Citation: Gusau, S.M. (2024). Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 33-46. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.005.
Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-)
Sa’idu
Muhammad Gusau,
Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Tsakure: An bibiyi rayuwar Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe ne, wanda a bisa
tsarin zahiranci ya zamanto matattari na rumbun wasu mabambantan matanonin waƙoƙi na makaɗan baka na Hausa. A falsafar Ibrahim Gobir dangane
da waƙar baka, ya
samar da guruf-guruf daban-daban a Manhajoji na sada zumunta waɗanda suka haɗa da Manhajar WhatsApp da ta FaceBook da ta Instagram da dai sauran
makamantansu waɗanda ake
amfani da salula da nau’o’in wayoyin hannu da Kwamfutoci da dai sauran
dangoginsu. Misali a WhatsApp ya buɗe Guruf wanda
ya kira Diwanin-Waƙoƙin-Baka inda
yake da mabiya sama da ɗari biyu da
tamanin (280 followers), yayin da a Instagram yana da mabiya kimanin ɗari shida da saba’in (670 followers). A waɗannan manhajoji ana isar da wasu waƙoƙi ko hotuna
waɗanda makaɗan baka na Hausa suka aiwatar a daɗaɗɗen lokaci da
a halin da muke a ciki. Waƙoƙin bakan nan na Hausa sun shafi waƙoƙin Sarakuna
da na jami’an mulki, da na ‘yansiyasa da
na sojoji da na attajirai da na ma’aikata da na Shaihunan Malamai da na mafarauta da na
‘yantauri da na dabbobi da na tsuntsaye da na da na sauran masu sana’o’i da na
gulabe da na garuruwa da da na sauran al’umma. Ta haka ne mabiya waɗannan guruf-guruf suke isar da saƙonnin
tambayoyi dangane da wasu muhallai waɗanda sukan
shige musu duhu a zubi na layuka ko ɗiya na
matanonin waƙoƙin baka. Sau
da yawa ma, sukan nemi bayanai game ko fashin baƙi na wasu ƙanana ko
manyan ma’anoni ko manufofi na furucin matanoni na waƙoƙin baka. Haka
kuma a kan kawo sunaye da tarihin rayuwa da hotuna na wasu makaɗan Hausa, marigaya da rayayyu, tsofaffi da manya da
matasa da yara, maza ne ko mata, daɗa shahararru
ne ko fitattu ko masu tasowa. Sannan akan kawo wasu kayan tarihi da na al’adu
waɗanda suke
jejjefo su a cikin matanoni na waƙoƙinsu da hotuna na wasu makaɗan baka. Sukan gabatar da kacici-kacici, musamman
kan tarihin rayuwar wasu Sarakuna na Gobir da na wasu Sarakuna a Ƙasar Hausa.
Fitilun
Kalmomi: Gobirawa, Makaɗan Baka, Ibrahim Hassan Bagwashe
Gabatarwa
Jinsin Hausawa, Gobirawa, jinsi ne na mutane masu ƙwazo, masu fafutuka a kan dukkan abubuwan da suka sa a gaba,
ko hankalinsu ya karkata a kansu. Ta haka, suka zama masu bajinta, masu sa kai,
masu kwarjini, masu jaruntaka, masu juriya. Ta wani gefe kuma, suka zama masu
azanci, masu nuna hazaƙa, masu basira,
masu zalaƙa.
A muƙalar nan, za a
waiwayi rayuwa ta wani matashin Bagobiri, mai yawan ƙwazo, sha turmuza, mai ɗaga
hannu ya yi kirari. Haka kuma matashi ne mai tarbiyya, mai biyayya, mai haƙuri. Mutum wanda ya karkatu da himmatuwa a cim ma maslaha
mai janyuwa i zuwa ga bunƙasuwa da ilmantar
da al’ummar da yake a cikinta. Wannan gwarzon Bagobiri kuwa shi ne Malam
Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe, mawaiwayi, matattari, mafaɗaɗin rumbu da rudu da matanoni na waƙoƙin mabambantan
makaɗan baka na Hausawa waɗanda
suke rerawa da sadarwa ga al’ummar Hausawa bisa kowace kusurwa ta Ƙasar Hausa.
Ba abu ne kawai na jan hankali ba, rayuwa ce bisa zahiranci,
wadda aka gani, aka tabbatar, aka shaidar a ƙasa da kuma a salkunan gidaje na masu bin diddigi cikin
ganowa da fahimtar waƙoƙin makaɗan baka na Hausa.
Mutane, musamman ma waɗanda
aka ambata a baya, za su zaƙu
ainun, kai har ma su cika su tumbatsa, irin ta kwari ko randa ko tulu, domin su
ɗanɗani ko su lashi wani basɗi na
tarihin rayuwar wannan mutum wanda yake a gaɓarsa.
An raɗawa wannan takarda batu da aka sarƙa masa kalmomi: Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan
Baka, Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-).
Ƙananan batutuwa a wannan muƙala sun haɗa da:
·
Asali
na jini da Salsalar Ibrahim Gobir;
·
Haihuwa
da Tasowa ta Ibrahim Hassan;
·
Matsayi
na Ilimin Alƙur’ani
da na Boko;
·
Durmuya
a Waƙoƙin Baka na Hausa da sa-kai a wasu kafafe da Manhajojin
Sadarwa;
·
Garin
da Ibrahim Hassan Gobir yake zaune yana Gudanar da Kasuwanci da Sauran
Hidimomi;
·
Aure
da Kafa Usra.
A siga ta wannan rubutu kuwa an karkata ainun a tattaunawa
da lura da tsinkaya, tun ma ba ta ɓangarorin
da suka danganci al’amura na hada-hadar Malam Ibrahim Hassan Gobir ba. Har wa
yau kuma, an bi ta turbar yin bayanai da sharhantawa da kuma ta tantance rayuwa
ta wasu kadadu na tattakin Hausawa. Bisa jumla, wannan muƙala za ta yi magana ne game da rayuwa ta Ibrahim Hassan
Gobir tun daga asalin zuriyyarsa zuwa yau.
Asali na Jini da Salsalar Ibrahim Gobir
Asali na Jinin Ibrahim Hassan
Asali na jini na Ibrahim, jini ne da ya samo shi daga jini
na Gobirawa,[1] a
ɓangaren Sarkin Gobir Hassan Ɗanhalima, Sabon Birni (1864-1871).
Domin haka, iyaye da kakanni na Ibrahim suna daga cikin
Gobirawa waɗanda suka ba wa Hassan Ɗanhalima, Sarkin Gobir na Sabon Birni goyon baya a zucci da
zahiri kuma a yaƙazatan, har wa yau
kuma daga kakannin na Ibrahim akwai wanda Sarkn Gobir Sabon Birni Umaru
Jari-Kada (1904-1915) ya naɗa shi Sarkin Ɗiyan Gobir a Sabon
Birni.
Salsalar Ibrahim Gobir
Taƙaitacciyar nasaba
ko salsala ta Ibrahim Gobir ita ce:
Nasabar Uba: Hassan Ibrahim
shi ɗa ne
na Alhaji Hassan da ake kira Bakwai ko Babari ɗan
Hillo Giwa, ɗan kuma Sarkin Ɗiya wato kakan Ibrahim na biyu.
