Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Yana Tuhumana Da Aikata Zina Saboda Bai Tarar Da Budurcina Ba A Saduwar Farko

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam barka  da war haka  da fatan Allah ya sada mu da alkhairi. Tambayata anan itace budurwa ce akayi mata aure sai ya kasance a saduwan ta nafarko da mijin bai jita kamar yanda ake bada labarin 'ya budurwa take ba sai  yace mata shifa yanda yake tunani bahaka yasamuba don  Allah ta faɗa masa gaskiya in ta taɓa yin zina kafin Auren su don shikam bai taɓa yi ba sai ta cemasa yanzu meza ta masa don ya yarda  cewa bata taɓa zina ba sai yace ta rantse masa da Alqurani kafin ya yarda shikennan sai tayi Alwala ta dau alqurani ta rike ta ce masa  wallahi tallahi narantse da Alquani ban taɓa zina ba inkuma na taɓa nayi qarya Allah yatozarta ta tayi masa irin wannan rantsuwar ya kai sau shida alokaci daban daban haka shima yayi mata irin  wannan rantsuwar Duk lokaci da tamasa. tambayar malam sune:-

1. inkarya take ya halasta ayi irin wannan rantsuwar don  kare mutunci?

2. In bai halastaba tozarta na iya afkawa Wanda yayi karya daga cikin su?

Kuma agarin da suke an yarda cewar duk wanda yayi irin wannan rantsuwar akan karya baya gamawa lafiya

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Da farko dai shi wannan mijin, tabbas ya zalunceta bisa wannan tuhumar da yake yi mata. Domin kowacce mace tana da irin halittar da Allah yayi mata. Ba dole ne idan anzo saduwar farko sai an tarar da murfin budurci ba. Sannan akwai dalilan dake janyo fashewar murfin budurci Misali kamar

1. Ɗaukar kaya mai nauyi.

2. Faɗuwa daga wani tsauni ko bishiya.

3. Wasu daga cikin wasannin motsa jiki.

4. Daɗewar shekaru kafin aure.

Za ta yiwu ita wannan matar ta haɗu da wani daga cikin dalilan nan.  Don haka ya zalunceta ta fuskar tuhumar da yayi mata, da kuma rantsuwar da ya sanyata tayi masa.

Shi Alqur'ani zancen Allah ne. Zance kuma yana daga cikin siffofin Allah. Kuma ya halasta mutum yayi rantsuwa da sunayen Allah ko siffofinsa Maɗaukaka.

Ɗaukar Alqur'ani ko rikeshi yayin yin rantsuwa, wannan ba sharaɗi bane game da sahihancin rantsuwar. Ko da baki mutum ya furta yace "NA RANTSE DA ALQUR'ANI" Shikenan rantsuwa ta afku. Kuma duk wanda yayi rantsuwar fajirci (wato rantsuwar Qarya) to hakika ya aikata kaba'ira. Wajibi ne ya tuba domin samun sauki awajen Allah. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya lissafa rantsuwar Qarya cewa tana kwashe albarkar rayuwa, kuma tana talauta mai yinta.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments