إِنَّ الأُمورَ إِذا الأَحداثُ دبّرها
دونَ الشُيوخ تَرى في بَعضِها خَللا
إِنَّ الشَباب لَهُم في الأَمرِ معجلَةٌ
وَلِلشُيوخ أَناة تدفع الزللا
-الصفدي
Y. A. UMAR
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Rahama, tsira da aminci su ƙara tabbata akan FIYAYYEN HALITTA da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Haƙiƙa tattaunawa yana ta gudana a duk matattaran al'umma, a sama da ƙasa, ma'ana; online and offline, gameda shirin zanga-zanga wanda aka shirya shi da manufar nunawa gwamnatin tarayya, irin wahalan da talakawa suke ciki a wannan ƙasa tamu mai ɗimbin abin mamaki, wato Najeriya. Wannan shiri na zanga-zanga, ance matasa ne suka shirya shi, amma koda yake ana ganin akwai masu take musu baya wajen ganin sunyi wannan aiki, wanda wasu masana da dama sukace, yana cike da haɗarurruka ga ƙasar kanta da su kansu masu shirin zanga-zangar, da sauran ƴan ƙasa waɗanda basuji ba, basu gani ba. Ga masu bibiyan labarai, jaridar Guardian ta ruwaito cewar, gwamnatocin Amurka, Ingila da Canada sun gargaɗi ƴan ƙasashensu akan zuwa ko yawo a ƙasar, musamman mazauna Najeriya a dalilin shirin zanga-zanga.
Tun lokacin da aka sanar da aka sanar da shirin
zanga-zangar, abubuwa suke ta faruwa kullum. Daga nusarwar da malamai sukayi
akan haramcin zanga-zanga a musulunci, zuwa martanin matasan ta hanyar cin
zarafin malaman a kafafen sada zumunta na zamani, zuwa magantuwar gwamnatin
tarayya ta hanyar jami'an ta da yawa, zuwa yunƙurin Majalisar Wakilai, zuwa magantuwar
gwamnonin jam'iyyar APC, zuwa sanar da buɗe
shafin neman rance ƙarƙashin Ma'aikatan Matasa da Wasanni, zuwa sanar da shirin ɗaukan aiki a kamfanin man Ƙasar,
wato NNPCL, zuwa maganan jagoran Kwankwasiyya, zuwa matsayin hukumar ƴansanda
da sojan Najeriya akan zanga-zangar, zuwa matsayin da Ƙungiyar Kiristocin
Najeriya (CAN) ta ɗauka,
zuwa ziyaran malaman addinin Islama ga shugaba Tinubu, zuwa matsayin Peter Obi
akan zanga-zangar, zuwa yau Litinin da ake saura kwanaki kaɗan don gudanar da zanga
zangar. Duk waɗannan
abubuwa da suka faru kuma suke faruwa zuwa yanzu, sunci tura wajen isar da saƙon su
zuwa inda suke so ya isa, ma'ana, wajen sauya akalar waɗanda suke so su isarwa da saƙon.
Idan mun lura, an rabu gida biyu ne akan wannan
zanga-zangar, masu neman dakata da masu yin zanga-zangar, sai kuma masu goyon
baya. Don haka, duk wanda yayi magana yanayi ne don chanja ra'ayin waɗanda yake isar da saƙon sa
garesu. Masu hanawa suna buri ne wajen ganin masu shirin zanga-zangar sun
janye. Masu shirin zanga-zangar kuma, suna buri ne gwamnati ta magance matsalar
da suke ciki, wanda a cewar su, itace silar shirya wannan zanga-zangar. A
fahimta ta, duk ɓangarorin
biyu ko kuma ɓangaren
masu yunƙurin
hanawa, sun gaza wajen samun abinda suke so. Toh shin, masu shirya zanga-zangar
zasu samu tasu biyan buƙatar bayan fara zanga-zangar?
Wannan tambayar itace masana da yawa suke ta ƙoƙarin
amsawa ta hanyar kawo dalilai da dama, ciki har da tarihin irin yadda waɗannan zanga-zangar ta
kasance a wasu ƙasashe da ma ƙasar nan, da wasu zamunnan baya, da
zamanin ma da muke ciki. Akan hakan ne, nima naga dacewar na furta tawa
MATSAYAR. Ko ba don komai ba, saboda nima ɗan
Najeriya ne, kuma matashi, kuma wanda yake fama da tsadan rayuwa, saboda
zaluncin shugabannin ƙasata, Najeriya. Da kuma tsare-tsaren rashin tausayi da jinƙai
wanda gwamnatin Najeriya ta ringa sanarwa da aiwatarwa, ba tareda tunanin mezai
faru ba, ko yaya talakawa zamuyi ba. Alhalin ita gwamnatin bata samar da wani
tsari ba, akan yadda zata inganta rayuwar al'umma ta hanyar bunƙasa
tattalin arziƙin ƴan ƙasa. Mubar wannan a gefe, domin ba shine manufar rubutun tawa
ba.
Manufata itace, kawo ƙarin dalilai da suka sanya matasa da
sauran ƴan
ƙasa
shirya wannan zanga-zangar bayan zallan tsadan kayayyakin masarufi da ƙarancin
abin hannu da tsukewar hanyoyin samun kuɗaɗen shiga. Amma fa kowa ya
sani, ni mai wannan rubutu, na zaɓi
wannan jam'iyya, da kyakykyawar fatan zata iya kai ƙasar ga tudun mu tsira
kamar yadda aka tallata su a yayin yaƙin neman zaɓe,
musamman, irin yadda aka nuna ƙaƙarin ɗan
takaran, wato shugaba Tinubu wajen mayar da Legas yadda take a yanzu, hakanan
shima mataimakin sa, Kashi Shettima da abinda yayi a Borno.
Idan zamu iya tunawa, gwamnatin Buhari itace ta samar da
shirin na N-Power domin samar da ayyukan yi da madogaran rayuwa ga matasan da
suka gama makaranta da waɗanda
basuyi karatun ba ma, kuma basuda aikin yi. Aka shirya shi a ɓangarorin buƙatun
al'umma dabam dabam, kamar Ilimi da kiwon lafiya sai kuma sana'o'i. An gudanar
da wannan shiri na tsawon shekaru kuma matasa da dama sun samu shiga cikin
shirin inda suka samu daman buɗe
wajajen sana'o'i da kasuwancin su a dalilin shirin. Amma a wanda ya zama na ƙarshe
a gwamnatin Buhari, an ɗauki
matasa da suka gama makaranta a tsarin shirin na N-Teach domin su koyar a
makarantun gwamnatin da alƙawarin za'a biya su dubu talatin a kowace wata na tsawon
shekara guda, aka tura su makarantu sukayi aiki, tun daga watan Satumba na
2022, zuwa watan Yulin 2023. Amma, kwata-kwata na watanni uku aka biya su!
Shikansa biyan, anyi shine a watannin Fabrairu da Maris na shekara 2023,
lokacin zaɓen shugaban
ƙasa.
Sauran haƙƙin
na watanni tara, har yanzu, kuma ko labari babu akan yaushe za'a biya. Sai alƙawuran
ƙarya
da yaudara da gwamnati take tayi wa matasan. Ance an ƙwato kuɗin daga hannun wasu wai
"consultants" kuma za'a biya, daga nan sai ji mukayi an cire minista
da shugaban hukumar da take kula da shirin bisa zargin almundahana. Daga nan
kuma babu wani labari. Na biyu, gwamnatin ta ƙaddamar da wani shiri na baiwa ƴan ƙasa
kyautar Naira dubu hamsin, ga mutane dubu ɗaya
a kowace jiga, da kuma rancen kuɗin
farfaɗo da kasuwa ga
masu kasuwanci, wanda jama'a suka cika, amma ƴan ƙalilan ne suka samu wannan kuɗi na dubu hamsin, rance kam
babu wani labari akai. Har ila yau, gwamnatin ta bayar da tallafi akan a raba
wa talakawa don yaye raɗaɗin talauci da yunwa da suke
fama dashi, amma wannan tallafi tunda ya shiga hannun gwamnoni, labari akansa
ya ƙare.
Kuma gwamnatin tarayya batayi wani yunƙuri na sauya labarin ba, sai kawai ta
sake basu wasu tirelolin na hatsi, wanda shima yanzu an fara ganin sa ana
shirin kai shi kasuwa! Duk wani shirin da gwamnatin tayi alƙawarin
yin sa don talakawa, babu wanda talakawa suke mora a halin yanzu. Har waɗanda ta gada daga gwamnatin
baya, kamar NG-CARES!
Duba da waɗannan
abubuwa da wasunsu, kamar kashe kuɗin
ƴanƙasa
wajen gyaran gidajen shugaban ƙasa da mataimakin sa da kuma chanja
jiragen fadan shugaban ƙasa da ƙarin alawus ga ƴan majalisu, da sauran abubuwan da ƴan
Najeriya suke ganin rashin tausayi ne da damuwa da halin da suke ciki, don haka
dole su fito su nunawa gwamnati cewar, ba zasu yarda a kashe su a tsaye, kamar
yadda duk me fahimta haka zai fahimta.
Toh amma hakan itace hanyar samun gyaran ko kuma hanyar da
wasu masana cikin malaman addini da na zamani suke ta ƙira akai? Amsar wannan
tambayar, itace manufar rubutuna na biyu. Wato zanyi ƙoƙarin kawo wasu hanyoyi da
nake ganin zasu taimaka a shawo kan masu zanga-zangar, da ma kawo sauƙi wa
al'umma. Da yawan waɗannan
shawari, wasu sun bayar a wajaje dabam dabam.
Kamar yadda na ambata a baya, daga cikin manufar da ta sanya
ni yin wannan rubutu, akwai ƙoƙari da fatan ganin an samu mafita a
halinda ake ciki. Kuma nayi imani cewa, waɗanda
abin ya shafa kai tsaye wato matasan da kuma talakawa masu fama da rayuwa ƴan
Najeriya, ya kamata su faɗi
abinda suke ganin zai taimaka a samu gyara. Duk waɗannan abubuwa na samu kaina a ciki, ni dai
matashi ne kuma ɗan
Najeriya. Na samu shiga cikin shirin N-Power a zango na uku kaso na biyu, wato
Batch C Stream II. An tura ni koyarwa a wata Makarantar Ƙaramar Sakandare a cikin
garin Bauchi, inda nakai takardar turo ni daga N-Power da sauran takardu wa
shugaban makaranta. Bayan tattaunawa da tantancewa, sun tambaye ni me zan iya
koyarwa, inda nace musu komai zan iya koyarwa har Arabic da Islamic Studies,
ba'a maganan Math da Comouter, domin takarduna sun nuna musu zan iya. Sai suka
bani Basic Technology wa yaran aji ɗaya.
Haka kuma na koyar tsawon shekarar karatun 2022/2023, kuma na tsawon zanguna
ukun. Ajujuwa guda huɗu
ne saboda yawan yaran, kuma ko wani aji akwai ɗalibai
sama da 70! Kenan, na koyar da yara kusan ɗari
uku (300), duk ƴan aji ɗayan
sakandare ko kuma 'Basic Seven'! Haka nayi wannan aiki cikin wahala da
sadaukarwa, da zimman taimakawa wajen yaye jahilci a makarantun da ƴan'uwanmu
ƴaƴan
talakawa suke zuwa. Duk wanda yasan makarantun gwamnati a jihar Bauchi dai,
yasan babu kayan koyarwa balle na koyo, haka malaman suke fama, kuma nima haka
naje nayi wannan fama. Abun sai wanda ya gani, 'very bad' ma yayi kaɗan ya siffanta lalacewar.
Daga cikin abubuwan wahala a wannan aikin shine makin na jarabawa, Amma shima
haka nayi su, koda yake nakan nemi taimakon wasu abokan aiki na a wani wajen
aikin dabam. Amma a wani karon ma, ko takardar da yake ɗauke da sunayen yaran na ko wani aji wanda
za'a shigar da jarabawar wato 'score sheet' babu, sai dai na rubuta sunan yaran
a fallen takardar 'fullscap' da abinda kowa ya samu na kai musu makaranta!
Banda wahalan da nasha wajen zuwa makarantar, musamman saboda banida abin hawa,
Achaɓa nake zuwa nake
dawowa, kai wataran ma da ƙafa nake takawa naje na dawo. Gashi wni lokacin ana tsananin
rana, domin makarantar rana ce, suna fara darasi ne shabiyu da rabi na rana,
12:30pm zuwa huɗu da
rabi na rana, 4:30pm. Amma a hakan, saida shugaban makarantar ya sanya mun
"baka miss", wato dai bana fashin zuwa, a ranakun da mukayi ƙa'idar
zanje, kuma a lokutan. Kai har samar da rubutaccen darussan da zamuyi a kowani
zangon karatu nayi, wato 'lesson note'. Ina nufin wanda kwamfuta ta rubuta,
kuma ni nayi rubutun a kwamfuta da kaina, kuma na buga shi ina amfani dashi
wajen shiga aji don koyarwa. Haka nayi tsawon zangunan karatu uku, amma abin
takaici, abin kaico, abin Allah wadai, abin baƙin ciki, Gwamnatin Tarayyar Najeriya bata
biya ni haƙƙin
da na chanchanta ba, na Naira Dubu Talatin N30,000 duk wata. Ko kuma ta bayar
wasu jami'anta suka handame, kuma aka bar su! Irin wannan abu da me yayi kama?
Ace ƙasar
ka ce ta cuceka a lokacin da kake buƙatar taimako, ta zalunceka, ta kashe duk
wani zimma da kake dashi na ganin ka taimaka wajen gyaruwan ƙasar
ka.
A irin wannan halin, duk wani kira da za'ayi wa matasa irina
da su fito su nuna wa gwamnati ɓacin
ransu da rashin amincewarsu da irin tsarin da ake gudanar da ƙasar
su akai, da irin yadda hakan yake barazana wa goben su, toh sai tsananin dace
ne zaisa bazan shiga ba. Amma duk cika-cikai da sharuɗɗan na shiga cikin irin wannan abu sun cika.
Ba kawai zanga-zanga ba, ko wasu laifuka ne irin na ta'addanci aka kira mutum
zai iya shiga, saboda neman mafita, kuma wasu irin waɗannan matasan sunada fikira da baiwa mai tarin
yawa, wanda ƙasar
su ko al'ummar bata damu dashi ba. Ba ni kaɗai
bane, akwai ire ire na da yawa, waɗanda
gwamnatin ƙasar
nan da ta jihohin su, suka musu zalunci da rashin adalci iri dabam dabam, kuma
suna ƙulle
da abin a ransu, kuma suna jin haushi da takaicin abun, kawai sun rasa yadda
zasuyi su bayyana wa gwamnati ne, kwatsam sai ga dama ta samu, WAYE ZAI IYA
HANASU? Suma bazasu iya hana kansu ba! Domin, sunce "hungry man is an
angry man", wato "duk mayunwaci, mafaɗaci
ne" ko kuma fusatacce ne, ai kusa yake da yin faɗa saboda fusata. Kuma da yawan waɗanda zasu fita wannan
zanga-zangar, a halinda suke ciki kenan. Gwamnatin taƙi ko ta gagara yin abinda
ya kamata. Ai kuwa kunga dole talakawan ƙasa su fito zanga-zanga. Koda yake, NI
bazan fita ba.
Toh meyasa ni bazan shiga wannan zanga-zangar ba? Kamar dai
yadda nayi take ga rubutun nan, wato MATSAYATA, dalili na uku na yin rubutun
shine bayyana matsayata don tayiwu, na samu wasu su yarda dani akan ƙin
fita ita wannan zanga-zangar. Hakanan, ina fatan kiran da zanyi, zai iya kaiwa
kunnuwan waɗanda
zasuyi gyara akai. Kamar yadda zantuka suka gabata daga masana dabam dabam akan
halaccin zanga-zanga a tsarin mulki irin na Dimokraɗiya, domin hatta shi kansa shugaba Tinubu,
wanda a halin da ake ciki shi yafi kowa cin moriyar Dimokraɗiya, yace ya taɓa shiga zanga-zanga a baya.
Wato shima tsohon ɗan
zanga-zanga ne. Sai dai fa, mu bamu bautan Dimokraɗiya. Munada Ubangiji wanda ya turo mana da
manzanni don su koya damu yadda zamu bauta maSa ta hanyar addini. Akan haka na
tattara bayanai da dalilaina na ƙin shiga zanga-zangar kamar haka;
1. Ni dai musulmi ne, kuma malaman musulunci sunce baya
halatta ayi fito-na-fito da shugaba, ta hanyar zanga-zanga. Kuma na yarda da
wannan koyarwa. Kuma ina ƙiran duk matasan masu wannan shiri daga cikin musulmai, da
suma subi wannan kira. Hakanan, suma kiristoci su bi wannan kira na barin fita
wannan zanga-zangar, musamman saboda CAN tace bata goyi baya ba, kamar yadda
jarida Daily Trust ta rana Lahadi ta ruwaito, cewar reshen CAN na jihar Neja,
tayi kira wa matasa da kar su fita. Don haka, mu saurari maganan manyan mu kuma
jagororin mu a addini, mu ƙaurace wa fita wannan zanga-zangar.
2. Duk zanga-zangar da muka san an taɓayi a baya, ko anan ƙasar ko a wata ƙasar,
yawanci bata haifar da ɗa
me ido ba! Musamman idan ta haɗu
da gwamnati irin na shugaba Tinubu, saboda zasu iya yin komai don tabbata a
mulki, kamar yadda sukayi don su hau mulkin. Yaushe muke tunani zasu bari a
musu adawa me tsanani irin zanga-zangar ƴan ƙasa wanda wahalan rayuwa ta sanya su
fito. Kuma duk munji irin gargaɗin
da akeyi akan cewar, ɓata
gari suna iya shiga cikin zanga-zangar don tayar da husuma, ɓarnata dukiyar al'umma, ko
sace-sacen kayan jama'a. A yanzun, akwai hasashen da jami'an tsaro sukayi a
Yobe cewar, ƴan
Boko Haram suna shirin shiga cikin ƴan zanga-zangar don kai hari wa jami'an
tsaro. Sun bayyana haka ne bayan harin da aka kai wani chaji ofis anan jihar
Yobe. Toh kunga babu wani buƙata ko alfano, mu bada ɓata gari mafaka domin suyi
aika-aika.
3. Da yawan matasan da zasu shiga wannan zanga-zangar, babu
umurnin iyayensu akai, bal, wasu ma iyayen nasu sun hanasu, amma sunyi kunnen
uwar shegu, sun rantse sai sun shiga. Toh duk abinda zamuyi, mu kula da haƙƙin
iyayenmu, domin saɓa
musu yana cire albarkan dake cikin aiki. Yana kuma janyo tasgaro ga aikin.
Saboda girman haƙƙin su. Don haka, yaku ƴan'uwana matasa, na rantse muku da Allah,
duk wanda ya haɗa
hanya da wanda yake cikin fushin iyayen sa, toh shima sai matsala ta sameshi.
Na tuna wani abu da ya faru dani da wani abokina, shekaru kusan goma yanzu.
Wata rana, wannan abokin nawa yace don Allah na raka shi gidansa da yake ginawa
acan wani unguwa mai nisa, saboda inada mashin sa'ilin nan, sai nace masa toh
badamuwa. Chan da yamma lis, sai na ɗaukeshi
muka tafi. Munyi dab da isa wajen, sai mashin tayi faci, cikin ikon Allah kuwa,
muka samu masu faci a kusa da wajen. Lokacin da muka iso wajen masu faci, tuni
magariba yayi. Sai muka bayar da facin mukaje yin Sallah, bayan dawowar mu, sai
me faci yace ai ƙusa muka taka kuma ya lalata tif ɗin, gaskiya a shawarin sa, sai dai mu chanja
tif, mukace babu damuwa, a ina za'a samu tif a daren nan, yace babu, amma
yanada tsoho mekyau, wato second, muka yi ciniki aka sanya tif. Koda nazo biyan
kuɗi, sai na rasa
lalitar ajiyan kuɗina,
wato wallet. Shi kuma daman bashida kuɗi
a sa'ilin. Mukayi jungum-jungum a gaban mutumi, sai kawai na tuna cewar, ta
yiwu na mantashi a gida ne. Sai nace bari naje na ɗauko. A lokacin babu yawan transfer, koda yake
ni inayi, amma da yawan mutane har masu shaguna, basuyi. Sunfi gane a basu kuɗi a hannu. Ga waje da nisa,
bama kusa da inda bankuna suke bane, toh ko kusa ne, ina katin cire kuɗin, shima yana cikin
lalitar. Haka dai nahau achaɓa
don ɗauko lalitar tawa
a gida. Koda na iso gida nabar me mashin yana jira na a ƙofar gida, ina zuwa ƙofar ɗakin, sai makullin yace ɗauke ni, ashe nabarshi a
jikin mashin domin suna tare ne da makullin mashin ɗin. Ai sai kawai na tsaya turus, na rasa
madafan kamawa. Sai na yanke shawarin na ranta na koma kawai, haka kuwa akayi,
na ranta na koma. Na biya mai achaɓa
da mai faci muka kamo hanyar dawowa gida batareda munje gidan ba, saboda dare
yayi domin har anyi sallar Isha'i. Muna tafiya a hanya, kawai sai abokin nawa
yake gayamun yadda sukayi da Dikko, wato mahaifiyar sa, kamar yadda suke
kiranta. Kawai nan take sai naga ashe ba a banza irin wannan ibtila'in ta same
mu ba, shi ya janyo mana. Kuma na sanar dashi hakan, domin shi baiyi tunanin
haka ba, aganinsa ma, abinda ya faru tsakaninsa da mahaifiyar sa ba komai bane.
Namai faɗa kuma nace
dole mu shiga ya bata haƙuri, haka kuma akayi, ko ba don komai ba, domin abin ya tsaya
a haka. Ya ƴan'uwana
matasa, kunji kaɗan
daga abinda ke iya zuwa ya dawo dalilin saɓawa
iyaye. Ahir ɗinku ku
fita zanga-zanga, alhali iyayen ku sun hanaku.
4. Zanga-zangar ba zatayi nasara ba saboda masu shirya ta da
masu goyon bayan ta, sunci naman bayin Allah. Zagin malamai babban laifine,
domin Allah da manzonsa ne sukayi umurni da a musu biyayya, a girmama su kuma a
mutun ta su, toh duk wanda yaƙi bin wannan umurnin, kuma ya wuce gona
da iri, har yaci namansu, ya zagesu, ya shiga hurumin su, toh wallahi ya shiga
uku. Domin malamai sunce ita namar malami gubace, duk wanda yaci toh zaiga
sakamakon aikin sa tun anan ba sai anje chan ba. Inada yaƙin in
cewa, wallahi duk wanda ya zagi malamai kuma ya fita wannan zanga-zangar, toh
bazaiga da kyau ba. Amma duk matashin da yake musun haka, toh ya jira ya gani.
Wata rana a masallacin unguwar mu inda nake sallah, bayan anyi sallar Magriba,
sai limami ya fara nasiha, daman baƙo ne, yana zuwa ne yin karatu a
masallacin duk sati. A bayanan sa sai yayi gargaɗi
akan kar wani matashi yace zai fita, domin babu amfani a cikin fitar, kuma
akwai yiwuwar a samu aukuwar fitina a dalilin zanga-zangar. Kawai sai wasu
marasa kunyan yara da sukayi sallah a wani zaure a bayan masallacin saboda
cikan waje kuma ga ruwa, sukace "AI SAI KAZO KA HANA MU" irin wannan
jara'a na waɗannan
yara yayi muni, saboda kawai sunajin cewa su marasa kunya ne. Da na kalli
yaran, nayi nazarin al'amarin daga baya, sai naga yara ne da basu jin maganan
iyayensu ma balle na wani. Amma kuma nasan cewar, tabbas zasu gamu da gamonsu,
muddin suka fita wannan zanga-zangar. Domin wallahi sai Allah Ya jarrabe su
akan wannan rashin kunyar da sukayi. Toh ba su kaɗai
ba, hakane zai faru ga duk wanda yayi makamancin wannan. Don haka, ina kiran
sauran masu hankali a cikin wannan zanga-zangar da su kiyaye haɗa hanya da waɗanda suke cikin fushin
Allah, domin duk abinda zai sami masu laifin, suma zai shafesu. Allah Ya sauwaƙe.
5. Shin ko mun tuna abinda ya faru a ƙasashen Larabawa bayan
zanga-zangar da sukayi wa shugabannin su? Mu ɗauki
misalin Libya, sunyi zanga-zanga kyautatuwar rayuwarsu, amma yanzu haka baya
sukaci, abinda suke samu da suka raina yasa suka fita zanga-zangar, sunbar
samu. Kuma daman waɗanda
suka shirya zanga-zangar daban, da manufar su, amma wasu suka shiga cikinsu da
nufin hamɓarar da
gwamnati, sunyi nasara, amma cigaba ce irin na mai tonon rijiya. Toh ya faru da
yawa irin haka, don haka mu kula.
6. Saboda duk al'amarin da yara suka farar dashi ana samun
matsala da tasgaro a cikinsa, saboda su yara suna da gaugawa a al'amura. Saɓanin manya, dattawa waɗanda suke da haƙuri da
bi a sannu, toh sukam, ba'a samun tasgaro a al'amuransu. Haka Assafady ya faɗa, kuma duk munsan hakane.
Wannan zanga-zangar ma yara ne suka shirya ta, kuma gaugawa ce ta ɗebe su, don haka nasarar
zanga-zangar take ƙasa take dabo.
Toh idan ba za'ayi zanga-zanga ba, me za'ayi, yaya za'a samu
biyan buƙatar?
Toh sai muce tazo gidan sauƙi, domin akwai hanyoyi da yawa za'a bi a samu mafita akan
wannan hali na ƙunci da ake ciki. Ga kaɗan
daga abinda nake ganin za'ayi a samu sauyi;
1. Mubi koyarwa da shiriyar malamai akan wannan abu, domin
su haska mana abinda Allah Yakeso kuma ya yarda dashi, su koyar damu yadda ya
kamata muyi yayin hali irin na ƙunci, rashin tabbas, jarrabawa kamar irin
wannan. Kuma sunyi bayanai masu yawa akan haka, sunyi ta koyarwa, don haka a
koma a saurara.
2. Shin mun tuna cewar wata guda ko biyu da suka wuce mun
shiga matsatsi a ƙasar nan, saboda rashin wutan lantarki? Wutan yayi tsada kuma
yayi ƙaranci
matuƙa
da gaske. Ta yanda mukam a unguwar mu, wutan da muke samu a lokacin bai wuce
awanni biyu ba a wuni! Har saida muka ce, hala bamuda wani tsari ne, wato
'band' kamar yadda suka rarraba masu shan wutan zuwa bands, Band A, Band B,
Band C, da sauran su. Toh mukam saida mukace bamuda wani band, saboda kason da
ake bamu yayi ƙaranci matuƙa. Ba irin wahalan da bamusha ba a
lokacin, saboda hatta chajin kwamfuta sai nakai wajen chajin kuɗi, gashi a lokacin ina
cikin tsananin buƙatar chajin saboda karatuka na a yanan gizo. Shin don Allah
matasan, zanga-zanga muka yi matsalar ta gyaru? Amma yanzu Yaya labarin wutan
lantarkin? A dai yankin da nake a Bauchi, mukan samu hasken wutan lantarki na
tsawon awanni ashirin mafi ƙaranci a kullum. Saɓanin
yadda muke samu kafin ma a samu wancan matsalar. Kafin wannan rashin wutan,
awanni bai kai goma ba muke samu a kwana guda, amma yanzu ninkin wannan muke
samu batareda wani zanga-zanga ba, muka samu wannan cigaban.
3. Kafin matsalar hasken wutan lantarki, ai mun shiga
matsalar kuɗi a hannu,
wato 'cash'. Haka kawai aka sanya mutane a damuwa, mutum da kuɗinsa bai isa ya cire ba
balle ya kashe, aka takura mutane matuƙar takurawa. Amma yau ina wannan wahalar
take? Itama zanga-zanga muka yi ta kawu? Ya kamata mu rinƙa tuna
irin haka. Akwai su da yawa. Shin mun tuna lokacin tashe-tashen hankulan Boko
Haram, da irin tsoro da firgici da muka shiga, zaman ɗar-ɗar
da jimami? Yaya akayi muka fita, zanga-zanga muka yi matsalar ta gyaru? Meyasa
muke ganin dole sai zanga-zanga ne zai gyara wannan? Muyi tunani mana, ya ƴan'uwana
matasa ƴan
Najeriya.
Amsoshin duk waɗancan
tambayoyin shine, ba zanga-zanga mukayi ba, haƙuri mukayi muka koma ga Allah, sai Allah
Ya taimake mu Yaji kukanmu Ya share mana hawaye Ya fitar damu daga waɗancan matsaloli. Toh a
wannan karon ma, Allah Yana nan, kar mu gajiya da yin haƙuri da fawwala maSa
al'amuran mu, tabbas Yana ganin bayinSa, Yasan halinda suke ciki.
RUFEWA
A ƙarshe, ina kira ga gwamnati da ta gyara salonta wajen kula da ƴan ƙasa da
magance damuwoyinsu. Tabar yaudara da alƙawuran ƙarya don ta samu abinda take so, ta sani
yaudara da ƙarya
basa tasiri na har abada. Misali, gwamnatin tarayya ta sanar da sayar da
shinkafa a Naira dubu arba'in (N40,000) buhu, kamar yadda ta taɓayi a baya na wani shinkafa
da akace Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ce take sayarwa, wato Custom. Amma
haka abun ya zama labarin ƙanzon kurege! Toh wannan ɗin
ma, akwai yiwuwar haka. Batun ware biliyan ɗari
da goma (N110 billion) don shirin bada rance wa matasa, wato shirin NYIF wanda
ministan matasa da wasanni ta sanar da ƙaddamarwa, duk gwamnati ta tabbatar ba
yaudara bane kamar na kyauta dubu hamsin da rancen miliyan guda. Domin a wajen ƴan ƙasa,
an daɗe ana ruwa ƙasa
tana shanyewa. Ina fatan wannan gargaɗi
zai shiga kunnuwar da ya kamata.
Sa'adu Zungur dai ya ce;
Mu dai burinmu faɗa
muku
Ko ku karɓa
ko ku yi dariya,
Dariyar ku tazam kuka gaba
Da nadamar maiƙin gaskiya.
Yusuf Abdullahi Umar
(yusufaumar97@gmail.com)
Bauchi, Najeriya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.