𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salam malam, Dan Allah mene ne hukuncin wannan auren? mutum ne sai yayi wata shida ko huɗu bai sadu da matarsa ba, kuma lafiyarsa kalau, kuma da chan ba Hakka yake ba sai da yayi sabon aure. naji Mutanen suna cewa ba aure a tsakanin mu har sai ya kuma bani sadaki, sannan innayi jini uku sannan zan zama matarsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salam Wa Rahmatullah:-
Kina nan a matsayin matar sa tunda bai yi niyyar
yi miki ILA'I ba. Amma in dai haka tana faruwa to ya zalunce ki. Domin ita
saduwar Aure hakki ne wanda dukkan ma'aurata suke da shi akan junan su. Kuma
duk wanda yaki ba ma ɗayan hakkin sa zai afka cikin laifi da kuma
fushin Ubangiji.
Hadisi Ingantacce Ya Tabbata Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam Yana Cewa
عن أبي هريرة رضي
الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم-: ”إذا دعا الرجل امرأته إلى
فراشه فأبت فبات غضبان عليها؛ لعنتها الملائكة حتى تصبح“
{مسلم: ١٤٣٦}
An Karɓo Daga Abi-Hurairah (RA) Ya ce: Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: “Idan Miji Ya Kira Matarsa Zuwa ga
Shinfidarsa Taqi Zuwa, Za ta Kwana Ana Fushi da Ita; Mala'iku Zasu Dinga tsine
Mata Har Gari ya Waye”. {Muslim: 1436}
Hadisin Ba iya kan Mata kaɗai ya tsaya, an fi jingina Hadisin akan Mata ne sabida, Mace ko
Sha'awar ta ya motsa ko Bai motsa ba Namiji na iya Jima'i da ita. Amma Namiji
dole ne sai Sha'awar sa ya tashi kafin zai iya yin Jima'i Amma Kuma Bai Hana
cewa idan Matar ka ta neme ka kaqi.
Ba daidai bane don mutum yayi sabon aure shikenan
sai ya rika wulakanta uwar gidan sa yana tauye mata hakkin ta Allah yana cewa:-
وَلَنْ تَسْتَطِيْعُوْۤا
اَنْ تَعْدِلُوْا بَيْنَ النِّسَاۤءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ فَلَا تَمِيْلُوْا كُلَّ الْمَيْلِ
فَتَذَرُوْهَا كَالْمُعَلَّقَةِۗوَاِنْ تُصْلِحُوْا وَتَتَّقُوْا فَاِنَّ اللّٰهَ كَانَ
غَفُوْرًا رَّحِيْمًا
Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ
dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata ga ɗaya daga cikinsu, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye... [Suratul
Nisa’i 4:129]
Kun ga anan Ubangiji ya fi mu sanin kan mu. shi
yasa yace ba za mu taɓa yin hakikanin adalci ba. ana nufin cikakken
adalci wajen soyayyar da ta ke zuciya, ko Kulawa wajen kwanciyar aure da sauran
su.
Toh amma Allah yace mana kar mu karkata wajen mace
guda. Domin kuwa a cikin hadisi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya
bamu labarin cewa masu aikata irin wannan za su tashi a ranar Alkiyamah suna
tafiya a karkace, gefen jikin su guda ya shanye.
Nisan wata hudu shi ne mafi nisan kwanakin da bai
kamata Namiji ya haura su ba tare da ya kusanci matar sa ba. Duk wanda ya haura
haka ba tare da wani dalili wanda shari'a ta yarda da shi ba, toh hakika ya
zama azzalumi. Shi kuwa Azzalumi ba shi da daraja a wajen Allah. Allah shi
kiyaye mu. Maza a ji tsoron Allah.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.