Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Ya Kamata Na Yi Sallar Qasaru?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum warahmatullah wa barakatuhu malam dan Allah ina tambaya ne akan kasaru, a ina yakamata ayita kuma waye ya kamata yayi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikumus salamam Warahmatalahi wabarkatahu

An shar’anta wa matafiyi yin qasarun sallloli masu raka’a huɗu (Azzahar, La’asar, Isha) zuwa raka’a biyu, haka kuma zai iya haɗa sallar azzahar da la’asar, magariba da isha, saboda faɗin Allah Maɗaukakin Sarki:

وَإِذَا ضَرَبْتُمْ فِي الْأَرْضِ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَقْصُرُوا مِنَ الصَّلَاةِ إِنْ خِفْتُمْ أَن يَفْتِنَكُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنَّ الْكَافِرِينَ كَانُوا لَكُمْ عَدُوًّا مُّبِينًا

Idan kuka yi tafiya a bayan qasa to babu laifi a kanku ku rage (qasaru) sallah, in kuna jin tsoron kada waɗanda suka kafirta su fitine ku, haqiqa kafirai maqiyanku ne masu bayyana qiyayya”. (Suratul Nisa’i aya ta 101).

Da abinda ya tabbata daga Anas dan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun fita tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) daga Madinah zuwa Makkah, ya kasance yana mana sallah raka’a bibiyu, har muka dawo” [Nasa’i ne ya rawaito shi].

Matafiyi zai fara qasaru da ya bar gidajen garinsu. Ba ya halatta ya yi qasaru a cikin gidan da yake zaune, saboda bai tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi qasaru ba har sai bayan ya fita (daga gari).

Idan matafiyi ya isa wani gari, kuma ya yi niyyar zama kwana huɗu ko sama da haka, to wajibi ne a kansa ya cika sallah.

In kuwa ya yi niyyar qasa da kwana huɗu to ya hallata ya yi qasaru, idan kuwa bai niyyar wasu kwanaki qididdigaggu ba, kawai dai yana da wata buqata ce, duk lokacin da ya qare ta zai koma, to wannan ya halatta ya yi ta qasaru har sai ya dawo, koda kuwa lokacin ya wuce kwana huɗu.

Wajibi matafiyi ya cika sallah idan ya yi sallah bayan liman mazaunin gida, koda kuwa raka’a ɗaya ya samu a tare da shi.

Idan mazaunin gida ya yi sallah bayan matafiyin da yake qasaru, to wajibi ne a kansa ya cika sallah bayan liman ya yi sallama

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

Kilometre Nawa Ne Sallar Qasaru Take Hawa Kan Mutum?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. Malam barka da warhaka. Dan  Allah malam inaso ayi min cikakken bayani akan sallar qasaru. Shin kilometre nawa ne ya kamata mutum idan zaiyi ya zama qasaru ya hau kanshi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Ana yin qasaru ne a tafiyar da takai tsawon Mil Arba’in da Takwas (48 Miles), matafiyi zai yi kasaru akan hanyarsa ta tafiya, ko tsawon kwanaki nawane kafin ya isa inda yake da nufin zuwa. Saidai idan matafiyin yana da niyar yin kwanaki Huɗu (4), ko fiye da haka, kimanin kwatan kwacin da zai yi Salloli 20. To, da zarar ya isa masaukinsa kasaru ta kare.

Amma indan tafiyar batakai kwana huɗu ba (Salloli 20), to, matafiyin zai iya cigaba da kasarun sa har ya dawo garinsa.

A cikin Mazhaba ta Imamu Malik, ana yin qasaru ne a tafiyar da takai tsawon Mil Arba’in da Takwas (48 Miles) kawai. Kuma matafiyi zai cigaba da kasarun sa matukar be yi niyar zama tsawon kwana huɗu (4) ba, Ko da kuwa ya wuce kwana huɗu, in dai tun alasi be yi kudirin yin kwana huɗun ba.

A misali mutum ne ya yi tafiya don wata bukatarsa, kuma ya kudiri cewa duk sanda ya samu abinda ya ke nema, to, washe gari zai dawo gida. To, irin wannan mutumin zai yi tayin kasaru har tsawon kwanakin da ya yi yana jiran biyan bukatarsa.

An samu wasu kalilan daga cikin magabatan da suke ganin cewa za’a iya yin qasaru a tafiyar da takai mil 3, matukar dai a al’adance al’umar tana ɗaukar irin wannan a matsayin tafiya. Sannan akwai wasu ‘yan kalilan da suke ganin cewa mutum zai iya yin qasaru tsawon kwana 10, ko 15 koma fiye. Amma fa wannan ra’ayi ne na ‘yan kalilan a cikin magabata, wanda ya saɓawa ra’ayin mafi yawan magabata. Kuma manyan malamai sun yi hani da ɗaukar irin wannan ra’ayin.

Allah she ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments