa da ƙa'idojinta babi ne mai zaman kansa a ilimin nazarin waƙar baka.

    A koma ga ayyukan Farfesa Gusau don ƙarin bayani.

    [3:43pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ikon Allah!!! To saboda iyawa kana iya sauya masa waɗan nan kalaman ya zuwa naka tunanin/hasashen?

    [3:47pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Dama shi ne fahimtata kuma nike ƙoƙarin jawo hankali a kai.

    [3:47pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Babu buƙatar wannan dogon tawilin domin ba sharhi ko fassara nike nema ba.

    [3:48pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Mawaƙan baka kan yi ƙare-ƙare da rage-rage da canje-canje a waƙoƙinsu saboda canzawar lokani da wurin rerawa da sadar da waƙa.

    [3:53pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ikon Allah!!! Waɗan nan ƙare ƙaren na iya canzuwa ga manazarci ko mai sharhi akan Waƙoƙin nasu?

    [4:29pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Ai aikin mai nazari da sharhi shi ne fara bayyana 'yadda aka yi' kafin 'yadda za a yi. '

    [10:16am, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Malam Yusuf gajeriyar mallaka ana haɗe ta da suna ne: Malumanmu ba maluman mu ba.

    [1:28pm, 29/02/2024]: "Ina banga - banganga mai 'yar mahuta, Alade wurin shan giya kah hi suna" inji Makaɗa Sa'idu Faru a cikin wata Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [1:33pm, 29/02/2024]: Salaam.... Malamaina don Allah a cikin Wakokin Sarkin kudu Maccido na Sa'idu Faru wace waƙa ce ya ambaci 👆Alade, a taimaka da gindin waƙar.

    [1:44pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Ina sa ran:

    Bajinin gidan Bello Manman na Yari,

    Sarkin kudu Maccido ci maraya.

    [4:34pm, 29/02/2024]: Masha Allah, kyaun dattijo magana biyu. Ya ce e, in aka sami gyara ya ce a'a.

    [4:39pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Kyan dattijo magana uku: í, áâ, éh!

    [5:13pm, 29/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi: Wane Karin harshen? I & eh duk guda ne.

    [5:28pm, 29/02/2024] +234 706 685 1000: Tau hwa! Fage na manyan masana. Allah ya ƙara basira.

    Tambaya.

    Ko Sa'idu Faru ya taba jira baitoci biyu zuwa uku a cikin wakokinsa, da kalmomin ingilishi?

    [5:41pm, 29/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Da wuya a samu hakan, musamman ga mawaƙan da ba 'yanboko ba. Shi yana cikin irinsu.

    [6:20pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Inda ko Larabci ne.

    [6:43pm, 29/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A ɗan nawa gajeren nazarin akan Makaɗa Sa'idu Faru ban san in da a cikin waƙoƙinsa ya jero ɗan waƙa guda uku na Ingilishi ba.

    A wata waƙar da ya yi wa Marigayi Mai martaba Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman mai amshi 'Mai ɗamara Ɗan Ali, Ɗan Shehu sadaukin Sarki' akwai inda ya kawo wani zance a cikin Ingilishi inda ya ke nuna ya je wajen wani da Kiɗa da waƙa sai ya juye baki yana yi masa turanci/ingilishi, shi kuma ya sanar dashi Kiɗi da waƙa su ya iya shi bai iya turanci ba.

    A hakan ne ya ke cewa "I no Ingilishi ni ban iya turanci ba".

    Akwai caffiya da ɗan amshinsa Malam Ibrahim (Ibrahim Sa'idu Faru, halinfansa na yau) ya yi da kalmomin turanci a cikin Waƙar Marigayi Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi 'Farin cikin musulmi duk kai mu ka taƙama yau, Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja', yana faɗin " wani undesirable element..

    A cikin wata waƙarsa ta Marigayi Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.. sun kawo wata kalma mai kama da ta turanci inda suke cewa " Kuma ya samu yardi ga ob Lamiɗo babba.

    A Waƙarsa mai amshi 'Farin cikin musulmin duniya ta Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III yana cewa "Farin cikin mu mutanen nozan/northern riƙon da kay yi Alhaji Macciɗo". Na san ba za a rasa ire -iren waɗan nan ba.

    Allahu Wa'alam!.

    [7:07pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Rumbun nazarin waƙar baka ya samu ƙarin kalma: 'caffiya' wadda take daidai da 'rakiya'.

    [7:10pm, 29/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Abdu wakilin local asorati/ Local Authority... Kamar yadda ya kira Ƙanen Marigayi Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu da ake kira Alhaji Abdu Mafara a cikin Waƙar shi Ɗangwaggo Bunguɗun mai amshi 'Gwabron Giwa kana da martaba, Usumanu na Bunguɗu Uban Marafan Keku na Atto mai wuyak karo'.

    Afuwan, Alhaji Bello ne ba Alhaji Abdu Mafara ba. 🙏🙏🙏

    "Ana ta tsoron kai ba ka jin tsoro!

    Baba halin Alu kai yi mai Raba".

    Ƙi garaje uban Shamaki.........

    Maigirma Sarkin Gobir Na Bunguɗu anya Alu mai Raɓah ne?

    Saboda wanzuwar Sarkin Musulmi Abubakar II da aka fi sani da Abubakar mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi sai ina ganin kamar an fi tafiya akan cewa shi ne yake danganta wanda ya yi wa waƙar dashi.

    Abu na biyu kuma shi ne wanda aka yi wa waƙar yana da dangantaka ta jini da Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar mai Raɓah ɗin da nike cewa kamar shi ne Makaɗa Sa'idu Faru ke ambata a cikin wannan ɗan waƙar.

    Shi wanda aka yi wa waƙar, Sarkin Gabas Talata Mafara Alhaji Shehu ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ne, Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne.

    Da Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar mai Raɓah da Sarkin Musulmi Mu'azu duka ɗiyan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne. Wannan ya ƙara mani ƙwarin gwiwar cewa shi ne Malamin Waƙa ke ambata/nufi. Amma a sake sauraren wannan ɗan waƙar domin tantance abun da ke daidai.

    Godiya mai yawa tarin yawa Maigirma Danmadami. Ina jin daɗin wannan dan waƙar ne.

    Assalamu Alaikum

    Ko Makada Saidu Faru yayiwa Sarakunan Zazzau Waƙa?

    Allah ya saka wa Shehunmu da alheri. Ya ƙara lafiya da nisan kwana.

    Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Ya yi wa Marigayi mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris Waƙa.

    Jagora: Shi ad da halin ga na Bubakar

    Y/Amshi: Ba da doki garai ba komi ba na,

    Jagora: Shi ad da halin ga na Bubakar

    Y/Amshi: Ba da moto garai ba komi ba na

    Jagora: Macciɗo roƙon mota niz zaka

    Y/Amshi: Kai bari katce iyakag gargare

    Jagora: Macciɗo roƙon mota niz zaka

    Y/Amshi: Kai bari katce iyakag gargare,

    Mai roƙon doki don suka,

    In a ba shi mato amsa ya kai,

    Mai roƙon riga kwakwata in an ba shi shabka amsa ya kai,

    Mai roƙon riga yar diga in an ba shi kore amsa ya kai,

    Kana shire Baban Yan Ruwa...

    1. "Kai bari katce iyakag gargare"/me ne ne gargare?2. " Kwakwata da Shabka da Yar diga da Kore duk nau'in sutura ne/riguna ne na alfarma. Ko zamu samu sharhin da zai ƙara fito muna da surar waɗan nan riguna/kayan ado na alfarma ƙara - ƙara?

    Ina manoma? A ɗan sanina "gargare" shi ne wurin da aka ba mutum ya nome cikin gona. Saboda haka gargare bai kai yawan gona ba.

    Don Allah kada a dogara da wannan bayani saboda ni sanina da gona shi ne zuwa yin shuka gonar mallamina na zaure, kuma yadda ma ake shuka a lokacin ban iya ba😂

    Ranka ya daɗe barka da asuba. Haka ne, gargare ba a wajen noma ba ne kawai ake samun sa ba, a kowane irin al'amari da ake yi a gona ana samun sa tun daga sassabe zuwa huɗa da shuka da zuba taki da noma da cirar shuka da girbi da ma cire kayan gonar.

    Gargare na nufin iyakar inda aka tsaya da wani aiki a gona ko dai domin an gaji a tsaya a huta ko kuma saboda daidaita aiki ya tafi kamar yadda ake buƙatar sa.

    Yaran Malamin Waƙa suna ankarad dashi cewa a wajen babban ubangidansa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ya daina iyakance roƙo saboda komai yana iya samu daga wajen sa har ma abun da bai roƙa ba ko abun da ya fi gaban wanda ya roƙa.

    Muna godiya sosai Ranka ya daɗe da buɗa muna fage da wannan bayani.

    Ai gargare ana nufin tsawon kuyyar da mai noma kan datsa a lokacin da yake noman. Wato kamar a ce tsawo kuyyen ya kai kimanin rabin "kilometer" to sai ya rika datsawa kamar guuntu shida ko fiye da hakan idan ya gama wannan ya dora wannan har ya kammmala. Ko mutun daya ko fiye na yin gargare wajen noma, haka kuma zabi ne ga mai gona ko 'yan kwadago.

    Da kyau Maigirma Sarkin Gobir Na Bunguɗu kuma Shaihin Malaminmu Dr Haruna Umar Bunguɗu. Godiya sosai da wannan ƙarin bayani.

    Rankaidade barka da ka tashi lafiya? Ya ibada? Allah ya ƙara maka. Kwarin guiwar wanzar da ibada, Ya kuma karbi dukan ayyukkan da ka yi da addu'o'in da ka yi mana da kasarmu. Amin Ya Hayyu Ya Qayyum.

    Haƙiƙa tun daga bayanin da ka yi na kalmar ba fahimci abin da Faru ke nufi cikin waƙar tasa. Shi dai gargare ba duk gona ba ne. Na gode ƙwarai Hon sir

    Dalili da sanin haka na fara bayanina da "Ina manoma".

    Dr. Haruna barka juna. Ina fatar duk iyali na lafiya amin Ya Arhamar rahimina.

    Muna godiya sosai da ƙaruwar da mu ke yi Ranka ya daɗe. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    ... Waƙa ɗai mukai kamar an aza gargare...

    A kai a kama zan kyawo in don kwaramniya ba fasali ba ta...

    A sha hura ayi wasa Ɗan Tumba shan hura ba lahani ba ne....

    Madallah Danmadami da Sarkin Gobir na BUG da bayanin gargare.

    Ba kamay yadda maitambaya yac ce ba "gargare shine wurin da aka ba mutum ya nome cikin gona". Karin bayani nanniya shine, shi wanga wurin, da aka diba cikin gona aba wani ya noma, shi aka cema GAMANA.

    Sai dai a bayaninsa kamar ba yana nufin an baiwa mutum wani wuri ba ne a cikin gonar ya noma, a'a an ba shi wurin ne domin ya nome.

    Dalili ke nan da na fara bayanina da "Ina manoma?". Na kuma ce kada a dogara da bayanin. Alhamdulillahi! Yanzu ga manoma nan suna ba mu ilmi.

    Haƙiƙa. Haka nake nufi. Ka san bami ne ni ga harkar noma! Ban ma kai ga bamin ba

    *Noma/Nome....

    Ya noma na nufin ya mallaki wurin na wani lokaci akan wani sharaɗi/wasu sharuɗɗa. Da wannan sai a ce an ba shi Gamana.

    Ya nome na nufin an nuna masa wani wuri a cikin gona aka ce ya nome daga wannan wajen ya zuwa wancan wajen, an samu gargare kenan.

    I! Yallabai, na ga ka bidi manoma.

    Asalin kalmag gargare ta malamman zaure ce. Daga larabci.

    Misali nassinga 👉🏽Allah yana karbar tuban bawanai 'ma- lam -yu GARGIR'.

    Sai malammai sunka hausance kalmat suna cewa GARGARA, ma'ana IYAKA.

    Gargara👉🏽gargare.

    To kuwa akwai yar tambaya ga bayaninka na farko cewa gargare daga Larabci take. Don Allah tuntuɓi masana ilmin harshe

    "Lallai Amale a waƙar Isah Maikware ya ce ".... ya sha gargara.... "

    Tabbas kalmar Latabci ce, mallakar malaman zaure. Manufarta kuma ita ce ƙarshen abu.

    Gargare kama a gona katsa shi ake yi ko datsawa ko iyakancewa.

    Wannan ma'ana ce kuma Makaɗa Sa'idu Faru ya yi luguden ta a waƙar.

    Babu shakka duk mai harkar hatshen Hausa yana da buƙata da masaniya da harshen Larabci.

    Wannan ba gargare yake nufi ba, gangara ce kamar ka hau tudu ka gangaro.

    Amma dai akwai waƙar Garba da ya yi "Ba ka san wuyag gargare ba"

    Ni abin da na fahimta a nan ita ce. Gargara daban gargare daban. Sannan za a ce Hausawa ba su da kalmar gargare sai da suka haɗu da Larabawa?

    A misalin da ya kawo na waƙar Amali ne na ce mashi gangara ne ba gargara ko kargare ba.

    A Larabce غرغر kalima ce mai tafiya da ma'anarta wato homophone a Turance. A ma'ana ta hatshe kuma tana nufin irin sautin ruwa idan an kurkura shi a maƙoshi. A ma'ana ta fannu kuma tana nufin rayuwa ta zo ƙarshe idan ta iso a maƙoshi ta fara bayar da irin wannan sauti.

    " Ga Garba can zamu

    jiɗa/sabka,

    Namijin da noma kawa

    haske.

    Jagora: Sannu da jeha kalme ga yashi....

    Y/Amshi: Sannu da.... mummuƙen laka,

    Bai san wuyag gargare ba,

    Ga Garba can za ni shiɗa/sabka,

    Namijin da noma kawa haske

    Kuma Hausawa sun fi Larabawa zama manoma.

    Amma kuma Dr. Ƙaura takan ɗauro Hausawa su daina amfani da kalmarsu su ɗauki ta baƙi. Misali a Zariya nakan ji Zagezagi na cewa "wundo" madadin taga

    Shin Sa'idu "Faru yake ko Hwaru"?

    Haka fa yac ce. Wato idan an aza gargare haka za a dinga kama kuyyai ana ta noma. Da an kai ƙarshe a sake kama wasu a juyo ba a zamnawa sai an kai inda za a tsayawa a sha hura a huta a ci gaba da aiki. Ka ga a nan uban kiɗa a bayar da yadda a ke gudanar da noma cikin ƴan ɗiya kaɗan masu hikima.

    Hwaru yake amma, Malamanmu Faru suke rubutawa.

    Ga faɗa Hwaru akan faɗa. Amma ga "Daidaitacciyar Hausa" Faru ake rubutawa ko faɗa

    Ai a ilmance gafarta Malam, tsakanin Balarabe da Bahaushe, dole ne ɗayansu ne ya ari kalmar daga ɗaya.

    Shi kuwa aro na komai yana da ƙa'ida kamar yadda masana irin su Ibn Khaldun suka tabbatar.

    Idan kuwa babu aro, sai koma ga zancen مصادفة kamar yadda wasu manazarta harshe suka tabbatar.

    In dai a bakin Saɗu Faru ne to, gargare ya ce ba gangare ba.

    Ana maganar Amale ne.

    Wani abu da zai ba ka sha'awa kuma gafarta Malam shi ne, asalin kalmar nan a wurin Balarabe da Bahaushe duka ɗaya ne wato: غرغر. Ya'un ɗin nan ta farko ta lamiri ce.

    Haka a Hausa daiwar kalmar wato lexeme a Turance ita ce: gargar. Wasalin e ko a kuma morpheme ne, kamar dai yadda ka sani.

    Ka kuwa san a ilmance ba za ta yiwu ba Larabci ya zama shi ne ya ari wannan kalma daga Hausa.

    Wani abu da zai ba ka sha'awa kuma gafarta Malam shi ne, asalin kalmar nan a wurin Balarabe da Bahaushe duka ɗaya ne wato: غرغر. Ya'un ɗin nan ta farko ta lamiri ce.

    Haka a Hausa saiwar kalmar wato lexeme a Turance ita ce: gargar. Wasalin e ko a kuma morpheme ne, kamar dai yadda ka sani.

    Ka kuwa san a ilmance ba za ta yiwu ba Larabci ya zama shi ne ya ari wannan kalma daga Hausa.

    Wani abu da zai ba ka sha'awa kuma gafarta Malam shi ne, asalin kalmar nan a wurin Balarabe da Bahaushe duka ɗaya ne wato: غرغر. Ya'un ɗin nan ta farko ta lamiri ce.

    Haka a Hausa saiwar kalmar wato lexeme a Turance ita ce: gargar. Wasalin e ko a kuma morpheme ne, kamar dai yadda ka sani.

    Ka kuwa san a ilmance ba za ta yiwu ba Larabci ya zama shi ne ya ari wannan kalma daga Hausa.

    Amin.

    [12:02pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ai gafarta Malam, duk abin da Bahaushe yake tinƙaho da shi yau na aro ne.

    Malanmu magabata a wannan fage sun daɗe da tabbatar wa duniya da cewa Hausa harshe ce ba jini ba. Duk wanda ka daduga a ƙasar Hausa kuma zai gaya maka asalinsa.

    Waɗanda ke kiran kansu Hausawan asalin ma, masana a wannan fanni sun bayyana yadda suka samu.

    [12:03pm, 02/03/2024]: Wato ni a ko yaushe na ga ana ƙoƙarin mayar da kalmomin Hausa zuwa ga asalin na aro daga Larabci ina mamakin shin ko an san Hausa tsohon Harshe ne wanda ke da alaƙa da Larabci da Ibraniyanci da amharic da Sumerian tun fil azal? Ni ba masani ne game da Larabci ko Hausa ba amma dai na san akwai alaƙa sosai tsakanin Hausa da Larabci tun farko. A tsarin da Greenberg ya yi na Harsunan Afrika ya sanya Hausa cikin babban zauren da ya kira Afro-Asiatic wato harsunan da ke Afrika kuma suna da alaƙa da Asiya. A nan cikin Afirka kuma ya haɗa shi da Kare Kare, Bolewa, Margi, Buduma, Angas da Sauran su waɗanda ya kira Chadic group of Languages. A sani Larabci ba Harshen Afirka ne ba. Hausa ce da Misiranci da Habashanci suke na Afrika. Kalmomin da suka shafi addini da yawa Hausa ta aro daga Larabci amma irin gargare da ya shafi noma da Bahaushe ke yi tun lokacin da mutum ya zauna cikin garuruwa ya kuma sami fasahar noma da kiwo da ƙira yaya za a yi a ce an aro kalmar daga Larabawa waɗanda ko irin noman mu ba su yi?

    [12:07pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Allah ya gafarta Malam. Akwai ƙanshin gaskiya a cikin batunka. Amma, ba kalmomin addini kawai Hausa ta ara daga Larabci ba, akwai na harshe da na ala'ada da kuma adabi.

    [12:19pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: To fa! Masana Ilmin Harshe sun shigo! Ni dai a ganina noma ga Bahaushe "Na duƙe tsohon ciniki, kowa zo duniya kai ya tarar" ne. Ta fuskar Adabi da Falsafa, in ganin zan fi yarda da cewa babu wanda ya san takamaimen lokacin da Bahaushe ya fara noma, sau dai hasashe

    [12:23pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:.... Ko wa zo duniya kai ya tarar.

    Shi ya sa muka ce Balarabe ya riga Bahaushe noma, domin ya riga shi samuwa a duniya.

    [12:24pm, 02/03/2024] +234 812 462 9009: Me ya ke nufi da su ne Hausawan asali? Ai duk Bahaushe na asali ne idan ba na mu'amala ba ne.

    [12:25pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Wai duk wanda ba su ba a harshen, ɗan rakiya ne.

    [12:25pm, 02/03/2024] +234 812 462 9009: Babu wata shaidar cewa Balarabe ya riga Bahaushe a duniya. Hasali ma Gidan ɗaya ne.

    [12:32pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Wallahi ya kamata mu mai da hankali ga waƙokin Sa'idu Faru. Tattaunawa kan ilmin harshe kan ɗauke hankali, a samu wani Zaure ba wannan ba. Shawara ce kurum na bayar

    [12:53pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Afuwan! Ban taɓa sha'awar Ilmin Harshe ba. Ko a jami'ar da na yi sai da aka tursasa min sannan na ɗauki kwasakwasansa. A lokacin ba a lura da an yi kuskure ga rubuta ƙa'idojin zaɓen kwasakwasai ba.

    [12:59pm, 02/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Shi ya sa Malam ka gagara a kan inda ka sa gaba, Kuma sai ka kai mutun ga bango idan bai ankara ba! 🤣🤣

    [1:07pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Wallahi Dr. Haruna Ilmin Harshe ne nake ganin kamar na lissafi yake, ni kuma na tsani lissafi don ban iya shi ba, har ma wani mallamina Bafalasɗine ya taɓa rubutu a kan takardar jarabawata ta lissafi wai don Allah kar na sake rubuta masa waƙa!!!

    [1:30pm, 02/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haka ne Malam, ai duk mai tsayawa kaifi guda yakan shahara a manufofinsa muddin bai zan raggo ba.

    [1:40pm, 02/03/2024] Mal. M.A. Umar Ƙwarai kuwa prof. Musamman fannin kamanta sauti "Acoustic phonetics". A irin ci gaban fasahar sadarwa ta ƙarni na 21, ana iya samar da manhaja wadda za a koya mata siffofin kamannin waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru, daga bisani sai ta ci gaba da samar da wasu ɗiyan waƙa tamkar na Sa'idu Faru....

    [1:49pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Assha! Watarana kuma maƙiya Musulmi su ƙirƙiro abubuwan da za su yaudari wawayen Musulmi su ce hadissai ne! Allah Ya yi muna kariya amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu Ya Rabbal alamina Ya Arhamar rahimina

    [1:53pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ka san akwai waɗanda suka taɓa ayoyin Alƙur'ani? Suka kira shi al- Furqan. Ba su san da cewa Allah Ya yi alkawalin kiyaye abinSa ba

    [2:01pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Malam Arabi wannan aiki zai yi kyau. Kuma kamata ya yi a ɗora gaba ɗaya Waƙoƙin baka na Hausa a kai.

    Ta wannan hanya za a iya Samar da abin da masana suka daɗe suna hasashe, wato ƙirya a Waƙoƙin baka na Hausa.

    [2:14pm, 02/03/2024] Dr. I.I. Dutsinma: Anya dai dai ne a cire ilimin harshe a kan duk wani abu da za a furta ko a rubuta?

    Waƙa furuci ne fa. Furuci kuma ilimi ne na harshe.

    Gaɓoɓin kalmomin da za a samar don gina kalma, kalma ta gina jimla, jinla kuma ta gina dogon bayani. Ta yaya za a cire ilimin harshe to?

    Daga cikin maudu'ai da za a yi nazarin waƙoƙin wannan Bawan Allah kuma akwai ɓangaren harshe.

    Ina da rubuce rubuce a kan harshe da Adabi

    da harshe da Al'ada. Wasu kuma harshe da Waƙoƙin Baka.

    Idan dai za a furta ko a rubuta harshe na da haƙƙi. Kada a cire harshe.

    [2:22pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau ya fara wannan aiki shekaru arba'in da suka gabata. Daga bisani nazari mai suna 'gidan dara' ya rinjaya.

    [2:46pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Wallahi ba ni da ja ko ƙalilan. Abin da nake nufi shi ne mu daina gardandami a kan ko kalmar Hausa kaza daga harshe kaza take, har mu kai ga ƙabila kaza ta riga wata duniya, da makamancin haka. Wasu suna ganin fa'idar yin haka amma ni gare ni waɗannan ba su ƙara muna kome ga fahimtar abin da wannan Zaure ya sa gaba

    [2:52pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Na taɓa gani a social media inda aka ce an nemi AI da ya yi makamancin Alƙur'ani amma ya kasa. Hadissai ne ban gani ko ji ba.

    [2:54pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Tattaunawa dai ba gardandami ba.

    [3:05pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Amma ai kalmar da ake magana a kanta, an cirato ta ne daga bakin Makaɗa Sa'idu Faru.

    [3:37pm, 02/03/2024] Dr. I.I. Dutsinma: Wai kare ya mutu a saura.

    Haka ne. Ai ba za a kaucewa bambance-bambancen kalmomi ba saboda tazarar ma'ana tsakanin kare-karen harsunan Hausa da muke da su.

    Ni Bafillatanin Katsina ne, don haka baki na na Katsinanci ne. Na ga kalmomi da yawa waɗanda ban san su ba amma akwai su a Zamfaranci da Sakkwatanci a wannan zauren.

    Allah Ya sa mu dace.

    [6:06pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Nazari ya nuna cewa, wasu Makaɗa waƙa suke fara samarwa kafin kiɗa. A yayin da wasu kuwa kida' suka fara samarwa kafin waƙa.

    Wane ɓangare ne Makaɗa Sa'idu Faru ya faɗa a cikin waɗanan rukuna biyu?

    [6:46pm, 02/03/2024] Mal. B. Lauwali: Irin wannan mahawara da Malammu su ne tabbakawa akwai darasin dauka ga kananan dalibai irina. Su na mutunta junansu wajen yin raddi, tare da kalamai na nuna son a gudu tare a tsira tare. Allah Ya ba mu iKon koyi da irin wannan hali nasu.

    [8:01pm, 02/03/2024] Malama H.A. Mayana: Tau mu kananan dalibbai ne Allah ya gafarta mlm zanso inji kiɗa ko waƙa wanene ya fara dashi domin in ƙara da abunda nike da shi a hannuna ni da yan uwana dalibbai abunda nasani game da makada saidu faru shine makada saidu faru ya koyi waƙa wurin mahaifin shi makada Abubakar wakokinsa, suka dada kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da kwakwalwar da Allah ya ba shi. Tun saidu faru yana da shekaru goma aka fara zuwa yawon kiɗa gari gari dashi. bayan da ya cimma shekaru shashidda sai ya "soma karbi"a wannan lokaci ne kuma aka hadasu tare da kanensa muazu wanda shine Dangaladimansa. Baya ga tsohonsa makada Abubakar Saidu faru bai kiɗa ga kowane makadi ba dukkan salailai iri iri da yake sakawa a wakokinsa tushensu mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta gane fasalin waƙa. da tsohon saidu faru ya rassu sai ya dauki gabatar waƙa. ya sa himma da kwazo yana tayi. da saidu faru ya samu cin gashin kansa ya fara da wata waƙa mai daɗin gaske kunshe da tarin hikimomi ga kadan daga cikinta:Tushe Bi da maza dan jodi na iro iro magajin shehu da Bello.  Hasken hitila ba dai da wata ba,. Tauraro haskenka subahin,.  Dawa ya kora dimau na wakili,. Uban sarkin zagi Bello na yari.  Ruwa da kada dibgau na magaji,. Sai tsohon wawa ka shigarsu. Wannan waƙar da ya fara yi ita yayiwa tsohon sarkin yamman faru Ibrahim

    [8:17pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ya salam. Allah ya ƙara sani gafarta Malama.

    Abin da ake nufi shi ne lokacin ƙulla waƙa. An lura Jankiɗi kiɗa yake fara samarwa. Shi ya sa a ƙungiyarsa ake da ƙiryoyi gadaddi.

    Amma, Maidaji Sabon Birni waƙa yake fara samarwa. Shi ya sa waƙoƙinsa suka yi kama da na 'yanmata.

    To, shi ne muke neman a kallar mana Faru a gano nasa rukuni.

    [8:26pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ƙulla waƙa babban ginshiƙi ne a fagen nazari. ☝️

    [8:38pm, 02/03/2024] +234 703 928 3077: Salam, haka ne, don ko a Kamus na Hausa ma'anar kowacce kalma daban, gargara magagin mutuwa, gargare kuma kadada, wato ratsin datse da ake yi wa kunya a gona.

    [9:04pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Jamil.

    Ratsin datse ɗin shi ne gargare a Ƙamusancen, ba farfajiyar kadadar ba. Abin da yake nufi kuma shi ne iyakar kadada ko ƙarshenta.

    Ka ga sun haɗa ma'ana da magagin mutuwa, wanda yake nufin ƙarshen rayuwa ko iyakarta.

    Wallahu A'alam.

    [9:25pm, 02/03/2024] Prof. B.B. Usman: Ni na lura cewa idan zai fara sabuwar waƙa ne yake jagorancin irin amon sautin da za a aza waƙar a kansa ne zai buɗe da kiɗa, amma idan tsohuwar waƙar da yaran sun san ta, sai ya fara da kalaman waƙar.

    [11:36pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Wato dai waƙa da kiɗanta take zuwa. Kiɗan kuwa bai tsaya ga kayan kiɗan da akan rataya ko busa ba. Hannu, da ƙafa da motsin wata gaɓar jiki, da bugun zuciya duk waƙa na sanya musu irin kiɗan da ta ƙunsa.

    [9:02am, 03/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Allah gafarta Malam.

    Kamar yadda kuka karantar da mu, wannan ƙulli ne na lokacin sadarwa.

    Amma, ƙulli na lokacin shiryawa wanda makaɗi kan yi a gida. A nan gizo yake saƙar.

    An lura da wannan yanayi ne kuam sakamakon yadda za ka iya fita wata waƙa ka shiga wata, na makaɗi, ko ta wani makaɗi daban, ba tare da ka tantance ba.

    'Ya'ya da jikokin wasu makaɗan sai suka hutar da kansu neman sabuwar ƙirya ko sabon rauji tunda ga na gado, sai kawai su hau.

    Misali:

    Waƙa nikai ita ni iya,

    Ita za ni wa Sarkin Kano. (S. Faru)

    Da kuma:

    Sarkin Musulmi Bubakar,

    Dattijo Baban Macciɗo. (M. Shata)

    Da kuma:

    Ga Sarki nan an naɗa,

    Kuma ga masoya sun zaka. (S. Kakadawa)

    A hannu ɗaya kuma akwai:

    Dangalin Hausa Ubangijin su Wambai Sarki,

    Mai halin Atto na Bello ɗan Hasan ci fansa. (S. Jankiɗi)

    Da kama:

    Hanƙuri yay yi Jitau muna yaba ma girma,

    ɗauki mulki kai Jallah yan naɗa ba su ba. (B. Tambaya)

    Wallahu A'alam.

    [2:50pm, 03/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Kakan wani ba shi da yaƙi,

    Ko can ɗandaudu na shi,

    Inda dai shahwa kwalli na,

    Da kakanai ka suna. "

    [3:06pm, 03/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Waƙag ga da nam maka Mammadu,

    Na ji daɗinta Mamman Sarkin Kudu. "

    [4:57pm, 03/03/2024] +2348161747863: Allah gafarta, barka da wannan lokaci. Makada Sa’idu Faru makadin Shiri ne. Furniss (1996:177). Haka kuma, a hannu guda yakan shirya waƙa nan take. Makada Sa’idu Faru yakan samu baiwa daga Allah maɗaukakin Sarki yayin shirya waƙa ko tunanin samar da ita, ko kuma ya samu bunƙasar tunani a dalilin tasirin wasu abubuwa da suke kewaye da a muhallinsa. Tun a ƙwaƙwalwa yake fara tsara ta, ta hanyar tunanin kalmomin da za su dace da waƙar da zai samar. Daga bisani kuma, sai ya samar da gangar jikin waƙar ta bin wasu matakai irin na samar da rauji da ga6ar farko ta kalma, sannan kiɗa da kalma (kalmomi) da saɗara da gindin waƙa da ɗan waƙa da kuma ɗiyan waƙar. Wato, matakan ƙulla waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru suna iya kasancewa kamar haka:

    +tunani+jagora+ƙungiya+rauji+kiɗa+kalma+saɗara+G/Waƙa+ɗa+ɗiya.

    [6:08pm, 03/03/2024] +2348161747863: Wannan yasa Gusau (2014) ya bayyana halayyar makaɗan baka na shiri ta kallon yanayin yadda suke shirya waƙoƙin nasu. Yana cewa, “ waƙoƙi na shiri su ne waƙoƙin baka waɗanda ake tsayawa a ke6e, kuma natse a tsattsara su ta yadda za a za6o musu kalmomi da jumloli a ka ko a rubuce, a samar da murya bisa rauji mai nagarta, sannan a ɗora musu kiɗa a kuma bi ta da rerawa”. A bayanin Malam, ya nuna cewa, yawancin waƙoƙin shiri ana fara samar da waƙa ne kafin kiɗa. Allah ne Masani.

    [5:50am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Akwai a cikin Waƙarsa ta Yaƙin Basasar Nijeriya (1967-70) inda ya ke ƙarawa Sojojin Federal ƙwarin gwiwa.

    "Jahag Gabas wada duk

    kun ka shira ta watce..

    [6:38am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Akwai a cikin Waƙarsa ta Marigayi Maigirma Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu.

    " Kwaɗɗo na can na kiran ruwa,

    Ya kakkace kiran su ɗai ya kai....

    [6:42am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Akuɗubɗun Akuɗunɗun,

    ɗan Sarki da wuyan gora،

    Zauna mu ji labarin Ƙayad da kakai Soto. "

    [6:42am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Akwai a cikin Waƙarsa ta Marigayi Maigirma Dagacin Banga, Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar.

    " Kai ni bana sai nayi

    lalaben Kwaɗɗo na kai gaban wuta.

    [6:46am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Gwauron giwa Uban Galadima,

    ɗan Sambo Rungumi,

    Gamsheƙa Amadu na mai Gamji,

    Kai a Uban Zagi. "

    [6:50am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Amma Gamsheƙa ya ce ba Gamshiƙan ba.

    [6:51am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Shi Sarkin Yaƙi Sale Gamshiƙan Sarkin Kiyawa Amadu ne.

    [6:52am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sunansa Sale ba Amadu saboda haka ba zai ce masa Gamsheƙa Amadu ba.

    [6:52am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Mene ne Gamshiƙan?

    [6:53am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Daga kalar Maciji ne.

    [6:53am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Me ne ne Gamsheƙa?

    [6:53am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Maciji Gamshiƙa

    [6:54am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Dabbantarwa ce.

    [6:54am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana: To Gamsheƙa yake a daidaitacciyar Hausa. A ƙara bincikawa.

    [6:57am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Gamshiƙa ne karin harshen da Makaɗin ya faɗi. Daidaitacciyar Hausa kuma ta na nan a wurinta.

    [7:01am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ban da kai ban taɓa jin wani Ɗan Gusau da ke kiran Maciji Gamshiƙa da sunan Gamsheƙa ba.

    [7:01am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Na zo Gusau tun 1978.

    [7:04am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: September, 1978 ya zuwa yau ban da kai ban taɓa jin wani a Gusau yana ambatar Maciji Gamshiƙa da Gamsheƙa ba.

    Amma fa tun da ita ce daidaitacciyar Hausa ba ni da ja, sai dai kuma na riƙe wannan tawa fahimtar a matsayin madogara.

    [7:57am, 04/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haka ne Rankaidade ai wallahi ni tsoro nike ji idan ban san mai lamba ba don kar in yi mai wani abin da bai dace ba.

    [8:00am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ilminka ya amfane ka Dr. Haruna. Allah Ya ƙara yi ma Jagora, amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu

    [8:13am, 04/03/2024] Dr. H. Yelwa: Janzakara ya yi kikiriki

    Ya tare garkag gidan ubanai

    Ya bak KWADDO yana cikin rame

    Ya mirgide tsara

    [8:13am, 04/03/2024] +234 803 637 4958: Allah ya saka da alheri. Misalin homophones a Turanci shine kamar: sort/sought, red/read (past tense), key/quay, check/cheque, principle/principal etc. Akwai kuma homonyms, misali: bank (financial)/bank (of a river), sound (loudness)/sound (good quality as in sound education). In fatar ban saki layi ba.

    [8:34am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Amfani kuma da 'homonym' a waƙa shi na kira salon dibilwa. Misali, Mu'azu Haɗeja a wata waƙa ya ce:

    /Allah kai ka isa da isarka kai ne mai isa/ Ka isar da masu isa isa in sun isa/

    Shi kuma Kassu Zurmi ya ce:

    /Ku ba shi in kuna ba shi/

    /Shayi dai ɗa na/

    /Ba haka munka so ba ɗan yaro/

    /Ai mun san ɗa na tun da anka haiho shi/.

    Dibilwa a Ingilishi shi ake kira "pun"

    [8:50am, 04/03/2024] Mal. B. Lauwali: Ina rokon wannan zaure mai albarka ya taimaka min da bayanin wadannan. Bajimi da amale da Kuma toron giwa. Na gode

    [9:00am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Bajimi ko bajini> namijin nagge kosasshe ake kira bajini amma ga waƙa ko maganar yau da kullum in ana son a yaba mutum akan kira shi bajini, wato ya ƙasura ko kuma na hannun dama, misali Bajinin Bubakar, wato na hannun daman ko ɗan gaban goshin Bubakar

    [9:02am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Amale> raƙumin da ya ƙosa. A waƙa ko maganar yau da kullum ana nufin mutumin da ya ƙasura cinjim

    [9:02am, 04/03/2024] +234 803 257 6475: To ai ko da za 'a yi amfani da daidaitacciyar hausa, su masana harshe sun me ake nufi da Karin harshe, Kuma dole be akwai wanna bambancin. Don haka Kamar yadda ka fada my mum tsayu ga abinda makadin ya fada"Gamshika".

    Kuma a duk inda masanin harshe yake ban taba jin ya kyamaci wanna bambancin ba.

    [9:04am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Toron Giwa> namijin giwa ke nan. A waƙa ko maganar yau da kullum ana nufin wanda ya ƙasura kamar bayanin amale/amali a sama

    [6:40am, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Ina cikin daji sai Gyado ka saƙƙwata ta, Daudu da duy yag ganan ya buɗek ke haƙori.. Inji Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba a faifansa na Marigayi Mai Martaba Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman mai amshi 'Alhaji Ɗan Ali ci fansa, abun biya ka ke ɗan Shehu'.

    [12:17pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Assalamu alaikum!

    Ga mu dai cikin ikon Allah mun sake dawowa wannan zaure mai albarka.

    Muna bayar da haƙuri ga duk wanda muka sosa wa rai. Duk wanda ya sosa namu kuma, mun yafe.

    Allah shi yafe mana baki ɗaya, amin.

    Malamin waƙa ya ce:

    "Albarkar Abubakar,

    Na bat shan hurad da ba nono,

    Ba ni cin tuwo in ba tsokoki,

    A ba ni gumi wanda adda kyau,

    In gasa yatsuna. "

    Gwabron Giwa na shamaki..............

    [1:01pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.

    Madalla, amin ya rabbal alamin 🤲🏾🤲🏾🤲🏾🙏🙏.

    ... A ɓarje gumi wanda da ad da kyau in gasa/in luma yatsu na.... 

    [3:53pm, 06/03/2024] Malama H.M. Kurawa:

    "Kowas samu so ga sarki,

    Ba tambaya akai ba,

    Sai a gani ga riguna nai".

    Bajinin gidan...

    [3:57pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍

    ... Shiryayye Uban Magaji

    Garba ruwan kashin fari/hwari,

    Baban Amadu gizago

    [4:07pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A halin yanzu garin Torawa na cikin Masarautar Birnin Magaji.

    [4:10pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ɗan Isa da Ƙawari kuma suna nan a Masarautar Ƙaura Namoda. Ƙasar Ɗan Isa ke da hedikwata a garin Dogon Kaɗe da laƙabin Sarautar "Sarkin Fulani".

    [5:21pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Jama'a shin don Allah ko Makaɗa Sa'idu Hwaru ya yi wa Sardaunan Sakkwato Amadu waƙa?

    [6:08pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Mu ka kiɗi mu ak kiɗi,

    Saboda mu Allah yaw wa,

    Gudunmawa da waƙa,

    Haw wata na kiɗe/ije wata. "

    [6:46pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora: " Ya mirɗe maza yanzu

    ba mai ƙara ja mai,

    Y/Amshi: Kai ab Bello kai ah Hassan,

    Kai ad da kowa,

    Jagora: Gazagurin gidan Dange...

    Y/Amshi: Duk mai gaba da kai bai

    bakwai bai sha kunu ba,

    Ya mirɗe maza yanzu ba mai ƙara ja mai,

    Kai ab Bello kai ah Hassan,

    Kai ad da kowa,

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa na farko, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Turken Waƙa: Ya mirɗe maza yanzu ba mai ƙara ja mai,

    Kai ab Bello kai ah Hassan,

    Kai ad da kowa.

    [9:03pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Malamin Waƙa ya ce:

    "Wane ba yaro ne ba,

    Shekara sittin yab ba ni,

    Gyaran fuska ka sa,

    Ana ce mai ɗan yaro. "

    Wazame ukku ya aje don gyaran fuska,

    Wanga ya zo da safe,

    Wanga ya zo da rana,

    Wanga guda ko yana zuwa goahon Isha'i. "

    Amshi: Sai na zo in yi mai kiɗi.......................

    [9:05pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Malamin Waƙa ya ce:

    "Wane ba yaro ne ba,

    Shekara sittin yab ba ni,

    Gyaran fuska ka sa,

    Ana ce mai ɗan yaro. "

    Wanzame ukku ya aje don gyaran fuska,

    Wanga ya zo da safe,

    Wanga ya zo da rana,

    Wanga guda ko yana zuwa goahon Isha'i. "

    Amshi: Sai na zo in yi mai kiɗi.......................

    1984.

    [9:10pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍😁👌✊

    Karin Waƙar Marigayi Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III ce ya mai amshi 'Sai nazo in yi mai Kiɗi in ƙaro ilmi, Mamman bajinin Magaji mai takakkay yaƙi' ya yi amfani da shi a wannan Waƙar ta Marigayi Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Muhammad Kabir Ɗanbaba OFR a shekarar 1984. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [9:15pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Tabbas Maigirma ɗanmadami.

    A ciki yake cewa:

    "Lafiya Manyan Hausa,

    Korau mai ɗamarad daga,

    Da gaskiya yaka komi na duniya,

    Bai san ƙarya ba. "

    [9:24pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ina ganin wannan kamar wani salo ne da za a iya dangantawa ga Makaɗa Sa'idu Faru. kalli amshin waɗannan waƙoƙi nasa biyu mabanbanta:

    Koma shirin yaƙi,

    Jandamishin gidan Kure Abdu.

    Da:

    Koma shirin yaƙi,

    Jandamishin gidan Abdullahi.

    [9:44pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne Maigirma Ɗanmasani. Sai dai kamar kusan Makaɗan Baka na da wannan ɗabi'ar.

    Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi irin wannan salon a Waƙoƙinsa na Marigayi Mai Martaba Sarkin Misau Muhammadu Manga da Marigayi Sardaunan Dutsi, Senator Bello Maitama Yusuf.

    Amshin Waƙar Sarkin Misau shi ne "Ci da ƙarfi Mamman Manga ya bi da arna, ƙi sake mazan daga".

    A faifan Bello Maitama Yusuf kuma yana cewa "Ci da ƙarfi Mamman Bello ya bi da arna, ƙi sake mazan daga".

    Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali a faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III (duk da yake ba rerawarsa ba ce, rerawar Halifansa Ummaru Mai Sa'a ce) yana cewa " Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, Abubakar Uban Sarakuna".

    Sai kuma a cikin wata Waƙar tasa ta Dagacin garinsu (Tubali) Magaji Shadawa yana cewa "Tattaki maza ɗan Shehu na Babba, gamda'aren Salau mazan ƙwarai".

    Ba batun Dr. Mamman Shata Katsina ake yi ba, shi da yana iya yi wa mutum 100 Waƙa da amshin Waƙa guda ɗaya, musamman amshin da ya ke cewa "Sadauki Shehu Magajin Mamman" da kuma "Haka nan ne Mamman Ƙanen Idi wan Yelwa". Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [6:30am, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ko alama Maigirma Ɗanmasani. Ta Sarkin Kudun Sakkwato ta riga ta Sarkin Katsinan Gusau domin ko a shekarar 1981 da Malamin waƙa ya je Birnin Magaji wajen Ɗan Alin Birnin Magaji Muhammadu Mode Usman ya rera ta a matsayin Waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a gabanmu. Ta Sarkin Katsinan Gusau kuma ya yi ta ne a wajen naɗinsa a shekarar 1984.

    [7:31am, 07/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Malamin Waƙa ya ƙara da cewa:

    "Sarkin Katcinan Gusau na yau jikan Modibbo,

    Allah yab ba ka duniya,

    Kyauta sai Allah. "

    Amshi:

    Sai na zo in yi mai kiɗi................

    [7:42am, 07/03/2024] Fugus Isa Sarkin Fada: Allah Ya ƙara sani. Mu daliban ilimi muna fa'idantuwa kwarai.

    [8:40am, 07/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Tabbas!

    Manyan Malanmu a wannan fage sun daɗe da lura da wannan yanayi.

    Gusau (2014) ya dunƙule yanayin ya zana masa duna ɗani a Waƙoƙin Baka na Hausa. Ƙarshe kuma ya karkasa shi rukunna.

    ✊✊✊😃

    [9:14am, 07/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Sir! Na tuna wani ɗa:

    "Ka ba ni gida kuma ka ba ni gona,

    Kai mani Sarkin kiɗin Gusau,

    Don in dawo nan,

    In da ko kai hakan ga da,

    Korau ka kyauta.

    Amshi:

    Sai na zo in yi mai kiɗi...........

    [9:55am, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Aikin rinjaya yay yi

    makaye,

    Ya kwan da shirin maza,

    S/Kabi gamda'aren

    Kilodi".

    [10:23am, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Maigirma Ɗanmasani.

    Waƙar Marigayi Maigirma Sarkin Kabin Keɓɓe, Jihar Sakkwato Alhaji Labbo ce.

    Kilodin da yake ambata laƙabin Sarautar wani Ƙauye ne da ake kira Margai a cikin Gundumar Keɓɓe ɗin. Daga gidan sarautar Keɓɓe ake tura wanda ke yin Dagaci a Margai. Shi kansa wanda aka yi wa wannan Waƙar ya taɓa zama Kilodin Margai kafin ya ci sarautar Keɓɓe. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [2:12pm, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa Allah ya gafarta Malam. A Margai ne aka haifi Honorable Alhaji Lawali Labbo, shi ne dalilin da ya sa ake kiransa da sunan Margai ɗin a cikin sunansa.

    Ya taɓa zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato a lokacin mulkin Malam Yahaya Abdulkarim Mni Sarkin Rafin Sakkwato na NRC kafin ya sake dawowa Majalisar har ma ya zama Speaker ko a lokacin mulkin Garkuwan Sakkwato, Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa ne (?).

    [9:39pm, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Tun da muna tattaunawa ne akan Makaɗin Sarakai da Sarakai da Sarauta ne, ga wata ɗabi'a nan ta cire Alkyabba idan wani Saraki ya haɗu da wani Sarakin.

    A wannan bidiyon☝️☝️☝️Mai Girma Galadiman Kano ne, Alhaji Abbas Sanusi aka cire wa Alkyabba yayin da suka haɗu da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR. Ko wane sharhi zamu samu akan wannan ɗabi'ar daga masananmu? ☝️☝️☝️

    [10:09pm, 07/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle irin wannan ɗa'a akwai ta. Haka nan wurin gaisawa da juna. Sarakunan suna sane da waɗanda ke tsaye ƙiƙam da masu duƙawa. Misali, idan Sarkin Kano zai gaisa da Sarkin Musulmi to shi ne zai ɗan durƙusa idan a tsaye suke musabaha, shi kuwa Sarkin Musulmi ya kasance a tsaye ba tare da durƙusawa ba.

    Tsakanin talakkawa kuwa gaisuwa kan banbanta daga nahiya zuwa nahiya. A Kano ko da babba ya miƙa hannunsa ga na ƙasa da shi domin su yi musabaha, to ƙaramin ba zai kama hannun babba ba, saɓanin yadda abin yake a Sakkwato. Na kasa canzawa da nake karatu a BUK. Idan malamaina suka ba ni hannu sai in kama, abokaina Kanawa su kuwa sai na ga duk sun kauce. Wani abokina har da ce min ya yi ai ba a karɓar hannun babba a yi musabaha amma wallahi na kasa yi

    [10:12pm, 07/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ka lura sosai musamman Kano da Zariya. Ban Sam ma Katsina ba

    [10:16pm, 07/03/2024] +234 802 663 3308: Mafi yawanci an fi ɗabbaka wannan al'ada ta girmamawa, a tsakanin Sarki da sauran masu riƙe da sarautu.

    Yana daga cikin girmamawa, idan Basarake ya zo gaida Sarki dole ne ya cire alkyabba, koda kuwa a kan Doki ne za a yi gaisuwar.

    [10:57pm, 07/03/2024] +234 812 462 9009: Wato ɗabi'a ko al'adar saukar da alkyabba idan wani Sarki ya haɗu da Sarkin Musulmi tana faruwa tsakanin Sarkin Musulmi da Sarakunan da aka bai wa tuta daga Shehu Usmanu ko Muhammadu Bello ne. Da na san wannan abun ya kan faru duk lokacin da ɗaya daga cikin waɗannan sarakuna suka ziyarci Sarkin Musulmi a Sakkwato kawai ba a ko'ina suka haɗu ba. Wannan yana nuna cewa da yake shi ne matsayin wanda ya ba su tuta to a lokacin haɗuwar shi kaɗai ne Sarki. Amma da ya buga ya saukar da alkyabbar sai kuma ya mayar.

    [11:00pm, 07/03/2024] Malama H.M. Kurawa: Akwai wani kakana hakimi a masarautar Kano, kunne 2 yake yi. Watarana mun taho Kano da shi, daf da za mu shigo, sai na ga ya lanƙwashe kunnuwan rawaninsa sun koma ciki.

    [9:34am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ko da aka yi Jihar Zamfara Shinkafi da Birnin Magaji ne ba Ƙananan Hukumomi ba daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar 14.

    [9:35am, 09/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Tabbas Maigirma ɗanmadami. Allah ya ƙara girman daraja.

    Babban abin cewa dai shi ne, wannan aiki na Gusau ba zai wadatar ba a wannan taro, domin Fwaru ya rayu na tsawon wani lokaci bayansa da, abubuwa da dama sun faru a rayuwarsa.

    Lalle ne a yi wa aikin kashin ƙanfa a yanzu.

    [9:37am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Anka da Gummi da Bukkuyum da Bakura da Talata Mafara da Maradun da Maru da Bunguɗu da Gusau da Tsafe da Ƙaura Namoda da Zurmi ne Ƙananan Hukumomi 12 da ke yankin Zamfara a lokacin da aka ƙirƙiro ta watan Oktoban shekarar 1996.

    [9:40am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne, yana ɗaya daga cikin aikin da wannan babban taro zai yi In Shaa Allah. Nasan Masananmu da Manazarta suna akan bincike domin ƙwaddamu.

    [9:41am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Daga Kamfani 47 dake Tsohon Lardin Sakkwato, 15 ne ke yankin Zamfara a lokacin da aka ƙirƙiro Jihar Zamfara a shekarar 1996.

    [9:42am, 09/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A lokacin muna makaranta kuma hankalinmu bai yi karfi ba!

    [9:43am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kamfanonan kuma sune:- Anka da Gummi da Bukkuyum da Bakura da Talata Mafara da Maradun da Maru da Bunguɗu da Gusau da Ɗansadau da Kwatarkwashi da Tsafe da Ƙaura Namoda da Zurmi da Moriki.

    [9:44am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Daga baya aka yi kamfanin Birnin Magaji da Shinkafi.

    [9:44am, 09/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: "Ga kamfani ya buda ya kasa ku diba ku tahi! Inji Sani Sabulu Kanoma.

    [9:46am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kamfanin Moriki da Kwatarkwashi da Ɗansadau ba su yi sa'ar zamani ba, sai ba su zamo hedikwatocin Ƙananan Hukumomi ba kamar yadda sauran yan uwansu 12 suke tun gabanin samun Jihar Zamfara.

    [9:49am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla. Makaɗa Abu Ɗan Kurma Maru zuriyar su Makaɗa Ibrahim Gurso Sarkin Makaɗan Talata Mafara kenan. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [9:49am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A shekarar 1987. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [9:51am, 09/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Madallah Hon. Sir. Haƙiƙa Gusau ya kwatanta ga yin adalci saboda ko bayan nuna shekarar da aka buga wannan littafi, ya kuma nuna shekarar da ya shirya shi.

    Kada a manta a 1987 akwai ƙarancin ƙwararrun masu buga littaffai a Arewa, sannan kuma akwai ɓata lokaci kafin a buga ta fuskar kamfanoni da fuskar mawallafa. A halin yanzu ga yadda na san Farfesa S M Gusau a matsayin mawallafi kamar shanshani kuma da ake da kamfanoni masu buga aiki ya fito da kyawo kamar yadda yake buƙata, ina kyautata zaton cewa tsawon lokacin da yake ɗauka ya buga littafinsa bai wuce watanni shidda da yardar Allah

    [9:51am, 09/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Amin Ya Hayyu Ya Qayyum. Ka makadan dauri, shi har makarantar allo yake da ita a gidansa inda yake karantar da yara.

    [9:55am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sai dai waɗan nan Kamfanonan na nufin Gundumar Uban Ƙasa/Hakimi.

    Wasu tun kafin 1903 lokacin da Turawan Mulkin Mallaka na Ingila suka ƙwace mulkin a hannun magabatanmu suke da wannan matsayin, misali Gusau da Kaura Namoda da Zurmi da Anka da Tsafe da Bunguɗu sun daɗe da irin wannan matsayin. Ɗansadau ta zama hedikwatar gunduma ne a cikin shekarar 1939, lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka haɗo garuruwan Kuyambana da Ƙasar Daraga (Ɗankurmi) da Ɗangulbi suka yi Gundumar Ɗansadau da hedikwata a garin Ɗansadau.

    [9:57am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kamfanin da Makaɗa Abu Ɗan Kurma Maru ke magana na Furojet/Waldibankin duniya kuma na nufin Service Center/Gidan Gona/Gidajen gona inda Malamin Taki da Malamin gona ke zama domin hulɗa da manoma.

    [10:01am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla da wannan ƙarin bayani Ranka ya daɗe. Haƙiƙa Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau zaƙaƙuri ne, samuwarsa a wannan bagire ba ƙaramin arziki ba ne zuwa garemu. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    [10:11am, 09/03/2024] Prof. A.B. Yahya: A shekarar da muke karatun M. A. (Hausa) mu biyar, shekara guda ake iya yin sa a BUK, amma mu biyu, da shi da ni, ne Allah Ya ba ikon kammalawa cikin shekarar guda

    [10:19am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe akwai wasu abubuwa da kuke yi kai dashi dake burgeni sosai.

    Kun zamar muna fitila mai haskaka muna domin fita daga cikin duhun jahilci. Ba ku rowar ilimin da Allah ya baku, ba kamar wasu takwarorinku da ke ɓoyon ilimi ba. Allah ya ƙara maku lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    [10:23am, 09/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Gusau saurin wallafa ne da shi, malamin da ya duba shi naci da sauri ne da shi. An gamu an dace ke nan. Ni kuwa kamar kunkuru nike amma mallamin da ya duba ni mai naci ne da sauri. Ka ga ni kamar tursasa ni aka yi😂

    [11:26am, 09/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Yakan fi haka gafarta Malam. A ɗan matsatina na ƙaramin ɗalibin turakarsa ta karatu na san bayan baiwar da Allah ya yi masa a fagen wallafa, yakan ɗauki lokaci sosai yana bauta wa rubutu. Da yawa a raina nake kwatanta shi da Zuhairu Ibn Abi Sulmah.

    [3:01pm, 09/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Wallahi Maigirma ɗanmadani.

    Shekaru fiye da 30, duk lokacin da Gusau yake kan wata wallafa muna ganewa:

    1) Sau da yawa sai dai abincinsa na dare ya iske na rana kan tebur. ƙatshe kuma ko ɗaya ba zai ci ba dai bayan sallar Isha'i.

    2) Idan kuma ya fito ban-iska gad da Magriba, za mu ga jininsa ya tafasa sosai, ba ya son magana da kowa.

    Haka zai koma bayan ɗaki ya zauna shi kaɗai abinsa.

    To, da mun ga haka mun dan akwai sabon aiki tafe.

    Sai dai ina ba wa Malam Gusau haƙuri. In a yi ta kama yi ake yi. Idan baba ta jiƙa kuwa sai rini. 🤣🤣🤣🤣🙏🙏🙏

    [9:04pm, 09/03/2024] Dr. A.R. Bakura: Idan an ce gyara, wato an yi kuskure ke nan. Sai dai a ce akwai ƙarin bayani. Saboda a daidai wannan lokacin Maradun da Bakura duk sunan cikin ƙaramar Hukumar Talata Mafara ne, tamkar yadda Bungudu ke cikin Gusau, Maru ta kasance a Anka. Da fatan an fahimta.

    Shi ya sa muke cewa, Gobir bata cikin Hausa Bakwai. Turawan Mulkin Mallaka ne suka tunkuɗe Zamfara suka kawo Gobir domin su sami gindin zama.

    [12:08am, 10/03/2024] Dr. A.R. Bakura: Idan ana maganar sauran Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau, zan Iya cewa babu na biyunsa. Tun sanina da shi, na san shi mutun ne marar kasala kuma haziki marar ƙeta ga aiki tukuru kamar injin.

    Ina tunawa, muna ɗalibta a A. T. C. Maru, shi ne Shugaban Sashen Hausa, kuma ya koyar da masu share fagen fara karatun EN, SI, I, kuma ga EN, SI, I, 1&2. A ajinmu mun Kai kusan 50, idan ya tara aikin jingar da ya bayar yau gobe cikin ikon Allah zai mayar muku da ita bayan ya gyara kura-kurai. Hasali ma ya ƙayyade ƙarancin shafukan da za a gabatar masa wadanda ba su kasa 10 ba.

    Shi ne malamin da na ga ya ba ɗalibansa handout mai shafi 212, kyauta a daidai lokacin sai da ya yi amfani da keken rubutu aka tafa a sitansil kana aka gurza. Ya yi wa aikin suna: Nazarin Za6a66un Waƙoƙin Baka Na Hausa. An kammala tafa aikin cikin watan Agustan 1984.

    Nawa na nan, har an yi mini tadarishinsa.

    Farfesa Gusau halayensa na gado ne. Ya taso babban gida na ilimi da malanta tare da yi wa al'umma hidima domin gina su.

    Shi ne wanda ya Soma aza ni kan tafarkin bincike da wallafe-wallafen littafin. Har kullum da mun haɗu sai ya tambaye ni sabuwar wallafar da na aiwatar. Muna daɗa rokon Allah ya ƙara masa lafiya da yawan rayuwa mai albarka. Ya Kuma jiƙan iyaye da kakanni. Ya haskaka kaburburansu. Ya arzutta shi da cikawa da Imani. Amin.

    [11:55am, 10/03/2024] +234 803 852 9952: Lallai Farfesa S. M. Gusau kam bai yi rowar ilimi ba. Hannayensa masu albarka sun bai wa alkalaminsa dama ya rattabo mana tarin ilimin da yake kimshe cikin kwakwalwarsa wadda zuciyarsa ta hararo a fagen adabi da kuma tarihi. Allah Ta'ala ya ƙara mana irin su. Allah Ta'ala ya sanya mu a danshinsu.

    [12:02pm, 10/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Na'am. Sirrin shi ne Gusau ya wadatu ne, da baiwar da Allah ya yi masa, ya kuma gode. Ya tsaya inda Allah ya aje shi, ya kuma miƙa wuya ga hukuncinsa.

    Duk kuwa wanda ya ɗauki irin wannan tafarki, Allah ba zai tozarta sa ba.

    [2:02pm, 10/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ikon Allah. Maigirma ɗanmadami. To, lalle ni ne ban ji daidai ba.

    Yadda ka jiya ɗin nan shi ne daidai.

    Ba mujamala ce na yi ba. Ka fi ni nutsa cikin wannan sha'ani. Allah ya ƙara sani.

    [9:32pm, 10/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Wani abu da na lura da shi shi ne irin wannan bayani naka Hon yana da matuƙar amfani. Dalilina shi ne yadda muke saka sunayen 'ya'yanmu ta amfani da sunayen magabata, domin neman lada da kuma tuna baya. Idan zamani ya yi tsawo sai ruɗani ya kutso, shin wanen nan shi ne wane? Idan babu bayanai irin waɗanda kake yi sai a kasa ganewa. Misali, mutane da yawa sun ɗauka cewa Nana Uwar Daje ita ce Nana Asma'u 'yar Shehu Usmanu, alhali wadda ake kira Nana Uwar Daje sunanta Maryam kuma wasu masana sun ce ita ma 'yar Shehu Usmanu ce kamar Asma'u matar Waziri Giɗaɗo.

    [9:37am, 11/03/2024] masters dtj: Gaskiya ni ma na sami waraka daga wannan bayani. Domin a da na yi zaton cewa Nana Uwar Daje ita ce Nana Asma'u. Wallah saboda tsananin ƙauna da nake yi wa wannan baiwar Allah yanzu haka ina da 'yata mai sunan Nana Asma'u. Allah ya gafarta wa magabatanmu.

    [2:44pm, 12/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Kashi bakwai kak kwasa,

    'Yan Sarki na kallo,

    Gidan Bani kai kak kai,

    Ga irin wagga martaba. "☝️☝️

    [4:57am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Kashi bakwai kak kwasa

    yan Sarki na kallo,

    Gidan bani kai kak kai

    ga irin wagga maslaha,

    Dud gidan bani kai kak

    kai ga irin wagga maslaha,

    Ga ka ɗan mai daraja,

    Ga ka jikan Usumanu

    kurɗabi na fodiyo,

    Ga ka Sarkin nasara,

    Ga ka Alhaji Macciɗo,

    Ga jikka ta yi dubu,

    Ga ka mallami ka ke,

    Ga ka mummuni ka ke,

    Abin da Allah duk kai

    ma mutun Baba yai maka".

    [5:31am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa Hon sir. A binciken da na yi na gano ce wannan Nana Uwar Daje sunanta na yanka Maryam, ta kuma haifi ɗiya da aka sa mata suna Maryam. Don haka ita maifiyar aka yi mata laƙabi da Nana Uwar Daje. Nana kuwa laƙabin girmamawa ne kamar Modibbo da ke nufin Malama. Nana kuwa watakila na nufin "shugaba". Wasu wurare ba lalle sai mai suna Maryam ake wa laƙabi da Nana ba. Maryam dai da muke magana a nan 'yar Shehu Usmanu ce

    [5:35am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Madalla da wannan ƙarin bayani Ranka ya daɗe.

    Ita Nana Asma'u matar Malam Usman Giɗaɗo Ɗan Lema tagwaye/tawaye ne, ita da Hassan ɗin ta. Ina kyautata zaton Hassan ɗinta ne mahaifin Malam Halilu Sardaunan Sakkwato na farko wanda Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya fara naɗawa a matsayin Sardauna ya kuma kai shi garin Marnona a matsayin Sarki/Hakimi.

    [5:39am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Hassan ɗinta ya riga ta rasuwa da nisa

    [6:08am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ana iya tabbatar da wannan idan an koma ga littafin: "Collected Works of Nana Asma'u.... " Na J. Boyd da Mark.

    [6:11am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: J. Boyd ta yi wani aiki akan Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III da ke nuna an haife shi a shekarar 1926, ba kamar yadda mafi yawan manazarta/masu sharhi suka tafi akan cewa an haife shi a shekarar 1928 ba.

    [6:19am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Sir! Kamar yadda kuka karantar da mu, wannan ɗabi'ar marubuta ce, musamman tarihi.

    Farfesa Gusau a ayyukansa akwai wurare da dama da ya nuna an haifi Mujaddadi Shehu Usmanu a 1745. A wasu wuraren kuma ya nuna 1754.

    Wasu marubuta sukan buga lissafi ne da shekarar Hijiriyyah, a yayin da wasu kuma suke bugawa da Miladiyyah.

    Wasu kuma ajizanci ne irin na 'yan adamtaka.

    Wallahu a'alam.

    [6:22am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa Maigirma Ɗanmasani kuma hikimar da ke cikin irin wannan lamarin shi ne ke bayyanar da ajizancin da ka ambata, Allah ya datar damu, amin.

    [6:26am, 13/03/2024] Malama H.M. Kurawa: Na taɓa ganin irin wannan, sai na yi zaton musayar gurbi ne: 45/54 daga wajen ɗaɓi.

    [6:31am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Malama wani lokaci akan samu hakan ta fuskar ɗaɓi tabbas.

    [6:38am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Dangane da alƙaluman da Gusau ya bayar a nan ina kyautata zaton cewa rikicin na'ura ne, musamman kwamfuta. Sau da yawa wasu kalmomi masu ƙarewa da "i", ga misali, na'ura kan mayar "i" ɗin da yake karami zuwa babba, "I". Inda Gusau ya shigo a nan bai wuce rashin lura wanda duk marubuci bai tsira gare shi.

    [6:42am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa. Rikicin na'ura ne. A wayata da kwamfuta nakan samu haka muddin ban taskace ba

    [6:49am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Allah gafarta Mal. Ai wasu daga cikin waɗannan ayyuka nasa, an yi su ne tun kafin fasahar Kwamfyuita ta zo mana.

    Amma, ina da yaƙini har ga Allah cewa, akwai wani dalili ko wata hujja da ya dogara a kansu.

    Sau da yawa jigon wallafa kan haifar da irin haka.

    Wallahu a'alam.

    [6:55am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Sake tambayar sa. Gusau mai nazari ne, ba sai ga littaffan Shehu Usmanu zai samu shekarar haihuwarsa ba.

    [7:01am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko mai bugun tafureta kan yi irin wannan tuntuɓe

    [7:04am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Akan samu tuntuɓe har a harshe, a rubuta kalmar Ingilishi alhali harshen da ake rubutu da shi wani ne daban

    [7:15am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Tabbas! Shi ya sa nake cewa, duk abin da ka ga Gusau ya rubuta, yana da hujja kuma mai ƙarfi.

    [7:18am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Tabbas. Ni ban ɗauka abin da Gusau ya rubuta kuskure ne ba. Ban kuma ce ba ya kuskure ba. Amma, ina cewa ne, yana da hujja a kai, domin ba ya ƙwai sai da zakara.

    [7:42am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Waye ni? Ni ɗin me? Me aka yi aka yi ni? Ana babbakar giwa ai ba za a ji ƙaurin kusu ba.

    [10:15am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ƙauna ƙarfi ne da ita. Sai ta hana masoyi ganin laifin masoyinsa ko da rana tsaka, kai ko da wasu na ƙoƙarin su kare masoyin daga abin da ke kusa da shi ba da yinsa ba sai masoyin ya tsammaci liƙa masa za a yi..

    [12:22pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Na taɓa rubuta wata jinga da wani malamina ya ba ni. To da yake Bature ne don haka cikin Ingilishi na rubuta aikin. Sai bayan ya gama gyara ya zo aji da takardata. Kamin ya ba ni sai ya ce in zo in yi masa bayanin wata kalma da ya kewaye da jan biro. Shi dai ga shi Baturen Ingila amma ya kasa ya fahimci wace kalma ce na rubuta cikin aikin da na rubuta cikin Ingilishi.

    Duba kalmar ke da wuya sai na ga ashe Hausa ce na rubuta. A takaice kalmar Ingilishi da na yi niyyar in rubuta sai na rubuta kalmar Hausa da take ma'anar ta Ingilishi ɗin. Wallahi ban san yadda aka yi na rubuta ta ba. Haka ya auku ne lokacin da ina karatun digiri na biyu.

    [12:48pm, 13/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Allah Sarki, ai abin a zuuci yake. Haka ne watarana wani Malamin yana yi mana wata public lecture sai ya yi amfani da kalmar handamise! Sai na ga mutanen kudanci da ba su jin Hausa su fito da dictionary suna neman ma'anar kalmar.

    [12:51pm, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Na taɓa jin wata kalma "Political Gigita" da ake ta'allaƙawa zuwa ga Shaihin Malaminmu Mahdi Adamu Ngaski, Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Ko gaskiya ne shi ya ce hakan, ko ba shi ba ne, Allahu Wa'alam!

    [12:52pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Shi wannan kila da sani ya yi amfani da kalmar. Amma ni ba da sani ba. Ina jin ma kalmar "wanda" ce na rubuta a madadin "which" da yake aikin cikin Ingilishi ne na rubuta ba Hausa ba

    [1:22pm, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ni ma na taɓa ji daga bakin wani Dr. Educationist a Buk, ya ce:.... Handamization.

    Amma wannan ba kuskure ba ne tsananin gwaninta ne a harshe. Malamin yana sane ya yi wa dawonsa miya.

    [1:38pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Idan kana so ka tambai Prof S M Gusau a keɓe, Malam mene ne salon hauhawa? Kuma mene ne asalinsa? Da kyar idan bai sa tambayar mala ba, ko ya ce ka tambai wanda ya turo ka 😂😂

    [1:39pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ba zai faɗa ma ba saboda ladabi. Ko ni ma haka sai kaɗan. Cikin aji ne asalin kalmar

    [2:58pm, 13/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ai ya sade kalmar ko ina yana iya amfani da ita, na san a lokacin mulkin Sani Abacha ne, sai ya "under your regime Muhammad Sani people are allowed handamising government property?"

    [4:04pm, 13/03/2024] +2348161747863: A kodayaushe Malam Gusau yakan koɗa tare da ɗaga darajar abokin karatunsa. Da nuna wa ɗalibai irin baiwa da Allah ya yi masa ta ilimi. Wannan yasa kusan idan ka zauna da Malam Gusau a aji ko a gida, sai ya ba ka labarin wannan aboki nasa mai albarka. Har yakan bada labarin lokacin da suke ajin Baba ɗangambo, a cikin hanyoyin nazarin salo akwai ‘sauka’ da Baba ɗangambo ya kawo, a nan take wannan aboki na Malam Gusau shi ma ya ƙirƙiro sabon salo da ya kira da ‘HAUHAWA’.

    Muna addu’a Allah ya ƙara muku lafiya, ya kuma albarkace mu da ilimin da Allah ya ba ku.

    [7:58pm, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Shi Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar/Sale Ɗan Abu/Salihu Abubakar ya yi Sarauta a cikin 1930s zuwa cikin 1960s. Saboda haka ya shaidi mulkin mallaka na Turawa dake yin D. O/District Officer da a lokacin Jami'in mulki ne a matakin yanki kamar Ƙaura Namoda inda can ne Dagacin ke biya a hukumance.

    Kenan an yi lokacin da D. 0n dake duba yankin Ƙaura Namoda Baturen Ingila (Jan D. O) ne. To shi ne fa Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ke tabbatar ma Sarkin Yaƙi cewa ko kusa kada ya razana ko da kuwa zasu yi arangama da D. O ko da Bature ne ballanta lokacin da aka samu mulkin kai, aka kawo D. O ɗan Ƙasa saboda Ƙasar ai asali tasu Sarkin Yaƙin ce, kowa ya shigo ya shigo cin arziki ne.

    [8:50am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍👍👍

    "Su Boƙoboƙo ana zanne ana kumburin wuya,

    An kashe kunya an bakka kana zanne gungume".

    [8:51am, 14/03/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Gaka sarkin NASARA..

    Gaka MALAMI kake..

    Gaka MUMMUNI kake..

    ƘURƊABI na HODIYO..

    [8:52am, 14/03/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Shin Wai dan Allah mi maƙaɗa ka nuhi da "GUNGUME"

    Ko irin itacen nan da ake ɗaure mahaukata ?

    [8:53am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    "Kashi bakwai kak kwasa yan Sarki na kallo,

    Gidan bani kai kak kai ga irin wagga maslaha,

    Dud gidan bani kai kak kai ga irin wagga maslaha,

    Ga ka ɗan mai daraja,

    Ga ka jikan Usumanu kurɗabi na fodiyo,

    Ga ka Sarkin nasara,

    Ga ka Alhaji Macciɗo,

    Ga jikka ta yi dubu,

    Ga ka mallami ka ke,

    Ga ka mummuni kake,

    Abin da Allah duk kai ma mutun Baba yai maka".

    [8:57am, 14/03/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Yallaɓai ai "GUNGUME" ko daukuwa baiyi ko? 😆

    [8:59am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sai dai mirgina kenan Ɗangaladima. Kaga dai rashin amfani ya sake bayyana.

    [9:01am, 14/03/2024] Sarkin Rafin Gobir Kuɗabi

    Shin Yana kwatanta shi ne da Littafin kurɗabi yu dari zuhudu kaƙi Duniya ɗan malan,

    [9:04am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ƙwarai kuwa Maigirma Sarkin Rafin Gobir domin hanyar Kakansa Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da yake akai.

    [9:07am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kowab bi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a cewar Malamin Waƙa zai tsira duniya da ƙiyama saboda kau horo shi kai akan ayi daidai a kuma daina abun da ba daidai ba tamkar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi na nan a raye.

    [9:34am, 14/03/2024] Sarkin Rafin Gobir Maigirma Danmadami Birnin magaji, niko na yi zaton yana kwatanta muhammadu maccido ne da Littafin kurɗabi saboda tarihin Wanda ya Rubuta shi, kasan abukanai ne guda biyu asalan suna-atare akodayaushe bayanda sukasamu wani dogon lokaci basuhadu ba, da ɗayan yasamu labarin bayan rabuwarsu ɗayan ya yi Arziki sosai duniya tasamu sai shi ɗayan yashiryo Mai tahiya takanas tare da tsara wannan waƙen Wanda idan ka kalura da waken ko littafin gabaɗai yana hani ne da kwaɗayin Duniya da sha'awa abinda acikinta, shine dalilin da Almajirai kayima littafin kirari da zuhudu kaƙi Duniya ɗan malan

    [9:37am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Babu mamaki Maigirma Sarkin Rafin Gobir, dama wannan abun da na gabatar tawa fahimta ce la'akari da abubuwan da aka jero a cikin ɗiyan Waƙar har ya zuwa ƙarshe.

    [9:41am, 14/03/2024] Sarkin Rafin Gobir Duk daine fahimta mu, abin nuhi sakon makada yakai ga maigidansa da Kuma Al'umma sugane cewa mutun ne Mai tawaliu da kaucema kuɗayin Duniya s/m maccido Allah yajikan shi da Rahama

    [3:17pm, 14/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Jama'a, adabi fa ba wahayi ba ne. Muddin manazarcin adabi yana iya kafa hujja ga iƙrarinsa daga adabin da yake nazari, to ya kamata a mutunta ra'ayinsa. Ƙololuwar abin da wani mai nazari ke iya yi shi ne ya kawo wani ra'ayi ba tare da ya soke ra'ayin wani ba. Ta haka ne ilmin adabi ke ginuwa.

    [6:21pm, 14/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Gabas ga Sakkwato,

    Ni Sule mai Zurmi nis sani,

    Ban san kowa ba.

    [12:11am, 15/03/2024] Dr. A.R. Bakura: Wannan zancen fari ne fes ba wani surki. Musamman idan aka yi la'akari da yadda duniya ta zama kusa sakamakon cigaban zamani.

    Bai dace ba a soke wani aikin da magabatanmu suka aiwatar a can baya, ko da mutun yana da kwakkwarar hujja. Abin da ya dace, a fagen ladabi shi ne, sai a nuna cewa, Allah ne bai nufi hannayensu da dafa wannan fage da shi ya kafa hujja da shi ba.

    Wannan shi ne cikakken ladabi a fagen nazari.

    [10:45am, 15/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A rana mai kamar ta yau, 15/03/amma fa a shekarar 1903 ne Turawan Mulkin Mallaka na Ingila suka ci Cibiyar Daular Usmaniya wato Sakkwato da yaƙi wanda aka yi a Giginya. Haka ma dai a wannan ranar ce a shekarar 1903 a garin Dange hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shunin Jihar Sakkwato ta yanzu aka haifi Malam Abubakar ɗan Malam Usman ɗan Malam Mu'azu ɗan Malam Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi wanda ya zama Sarkin Musulmi a ranar 20/06/1938 da laƙabin Sarkin Musulmi Abubakar III.

    Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [11:47am, 15/03/2024] Dr. I.I. Dutsinma: Slm

    Amma kuma wasu littafan tarihin na nuni da 1908 aka ci daukar Usmaniyya da yaƙi

    1903 idan zan iya tunawa an haifi Sarkin Musulmi Abubakar ne a 1903. But i stand to be corrected.

    [11:49am, 15/03/2024] +234 703 232 2222: Wannan maganar ai Babu jayayya a ciki na cin Daular Hodiyawa a alif 15/03/1903

    Babu ko jayayya a ciki

    Akramakallahu

    [11:56am, 15/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu. Allah ya gafarta Malam zance mafi shahara dai shi ne an ci Sakkwato a ranar 15/03/1903 kuma a ranar ne aka haifi Sarkin Musulmi Abubakar III.

    [12:13pm, 15/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Sun tarad da Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I ɗan Sarkin Musulmi Ahmadu (Zaruƙu) ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I/Abubakar Atiku/Mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ke mulki. Ya ci sarauta ranar 13/10/1902 ya zuwa wannan rana ta 15/03/1903 lokacin da ya fita daga Sakkwato zuwa Ɓormi dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Funakayen Jihar Gombe ta yau inda a can ne suka bishi suka kashe shi a watan Yulin shekarar (1903).

    Bayan fitarsa daga Sakkwato ne suka naɗa Muhammadu Attahiru II ɗan Aliyu Babba ɗan Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a matsayin sabon Sarkin Musulmi a ranar 21/03/1903, ya kuma yi mulki har zuwa shekarar 1915.

    Saboda haka idan ance an ci Sakkwato a shekarar 1908, to kenan a lokacin mulkin Sarkin Musulmi Attahiru II ɗan Aliyu Babba ɗan Bello ɗan Shehu ake nufi wanda ba haka abun ya ke ba.

    [12:23pm, 15/03/2024] +234 812 462 9009: Ai yadda maganar take shi ne da yake akwai Sakkwato ita ce helkwatartar Daular Usmaniyya kuma an ci ta da yaƙi ranar 12/05/1903 har ma Sarkin Musulmi Attahiru I ya yi hijira ya bar gari an naɗa wani daga ranar nan ne za ya ɗauka an ci Sakkwato ko da ko ba ci sauran sassan ta ba sai daga baya.

    [8:40am, 18/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Assalamu don Allah a turo man waƙar Malamin Waƙa ta.. inda yake cewa

    Gamshikan Amadu na mai Gandi.

    Can gaba ya ce

    Shi ko tuji da ad da girman baki....

    Dan nan bubukuwa da tar tura

    [10:16am, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Zama Giwa ta fito kiyo tai miƙa ta zo ta sha ruwa,

    Y/Amshi: Kuji Ɗan Zomo na hwaɗin hwaɗama su Tsari, Tsara mu tai gida

    Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,

    Jagora/Y/Amshi: Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,

    Jagora: Gurnanin Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora ɗemuwa,

    Y/Amshi: Ga wani ya yi Kokuwa da wan ƙarfi nai,

    Ya hwaɗi ya kare,

    Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,

    Jagora/Y/Amshi: Tun dai ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,

    Jagora: Ko jiya na iske Gamdayaƙi da Tuji sun iske Jinjimi,

    To sun ko murɗa gardama,

    Sun iske su Bubuƙuwa ruwa,

    Y/Amshi: Dan naan niko ina gaton gaɓa,

    Sai nik kwaɗa gaisuwa,

    Su ko sun daƙile ni dud,

    Niko niƙ ƙara gaisuwa,

    Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya amsa gaisuwa,

    Jagora: Dan nan sai Jinjimi da yad darzaza ya suntule shi dud,

    Y/Amshi: Shi ko Tuji da ad da girman baki yak kwashe Jinjimi,

    Dan nan Bubuƙuwa da tar rura tag gangame su dut,

    Jagora/Y/Amshi: Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,

    Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,

    Y/Amshi: Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,

    Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,

    Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,

    Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Dagacin Banga, Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1934 zuwa wafatinsa a shekarar 1963), Ta Makaɗa Sa'idu Faru mai taken "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi. Rubutawar Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

    Talata, 21/11/2023.

    [2:46pm, 18/03/2024] Malama Maimuna Sulaiman: Assalamu Alaikum Ina yi wa kowa fatar alhairi, Allah ya karbi ibadunmu. Muna ta ƙara godiya ga iyayenmu da Malamanmu bisa wannan namijin ƙoƙari da suke yi. Allah ya saka da aljannah.

    Don Allah Ina neman alfarma idan akwai Mai hotunan tsuntsayen nan, da Makada Sa'idu Faru ya lissafo a waƙan nan ya turo muna. Nagode.

    [3:00pm, 18/03/2024] +234 703 232 2222: Hmmm

    Ai Wagga Magana Bata ko Karin bita akan abunda kahhwadi

    Sai dai Kawai a samu Karin Aiki a group

    Tunda Kowa ya yi Laushi Kamak Karen da yassha Rana 🐶........ 😅

    Maigirma Danmadamin Birnin Magaji

    Ho da hwamag giginya....... 🙈

    [3:06pm, 18/03/2024] +234 703 232 2222: Kabi, Kaabi Kawuce Ba garin Zama ba ta Kanta

    Makiyin Ku Wanda yab bauce Ku....... 😅😁😅😁

    [3:07pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaiki Salam Warahamatullah Wabarakatuhu, amin.

    Za a turo waɗan da ke akwai, a kuma turo sauran da ƙila ba a samun su a wannan yankin namu a halin yanzu sai masana su taimaka muna da sunayensu.

    [3:28pm, 18/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Beguwa. Na taɓa jin ana kiran ta, ƙayam maƙaya. Idan aka rutse ta sai ta sako ƙayar da ke jikinta. Kariyar da Allah Mahalicci Ya yi mata ke nan.

    Ita kuwa bushiya dunƙulewa take yi idan aka rutse ta, duk wanda ya taɓa ya soke kansa. Kada ma komi yunwar da yake ji, sau guda zai taɓa ta bisa rashin sani, ba zai ƙara ba. Na ga haka a TV da ke nuna halittu

    [8:48pm, 18/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Lafiya jikan Usumanu×2

    Mujaddadi na daɗa, Babu kokwanto,

    Farilla ba nafila ta ba. "

    Hattara Sarkin Kudun Hausa.

    [10:41pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Tsuntsun da zai kama kifin kamar zalɓe

    [10:41pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Malam me ne ne Karfasa?

    [10:43pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Mai kasada Zalɓe/Zalɓi...

    [10:44pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Jan tsuntsun nan kuma sunansa Dale.

    Muna yara idan muka je korar tsuntsaye da ke cin gero har waƙa muke yi wa wannan tsuntsun.

    Misali:

    "Dale na ba ni shawa,

    Ba irin buwa ta ba,

    Kafin in jefa bindo,

    Ga dame goma ta ci. "

    [10:45pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Zalɓe tsuntsu ne mai dogon wuya kuma ya fi yin farautarsa a bakin ruwa inda yake kama kifi

    [10:45pm, 18/03/2024] Mal. M.A. Umar Kifin da tsuntsun ya kamo, ana kiransa gargaza.

    [10:47pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Daga cikin hotunan nan akwai:

    Dale

    Buwa

    Shaho

    Mujiya

    Kwala

    Balbela

    Botaro

    Tcaddi

    Waiwaya

    [10:48pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 😁😅🙏... Shi kuma Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba yana cewa "Na ishe Dale tai ƙawa ga jama'at ta ba ƙawa", a cikin faifansa na Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai'.

    [10:56pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ya kan tura ƙafarsa a cikin rame/ramin da ya tabbatar akwai Maciji a ciki. Ya kan gume yatsun ƙafar da ya jefa a cikin ramen/ramin idan Maciji ya haɗiye ta sai ya buɗe yatsun a cikin bakin Maciji ya fito dashi waje abun kalaci ya samu kenan.

    Wannan ɗabi'ar ce ta sanya Bahaushe ke yi wa Zalɓe/Zalɓi kirari "Mai Kasada", har ma wasu daga cikin Mawaƙan Baka Na Hausa su ka saka wannan batu a cikin wasu Waƙoƙinsu.

    Dr. Mamman Shata Katsina a Waƙarsa ta Sarkin Sulluɓawan Katsina/Hakimin Kaita Suleiman Usman Nagwaggo (Sule Jikan Korau) ya ke ce masa "Mai kasada Zalɓe/Zalɓi..../ amshin Waƙar shi ne " Na gode Sule jikan Korau".

    Dale

    [5:38am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Dale

    Mujiya

    [5:39am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Mujiya

    Shaho

    [5:41am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Shaho

    Tcaddi/tcalli/shaboli

    [5:42am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Tcaddi/tcalli/shaboli

    [5:46am, 19/03/2024] Prof. A.B. Yahya: To me ya sa kuma ake kiran wannan tsuntsu da 'yas sha-boli ko 'yatc-tcaddi?

    [6:02am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari A ɗan bayani da na samu shi ne wai tana shan boli (fitsari). Tcaddi kuwa wannan tuma da take yi, domin ba fafiya take yi da ƙafa ba kamar sauran tsuntsaye

    Botoro

    [6:09am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Botaro

    Buwa

    [6:11am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Buwa

    Goto

    [6:14am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Goto

    [11:55am, 19/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Kakan wani ba shi da yaƙi,

    Ko can ɗandaudu na shi,

    Inda dai shafa kwalli ne,

    Da kaka nai ka suna.

    Da madubi nai da hoda,

    Da farar riga da kore,

    Da gani nai ka ga ?????

    Geme cinjim da shuni. "

    [2:24pm, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Katsinawa na da wata rawa da ake yi mai suna "moli" kuma ga dukkan alamu a wajen wannan tsuntsun aka samu wannan rawar

    [2:35pm, 19/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Mu ma Gusau 'yar moli muke cewa da ita.

    [2:44pm, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Ban yi mamaki ba domin Gusau wani yanki ne daga cikin ƙasar Katsina

    [9:20pm, 19/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Wata ƙil kamar flamingo kenan, rawar da wasu jajayen fata suka kwaikwaya daga tsuntsu mai wannan suna.

    [11:26pm, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Salaam. Ina cigiyar wata waƙa da ake cewa:

    "Da kare, da biri da baƙar mussa,

    Suna gardamar dogon bindi,

    Sai tsari yaz zaka yaw wulga,

    Yac ce na fi ku tsawon bindi,

    Tunda ni ka koro maza daji,

    Su bar iri wajen shuka,

    Fakkara tac ce da mun tone,

    Jaka tac ce da mun huta,

    Akuya tac ce ba ku huta ba kam,

    Don saishe mu akai a sawo damma,

    A aza miki dole ki kawo su,

    Jaka tac ce ba dole ba kam,

    Don tuma nikai in yasshe su,

    In sheƙa dole a kamo ni. "

    Don Allah wa ya yi wannan waƙar?

    Ina za a same ta?

    Ina kamun ƙafa ga ma'abuta ilimi na wannan zaure.

    Na gode

    Naku Haruna Umar Maikwari.

    [1:33am, 20/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Akwai dai hikima ta fuskar yadda Bahaushe yake ganin waɗannan dabbobi; da kuma dangantakar rayuwarsu da ta Bahaushe; idan aka natsa za a fahimci cewa mawaƙin ya wakilta wasu rukunan mutane masu halaye daban dabam, da waɗannan halittu

    [3:49am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Jama'a kowai yi tuwon gishiri,

    Da mi yaka kayan miya?

    [5:40am, 20/03/2024] Malama H.M. Kurawa: Malam da ina karantawa sai na ji raujin kamar ba irin na Sa'idu Faru ba. Allah ya sa a dace, mu ji.

    [8:26am, 20/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ba waƙar baka ce ba. Wasu gutsattsarin kalmomi ne a cikin sigar waƙa. Ina tunawa an koya mana su muna Firamare:

    Da kare da biri da baƙar mussa,

    Ana rigimar dogon bindi,

    Sai tsari yaz za ka yar ratsa,

    Yac ce ku tsaya duk na fi ku,

    Ni ne mai koro maza daji,

    Su baro tsabarsu wurin shuka,

    .....................

    [9:37am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haba! Ni fa na kasa tunawa sai waƙar siyasar NPN ta Dankwairo inda yake cewa;

    Da kare da biti da bam mussa,

    Bannar da kukai an gane!

    [10:08am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Jitam mai Ƙaura,

    Garba amanaɗ

    Ɗanmaliki".

    [10:24am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Duhun buda...

    Baya ɓad da Giwa

    ƙarya a kai".

    [10:45am, 20/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Radda kay yi shukka tah hito da mi kaka noman shukat?

    Amsa muna tambayar, mu amsa maka taka.

    [11:05am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora: Da ku masu bakandama

    Da ku masu jalalaini..

    Y/Amshi: Ku tabbata danƙo Mu'azu ya yi ishiriniya

    Jagora: Ni mai ishiriniya ta waƙa

    Danƙo ƙanen Gyaɗa

    mai kwana Kiɗi

    Y/Amshi: Domin ni dai in ana bamu

    ba gajiya nikai ba ramtsat turu nikai,

    In turu yam mace,

    Mu ja attafiyatu azzakiyatu mu sallame,

    Mu ɗauko tabbayyada abilahabi watabbama,

    Mu jawo yash shamsu walluhaha,

    Waƙa muyi ta ɗori sai tai wata guda sai zaƙi takai,

    Cakwai zad daɗin bugu,

    Gwabron Giwa,

    Jirayi gaba ɗan Amadu..

    [1:33am, 20/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Akwai dai hikima ta fuskar yadda Bahaushe yake ganin waɗannan dabbobi; da kuma dangantakar rayuwarsu da ta Bahaushe; idan aka natsa za a fahimci cewa mawaƙin ya wakilta wasu rukunan mutane masu halaye daban dabam, da waɗannan halittu

    [3:49am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Jama'a kowai yi tuwon gishiri,

    Da mi yaka kayan miya?

    [5:40am, 20/03/2024] Malama H.M. Kurawa: Malam da ina karantawa sai na ji raujin kamar ba irin na Sa'idu Faru ba. Allah ya sa a dace, mu ji.

    [8:26am, 20/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ba waƙar baka ce ba. Wasu gutsattsarin kalmomi ne a cikin sigar waƙa. Ina tunawa an koya mana su muna Firamare:

    Da kare da biri da baƙar mussa,

    Ana rigimar dogon bindi,

    Sai tsari yaz za ka yar ratsa,

    Yac ce ku tsaya duk na fi ku,

    Ni ne mai koro maza daji,

    Su baro tsabarsu wurin shuka,

    .....................

    [9:37am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haba! Ni fa na kasa tunawa sai waƙar siyasar NPN ta Dankwairo inda yake cewa;

    Da kare da biti da bam mussa,

    Bannar da kukai an gane!

    [10:08am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Jitam mai Ƙaura,

    Garba amanaɗ Ɗanmaliki".

    [10:24am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Duhun buda...

    Baya ɓad da Giwa ƙarya a kai".

    [10:45am, 20/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Radda kay yi shukka tah hito da mi kaka noman shukat?

    Amsa muna tambayar, mu amsa maka taka.

    [11:05am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Da ku masu bakandama

    Da ku masu jalalaini..

    Y/Amshi: Ku tabbata danƙo Mu'azu ya yi ishiriniya

    Jagora: Ni mai ishiriniya ta waƙa

    Danƙo ƙanen Gyaɗa mai kwana Kiɗi

    Y/Amshi: Domin ni dai in ana bamu

    ba gajiya nikai ba ramtsat turu nikai,

    In turu yam mace,

    Mu ja attafiyatu azzakiyatu mu sallame,

    Mu ɗauko tabbayyada abilahabi watabbama,

    Mu jawo yash shamsu walluhaha,

    Waƙa muyi ta ɗori sai tai wata guda sai zaƙi takai,

    Cakwai zad daɗin bugu,

    Gwabron Giwa,

    Jirayi gaba ɗan Amadu..

    [6:42pm, 23/03/2024] Mal. A.R. Mayana:

    "Gardaye zo ka yi man iso,

    Fwaɗa mashi murna niz zaka,

    ɗan Sardauna jikan Hasan,

    Babban ɗa ga Baura Sarkin Kudu. "

    [10:49pm, 23/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ɗan Sardauna jikan Hassan...

    Ɗan Sir Ahmadu Bello GCON, KBE Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na ƙarshe.

    Jikan Hassan....

    Jikan Sarkin Musulmi Hassan ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    Babban ɗa ga Baura...

    Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    [5:15am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Modibbo Usman ɗin nan shi ne mahaifin Abubakar III. Mahaifin Usman da Hassan guda ne, wato Sarkin Musulmi Mu'azu. Hassan shi ya riƙa Abubakar III kuma kamar yadda al'adun kasar Hausa suka tanada, mutum yana dubin ɗan'uwan mahaifi a matsayin mahaifi. Don haka Abubakar ya kasance mai tsananin riƙon Hassan a matsayin mahaifi kuma Hausawa sun fi ɗaukar mutum a matsayin ɗa ga ɗan'uwan mahaifinsa, dalili ke nan da mawaƙa ke ambaton Abubakar III da ɗan Hassan.

    [6:12am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa Ranka ya daɗe!

    Shi kuma Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ne, kenan Mahaifinsu ɗaya da Sarkin Musulmi Abubakar III.

    Dalilin hakan ne Ɗan Tumba Rungumi ya kwatanta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III da "Babban Ɗa" ga Baura. Allah ya jaddada masu rahama, amin.

    [6:21am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa! Ya kamata a yi wani bincike ta nazarin waƙoƙin baka na tsofaffin mawaƙa, ba na yau ba, da nufin a fito da al'adun Hausawa da m'anoninsu kan shiga duhu ga manazarta da baƙi. Wannan zai iya farfaɗo da wasu kyawawan al'adu da matasa a yau ko dai suka yi watsi da su ko kuma ba su san su ba.

    [6:32am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa Ranka ya daɗe wannan abun so ne ko da lamurran da muke ciki na gushewar kawaici da mutunci na samun kwaskwarima.

    Ina iya tunawa a watan Afrilun shekarar 1996 bayan an ayyana Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III a matsayin sabon Sarkin Musulmi, ni da sauran abokan aikina da ke ɗauko rahoto daga Fadar Gwamnatin Jihar Sakkwato muka tarbi Sarkin Sudan Na Wurno Shehu Malami domin muji ta bakinsa akan lamarin.

    A cikin tambayoyin da muka yi masa akwai wadda muka ce masa mun yi tsammanin shi ne zai kasance sabon Sarkin Musulmi bayan cire Sarki Ibrahim Dasuƙi. Amsarsa ta bamu mamaki matuƙa, domin ya sanar damu cewa "muddin ɗiyan Sarkin Musulmi Abubakar III suna buƙatar wani abu, to ni kuma na ba wannan abun baya har abada, kuma zan yi iyakar yi na domin ganin sun mallaki wannan abun, saboda ban san daɗin Mahaifina ba kamar yadda nasan daɗin Mahaifinsu". Allahu Akbar!!! Allah ya jaddada masu rahama, amin.

    [7:04am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Maigirma Ɗanmasani.

    Ko an san dalilin kiran Shehu Malami Sarkin Sudan da laƙabin "Na'aɗɗa kuwa?

    [7:17am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Daga wata hadimar gidansu ce da ake kira "Aɗɗa" wadda ita ce ta yi hidima dashi tun bai wuce ɗan shekara biyu zuwa uku ba.

    Mahaifiyarsa ta rasu ne wajen haihuwar ƙanwarsa dake bi masa, saboda haka ita "Aɗɗa" ce aka damƙawa alhakin kula dashi. Wannan ne dalilin shaƙuwarsu har ya kasance ana kiransa da nata, wato "Na'aɗɗa".

    A wata tattaunawa da na yi da ita ta nuna mani jin daɗinta na ganin akwai sunanta a cikin sunan Sarkin Sudan Shehu Malami da ya sanya sunan nata ya shiga duniya. Ta kuma bayyana godiyarta zuwa ga Sarkin Sudan Shehu na yadda ya riƙe ta da amana da mutunci da kyautatawa.

    [7:33am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Sunan Maton Sarkin Sudan alferi ya hi mugunta".

    [7:34am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Aikin Bunza manazarta da dama sun yi irinsa kamin sa. Abin da nake nufi a karaɗe waƙoƙin mawaƙa da dama da nufin zaƙulo tarin al'adun Hausawa da ke neman su shige duhu. Misali, a kan wace al'ada ce Hausawa ba su cika ambaton sunan mahaifa ba? A wani taro da na taɓa halarta a kan waƙar Najeriya ta Shehu Shagari kuma shi ma yana wurin a matsayin baƙo na musamman, an gabatar da shi da sunan, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Lokacin da zai yi jawabi sai ya fara da cewa sunansa Shehu Shagari.

    Haka za ka yi ta gani ga magabata, kuma akwai ƙalilan cikin matasan yau, suna yin haka. Akwai Ibrahim Gusau da Abdu Sakkwato da Yahaya Gusau da Abubakar Imam da Sa'adu Zungur da Mu'azu Haɗeja da Yusufu Kanta da mafi yawan sarakunanmu. Babu sunayen mahaifa liƙe ga sunayensu. Na ga Prof. Ibrahim Muhammad Malumfashi yakan rubuta Ibrahim Malumfashi kwanan nan.

    [7:35am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Sosai! Musamman kafin Hausawa su iya karatu da rubutu

    [7:48am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Su kansu mawaƙan abin ya shafe su: Salihu Jankiɗi da Musa Ɗanƙwairo da Ibrahim Narambaɗa da Aliyu Ɗandawo da Barmani Coge da dai sauransu

    [12:01pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Masu yin ma Hausawan ne. Mai da ruwa rijiya ba ɓanna ba

    [12:03pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haka ne. Waƙar ma na cikin al'ada. Ta cika ta batse ne saboda haka ta zama mai cin gashin kanta!

    [12:05pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Mamman Gawo Bahaushe ne da ya iya karatu da rubutu.

    [12:25pm, 24/03/2024] +234 806 409 4889: Na zaka in yi ziyara,

    Ganin Muhammadu ni daɗi yaka yi min,

    Inda duk giwa tat tashi tay yi girgiza,

    Tai mika tar rufe wuri,

    Sai ka ga yan namu suna gudu suna kwanto wasu na kare wasu.

    Karyar banza rijiya takai,

    Ruwa na gulbi na garainiyya.

    Kamfarakin Sarkin Kiyawa ginshikin alkali,

    Baba gwarzon Galadima zaure mijin gida.

    Ga waƙa nan wadda nay yi ma,

    Da, tara ta mun bar takwas gida,

    Sai in kai murnan zakkuwarmu,

    In aika ko yanzu su taho,

    Mu ka kiɗi, mu ak kiɗi saboda mu,

    Allah yay yi wa gudummuwa,

    Da waƙa ha wata na ije wata.

    Taron bara da munka zo Kaduna,

    Ka ciri lamba naj jiya kwarai,

    Sarkin Yawuri dai aka fadi,

    Uban tafiya lardin wadanga duk,

    Sarkin nan ya kammala kwarai da kyawo,

    In ji wadan Rigachikun,

    Sa'ad da Bature yay yi dariya,

    Da yag ga mutane Yawuri,

    Suna da haske ga wasu na ta wagara.

    Ga wani sarki ba shi da zagi,

    To kuma sannan bai da guzuri,

    Garin rogo dai suka ta ci da guru,

    Kowane na aza ruwa.

    Taho da shirin daga,

    Ginshikin Galadima namijin jiran maza,

    Amma shi ko har da dama dama,

    Ga wani sarki na ta kumburi,

    Da yaranai sun sha mashi fura.

    Ga wani kambolon uban kasa,

    Da yara nai wajjen guda hudu,

    Ba ko mai suturar kwabo hudu,

    Ya shiga mota ya yi tagumi,

    Da kwandon dunya yay yi guzuri.

    Na zaka in ziyara,

    Ganin Muhammadu ni daɗi shi ka yi min.

    Allah bar min Mamman na Audu,

    Mu kuma Allah bar mashi muwa.

    ________

    Barkan mu da hutun karshen mako

    Allah ya karbi ibadan mu

    Mu sha ruwa lafiya.

    [9:25pm, 24/03/2024] Alh. A. Nakawada: Congratulations to the organisers in advance.

    Allah Yasa wanga taro ya gano muna 6oyayyun wakokin Sa'idu Faru, wadanda ga alama wasun su sun salwanta. Wasu kuma zasu salwanta idan ba ayi himma aka taskace su.

    Misali, akwai waƙar nan da nake ta jan hankali akan ta, mai amshin: "na zaka in yi ziyara wurin Galadiman Birnin Kano

    Arna tsoro nai su kai". Ita wannan waƙar wasu bayanai masu qarfi sun nuna Galadiman Kano wanda Tijjani Hashim ya gada, aka yi wa ita. Ance kuma mutumin Sa'idu Faru. Na tabbatar kuwa a zaman shi da shi ya yi mashi waƙa fiye da ɗaya. Akwai ire-iren wadannan wakokin da ya kamata mu yunqura mu zaqulo domin taskacewa.

    [9:38pm, 24/03/2024] +2348161747863: Assalamu alaikum. Allah gafarta malam barka da war haka. Makada Sa’idu Faru wace waƙa kuwa ya yi ta karshe a rayuwarsa kuma wa ya yi wa ita?

    [10:04pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle kam! Ashe haƙata ta kusa cimma ruwa: Taron nan na Sa'idu Faru da Waƙoƙinsa ya roƙi Jami'ar Tarayya ta Gusau ta naɗa Hon Ɗanmadami a matsayin Rumbunan Waƙoƙin Hausa na Baka!

    [1:37am, 25/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko waɗanne waƙoƙi suna da wannan matsala ta salwanta. Na baka kan salwanta saboda a ka suke ba a rubuce ba; su kuwa rubutattu mafi yawan mawallafansu ba su cika damuwa da baza su ba, musamman masu ilmin Addini. Ba wai ba su sha'awar su ba, a'a taƙwa da tsufa kan yi tasiri ga haka. Amma waɗanda suke ganin waƙoƙinsu wa'azi ko nasiha ne ƙwarai sukan so su taskace su su baza su. Misali, Wazirin Gwandu Alhaji (Dr.) Umaru Nassarawa Birnin Kabi da Ɗangaladinan Wazirin Sakkwato Alƙali (Dr.) Bello Giɗaɗawa ƙwarai suka so ganin an taskace waƙoƙinsu a diwanoni. (B. B. Usman yayin bincikensa kan waƙoƙin Wazirin Gwandu, A.B. Yahya yayin nasa bincike kan waƙoƙin Dangaladima da kuma tattara diwanin mawallafin, duk sun tabbatar da haka.)

    [1:44pm, 26/03/2024] Mal. M.A. Umar Assalamu alaikum...

    Ko ana samun ɓurɓushin Hadisi a wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru? Idan ana samu, ina miƙa ƙoƙon bara.

    [1:51pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu. Daga cikin Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi "Kana shire Baban Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo" aka samu waɗan nan ɗiyan Waƙar 👇. Me za a kira wannan kenan?

    Jagora: Alhamdulillahi shukurni

    Y/Amshi: Rabbil alamina ni nau nuhi,

    Jagora/Y/Amshi: Ka san Kiɗi ba karatu ba na,

    Mui astangafari in mun gama,

    [1:53pm, 26/03/2024] Mal. M.A. Umar A tura mana ire-irensu, za su taimaka wajen fito da abin da ake hasashe insha Allah!

    [1:56pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Malam suna yi ke nan?

    [2:05pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A duba wasu daga kalaman "Jagora" a cikin waɗan nan ɗiyan Waƙar ƙila a dace da ɓurɓushin abun da ake nema Malam. ☝️

    [2:33pm, 26/03/2024] Prof. A.B. Yahya: To Dr. Muhammad Arabi Umar, ya kamata ka yi muna tsokaci kana danganta waɗannan hadissai da ɗiyan waƙar. Zan yi mamaki in ƙaru ƙwarai kuma in sake tunanina kan zurfin ilmin Sa'idu Faru.

    [2:44pm, 26/03/2024] Dr. S.S. Abdullahi: Salam, wani dalibi kuwa yana farautar "Karin Magana a Farfajiyar Tafashen Sa'idu Faru" wadanne daga cikin wakokinsa ake samun wadannan diyan Waƙa? Hon Danmadamin BMJ Bismillah!

    [2:57pm, 26/03/2024] Prof. A.B. Yahya: A hasashena kusan duk inda ka ji Faru ya kawo maganar dabbobi ko tsuntsaye ko zambo to to ba za a rasa karin magana ko tatsuniya ciki ba.

    [3:52pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora: Mai kabrak Kiɗi zo ka sha Waƙam mu kyauta/banɗas

    Y/Amshi: Kuma in baka kuɗɗin Kiɗi Dogo da wayo...

    [3:55pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jagora: Na ishe Dale tai ƙawa ga jama'at ta ba ƙawa...

    [4:00pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Duka al'amarin duniyag ga ko mi na ne,

    Wani mayen wani...

    [4:02pm, 26/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Salaam. Ko me Sa'idu Faru ya ce game da gine-ginenmu?

    [4:12pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:.... Kuma ka bani Rihenin da zamu ci tare da barwai na.... A cikin Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba mai amshi 'Gwabron Giwa na Shamaki baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daga'.

    [4:23pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Zama kai ag ginshiƙi, kana tsaye bango baya razana ko da an shekare ruwa.../Ga bangon Shigafa nan. Ya yi wannan kalamin ne a cikin Waƙar Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar mai amshi "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu Na Maigandi Kai aa Uban Zagi '.

    [5:08pm, 26/03/2024] Mal. H.U. Maikwari Lallai akwai abin da ya dace a tsinta a wannan ƙaulin.

    Mun godiya Maigirma Hon (Dr) Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji. Ɗanmasanin Waƙar Baka.

    Bajinin Adabin Baka.

    [5:40pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042:

    "Zama ɗaki ko yana ruwa,

    Muazu ai ya dara wuri,

    Koda Sarkin yaƙi na yi man rowa,

    Na bar biyar wani"

    [6:54pm, 26/03/2024] +234 705 558 5055: Allah Ya ƙara sani Dr. ko a kwai in da Sa'idu Faru ya kawo baitoci masu dauke da sifofin launi

    [7:21pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: Kakan wani ba shi da yaƙi ko can Ɗan Daudu na shi

    Y/Amshi: In da dai shahwa kwalli na da Kaka nai ka suna,

    Da madubi nai da hoda,

    Da hwarar riga da kore,

    Da gani nai ka ga Kure,

    Geme cinjim da shuni

    A cikin Waƙarsa ta Marigayi Maigirma Sarkin Zamfaran Zurmi Suleimanu Muhammadu Sambo mai amshi "Babban Bajinin Gidan Sambo shirinka daban da raggo, jikan Mamudu Sarkin nasara Baban Baraya".

    An samu kalar fari da shuni/Ɗanyen haki a cikin waɗan nan ɗiyan Waƙar.

    Kore da ya ambata anan ba na launi ba ne, na nau'in sutura/riga ne.

    [7:37pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kamar haka na ce Malam Imrana. Barkammu da shan ruwa dafatar Allah ya karɓi ibadunmu, amin.

    [7:41pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Barkan mu juna ranka ya daɗe. Sai naga kamar kore

    [7:43pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Akwai Koren akwai Kuren a cikin ɗiyan Waƙar.

    [7:53pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Koren na launi da kure na Sarkin fawa

    [7:56pm, 26/03/2024] Alh. A. Nakawada: Toh. Ai na aza kure na hyena 🤔

    [7:57pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Halayyar su guda, duka biyu.

    [7:57pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A'a, Kore ba na launi ba ne a wannan bagiren. Kalar Riga ce da ake kira Kore. Ya ambaci riguna guda biyu, farar riga da kuma kore, kenan farar rigar na iya kasancewa Kwakwata ko girken Nupe ko girken Zazzau sai kuma gashi da wata rigar nau'in/siffar da ake kira Kore, gemen nashi kuma cinjim da kalar Shuni. Shi kuma ya zama Kure/Sarkin Fawa/Mahauci/Barundaye/Barunje/Barunji/Runji.

    [7:59pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Lalle akwai riga kore

    [8:00pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Siffar shigar Sarkin Fawa ce ya kamanta.

    [9:17pm, 26/03/2024] +2348161747863: Makada Sa’idu Faru bai fiya baddala nassin hadisi ba a cikin wakokinsa sai dai ya yi ishara ga nassin ko ya furta wasu kalmomi wadanda za a iya karfafar su da nassin hadisi. Amma bai fiya kawo hadisi kai tsaye ba ko a baddale.

    [10:40pm, 26/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ashe? Kore ai rigar ta samu sunan ne daga launin kore, wato tsana (launin shuka)

    [6:14am, 27/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ikon Allah! Ranka ya daɗe ashe riga kore sai mai kalar shuka/launin kore?

    [6:24am, 27/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ganin na yi kuna maganar launi na ga kamar ba ku gane Sa'idu Faru yana maganar riga mai launin kore yake nufi ba. Kore kuwa tsanwa ake nufi, akwai sutura kore kuma ga da kore abin ƙawa ne (kila har ga yau). Ko ka lura da wani rawani sa Sardauna yake naɗawa?

    [6:28am, 27/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ƙwarai kuwa na san wannan rawanin na Marigayi Maigirma Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello GCON, KBE.

    [6:54am, 27/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Amma ko ni ne ban fahimci Sa'idu Faru ba Hon. ? Don Allah faɗa mini don kada in zauna cikin duhu

    [7:08am, 27/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A'a Ranka ya daɗe ƙila taka fahimtar kai da Malam Imrana Mukhatar Mafara ce daidai bisa ga tawa.

    [12:00pm, 27/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Kore a ma'ana ta harshe na nufin kalar tsanwa.

    Amma a ma'ana ta fannu kamar yadda Makaɗa Sa'idu faru yake nufi wata nau'in riga ce da aka rina sosai da baba har tana walƙiya.

    Wasu Hausawa kai tsaye suna ce wa wannan riga baƙa.

    Dubi abin da Dr. Mamman Shata ya ce:

    "Kyawon dattijo ya sha shuni,

    Tsoho ko yai fara da baƙa. "

    Rawanin da aka yi masali da shi irin wanda Sardauna ke naɗawa shi ma irin wannan rini ne ake yi masa. Amma, sunansa 'ɗankura'

    Tabbas, riga fara da kore/baƙa da rawani ɗankura kayan ado ne na ƙasaitattun rundawa. Amma, an wayi gari duk wanda ya ji gishiri, na iya caɓawa.

    Barkarmu da Asuba.

    [9:46pm, 27/03/2024] Mal. A.R. Mayana: "Fwarin maciji cizonka ba dahi,

    A yi gumba a sha a samu lafiya,

    Gumba ko ba cizon ƙwaro taimako takai. "

    [3:22pm, 29/03/2024] Malama H.M. Kurawa: "... Ka kai kamab Bello ka gadi Moyi,

    Saura ka kai,

    Inda Maihausa yak kai".

    Bajinin gidan Bello,

    Mamman na Yari,

    Sarkin Kudu Macciɗo,

    Ci maraya.

    1. Wane ne Bello kuma wane ne Moyi? Yaya nasabarsu take da Macciɗo?

    2. 'Maihausa', wa yake nufi, menene cikakken sunansa?

    Na gode 🙏

    [3:40pm, 29/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 1. Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi kenan. Mahaifin Baban Kakansa, Sarkin Musulmi Mu'azu ne. Domin Sarkin Musulmi Mu'azu ne ya haifi Modibbo Usman wanda ya haifi Sarkin Musulmi Abubakar III wanda ya haifi Muhammadu Macciɗo. Shi kuma Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne.

    1 (b). Muhammadu Moyin biyu ne ko uku. Ɗaya shi ne Muhammadu Moyi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio wanda ya taɓa riƙe muƙamin Sarkin Kabin Silame a lokacin Ribaɗi. Silame hedikwatar gunduma ce a Ƙaramar Hukumar Mulkin Silame dake Jihar Sakkwato a halin yanzu. Bayan tashin/fitar Kabawa daga hedikwatarsu da ake kira Surame wadda Sarki Muhammadu Kanta ya girka a cikin ƙarni na 16 (a halin yanzu kufai/kangon Surame na nan a cikin Ƙasar Silame ta yau). Babu mamaki daga Tsohuwar Surame ce Silame ta samo wannan suna nata, Allahu Wa'alam!

    Akwai Muhammadu Moyi daga zuriyar Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio wanda ya taɓa riƙe muƙamin Sarkin Bauran Dange. Akwai kuma Muhammadu Moyi da ya fito daga zuriyar Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio. Shi ne Kakan Marigayi Mai Martaba Sarkin Kayan Maradun Ibrahim Maigandi II wanda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi wa waƙar nan mai amshi " Jikan Moyi Iro ɗan Mamman tura haushi, ja gaba tsayayye". Ya yi Sarkin Ƙayan Maradun daga shekarar 1923 zuwa 1929. Shi ne Mahaifin Malam Fadama Nuhu wanda ya haifi Marigayi Sarkin Ƙayan Maradun Ibrahim Maigandi II da muka ambata a sama.

    Saboda kasancewar dukan Moyin guda uku sun fito ne daga Zauren Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi duk wanda aka aza a wannan gurbin yana iya shiga domin shi ma Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III daga wannan Zauren ne ya fito. Allahu Wa'alam!

    2. Mai Hausa a wannan ambaton shi ne Mahaifin Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo, wato Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III domin shi ne jagoran Tutocin Shehu Mujaddadi a lokacin da aka yi wannan Waƙar. Yammawa kuma suna kiran Sakkwato a matsayin Hausa tun bayan kammala Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya. Allahu Wa'alam!!!

    Danganta shi da ya yi da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio cewa "ka kai kamab Bello... ina ganin fata ce na ya kasance Sarkin Musulmi.

    Inda kuma ya ke cewa "Ka gadi Moyi.... Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya yi hakimci a Talata Mafara daga shekarar 1953 zuwa 1956 da aka ɗauke shi. Kenan da Muhammadu Moyi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda ya yi Sarkin Kabin Silame da Muhammadu Moyi dake gidan Sarkin Musulmi Mu'azu wanda ya yi Sarkin Bauran Dange da Muhammadu Moyi ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Attahiru/Atto ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda shi ma ya yi Sarkin Ƙayan Maradun duka dai sun yi hakimci ko sarauta kamar yadda Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya taho daga bayansu ya yi.

    [10:04am, 06/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Alibawa kuna ganin hwansak ku wurin Sule babu dama, Giwa ta sha ruwa tai miƙa ta taushe gurbi.... Inji Ɗan Umma Uban Kiɗi a faifansa na Marigayi Maigirma Sarkin Zamfaran Zurmi, Suleimanu Muhammadu Sambo mai amshi ɓabban Bajinin gidan Sambo shirinka daban da raggo, jikan Mamuda Sarkin nasara Baban Baraya'. Allah ya kyauta makwanci, amin. A wannan hoton ga Giwa nan ta sha ruwa ta na neman ta taushen gurbin.

    [10:17am, 06/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Daudu kullun mahwalki nikai sabo, Shehu ya bamu doki da kaya nai, Danda hwari biyat wanda an nan haka, inda Liman ka bi zai Masallaci", cewar Ɗan Tumba Rungumi a Waƙarsa ta Marigayi Maigirma Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo mai amshi 'Shehu Ɗan Shehu ganɗon ƙasah Hausa'. Wannan shi ne Dokin da ake kira Danda fari biyar domin duka ƙafafunsa na da kalar fari da kuma fari a goshinsa.

    [11:11am, 09/04/2024] +234 803 852 9952: Abubuwa da dama suka haifar da haka. 1. Mutanenmu sun saba yin abu a kirarren lokaci. 2. Halin yau: galibi mutane sun rage sha'awa ga harkar bincike sosai, sai dai a yi ta shiga aji kawai. Shi din ma a daburce. Amma wannan gwamnati ta jawo. 3. Galibin Malamai suna halarta irin wadannan tarurruka ne domin fafutukar neman "promotion". Da zarar an haye, shike nan. 4. Sha'anin tattalin arziki da tsadar rayuwa da kuma halin firgici da ake ciki na rashin tsaro a kasar da kuma yankin. Kila wadannan abubuwa ne suka jawo jinkirin. Amma kar a fitar da rai. "Gate crushers" suna nan tafe.

    [7:25pm, 11/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: @ Malam Murtala Isa. Muna maka maraba da shigowarka wannan Zaure da wannan Waƙar ☝️wadda ita ce Waƙar Makaɗa Sa'idu Faru ta farko bayan ya fara jagorancin Ƙungiyar Kiɗa ta gidansu daga Mahaifinsu, Makaɗa Abubakar Aliyu Mai Kotso/Abubakar Kusu a cikin 1940s/1950s. Waƙar Dagacin Ƙauyensu (Faru) ce, watau Sarkin Yamman Faru Ibrahim Abubakar/Mai Abu Faru ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Bubakar/Abubakar ☝️

    [7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.

    [12:48am, 14/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Dukanku ku biyu bisa hanya kuke. Abin la'akari shi ne da baiti da ɗa ra'ayi ne, babu wanda yake wahayi. Kowa ya yi rawarsa tare da hujja ko hujjoji.

    [6:38am, 14/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Maigirma Ɗanmasani barka da kwana da fatar munyi Sallah lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu ya jiƙan magabatanmu, ya shirya muna zuriyarmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Ina goyon bayan Ranka ya daɗe akan wannan batu domin abun duka ƙirƙira ne kamar theories da masana ke kawowa su kuma tsayu akan su ta hanyar kafa hujjojin da mabiyansu ko ɗalibansu zasu dogara dasu wajen watsa su domin al'umma su aminta dasu.

    To tunda abun kamar mashaba/mashabobi ne kenan kowa na iya ɗaukar abun da ya sauƙaƙa a wajensa.

    [7:50am, 14/04/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Shi dai baiti an riga an saba da shi domin shi ne tushe, da ko diyan waƙa kuwa daga bisani ne ake son su tsayu.

    [8:44am, 14/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni matsalar da ta daɗe wurina ina ta tawan ta ita ce, "Idan aka samu waƙar mawaƙi da rerawa da dama, watakila ya kamata manazarcin ta ya natsu ya tsamo ɗiyan da wata rerawa ta ƙunsa amma babu ga wata rerawa ya saka. Har nakan yi tunani cewa da yake mawaƙi guda ne ya rera dukansu, yin haka ba aibu ba ne. Yanayi, da haliyyar mawaƙin, da tasirin wanda aka tsara waƙar don shi a kan mawaƙin, da tasirin masu saurare kan mawaƙin (shin a gaban wanda aka tsara wa waƙar ko kuma ba a gabansa ba ne mawakin yake rera waƙar, misali a dandalin wata jami'a ne amma ba a gaban wanda aka tsara wa waƙar ba), duk waɗannan dalilai ne masu haifar da wata rerawa bayan ta farko.

    [11:12am, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada: Yalla6ai, ni na yarda "ɗan waƙa'a" ne daidai bisa ga kasancewar akasarin masana sun amince da hakan.

    Shi yasa nace: "Na sani. Amma na fi son in yi amfani da baiti" musamman a irin wannan informal setting.

    Amma kamar yadda nace a can farko, nafi jin daɗin in yi amfani da baiti. Watakila saboda shi na saba dashi kuma ya fi sauqin rubutawa, da saukin faɗa da baki, kana an fi saurin gane abin da mutum yake nufi😬

    [7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.

    Shirin yaki

    [11:41am, 14/04/2024] Mal. M.A. Umar Ni kiɗin yaƙi niy yi ma,

    Abu na Isau,

    Ba ni son,

    Kana zannawa banza,

    Ka ɗauki takobi,

    Da bindigogi da bakunkuna,

    Ka sa sirdi,

    Ba mu sansani,

    Sai bakin Tsabre,

    Kano da Katsina,

    Kwantagora,

    Hab Borno,

    Riƙon Namoda na,

    Shi na hac can,

    Garba ka amshe riƙon,

    Dud da Ummaru,

    Ummaru yab bar ma,

    Garba ka hisge riƙon,

    Dud da Ummaru,

    Ummaru yab bar ma.

    Amshi:

    Gwauron giwa na Shamaki,

    Baba Uban gandu,

    Abu gogarman Magaji,

    Mai kansakalin daga.

    [2:26pm, 14/04/2024] +234 806 951 3160: Allah ya gafarta Malam, daɗin daɗawa, mai nazari ka iya dubawa ya ga ƙari ko ragin da aka samu a rerawar a waƙar farko ce ko a ta biyu.

    Misali, idan a waƙa ta biyu aka samu ragi, a iya hasashen matuwa, kasancewar ajisancin ɗan'adam ko kuma mawaƙin yana sane ya yi haka saboda wasu dalilai da za a iya ji daga gare shi ko waninsa. Ko shi manazarcin ka iya tsinkayen dalilin yin ragin. Haka ma samun ƙarin ɗiya a rerawar waƙar ta biyu.

    [2:40pm, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada: Nima na ta6a yin irin wannan tunanin na haɗa hancin versions na waƙa da aka rera ta a lokuta daban-daban. Sai na fahimci abin zai yi wuya. Dalili kuwa wasu wakokin ana maimaita su da yawan gaske. Sannan kuma banbancin lokacin da aka yi su ana samun tazara. Sannan za a iya samun matsalar sanin inda za a dasa wasu baitocin, saboda ita ma waƙar tana da structure da Makadi ya yi mata. Ya tsara yadda zai bude ta, ya tsara abun da ya ce ya fada bayan ya bude ta, ya tsara daidai inda ya kamata ya yi zambo ko ya kawo salo, ya tsara inda zai yi wata doguwar gangara ko hira, ya tsara wurin dai zai shigo da gaisuwa da godiya ga mutanen shi ko ambaton masoya da yanuean wanda aka yi wa waƙar da dss. Sannan wasu baitocin ba tsayayyun baitoci na waƙar ne ba. Suna kawo su ne saboda wasu dalilai da suka waƙana a lokacin da ake rera waƙar. Daga nan kuma sun ajiye wadannan baitocin ba za su sake maimaita su ba.

    Inda wannan group na general Makada da Mawaƙa ne da na kawo maka misalai na abin da nake nufi.

    [2:47pm, 14/04/2024] Malam Jibril Yusuf: Allah ya ba shi lafiya.

    Allah gafarta Malam mene ne mazallako da maiso da kora? Kalmomin duk baƙi ne a wajena.

    [3:16pm, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada: Okay, yanzu na fahimta. Wannan watakila zai iya tasiri ga wakokin da ba a buga ko rera su da yawa ba. Kuma zai yi tasiri ga wakokin wasu Makada da Mawaƙa wadanda wakokin da su maimaita rera su ba zai wuce sau biyu ko uku ba.

    Amma akwai wakokin wasu Makadan da za ka samu an maimaita rera su yafi sau 20, wasu ya fi 30 zuwa sama.

    [3:39pm, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada: Yana da kyau ayi haka din. Sai dai abun da zai iya yiyuwa shi za a yi.

    Ni ina ganin da ace a hade wakoki rerawa daban-daban a wuri guda, zai fi kyau idan an tsakace su daban-daban, ko wace a muhallin ta, domin kaucewa creating confusion. Sai ace rerawa ta 1, ta 2, ta 3 dss.

    Abin da yasa nace haka shine, za ka samu wata waƙa an yi ta a 1950, sai aka ta maimaita rera ta har zuwa 1990s. A ciki za ka samu Makadi ya kawo batutuwan da suka faru a wadannan lokuta mabanbanta da sunayen mutane da suka wanzu lokuta mabanbanta. Idan aka ce a gwamatsa su wuri ɗaya za a iya samun confusion gaskiya. Kuma wasu wakokin suna da tsayi. Wata waƙa za ta kai minti 15 wata 20 har zuwa 30 ko fiye

    da haka.

    Kamar yadda na faɗi da farko idan waƙa ba ta wuce rerawa biyu zuwa uku ba kuma tazarar lokacin da aka rera su ba tsayi, zai iya yiyuwa. Amma ace waƙa an yi ta lokacin Sardauna, misali, an ambaci mutanen gwamnati da siyasa da alummah na wannna lokacin, bayan lokuta an maimata fiye da so ashirin, kuma a ko wace maimaitawa za a samu irin ambato na wadancan ababe, sannan ace a hade komai a wuri guda? Zai iya kawo rudu ga manzarta da kuma tarihi. Zai yi kyau a bar ko wace rarawa a mazauni da matsayin ta. Illa dai ayi ƙokarin taskace su.

    [3:44pm, 14/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Haka ne amma waƙa ba Hadisi ba ce, daɗi da fahimta da hujja ake so a nazarin adabi. Ni ma ban aminta da cin amanar adabi ba.

    Babbar matsala mai ban tsoro a yau ita ce, "Yaya za mu yi da AI? A zauren nan wani ya taɓa cewa ana iya tsara magana (waƙa) wadda idan aka saurara ba za a iya rarrabewa tsakaninta da ta wani mawaƙi da aka sani ba, duk sanadiyyar AI. Watakila Dr. Abu-Ubaidah na iya ƙarin bayani a nan.

    [7:38pm, 15/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa! Sun haɗu a lokacin da Muhammadu Macciɗo yana riƙe da Sarautar Sarkin Kudun Sakkwato, suka yi zamaninsu har zuwa wafatin Mawaƙin a shekarar 1987. Shi kuma Muhammadu Macciɗo ya zama Sarkin Musulmi a watan Afrilun shekarar 1996, Allah ya yi masa wafati a shekarar 2006 sanadiyar hatsarin/haɗarin Jirgin Saman ADC Airlines. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.

    [3:26pm, 16/04/2024] Mal. B. Lauwali: Ina rokon wannan zaure ya taimakamin da waƙar Sa'idu Faru inda yake cewa: 'Yan Sarki kui ta biyayya da biyayya aka sarki....... In zamaninka ya zaka ba sai an yi gada-gada ba. Na gode

    [3:57pm, 16/04/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A da na dauka na Sakkwato ne, amma yanzu sai in ce na Zamfara saboda ku ne Sakkwatawa kun ce ba ku gane ba, amma dai duk Bazamfare ya san wadannan kalmomin, saboda a ciki muka tashi.

    [5:28pm, 16/04/2024] Mal. M.M. Yankara: Salam

    Don Allah a taimaka min da waƙar Sa'idu Faru wadda yake cewa:

    "Na yi mahwalki nai

    Sallah Makka,

    Nai Ɗawafi,

    Kuma na rungumo

    hirami da bagaruwa da

    tasbahohi/casbahohi,

    An ce mani Alhaji baital

    fasalin Kiɗi,

    Wanga mahwalki in

    Allah ya nuhwa a

    shirya shi ya zan haka..

    [5:31pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ba wuri ko gari guda na tashi ba. Firamare kurum na yi cikin Sakkwato kuma birni, birni kuwa bai aje Hausa gangariya, kauye ya fi shi.

    [5:46pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Wannan sai Hon. Ɗanmadami. Na dai san wata karin magana da ke kusa da abin da ka ruwaito mai cewa:

    MAI LAYA KIYAYI MAI ZAMANI

    [5:49pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe bani da wannan Waƙar mai amshi "Hwarin cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau, Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja".

    [6:04pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Allah Sarki. Wani na gani a wanga Zaure yana tambaya. Kila ba ka lura da tambayar ba. Ga ta:

    Ina rokon wannan zaure ya taimakamin da waƙar Sa'idu Faru inda yake cewa: 'Yan Sarki kui ta biyayya da biyayya aka sarki....... In zamaninka ya zaka ba sai an yi gada-gada ba. Na gode

     (Allah rufa asiri ya yi tambayar)

    [6:06pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne Ranka ya daɗe. Bayan kayi wannan maganar ne sai na lura da tambayar da wancan Malamin ya yi.

    Shi ne dai nike cewa ba ni da ita, amma nasan Waƙar mai amshi "Hwarin cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau, Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja".

    [6:12pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Sakin Makaɗan Gusau Tambai ya wanki wannan waƙa ya yi wa Maimartaba Sarkin Katsinan Gusau Alh. Muhammad Kabir Danbaba.

    "Da mai zakkuwa da gaskiya,

    Da mai zakkuwa da ƙarya,

    Allah shi ka fwaɗa mashi,

    Ɗan Sambo na ganin shi.

    Muhammadun Muhammadun ɗan Sambo mai darajja. "

    [6:15pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: In Shaa Allah idan na same ta zan turo maka Ranka ya daɗe. Ta na daga cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru guda 10 da aka samu a faifan Gidan Rediyo.

    [6:16pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: *Ko in ce waɗan da na sani/samu a faifai.

    [6:19pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Malam Aliyu, afuwan! Na lura da kana rubuta "fw" a madadin "hw" da na sani. Ko za ka ƙara mini bayani don Allah?

    [7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.

    [7:39pm, 16/04/2024] Mal. B. Lauwali: A taimaka man da wannan waƙa, inda Sa'idu Faru ke cewa: Da Allah muka takama Ba tsafi muka takama Ba Koway yarda da Allah Ba zai yi gada-gada ba.

    [7:49pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Sakkwatanci ce, Hausar Yamma ba ta Gabas ba kamar KT da KN da kuma "Daidaitacciyar Hausa". Wajajen Daura ne ban san yadda suke faɗin ta ba. Na dai san suna da "hy".

    [10:57pm, 16/04/2024] Dr Dangulbi FUG: Ina neman waƙar sarkin yakin Banga Salihu wadda makada Sa'idu Faru ya yi masha. A turo ta wannan zaure

    [6:42am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:.... Ba zai riƙa/riƙe Aljani ba.....

    "Farin cikin/Hwarin cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau,

    Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja ".

    [7:21am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Ba twsahi mu ka taƙama ba...

    [7:33am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: ??? "twsahi"

    [7:34am, 17/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Wace irin kalma ce kuma wannan?

    [7:45am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni ma ita nika tambaya. Kamar tsafi, kamar tciishi, wato abki/auki. Sai an furta watakila mu fahimta

    [7:45am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Daga tsafi a Yankinmu. Domin ba tsafi mu ke cewa ba, tswahi muke cewa.

    Afuwan, na yi kuskuren rubuta ta ne a maimakon tswahi sai na rubuta twsahi. 🙏🙏🙏

    [8:03am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle a Anka ana faɗar haka, da mafi yawan kasar Hausar Yamma. Muna kuma cewa tsahi.

    [8:16am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haka ne Haka ne Ranka ya daɗe.

    Anka ita ce hedikwatar Zamfarawa ta ƙarshe domin Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ne ya taso daga Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura zuwa Anka tsakanin 1815 zuwa 1824. Sun tarad da Anka a matsayin ginannen Birni daga gidan Sarauta wanda Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ya gina bayan masu jihadi (Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa da Malam Muhammadu Da'e/Daɗi wanda zuriyarsa ke Sarautar Maru da laƙabin Banaga ya zuwa yanzu da Malam Muhammadu Bachiri na Bunguɗu) bisa ga umurnin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi suka kore shi daga garinsa da ya assasa mai suna Birnin Banaga bayan ya baro gidansu watau Mafara. Birnin Banaga a halin yanzu kango/kufai ne dake Kudu Maso yammacin Maru.

    Daga wannan shiga ta Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo (1815-1824) ya zuwa yau anan Anka hedikwatar Zamfarawan da suka fara shigowa wannan yanki na Kasar Hausa a cikin 1300 take.

    Sun fara zama a Dutci/Dutsi dake cikin Masarautar Zurmi ta yau, suka koma Birnin Zamfara dake kusa da Isa ta Jihar Sakkwato inda Gobirawa suka riske su har ma suka mamaye su, suka ƙirƙiri sabuwar hedikwatarsu (su Gobirawan) a Gandun/Alƙalin Zamfara da ake kira Alƙalawa kafin masu Jihadi su mamaye su a 1804/8.

    Bayan Birnin Zamfara Sarkin Zamfara Abarshi shi da sauran jama'arsa sun zauna a Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro da Tumfafiya (Mazaunin Zamfarawan Mafara kafin su koma Talata Mafara) da Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura kafin daga bisani Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ya dawo Anka.

    [8:39am, 17/04/2024] Dr. S.S. Abdullahi: Tumfafiya mazaunin Zamfarawan Mafara da Gummi

    [8:44am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Haƙiƙa Maigirma Kogunan Gummi kuma Shaihin Malaminmu Dr. Abdullahi S/Gulbi.

    Daga nan ne Malam Ali Bazamfare/Ali Jan Masari ya fita ya je ya ƙirƙiri Daular Bukkuyum. Ɗansa Malam Muhammadu Waru ya je ya ƙirƙiri Masarautar Gummi. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya shirya muna zuriyarmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [9:20am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Wannan ya haska min yadda Yarima Ahmad yake jini biyu, da Bakura da Anka. A Anka ya yi sakandare, yana form 3 na je can karantarwa inda yake yaro mai basira amma ɗan ƙyamshe ne, bai da ƙiba😂

    [9:28am, 17/04/2024] +234 803 443 2042: Haka mutanen Bakura suke yan ƙyamshe ne, ba su da ƙiba

    [9:32am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Amma ina kyautata zaton ya gama da mutanen Anka.

    [9:35am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Mahaifiyarsa daga gidan Sarkin Zamfaran Anka Ahmadu ta fito.

    [9:37am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Da ni da Imran mun ƙaru. Allah Ya saka ma da mafificin alheri Hon. Sir

    [9:44am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Lokacin da na zaman Anka Sarkin Zamfara na lokacin classmate ne na wani yana a Farfaru Boarding Primary School, Sokoto. Ya rike ni da karimci sosai. Very humble person ne. Sarkin Zamfara Anka Lauwali sunansa. Allah Ya jiƙansa da rahma amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu

    [10:07am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Allah Sarki. Zamfarci ne ya yi mini ke nan. Bai san da ina iya kai tsaye in tambai Yariman ba?

    [10:17am, 17/04/2024] +234 803 443 2042: Walki ya jefe shi. Da fuskar Baɓurme muke kallon shi ba Bazanhwaren ba

    [10:22am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ai na zamna Anka tsawo shekaru huɗu na san ƙoramarsu da ake kira 'Yar Anka, na san Bagwai da Ɗangulbi da Dankurmi da Kwanar Maje kuma na ci hoce. Nakan sha iska gindin wani gamji da Anka round na Yamma ya bi kusa da shi. Na san kuma wani mawaƙi Ɗan Balɗo!

    [10:27am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Kada ku yi mai Zamfarci naku😂

    [10:27am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allah Sarki! Sani Ɗan Balɗo Waramu kenan, sai dai asalinsa Baɓurme ne.

    Ranka ya daɗe ka bar biye Malam Imrana kasan akwai wasan barkwanci tsakanin mutanen Mafara da Ɓurmawan Bakura😅✊🙏

    [10:28am, 17/04/2024] +234 803 443 2042: Ɓurmanci dai zamu yimai tunda shi ya iya

    [10:30am, 17/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Meye banbancin Zamfarci da ɓurmanci ne?

    [10:32am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni kuma ina so da kare ɗalibina domin ɗa ne ta bakin Kassu Zurmi, amma shi Yarima ɗan ne na kowace ma'ana, ba dibilwar Kassu ba!😂😂😂

    [10:36am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Jinsin jama'ar ba ɗai ba ne Maigirma Ɗanmasani. Ɓurmawa daga Tsohuwar Daular Borno suka fito, su kuma Zamfarawan Mafara daga Rano/Kano suka fito suka tarad da Ƙayatawa (Su Malam Imrana) a Mafara.

    [8:28am, 20/04/2024] Mal. A.R. Mayana: "Kai na yarda Tukur ya dawo,

    Don an ba mai tara mutane,

    Ba mai watse mutan birni ba.

    [9:23am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: 👍😁👌🙏..... Wada yazzo da lahiya Na Kanau kuma ya dawo da girma, Bajinin ci fansa Amadu mai takakka ga Arna....

    [9:56am, 21/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ashe ba cewa yake, "haka nan kuma.. " ba?

    [10:01am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A'a Ranka ya daɗe. Na Kanau kirarin Sarakunan Zurmi da Ƙaura Namoda ne saboda Sarkin Zamfaran Zurmi Kanau da aka yi, ya shahara sosai.

    Kamar a je Katsina ne a kira mai alaƙa da Sarautar Katsina da inkiyar Muhammadu Korau (Yanke Masheɗi Baƙon Sanau) a ce masa "Na Korau".

    [10:03am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Kanau da Isau da Loci dukansu Sarakunan Zurmi ne.

    [10:18am, 21/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Tooh! Ka ga jahilcina game da naƙaltar Zamfara ko?

    A kan haka a koyaushe nake dagewa lalle ɗalibaina su riƙa rubuta abin da mawaƙi ya ce kuma ya rubuta, kada su bi ma ɗaidaitacciyar Hausa'. A kullum nakan ba su misali da yadda a Kananci ake cewa 'ilimi', Sakkwatanci kuwa a ce 'ilmi'. Idan mawaƙi Basakkwace ya faɗi kalma ko ya rubuta ta kai kuwa don ka mayar da waƙarsa da kalmar Bakano sai karin waƙar ya sauya, watakila ma ya karye.

    [10:22am, 21/04/2024] +234 803 314 6863: Kanau da Isau na yi zaton wa ne da kane ance Babansu daya Alin Bawa kohaka labarin yake?

    [10:25am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Lallai tsatson su ɗaya duk da yake bani da takamaiman bayani akan yadda lamarin yake.

    [10:25am, 21/04/2024] Prof Nazir I. Abbas: Haka ne Allah gafarta Malam. Mu a mahangar harshe: "ilimi" da "ilmi" sai mu ce shafe wasali ne aka yi a nazarin tsarin sauti. Allah ƙara amfanar da mu daga iliminku👏

    [10:26am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A cikin Waƙarsa ta Marigayi Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba Ɗan Tumba Rungumi yana cewa "Ni Kiɗin yaƙi niyyi ma Abu Na Isau bani son kana zannawa banza....

    [12:28am, 22/04/2024] +234 803 257 6475: Assalamualaikum! 'Yan uwa masu albarka, ina tambaya musamman ga masana ilimin kwari (biology). Mine sunan Jinjimi, bubukuwa, da turanci?

    [7:49am, 22/04/2024] Dr. H. Yelwa: Biology 👉🏽Ilimin halittu ke nan kacokam

    Ilimin kwari👉🏽Entomology.

    Kilan kace ilimin tsuntsaye👉🏽Ornithology

    In ka bibiyi tattaunawad da anka yi a baya can, zaka ga tsuntsayen da ka' ambata tare da sunayensu da ma hotunansu.

    [1:09pm, 22/04/2024] Malama. S.S. Labbo: Assalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu Shehunnan Malamai Ina maku barka da warhaka. Don Allah Ina bidar wata alfarma, in akwai rubutacciyar waƙar Mai babban daki da shi Sa'idu Faru ya yi don Allah a taimaka min da ita. Na gode

    [8:51pm, 22/04/2024] Mal. M.A. Umar Za a samu Waƙar Mai Babban Ɗakin Ƙasar Kano/Mahaifiyar Marigayi Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero (Hajiya Asiya/Hasiya Bayero) a cikin wannan faifan ☝️

    [9:15pm, 22/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Allah Sarki. Wadda aka rubuta ta nema ba ta cikin faifai ba, amma kuma watakila ko ta cikin faifai ba ta mallaka ba. An ba ta shawarar da yake akwai ta ga faifai to ta juya da kanta, abin da ni ma ina goyon bayan haka don idan na yi haka nan na fi samun kwanciyar hankali. Sai kuwa idan mai juyar irina ne da bai canza waƙar zuwa "Daidaitacciyar Hausa".

    [9:35am, 23/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ya kamata a wannan taro wani daga cikin Malami ya gabatar da takarda a kan hanyoyon taskace waƙoƙin baka na Hausa. Akwai mazhanobi biyu da suka yi fice, Mazhabar Gusau (2009) da ta Bunza shi ma (2009). A zaɓi ɗaya ko a tabbatar da su, ko a zaƙulo wasu ko wata.

    [12:26am, 24/04/2024] Prof. A.B. Yahya: A farkon waƙar nan na ji Sa'idu Faru ya yi amfani da salon waskiya. Ban ji waƙar duka ba yanzu sai an jima ko gobe. Salon na waskiya yana cikin ambaton cewa daga Kano har ƙofar Lagos, har Ingila har bakin ruwan Yamma Babban Ɗaki guda ne. Ina sauraren ya ci gaba don ya ambaci Gabas sai bai yi ba saboda a zatona ya san kwaɓa ta zai yi saboda Gabas ga Hausawa Musulmi ba su kawo kome ga ransu in ba Ɗakin Ka'aba ba. Wato bai ambaci Gabas ba; ya yi amfani da salon waskiya ke nan.

    [12:50am, 24/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Dukansu ba sabbin ba ne. Tun zamanin zamunna ake taskace waƙoƙi da hanyoyin. Na Hausa akan samu irin haka cikin DAUSAYIN SOYAYYA na Bello Sa'id. Kundayen masana da dama kamar Ɗandatti Abdulƙar da Sa'idu Muhammad Gusau. Tun daga sunan da Sa'idu Gusau ya ba littattafansa za a fahimci cewa hanyar sananniya ce, wato DIWANI.

    [8:01am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: 😀👆🏽Madallah.

    Lallai ko shi a wani wuri da yah hwadi gabas, ya hwadi inda ag gabas din.

    "GABAS ƊAKIN KA'ABA shi muke dibi don haske

    To, ko Gobir akwai NaYakuba ga Jangwarzo Da imanin Shehu yai tudu Ummaru yad dawo".

    Buhuna

    Jagora: Zama zucci ga mai rabo

    Daudu yahi zama kusa

    Y/Amshi: Wata goma buhu goma a kan bamu na marmari,

    Jagora: Zama zucci ga mai rabo

    Daudu yahi zama kusa

    Y/Amshi: Wata goma buhu goma a kan bamu na marmari,

    Ga zakka metin na gumi don ayi ma tuwo,

    Ga kuɗɗi fan goma na zabbi ayi romuwa,

    Jagora: Hawan Sallah Baba ɗan

    Muhammadu yai kyau bana,

    Y/Amshi: Ku duba muna kaya na zuwa idi acan-acan,

    Turken Waƙa:Babban bajinin gidan Hassan Shehu na Yan Ruwa,

    Ba ai maka wargi bahago babu kahway yima.

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Talata Mafara, Sarkin Gabas Alhaji Shehu ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya yi sarauta daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969. Allah ya kyauta makwanci, amin. 

    Farin ciki

    "Babban gambun sirrin duniya Uban Alhaji Salihu", a cewar Ɗan Tumba Rungumi a Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai amshi 'Farin cikin musulmin duniya, mai martaba na Abubakar, ci fansa Alhaji Macciɗo'. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    [8:27am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: Saidu ya ambace ta;

    1. A cikin wace waƙace?

    2. Wa yay yi ma waƙat?

    3. A yi bitaɗ ɗan waƙat.

    [8:29am, 24/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... Hwarah hwatsa cinki sai ga mai ƙararrin kwana, a ciki a kwan rirriƙam mutun za shi garin kewa...

    A cikin Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba mai amshi " Gwabron Giwa na Shamaki baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daaga".

    [8:36am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: Haka ne, Honorabul!👆🏽😀

    Abu baban Shamaki na Jekada

    Dangalin Gabas Na Isau dan Mudi

    Kashi tahi giggilme ƙargage

    Hwarah HWATSA cinki sai ga maikararrin kwana

    A ciki akwan rirrikam mutum za shi garin kewa

    In ana yaki na Abubakar....

    Gaskiya wuringa👆🏽Saidu ya buga Hausa.

    To, mi an na wani abu kuma ƙargage?

    [8:38am, 24/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:... In da zamanin ana yaƙi ne Abubakar sai ya kama wanda am magudanci....

    [9:07am, 24/04/2024] +234 803 443 2042:..... shi bani sunai man noma,

    Ina zamne ina gida

    Ina ɗunkin turu na,

    Cikin albarkar Abubakar,

    Na bar shan hurar da ba nono, bani cin tuwo in ba tsokoki,

    a murje gumi wanda adda kyau,

    in dasa yatsuna"

    [9:12am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: 👆🏽😀Jumla bi-da-bi.

    Amma, in DASA yatsuna yaka cewa, ko in GASA yatsuna?

    [9:18am, 24/04/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ko kuma in nasa yatsuna?

    [9:22am, 24/04/2024] +234 803 443 2042: "In dasa" yake cewa maigirma Perm Sec. Watau kamar ya ce in soka yatsuna amma saboda lalurar waƙa, sai ya ce in dasa

    [9:25am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: Madallah Mal Imrana. Hausat tashi ce sai ta ba mutum dariya, yadda yaka jerota. 

    [6:40pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: Don Allah me ya sa, kamar yadda Sa'idu Faru ya ruwaito, Bahaushe ya ce mai ƙararren kwana duniya kurum zai ci farar fatsa? Kuma fatsar ce kuma ake kira mamari?

    [6:46pm, 26/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe saboda sai kifin da aka nufi mutuwarsa/ajalinsa ya yi ne zai haɗiye farar fatsa. Domin da zaran ya haɗiye ta waje aka yo dashi sai cikin kwando ko gora daga nan sai talle, ya zama kalaci/cimaka/abinci kenan.

    Ba ita ce mamari ba, mamari a zare ake jera shi da yawa sai a saka ƙoto a zuba shi a ruwa, a ɗaure shi da dutci ko iccen dake cikin ruwan da ake Suu ɗin.

    [7:30pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: To ma sha Allahu. To ita fatsa launi launi ce?... akwai fara, akwai ja, akwai baƙa... ?

    Godiya nikai Hon. sir

    [7:32pm, 26/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ma Shaa Allah Ranka ya daɗe. Mai jikin silver na sani Sir.

    [7:33pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: Ka ga tashin birni ko? Larabawa sun dade da sanin haka, don haka sukan kai 'ya'yansu ƙauye don su tashi can su iya Larabci sosai

    [7:34pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: Ƙara haƙuri da ni don Allah, ke nan farar fatsa ta fi halaka kifi ko?

    [7:39pm, 26/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Eh Ranka ya daɗe tunda ita ci maza ce, da ya ga an jefa ta cikin ruwa naɗe da ƙoto/fara ko makamantan ta sai ya haɗiye a matsayin abincin da ya samu a banza.

    [10:52pm, 28/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Muna sane! Su Furnis da su paden duk sun yi. Amma, babu kamar waɗannan biyu da muka ambata.

    [10:38pm, 29/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Tsakin tama na Abashe ana shakkah haye ma Amadu ☝️

    [10:40pm, 29/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Sa'idu Faru ka Waƙam iko

    Komi kaj jiya ƙarya akai

    Sa'idu Faru ka Waƙam milki

    Komi kaj jiya ƙarya akai".

    [12:14pm, 30/04/2024] Fugus Ba shir Abdullahi: Assalamu Alaikum.

    Muna ƙara yin tuni dangane da biyan kuɗin rijista ga wanda zai gabatar da Maƙala kamar yadda aka sanar a sama.

    Idan an biya sai a tura rasiti ta wannan layi nawa a kan WhatsApp don zama shaida Insha Allah.

    [5:38pm, 01/05/2024] Mal. M.A. Umar Aslm. A taimaka mana da taƙaitaccen tarihin Hajiya Hasiya Mai Babban Ɗaki.

    Muna godiya!

    [6:54pm, 01/05/2024] +234 806 921 4605: Assalamualaikum Warahmatullah. Jama'ar wannan gida mai albarka barka da warhaka. Dafatar duk muna lafiya.

    Suna na Samaila Yahaya Jami'in hulda da Jama'a na Kungiyar marubutan Jihar Zamfara. Ina daya daga cikin wadanda ke bibiyar abin da ke gudana a cikin wannan gida. Bisa ga wannan ne nake bada shawara ga masu ruwa da tsaki na wannan taron karawa juna sani da za a fara ranar Juma'a da su duba yiyuwar aikewa da takardar gayyata ga Kungiyar marubuta ta kasa reshen Jihar Zamfara wato (Association of Nigerian Authors).

    Dafatar za a duba wannan kira. Allah Ya nuna mana ranar fara wannan taro a yi lafiya a kare lafiya Amin.

    [7:18pm, 01/05/2024] Fugus Ba shir Abdullahi: Muna godiya da waɗannan shawararwari masu muhimmanci. 👍🙏

    [12:32am, 07/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Ruwan da aka wanke tsaba kamar geron da aka dake, aka aje domin dabbobi su sha, kuma duk wani sauran abinci ko abin sha wanda bai cutar da dabba akan yi haka da shi, wato ya zama ƙasari. Manufa dai akan tara shi domin a ba dabbobi kamar awaki da tumaki da shanu.

    A ƙauyuka da birane iyaye kan tura 'ya'yansu su je gida gida domin su roƙo ƙasarin da za su ba dabbobinsu. Ba mamaki a wannan zamani a riƙa sayar da ƙasari. A yanzu dai a nan Sakkwato kyauta akan bayar da ƙasari domin yin haka wata hanya ce ta rabuwa da ƙazanta saboda babu abin da magidanta za su yi da ƙasari idan ba su da dabbobi, kuma kullum ne sukan tara shi muddin suna yin abinci ko abin sha.

    Ina fatar wannan bayani zai gamsar, amin.

    [6:53am, 07/05/2024] Malam Abubakar Tijjani: Na gode

    Na kuma gamsu, amma dukkan kasar Hausa haka ake kiransa, ko akwai bambanci a Hausar Nahiya ko karin Harshe?

    [11:29am, 07/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Na so a yi bayani kan kirarin da aka yi wa Sakkwato. Kila Hon. Birnin Magaji ne mai iya yin fashin baƙin. Saura kuwa irin Bawa Jan Gwarzo ta-ciki ke hana su😂

    [3:39pm, 07/05/2024] Sheik Hafizu Hadi: Assalamu alaikum. shuwagabanni Masu girma na wannan sashe, Mai kula da harsuna a wannan jami'a Mai AL barka. Ina Taya ku murnar kammala wannan taro lafiya. Da fatar Allah Shi Mai Mai ta Muna. Mai girma Danmadami Allah ya Saka Maka da alheri. Dan Allah ka ƙara Rika hannun wannan sashe na mu Mai Albarka. Allah ya Baka lafiya, yanda ka haskaka wannan sashe na mu, Allah ya ƙara haskaka tauraruwar ka a Duk Inda ka shiga. Mai girma zanna yanda ya sadaukar da dukiyarsa domin sama wa wannan sashe na mu girma da daukaka da a cikin Wannan jami'a Allah ya nuna Muna lokacin da zai Shigo cikin Wannan jami'a Yana a matsayin gwamna jahar zamfara. Ni dalibin ku ne a yi haƙuri da kura-kuran da za a Gani. Allah Shi taimaki wannan makaranta tamu da Malamanmu.

    [4:47pm, 07/05/2024] Mal. B. Lauwali: Amin, wallahi na karu da Danmasani sosai, haƙuri da karamin dalibi irina ba kowa ke iyawa ba. Ina da yawan tambaya ga duk abinda ya shige min duhu. Shi kuma Danmasani bai taba gajiya da yi min bayani ba. Allah Ya saka masa da alheri. Ba shi kadai ba, har da sauran 'yan kwamiti domin irin haƙuri sai dai a kwatanta ba zai lissahu ba. Mun gode

    [5:13pm, 07/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Don Allah ko mawaƙan Hausa na baka daga wata nahiya daban da nahiyar Yamma sun halarci wannan muhimmin taro? Na yi tambayar ne saboda na yi imani da sun halarta da sun amfana ƙwarai da Hausa da hikimomin tsara waƙa daga wannan nahiya in sha Allahu.

    Sarkin Musulmi Maccido

    [10:09pm, 02/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba.

    [12:05am, 03/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Waƙar Turakin Argungu Shehu (Kangiwa), ga alamar da ke cikinta Sa'idu Faru ya yi ta kamin 1979 lokacin da Turaki ya zama gwamnan Sokoto. Sa'idu Faru bai ambaci Turaki a matsayin gwamna ba, saboda haka mai yiwuwa lokacin da shi Turakin yana cikin shirin fitowa takara ne aka yi waƙar.

    Abin da ya saka mini tunani cikin waƙar nan shi ne kyautar mota da Naira ɗari biyar "don in aje in yi ta kwasar hetur"! Haƙiƙa a lokacin fetur bai da tsada a ƙasar nan. Har zuwa 1976 kamin mulkin OBJ na soja ya ƙara kuɗin fetur, nakan cika tankin motata da Naira biyar kacal!!!

    [8:38am, 03/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ƙwarai kuwa Maigirma HOD. Marigayi Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa yana cikin aikin gwamnati a lokacin Masarautar Argungu ta zaƙulo shi ta naɗa shi Turakinta na farko.

    Makaɗa da Mawaƙan Baka Na Hausa irin su Musa Ɗanƙwairo Maradun da Sani Aliyu Ɗandawo Yauri sun baje kolinsu a wajen bikin naɗin wannan sarautar.

    Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru da tawagarsa

    [12:17pm, 03/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru na uku daga gefen hagu da jama'arsa tare da Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji na uku daga gefen dama bayan kwamitin masaukayye ya saukar da tawagar Makaɗan yayin da suka shigo Gusau babban birnin Jihar Zamfara, Ranar Juma'a 03/05/2024 domin dakon Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru da Sashen Harsuna da Al'adu na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau ya ɗauki nauyin gudanarwa daga 3-6 ga watan Mayun 2024.

    [9:13pm, 22/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya jaddada masa rahama, amin.

    [10:09pm, 22/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Makaɗa Sa'idu Faru: Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo Abubakar III/Ya yi Sarki daidai wada mai yanzu yar riƙa ☝️

    [10:13pm, 22/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa da wannan kama na san Mai alfarma cikin shekarun 1970!!!

    [9:02am, 24/05/2024] Malam Bello Gedawa: Allah ya taimake ka na fahimta gaskiya. Na gode da wannan shawara. In sha Allahu zan gwada. Koda dai Basullube ni ke yallabai😃

    [9:04am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Halan Sulluɓawa ba Fulani ba ne?

    [9:05am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Na aza kamar Kanawa da Sakkwatawa ne

    [9:11am, 24/05/2024] Prof Nazir I. Abbas: Salam, Ni fa ban ganin rubuta wani abu da ya shafa Hausa cikin wani harshe a matsayin wani abun kyama ko kuskure. Hasali ma akwai wadanda ba Hausawa ba da za su iya sha'awar sanin wani abu game da harshen da kuma al'ummar ta hakan za a iya sanar da su.

    [9:13am, 24/05/2024] Malam Bello Gedawa: Allah ya taimaki shugabana, malamina kuma Shaihin malami, wane ni in iya amsa wannan tambaya a gabanku.. Wallahi ban isa ba.

    [9:19am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya: A'a don Allah. Na sha ganin Sulluɓawa, kai har da Gurumaɗa, da ke Fulfulde raɗam.

    [9:44am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Allah Sarki. A Zamfara musamman a Anka Sulluɓawa suna ji

    [9:46am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Kuma Sulluɓawa ai Fulani ne. Fulani sun kasu dangi-dangi

    [8:34am, 26/05/2024] Mal. A.R. Mayana: Maigirma Danmadami.

    1) Ko dukan Sarakunan nan kafin su dawo an naɗa wasu?

    2) Cire waɗanda aka naɗa bayansu aka yi suka dawo, ko ƙaƙa?

    Allah ya ƙara sani, amin.

    [3:52pm, 26/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Na'am Maigirma Ɗanmasani kuma Ɗangaladima barka da warhaka. A gaskiya bani da cikakken bayani akan wannan/waɗan nan tambayoyi naka.

    Abun da kawai na sani shi ne a Kwantagora da aka cire Sarkin Sudan Ibrahim ɗan Sarkin Sudan Ummaru Nagwamatce ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I/Abubakar Atiku/Mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a shekarar 1904, Kwantagora ta zauna babu Sarki har zuwa dawowarsa a shekarar 1906. Domin bayan Turawa sun cire shi su ka kai shi a Lokoja inda ya zauna har tsawon shekara biyu, sun bar Ƙasar babu Sarki sai a shekarar 1906 su ɗauko shi daga Lokoja su ka dawo dashi Kwantagora ya ci gaba da mulkinsa har zuwa wafatinsa a shekarar 1929.

    A Suleja kuma bayan walwale naɗin Malam Awwal Ibrahim da Gwamnatin Jihar Neja ta yi an naɗa wani ne a matsayin sabon Sarki. Malam Awwal Ibrahim kuma ya shigar da ƙara ya ƙalubalanci cire shi da aka yi inda ya samu nasarar abun da ya nema a Kotu cewa yana son a mayar dashi domin an cire shi ba bisa ƙa'ida ba, ya kuma samu hakan sai aka rushe wancan naɗi da Gwamnatin Jihar Neja ta yi aka mayar dashi. Allahu Wa'alam!

    [4:43pm, 26/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allah Hon. Yanzu fa wannan mayarwar da aka yi wa Sarkin Kano haƙiƙa 'yan siyasa dasa tuɗar da darajar masarautar suka yi. Na kuma 'yi imanin mai hali bai barin halinai. Allah Masani. Allah kuma Ya yi muna magani, amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu

    [4:49pm, 26/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Wallahi Ranka ya daɗe tun lokacin da aka janye ikon gudanarwa daga Sarakuna zuwa ga masu mulkin zamani aka dasa ɗambar wannan wulaƙanci ga Sarakuna Masarautunmu.

    Shigar masu jinin sarauta a cikin sha'anin siyasa wai domin su ceci gidajensu ko mutuncin sarauta/Masarautun a tawa fahimta zai ƙara dagular da lamarin ne kawai saboda kuwa ta kansu zasu yi, ma'ana tasu biyan buƙatar zasu saka a gaba. Allahu Wa'alam!

    Shaihin Malaminmu Abdullahi Bayero Yahya na Sashen Harsunan Nijeriya dake Jami'ar Jihar Sakkwato

    [5:47pm, 29/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allahu Akbar, kamar jiya ne wannan abu ya

    faru! Shaihin Malaminmu Abdullahi Bayero Yahya na Sashen Harsunan Nijeriya dake Jami'ar Jihar Sakkwato ne a gefen hagu (mai bulan kaya) ke gaisawa da Malam Bilyaminu Abubakar Gusau na Sashen Shirye - Shiryen Gidan Rediyon Gold City FM mallakar Gwamnatin Jihar Zamfara dake Gusau na farko daga gefen dama (mai kaya ɗanyen haki) yayin da Alhaji Murtala Alhassan Garkuwan Maru, Shugaban Sashen Shirye Shirye na Gidan Rediyon Jihar Zamfara (a tsakiya) ke sambarka a lokacin da Shaihin Malamin ya gabatar da jagabar manyan Maƙaloli a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru da Sashen Harsuna da Al'adu na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau, Jihar Zamfara ya shirya domin karammawa zuwa ga Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III da ya gudana a Dandalin yaye Ɗalibai dake harabar Jami'ar Ranar Asabar, 04/05/2024. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    [6:07pm, 29/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:

    Jagora: S/shaggu ka rabka kuwa,

    Kai taƙamab biri,

    Kuma saki tukkuwa ta wala,

    In na kiɗa kai ko Maba

    tadda gwarzon Sabongari nan dak kwana,

    Kai Magajin busa ka zanki busa,

    Da zamanin ana yaƙi na,

    Jagora/Y/Amshi: Maraɗi da bata kwan ukku,

    In ba aljihun Abu mai saje ba,

    Ginshimin S/fada ɗan Iro na Malan,

    Ubangijin Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.

    Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Nijeriya, Abubakar Garba.

    Ya yi sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    Turken Waƙa: Ginshimin Sarkin fada ɗan Iro na Malan,

    Ubangijin Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.

    [8:41am, 31/05/2024] +234 803 696 1436: Ina neman sunan waƙar sarauta ta farko da Alhaji Musa Dankwairo ya yi wa Sardaunan Sokoto Alhaji Ahmadu Bello a 1962. A taimaka mini da sunan waƙar.

    [10:27am, 31/05/2024] Malama. H.M. Kurawa: Kada marake giwa,

    Ba a haye ma Barde,

    Amadu ɗan Ibrahim,

    Baka yada gudun arna ba.

    [10:41am, 31/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: A gaishe da Malama. Ɗan ƙarin bayani wannan Waƙar ita ce ta farko wacce/wadda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya fara rerawa zuwa ga Marigayi Maigirma Firimiyan Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato.

    Ya yi masa ita ne a lokacin yana Daudun Kiɗi/Ɗan Amshi a Ƙungiyar Kiɗa ta yayansa/wansa Makaɗa Abdu Kurna ɗan Makaɗa Usman Ɗankwanaga ɗan Makaɗa Kaka Allahu ya jaddada masu rahama su da sauran magabatanmu, ya shirya muna zuriyarmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    [10:52am, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Hon Kai fa ne Rumbunmu! Ni kuma waƙoƙi biyu nake buƙata, ɗaya ta Kurna wadda ke faɗin/ In ka ga gashi na ta tashi bisa//Gun gije yaka tabbata/.

    Ɗaya kuwa ta Ɗanƙwairo mai cewa,/Ga Giwa ga hili tsakak karkara//Mahalba ina masu son suna/.

    [11:19am, 31/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Ranka ya daɗe barka da kwana dafatar Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

    Ta Kurna Waƙar Sarkin Ƙayan Maradun Abubakar/Bubakar ce wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1939 zuwa 1960 lokacin da aka cire shi. Ɗayar kuma ta Yandoton Tsafe Aliyu II ce wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1960 zuwa rasuwarsa a shekarar 1991. Allah ya kyauta makwanci, amin.

    In Shaa Allahu za a lalubo su Ranka ya daɗe.

    [11:24am, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Ina godiya Hon sir. Dalilin biɗar su gare ka shi ne kular da kake yi da yaren da mawaƙa suka yi waƙoƙinsu.

    [8:15pm, 31/05/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Makada Alhaji Musa Dankwairo yana harzuka Maimartaba 'Yandoton Tsafe idan ya zo kan wannan dan waƙar. Wata rana da ya je a lokacin Sarki na cikin wata rashin lafiya amma sai da Sarki ya sa aka yi shela duk aka hadu garkar Sarki. Ko da ya zo nan ya ce "ga giwa ga hili tsakak karkara mahalba ina masu son suna? Sarki kuwa ya mike tsaye ya bude hannuwansa kamar mai kirari! Sai da aka rirrika shi ya zauna.

    [9:20pm, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Lalle irin wannan turken ko tubalin waƙa take yake yamutse Basarake. A nazarin waƙa ana kiran sa "zuga".

    [9:22pm, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Ashe da Ɗankwairo ya yi ɓarna

    [9:32pm, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Haka nan kuma an taɓa faɗa mini cewa akwai lokacin da 'Yandoto ya fita tanadi, an kai wani ƙauye sai aka ji wani gida an sa kaset mai dauke da wannan waƙa, to da 'Yandoto ya waƙar kuma wannan dan da ke ɗauke da tubalin sai kuwa nan a kan doki 'Yandoto ya harɗa tamatele!, ya ce ma bafadensa "Sarkin fada a'a muke?"

    [5:36am, 01/06/2024] Dr Yusuf Gama: To ai wadannan bayanai abubuwa ne masu amfani ga daliban ilimi da manazarta, domin za a iya rubuta makala sukutum da guda a kan irin wannan batutuwan, misali: Dangantakar Sarki da Waƙa da kuma Makadi/Mawaki: Tasirin Wakokin Dankwairo Ga Jin Isar Sarautar Aliyu Yandoto, ko wani taken makamancin wannan, musamman ma in za a iya tattaro ire-iren wadannan al'amura da suka faru.

    [6:50am, 01/06/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A waƙar Sarki Ibrahim na Suleja Dankwairo yana cewa " waƙar da na yi maka tai ma daɗi,

    Ko ni da niy yi ta tai man daɗi.

    [3:32pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Sa'idu Faru ya ce, cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri, ko baya ga wannan waƙa akwai wasu tara gida, idan sarki ya yi na'am da wannan to yana aikawa gida su zo.

    Wannan magana tubalin roƙo ne cikin salon kambamawa/kambame/kambame zulaƙe domin Sa'idu Faru ya samu babbar kyauta daga sarkin.

    Ga alamu wannan salo mai tagomashi ne ga mawaƙan sarauta. Ɗanƙwairo ma yakan yi amfani da shi. Misali cikin wakoƙin da ya yi wa 'Yandoton Tcahe akwai wata da yake faɗin,/In dai ana hidda hakkinmu daidai/ Sai an ji launi iri banban/.

    [5:54pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Akwai wata dabbar daji da Kassu Zurmi ya yi amfani da kirarin da ake yi mata wato, "Awakin banza". Wace dabba ce Kassu ke nufi cikin waƙarsa ta Garugaru? Don me ake ce mata "Awakin banza"?

    [6:06pm, 01/06/2024] Dr Rabiu Ba shir KASU: Allah gafarta Malam kirarin biri ne. Akan ce biri awakin banza/tumakin banza

    Komai yawansu ba sa taki.

    [6:12pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa! Kuma birai ne da suka fi yawa a nan ƙasar Hausa, jajjaye ne masu yawo cikin gungu kamar awakinmu. Hasashena ne kurum.

    Makaɗa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri

    Alhamdulillahi! Muna godiya sosai da fatan alheri da addu'o'inku zuwa ga Ɗan Uwa, Makaɗa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri a kan wannan abun alheri da ya samu na mayar da aikinsa zuwa Ƙasar Morocco da Hukumar Shige Da Ficen Nijeriya ta yi masa. Allah ya karɓa, amin.

    A wata tattaunawa da na yi dashi ta wayar salula Ranar Asabar, 01/06/2024, na tambaye shi ko ba za mu sake jin motsinsa a fagen Kiɗa da waƙa ba domin yanayin aikin da zai samu kansa a ciki nan gaba kaɗan? Makaɗa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri ya amsa mani cewa "In Shaa Allahu bani da ƙudurin barin wannan sabga ta gidanmu dake da zummar ci gaba da kariya ga al'adunmu, ko da wane irin girma na samu a cikin wannan aikin hukuma da nike yi".

    Da wannan muke yi masa godiya akan wannan tunani nasa da kuma ƙara yi masa addu'ar samun cikakkiyar nasara mai albarka a kowane fanni, amin.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara. Asabar, 01/06/2024.

    [6:41pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Salon Kinaya ne Kassu ya yi wa wani Musa cikin mutanen Jangerawa a waƙar GARUGARU. Kassu yana nufin Musa bai da amfani, ko a cikin sana'ar tauri ko sana'ar farauta, ban dai fahimta ba. Amma dai ai duk wadanda suka taru a dajin nan in ba Garugaru ba duk birai ne awakin banza ga Kassu saboda Garugaru ne kurum ya yi masa ƙwazo mai daɗi kamar ya dama zuma ya sha!

    [6:46pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma sha Allahu. Ina murna da jin haka. Ina malaman boko da suka karanta Hausa amma suna ɓoyon a ce Hausa suka karanta?

    [7:28pm, 01/06/2024] Dr Rabiu Ba shir KASU: Ma sha Allah da wannnan gagarumar nasara da aka samu, Allah ya saka masa da alheri. Kai kuma Allah ya ƙara maka kwarin guiwa na ƙoƙarin ganin Waƙar baka ta habaka.

    Zan so in samu Wakokin makadin, domin ban taba jin su ba gaskiya.

    [7:51pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Waƙar GARUGARU da Kassu Zurmi cike take da salon Kinaya kamar "biri awakin banza* da "jan zakara" da sauransu. Fito da da sauran kana mai bayanin abin da Kassu ke nufi da kowane.

    [8:08pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Nuna salailan kinaya da alamtarwa/alamu da ke cikin waƙar Garugaru ta Kassu Zurmi kana mai bayyana manufar mawaƙin da kowane salo

    [8:34pm, 01/06/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Shi ne Ɗansa na biyu, mace ce ta farko shi ke bi ma ta, saboda haka shi ne babba a cikin sauran 'ya'yan maza.

    Bai kuma yi biyar Mahaifin wajen Waƙa ba, hasali ma yana yi masu faɗa cewa su ci gaba da neman ilimi. Cikin ƙaddarawar Allah SWT sai gashi Suferitandan na Shige da fice, Alhaji Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri ya gade/gaje gida.

    Kenan tarihi ne ya maimaita kansa domin Kakansa Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni (duk da yake shi baya gaji/gadi Kiɗa da waƙa ba ne) ya sha tsangwama daga Mahaifinsa akan shigarsa wannan sabga ta Kiɗa da waƙa.

    Da tsangwamar ta yi masa yawa ne ya dinga gudu zuwa wani gari da ake kira Augie a cikin Masarautar Argungu, Jihar Kabi ta yanzu ya ci gaba da wannan sabgar.

    A can ne ma ya yi auren fari, ya auri Hajiya Hauwa'u (Laraba) wadda ita ce ta haifar masa Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo Yauri a garin Argungu a cikin shekarar 1943 (tana raye a gidan ɗan ta, Marigayi Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a Yauri, a halin yanzu), shi ne ya haifi Makaɗa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri. Allah ya jiƙan magabatanmu, amin.

    [8:43pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Allahu Akbar! A kullum na karanta irin wannan tarihi nakan ji an ƙarfafa iƙrarina da ke nufin waƙa baiwa ce ba koyon ta ake yi ba.

    [1:27pm, 18/06/2024] Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara: Daular Zamfara: 1300 Zuwa Yau A Takaice

    Daular Zamfara samu ne a cikin 1300 ta hanyar jagorancin wani mutum da ake kira "Dakka" da ake kyautata zaton ya fito da jama'arsa ne daga Gabas ta tsakiya. Sun fara yin hedikwata a wani wuri da ake kira "Dutci/Dutsi" dake cikin Masarautar Zurmi ta Jihar Zamfara ta yau.

    Daga nan ne ɗansa da ake kira "Bakurukuru" ya ɗauke hedikwatar daga Dutci/Dutsi zuwa Birnin Zamfara dake cikin Gundumar Isa ta Jihar Sakkwato ta yau a cikin ƙarni na 15. Anan ne Gobirawa suka tarad dasu a cikin ƙarni na 18 har ma suka nemi su ba su wurin zama domin a lokacin su Gobirawa sun daɗe da samar da Ƙasarsu bayan fitowarsu daga inda ake kira "Gobur"/Gubur" da ake kyautata zaton a cikin yankin Saudi Arabia ta yau ne.

    Zamfarawa sun ba su Gonar Alƙalinsu da ake kira Alƙalawa a lokacin mulkin Sarkin Zamfara Malo, kafin daga baya Gobirawan su mamaye su a lokacin mulkin Sarkin Zamfara Maroƙi a shekarar 1764 har ma su mayar da Gonar Alƙalin Zamfara a matsayin sabuwar hedikwatarsu da suka kira "Alƙalawa/Alkalawa" a zamanin mulkin Sarkin Gobir Ibrahim Babari.

    Daga lokacin har zuwan Fulani masu jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya a cikin ƙarni na 19, Zamfarawan nan da Gobirawa suka mamaye sun yi ta yawo suna kafa hedikwatoci na wucin gadi a Kiyawa ta Masarautar Birnin Magaji da Banga da Kuryam Madaro dake Masarautun Birnin Magaji da Ƙaura Namoda a Jihar Zamfara ta yanzu da Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura kafin tsakanin 1815 zuwa 1824 Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ya ɗauko hedikwatar daga Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura zuwa Anka inda take ya zuwa yau. Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura na cikin Masarautar Bakura, Anka kuma ta na cikin Masarautar Anka duka dai a Jihar Zamfara ta yau.

    Akwai jinsin Zamfarawa na biyu da suka ƙirƙiri Talata Mafara da Bukkuyum da Gummi dake Jihar Zamfara ta yau. Su kuma sun fito ne daga Rano/Kano ne a cikin ƙarni na 18, a lokacin Daular Gobir ta mamaye waɗan can jinsin Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi da Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro da Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura da Anka.

    Haka nan zaman ya ci gaba har bayyanar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a cikin ƙarni na 19 a lokacin da jihadin jaddada Addinin Musuluncin da ya jagoranta na Daular Usmaniya ya mamaye Gobirawa da sabuwar hedikwatarsu ta Alƙalawa/Alkalawa a cikin 1804 zuwa 1808 wanda shi ne abun da ya karya ƙarfin Daular Gobir har ma ya yi sanadiyar samar da sabuwar hedikwatarsu a Tcibiri ta Jamhuriyar Nijar ta yau daga baya kuma suka samar da Sabon Birnin Gobir ta Nijeriya a lokacin mulkin Sarkin Gobir Hassan Ɗan Halima.

    Tsakanin ƙarni na 17 da ƙarni na 18 da ƙarni na 19 wasu jinsin mutane sun shigo wannan yanki da ake kira Zamfara suka ƙirƙiri Masarautu.

    Misali, Katsinawa zuriyar Ƙauran Katsina Mayaƙi Gemun Dodo sun ƙirƙiri Kwatarkwashi da Tsafe, wasu Katsinawan kuma suka samar da Ƙasar Ɗansadau. Fulani Ashafawa daga yankin Yandoto suka samar da Gusau a ƙarƙashin jagorancin Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa.

    Fulani Kasarawa daga Katsina ta hannun Malam Ibrahim Ɗan Zundumi suka samar da Bunguɗu, Fulani Adarawa daga yankin Nijar ta yau, watau su Malam Muhammadu Daɗe/Da'e da ɗansa Ummaru wanda ya zamo Sarkin Maru na farko da laƙabin Banaga suka samar da Maru, Fulani Alawa ta hannun Malam Muhammadun Aya daga Mali ta yau suka samar da Birnin Magaji.

    Fulani Alibawa daga Nijar ta yau a ƙarƙashin jagorancin Abu Amil da Muhammadu Namoda da Ummaru Ɗan Jeka da Gatari da Makauru suka samar da Zurmi da Ƙaura Namoda da Moriki da Kware da Kuryad Dambo.

    Borno - Fulata/Fulata - Borno ta hannun Muhammadu Wauni suka samar da Bazai/Jangeru, Fulani daga Gwandu ta hannun Malam Muhamman Ballo suka samar da Badarawa/Shinkafi. Ɓurmawa suka fito daga Tsohuwar Daular Borno suka ƙirƙiri Bakura.

    Fulani Jallawa daga yankin Jamhuriyar Nijar ta yanzu ta hannun Malam Muhammadu Ɗan Naɓore da Malam Madaro suka samar da Rawayya da Kuryam Madaro. Zamfarawan da ake kira "Ƙayatawa" a ƙarƙashin jagorancin Malam Abarshi suka samar da Masarautar Ƙaya/Maradun kafin Fulani Torankawa ta hannun Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio su karɓi ƙasar a 1870.

    Haka aka yi ta wannan zama har bayan Jihadin Daular Usmaniya na shekarar 1804 har kuma zuwan Turawa. Bayan Turawa sun ci Sakkwato, Cibiyar Daular Usmaniya Ranar 15/03/1903 sai duka waɗan nan wurare suka zama ƙarƙashin mulkin Ingila har zuwa samar da Ƙasar Nijeriya a 1914 da samar da Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya mai yancin kanta a shekarar 1960, kenan a ƙarƙashin Lardin Nijeriya ta Arewa.

    A shekarar 1967 aka yi Jihar Arewa maso yamma mai hedikwata a Sakkwato (Sokoto, Niger, Kebbi, Zamfara na yau). A shekarar 1975/76 aka yi Jihar Sakkwato mai hedikwata a Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara), a Shekarar 1991 aka yi Jihar Kebbi daga Tsohuwar Jihar Sakkwato, sai kuma a shekarar 1996 aka yi Jihar Zamfara daga Tsohuwar Jihar Sakkwato inda aka tattara waɗan can wurare da muka ambata a sama, Anka, Talata Mafara, Bukkuyum, Gummi, Gusau, Yandoto, Maradun, Tsafe, Kwatarkwashi, Ɗansadau, Zurmi, Ƙaura Namoda, Moriki, Bunguɗu, Maru, Birnin Magaji, Shinkafi, Kware, Kuryad Dambo, Rawayya da Kuryam Madaro da Bakura aka ba su Jihar Zamfara da hedikwata a Gusau.

    Wadan nan wuraren/yankunan ne aka mayar Masarautun yanka guda 19 bayan an ƙirƙiro Jihar Zamfara. Guda 11 masu daraja ta ɗaya, guda 8 masu daraja ta biyu.

    Anka, Gusau, Zurmi, Ƙaura Namoda, Tsafe, Bunguɗu, Maradun, Talata Mafara, Bukkuyum, Gummi da Bakura sune masu daraja ta ɗaya.

    Birnin Magaji, Moriki, Shinkafi, Kwatarkwashi, Maru, Ɗansadau, Jangeru/Bazai da Birnin Yandoto sune ke da daraja ta biyu.

    A duba Tarihin Zamfara na Dr. Kurt Krieger wani Bajamushe da aka wallafa a shekarar 1959 da The Rise and Collapse of Zamfara Kingdom (PhD Thesis Na Dr. Garba Nadama, ABU Zaria, 1976) da Muƙalar Prof. Kabir Suleiman Tsafe mai Taken "Jihar Zamfara: Tarihinta Da Ƙalubalenta Da Ribatarta A Tarayyar Nijeriya" da ya gabatar a Taron Bikin Cika shekaru 20 da Ƙirƙiro Jihar Zamfara da aka gudanar a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara a watan Oktoban 2016.

    A duba Kundin PhD na Dr. Sanusi Shehu Gusau (UDUS, duk da yake ban tantance take/tittle da shekara ba) da Kundin Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Daular Zamfara na UDUS, 2020 da Kundin Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Daular Gobir na UDUS (ban riƙe shekara ba) da Littafin Infakul Maisur na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio da Littafin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero, Kano akan Masarautun Katsinar Katsinar Laka dake cikin Daular Usmaniya da kuma The Fascinating Zamfara Emirates na Malam Ibrahim Tambuwal (dake jiran ɗaɓi) domin samun ƙarin bayani akan wannan batu.

    [7:52pm, 28/06/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: LAƘABIN SARAUTAR BANAGA DAGA TSOHUWAR DAULAR ZAMFARA NE ASALINTA:

    Banaga sunan wani Mayaƙi ne da ya fito daga jinsin Zamfarawan da suka samar da Masarautar Mafara/Talata Mafara ta yau. Waɗan da ke da zumunci da Zamfarawan Masarautar Bukkuyum da Gummi dukan su dai suna a Jihar Zamfara ta yau ne.

    Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau muzakkarin gaske ne da ya fito daga tushensa tun suna zaune a Tunfafiya (Tunfafiya tana akan Titin Gusau zuwa Sakkwato, yan kilomitoci kaɗan kafin zuwa garin Talata Mafara, hedikwatar Masarautar Zamfarawan Mafara ta yanzu a Jihar Zamfara) a ƙarshe ƙarshen ƙarni na 18.

    Ya tasarwa Kudu maso gaba shin Tunfafiya/Mafara sai da ya ƙirƙiri gari da ya kira da Birninsa, watau " Birnin Banaga". Anan ya zauna har zuwa bayyanar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da mataimakansa da suka shigo yankin daga wajensu na asali, kenan su Malam Muhammadu Daɗe/Daɗi/Da'e wasu Fulani Adarawa da suka fito daga wani yanki na Jamhuriyar Nijar ta yau.

    Daga Birnin Banaga ne (a halin yanzu wannan Birni ne ake kira "Tsohon Birnin Banaga dake cikin Masarautar Maru a Jihar Zamfara) ya dinga kai samame ya zuwa iyakar Daular Katsina ta yamma (gabas da shi kenan) ya kuma matsawa Masarautar Maska lamba da hare-hare, uwa uba ya hana sakewa ga masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya.

    Da al'amarinsa ya yi tsanani ne Malam Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya umurci Malam Muhammadu Daɗi/Daɗe/Da'e da zuriyarsa da a lokacin suke zaune a yankin Jabaka (Jabaka hedikwatar gunduma ce a Masarautar Maru ta yau) da Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa dake zaune a yankin Yandoto da Malam Muhammadu Bachiri dake Bunguɗu da Malam Karaf dake Kannu (Kannu gunduma ce a halin yanzu a cikin Masarautar Birnin Magaji) da su fitar da shi daga wannan yanki.

    Da wannan ne sai suka yi masa taron dangin da ya sanya ya fice daga wannan Birni nasa, watau "Birnin Banaga". Ya je yamma ya ƙirƙiri sabon mazauni da ya kira "Murai"/"Morai" ya ci gaba da mulkinsa da laƙabin "Banagan Murai" (Murai/Morai hedikwatar gunduma ce a Masarautar Talata Mafara a Jihar Zamfara).

    Ya sake fita daga Murai ya je yamma ya ƙirƙiri garin Anka ya ci gaba da rayuwa tare da jama'arsa har zuwa shiyoyin 1815 zuwa 1824 lokacin da Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo daga zuriyar Sarkin Zamfara Abarshi (Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi ta Ƙasar Zurmi, Jihar Zamfara tun a shekarar 1300 da Birnin Zamfara a Ƙasar Isa, Jihar Sakkwato har zuwa 1764 da Kiyawa a Masarautar Birnin Magaji da Banga da Ƙuryam Madaro dake Masarautar Ƙaura Namoda da Sabongarin Damri a Masarautar Bakura duka a Jihar Zamfara) suka sake fitar dashi da jama'arsa duk da yake ba ta hanyar yaƙi ba.

    Daga Anka ne ya fita ya sake girka wani gari da ya kira "Sabon Birnin Banaga" da ke Kudu maso gaba shin Anka (wannan gari hedikwatar gundumar Sabon Birnin Banaga ne a Masarautar Anka, Jihar Zamfara) inda a nan ne Allah SWT ya yi masa wafati.

    Kenan daga Tunfafiya zuwa Birnin Banaga zuwa Murai zuwa Anka zuwa Sabon Birnin Banaga ne Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ya yi rayuwarsa.

    Daga baya ne masu jihadi suka mayar da garin Maru a matsayin sabuwar hedikwatar wannan yanki da Birnin Banaga yake, suka naɗa Malam Ummaru ɗan Malam Muhammadu Daɗi/Daɗe/Da'e a matsayin jagora da laƙabin "Banaga" a matsayin Sarautarsa domin taskace Tarihin wannan muzakkari watau Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau.

    Daga wannan ne wasu Masarautun Arewancin Nijeriya suka ari laƙabin wannan Sarauta ta "Banaga" suka ci gaba da amfani da ita/shi.

    Allah SWT ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, ya yalwata bayanmu, amin.

    Ana iya duba "Tarihin Zamfara" na Dr. Kurt Krieger wani Baturen Jamus da aka buga a shekarar 1959 da "The Rise and Collapse of Zamfara Kingdom" PhD Thesis na Dr. Garba Nadama (ABU Zaria, 1976) da "The History of Zamfara from 1764 to 2013" PhD Thesis na Dr. Sanusi Shehu Gusau (UDUS, 2017) da Littafin Infaƙul Maisur wallafar Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da kuma Littafin Shaihin Malami Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero, Kano da ya wallafa akan rawar da masu jihadi suka taka a Katsinar Laka domin samun ƙarin bayani. 

    [3:42pm, 29/06/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: FITAR BANAGA ƊAN BATURE ƊAN DANAU DAGA ANKA ZUWA SABON WURIN DA YA KAFA, WATAU " SABON BIRNIN BANAGA.

    Akwai magana/maganganu guda biyu game da wannan fitar ta Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau daga Anka da suka fi shahara a Tarihin samar da Anka a matsayin hedikwatar ƙarshe ta Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi da Birnin Zamfara da Kiyawa da Banga da Ƙuryam Madaro da Sabongarin Damri tsakanin 1300 zuwa 1815/1824.

    Ta farko ita ce wacce/wadda Dr. Kurt Krieger ya tafi akai cewa Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo (1815-1824) ne ya yi wa Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau sammu da aka haɗa a kaɓakin Tuwo aka ɗauka daga Sabongarin Damri zuwa Anka. Har Bawan Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo wanda ya ɗauki sammun zuwa Anka ya ambata a cikin aikinsa "Tarihin Zamfara" (wanda akasari daga rubutun magabata ne da suka mulki Daular Zamfara da aka rubuta a cikin Ajami da ya karɓe daga Fadar Sarkin Zamfaran Anka a cikin 1940s/50s) ya tafi dashi Ƙasar su, Jamus. A shekarar 1959 kuma ya wallafa wannan Littafi nasa mai suna "Tarihin Zamfara" wanda kusan shi ne madogara ta biyu akan Tarihin Daular Zamfara bancin Infaƙul Maisur na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.

    A ciki ya bayyana cewa bayan wannan Bawa ya girke wannan kaɓakin tuwo a Ƙofar gidan Banaga Ɗan Bature a Anka (a gidan ne Sarakunan Zamfara tun daga Sarki Ɗan Baƙo, 1815-1824 ya zuwa yau suke sarauta) da ya fito Sallar Asuba ya yi kiciɓis da shi sai sammun ya shige shi.

    Da hantsi ya tara hakimansa da manyan mutanen garin ya sanar dasu cewa zasu tashi daga Anka ba tare da ɓata lokaci ba, ya yanke shawara umurni ne ya ke basu. Saboda haka a ranar suka kimtsa kayansu, su ka fice daga garin, suka tsallaka Kogin Zamfara dake Kudu da Anka ya sake kafa sabon zama da ya kira "Sabon Birnin Banaga" inda na ambata a cikin rubutun da ya gabata cewa anan ne Allah ya yi masa wafati. Na je garin a cikin farko farkon shekarar 2011.

    Magana ta biyu kuma akwai bayanin da ke nuna cewa umurnin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne Sarakunan Zamfara na wancan lokaci da ke zaune a Sabongarin Damri su ka bi wajen fitar da shi daga Anka da zummar su zauni wurin a matsayin sabuwar hedikwatarsu duk da yake ba a bayyana ko ta wace hanya suka bi ba wajen aiwatar da wannan umurni ba, ban kuma ci karo da wannan bayani a rubuce ba. Allahu Wa'alam!!!

    Fatsa ko hwatsa

    Fatsa/Hwatsa

    [11:21am, 01/07/2024] Prof. A.M. Bunza: Mamari/ƙugiya sai an saka zare za ta zama fatsa.

    [11:32am, 01/07/2024] Dr. Ali Usman Umar Lafiya: Madalla da wannan ƙarin haske, garnaƙaƙin Farfesa. 🙏🏼

    [11:36am, 01/07/2024] Sarkin Rafin Gobir Nikuma atawa mahanga wannan aikin na jafa mamari da zare da iccen da akeyi wato sigar wannan ta kama kihin itace Hwatsa/fatsa,

    Domin ko'an handa mamari da zare ba'akiransu hwatsa Sai dai akirasu mamarin hwatsa ko zaren Hwatsa

    Misali idan mutun nadaniyar yin hwatsa zakaji ya ce wannan mamari zaiyi hwata ko wannan zaren zaiyi hwatsa kokuma wannan iccen zaiyi hwatsa ko zankama hwara hwatsa

    Kenan Sai anhada abubuwa guda hudu 4 sannan za'aiya hwatsa

    Mamari

    Zare

    Icce

    Hwara/fara

    Saboda haka wannan sigar ta kamun kihin itace Hwatsa/fatsa

    Maassalam,

    [11:43am, 01/07/2024] +234 703 232 2222: Sosai Sai an saka zare Da DanKaru Da Sanda Zata Zama Hwatsa/fatsa

    Sannan Akwai Roka Hwatsa/Fatsa wadda akeyi da zare Mai Wanda Daga karshe inda mamari yake a daure Sai a daura mata adaura mata Dutse Domin mamarin ya nutse a kasa sosai..........

    [11:53am, 01/07/2024] Sarkin Rafin Gobir Dan uwana malan Abdullahi idan ansaka zare da mamari ba'akiransu hwatsa Sai dai akirasu anhada kayanyin hwatsa

    Domin wanda yatahi wajen yin hwatsa bacemashi yatahi wurin sun kihi Sai dai ace wane yatahi wurin hwatsa

    Amman wanda yatahi da Homa Sai ace wane yatahi wurin su, sunkihi

    [11:58am, 01/07/2024] Dr. Ali Usman Umar Lafiya: Madalla da waɗannan bayanai naku. Ni, a karan kaina, na ƙaru sosai. Daga cikin abubuwan da suke samar da fatsa kenan akwai:

    Ic (c)e/sanda

    Zare

    Fara

    Mamari

    Dutse*

    Tambayata ita ce, mene sunan abincin (mis: tana, ko gayan tuwo da akan maƙala a jikin mamarin) da ake yaudarar kifi da shi? Don Allah, kuma ina son ƙarin bayani game da laƙa/ɗaura dutse a jikin mamarin. Na gode.

    [1:05pm, 01/07/2024] Sarkin Rafin Gobir Wato atawa fahimta sigar kama kihi Gabaɗaya kusan kowane ɓangare na ƙasar Hausa Akansamu Babancin yanayin da kowa ke irin tashi dabara kamun kihi.

    Wasu lokutta ma Akansamu Banbancin yanda wasu ke kiran shikanshi wani kalan kihin da kayan kamun kihin,

    Misali mu awajanmu bama amfani da kowane irin Dutci a wajen yin hwatsa kawaidai idan mukasamu mamari da zare da icce/sanda da Hwara shikenan komi yahadu, Sai bakin Gulbi wurin hwatsa/fatsa,

    Yanzu ga maganar tuwo ka kawo nidai atamu Al'ada ta hwatsa bansan Anayin amfani da tuwo ba. Maassalam. 



    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.