Citation: Bungudu, H.U. & Idris, H.T. (2024). Salon Zayyana a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 271-277. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.035.
Salon Zayyana a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Daga
Dr. Haruna Umar
Bunguɗu
(Sarkin Gobir na
Bunguɗu)
Ƙibɗau: harunaumarbungudu@gmail.com
Lambar waya: 08065429369
Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi da Ƙere-Ƙere Ta Gwamnatin Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara
Da
Hauwa Tanko Idris
Ƙibɗau: tankoidrishauwa@gmail.com
Lambar waya:
08038025492
Sashen Hausa
Kwalejin Ilmin Addinin Muslunci Da Shari’a Ta Malam Aminu Kano, Jihar Kano
Tsakure
Wannan muƙala ta
mayar da hankali ne wajen gano ire-iren dabbobi da tsuntsaye da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a zubin waƙoƙinsa.
Manufar binciken ita ce fito da hikimomin Uban kiɗi na amfani da dabbobi da tsuntsaye wajen fitar da
ma’anoni a wasu waƙoƙinsa waɗanda ya riƙa yi wa jama’a
daban-daban. Ra’in da aka yi amfani da shi a wannan aikin binciken shi ne ra’in
waƙar baka
Bahaushiya na Gusau (2003). Hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattaro
bayanan wannan aikin sun haɗa da sauraren waƙoƙin Malamin
waƙa wato
makaɗa Sa’idu
Faru tare da tattaunawa da wasu masana da masu sha’awar nazarin waƙoƙin nasa.
Bugu da ƙari, ba a
iyakance yawan waƙoƙin da za a nemo sunayen waɗannan dabbobi da tsuntsaye da makaɗin ya yi amfani da su ba, domin ba dukan waƙoƙin nasa
ne ya yi hakan ba, sai dai a kalli waƙoƙin a zaƙulo
ire-iren waɗannan
turakun.
Gabatarwa
Waƙar baka aba ce wadda take buƙatar shiryawa da tsara batutuwa a samar da gangar jikinta cikin azanci da
hazaƙa da naƙaltar harshe da
ake amfani da shi. Daga nan , sai a rera ta tare da amshi a kuma daɗa fito da armashinta ta amfani da
sautin kiɗa.
Rairawa da zaƙin murya da
sauran abubuwan da suka danganci rauji abubuwa ne muhimmai a wajen samar da
nagartar waƙoƙin baka. Waƙoƙin baka suna
tafiya ne tare da sautin kiɗa, amma akwai
wasu waƙoƙin waɗanda ba a haɗa su da wani amon kiɗa. Harshen da makaɗan baka suke amfani da shi a bisa kansa cikakke ne, Domin kuwa, wasu sukan
ce harshen waƙa taƙadiri ne saboda yakan bauɗe wa wasu ƙa’idojin nahawu. Kauce wa daidaitacciyar ƙa’ida kuwa salo ne a waƙa, amma duk da
lalurar da kan sa makaɗan baka
su karya ƙa’idar nahawu, waƙoƙinsu suna hawa bisa ingantaccen tsari na musamman, mai ɗaga hankali, mai amsa-amon kari da
yake daidaita layuka cikin ɗiya. Har
wa yau, a waƙoƙin baka ana amfani da hanyoyin adonta harshe da sauran
dabarun nuna gwaninta da burgewa. Waƙar baka
tana tafiya da lokaci na aukuwar sababbin al’amura. Muddun dai makaɗi na raye, yakan so ya yi wa waƙa daɗi ta kawo
wasu abubuwan da suke faruwa na rayuwa, wajen yin wannan aikin ne
yake faɗawa tarkon rage
wasu ɗiyan. Haka kuma a
waƙar baka ba ta da tsayayyar doka ko ƙa’ida dangane da shirya layuka a ɗiyanta wato babu wata doka da take ƙayyade
yawan layukan ɗan waƙa. Makaɗan baka ba su tauye kansu wajen shirya layukan ɗiyan waƙa a kan wani ƙayyadajjen adadi, sukan numfasa, su ƙara ‘ɗa’ inda
duk saƙo ƙarami ya ƙare, kuma yin haka ba zai ruguza musu tsarin karin
murya ba.
Taƙaitaccen
Tarihin Makaɗa Sa’idu
Faru
An haifi
makaɗa Sa’idu Faru a
garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, ƙaramar hukumar Maradun a wajejen shekara ta 1932. Ana
kuma yi masa laƙabi da Ɗan’umma‛ wanda
matar ƙanin ubansa ta sanya
masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma. Shi ya sa ita kuma
ta dinga kiran sa Ɗan’umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na
yanka wato Sa’idu. Shi kansa Sa’idu Faru yakan yi wa kansa da kansa kirari yana
cewa: Ɗan Ummma Rumgumi ko Ɗan Tumba
Rumgumi (Gusau, 1996:117).
Sunan mahaifin
Sa’idu Faru shi ne makaɗa
Abubakar ɗan Abdu,
shi kuwa makaɗa Abdu,
Alu Maikurya ya haife shi. Ashe ke nan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu Maikurya. Sai dai mahaifiyar Sa’idu mutuniyar Banga ta cikin ƙasar Ƙaura-Namoda ce.
Sa’idu Faru kamar sauran makaɗan fada ya yi gadon kiɗa ta
wajen mahaifinsa. Kakansa na sama makaɗa Alu makaɗin kurya
ta kiɗin yaƙi ne wadda ake yi wa kirari kurya gangar mutuwa. Makaɗa Alu ya yi waƙoƙi da yawa a zamani da yawa a tsawon lokaci.
Sa’idu
Faru ya yi ƙuruciyarsa ne a garin Banga ta Ƙaura Namoda, amma kafin ya girma ƙwarai sai
ya koma wurin tsohonsa makaɗa Abubakar
a Faru. Makaɗa Sa’idu
bai samu ilmin muhammadiyya da yawa ba, sai dai an sa shi makarantar allo inda
yai zurfi ga karatun Alƙur’ani mai
tsarki. Haka kuma ba a sa shi makarantar bako ba, domin haka bai san komai ba
game da sha’anin boko. Alal haƙiƙa tun yana yaro sha’anin kiɗa da waƙa ya ɗauke masa
hankali. Makaɗa Sa’idu
Faru ya koyi waƙa wurin mahaifinsa
makaɗa Abubakar, waƙoƙin suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da
hikima tare da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi. Tun Sa’ida Faru yana da
shekara goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan da ya cimma shekaru goma sha shida ya soma karɓa. Baya ga
tsohonsa makaɗi
Abubakar Sa’idu Faru bai koyi kiɗa wurin kowane makaɗi ba, dukkan salailai iri-iri da yake sakawa a waƙoƙinsa tushen su mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta
gane fasalin waƙa, ya sa himma da
ƙwazo har zuwa lokacin da Allah ya karɓi ransa.
Sa’idu
Faru ya samu cin gashin kansa, ya fara da wata waƙa mai daɗin gaske ƙunshe da tarin hikimomi ga kaɗan daga cikinta a shekarar 1940:
Jagora : Bi da maza ɗan Joɗi na
Rwafi,
‘Y/Amshi : Iro magajin Shehu da Bello.
Jagora : Dawaya kora ɗimau na Wakili.
‘Y/Amshi : Dawaya kora na ɗimau na Wakili.
Jagora : Dawaya kora na ɗimau na Wakili.
‘Y/Amshi : Dawaya kora ɗimau na Wakili,
: Uban sarkin gida Bello da Yari.
Jagora : Ruwa da Kada,………………
Wannan waƙar da ya fara yi ita ce wadda ya yi wa tsohon Sarkin
Yamman Faru Ibrahim. Daga nan Sa’idu Faru ya ci gaba da yi wa sarakuna da
‘ya’yan sarakuna waƙoƙi, har zuwa lokacin da ya sadu da sarkin Kudu Muhammadu
Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi
Abubakar. Ya samu yi wa Sarkin Kudu Macciɗo waƙoƙi tun lokacin da
yake Mafara yana riƙe da muƙamin sarkin Gabas watau uban ƙasar Talatar Mafara.
Makaɗa Sa’idu Faru yana da matan aure
guda uku (3) tare da ‘ya’ya ishirin da shida (26) maza da mata, a cikinsu goma
sha ɗaya (11) sun
rasu, saura goma sha biyar. (15). Yana kuma da jikoki. Sa’idu Faru ya rasu a shekarar
1987 a sanadiyyar rashin lafiya da ya yi fama da ita.
