Ticker

6/recent/ticker-posts

Hadisan Manzon Allah Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata a Gare Shi

Haɗannan waɗansu ne daga cikin hadisan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Allah ya ba mu damar amfani da su da duk sauran ingantattun hadisai, amin.

Ana iya turo mana tsokaci ko gyara cikin ɓangaren comment da ke ƙasa.

Fatar mutuwa!🥀

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Kada ka yi fatar mutuwa, domin idan kai mai kyautatawa ne, to samun damar ƙara kyautatawa a kan kyautatawarka ne ya fi." (Sahihut Tagrib: 3368)

Hadisai

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Amma game da fitinar ƙabari, a dalilina ne fa za a muku jarabawa, kuma game da ni ne za a tambaye ku." (Sahibul Jamiis Sagir: 1361)
Hadisai
Barka da Juma'a🕌🕋
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mutanen da za su saura a ƙarshen duniya su ne waɗanda babu alheri a gare su. Za su koma ga addinin gargajiya." (Sahihu Muslim: 2907)
Hadisai

Juma@t Mubarak💐🌷
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Sa'a (ta ƙarshen dunya) ta matso, sai dai kuma su mutane hakan ba ya ƙara musu komai face nisanta (daga Allah)." (Sahihul Jami'i: 1146)

Hadisai

Juma@t Mubarak💐🌷
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Sa'ar ƙarshen duniya ba za ta tsaya ba sai alfasha ta yi yawa har ana alfahari da ita, sai an yanke zumunci, sai maƙwabtaka ta munana." (Takhrijul Musnad: 6872)
Hadisai
Juma@t Mubarak💐🌷
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Daga alamomin matsowar sa'ar ƙarshen duniya, za a yawaita maganganu masu kyau sai dai kuma za a rage kyawawan ayyuka." (Silsilatus Sahiha: 6/774)
Hadisai
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, fasiƙi zai samu ikon faɗar magana ta shugabancin al'umma." (Sahihu Dala'ilin Nubuwwa: 388)
Hadisai
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, sakarai zai samu ikon faɗar magana ta shugabancin al'umma." (Takhrijul Musnad: 7912)
Hadisai
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, mutumin banza zai samu ikon faɗar magana ta shugabancin al'umma." (Silsilatus Sahiha: 2253)
Hadisai
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, mutumun banza zai samu ikon faɗar magana ta shugabancin al'umma. (Silsilatus Sahiha: 2253)
Hadisai
Mu faɗaka...
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, akwai kwanakin da hajilci zai sauko, za a ɗauke ilimi (na addini), kuma kisa zai yawaita." (Al-Bukhari: 7062)
Hadisai
Mu faɗaka...
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, za a ɗauki maha'inci shi ne mai amana, a ɗauki mai amana shi ne maha'inci." (Sahihu Ibn Majah: 3277)
Hadisai
Mu faɗaka...
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Daga alamomin sa'a (ƙarshen duniya) za a ɗauke ilimi (na addini), jahilci zai tabbata, za a sha giya, kuma zina za ta yawaita." (Al-Bukhari: 80)
Hadisai

Mu faɗaka... 
Manzon Allah (SAW) ya ce: "A kusa da sa'ar ƙarshen duniya, akwai waɗansu shekaru masu yaudara. Za a gaskata maƙaryaci kuma a ƙaryata mai gaskiya." (Silsilatus Sahiha: 2253)
Hadisai

Post a Comment

0 Comments