Ticker

6/recent/ticker-posts

Fassarar Mafarkin Shugabanni

TAMBAYA (127)

Assalamualaikum .Mutun ne ya ke ta mafarki da shuwagabin Nigeria,tun daga alhaji shehu shagari har zuwa Bola Ahmed Tinubu cewa gashi ya zauna tare da kowane dayan su alokacin shi cikin walwala da anashuwa.Gafarta malam meke fasarar wannan mafarki ?

✍️AMSA A TAQAICE

(Mafarkin shugabanni yana nuna nasara da kuma albishir na alkhairi)

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

Alhamdulillah

To dan uwa, mafarkin ganin, shugabanni, dattawa, manya, masu fada aji, masu tunani, malamai dukkan fassarar wadannan yana nuna nasara da kuma albishir na alkhairi kamar yanda Tabi'i Muhammad Ibn Seerin (Rahimahullah) yayi bayani a cikin littafinsa na "Qamus din fassarar mafarki"

SHARHI

Sanin kanmu ne cewar shi mulki siffar Allah ne. Yana bada mulki ga wanda Ya so kuma a lokacin da Ya so. Shine ya bawa Fir'auna mulkin Misra (Egypt) don ya jarraba shi kamar yanda ya bawa Annabi Sulaiman (Alaihis Salam) mulkin duniya don ya jarrabashi. Na farko ya samu damar mulkar gari guda daya tak saidai bai tafiyar da mulkin yanda Allah yake so ba, shi kuma na biyu ya samu damar mulkar duniya gaba daya amman hakan bai rude shi ba, yayi mulkin adalci yanda Allah Yake so

Kenan mafarkin shugabanni mabanbanta kuma an zauna dasu zaman walwala da annashuwa yanada alaqa da wanda yayi mafarkin

Masu zagin shugabanni basa irin wannan mafarkin la'akari da kullum suna kwantawa ne da bakin cikin shugabancin da ake musu sabanin shi kuma wanda yake addu'a gare su da nema musu yafiyar mahaliccinsu kullum kokari yake ya ga an yada alkhairinsu komai kankantarsa da kuma boye sharrinsu komai girmansa

Haquri akan halayen shugabannin da kuma tawakkali ga Allah akan zama a Nigeria ba komai bane face jarabawa daga Allah wannan dabi'a ce da take bayyana musamman ga dattawa nagari

Don haka wanda yake irin wadannan mafarkan sai ya ci gaba da riqo da addininsa da koyi da sunnar wanda yazo da addinin da kuma ci gaba da yin addu'a ga shugabanninsa don samun kubuta daga halin da mutane suka tsinci kansu na zagi da aibanta shugabanni

Ya Allah ka shirya mu ka rabamu da fasiqanci (zagin musulmi) domin kuwa daga cikinmu ai ake samun shugabannin

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments