Hukuncin Kome Bayan Saki Uku A Dunkule A Kalma Ɗaya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Malam mutumne ya saki matarsa saki uku adunkule a kalma ɗaya ko arubutu ɗaya shin yanada ikon dawowa da ita?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    An yiwa SHEIKH ABDUL-AZIZ BN BAAZ RHMHLH irin wannan tambayar sai ya amsa da fuskoki 2:

    1. Jamhuran Malamai sun tafi akan cewa wanda yayiwa matarsa saki 3 adunkule alokaci guda ta saku dukka 3 bashi ba auranta sai tayi sahihin aure in mijin ya mutu ko yasaketa bayan ya kusanceta in yaso tsohon mijin yasake aurenta in yana bukata, sun kafa Hujja da Hadisin ABDLH IBN ABBAS R/A

    [ ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ : ‏] ﻛﺎﻥَ ﺍﻟﻄَّﻼﻕُ ﻋﻠﻰ ﻋَﻬْﺪِ ﺭَﺳﻮﻝِ ﺍﻟﻠﻪِ ﷺ، ﻭَﺃَﺑِﻲ ﺑَﻜْﺮٍ، ﻭَﺳَﻨَﺘَﻴْﻦِ ﻣِﻦ ﺧِﻼﻓَﺔِ ﻋُﻤَﺮَ، ﻃَﻼﻕُ ﺍﻟﺜَّﻼﺙِ ﻭﺍﺣِﺪَﺓً، ﻓَﻘﺎﻝَ ﻋُﻤَﺮُ ﺑﻦُ ﺍﻟﺨَﻄّﺎﺏِ : ﺇﻥَّ ﺍﻟﻨّﺎﺱَ ﻗَﺪِ ﺍﺳْﺘَﻌْﺠَﻠُﻮﺍ ﻓﻲ ﺃَﻣْﺮٍ ﻗﺪْ ﻛﺎﻧَﺖْ ﻟﻬﻢْ ﻓﻴﻪ ﺃَﻧﺎﺓٌ، ﻓﻠﻮْ ﺃَﻣْﻀَﻴْﻨﺎﻩُ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻓﺄﻣْﻀﺎﻩُ ﻋﻠﻴﻬﻢ .

    ﻣﺴﻠﻢ ‏( ٢٦١ ﻫـ ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ١٤٧٢ • ‏[ ﺻﺤﻴﺢ ]

    Wato ya kasance a zamanin ANNABI Sallallahu alaihi Wasallam da ABUBAKAR da shekaru 2 azamanin UMAR R/A- saki uku adunkule- saki ɗaya ne, daga baya UMAR yamaida ukun adunkulen uku ne yayinda yaga ana wasa da saki, (MSLM, SAHIH ABU DWD)

    Don haka sukace tunda karshen lamari UMAR ya maida saki 3 yasaku 3 kuma SAHABBAI R/A basuja dashiba to don haka ba dawowa.

    2. Wasu Ma'abota ilimi kuma sunce saki uku adunkule saki ɗaya ne, tunda haka yake a zamanin ANNABI Sallallahu alaihi Wasallam da ABUBAKAR R/A kamar yadda yazo a hadisinda muka kawo abaya, Kuma sun kafa hujja da Hadisin IMAM AHMAD daga IBN ABBAS

    [ ﻋﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ : ‏] ﺃﻥ ﺃﺑﺎ ﺭﻛﺎﻧﺔَ ﻃﻠَّﻖ ﺍﻣﺮﺃﺗَﻪ ﺛﻼﺛًﺎ ﻓﺮﺩَّﻫﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﻨﺒﻲُّ ﷺ ﻭﻗﺎﻝ : ﺇﻧﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺓٌ

    ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ‏( ١٤١٩ ﻫـ ‏) ، ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ٤٢٠/ ٢١ • ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ

    Wato ABU RUKANAH yasaki UMMU RUKANAH saki 3 adunkule sai ANNABI Sallallahu alaihi Wasallam yace ɗaya ne. Kuma suka kafa hujja da faɗin ALLAH a Suratu Baqara Aya ta 229:

    الطَّلَاقُ مَرَّتَانِ

    Saki marra biyune.

    Wato ɗaya bayan ɗaya ba dunkalasu alokaci ɗaya.

    Cikin waɗanda suka tafi akan hakan cikin SAHABBAI Akwai (IBN ABBAS, ALIY IBN TALIB, ABDURRAHMAN IBN AWF, ZUBAIR IBN AWWAM, IBN MAS'UD, cikin TABI'AI akwai MUHD IBN IS'HAQ da dandazon Maluma, a 'yan baya akwai IBN TAIMIYYAH da dalibinsa IBNUL QAYYIM,

    Kuma inji BN BAAZ- Wannan shine fatawata saki 3 adunkule 1 ne don aiki da nassosi da kuma rahama ga Musulmai, dubi- (ALFATAWA- KITABUD-DA'AWA na BN BAAZ)

    ◼IBN HAJR yace= gameda Hadisin ABU RUKANAH- nassine akan saki 3 adunkule saki 1 ne babu tawili, (FAT-HUL BAARY)

    ◼IBNUL QAYYIM yace= Wannan ANNABINE Sallallahu alaihi Wasallam da kansa da KHALIFANSA ABUBAKAR R/A da dukkan SAHABBAI tun daga zamaninsa zuwa zamanin ABUBAKAR zuwa shekaru 3 na zamanin UMAR suna kan saki 3 adunkule 1 ne, da mai irge zai irga SAHABBANDA ke ganin saki 3 adunkule ɗaya ne SAHABBAN sunfi dubu, (ZADUL MA'AD & IGATSATUL LAHFAN & KHASHIYAR BUKUGUL MARAM)

    ◼IBN ABBAS (TURJUMANUL QUR'AN) shima kansa afarkon lamari yana bada fatawar saki 3 adunkule saki ukune, daga baya yasauko daga wannan fatawar yajenyeta yadawo zuwaga Saki 3 adunkule saki ɗaya ne,

    NACE: A zamaninnan yafi dacewa murinjayarda fahimta na biyu, na saki 3 adunkule saki 1 ne domin ya sami asali tun daga ANNABI Sallallahu alaihi Wasallam kuma shine sauki akan nafarkon- kuma ALLAH Yace <<ALLAH yana sonku da saukine baya sonku da tsanani>> Kuma Yace <<ALLAH yanason yasassauta muku domin an halicci mutumne mai rauni>> kuma munada yawan mata da karancin maza da yawan fitintinun fasikanci da zinace zinace, yadace ayi aiki da wannan fatawar na ANNABI Sallallahu alaihi Wasallam don toshe ɓarna.

    Kuma ya dace muyi aiki da hukuncin UMAR IBN KHATDAB yayinda mukaga maslahar rabuwar, kamar mijin hana zaluntarta da duka ko yunwa ko shaye shaye ko rashin ibada- sai yayi mata saki 3 adunkule sai azartar masa ukun, tunda UMAR R/A ya zartarne don maslaha kuma yana daga cikin KHULAFA'UR RASHIDEEN da ANNABI Sallallahu alaihi Wasallam ya umurcemu mubisu, kuma ALLAH  Yace <<mazaje nada ikon mayarda matayensune in sunso maslahane>> ashe in babu maslaha bai halattaba koda sakin ɗaya ne ballantana 3 adunkule.

    WALLAHU A'ALAM.

    Amsawa :Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.