Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Magidancin Da Ya Yi Wa ’Yar Cikinsa Fyade

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, jiya na ga video clip na wani magidancin da ya yi wa ’yar cikinsa fyaɗe, a ƙarshe kuma da sai aka fara mayar da maganar wasan kwaikwayo, aka fara nuna wai wanda ake zargin yana da taɓin hankali! Wannan ba zai yi justifying (ya gaskata) abin da wasu shugabanni suka yanke na dandaƙe irin waɗannan mutanen da kashe su kawai ba?! Abin yana neman ya ƙazance fa!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Duk yadda al’amura suka lalace ko suka ƙazance, kamar yadda ka faɗa, mafita dai ƙwara ɗaya ce kawai: Komawa ga hanyar da Allaah Maƙagin Halittu ya tsara. Allaah Ta’aala ya ce

ظَهَرَ الْفَسَادُ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِي النَّاسِ لِيُذِيقَهُمْ بَعْضَ الَّذِي عَمِلُوا لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ ١٤۝

Ɓarna ta bayyana a tudu da teku saboda irin abin da hannuwan mutane suke aikatawa, domin ya ɗanɗana musu sashen abin da suka aikata, ko wataƙila su dawo kan hanya. (Surah Ar-Ruum: 41)

Wannan nuni ne a kan cewa

1. Ashe duk abin da ya yawaita a wannan zamanin na rashin albarkar rayuwa, da karayar tattalin arziki mai kai wa ga yawaitan talauci, da rashin tsaro da aminci da kwanciyar hankali, da yawaitan nau’ukan cututtuka masu kai wa ga yawaitan mace-mace da sauransu, duk tushensu abu ɗaya ne: Saɓon Allaah kawai.

2. Taurarewa da kangare wa dokokin Ubangiji Ta’aala ta hanyar Munafunci ko kafirci ko mushirikanci ko fasiƙanci ko zalunci da sauran laifuffuka makamantansu, su ne ummul-habaa’isin dukkan bala’o’i da masifun da ake fama da su a duniyar yau.

3. Hikima ko dalilin sauke wa al’umma irin waɗannan masifun da bala’o’in ba kamar yadda waɗansu suke tunani ba ne cewa: Wai domin sakamako ga laifuffukan da jama’a suke tafkawa ba ne, amma dai domin fatar al’umma su tuba daga laifuffukansu ne, kuma su dawo kan hanyar Allaah Ta’aala.

Don haka, duk wata hikima ko dabara da mutane za su tsara ko su bi don kauce wa aukuwar irin waɗannan bala’o’in da masifun a cikinsu ba zai haifar musu da mafita ko ya biya buƙata ba, in dai ba komawa suka yi ga hanya guda ɗaya ta Allaah Maɗaukakin Sarki ba. Duk muna ji da gani dai a yau yadda ƙwarar cutar covid-19 ta gagari manyan ƙasashen duniya!

Kyara ko ɗauri ko duka ko tara ko dandaƙa ko kisa da sauran hanyoyin da hukumomi suke tunanin bi duk ba hanyoyi ne na warware wannan matsalar nan ta fyaɗe ba. Kuma ko da shekaru dubunnai za a ɗauka ana kururuwar da yin amfani da ita, wannan ba zai taɓa biya buƙata ba. Domin gazawa ko zaƙewa a cikin hukunci ko dokar Ubangiji ba sa maganin matsala.

Hanya guda ɗaya tilo kuma ƙwara guda tak da za a bi don maganin matsalar ita ce abin da Shari’ar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta bayyana

1. Idan wanda aka kama da laifin ya zama baligi ne mai hankali da zaɓin ransa, wanda kuma bai taɓa yin aure ba sai kawai a tsayar da shi a gaban jama’a, a zuba masa buloli har guda ɗari cif-cif, ba tare da nuna wani tausayi gare shi ba. Sai kuma a kore shi daga garin na shekara guda.

2. Idan kuma mazinacin baligi ne mai hankali mai zaɓin rai wanda kuma ya taɓa yin aure ko da sau guda ne a rayuwarsa, to bayan bulolin sai a ƙara masa da wannan hukuncin: A tsayar da shi a gaban mutane, kuma a sanya su yi ta jifan sa da duwatsu har sai ya mutu.

