Ticker

6/recent/ticker-posts

Barkanci Daga Taskar www.amsoshi.com Kashi na Dari Biyu Da Sittin Da Hudu

Waɗannan jerin labaran barkwanci ne daga taskar www.amsoshi.com. Kuna iya turo mana waɗansu labaran barkwanci a sashen comment da ke ƙasa.
Mun gode.
Yanzu fa cin kaza🐦 daga amarya sai ɗan kaciya.
Barkanci
Ba za ka san ana zafi ba, sai ka leƙa window da tsakar dare ka ga aljanu ba riga suna ta faman fifita.🌚
Barkanci
Jokes...
A man who treats his wife nicely deserves another woman. 🤪
Barkanci
Barkwanci...
Duk soyayyar da mai mata yake miki, da zarar kin turo masa hoto, kallo ɗaya yake yi ya goge. 🏃‍♂️🏃‍♂️
Barkanci
Barkwanci...
Yaushe rabon da ka ji an ce mace allurar cikin ruwa ce?? 😀
Barkanci
Barkwanci...

Wani ya auri wata 'yar Sakkwato, 'yar shekara 17. Ya dawo gida shan ruwa aka ce ta bi 'yan tashe.

Barkanci
Barkwanci...

Matan Zamfara ko kai maraya ne sai sun tambaye ka kuɗi. 🤭🤭
Barkanci
Barkwanci...
Sojoji masu dutin dare🦟🦟
Sojoji masu dutin rana🪰🪰
Barkanci
Barkwanci...

Yau an ce ni zan dafa abinci a gidanmu. Shin wai da wane irin sabulu ake wanke shinkafa?
Barkanci
Barkwanci...

Mijinta ya kalle ta ya yi murmushi, ya ce: "Su Zainab an ci kuɗin cefane an yi ɓulɓul."
Wace amsa za ki bayar?
Barkanci
Barkwanci...
Shawara ga mata:
Duk wadda ba ta samu kuɗin salon ba, to ta wanke kanta da karkashi. Ga santsi ga sheƙi.🌿
Barkanci
Barkwanci...
Mata mutanenmu! Sai ka ga mace ta je tana ta kashe wa ƙafarta kuɗi a kan wanda yake wanka da Omo.🧑‍🦯

Barkanci
Jokes... 
Two ladies on a bus were engaged in a heated dispute over the last seat when the bus driver intervened with wisdom. He shouted: “Let the ugly one take the seat.” Both the ladies stood for the rest of the journey! Argument solved!
Barkanci
Barkwanci...
Babu irin masu kai mutum Hajji ko Umara ne, idan ya dawo ya riƙa biya da kaɗan-kaɗan? 🤷‍♂️🥳
Barkanci
Barkwanci...
Idan aka lura, ayyukan gida na yi wa mace yawa. Duk namiji mai tausayi zai yi ƙoƙarin samo wa matarsa abokiyar zama 🧕🧕domin tausayawa. 👨‍🦯

Barkanci
Barkwanci...
Abin alfahari ne a gare ki 'yan mata su nuna suna son auren mijinki. Hakan na nuni da cewa kin auri mijin ƙwarai. 👳‍♂️
Barkanci
Barkwanci... 
Ni fa babu abin da yake ɓata min rai in na shiga jirgi irin 'tsayawa shan mai' 🙈🙊😷
Barkanci
Barkwanci...
Mene ne ya fi ɓata muku rai dangane da shiga jirgin sama? ✈️Ni dai abin da na fi tsana shi ne, idan ya kafe a ce mu fito mu tura. 😒
Barkanci
Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, ko dai gulmar 'ya mace ta 'ya mace ce??
Barkanci

Post a Comment

0 Comments