Malam
Hassan, Mahaifin Ibrahim Gobir[2]
Sunan
Mahaifiya
Mahaifiyar
Ibrahim Hassan Gobir ita ce: Rabi. Rabi, uwa ce ma-ba-da-mama, wadda ta kula da
ɗanta Ibrahim, kuma ta
daɗa taimaka wa mijinta
Malam Hassan a tsayar da tarbiyya da koya wa Ibrahim dabarun zaman rayuwa. Rabi
ta ƙarfafa
wa Ibrahim ainun a yayin karatunsa da a hidimominsa na yau da kullum.
Malama Rabi,
Mahaifiyar Ibrahim Gobir Bagwashe
Mazaunin
Farko na Magabatan Ibrahim
Kamar
yadda aka riga aka bayyana a Ƙarin Bayani na 1, kakannin Ibrahim sun
iso, suka kafa mazauni na Birnin Tsibiri, suka ci gaba da zama. A
zamanin Mulki na Sarkin Gobir Bawa Ɗangwanki (1936-1958)
a Tsibiri sai wata matsala ta haɗa su da Hassan Ɗanhalima, wani
fitaccen Ɗandaladiman Gobir.
Daga
nan ne Hassan Ɗanhalima ya nemi Abdurrahman Ɗanyan-kasko ya ba shi
mazauni, sai ya baro Tsibiri, ya je, ya kafa Birni nasa a Fadamar
Kanwa. A tasowar ce Hassan Ɗanhalima ya tafo da iyalinsa da
jama’arsa har kuwa da kakanni na Ibrahim Bagwashe. A shekara ta 1945, ruwan
sama ya ci ƙarfin Birnin Fadamar Kanwa, musamman ma yana a kware ne.
mazauwa Fadamar Kanwa suka tashi suna barin birnin, har kuwa gami da shi Hassan
Ɗanhalima
jagaban jama’a. Sarki Hassan Ɗanhalima ya koma Sabon Birni, Birni
wanda yake a kan tudu. Su kuma kakanni na Ibrahim suka tashi, suka je Katsira,
ƙauye wanda yake gabas da Sabon Birni, kimanin
tazara ta tafiyar kilomita huɗu (4).
Dukkan
abubuwan da aka yi ba a daina su ba, magabatan Ibrahim sun ci gaba da gudanar
da hulɗoɗi tsakanin Katsira
da kuma Sabon Birni har kuwa a yayin da ta zama Ƙaramar Hukuma, a
cikin Jihar Sakkwato ta yau.
Sabuwar Masarautar
Sabon Birnin Gobir
Haihuwa
da Tasowa ta Ibrahim Gobir
Haihuwar
Ibrahim Bagwashe
Allahu
ya ƙaddari
samuwar ɗan’adam bisa umumiyya
ta hanyar haihuwa a tsakanin tsatso na uba da uwa a kuma matsayi
na ma’aurata, miji da mata. A bisa tsari na addinin Musulunci, jinsuna da ƙabilu na mutane tun a
farkon zaman duniya sukan fito a tsakani na uwa da uba (Dubi Hadisi na
Abu-Huraira, Ruwayar Tirmizi, Hadisi na 3955 a cikin littafi na Sunani
al-Tirmizy (?) da kuma a sura ta Al-A’araf (7), aya ta 172. A kuma dubi ƙarin bayani na 172:
‘Ka kuma tuna lokacin da Ubangijinka ya fitar da zuriyyar ‘yan’adam daga
tsatsonsa… (Rijiyar Lemu, M. S. U. (1442/2021) Fayyataccen Bayani na
Ma’anoni da Shiriyar Alƙur’ani, Juzu’i na 2. Sh.:387.
Amman: Bayinat Centre for Ƙur’anic Studies).
Malam
Hassan (Mahaifi) da Malama Rabi (Mahaifiya) su ne suka haifi jariri a
matsayinsu na miji da mata. Sannan suka raɗa masa suna Ibrahim[3].
An ba shi suna na Manzo, mai daraja, domin ya albarkatu da kyawawan halaye na
mai wannan suna, Annabi, Manzo Ibrahim, Halilul-Lahi.
An
haifi Ibrahim a zaman na gari ko mazauni da ake kira Katsira, wanda yake
a nahiyar gabas da garin Sabon Birni na Hassan Ɗanhalima a Ƙasar Fadamar Kanwa. A
yau Katsira[4]
ƙauye ne wanda yake da nisan Kilomita huɗu (4) daga Sabon
Birni, Ƙaramar Hukuma a cikin Jihar Sakkwato, kamar yadda aka faɗa a baya kaɗan.
Matsayi
na Neman Ilmin Alƙur’ani da na wasu Ƙananan Littattafan
Musulunci da kuma na Boko
Neman
Ilimin Addinin Musulunci
Tun da
Hausawa suka karɓi addinin Musulunci,
suke bibiyi hanyoyi na karatu da tilawar Alƙur’ani, mai girma da kuma
koyo na sauran fannoni na addinin Musulunci. Sannan Hausawa sun saduda tare da
mayar da hankali a hidimta wa Alƙur’ani, mai tsarki, da
bibiyar gwadabu na Shari’ar Musulunci.
A
lokacin da Ibrahim ya tasa, ya fara gwadawa da iya furta muhimman ƙwayoyin sauti na
Hausa gwargwadon iyawarsa, sai iyayensa suka sanya shi Makarantar Zaure ta
koyon karatu da tilawar Alƙur’ani, mai daraja. Ya bi
sahu na koyo da ƙididdige babbaƙu da farfaru (Baƙaƙe da wasulla) tare da
haddace wasu ayoyi da ƙananan surori na Littafin Alƙur’ani, mai nassi na Ilahi.
Haka
kuma akwai wata al’ada wadda mazauna wasu ƙauyuka da tungage,
musammanmahaifa suke ƙarfafawa, kuma suke giramawa a harka ta koyon karatun Alƙur’ani wadda suke tura yaro,
ya fita, ya bar ƙauyensu, ya je garin Mungunu na Ƙasar Maiduguri, ya
yi satun Alƙur’ani. Za ya fara cim ma karatun Zuƙu, sannan ya sauki Alƙur’ani, mai girma. An tura
Ibrahim Gobir ya je Mungunu, ya sami shekaru uku (3), ya yi karatun Zuƙu[5] na allo, ya sauki Alƙur’ani, mai tsarki a matsayin
karatun allo.
Kazalika
kuma bisa al’ada ta zamantakewa, a matsayin Bagobiri mazaunin Ƙasar Hausa, Ibrahim
Hassan Gobir, ya karanci ƙananan littattafai na furu’a tare kuma da fahimtar
shika-shikai da hukunce-hukunce na addinin Musulunci gwargwadon bukata.
Ilimin
Boko
Bayan
ilimi na makarantun addinin Musulunci, Ibrahim ya kuma yi karatu na Makarantar
Firamare a mahaifarsa Katsira daga shekara ta 1993 zuwa shekara ta 1999.
Daga
nan kuma Malam Ibrahim ya zarce da karatu na ilimin boko a Makarantar
Sakandaren Gwamnati[6] ta Sabon
Birni daga 1999 zuwa 2005.
Duk da
Ibrahim Hassan Gobir bai zurfafa karatunsa na ilimin Turai ba, yana matuƙar fahimtar harshen
Ingilishi ta hanyar magana da rubutawa da kuma sadarwa[7].
Wannan kuwa ya wanzu ne saboda kazar-kazar da faɗi-tashin da yake ta yi a cikin al’ummu
nau’i-nau’i, da yin mu’amaloli da mutane masu harsuna daban-daban.
Durmuya
da Cakuɗuwa da Waƙoƙin Baka da sa-kai a
wasu Kafafe da Manhajojin Sadarwa
Tun
Ibrahim yana ƙarami ya kasance mai ƙauna tare da mayar da
hankali a sauraron waƙoƙin da makaɗan baka na Hausa suke rerawa, suna sadarwa ga
al’ummar Hausawa. Kamar yadda za a lura, Ibrahim ya tashi a cikin babban gida
na al’umma ta Gobirawa waɗanda suke a ko da
yaushe a zazzaune a cikin gidajen gandu. Gidan su Ibrahim ya ta’allaƙa da hidimomi na
Sarauta da jagoranci bisa harkoki na jama’a. Mu’amalolin da suka ci gaba da yi
ke nan a zama na Katsira da a Sabon Birni da dukkan farfajiya ta Ƙasar Fadamar Kanwa
da ta Daular Gobir ta Birnin Alƙalawa. A gabansa, masarta da
makaɗan baka da masu
kirarin baki da dangoginsu suke ta aiwatar da basirori da azance-azance da zalaƙoƙi, suna rerawa da
sadarwa ga majiɓinta ayyukan nasu na
hikimomi da fasahohi na harshe da na aiwace ko aikace.
Ibrahim
Bagwashe ya taso a durmuye a cikin hikimomi da fasahohin nan tun kuwa a zango
na karatun Firamare da na Sakandare da kuma a halin ƙuruciya da yarinta.
Ta haka hikimomin suka kutso a cikin tunaninsa, suka ja hankalinsa sosai ainun,
ya karkatu haiƙan zuwa sauraro da sauwara su da haddace su, tun ma ba waƙoƙin makaɗan baka ba.
Haka
kuma, Ibrahim ya janyu zuwa sabga ta ji da sauraro na shirye-shirye da wasu
gidajen Rediyon na lokutan da suke sanyawa, suna gabatar wa jama’a masu
sauraro. Gidajen Rediyon kuwa su ne kamar Gidan Rediyon Rima, Sakkwato a
shirye-shiryensa na waƙoƙi da kaɗe-kaɗen Hausawa, musamman shirin da Malam Ahmad Isa ya yi ta
gabatarwa.
Ga kuma
Gidan Rediyo na Kaduna, musamman NBC Kaduna wanda ya yi ta gabatar da
shirye-shirye na zaɓe daban-daban
musamman da Alhaji Halilu A. Getso da Alhaji Ibrahim Maigandi da sauransu suka
yi ta gudanarwa. A cikin shirin ne suka yi ta zaɓo tsofaffi da sababbi na waƙoƙin baka da makaɗan Hausawa iri-iri
suka aiwatar suna jiyar da masu sauraronsu.
Ire-iren
shirye-shiryen Gidajen Rediyo nau’i-nau’i, Ibrahim ya yi ta sauraro waɗanda suka ta’allaƙa a kan waƙoƙin baka na Hausa.
Himma
ba ta ga raggo, a falsafar Ibrahim Gobir game da waƙar baka, sai ya cim
ma wani zango na yin tsimi da tanadi daga kuɗaɗen da ake ba shi ya yi tara[8] a
Makarantar Firamare. Ta haka ne ya yi ta ƙoƙarin sayen kasa-kasai
na waƙoƙin baka yana mallakarsu. Ibrahim ya tattara mabambanta waƙoƙin baka masu yawan
gaske. Ya kuma sami wata natsattsiyar dama a gidansu ta yadda mata wato
iyayensa da yayyensa, sun riga sun mammallaki Rediyoyi masu kaset[9]. Sai
kuma ya sami wata faraga wadda suka ba shi sauli da yake amfani da rediyoyin na
mata, yana sassaka kasa-kasan yana ji, yana sauraro, yana kuma rirriƙewa, musamman a duk
lokacin da ba ya wani aiki.
Sannu-a-hankali,
mutane na haujin mazaunin Ibrahim Gobir suka fahimci malakar da Allah ya ba shi
a ƙwanƙwance matanoni na waƙoƙin baka. Wannan ne ya
janyo, mutane, tsofaffi da manya da ma yara da sauransu, suka dinga yi wa
Ibrahim tambayoyi, yana amsa musu bisa dace dangane da wasu muhallai waɗanda sukan shige musu
duhu a zubi na layuka ko ɗiya na matanonin waƙoƙin baka. Sau da yawa ma, sukan
nemi bayanai game da tarjama ko fashin baƙi na wasu ƙanana ko manyan
ma’anoni ko manufofi na
furucin matanoni na waƙoƙin baka. Waƙar baka ta shiga
rayuwar Ibrahim Gobir ta kuma sami gindin zama, ta yi zamne daram.
A yau
da goben rayuwa, Hausawa a Ƙasar Hausa suka sami shigowar wasu
sauye-sauye daga zuwan baƙin[10] na wasu
baƙin
abubuwa da kayayyaki da sauransu. sai kuma aka cim ma zango na isowar kafofin
sada zumunta a hanyoyin sadarwa na yanar Gozo[11] da
kuma suka shigo da wasiɗar manhajoji iri-iri[12].
Kafar
WhatsApp
Alami na Kafar
WhatsApp
Malam
Ibrahim Hassan Gobir ya yi wata gagarumar huɓɓasawa ta buɗe Guruf a WhatsApp mai
suna: Diwanin - Waƙoƙin - Baka[13].
An fara
fito da babbar madosa da manufa ta wannan Guruf a yayin da aka ɗora masa hoton wata ƙungiyar masarta wadda
ta ƙunshi
makaɗa na ganguna da masu
bushe-bushe.
Makaɗa da Mabusa Masu Nuna
Alamun Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka
Guruf
na Diwanin-Waƙoƙin-Baka, wani muhalli ne wanda aka keɓe shi domin rayawa da
adanawa da bunƙasa ayyuka na al’umma, ciki kuwa har da waƙoƙi da ayyuka na makaɗan baka na Hausa a
cikin wannan al’umma ta masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen manhaja ta
WhatsApp.
An ƙididdige za a samu aƙalla masoya da mabiya
wannan Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka ɗari biyu da tamanin
(280). An kuma ayyana wa wannan Guruf wasu Jagorori, masu gabatar da abubuwa
nasa, da suka haɗa da:
i.
Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Jami’ar
Bayero, Kano
ii. Alhaji
Ibrahim Mohammed, Ɗanmadamin Birnin Magaji
iii. Hajiya
Bilkisu Yusuf Ali, Kano
iv. Malam
Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe Sabon Birni, Abuja
v. Alhaji
Sama’ila Gobir, Sarkin Rafin Sabon Birni, Abuja
vi. Malam
Hussaini Dogo, Sarkin Yaƙi
vii. Malam
Jafar Jafar Ɗanjarida
viii.
Alhaji Ibrahim Musa Ɗanƙwairo, Maradun, Abuja
ix. Alhaji
Ado Ahmad Gidan Dabino, Kano
x. Malam
Ibrahim Shira, BASU, Gaɗau, Bauchi
Wasu
abubuwan da ake bijirowa da su a Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka sun ƙunshi:
a.Ilimantarwa
da fahimtarwa da adana wasu Waƙoƙin Baka na Hausa waɗanda Makaɗan Baka suke ta saka
himma a rerawa da sadar da su;
b.
Sunaye da tarihin rayuwa da hotuna na
wasu makaɗan Hausa, marigaya da
rayayyu, tsofaffi da manya da matasa da yara, maza ne ko mata, daɗa shahararru ne ko
fitattu ko masu tasowa;
c. Wasu
kayan tarihi da na al’adu waɗanda suke jejjefo su a cikin matanoni na waƙoƙinsu da hotuna na
wasu makaɗan baka, kamar:
Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina
Alhaji Muhammadu Sarkin Taushin Katsina da Jama’a ko Ƙungiyarsa
Wata Kawa ta Dabboin Layya a
Sallah Babba irin ta Gobir da Zamfara da Katsina da Kabi da Sakkwato
Wata Tanda Babba ta yin Masa/Waina
d. Text Box:
Janar Murtala Ramat Mohammed, Makaɗa da yawa sun yi masa waƙoƙi
Hotuna na wasu manyan Turaku na Al’umma da masu jarunta da kuma mutane waɗanda suka yi fice har aka jefo maganganu ko ɗiya a wasu waƙoƙin baka na Hausa.
Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar
Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da Chief Olusegun Okikiola Obasanjo
e.Wasu hotuna da aka tsartsarmo bayanansu a wasu waƙoƙin baka na Hausa:
Wani Yanayi na Gona a Ire-Iren Gonaki da Makaɗan Noma Suke Waƙewa
Ustaz Nasiru Wada
Waziri Khalil a zaune a Ɗakin
Heinrich Barth na Kayan Tarihi a Birnin Agadez, Jamhuriyyar Nijar
Wasu Ɗalibai Masu Koyon Hausa a Wata Jami’a ta Ƙasar Sin (China) Suna yin Ɗanin Rerawar Waƙar ‘Jaruma’ ta Hamisu Yusuf Breaker, Kano
f. Har wa yau kuma, wasu magoya bayan Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka sukan kaɗo ko zayikke da wasu hotunan makaɗan baka na Hausa masu yin amfani da zallar kiɗa[14], su dinga ɗora furuci na muryoyin kalmominsu, suna rerawa tare da sadar da waƙoƙi:
Wani Bello Makaho
yana ɗora furuci na muryar
kalmominsa a wani amon kiɗa yana rera waƙa (28/7/2023)
g. Har wa yau kuma, wasu magoya baya na wannan guruf sukan fito da wasu halaye da makaɗan baka na ƙasashen Afirka da na wasu nahiyoyin duniya suke gudanarwa domin a daɗa ƙaruwa da hikimomi da basirorinsu.
Wani soja na Jamhuriyar Nijar a Ɗakin Sitidiyo yana rerawa da sadar da waƙar baka[15]
Ga
wani misali kamar wannan:
Wani Mutumin Ƙasar Guinea Conakry yana
kaɗa wani abin kiɗa, yana rera waƙar baka[16]
Kafar Facebook
Kazalika, wani ƙoƙari da kazar-kazar na
Malam Ibrahim Gobir, Bagwashe ta fuskar daɗa rayawa da cusa ƙauna da bibiyar waƙoƙin baka na Hausa sun
janyo ya shiga, ana damawa da shi a kafa ta Facebook.
Alami na Kafar
Facebook
i. A
kafa ta Facebook, Ibrahim Hassan ya kakkawo wasu waƙoƙi da makaɗan baka na Hausa suka
aiwatar a daɗaɗɗen lokaci da a halin
da muke a ciki. Waƙoƙin bakan nan na Hausa sun shafi waƙoƙin Sarakuna da na
jami’an mulki, da na ‘yansiyasa da na sojoji da na attajirai da na ma’aikata da
na Malamai da na Shaihunan Malamai da na sauran Al’umma. Wasu daga waƙoƙin na makaɗan Hausa da Ibrahim
yake ta kawo su a Facebook sun ƙunshi:
· Wasu
waƙoƙin Dr. Alhaji Mamman
Shata, Katsina;
· Wasu
waƙoƙin Zabiya Gumsu
Maiduguri;
· Wasu
waƙoƙin Makaɗa Idi Ɗangiwa Zuru;
· Wasu
waƙoƙin Makaɗa Jatau Kamba;
· Wasu
waƙoƙin Binta Zabiya
Katsina;
· Wasu
waƙoƙin Zabiya ‘Yardaudu;
· Wasu
waƙoƙin Sale Nadingim;
· Wasu
waƙoƙin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo, Maradun;
· Wasu
waƙoƙin Malam Yahaya
Makaho, Kaduna;
· Wasu
waƙoƙin Dr. Aminu Ladan
Abubakar, Sarkin Ɗiyan Gobir;
· Wasu
waƙoƙin Buda Ɗantanoma Argungu;
· Wasu
waƙoƙin Hamza Caji, Kano;
· Wasu
waƙoƙin Muhammadu Dodo
Maitabshi, Bakura Sakkwato;
· Wasu
waƙoƙin Abubakar Akwara
Sabon Birnin Gobir; Wasu waƙoƙin Mamman Sodangi
Katsina;
· Wasu
waƙoƙin Nadada Sabon
Birnin Gobir;
· Wasu
waƙoƙin Sarkin Tabshi,
Salihu Jankiɗi Gusau, Sakkwato;
· Wasu
waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Maidaji,
Sabon Birni;
· Wasu
waƙoƙin Nagelo Kano;
· Wasu
waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru;
· Wasu
waƙoƙin Nageda, Kano;
· Wasu
waƙoƙin Aliyu Gurso,
Tatatu Mafara;
· Wasu
waƙoƙin Alhaji Abdurrahman,
Sarkin Kotso, Kano;
· Wasu
waƙoƙin Hadiza Potiskum;
· Wasu
waƙoƙin Zabiya Tagoje;
· Wasu
waƙoƙin Zabiya Hamma
Zariya;
· Wasu
waƙoƙin Zabiya Hauwa Ƙanƙara, Zariya
· Wasu
waƙoƙin Zabiya Tani
Kerawa, Zariya;
· Wasu
waƙoƙin Zabiya Hafsatu
Kanuri, Sakkwato.
ii. Tabbas,
a Kafa ta Facebook, Ibrahim yakan kuma gabatar da kacici-kacici, musamman kan
tarihin rayuwar wasu Sarakuna na Gobir da na wasu Sarakuna a Ƙasar Hausa. Sannan
yakan gwamawa da ambaton sunaye da hotuna na wasu kayan tarihi na al’adun
Hausawa;
iii.Akwai
kuma wasu lokuta da yake jefo hotuna na lokacin salloli, babba ko ƙarama, sannan yakan
aika gaishe-gaishen salla-babba da na salla-ƙarama, da wasu
bukukuwa na hidimomin aure ko suna ko makamantansu;
iv.Yakan
kuma yi gaisuwa ta ta’aziyya da ɗora hotuna kamar ta’aziyyar rasuwar Auwal
Garba Ɗanbarno;
v. Ɗora gaishe-gaishe na taya murna da nuna ƙauna ga abokai da
masoya da ‘yan’uwa da ire-irensu;
vi.Na
kuma lura Malam Ibrahim, matashi ne wanda ya kasance a ƙarƙashin shiriya ta
Allahu, duk kuwa da yanayin himma da kazarniya nasa. Domin haka, a Kafa ta
Facebook Ibrahim ya nace matuƙa a wajen yi wa iyaye, uwa da uba
addu’a. Allah ya yi musu rahama, ya gafarta musu, kamar yadda suka yi masa
kyakkyawar tarbiyya, suka ɗora shi a kan turba ta ilimi da kuma suluki na
darajantawa da girmama manya da magabata;
Ya Allah ka Shayar da iyayena, Uba da Uwa, ka kuma shayar
da su daga tsarkakan Gulabe na Aljannah (Ibrahim Gobir Bagwashe)
vii. Ibrahim
ya zamanto mai son maganganun barkwanci, musamman na tsakanin jinsunan Hausawa,
masu wasa da juna da ambaton al’amura domin tuna baya. Kazalika, na fahimci, ba
mutum ne mai yin fushi da ire-iren kalamai na barkwanci da ake gaya masa ba.
Karanci wasu kamar haka:
a.‘Zan
zaɓi Katsinawa, cikinsu
kuma babu Waziri, babu Magajin Gari a cikinsu’ (Ibrahim Hassan, Afrilu, 2023,
Facebook).
b.
‘Kere baban Sanda, a riƙa, a saɓa, a laga, a jingina,
a dogara, a wurwura, a zungura, a jifa’ (Katsina, Bashir Abubakar, 15/9/2023,
Facebook).
c. ‘Kwanan
baya na ji kana cewa mutane masu kiran ka da masu yi maka Teɗt ba ka dubawa su yi haƙuri. To, me ya sa
suke kiran ka ne?’(K/Soro, Murtala Sulaiman (28/5/2023) Barkanmu da salla,
Facebook).
d.
‘Lokacin ana ƙauye ba a zo birni
ba’ (Ƙ/Soro, Bello (28/6/2008), Facebook).
e.‘Bagobiri
ba lissafi. To, mene ne dalilinka na rashin ɗaukar? An yi ma yawa! To…’ (Shinkafi, Bello
(11/6/2023): Ibrahim Hassan Gobir, Facebook).
f. ‘Wanga
gaye ya samu harka. Motoci kake sayarwa haka?’ (Kurfi, Mainasara Yakubu
(11/6/2023): Ibrahim Hassan Gobir, Facebook).
Kafa ta Instagram
A bisa agalabiyya ta Kafa ta Instagram, akan ɗora hotuna ne na mutane da na abinci iri-iri da na kayan abinci da ma’aska da makitsa da mawaƙa da makaɗa da ma’aurata da waɗanda suka rabu a aure da masoya da maƙawabta da masu cakirewa da masu wuce-gona-da-iri da ‘yanwasa na kwaikwayo da na finafinai (‘yan fim) da duwatsu da gulabe da ƙasashe da birane da garuruwa da sauran abubuwan da mabiya Instagram suke ɗoɗɗorawa. Manhajar takan keɓe kadadu da za a iya sassaka waɗannan nau’o’in hotuna na abubuwa da aka bayyana a baya.
Alami na Kafa ta Instagram
Ta lura da bi’ar
manhajar nan Ibrahim Hassan Gobir ya shige ta, ya shagaltu sosai, ya ɗora hotuna da wasu
dangogi na hidimomi da abubuwa na ‘yan’uwa da abokan arziki, tun ma hotuna na
wasu makaɗan baka na Hausa
kamar Sani Aliyu Ɗandawo Yawuri da na ɗansa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yawuri. Ya
kuma sassaka hotuna na wasu ‘yan wasannin kwaikwayo a fejinsa kamar Rabilu Musa
Ɗan’ibro.
A mazaha ko manhaja
ko Kafa ta Instagram, Ibrahim Hassan Gobir yana da mabiya kimanin ɗari shida da saba’in
(670).
Garin
da Ibrahim Hassan Gobir Yake Zaune yana Gudanar da Kasuwanci da Sauran Hidimomi
A wani lokaci da
Ibrahim Gobir ya kai wani zango na neman ilimi na Alƙur’ani, mai tsarki, sai ya ci
gaba da tambayoyi da neman fatawoyi na daɗa fahimtar hukunce-hukuncen ibada na addinin
Musulunci. Kuma a daidai zangon ne ya sami tushen karatun boko na Firamare da
na Sakandare, sannan ya janye shamaki, ya zama mai wayewa. Daga nan ne
ya tsunduma a fahimtar makamar rayuwa ta yau da kullum.
Ibrahim Bagwashe yana
cikin gudanar da rayuwarsa a gida a tsakanin Katsira da Sabon Birni da
tafiye-tafiye na buɗe ido da ƙaruwa da makamar
zamantakewa, Allah, cikin ikonsa da yardarsa, sai yayansa, masoyinsa, Alhaji
Hassan Atace, wanda yake zaune a Abuja yana tafiyar da kasuwancisa, ya
nemi ya je da Ibrahim Abuja, ya riƙa masa al’amuran saye
da sayarwa. Ilai kuwa, magabata suka tsayar da shawara, suka aminta da a yi
haka.
Alhaji Hassan Atace,
Abuja
Area 1 Shopping Centre, Garki, Abuja
A yau, Ibrahim Hassan
Gobir, Bagwashe, yana zaune ne a Abuja, yana ta gudanar da harkoki na
kasuwanci, musamman saye da sayarwa. Yana a tare da ɗan’uwansa cikin
zumunci da amanar Allah da kiyayewarsa. Allah ya ci gaba da tallafa musu, ya ɗaukake su.
Aure da Kafa Usra
Allahu ya ba Malam
Ibrahim Bagwashe damar ya yi aure domin ya cikasa wata muhimmiyar sunna ta
Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama ta kafa usra[17]
wato iyali, ya daɗa cikasa rumbun
‘yan’uwa, ya samar da nasaba maɗaukakiya, mai ɗimbin daraja, mai albarkatu.
Iyali na Ibrahim ko
mata tasa da ya aura, sun zauna da ita cikin aminci da mawadda. Allahu ya yi wa
matar Ibrahim rasuwa ran 14/1/2022. Allah ya jiƙan ta, ya gafarta
mata, ya yafe dukkan kura-kuranta.
Har wa yau kuma,
Allah ya azurta Malam Ibrahim Gobir da samun ɗa namiji wanda aka raɗa wa suna SAMA’ILA.
Muna addu’a, Allahu ya daɗa shirya shi, ya ɗora shi bisa turba mai nagarta ta salihan
bayi. Ya kuma sami tarbiyya da albarka kuma ya kasance mai ƙauna da yi wa
iyayensa da dukkan magabatansa addu’a[18].
Sama’ila Ibrahim
Hassan Gobir
Kammalawa
Bayanai sun gabata a
wannan takarda wadda aka kawo ƙwarya-ƙwaryan jirwaye na
tarihin rayuwar Malam Ibrahim Hassan Bagwashe, Katsira, Sabon Birnin Gobir. Ta
haka aka tattaro muhimman abubuwan na tarihin mutum, matashi mai ƙwazon gaske, mai
kazar-kazar, mai ƙoƙari da fafutukar kalato tarihin magabata a Ƙasar
Hausa da waƙoƙin baka na Makaɗan Hausa. An yi nazarin nan ne a ƙarƙashin batu: ‘Gobir
Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe, Mashigin Waƙa (1985-).
A wannan batun ne aka
bibiyi bayanai masu yin nuni kan asali na jini da nasaba ko salsala da mazauni
na magabatan Ibrahim da haihuwarsa da tasowarsa da iliminsa na Alƙur’ani, mai gima, da na boko
da durmuya da sa-kai nasa a tanadi da sauraro da haddace waƙoƙin baka na Hausa da
kuma shigar Ibrahim cikin wasu kafofin sadarwa na WhatsApp da Facebook da
Instagram. Sannan da yanayi na kafa usra ta Ibrahim Bagwashe da kuma bazamarsa
a cikin hidimomi na kasuwanci a mazauni na Abuja.
Haƙiƙa, an yi wannan
rubutu ne domin a daɗa cusa himma tare da
mayar da hankali a kulawa da tattarowa da adanawa da kiyaye turasu na adabi da
na al’adu da na addinin Musulunci da al’ummar Hausawa ta yi matuƙar jimawa da ƙanƙame su.
Kiyaye maganganun
hikima na magabatanmu na da da na yanzu da tattalin gudanar da su, kyawawan
abubuwan zamantakewarmu ne a matsayinmu na al’umma ta Hausa. Dukkansu hidimomi
ne da ake tafiyarwa a yau da kullum da ma sauransu da suka shafi Hausawa. Waɗannan halaye ne da za
a dinga riƙe su, ana ci gaba da yaɗa su, ana daɗa tattalinsu da
inganta su, musamman ma yadda suka kasance sulukin rayuwar Hausawa.
Na daɗa lura tare da gane
Ibrahim Gobir ya zama zakaran-gwajin-dafi wanda ya kuma yi fice da zara, duk da
matsayinsa a shekaru, a hidimta wa adabi na waƙoƙin baka na Hausa.
Wani misali da Ibrahim Gobir ya assasa, ni ma na yi nuni a kansa, ba kamar
azamarsa da kulawarsa kan waƙoƙin baka. Ashe bai
zama wajibi ga kowane matashi, ya nutsu, ya dinga bibiyar waƙoƙinsa na Hausa a
mabiyu masu inganci ba, ba tare da ana yi musu ɗaukar-sakainar-kashi ba.
Wani abin la’akar a
nan kuma shi ne, tun-ran-gini, ran-zane, ake tsarawa da aiwatar da
shirye-shirye a gidajen rediyoyi na da can, musamman a Arewacin Nijeriya da
suka danganci zaɓe[19]
da a wasu shiraruwa waɗanda suke tsattsarma
waƙoƙin baka na Hausa. Waɗannan Gidajen Rediyo
na da can kuwa su ne kamar NBC, Kaduna ko Rima Rediyo ko NBC, Kano ko NBC,
Katsina da sauransu. Ire-iren gidajen rediyoyin nan bisa zahiri sukan shayar da
masu sauraro wasu waƙoƙin baka ta bin wannan tsari ko siga:
· Waƙoƙi na tsofaffi da daɗaɗɗun makaɗa, maza ko mata,
kamar na Sarauta da na Sarakuna. Daga bisani suka shigo da na ‘Yansiyasa da na
Sojoji masu riƙe da muƙaman Gwamnati.
· Waƙoƙi na sauran manyan
Makaɗa, maza ko mata,
kamar na mafarauta da na ‘yantauri da na attajirai da na sauran masu sana’o’i
da na Malamai da na manyan mata da wasu manyan ma’aikata da na dabbobi da na
tsuntsaye da na gulabe da na garuruwa da sauransu.
· Waƙoƙi na matasan makaɗa, maza ko mata kamar
na soyayya da na wasannin kwaikwayo da makamantansu.
· Waƙoƙi na makaɗan bege, yawanci maza
da suka ƙunshi waƙoƙin Manzon Allah,
sallallahu alaihi wa sallama, da na Sahabbai da na dukkan Ahlul-Baiti[20].
A yau kuwa, masu
shirye-shirye a Gidajen rediyoyin Arewa da Nijeriya har kuma gami da wasu
tashoshin Hausa a Gidajen Rediyoyin Ƙasashen Waje sukan keɓantu, musamman da:
· Waƙoƙin makaɗa matasa, maza ko
mata, tun ma ba waƙoƙin da su da kansu suke nuna suna buga su a ɗakunan Sitidiyoyi ba.
Ire-iren waɗannan waƙoƙi na matasa, su ne a
yau rediyoyi suka fi tsarmawa a shiraruwansu a bisa agalabiyya. Wasu daga cikin
waƙoƙin sun fi karkata a
kan soyayya ta tsakanin ‘yanmata da samari da a cikin finafinai da wasannin
kwaikwayo, ana yi kuma ana raye-raye ko da tsalle-tsalle. Wasu waƙoƙin kuma suna gwada
wasu al’adun gargajiya da na bukukuwan aure da makamantansu.
· Haka kuma akwai waƙoƙin wasu manyan makaɗa da mawaƙa, maza da mata, waɗanda suke bubbuga su a Gidajen Sitidiyo. Sannan Gidajen Rediyoyin sukan ɗoɗɗora su a sa’ilin aiwatar da wasu shirye-shiryensu.
Takardar nan tana yi
wa wasu masu aiwatar da shiraruwan rediyoyi a yau da masu sauraron waƙoƙin Hausa, su ajiye
budurwar zuciya a gefe, su fahimci waƙoƙin baka bisa halayya
da ma’anoni ko saƙonni, manya da ƙanana, da makaɗan baka suke ɗora asali na aiwatar
da su. Sannan kuma a dinga ware waƙoƙi masu nagarta bisa
wata fa’ida, sannan su kuma fitar da waƙoƙi ballagazazzu ko na
sharholiya ko na zage-zage, musamman ta la’akari da fuskar zaɓen kalmomi da tsara
furuci mai alfanu bisa tarbiyya ta shari’a da sunnar Manzon Rahama, tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi.
Alhamdu Lillah, ina
yi wa Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe wanda ya tsamo ni a cikin dubbai ya
ba ni dama in rubuta tarihin rayuwar nan tasa. Ina matuƙar godiya ainun. Ina
daɗa gode wa Allahu, mai
kowa, mai komai, wanda ya ba ni iko da sauli na haɗa wannan talifi.
Ni’imomi dukka Allah
ne yake ba da su ga wanda ya so. Muna daɗa tsarkake Allahu a kan hikimomin da ya bai
wa Ibrahim Hassan Bagwashe har ya sami azama ta raɓuwa da matanonin waƙoƙin baka na Hausa,
kuma yana amfanar da jama’a, yana zazzare ɓatagarin su daga ɗimbin salihansu.
Allahu ya daɗa yin tsira da aminci
ga Manzon Allah, Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wa sallama. Muna roƙon Allahu, tabaraka
wa ta’ala, ya tashe mu a ranar Mahshar a inuwar Manzon Rahama, Manzon Jiƙayi. Ranar da ba wata
inuwa sai kawai inuwa tasa. Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali
Muhammadin, kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima Fil-alamina Innaka
Hamidun Majidun. Allahumma salli ala Muhammadin, wa Ashabihi, wa Zurriyatihi,
wa Ahli Baitihi, wa sallama taslima. Muhammadur Rasulullahi, sallallahu alaihi
wa sallama.
Manazarta
Alƙur’ani, mai Tsarki.
Al-Tirmizy (Babu
Shekarar Bugawa) Sunan al-Tirmizy
Adamu, M. (1987)The
Hausa Factor in West African History. Zaria: Ahmadu Bello University Press
& Ibadan: Oxford University Press, Nigeria.
Augi, A. R. (2021) The
Gobir Factor in the Social and Political History of the Rima Basin C. 1650 to
1808 AD. Makurɗi, Nigeria: Aboki
Publishers.
Gusau, S. M. (1:2009;
2:2014; 3:2018; 4:2019; 5:2020; 6:2022) Diwanin Waƙoƙin Baka 1, 2, 3, 4 ,
5, 6. Kano:
Benchmark Publishers Limited; Kano: Century Research and Publishing Limited;
Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Baka na Hausa I. Kaduna: Fisbas Media
Services.
Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2013)
‘Mizani Tsakanin Waƙoƙin Hausa na Baka da Rubutattu’ a cikin Studies in
Hausa Language, Literature and Culture: The 1st National Conference:
(Ed. Yalwa L. D.; Gusau, S. M.; Ibrahim Birniwa, H. A.; Abdulƙadir, M. Y.; Chamo,
I, Y.; Kano: CSNL, Bayeru University & Zaria: ABU Press Limited.
Gusau, S. M. (2014) Makaɗan Hausa Jiya da yau.
A
cikin Garkuwar Adabin Hausa: A Festchrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Zaria: Ahmadu Bello
University Press Limited.
Gusau, S. M. (2014) Waƙar Baka Bahaushiya. BUK Inagural Lecture
No. 14. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M. (2016) ‘Ɗani a Waƙoƙin Baka na Hausa’ A cikin Journal of
Hausa Poetry Studies. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gusau, S. M. (2016) Makaɗa da Mawaƙan Hausa 2. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2021) Rayuwa
da Jajircewar Alhaji Dr. Aminu Ladan Abubakar, Alan Waƙa. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2022) Fannin
Falsafa a Ilmance. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing
Limited.
Gusau, S. M. (2023) Dauloli
a Ƙasar Hausa. Kano: WTPress,
Commercial Printing and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2023) Jagoran
Nazarin Waƙar Baka (Sabon Tsari). Kano: WTPress,
Commercial Printing and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2023) Nazarin
Al’adu da Adabi a Rayuwar Hausawa. Kano: WTPress, Commercial Printing and
Publishing Limited.
Muhammad,
A. S. (2012) ‘Nazarin Ayyukan Makaɗa Sa’idu
Maidaji Sabon Birni (1938-2000)’. Juzu’i na 1&2: Kundin Digiri na Biyu (M.
A.). Zaria: Sashen Harsuna da AL’adu, Jami’ar Ahmadu Bello.
Rijiar
Lemu, M.S.U. (1442/2021) Fayyataccen
Bayani na Ma’anoni da Shiriyar Al-ƙur’ani, Juzu’i
na biyu (2). Amman: Bayinat Center for Ƙur’anic
Studies
Salihu,
A. A. (1978) ‘Kaɗe-Kaɗen Hausawa da Bushe-Bushensu da Kayan yin su’ a cikin Makon
Hausa 13. Kano: Ƙungiyar Hausa, Jami’ar Bayero.
Usman, Y. B. (1981) The Transformation of Katsina (1400-1883)
Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited. ISBN 978 125 016.
Tattaunawa
Da Wasu Mutane
|
Suna |
Gari |
Shekara |
1. |
Malam
Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe |
Katsira, Sabon Birni & Abuja |
2023 |
2. |
Alhaji
Ibrahim Alhassan |
Sabon
Birni & Kano |
2023 |
3. |
Alhaji
Magaji Funtua |
Funtua |
2023 Wayar
Hannu |
4. |
Alhaji
Haruna Suleiman Gobir |
Sabon
Birni & Kano |
2023 |
Tsakure
Na Wasu Bayanai Da Hotuna Daga Wasu Kafofi Na Sadarwa
|
Sunan Kafar Sadarwa |
Shekara |
1. |
Kafar
Sadarwa ta WhatsApp, na Guruf Diwani – Waƙoƙin
- Baka |
2023 |
2. |
Kafar
Sadarwa ta Facebook, Shafin Ibrahim Hassan Gobir |
2023 |
[1] A
tarihance, ana bayyana Gobirawa mutane ne masu kuzari, masu ƙama da ƙarfin
jiki. Sannan kuma a shirye suke a ko da yaushe bisa ko-ta-kwana. Gobirawa masu
zafin nama ne. Wasu masu tarihi na rubuce sukan bayyana Gobirawa Hausawa ne,
masu taɗi ko magana da harshen Hausa, kuma a cikin harshen Hausa ne suke
gudanar da hulɗoɗinsu na zamantakewa a kuwa kowane ɓangare na rayuwarsu, kamar
gudanar da al’adu da maganganu na hikima da balagar harshen Hausa.
Idan
kuwa an amince Gobirawa Hausawa ne, ashe sosai haƙiƙa suna daga cikin mazauna
na farko a Ƙasar Hausa, wuri wanda ya zamanto a yankin Arewaci na Afirka
(Adamu, M. (1987) Zaria: ABUPress, Sh: 6-7). Gobirawa suna cikin zama na
Ƙasar Hausa ne saboda jaruntakarsu da shaja’o’i da bajintarsu da ƙirkizarsu
suka tsiri yin ƙaura zuwa wasu ƙasashe tsofaffi, musamman a Afirka ta Gabas da
ta Tsakiya da wasu Arewacin Africa da Yammacin Afirka.
A wata
ruwaya da ake badawa, an nuna Gobirawa, sun baro birnin Gubur da yake a cikin Ƙasar
Saudiyya, a ɓangarn Afirka ta Gabas daga Tsakiya, suka biyo ta wasu manya da ƙananan
garuruwa masu kuwa yawan gaske. Daga nan ne a kwana a tashi,a cikin yaƙi da
zaman lafiya, suka iso Gwararrame har zuwa Tsibiri da Gobir Tudu, zuwa
Alƙalawa, zuwa Fadamar Kanwa ta Sabon Birni. A kuma tattaunawar da na yi
da Ibrahim Hassan Gobir, Laraba, 26/7/2023, ya kawo wata ruwaya da yake faɗin:
‘Kakanninsu
Gobirawa sun taso daga Gubur, suka miƙo hanya tiryan-tiryan, a shirye cikin ɗaga
jijiyoyin jiki, har suka iso Alƙalawa, sai kuma suka je, suka kafa Gwararrame
da Birnin Lalle da Birnin Kunya, har kuma aka dawo Tsibiri. A Tsibiri
ne aka sami wata matsala tsakanin Sarkin Gobir Bawa Ɗangwanki da Ɗangaladima
Gobir a Tsibiri, Hassan Ɗanhalima (Saurari waƙar ; ‘Jikan Jari Ginshiƙ’i ta
Nadada Sabon Birni da Sa’idu Maidaji). Daga nan ne Hassan Ɗanhalima ya je ya
sami Abdurrahman Ɗanyankasko, Sarkin Musulmi, ya nemi ya ba shi mazauni.
Abdurrahman Ɗanyan-Kasko ya ba shi dama a sake ta ya shaci wurin da zai ishe
shi da jama’arsa a Ƙasar Fadamar- Kanwa. Wannan ne ya kawo kafuwar Fadamar-Kanwa
wadda Hassan Ɗanhalima ya Sarauce ta. Hassan Ɗanhalima ya yi dukkan waɗannan
yawace-yawace da kakannina har zuwa 1945 da ruwa ya malale Fadamar-Kanwa, aka
koma sabon wuri bisa tudu wanda aka kira Sabon Birni (Domin a ƙara samun
fashin baƙi tare da warware wasu matsaloli a dubi: Gusau, S. M. (2003) Dauloli
a Ƙasar Hausa. Kano: WTPRess, Commercial Printing and Publishing Limited)’.
[2]
Allahu ya albarkaci Alhaji Hassan da samun ‘ya’ya, maza da mata, kimanin
talatin (30). Daga cikinsu akwai yayye da ƙanne na Ibrahim Bagwashe. Daga
cikinsu, akwai Alhaji Salihu Bakwai da Alhaji Shu’aibu Nagoshi da Alhaji
Shu’aibu Kabo da Alhaji Hassan Atace, Abuja da sauransu.
[3]
Iyaye da ‘yan’uwa da abokai ba su karkata wajen sa wa Ibrahim wata alkunya
ba. An ci gaba da kiran sa kai tsaye da sunan da aka raɗa masa na Ibrahim.
Sai dai akwai wasu ƙalilan waɗanda suke yi masa laƙabi da Bagwashe ko
Iro ko Ibro ta hanyar taƙaita ƙwayoyin sauti na kalmar Ibrahim.
[4]
Kamar yadda aka nuna, wasu masana tarihi, suna ganin an raya tunga ko ƙauyen Katsira
a 1945, a shekarar da ruwan sama ya tayar da Birnin Fadamar Kanwa.
[5]
Karatun Zuƙu, shi ne almajirin Alƙur’ani tun daga matsayi na Ɗankuludo
ya bibiyi baƙaƙe da wasulla da ayoyi da surori na Alƙur’ani har
(114), ya iya karanta su cikin zubin Larabcinsu ba tare da lalle sai ya iya
tarjama su ba. Wannan wata fassara ce ta karatun zuƙu.
[6]
Wato Government Secondary School (GSS) Sabon Birni.
[7]
Wato Performance and Communication.
[8]
Wato break da Ingilishi.
[9]
Wato Recorder.
[10]
Kada a manta a Ƙasar Hausa an sami zuwa na wasu al’ummu baƙi, da suka shisshigo
dangane da wasu lokuta da ƙarni-ƙarni mabambanta kamar Fulani da Larabawa da
Turawa da Barebari da Nupawa da Yarbawa da Igbo da sauransu da yawa.
[11]
Yanar-Gizo ko Intanet.
[12]
Manhajoji ko kafofi sun haɗa da kafa ta WhatsApp ko Facebook ko Instagram ko
Twitter ko YouTube ko sauransu waɗanda ake amfani da salula da nau’o’in wayoyin
hannu da Kwamfutoci da dangoginsu.
[13] A
mahanga ta zahiri, Malam Ibrahim Gobir ya samo batun nan ne daga suna na wani
Littafi na Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau: Diwanin Waƙoƙin Baka. A yau
wannan littafi yana da juzu’o’i guda shida (1(2009); 2(2014); 3(2018); 4(2019);
5(2020) & 6(2022).
[14]
Haƙiƙa, amon murya da na kiɗa su ne suke haɗuwa su samar da waƙar baka ta
Hausa. Waɗannan abubuwa biyu (2) suke gamuwa har a iya rera waƙar baka, a kuma
sadar da ita. A yayin da ake furta kalmomi a matsayin muryar waƙar baka, wajibi
ne a daidaita nauyin kiɗa domin mai sauraro ya gane ƙananan saƙonni na kalmomin
da ake rerawa. Amma a lokacin da ake so a harraka mutane da kiɗa, sai shi kuma
makaɗi (wato mai furucin muryar waƙa) mai yin furucin murya ya tsahirta.
[15] Ɗakin
Sitidiyo, ɗaki ne wanda ake zuba wasu na’urori da Turawa suke yin su,
suke kuma ajewa a ɗakuna da suke kira Sitidiyoyi. Ta amfani da na’urorin ne
suke daidaita amo ko sauti na kiɗa. Ke nan Sitidiyo ɗaki ne wanda yake ƙunshe
da kayayyaki na yin kiɗa da daidaita amo kamar ganguna da kwamfutoci da
miksoshi da bigiloli da tasoshi da tsintsiyoyi da mikirifofi wato amsa-kuwa ko
lasifikoki da madangantansu.
[16] A
yau, a Ƙasar Hausa da Nijeriya, makaɗa masu aiwatar da waƙoƙin Hausa na baka
sun daɗa laƙantar amfani da ɗakin Sitidiyo. Yanzu ta kai, makaɗi yakan rubuta
zubin waƙar ne wato ta harhaɗawa da zaɓen kalmomin waƙa (composing), sannan ya
karanta su da furuci na muryarsa (voicing). Daga nan ne zai tafi, ya shiga Ɗakin
Sitidiyo, sai Makaɗan Sitidiyo, su ƙirƙira wa furucin na muryar waƙa, kiɗa
(Sound/Voice), su kuma sarrafa shi gwargwadon nauyi da zaƙin kiɗan da ake
bukata. Bayan haka, sai su ɗora murya ta furuci na mai waƙa (Jagora). Idan kuma
ana son waƙar ta zama ta Ƙungiya, sai a daɗa ɗora murya ta masu karɓi
(‘Y/Amshi) daga furuci na muryar jagora, sai a sarrafa muryar tasa ta zama
muryoyi na wasu mutane (miɗing). Na’ura ta Miksa, ita ce jagora wajen
sarrafa na’urorin sitidiyo. Na’urar ce kuma take yin wannan aiki, ba mai
shiryawa ko aiwatarwa ko rubuta waƙa ba, wanda kuma zai iya zama makaɗi da
kansa, ko wani mai tsara kalmomin waƙa. Ta wannan sabuwar hanya ce ake bi a
samar da Rauji na waƙar baka. A dinga sauraro kamar ko daidai-wa-daida
da Rauji na waƙoƙi na makaɗan baka na asali da wasu suke kira Makaɗan
Gargajiya.
To,
mene ne matsayin wannan sabon tsari na fitar da Rauji? A fannin nazarin
waƙar baka tun daga farko zuwa yau, idan aka sarrafa na’urori a Sitidiyo,
aka samar da irin raujin nan sabo, bai share Jagora da ‘Y/Amshi
ba, suna nan a matsayinsu kama da kafin zuwan na’ura. Domin haka, idan za a
wakilce su a takarda, dole a rarrabe yanayi na rubuta su zuwa waƙoƙi na ƙungiya
da waƙoƙi na kaɗaita, kamar haka:
a)
Ƙungiya: Jagora:-----------
:‘Y/Amshi:--------
b)
Kaɗaita: Jagora:-----------(kawai).
[17]
Usra, kalma ce ta Larabci wadda take nufi da iyali na mutum waɗanda suka haɗa
da matar aure da ‘ya’ya da jikoki da jikan jika da kama-kunne da tattaɓa-kunne
da sauransu (http://en.bab./a/dictionary/malay-english/usrah
ko kuma https://www.wordhippo/arabic-word).
[18]
Muna taya murna da yi wa Malam Ibrahim addu’a, Allahu ya daɗa aura masa mata
saliha ta gari, mai biyayya, mai kiyaye sirri da amanonin mijinta. Mata wadda
za ta zama mai kunya, mai kara, mai kiyaye ibada da hidimominta na gida. Mai
kyawawan hasloli, musamman a mu’amaloli na zaman aure.
[19]
Zaɓen yi wa masoya gaishe-gaishe, ba na ‘yantakara a Siyasa ba.
[20] Akwai wasu ayyuka da Gusau, S. M. (2008:448; 2023:26; 2022: 152-174; 2021: 48-50) ya gabatar waɗanda ya yi bayanai a kan makaɗan baka na Hausa inda aka rarraba su bisa dangantakoki na waƙoƙinsu, aka saka su a kadadu guda uku da suka haɗa da (i) Makaɗa masu yin waƙoƙin bege (ii) Makaɗa da Masarta masu waƙoƙi da kirari da kaɗa taken Sarauta ko fada (iii) Makaɗa masu waƙoƙin jama’a, na mutanen da ba a (i) ko na (ii) suke a ciki ba.
Download the article:
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.