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« خُذُوا عَنِّى ، خُذُوا عَنِّى ، قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلاً : الْبِكْرُ بِالْبِكْرِ جَلْدُ مِائَةٍ وَنَفْىُ سَنَةٍ ، وَالثَّيِّبُ بِالثَّيِّبِ جَلْدُ مِائَةٍ وَالرَّجْمُ »

Ku ɗauka daga gare ni! Ku ɗauka daga gare ni!! Haƙiƙa! Allaah ya sama musu mafita: Saurayi da budurwa: Bulala ɗari da ɗaurin shekara guda. Bazawari da bazawara kuma: Bulala ɗari da jefewa. (Sahih Muslim: 4509)

Wannan hadisi ƙarin bayani ne ga ayar Surah An-Nisaa’i

وَاللَّاتِي يَأْتِينَ الْفَاحِشَةَ مِنْ نِسَائِكُمْ فَاسْتَشْهِدُوا عَلَيْهِنَّ أَرْبَعَةً مِنْكُمْ ۖ فَإِنْ شَهِدُوا فَأَمْسِكُوهُنَّ فِي الْبُيُوتِ حَتَّىٰ يَتَوَفَّاهُنَّ الْمَوْتُ أَوْ يَجْعَلَ اللَّهُ لَهُنَّ سَبِيلًا

Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nemi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su. (Suratul Nisá'i : 15)

Wannan hadisi ya ƙunshi hukuncin da Shari’ar musulunci ta kafu a kansa kenan, dangane da mazinata: Ko dai bulala ɗari tare da jefewa ga wanda ya taɓa yin aure, ko kuma bulala ɗari tare da ɗaurin shekara guda ga wanda bai taɓa yin aure ba.

Daraja da martaba da ɗaukaka ga kowane musulmi ita ce: Yin biyayya da jayuwa kawai ga wannan dokar, sannan kuma da zartar da ita a kan duk wanda ya saɓa mata, a lokacin da ya samu iko da dama a matsayinsa na shugaban ƙasa ko shugaban jiha, ba tare da yi mata kwaskwarima ko gyaran fuska ba.

A nan babu bambanci ko mazinacin namiji ne ko mace ce ko kuma mata-maza ne. Haka ko ya yi zinar da baligi ne ko da wanda bai balaga ba ne. Sannan kuma ko da son ran abokin yinsa ne ko ba da son ransa ba ne (kamar ta hanyar fyaɗe), duk hukuncin dai ɗaya ne.

Abin lura dai kawai shi ne: Ana zartar da wannan hukunci ne idan dukkan sharuɗɗa sun cika kuma dukkan abubuwan da suke hana aukar da hukuncin a kan wanda ake zargi da laifin sun kau. Don haka ake buƙatar matuƙar yin taka-tsantsan da zurfafa bincike daga alƙali kafin zartarwa.

Tsai da wannan hukuncin daga alƙalin kotun musulunci a kan musulmin da aka bincika kuma aka tabbatar da ya aikata wannan laifin shi ne daidai kuma kyakkyawar hanyar samun ingantacciyar al’umma ce a duniya.

Amma saɓa wa wannan ta hanyar yanke masa hukuncin da ya gaza hakan, kamar tara ko ɗauri kawai, wannan ba zai gyara al’umma ba kuma ba zai hana cigaba da aikata laifin ba, kamar yadda ake ji da gani a ciki da wajen al’ummomin wannan zamanin.

Haka ma zaƙewa ko wuce-iyaka wurin yanke hukunci ga mai wannan laifin, kamar ta hanyar tsire shi, ko dandaƙe shi, ko cire mata mahaifa. Wannan duk ba zai gyara al’umma ya sa su daina aikata laifin ba, kamar yadda ake ji da gani a kan wasu dokokin makamantan wannan.

Harbe mutanen da ake zargi da fashi ko ta’addanci don kawai an same su da makamai, ko da kuwa ba a tabbatar da cewa sun taɓa tsare hanya ko sun taɓa kashe kowa ba, wannan zalunci ne. Ballantana kuma yafe wa mutanen da binciken kotu ya tabbatar da cewa sun mallaki muggan makamai kuma sun yi amfani da su wurin hallakawa da tarwatsa al’ummar da ba su taka musu ko sun zubar ba!

Wanda yake ta ƙoƙarin cusa lomar tuwo ta cikin hancinsa, da wanda ke faman ɗura ruwan rijiya a cikin man motarsa, sannan da wanda ya zauna yake ta nacin tura katin GLO a cikin layinsa na MTN misali, duk mun san wahalar banza kawai suke yi, kuma ba za su taɓa cin nasara ba. Kamar haka, duk mutanen da suka kama bin waɗansu abubuwa, suka kauce daga bin dokoki da tsarin da Ubangiji Ta’aala ya saukar musu: Wahalar banza kawai suke yi, kuma ba za su taɓa samun cin nasara ba.

Allaah ya ƙara fahimtar da shugabanninmu, su gane gaskiyar addini kuma su iya kafewa a kan yin aiki da shi. Allaah ya fahimtar da mu, ya ƙara shiryar da mu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments