Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yaya Mace Za Ta Gane Tana Dauke Da Budurcinta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum kamar yadda akace mace tana iya rasa budurcinta ta hanyan, tsalle-tsalle, ɗaukan abu mai nauyi, hawa bishiya, hawa keke da sauransu. To ta yaya mace za ta gane tana ɗauke da budurcinta.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Bisa ga amsoshi da muka samu daga iyaye da yan'uwa mata Masu yawa, yasa muka fahimci abubuwa kamar haka

Shi Budurci wani tantanine da yake cikin farjin mace Yana nan kamar jijiya kuma wata abune kaman fata kuma baya da qwari yana nan cikin farjin mace ana ce masa BIKARA Wanda matuqar bawai shigarsa akaiba babu yadda za'ayi ya kauce daga hanyar da yake, Sai dai Masu mummunan aikinnan wato Lesbians to shi suna iya rasashi sakamakon wannan aikin.

Shine zamuga Idan anyiwa yara fyaɗe ko dai anshigi mace ta qarfi kokuma dai shigar farjin ba daidai ba ma'ana akarkace ko a tanqware kodai a zumudi ake fasashi ba daidaiba har hakan ya janyo zubar jini domin an buɗe hanyarsa ba akan yadda ya dace ba. Har hakan yakan rabawa mutanenmu lissafi wasu suce sai anga jini adaren farko ne sannan mace take tabbatar da budurcinta. Kuma ba daga nan take ba.

Shi budurci aranar da aka kai mace namiji ya shigi mace indai ahankali yabita zaiji daga farkon shigansa yatarar da qofar arufe. Wanda inme hankaline da sanin yakamata zai dinga zuwa yana dawowa ne ahankali har fatar dake wajen  tareda jijiyar nan Mara qwari sudinga laushi suna rauni ahankali har yasamu yacimma burinsa inda mace za ta danji zafi Amma Na rashin sabobe. Sai dai baza'a ga jinin nan ba, saɓanin wadda aka shigeta da garaje ko da gwajin qarfin tuwo. Kuma zakuga baza ta kasa tafiyaba, sakamakon anbita a yadda musulunci yayi umarni.

Amma budurci tun adaren an fasashi sai dai za ta dinga jin zafi har sai anyi yan kwanaki sannan za ta saba sakamakon qofar da aka buɗe sabuwa ta matancinta (ma'ana kasancewanta mace). Shiyasa Wasu suke samun wani magani mai suna LOVE RICAN (Ana ce masa yauki da Hausa) Suna amfani dashi dan rage zafi da kuma wahala. Shi wannan magani ana sanya shine a gaban mace a lokacin saduwa. Saboda shi maganin yanada yauki ta yanda Zai rage wahalar.

Dan haka Bazai yiyu mace ta rasa budutcinta kwata-kwata ba hassai in na miji ya sadu da ita.

Saidai akwai abinda zaisa gaban mace ya buɗe (sune kamar abinda muka faɗa a cikin tambayar). To amma itama baza ta zama kamar wanda aka sadu da itaba.

Sannan ko mace ta aikata ɗaya daga cikin abinda aka ambata ba lallaine ta buɗe ba. Tananan a cikin budurcinta matikar bata ga alamomi ba.

Akwai alamomin da mace za ta iya gane budurcinta ya ragu kafin miji ya kusanceta.

1. Alokacin da ta hau bishiya ko take tsalle-tsalle ko ta hau keke, za taga jini yana zuba bayan lokaci kaɗan.

2. Lokacinda al'adanta yazo za taga yana zuba da yawa, ba kaman yanda ya saba zuwaba.

3. Za taji raguwan Ni'ima (wato Sha'awa)

4. Idan mace ta buɗe kafafunta Za taji iska yana shiganta can ciki.

To wayannan Alamu suna iya bayyana ga wanda budurcinta ya ragu, wato ta buɗe. Amma bawai ya karu bane.

Wannan shine a takaice abinda muka fahimta daga amsoshi da yan'uwa suka bamu akan wannan tambaya.

Muna Addu'ah Allah ya saka wa kowa da Alkhairi ya kara ilimi da basira.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments