Nazarin Kalmomi Masu Kishiyar Ma’ana (Antonyms) a Cikin Wasu Wakokin Makada Sa’idu Faru

    Citation: Bashir, A. & Yusuf, A.I. (2024). Title. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 375-382. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.053.

    Nazarin Kalmomi Masu Kishiyar Ma’ana (Antonyms) a Cikin Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Daga

    Abdullahi Bashir

    Sashen Harsuna da Al’adu
    Jami’ar Tarayya Gusau
    08036481158
    abdullahi.bashir@fugusau.edu.ng 

    Da

    Abu-Yazid Ishaq Yusuf

    Ɓangaren Ɗakin Karatu na Jami’a
    Jami’ar Tarayya Gusau, Jihar Zamfara
    08037953327
    abuyazidyusuf@fugusau.edu.ng

    Tsakure

    Wannan muƙala tana ƙoƙarin fito da wasu kalmomi na musamman waɗanda marigayi makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a wasu daga cikin waƙoƙinsa, a inda yake ambaton kalma tare da kawo akasinta ta hanyar nuna fifiko ko kasawa a tsakanin Sarakuna da mabiyansu ko abokan hamayyarsu. Irin waɗannan kalmomi sukan zo a cikin salon Mutuntarwa ko Dabbantarwa ko kuma Abuntarwa. Hakan yana faruwa ne a lokacin da yake yin zuga ko kwarzanta gwanayensa Sarakuna a cikin wasu ɗiyoyin waƙoƙinsa. Haka kuma, su irin waɗannan kalmomi suna iya zama sunaye ko wasu siffofi. A nan, an yi amfani da Ra’in dangantakar Tunani da Ma’ana (Mental Theory of Meaning) wanda John Locke (1689) ya ɓullo da shi, sannan Bertrand Russell (1970) da Neil Skinner (1971) suka yi amfani da shi a cikin ayyukansu. Wannan ra’i yana magana ne a kan ma’anonin kalmomi masu kishi da juna wajen bambanci da kuma yin zuzzurfan tunani kafin a gano bambancin nasu ta fuskar harshe ko al’ada. Domin kuwa, ra’in yana nuna yadda akan yi amfani da kalmomi wajen yin nazari da tunani ko samun manufofi a rayuwa. Sannan an gudanar da binciken ne ta hanyar saurare tare da yin nazari da kuma juyar sautin waƙa watau ‘Transcription’. Maƙalar ta gano cewa, yin amfani da irin waɗannan kalmomi yana bai wa mai sauraro shauƙi wajen sauraro tare da fahintar harshe ko samun ƙwarewa da gwanintar harshe daga bakin makaɗa. Domin kuwa, hakan ya taimaka sosai wajen bunƙasa harshen Hausa da aladun Hausawa. Misali; a cikin waƙarsa ta Marigayi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai taken ‘Kana shire Babban ‘Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo’ inda ya ambaci kalmomin kyawo da mummuna, samu da busasshe, mutum mai iko da mai roƙonsa da sauransu. Saboda haka, ɗalibai da sauran masu nazari za su iya fahinta tare da nazarin rukunin kalmomi da ma’anoninsu ta hanyar sauraron irin waɗannan waƙoƙi na baka masu muhimmanci a harshe.

    Fitilun Kalmomi: Waƙa, Kishiyar Maana, Fifiko da Kasawa

    Gabatarwa

    Harshe yana yaɗuwa ne ta hanyar reno da nuna kulawa daga masu magana da shi musamman waɗanda shi wannan harshe ya kasance masu a matsayin harshen uwa ko kuma harshen farko a gare su. Shi wannan yaɗo da harshe ke yi yana faruwa ne ta hanyar taimakon wasu ginshiƙai guda uku waɗanda su ne suke ɗaure ko rataye da wannan harshe. A harshen Hausa, akwai turaku uku da kan ɗaure kuma su jujjuya Bahaushe a duk inda ya samu kansa a duniya, waɗannan abubuwa kuwa su ne; Harshe da al’ada. Domin a duk inda cikakken Bahaushe yake rayuwa za a taras da shi yana yin biyayya a kan waɗannan abubuwa ta fuskar magana da harshensa na asali, sai kuma yanayin abincinsa da kuma suturarsa. Fagen adabi ya kasance tamkar wani ado ne ko kuma kwalliya ce da ake yi wa harshe wajen fito da hikima da fasaha da al’adu da ma sauran hanyoyin zamantakewa. Misali, a cikin waƙar baka ne ake ƙoƙarin baje fasahar harshe da ma yin luguden kalmomi ta hanyar yin amfani da salalai iri daban daban domin nuna ƙwarewa da fasaha da basira da zalaƙar harshe ta yadda mai sauraro zai zugu ko ya koɗu a yayin da ya ji wasu kalmomi suna fita daga bakin makaɗi ko mawaƙi waɗanda kan sanya masa shauƙi da ɗoki har ya yi kyautar da bai san ma ya yi ta ba. Aiwatar da sana’ar kiɗa da waƙa kan iya kasancewa gado ne ko haye, sannan samun damar yin kiɗa da waƙa da roƙa da ma tumasanci a gidajen sarakuna sai wanda ya isa, ma’ana sai wanda ya ƙware kuma ya iya allonsa domin kuwa, shi ma zai iya zama tamkar ɗan gida ta fuskar sutura da abinci da ma nuna iko a wasu lokuta. Makaɗan fada sun kasance daban da sauran rukunin makaɗan a cikin al’umma domin kuwa, ana yi masu kallon wata ƙima ta musamman kasancewar sun jiɓanci gidajen sarakuna da sauran masu mulki, waɗanda kan iya bambance su ta hanyar irin shigar da suke yi a lokacin bukukuwa da yawon giɗa a gidajen iyayen gidan nasu.

    Taƙaitaccen Tarihin Marigayi Alhaji Saidu Faru

    Marigayi Alhaji Sa’idu Faru wanda ake wa laƙabi da Malamin waƙa wani shahararren mawaƙi ne da aka yi a nan ƙasar Hausa. Wancan laƙabi ya samu ne saboda irin ƙwarewarsa da kuma nuna jaruntaka a harkar waƙa ta baka. Shi dai marigayi Alhaji Saidu  Faru an haife shi ne a wajajen shekarar 1932 a garin Faru da ke ƙasar Maradun a yankin ƙaramar hukumar Maradun a cikin jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Nijeriya. Sannan ya rasu a shekarar 1984. Bayan haka, makaɗin kan yi wa kansa kirari da “Mamman mai kwana ɗumi Na Mamman Na Balaraba” a cikin wasu waƙoƙin nasa duk da cewa, a gida ma akan yi masa laƙabi da ɗan Umma, watau matar ƙanen mahaifinsa (Gusau 2011:117). Marigayi Sa’idu Faru ya samu ilimin addinin musulunci a lokacin ƙuruciyarsa, sai dai hakan bai hana shi samun baiwar fasahar kiɗa da waƙa ba wadda ya gada daga mahaifinsa mai suna Abubakar Mai Kotso ɗan Abdu (Abubakar Kusu) wanda shi ma ya yi gadon kiɗa ne daga mahaifinsa mai suna Alu mai kurya. Ita kuwa mahaifiyarsa mutuniyar Banga ce da ke ƙasar Ƙauran Namoda (Gusau 2011:117). A nan, za mu iya cewa, Sa’idu Faru ya gaji kiɗa da waƙa daga mahaifinsa da kakansa, a inda ya rinƙa bin mahaifin nasa tare da yan uwansa wajen yawon kiɗa da waƙa, inda a nan ne ya samu ƙwarin guiwa da kuma basirar kiɗa da waƙa musamman irin na fada. Haka kuma, nuna sha’awarsa ga salon bayar da labarai da sanin tarihi da al’adu da yin sharhi a kan zamantakewar al’ummar Hausawa duk sun sa ya yi sabo da sarkuna da ‘ya’yan sarakai maza da mata a lardin Sakkwato. Sai dai hakan bai hana shi shiga sauran yankunan arewacin Nijeriya ba kamar Kebbi da Zamfara da Katsina da sauransu. Bugu da ƙari, a lokacin da ya bi tawagar mahaifin nasa zuwa fagen kiɗa da waƙa, Saidu Faru ya kasance wanda ya sadaukar da rayuwarsa dangane da harkar kiɗa da waƙa domin kuwa a nan ne ya fara yin suna har aka fara jin ɗuriyarsa a lokacin da ya fara jagorantar tawagar mahaifin nasa yana ɗan shekara talatin, kuma daga nan ne ya samu karɓuwa daga wajen sarakuna na wancan lokaci da ke lardin Sakkwato, watau Daular Usmaniyya.

    Duk da cewa, marigayi Alhaji Sa’idu Faru bai yi karatun zamani na boko ba sai dai ya yi zurfi a karatun Alƙurani mai tsarki kuma ya kasance jajirtacce a lokacin rayuwarsa musamman a fagen waƙa wanda hakan ya sa ya samu ɗaukaka kuma har ya fara haɗuwa da manyan mutane a sanadiyyar wannan sana’a tasa ta gado watau waƙa. Misali a tsakanin shekarar 1953 – 1956 ya haɗu da Mai Alfarma Sarkin Musulmi na 19, Marigayi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III a lokacin yana matsayin Sarkin Gabas, Uban ƙasar Talatar Mafara da kuma matsayinsa na Sarkin Kudun Sakkwato da Gusau, a inda ya ci gaba da yi masa kiɗa da waƙa kuma ya ɗauke shi matsayin Ubangidansa a cikin Sarakuna. A lokacin rayuwarsa, ya kasance ba ya yi wa kowa waƙa sai Basarake. Ya rasu yana da matan aure 3 da ‘ya’ya 26 da jikoki kimanin 20. Kuma ya bar ƙanensa Muazu Ɗangaladimansa na kiɗa da kuma ɗansa Ibrahim waɗanda su aka sa ran su gaje shi. Sannan ya azurata a sanadiyyar waƙa duba da irin kyaututtukan da samu daga iyayen gidansa ta fuskar sutura da Dawakai da kuɗaɗe da sauaransu, Allah Ya gafarta masa.

    Ma’anar Waƙa

    Haƙiƙa masana da dama sun yi tsokaci dangane da maanar waƙa musamman ta baka wadda ake ganin ita ce ta fi shahara a zamunan da suka shuɗe kafin da kuma bayan jihadi, watau ko da rubutattun waƙoƙi suka kunno kai sun shafa wa waƙar baka lafiya dangane da shahara a nan ƙasar Hausa, inda ake fito da al’adu da adabi da ma nuna ƙwarewa ko gwanintar harshe. An bayyana waƙa a matsayin wata tsararriyar magana da ake rerawa a kan kari ko rauji. Shi kuwa waƙe na nufin a yi wa wani mutum ko wani abu waƙa (CNHN, 2006:466). Har ila yau, Muhammad (1979:87) ya bayyana waƙar baka da ‘aiwatarwa a inda ta haɗa da rerawa da baki, sannan a sadar da ita a gaban jama’a, kuma wadda bisa yawanci ake yi a ƙungiya ta jagora da ‘yan amshi, kuma a haɗa ta da kiɗa’. a yayin da Yahaya (1997:04) yake cewa, “ita dai waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saqo cikin zaɓaɓɓun kalmomi da aka auna domin maganar tar era ba faɗawa kurum ba”. Bugu da ƙari, Ɗangambo (2007:6) ya ce, “waƙa wani saƙo ne da akan gina shi a kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, kari/bahari, amsa-amo/ƙafiya, da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓen su da amfani da su a cikin sigogin da ba haka suke a maganar baka/lafazi ba.” Ko da jin ma’anar waƙa daga bakunan masana za a fahimci cewa, waƙa wata baiwa ce da Allah Yakan bai wa ɗan adam wajen rerawa tare da isar da saƙonni ga jamaa.

    Ma’anar Waƙar Baka

    Waƙar baka daɗaɗɗiya ce wadda aka faro tun lokaci daɗaɗɗe mai nisan gaske. Waƙa ta rayu tana daɗa bunƙasa tana haɓaka har zuwa yau (Gusau, 2003). Haka kuma, Gusau (2011) ya ce, “waƙar baka fage ce wadda ake shirya maganganu da hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre haɗe da kiɗa cikin daidata rerawa. Haka kuma ya ƙara da cewa, “Waƙar baka ita ce wadda take zaburar da alumma tare da hankaltar da su zuwa ga dabarun tafiyar da rayuwa da za su bayar da damar a cimma ganga mai inganci (Gusau, 2011:1). Har ila yau, (Gusau, 2014:3) ya bayyana cewa, “Waƙar baka ta Hausa tana ƙunshe da manyan sigogi guda shida (6) da suka haɗa da kiɗa da yanayin aiwatarwa da rauji bisa murya mai hawa ko sauka ko faɗuwa da yanayin ƙulla kalmomi cikin sadar da ita a gaban jama’a. Kalmomi waɗnda aka zaɓa a ka shirya su suka zama matanin waƙa kuma aka rera su bisa waɗannna sigogi kuma aka sadar da su ga jama’a, su ne suke haɗuwa su zama waƙar baka ta Hausa”. Waƙoƙin Hausa na baka na gargajiya akan ƙage su ne bisa tsarin al’adun Hausawa na gargajiya ta hanyar zubin kalmomi da jumloli, sannan a ɗora masu amo na kiɗa ta amfani da kayan kiɗa waɗanda kuma Hausawan ne da kansu suke ƙirƙirar su da kansu gwargwadon yanayin wuri na ƙasar Hausa. Misali; bishi, turu, garaya, kuntugi, duma, kalangu, shantu, ƙwarya, molo, kotso, taushi, ƙaho, buta, gora, mandiri, fiyano da sauransu. Haka kuma, akan shirya irin waɗannan waƙoƙi a ƙungiya ko a kaɗaita (Bashir, 2019). Haƙiƙa, wannan nuna yadda ake fahimtar darussa da dama a cikin waƙar baka musamman waɗanda suka shafi al’adu da ɗabi’un Bahaushe na yau da kullum, kuma a nan ne ake bayar da tarihin rayuwar al’ummar Hausawa da sauran fasahohinsu da suka gada tun tale-tale.

    Ma’anar Kalma

    Kalma ta samo sunanta ne daga kalmar larabci ta al-kalmat, wadda ta ƙunshi haruffa, watau baƙaƙe da wasulla na wani harshe. haka kuma, akan harhaɗa su ne domin a yi amfani da su wajen isar da saƙo a tsakanin alumma. Domin kuwa, ta hanyar harhaɗa kalmomi ne da ake samar da jumla wadda take ƙunshe da wani saƙo da ake sin isarwa mia ɗauke da ma’ana. Kalmomi sun kasance a cikin sahu dangane da azuzuwansu na nahawun kowane harshe ta yadda za su kasance cikin tsari mai armashi. Zarruk (2005). ‘Kalma’ asali an aro ta ne daga larabci wadda ke nufin furuci ɗaya mai ma’ana sannaniya. Haka kuma, wannan furuci kan iya ɗaukar gaɓa ɗaya (ka) ko (kai) da sauransu, sannan ya ɗauki gaɓa biyu ko ma fiye da haka. Misali: (gida), (mutum), (gardama), (bagaruwa), (yarjejeniya), (tunkuɗeɗeniya) da sauransu (Yakasai, 2024:83). Sarkin Fada da Abdullahi (2024) sun yi magana a kan kalma wadda suka ce, ta ƙunshi ƙwayar maana ko kuma baƙaƙe da wasulla da ake iya ji ko a gani, watau mai ɗauke da wata ma’ana ta musamman.

    Azuzuwan Kalmomi

    Kowane harshe yana da irin tasa hanyar da yake bi wurin ginin kalmominsa da ma furta su, da kuma yadda ake jeranta su a cikin jumla domin bayar da ma’ana ingantacciya a cikin zantuka na yau da kullum. Kamar yadda shi ma harshen Hausa ya yi tozali da irin waɗancan hanyoyi ya kuma tabbatar da su a cikin tsari don samun karɓuwa da kuma isar da saƙo cikin sauƙi, wannan bai rasa nasaba da samun sauƙin koyon harshen Hausa. Bayan haka, irin waɗancan dokoki na nahawu kan yi tasiri matuƙa dangane da ginuwar zance ko jumla ba tare da saɓa wa harshen ko al’adunsa ba. Usaini (2017:78) ya kawo rukunan nahawu kamar haka; suna, wakilin suna, aikatau, sifa, bayanau da tsigalau. Umar (2009) ya bayyana rukunonin kalmomi a matsayin wani tsari ne na kalmomi a jere a cikin jimla masu bayar da cikakkiyar ma’ana. Wato, kalmomin su ke haɗuwa su bayar da jimla. To su irin waɗannan kalmomi na cikin jumla su ake kira sassan magana, ko sassan jumla, kuma su ne ke haɗuwa su ba da zance mai cikakkiyar ma’ana. Su kuma waɗannan kalmomi na cikin jumla, suna da nasu tsari na musamman, saboda ana kasa su ne rukuni-rukuni, gwargwadon irin aikin da kowanensu yake yi a cikin jimla. Haka kuma, akan tattara kalmomi masu nasaba da juna a ba su suna guda. Wannan shi ne ajinsu, kuma shi ne sunansu. Ibrahim da Abdulƙadir (1986) sun kasa kalmomin Hausa zuwa manyan rukunoni tara, watau Suna, Wakilin Suna, Aikatau, Sifa, Bayanau, Amsa-kama, Mahaɗi, Harafi da Motsin rai. Shi kuwa Amfani (2004) ya bayyana wasu matsaloli uku dangane da rabon kalmomin Hausa. Watau a ganinsa, wasu kalmomin Hausa an ba su kashin da bai cancance su ba. Misali, wasu kalmomi ba a saka su cikin kowane kashi ba. A inda wasu kalmomin har yanzu ba a yi matsaya ba a kansu.

    Ma’anar Suna

    Zaria (2014:4) ya ce, “sunaye dai a sanin Hausawa suna iya zamantowa sunayen yanka ko kuma laƙabi. Sannan malamin ya ƙara da cewa, masana nahawun Hausa suna ganin cewa muna iya samun sunaye kashi-kashi, a harsuna daban daban waɗanda za mu iya rarraba su. To, a Hausa ma akwai rabe-raben sunaye da dama.” Kuma malamin ya kawo misalai daga sunayen yanka, sunayen laƙabi, sunayen garuruwa ko wurare, sunaye gama-gari waɗanda suka hada da; sunayen dabbobi, abubuwa fai, sunayen abubuwa ɓoyayyu, sunayen haɗaka da sauransu. Usaini (2017:78) ya ce, “komai na duniya yana amsa wata kalma guda ko fiye a matsayin suna, da aka san shi da shi, a ɗaiɗaiku ko kuma a tarayya. A taƙaice suna kalma ce da ke ɗauke da gaɓa ɗaya ko fiye da ake amfani da ita don kiran abu mai rai ko maras rai.” Haka kuma, Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007) sun ce, “suna kalma ce ta nahawu wadda ke bayanin suna ko laƙabin kowane abu mai rai ko maras motsi, da wannan kalma ce ake kiran kowane abu. Bayan haka, kalmomin suna sukan samu ne ta hanyar haɗa saiwar suna ko saiwar aiki domin kuwa a Hausa akwai sunaye da dama waɗanda ake yi masu ɗafa goshi na ‘ba’ ko ɗafa ƙeya na wa’ misali Bahaushe – Hausawa da sauransu.

    Ma’anar Kalmomi Masu Kishiyar Ma’ana (Antonyms)

    Kalmomi masu kishiyar ma’ana sun kasance ne a matsayin kalmomi masu zaman ‘yan marina ta fuskar ma’ana da ma sigoginsu a harshe. Watau sukan taka rawa ne a cikin ajinsu na nahawu ta fuskar isar da saƙo a cikin zance ko a rubuce cikin jumla, a inda za a iya ganin kishi ko bambancin da ke tsakaninsu da takororinsu a rukunin kalmomin ajin nahawu. A duk lokacin da aka ambaci kalmar farko to, ana sa ran ɗayar za ta biyo baya domin cikar zance da kuma isar da saƙo ga mai sauraro ko mai karatu. Irin wannan yana zuwa ne daidai da abin da ɗan adam ya sani game da rayuwarsa. Misali, mutum da dabba, sama da ƙasa, hagu da dama, baƙi da fari, ciki da waje da sauransu. Fergusson (1992) ya yi bayani a kan kalmomi masu kishiyar ma’ana, inda ya kawo su cikin tsarin azuzuwansu danagane da nahawu, misali; suna, aikatau, sifa, bayanau, mahaɗi da sauransu. Wannan littafi ƙamus ne mai ɗauke da rukunin kalmomi da kuma kishiyoyinsu dangane da ma’ana. Haka kuma, Akwanya (2015:60) ya bayyana kalmomi masu kishiyar ma’ana a matsayin kalmomin da ke ɗauke da bambancin ma’ana ko da kuwa sun kasance a rukuni ɗaya dangane da jinsi ko kuma ajin nahawu, watau kamar bambancin ma’anar kalmar miji (husband) da mata (wife) ko kuma yaro (boy) da yarinya (girl) da sauransu. Waɗannan misalan kalmomin suna ne kuma masu rai ta fuskar halitta amma sai dai ma’anoninsu sun sha bamban.  Bugu da ƙari, irin waɗannan kalmomi masu kishiyar ma’ana kan taimaka wajen naƙaltar harshe da rubutu da yin tunani mai zurfi dangane da maanonin harshe, kasancewar sun yin hannun riga da juna ta fuskar ma’ana.

    Kalmomi Masu Kishiyar Ma’ana a Cikin Wasu Waƙoƙin Saidu Faru

    Su irin waɗannan kalmomi ana iya samun su a cikin wasu waƙoƙin makaɗa da mawaƙa na Hausa, inda suke ƙoƙarin nuna ƙwarewa da baje kolin fasaharsu da nfin isar da saƙo ga jamaa, musamman ta hanyaryabo ko habaici ko kuma zambo. Ga misalan wasu kalmomi da suka fito a cikin waƙar ‘Kana shire Babban ‘Yan Ruwa’ ta marigayi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo.

    Jagora: Yay yi mutun mai ƙoƙari,

    Sannan Yay yi mutun mai kyawo,

    Kuma Yay yi mutun mummuna,

    Sannan Yay yi mutun mai haske,

    Kuma Yay yi mutun mai dauni,

    Sannan Yay yi mutun mai samu,

    Kuma Yay yi mutun busasshe,

    Sai Yay yi mutun ɗan Sarki,

    Kuma Ya aza bawan Sarki,

    Sannan Yay yi mutun mai iko,

    Kuma Yaa aza mai roƙo nai.

    A nan, irin waɗannan kalmomi da aka kawo a cikin wannan ɗan waƙa da ke sama suna daga cikin kalmomi masu ɗauke da kishiyar ma’ana, watau waɗanda makaɗa Sa’idu Faru ya kawo a cikin waƙar da ya yi wa marigayi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo. Ga ƙarin wasu misalai masu zuwa:

    Jagora: Laihin yaro shi ƙiuya,

    Laihin babba shi yi rowa,

    Ina ƙamnak ka Muhammadu,

    Na tabbataƙ ƙamnata kakai,

    Ko kai niyya ba mu Dawakuna,

    Samnan Bahwade sara yakai,

    Yac ce ko ka ba mu Dawakuna,

    Randa Sallah ka tashi Ƙaura mukai,

    Yac ce ko ka ba mu Dawakuna,

    Ran da Sallah ka tashi ƙaura mukai.

     

    Jagora: Da inda rana ka fita gabas,

    Har inda rana taka faɗuwa,

    Dud ɗai na ga jikan Ɗanhodiyo,

    Babu wurin da mulki nai yatc tcaya.

     

    A nan ma makaɗin ya yi amfani da hikimarsa ta kawo wani yankin jumla mai ɗauke da kalmar ra na da kuma yin bayani a kan daga inda take fitowa, sannan sai ya yi amfani da hikima wajen ambaton inda take faɗuwa ba tare da ya ambaci yamma ba, wanda kowa ya sani cewa nan ne inda take faɗuwa. Hakan yakan sa mutane cikin tunani sosai don lalubo irin waɗannan ma’anoni don nuna ƙwarewa a harshe.

    Jagora:  Babban daji kake ɗan Abu.

    ‘Yan Amshi: Ko icce ko namun dawa,

    Ko manya ko ƙanƙane,

    Da mutun da dabba da itatuwa,

    Kowa ƙamnam Mamman yakai,

    Mamman jikan Attafiru,

    Baba na Sidi,

    Mamman gwarzon Cika.

    Kana tsaye Baban ‘Yan Ruwa,

    Na Bello Jikan Ɗanhodiyo.

     

    A cikin wannan ɗan waƙa, daga ƙarshe Yan Amshi sun yi ƙoƙarin yin koyi da uban gidan nasu wajen jero irin waɗancan kalmomi masu kishiyar ma’ana. Watau kalmar manya da ƙanana, watau abu mai girma da kuma ƙarami. Sai kuma mutum da dabba waɗanda suka bamabanta ta fuskar hallita da kuma mu’amala, misali harshe, ala’ada da sauransu.

    Haka kuma, a cikin waƙar Dagacin Falale da ke Gummi, watau Tudun Falale/Sarkin Tudun Falale Muhammadu Muhammadu Maidabo an samu wasu kalmomi masu kishiyar ma’ana kamar haka:

    Jagora:  Dogon Sarki yana da ban shawa rad da anka zo taro ya hi kyau da riguna.

    ‘Yan Amshi: Duw wanda ag gajere a aje shi gun rabon dawo.

    Jagora:  Ban cin kokuwa akwai maraba,

    Ɗan Ariguma ya bah hwaɗa maka Muhammadu,

    Ko wurin uwaye mata.

    ‘Yan Amshi: Kuna da tcetcetcere da ɗan marar abun wuya,

    Ɗan Karuwa dub ɓaci kaj jiya da kai muke,

    Ya riƙe da gaskiya Muhammadun Muhammadu.

     

    A nan, an kawo dogon sarki da gajere, sai kuma mata da marar abun wuya (namiji), sannan aka kawo yin kokawa da kuma rabawa, waɗanda dukkansu kalmomi ne da ke kishi da junansu ta fuskar ma’ana a yayin da makaɗin yake ƙoƙarin isar da saƙonsa ga masu sauraro.

    Bayan haka, binciken ya ci karo da wasu kalmomi masu kishiyar ma’ana a cikin waƙar da makaɗin ya yi wa marigayi Sarkin Kudu Alhaji Muhammadu Macciɗo Mai Taken “Ginshiƙin Magaji”.

    Jagora: Ginshimin Magaji gabanka da bayanka Bello na ba ka da garwaye.

    Amshi: Bello na ba ka da garwaye.

    Jagora: In wani na kwana,

    Wani na zaune in ji Ɗan Umma uban kiɗi .

     In wani na inuwa, wani na rana in ji Ɗan Umma uban kiɗi.

    In wani ya samu, wani ya rasa,

    Ita Duniya haka nan take.

    Mutum guda ka ga mai riga dubu,

    Mutum dubu ba su da ko kwabo.

    Ita duniya haka nan take.

    Amshi: Mutum guda ka ga mai mato dubu,

    Mutum dubu ba su da basukur.

    Ita duniya haka nan take.

    Jagora: Wanda bai san ɗadin Doki ba,

    Sai ya ce Jakki hikima garai,

    Wanda bai san ɗadin Mato ba,

    Sai ya ce Fanda hikima garai.

    Amshi:  Kuma in maganar zaƙi akai,

    Kowa nak kurɓa ruwan zuma ba ya koma batun maɗi.

     

    A ƙarƙashin waɗannan ɗiyan waƙa an samu ƙarin wasu kalmomi masu kishiyar maana. Misali kalmaomin inuwa da rana, sai samu da rasawa, akwai gaba da baya da kuma zuma da maɗi da sauransu waɗanda suke yin nuni a kan irin hikimomin da makaɗin ya yi amfani da su a cikin waƙoƙin nasa. Saboda haka, wannan bincike ya tabbatar da cewa, ana samun irin waɗannan kalmomi a waƙoƙin baka na Hausa, inda akan iya gane fasaha da zalaƙar iya zance da kuma nuna ƙwarewa wajen jera kalmomin hikima ko gagara gwari da tsofaffin kalmomi ko kalmomin aro da makaɗi yakan yi amfani da su musamman a harshensa na gado wanda da shi ne yake isar da saƙo a kodayaushe ga jamaa, kasancewarsa ɗan asalin wannan harshe.

    Tasirin Kalmomi Masu Kishiyar  Ma’ana a Cikin Wasu Waƙoƙin Saidu Faru

    A nan, makaɗin ya yi ƙoƙarin jero kalmomi a cikin sahu dangane da ajinsu na nahwahu, watau idan suna ne to, yakan yi ƙoƙarin kawo wata kalmar ta suna mai kishi da wadda ta zo kafin ita a cikin waƙa. Haka kuma, akwai wuraren da yake ambaton kalma tare da kawo kalmar da take hannun riga da ita nan take, duk dai don ya nuna fifiko ko ƙasaƙanci a tsakanin iyayen gidansa sarakuna da kuma talakawansu ko kuma kwarzantawa ta hanyar kwatanta waɗanda yake yi wa waƙar da kuma abokan hamayyarsu tare da nuna ƙwarewa a cikin harshe wajen nuna hikima da basira da zalaƙa da balagar zance, watau wanda masu nazari suke kira da nuna gwaninta a harshe ‘competance and performance’. Wannan ba abin mamaki ne ga Sa’idu Faru ba domin kuwa, duba da yadda ya taso tun cikin ƙuruciyarsa a ƙasar Hausa, da irin yadda kiɗa da waƙa suka kasance gado kuma abin tutiya a gare shi, a inda tarihi ya nuna yadda ya rinƙa bin kakansa da ma mahaifinsa wajen kiɗa da waƙa tun yana yaro. Haƙiƙa, wannan ya taimaka sosai wajen samun ƙwarewa a gare shi. Sannan, Allah ya yi masa wata baiwa ta hikimar iya zance wadda ba kowa ke da ita a rayuwa ba.

    Sakamakon Bincike

    Haƙiƙa a cikin wannan maƙala an fito da kalmomi masu kishi da juna (antonyms) waɗanda suka bayyana a cikin waƙar sarkin kudu Muhammadu Macciɗo ta marigayi Sa’idu Faru Malamin kiɗa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba. Duk da cewa, a fasahar makaɗi bai ma san yana ambaton wasu kalmomin ba, sai dai su zo masa kawai kuma har su yi daidai da wani tsari na harshe ko nahawu ta fuskar nazari, a inda masana da manazarta suke samun abin yin tsokaci daga cikin irin baiwar da Allah ya bai wa makaɗin. Kuma an lura cewa, su irin waɗannan kalmomi za su iya zama suna ko kuma sifa ta fuskar nahawu. A don haka, mai nazari zai iya lura da hakan a duk lokacin da ya saurari irin waɗannan waƙoki tare da yi masu duba na musamman to, tabbas za a fahince su a matsayin yabo ko zuga ga shi wanda ake yi wa waƙar ta hanyar bambanta shi da wanda bai kai shi daraja ba. Misali, a tsakanin sarki da talakansa (mai iko da mai roƙo) ko kuma a tsakanin mai kuɗi da talaka (mai samu da busasshe). Haka kuma, ya kawo kalmomi irin su ƙiuya da rowa, sai haske da dauni, ɗa da bawa da sauransu. Bugu da ƙari, an ɗauki waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a matsayin wadda irin waɗancan kalmomi masu hannun riga da juna ta fuskar ma’ana suka fito a cikinta kuma aka kwatanta su ta fuskar nuna bamabncin ma’ana. Ga misalin wani ɗa na wannan waƙa ta marigayi Alhaji Sa’idu Faru wanda sunan waƙar kacokan ya fito a ciki, kamar yadda za mu iya gani a layin farko na ɗan waƙar kamr haka:

    “Kana Shire Baban ‘Yan Ruwa,

      Na Bello Jikan Ɗanhodiyo....”. 

    Kodayake, waƙar ba ita ce Bakandamiyar makaɗin ba amma tana ɗaya daga cikin waɗanda suka shahara ga marigayi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo. Allah Ya gafarta masu, amin.

    Kammalawa

    Haƙiƙa, wannan bincike ya kammala ne bayan an yi ƙoƙarin kawo muhimman batutuwa da suka shafi ayyukan makaɗa Sa’idu Faru musamman waɗanda suka danganci yin amfani da kalmomi masu kishi da juna ko kuma akasin juna ta fuskar ma’ana a cikin waƙoƙinsa da ya yi wa marigayi mai alfarma sarkin musulmi na 18, Alhaji Muhammadu Macciɗo. Bayan haka, maƙalar ta fito da wasu ginshiƙai da suka shafi al’amarin sadarwa, watau kalmomi masu kishi da juna ta fuskar ma’ana. Haka kuma, su irin waɗannan kalmomi suna taimakawa ƙwarai da gaske wajen bunƙasa harshe tare da bambancewa a tsakanin babba da ƙarami ko mai hali da maras shi ko kuma mai tsafta da ƙazami da sauransu. Sannan an lura da yadda makaɗin ya laƙanci harshe sosai, da yadda yake ƙoƙarin ajiye kowace ƙwarya a kan gurbinta, a inda ake bambance a tsakanin iyayen gidansa sarakuna da kuma talakawansu ta hanyar yin amfani da irin waɗancan kalmomi masu kishi da juna.

    Shawarwari

    A nan, yana da kyau a ce, masu nazari sun fahimci yadda makaɗa da mawaƙa kan yi amfani da kalmomi daban-daban wajen isar da saƙo ga alumma ta hanyar faɗakarwa da ilimantarwa da ma nishaɗantarwa. Domin kuwa, ta nan ne za a iya fahimtar ma’anonin irin waɗancan kalmomi da Hausawa sukan yi amfani da su a cikin al’amuransu na yau da kullum.

    Haka kuma, daga cikin irin waɗannan kalmomi ana koyon dabaru da dama na tafiyar da rayuwa musamman dangane da zamantakewa. Misali, a kalmomin kishi ne ake iya fahimtar yadda kishi yake da yadda yake gudana a nan ƙasar Hausa ba wai sai a tsakanin mata masu kishi da juna ba, kasancewar shi kishi a tsakanin ɗan adam aka fi sanin sa. Sai dai, a yayin aiwatar da shi, abubuwa da yawa suna faruwa ne wajen haddasa rikici da ɓatanci ko aibatarwa a tsakanin mutum biyu masu kishi da juna.

    Bugu da ƙari, akwai buƙatar mai sauraro da mai karatu da kuma mai nazari da su rinƙa mayar da hankali sosai wajen laƙantar irin kalmomin da mai magana ko mai rubutu kan jero a yayin da yake ƙoƙarin isar da saƙo ga alumma domin hakan zai taimaka wajen tsettsefewa tare da fayyace rukunin kalmomi dangane da da nahawun harshe. Domin kuwa, ana bai wa waƙa daraja ta hanyar auna ta a kan mizani ko wani maauni da masana suka tanzar musamman a fagen nazari.

    Har ila yau, ta hanyar nazari ne za iya fahimtar irin yadda makaɗi ke yin zaɓen kalmomi dangane da turken waƙarsa da kuma ƙwarewarsa a harshe domin isar da saƙo ta hanyoyi daban-daban da za su sanya waƙar tasa ya samu karɓuwa ga masu sauraro.

    Manazarta

    1.      Akwanya, A. N. (2015) Semantics and Discourse: Theories of Meaning and Textual Analysis. Revised Edition, Enugu: University of Nigeria Press Limited.

    2.      Amfani, A. H. (2004) Waiwaye Adon Tafiya: Bitar Rabe-raben Azuzuwan Kalmomin Hausa: Takardar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilmi. Sakkwato: Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo.

    3.      and Publishing Limited.

    4.      Bagari, D. M. (1986) Bayanin Hausa: Jagora Ga Mai Koyon Ilmin Bayanin Harshe. Rabat, Morocco: Impremerie Elm’arif Aljadida.

    5.      Bargery, G. P. (1951) A Hausa-English Dictionary and English- Hausa. Oxford.

    6.      Bashir, A. (2019) Nazarin Karin-Harshe A Matsayin Tubalin isar da Saƙo A Waƙoƙin Narambaɗa. In Proceedings of the International Conference on Ibrahim Narambaɗa Tubali, Kano: Centre For Research in Nigerian Languages, Translation and Folklore. 

    7.      Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari). Zaria: Amana Publishers Limited.

    8.      Ɗangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Zaria: Amana Publishers Limited.

    9.      Fergusson, R. (1992) The Penguin Dictionary of English Synonyms and Antonyms. London: Penguin Books Limited.

    10.  Gusau, S. M. (1993) ‘Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Baka na Hausa’ in Studies of Hausa Language, Literature and Culture. Rufa’i, A., Yahaya, I., Bichi, A.Y. (ed). Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.

    11.  Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Company.

    12.  Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar HausaYanaye-Yanayensu da Sigoginsu’, Kano: Benchmark Publishers Company Limited.

    13.  Gusau, S. M. (2011) Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    14.  Gusau, S. M. (2014) Waƙar Baka Bahaushiya ‘The Oral Hausa Songs’, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

    15.  Gusau, S. M. da Funtua, A.I. (2011) Waƙoƙin Baka Na Hausa. ......... : Century Research Publication.

    16.  Ibrahim, M. S. (1976) Nazari a Kan Waƙoƙin Makaɗan Sarauta da Makaɗan Jama’a. ‘Takarda ta Uku don Cikasa wani Ɓangare Na Neman Digirin Hausa’, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero. 

    17.  Ibrahim,Y. Y. da Wasu. (1992) Darussan Hausa Littafi na Uku: Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: University Press Plc.

    18.  Isma’il, J. da Tanimu, M. ’Y. (2007) Harshe Da Adabin Hausa A Kammale: Kalmomin Hausa, Takardar da aka Gabatar a Wajen Taron Ƙara wa Juna Ilimi. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

    19.  Ƙanƙara, L. L. (2004) Siddabarun Harshe: Sabuwar Hanyar Nazarin Adon Harshe a Waƙoƙin Baka Na Hausa, Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    20.  Muhammad, D. (1979) ‘Interaction between the Oral and the Literate Traditions of Hausa Poetry’ in Harsunan Nijeriya, Vol. IX. Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.

    21.  Newman, P. (1937) The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar. New Heaven: Yale University Press.

    22.  Sa’id, B. (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.

    23.  Skinner, N. (1977) A Grammar of Hausa for Nigerian Secondary Schools and Colleges. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

    24.  Umar, M. B. (1987) Adabin Baka. Zaria: Hausa Publications Centre.

    25.  Umar, M. M. (2009) Bayanau da Amsa-Kama a Cikin Waƙoƙin Muhammadu Gambo Fagada. Takardar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilmi na Sashen Koyar da Harsunan  Nijeriya,  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, a kan waƙoƙin Muhammadu Gambo Fagada (Mai Waƙar Ɓarayi).

    26.  Yahya, A. B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services

    27.  Yusuf, M. A. (2011) Hausa Grammar: An Introduction. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    28.  Zaria, A. B. (2014) Sabon Nahawun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    29.  Zarruk, R. M. da Wasu (2005) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Littafi na Biyu: Don Ƙanana Makarantun Sakandire. Ibadan: University Press Plc.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.