Dabarun Gudanar da Bincike
An bi
wasu hanyoyi domin gudanar da wannan binciken waɗanda suka haɗa da tattaro dukkanin bayanansa ne daga tushe. A cikin wannan takarda an ɗauki wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru a matsayin tushen
bayani domin taƙaita nazari a
kansu. Haka kuma yana daga cikin dalilin wannan bincike na gano irin dabbobi da
tsuntsayen da makaɗa Sa’idu
Faru ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa.
Wani
masani ya kalli salo a waƙoƙin baka kamar haka:
Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi ke
kyautata zaren tunaninsa, ya sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa na
isar da saƙo a waƙa. (Gusau
2003:54).
Ga abin da wannan masani ya nuna salo shi ne dabarun da
mai magana ya ƙunsa a cikin zancensa da nufin isar da saƙo ta hanyar
da za a fahimce shi cikin sauƙi ko da wahala, a cikin raha ko cikin ƙosawa. Duk
ta hanyar da masu saurare suka ji jawabin daga hanyoyin da aka ambata, to shi
ne irin salon da mai zancen ya yi amfani da shi.
A wata ma’anar da aka bayar cewa aka yi:
Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka
bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya
ta yadda saƙon waƙar zai isa
ga mai saurare ko karatun waƙar. (Yahya 1999:3).
Wannan ma’ana ita ma kusan manufarta ɗaya da wadda ta gabace ta. Bayanin yana nuni ne ga irin dabarun da
mawaƙi yake
amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jama’a a cikinsa ba tare da gundura ba. Wato saƙonsa ya isa
cikin birnin zuciyar masu saurare cikin nishaɗi da ban
sha’awa[1].
Shi kuma wani malamin cewa ya yi:
Masana da manazarta suna ganin cewa salo yana da wuyar a
gane shi a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa dangane da
ma’anarsa. To amma muna iya cewa salo shi ne hanyoyin isar da saƙo[2],
(Ɗangambo 2007:34).
Bayanin wannan malami bai tsawaita ba. Ya taƙaita abin
da waɗanda aka fara ambata suka faɗa tare da ƙara bayyana
wahalar bayyana ma’anar salo ta amfani da kalmomi kawai. Duk da haka ya taƙaita ya ce
hanyoyin isar da saƙo su ne salo, waɗanda nake ganin su ne waɗanda waɗancan malamai da na fara ambata suka faɗa.
A bisa bayanan masana ana iya cewa, salo wata dabara ce
ta isar da saƙo ta hanyar zaɓen kalmomin da suka dace da abin
da ake zance ta yadda zuciyar mai saurare ko karatun abun za ta karɓe[3]
shi, ya Allah a cikin sauƙi ko tsanani.
Salon Zayyana
Salon zayyana wani salo ne da mawaƙa kan yi amfani da shi a cikin
waƙoƙinsu, inda
suke kwararo wasu kalamai waɗanda ke iya nuna a zuciya kamar ga abin nan yana
faruwa. Kamar kana tsaye kana kallo. Ga yadda masana suka ce game da ma’anar
zayyana:
Wani masani yana cewa:
Salon zayyana na nufin amfani da kalmomi a cikin waƙa tattare
da kalmomin na maganar da suka fito cikinta za su ƙirƙiro siffar abu ko yanayi a cikin
zuciyar mai karatu ko mai sauraren waƙar. (Yahya 2001: 89)
C.N.H.N Ta bayyana salon zayyana da “Ƙawata wani
abu: Zana sura ko kamannin wani abu”( C.N.H.N 2006:493).
Ɗangambo ya
ce:” Salon zayyana na nufin doguwar siffantawa ko hoto cikin bayani.” (Ɗangambo 2007:44)
Bunguɗu cewa ya yi: “Wannan salo shi ne wanda mawaƙi kan tsaro
bayanin faruwar wani abu, ko yadda zai faru a cikin waƙa ta har yadda mai saurare zai
ji kamar ga abin nan a gabansa yana faruwa. Wato bayanin da mawaƙin ya yi ya
sa idanun zuciyar mai saurare na ganin yadda abin ke gudana” (Bunguɗu 2015).
Salon Zayyana A Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Sa’idu
Faru
Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da waɗannan jinsi na dabbobi da tsuntsaye
a mafiya yawan ɗiyan waƙoƙinsa. Dubi yadda
ya kawo ɗiyan da
ya ambaci doki danda kamar haka:
Jagora : Mu’azu Kullum mahwalki nikai sabo,
‘Y/Amshi : Shehu ya ba mu doki da kayanai.
Jagora : Daudu kullum mahwalki nikai sabo.
‘Y/Amshi : Shehu ya ba mu doki da kaya nai,
: Danda hwari biyat wanda an nan haka,
: Inda Liman ka bi zai Masallaci,
: Komai shirin daga na Muhamman Bello,
: Shehu ɗan Shehu ganɗon ƙasah Hausa
(Sa’idu Faru: Waƙar Shehu Muhammadu Ɗangwaggo).
A wannan ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu
ya ambaci ‘doki’ danda hwari biyat. Wannan doki shi ne mai fari ga ƙafafuwansa guda huɗun da kuma fari a goshinsa. Wani kuma bayan farin da ke ƙafafuwansa, ana iya samun farin a cikinsa maimakon a
goshinsa. Malamin waƙa ya ambaci irin
waɗannan dawaki a
cikin waƙoƙinsa. Wanda ya
saurari waɗannan ɗiyan waƙar zai ga hoton irin wannan dokin da ya ambata. Dubi yadda yake cewa Daudu
ya ba mu doki da kayanai a wannan ɗan waƙar.
Haka zalika a wata waƙar ya ambaci wasu dabbobin kamar haka:
Jagora : Toron
giwa yana abun da yakai,
: Ya shigo dawa,
‘Y/Amshi : ‘Yan namu suna ta gaisai,
: Sun ba da gaskiya
: Bil’amo na cikin sabara,
: Ya soke kainai.
: Zomo ya taho ya wuce ya gaida toro
‘Y/Amshi : Shi ya yadda Allah ka wa kowa
nagarta.
(Sa’idu Faru, waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo).
A wannan
wurin makaɗa Sa’idu
Faru ya kawo sunayen wasu dabbobin kamar toron giwa da bil’amo (wato
alade) da zomo. Waɗannan duk
dabbobi ne da mutum zai riƙa ganin hotunansu
a cikin zuciyarsa idan ya ji yadda mawaƙin ya
ambato su a waƙarsa. Kalli yadda
ya ambaci waɗannan
dabbobin toron giwa yana abin da yakai ya shigo dawa, wato yana taƙama amma bil’amo na cikin sabara ya soke kainai.
A wani
wurin ya ambaci wasu dabbobin da cewa:
Jagora : In jaki ya gaza
da kaya,
: A aza ma raƙumi,
‘Y/Amshi : Ni na san
kwatancin irin kayanka jakki.
(Sa’idu Faru, waƙar Sarkin Kudun Sakkwato)
Ya yi wani ɗan waƙar mai kama da
wannan inda ya ce:
Jagora : Jakki
kankambab banza garai,
‘Y/Amshi : Wasu kaya sai bisa raƙumi.
(Sa’idu
Faru, waƙar Usman Dangwaggo Bunguɗu)
A cikin
waɗannan ɗiyan waƙoƙin ya kawo sunan jaki da raƙumi inda ya kwatanta irin ƙwazonsu wajen ɗaukar kaya inda ya nuna fiyayyar da
ke tsakanin jaki da raƙumi ta fannin ɗaukar kaya, wato dai duk kayan da
suka fi ƙarfin jaki raƙumi na iya ɗauke su. A cikin rayuwar mai
sauraren waɗannan ɗiyan waƙoƙin zai riƙa ganin hotunan
waɗannan dabbobin kamar
an ɗora ma jaki kaya
ya durƙushe saboda nauyinsu, amma an sauke an ɗora ga raƙumi ya tafi da su ba tare da wata matsala ba. Dubi yadda
mawaƙin ke cewa in jaki ya gaza da kaya a aza ma raƙumi. Sai kuma ya ce jaki kankambab banza garai, wasu kaya
sai bisa raƙumi.
Haka ya kira kwaɗo a wata waƙarsa ,
Jagora : Allah ya zubo ruwa,
: Hwadama duk ta shahe,
‘Y/Amshi : Masu hito has sun hwara hwaɗin,
: Yanzu tay yi kyau.
(Sa’idu Faru, waƙar Sarkin
Kudun Sakkwato Alhaji Macciɗo)
Makaɗa Sa’idu ya ambaci fasalin damina inda ruwa kan game wurare saboda yawansu a
wannan ɗan waƙar ta yadda mai sauraro zai ga hoton a zuciyarsa kamar ga
shi nan ruwa yana zuba kuma duk ko’ina ya cike da ruwan. Dubi cewarsa Allah ya
zubo ruwa hwadama dut ta shahe.
Haka kuma
Sa’idu Faru ya ambaci wata dabbar wato gada a wata waƙar:
Jagora : In wuri da mata ciki
: Hat tumag gada yakai.
(Sa’idu Faru, waƙar sarkin Tudun Falale)
Akwai hoton wata dabba a wannan ɗan waƙar wato gada, ita gada wata dabba ce mai kama da akuya wadda take
rayuwarta a cikin daji, kuma ba ta jin nauyin jikinta. Idan mutun ya ji wannan ɗan waƙar zai ga hoton kamar ga gada nan tana tsalle-tsalle, dubi yadda ya ambaci
halayyar wani mutum a wannan ɗan waƙar: In wurin da mata ciki har tumag gada yakai.
Haka kuma
shi ma maciji ya zo cikin waƙa kamar haka:
Jagora : Farin
maciji cizonka ba dahi,
: A yi gumba a sha a samu lafiya,
: Gumba ko ba cizon ƙwaro taimako takai.
(Sa’idu Faru, waƙar).
Akwai
hikima ga wannan mawaƙin domin fitowa
da wannan dabbar wato maciji amma fari wanda bai sa dafi idan ya ciji mutum, to
a nan sai ka ga hoton wani mutum da irin wannan macijin ya ciza sai aka ba shi
gumba ya sha ya sami lafiya babu wata wahala. Ya ce farin maciji cizonka ba
dafi a yi gumba a sha a sami lahiya.
A wani wurin kuwa a wata waƙar tasa ya kwatanta wasu dabbobi:
Jagora : Ahihiya da kunkuru
: Shawara guda sukai.
(Sa’idu Faru, waƙar Alhaji Muhammadu Bala Dagacin Falale).
Yahihiya ɗan uwan kunkuru ne yanayin halittarsu iri ɗaya ce, sai dai yahihiya a
ruwa yake rayuwa shi ma kunkuru a ruwa yake rayuwa duk tsarinsu ɗaya. Akwai hoton waɗannan dabbobin a cikin wannan ɗan waƙar, kamar ga su nan kwance suna shawara. Dubi yadda ya ce
a wannan ɗan waƙar yahihiya da kunkuru shawara guda sukai.
Makaɗa Sa’idu Faru ya kawo wata dabbar a cikin wannan ɗan waƙar:
Jagora : Ina bangabangan ga mai ‘yar mahuta,
: Alade
wurin shan giya kah hi suna,
(Sa’idu Faru, waƙar,Muhammadu Macciɗo).
A sifar wannan dabbar wato alade kamar ta wani
mashayin giya wanda ya sha giya take. Mai sauraron wannan ɗan waƙar haka zai riƙa ganin hoton alade. Kalli yadda ya ce alade wurin shan
giya kah hi kowa.
Haka a nan ma ‚
Jagora : Sai Bil’amo uban dubara,
: Shi ɗai yaz zo ga giwa,
: Yac ce albarkacinki niz zaka,
: In samu ruwan da nis sha,
: Giwa
ta ba shi hili,
: Ya sami ruwan da yas sha,
: Ya sha ya kuma ba ɗiyanai.
‘Y/Amshi : Yay wa dangi
kirari,
: Yac ce ya ƙwato da ƙarhi,
: Zomo
yac ce tsaya shege lallashin ta kay yi,
: In ƙarhi
gaskiya na,
: Koma ɗebo gabana.
(Sa’idu Faru, waƙar Sarki Sulaiman Muhammadu Bello).
Akwai irin wannan salon na zayyana a cikin
wannan ɗan waƙar kamar ga su nan suna tsaye suna gardandami a
tsakaninsu, wannan ya faɗi wannan
ya ce a’a, har dai a kai ga ‘yar ƙure. Dubi cewarsa
sai bil’amo uban dubara shi ɗai yaz zo
ga giwa, sai kuma ya yi wa danginsa ƙarya ya
ce ya ƙwato da ƙarfi, shi ko zomo
ya ƙure shi ya ce in da gaske ne ya koma ya ɗebo ruwan gabanai.
A cikin wasu waƙoƙin Uban kiɗi ya kawo hotunan wasu tsuntsaye domin aikin nasa ya tafi daidai. Dubi inda
ya ce :
Jagora : Da hasbiya da kurciya,
‘Y/Amshi : Shawara guda sukai.
Da
hasbiya da kurciya duk tsuntsaye ne waɗanda Ubankiɗi ya kawo
a wannan ɗan waƙar. Mai sauraron wannan ɗan waƙar zai ga hoton
wasu tsuntsaye nan biyu sun haɗe kansu suna shawara saboda sun yarda da junansu.
Jagora : Jan
zakara ya yi ƙiƙiriƙi,
: Ya tare garkag gidan Ubanai.
‘Y/Amshi : Ya bak kwaɗɗo yana
cikin rame,
: Ya lanƙwashe tsara.
: Gwauron
giwa uban Galadima,
: Ɗan Sambo
ginjimi,
: Gamshiƙan Amadu
na Maigandi,
: Kai a uban zagi.
(Sa’idu Faru, waƙar Sarki Sulaiman Muhammadu Bello).
Zakara wani tsuntsu ne wanda makaɗa ya kawo hotonsa a cikin wannan ɗan waƙar, inda mai sauraren zai ga kamar ga zakaran nan kuma ja yana ƙiƙiriki yana gyara
gashinsa. Haka kuma ya ambaci kwaɗɗo wanda shi ba tsuntsu ba ne.
A wani wurin kuma Ɗantumba Rungumi ya kawo ma masu saurare wasu hotunan tsuntsaye guda huɗu kamar haka:
Jagora
: Ko jiya na iske gamdayaƙi da tuji,
: Sun iske jinjimi,
: To sun kau mirɗa gardama,
: Sun iske su bubuƙuwa ruwa.
‘Y/Amshi : Dan nan ni ko ina gaton gava,
: Sai niƙ ƙwala gaisuwa
: Su ko sun daƙile ni duk,
: Ni ko niƙ ƙara gaisuwa,
: Dan nan kulmin da ac cikin gurbi,
:Ya amsa gaisuwa.
Jagora : Dan nan sai Jinjimi da yad darzaza,
: Yas suntule su dut.
‘Y/Amshi : Shi ko tuji
da ad da girman baki,
: Yak kwashe jinjimi,
: Dan nan bubuƙuwa da tar ruru,
: Tag gangame su duk,
: Dan nan nis san duniyag ga,
: Ko mina ne wani mayen wani.
Jagora : Ran nan,
‘Y/Amshi : Nis san duniyag ga,
: Ko mina ne wani mayen wani.
: Gwauron
giwa uban Galadima,
: Ɗan Sambo
ginjimi,
: Gamshiƙan Amadu
na Maigandi,
: Kai a uban Zagi.
Makaɗa Sa’idu Faru ya
zayyano wasu tsuntsaye guda huɗu a bakin ruwa waɗanda za a
iya ganin hotunansu suna wata gardama a kan wani abu da ya dame su. Daga ƙarshe sai wanda ya fi wani ƙarfi ya cinye ɗan’uwansa
har dai na ƙarshe wanda ya cinye dukan tsuntsayen wato bubuƙuwa.
A wani wuri kuma ya ambaci wasu
tsuntsayen kamar yadda ake ganin hotunansu. Dubi yadda yake cewa:
Jagora
: Tahiyag ga da kay yi da bani nan,
: Nib bi ka ina gudu ga ni nan,
: Na nib bi Gusau sai niw wuce,
: Kuma nib bi Kwatarkwashi niw wuce,
: Kuma nib bi ta Tcahe ina gudu,
: Can na kusa kai wa Zariya,
: Dan nan Daudu ni kau sai nit tsaya,
: Sai sarkin Zazzau nig gani,
: Ya ce man Muhamman ya tai haji,
: Sai nis saki hanya niy Gabas,
: Can na tava ‘yat tafiya kaɗan,
: Sai ni
ishe Suda na kiyo,
: Tana ta waƙas Sarkin kudu,
: Rai nai ya daɗe Sarkin kudu,
: Alasabbinane ɗan Amadu,
: Allah shi ƙara mai nasara,
: Nic ce Suda waƙa akai?
: Tac ce lalle waƙa nikai,
: Waƙam Muhamman Sarkin Kudu,
: Waƙan nan da Ɗan’umma yai mashi,
: Bancin uwat tsuntsaye nike,
: Inda kamam mulki na nikai,
: Da nai mai wasiƙa yai man kiɗi,
: Dan nan ni ko sai niw wuce,
: Can na taɓa ‘yat tahiya kaɗan,
: Sai ni ishe burtu na kiyo,
: Shina ta waƙar Sarkin Kudu,
: Rainai ya daɗe Sarkin Kudu,
: Alasabbinane ɗan Amadu,
: Allah ya ƙara mai nassara,
: Nic ce burtu waƙa akai?
: Yac ce lalle waƙa nikai,
: Waƙam Muhamman Sarkin Kudu,
: In na yi ta za ni wurin kiyo,
: In na so abinci sai na ije,
: Dan nan ni kau sai niw wuce,
.............................................
‘Y/Amshi : Kana shire Baban ‘Yan ruwa,
: Na
Bello jikan Ɗanhodiyo.
Suda wani tsuntsu ne mai yawan surutu wanda Hausawa kan laƙaba wa wani mutum wanda ke da yawan magana
sunan saboda surutunsa. Shi ma burtu tsuntsun ne mai izza
saboda irin halittarsa da kuma yadda mutane suke ɗaukar sa. A wannan ɗan waƙar ana iya
ganin hoton waɗannan tsuntsaye a tsaye suna
rera waƙa.
Abubuwan da Binciken ya gano
Wannan binciken ya gano cewa makaɗa Sa’idu faru ya kawo hotunan wasu dabbobi da tsuntsaye waɗanda ya ambata a cikin waƙoƙinsa, inda da
zarar mai saurare ya saurari waƙar zai ga kamar ga su nan a fili yana gani, kuma sai Uban kiɗi ya riƙa kawo sifofinsu ta yadda sai mutum ya gane su yake nufi. Misali, Tuji da ad da girman baki da sauran irinsu. Dubi wani wurin da ya riƙa haɗa tsuntsaye ko dabbobi masu
sifa kusan iri ɗaya yana
cewa shawara guda sukai.
Kammalawa
Godiya ta
tabbata ga Allah Maɗaukakin sarki wanda ya nufe mu
da kammala wannan binciken wanda ya kalli yadda makaɗa Sa’idu Faru yake saka dabbobi da tsuntsaye a cikin waƙarsa ta
yadda idan mai sauraren waƙoƙin zai riƙa ganin
hotunansu a cikin ransa wato wannan wani salo ne da masana suka sa wa suna
salon zayyana wanda wasu makaɗan suke amfani da shi wajen aiwatar da waƙoƙinsu. Mun
sami nasarar zaƙulo ire-iren waɗannan wuraren da ya yi hakan mun fito da su tare da sharhantawa don su amfanar da jama’a
musamman manazarta waƙoƙin Hausa.
Allah ya sa abin amfani ne.
Manazarta
Bunza, A.M (2006). Gadon Feɗe Al'ada. Lagos:
Tuwal publishers Limited.
C.N.H.N. (2006). Kamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University press.
Damgambo, A. (2007). Daurayar Gadon Feɗe Waƙa, (Sabon tsari), Kano: Amana Publishers Limited.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark publishers Limited.
Gusau, S.M. (1996), Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna:
Fisbas Media Services.
Muhammad, (2006).
Gudunmuwar waƙoƙin baka na yara wajen adana al’adar Hausawa, Kundin digiri
na biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero.
Muhammad, D. (1978). Waƙa Bahaushiya: Studies in Hausa
Language, Literature And Culture. Bayero University Kano.
Sarɓi S. A. (2007), Nazarin Waƙar Hausa, Samarib
Publishers.
Yahaya, I. (2010). Waƙoƙin addini na siyasa: Nazarin waƙoƙin Emmanuel Wise mai molo. Kundin digiri na biyu sashen koyar da harsunan Nijeriya da Afirka
Jami’ar Ahmadu Bello.
Yahya, A. B. (1997). Turken nazarin waƙa, Fisbas media service.
Yahya, A. B. (1996). Salo Asirin Waƙa, Fisbas media service.
Yahya, A. B. da Dumfawa, A. A. (2010). Waƙar motar siyasa: saƙon talakawa zuwa ga ‘yan siyasar zamani.
NNPC (1966), Ikon Allah. Zaria: Amana
printing Ltd.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.