Ticker

6/recent/ticker-posts

Fassarar Mafarkin Hanya

TAMBAYA (131)

Malam dan Allah nayi mafarki naganni awani guri ankawo ni a mashin bakowa agurin sai wasu masu kanyan kaki sai suka nunamin wata hanya doguwa bakowa sai sukace nabita sai nace barina jira en uwana sai na zauna muna magana da daya daga cikinsu har nabashi abu yanaci dan Allah afassara min

✍️AMSA A TAQAICE

(Wannan hanyar da suka nuna miki itace addininki wato Islam. Yan uwan da kika ce zaki jira zuwan su sune yan uwa musulmai masu kwadayin bin hanyar Allah Azzawajallah

Wanda kuke fira dashi dinnan kuma shine aikin da kike a duniya. Abinda kika bashi ya ci dinnan kuma shine halinki

Wannan abin hawan kuma mutuwa ce (wanda kowa zai hau kai). Wannan kuma yanada alaqa da yawan tunanin mutuwa da kike yi a ko da yaushe)

Bismillahir Rahmaanir Raheem

A cikin littafinsa, mai suna "Qamus din Fassarar Mafarki", Imam Muhammad Ibn Seerin (Rahimahullah) yace

"Ganin hanya a mafarki yana nufin shari'a ko kuma hanyar Allah. Ganin hanyoyi da yawa kuma na nufin bidi'ah da kaucewa daga hanyar Allah

Miqaqqiyar hanya a mafarki na nufin hanyar Allah, ko kuma imanin mutum akan addinin Allah ko kuma bin Sunnar ManzonSa (Sallallahu alaihi wasallam) ko kuma bin tafarkin malamin mutum. Tafiya akan miqaqqiyar hanya na nufin tuba daga zunubbai da neman hanyar Allah. Ganin hanyoyi dayawa na nufin gaggawa, raguwar imanin mutum, kokwanto, gafala ko kuma ridda

Hanya a mafarki na nufin: qarfi, dawwama, rayuwar da ta wuce, shekaru, ci gaba, misali mai kyau ko misali mara kyau. Boyayyiyar hanya a mafarki na nufin fariya, bidi'a da kuma zaluntar kai"

SHARHI

Wannan hanyar da suka nuna miki itace addininki wato Islam. Yan uwan da kika ce zaki jira zuwan su sune yan uwa musulmai masu kwadayin bin hanyar Allah Azzawajallah

Wanda kuke fira dashi dinnan kuma shine aikin da kike a duniya. Abinda kika bashi ya ci dinnan kuma shine halinki

Wannan abin hawan kuma mutuwa ce (wanda kowa zai hau kai). Wannan kuma yanada alaqa da yawan tunanin mutuwa da kike yi a ko da yaushe

An karbo daga Abdullahi Ibn Mas'ud (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya zanawa sahabbai miqaqqen layi da hannunsa akan yashi. Sai ya cewa sahabbai wannan miqaqqen layin shine hanyar Allah

Sannan kuma sai ya sake zana wasu layukan daban a gefe da gefen wancan miqaqqen layin. Yace: "Wadannan qananan hanyoyin a kowannensu da akwai wani shaidani mai kira don a kaucewa bin hanyar Allah". Sai ya karanta ayar nan da Allah yace

( وَأَنَّ هَٰذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ ۖ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَن سَبِيلِهِ ۚ ذَٰلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ )

الأنعام (153) Al-An'aam

"Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa"

(Musnad Ahmad 4437 | Al-Arna'ut yace Sahihin Hadisi ne)

Kenan kinga sai ki kara dagewa da bin tafarkin Musulunci da koyi da Sunnah, ki guji yan Bidi'ah da Bidi'ar su. Kada ki rabu da Ahlus Sunna wal Jama'ah sune kuma ake kiransu da ahlul-hadeeth, ahlul-ittibaa', al-firqatun najiya, ahlul-aathaar, at-taa`ifatul-mansoorah

Yake yar uwa, ki damqe igiyar Allah. Kada ki manta da fadin Allah (Subhanahu wata'ala)

وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا ۚ

آل عمران (103) Aal-Imran

"Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba"

Wannan mafarkin na alkhairi ne wanda ake kiransa da ru'ya

Idan kina da miji ki dinga biyayya ga umarninsa matuqar bai sabawa shari'ah ba idan kuma ba ki da aure to ki samu miji nagari wanda yayanki zasuyi alfahari dashi

Ina miki fatan alkhairi fid dunya wal akhira

Wallahu ta'ala a'alam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments