Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2023) ““Taubasantakar Narambaɗa da ‘Ya’yan Sarakuna” Proceedings of International Conference on Ibrahim Narambaɗa Tubali, Center for Research in Nigerian Languages, Translation and Folklore, Bayero University, Kano Pages 55–61 ISBN: 978-978-2111-47-3
Taubasantakar
Narambaɗa Da ’Ya’yan Sarakuna
Daga
Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
ibrasskg@gmail.com
Shashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
1.0 Gabatarwa
Wasannin barkwanci da ake samu
tsakanin Hausawa da wasu ƙabilu ko tsakanin su da juna ta la’akari da wasu ‘yan
bambance-bambance na matsayi ko yanayin dangantaka, ta samar da wata kafa ta
annashuwa. Wannan ya sa za a ga dattijo da yaro suna ba’a gwanin ban sha’awa.
Za a ga masu mabanbantan sana’o’i suna raha da zumunci na ba’a a tsakanin su.
Wannan yanayi yakan haifar da zumunci da ɗebe kewa da annashuwa a
zukatan mutane. Haƙiƙa wannan wasa na barkwanci ya samar da wata dama ta
cike tazarar da ke tsakani mutanen da yanayin rayuwarsu ta nesanta da juna matuƙa. Nazarce-nazarcen da
masana suka yi a kan wannan al’adar sun bayar da haske a kan hakan. To sai dai
wani abin da aka lura da shi a wannan fage shi ne giɓin da manazarta suka
bari na duban irin hulɗar da ta wanzu tsakanin wasu
rukunin jama’a da makaɗan Hausa wanda ya buɗe
wani sabon shafi na wasannin barkwanci. Kamar yadda reni da ba’a ke wanzuwa a
tsakanin sassan mutane daban-daban a cikin al’umar Hausawa, haka abin yake
wanzuwa a tsakanin rukunin wasu makaɗan Hausa da wasu mutane
na musamman waɗanda suke da dangantaka da waƙar da suke yi.
Ƙudurin wannan maƙala shi ne ta dubi irin
wannan wasa na barkwanci da ke tsakanin wani aji na makaɗan
Hausa da wani rukuni na jama’a. Wato tsakanin Makaɗan sarakuna da ‘ya’yan
sarakuna. Ayyukan da suka gabata musamman na nazarin waƙoƙin sarakuna sun taƙaita ne a kan duban
zambo da habaici a fasulan jigo ko turaku. Tunanin wannan nazari shi ne, lokaci
ya yi da za a sauya alƙiblar daga kallon salo da jigo zuwa danganta ainihin
lafuzzan waƙoƙin da abin da al’ada ta tanada kamar wasannin
barkwanci. Wannan nazari ya ɗauki rigar barkwanci da
ke tsakanin taubasai ya zura a wuyan makaɗan Hausa ta la’akari da
irin ba’a da suke yi wa ‘ya’yan sarakuna kuma ba yadda suka iya da su kamar dai
yadda abin yake tsakanin taubasai. Nazarin ya yi amfani ne da Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa a matsayin zakaran auna wannan
tunani na kallon raha da take wanzuwa a tsakanin makaɗa
da ‘ya’yan sarakuna. Wannan tunani na amfani da Narambaɗa
ya tuzgo ne bisa la’akari da matsayin da ya taka a wannnan aji na makaɗan
sarakuna da kuma kyakkyawar dangantaka ta raha da ta ƙullu a cikin waƙoƙinsa, tsakaninsa da
‘ya’yan sarakuna.
1.1 Taubasantaka
A Ƙamusun Hausa (2006, sh.433)
an bayar da ma’anar Taubastaka da “dangantakar ɗan mace da ɗan
namiji ko ‘yar mace da ɗan namiji.” Akan kira wanda ko
wadda aka haɗa wannan dangantaka da shi ko da
ita taubashi (namiji) ko taubashiya (mace). Wannan dangantaka a al’adar Hausawa
an yi mata tanadin wasan barkwanci na musamman. Barkwancin da Hausawa suke yi a
sakamakon wannan dangantaka yana da ƙarfi matuƙa domin dangantaka ta
jini ta haifar da ita. Don haka, ba yadda mutun zai yi idan yana ganin ya cutu
a sakamakon wannan wasa illa ya yi haƙuri domin ba zai iya
kankare ko rushe dangantakar ba. Tukur (1999) ya nuna cewa, duk inda taubasai
suka haɗu, suna takalar juna da ‘yan
zantuttukan barkwanci na ban dariya da gori. Haka kuma duk yadda wasan ya yi
zafi, ba ya haifar da faɗa a tsakanin su illa ma
ya ƙara
musu dankon zumunci. A ƙunshiyar wannan wasa, ɗan namiji yakan kalli ɗan
mace a matsayin bawa ta la’akari da cewa, ba ya iya gadon gidan da uwarsa ta
fito kasancewar mace ta haife shi. Wasa tsakanin taubasai wasa ne mai ban
sha’awa da ake yi musamman idan mutanen da suka haɗa alaƙar suka iya bakinsu.
Sukan shammaci kan su ta kiran juna da sunayen ban dariya ko ma su yi wa juna ƙazafin wani mummunar
abin da ba a aikata ba.
1.2 ’Ya’yan Sarki
‘Ya’yan sarki ga Bahaushe yana
dubuwa ta fukoki guda biyu. Yana iya kasancewa ‘ya’yan sarkin da ake magana a
kan sa. Wato ‘ya’yan da ya haifa. A ɗaya ɓangaren
kuma musamman idan an yi la’akari da abin da makaɗan baka na Hausa suke
nufi a cikin waƙoƙinsu, to yana nufin duk wani jinin sarauta ko kuma
wanda ya gaji sarautar kuma zai iya zama sarki. Makaɗan fada na Hausa suka
yawaita ambaton ‘yan sarki ko ɗan sarki ko ‘ya’yan sarki a cikin waƙoƙinsu bisa dalilai da
yawa. Sukan mayar da hankali gare su idan suna yaba sarki sai su rinƙa kushe su ta hanyar yi
musu zambo ko habaici. Mawaƙan fada ba su cika mayar da hankali a kan mata daga
cikin ‘ya’yan sarki ba. An fi lura da abin da mazan suke yi na burgewa ko na
kasawa wanda shi kan zama wani jigo a waƙa ta fuskar yabo ko
kushewa. Komai girma ko matsayi ko muƙamin mutum a al’uma,
makaɗan Hausa ɗan sarki suke kiran sa
in dai ya gaji sarautar.
2.0 Narambaɗa a
Matsayin Taubashin ’Ya’yan Sarakuna
Makaɗa Ibrahim Narambaɗa
ya yi ƙoƙarin gina dangantaka
tsakanin sa da ’ya’yan sarakunan da yake yi wa waƙa kamar dai yadda abin
yake tsakanin taubasai. Ya sami cin nasarar sa wannan riga na alaƙa ne ta amfani da
fasahar da Allah ya ba shi na iya cusa barkwanci a cikin waƙoƙin nasa. Zai iya yuwuwa
ya kasa aiwatar da irin wannan wasa in cikin waƙa, sai Narambaɗa
ya mayar da alaƙar kamar yadda take a tsakanin taubasai. Shammatar da
yake yi wa ‘ya’yan sarakuna da kuma muzanta su da yake yi, yakan sa raha da
annashuwa a zukatan mutane masu sauraro, ya kuma ƙara danƙon zumunci tsakaninsa da
waɗanda yake yi wa barkwacin. Ire-iren waɗannan
wasannin ba’a a waƙoƙin Narambaɗa ƙage ne kawai. Yakan
bayar da siffofin mutanen da yake muzantawa ta yadda masu sauraro za su iya
gane wanda yake yi da shi kai tsaye. Su kuma ‘ya’yan sarakuna a ɗaya
ɓangaren dole su bi shi da lalama ta hamyar yin ba’a da
shi da ma ‘yan kyaututtuka domin su fanshi kansu tamkar dai yadda irin wannan
hulɗa ke shiga tsanin taubasai.
2.1 Nau’o’in Taubasantakar Narambaɗa da
’Ya’yan Sarakuna
A wannan fasalin, an dubi tarin
misalan waɗannan wasanni na barkwanci da
Narambaɗa ya yi ta furtawa ga ‘ya’yan
sarakuna ta hanyar karkasa su a rukunoni daban-daban ta la’akari da abin da
kowane rukuni ya ƙunsa.
2.1.1 Danganta ’Ya’yan Sarki da Munanan Ɗabi’u
Munanan ɗabi’u a wurin Bahaushe
su ne ɗabi’un da al’ada ba ta aminta da su ba. Duk wanda ya
aiwatar da su to ya zubar da mutuncisa a idon jama’a. Akan yi masa kallon
mutumin da ya rasa wata daraja ko kima da ya kamata a ce yana da su. Ire-iren
waɗannan munanan ɗabi’un a wurin Hausawa
sun haɗa da ƙarya da rowa da sata da zina da
gulma da ƙeta da rashin kunya da dai sauran su. Narambaɗa
a cikin waƙoƙin da ya yi wa wasu sarakuna, yakan fito da waɗannan
wasannin na barƙwanci ta hanyar nuna cewa, wasu ‘ya’yan sarakuna sun ɗabi’antu
da waɗannan halaye. Yana yin haka ne domin ya ƙara fito da kimar sarkin
da yake yi wa waƙa, a ɗaya ɓangaren
kuma ya munana abokan hamayyar sarki waɗanda su ne ‘ya’yan
sarakunan. Narambaɗa yana yin wannan cushe ne ga
taubasan nasa cikin raha ta yadda mai sauraro zai fahimci ba’a yake yi musu
kamar dai yadda taubashi yake gaya wa abokin taubastakan nasa. Misali:
Jagora: Ka ga ɗan sarki da kunnuwa da
hwaɗi,
Ga
ya da ƙarya ga ya da rowa,
Yara: Ko ka girmama shi ba ya sarki.
(Bunza, 2009, sh.396).
Samun ɗan sarki maƙaryaci kuma marowaci a
al’uma ba ƙaramar illa ba ce. Ko da talaka aka kira haka to an
muzanta shi. Da waɗannan munanan ɗabi’u
Narambaɗa ya kafa hujjar cewa, ko ya
girmama su, sun riga sun nakasa kansu. A wani misalin kuma, mutum ya zama Ɗanbashirwa (mai zawo a
kasuwa) ba ƙaramar mummunar ɗabi’a ba ce da ba mai so
a danganta shi da shi da ita. To amma kasancewar Narambaɗa
taubashi ne ga ‘ya’yan sarki, bai damu ya yi musu irin wannan kallo ba. Ga abin
da yake cewa:
Jagora: Ɗan sarki duk mai hankali,
Ɗan sarki duk mai arziki,
in
dai ba Ɗanbashirwa na ba.
Ya
san abu Allah ad da shi,
Yara: Ya ɗauki biya domin
gaba.
(Bunza, 2009, sh.527).
Har wa yau a waƙar “Sarkin Tudu Bala,”
Narambaɗa ya jero wasu munanan ɗabi’u
guda shida ya danganta su da taubasan nasa, ya kuma nuna ba a zama da masu shi
lafiya. Waɗannan halaye kuwa su ne munafuci,
da azuzanci (ɗabi’ar ƙirƙiro ƙarya a danganta da
mutum) da butulci da ashararanci da ɓarna da kuma ɗabi’ar
ƙule
mutane. Ga abin da yake cewa:
Jagora: Sarki ka ga mutum shidda
Yara: Babu mai zaunawa lahiya da su.
Jagora: Wanga guda tsohon Munahuki
wanga Azuji wanga Butulu,
guda Ashararu guda Maɓannaci.
Yara: Akwai wani na nan mai ƙule
mutum.
(Gusau,2003,
sh.78).
2.1.2 Dabbanta ’Ya’yan Sarki
Daga cikin hanyoyin da Narambaɗa
yake amfani da su wajen aiwatar da wasan barkwanci ga taubasansa ‘ya’yan
sarakuna shi ne ya dabbantar da su. Ko dai ya kira su da sunan wata dabba kai
tsaye ko kuma ya siffanta su da halaye ko ɗabi’u na wasu dabbobi.
Wani abin sha’awa da irin wannan wasan barkwanci na makaɗin
shi ne, a kullum ba ya danganta su da dabbobi ko halayen dabbobi masu nagarta
kamar zaki ko giwa. Sai dai ya ƙasƙantar da ɗan
sarki ta hanyar kwatanta abin da ya yi na kasawa da rayuwar wata dabba. Ga abin
da Narambaɗa yake cewa:
Jagora: Ai, Baban Shamaki karo sai rago,
Yara: Bunsuru
kau da gabanka
kar
a jima bakin banza.
(Bunza, 2009, sh.356).
A
nan ya yi wa wani ɗan sarki barkwanci ta hanyar
kiransa bunsuru da nuna ba zai iya karo da rago ba wanda shi ne ubangidansa.
Haka a cikin wannan waƙar ya kira wani ɗan sarki da burgu domin
ya nuna irin halin da yake shiga idan ana ruwan sama. Ga abin da yake cewa.
Jagora: Haka a yini ruwa a kwan ruwa
kwaɗɗo
sai lela,
Yara: Shi Burgu
na cikin rima
Wahala
ta kammai.
(Bunza, 2009, sh.356).
A waƙar “Gwarzon bahago ɗan Iro,” kai tsaye
Narambaɗa yi wa wani ɗan
sarki barkwancin kiransa zakara.
Jagora: Ɗan sarkin da kag ga ya
lalace,
Ya
shiga taɓin Bori,
Ba
shi da niyyar sarki,
Yara: Daɗa hwa sai yawo
Ya
zan zakaran ’Yaɗɗamna,
Jagora: Katakoro zakara,
Yara: Katakoro zakara ’Yaɗɗamna,
(Ibrahim Narambaɗa,
waƙar
‘Gwarzon bahago ɗan Iro,Mp3)
2.1.3 Fifita
Sarki a kan ’Ya’yan Sarki
A waƙoƙin Narambaɗa
na sarakuna yakan yaba sarki ya rinƙa nuna fifikonsa a kan kowane
mahaluki da ke a ƙarƙashin mulkinsa. Daga cikin waɗanda
suke ganin su ma wani abu ne kuma suna iya zama sarki su ne ‘ya’yan sarakuna.
Narambaɗa yakan yi amfani da damar da yake
samu na dangantakar taubastaka da ke tsanin su ya nuna musu fifikon sarki a kan
su. Yakan yi hakan ne cikin raha da ba’a, galibi ya kwatanta abubuwa guda biyu
ta nuna sarkin shi ne ya fi fifiko a kan ’ya’yan sarki. Misali:
Jagora: Ai, ga Giwa tana abin da ta kai,
Yara: Ga ‘yan
namu na kallonta babu damar cewa komai
Gwarzo
shamaki na Malam Toron Giwa,
Baban
Dodo ba a tamma
Da batun banza.
(Bunza,
2009, sh.352).
A nan ya kwatanta Sarki da Giwa a
cikin dawa, su kuma ‘ya’yan sarki su ne sauran namu daji waɗanda
ya kira ’yan namu. A wani misalin
kuma yana cewa:
Jagora: Maɗi bai kai ga zuma ba,
Yara: Kowal lasa shi ka hwaɗi,
Kwandon
wake
bai kai ga damen gero ba.
Jagora: Ai ɗan
akuya
ko ya yi ƙofoni,
Yara: Ya san bai yi kamar Rago ba,
Jagora: Ɗan sarki komi yaƙ ƙasura,
Yara: Kak ka raba shi da bawan sarki.
Gogarman Tudu jikan Sanda
Maza su yi tsoron ɗan
Maihausa
(Bunza, 2009, sh.364).
A waɗannan ɗiyan
waƙa
Narambaɗa yana nuna wa jama’a irin fifikon
da sarki yake da shi idan an kwatanta da sarki. Ya kwatanta maɗi
da zuma, kwandon wake da damin gero, ɗan akuya da rago. Daga ƙarshe dai ya ƙasƙantar da ɗan
sarki ta nuna cewa ba shi da bambamci da bawan sarki. Haƙiƙa wannan wani nau’i ne
na barkwanci da Narambaɗa ya yi amfani da dangantakarsa da
‘ya’yan sarki ya ƙasƙantar da su zuwa matsayin bayin sarki muddin dai ba su
ke kan karagar mulki ba. Taubashi kaɗai zai iya yi wa ɗan
sarki haka a zauna lafiya.
2.1.4 Fito
da Kasawar ’Ya’yan Sarki
A wata fuska kuma na wasan
barkwancin Narambaɗa da ’ya’yan sarakuna, yakan ƙasƙantar da su ta hanyar yi
musu ƙage
da kasawarsu kamar dai yadda taubashi a kullum ba ya nuna ƙoƙarin abokin taubastakar
nasa. Narambaɗa yana cewa:
Jagora: Ga wani ya ce ba ya sarauta,
Yara: Wai sai ta faɗi gasassa,
To, ko ta faɗi
gasassa,
Yara: An san ɗan sarkin da ka Sarki,
An bar sarki da kumama.
(Bunza, 2009, sh.400).
A al’adance, idan aka shaidi mutum
kumama ne, ba za a taɓa shirya wani abin da ake son nuna
zaruntaka da shi ba, ballantana a ce ya yi sarauta. Wannan wani tunani ne na
makaɗin ya nuna wa ɗan sarkin ya tanadi
rariyar tace waɗanda ba su iya yin saurauta amma a
barkwance. A wani misalin kuma Narambaɗa yana cewa:
Jagora: Gidan ga mutum huɗu
ba su sarauta,
Da Sambalko, da Satoto,
Shi wanga na ukku Ƙazami,
Yara: Na cikon na huɗu ɗinsu
Azuji.
(Bunza, 2009, sh.400).
A nan ma Narambaɗa
ya yi amfani da kalmomin kasawa ya danganta su da wasu ‘ya’yan sarki don kawai
ya muzanta su. Waɗannan duk kalmomi ne da ke iya
bayyana a cikin wasan barkwanci na taubastaka.
2.1.5 Cusa
wa ‘Yayan Sarki Lalurar Nakasa
Wasan barkwanci na taubasantaka
yakan ba mutum dama ya siffanta abokin wasansa da wata nakasa kamar kuturta ko
makanta ko ƙusumbi ko hauka da dai sauran su. Yi masa irin wannan
wasa zai ga ya munana shi duk da yake a zahiri yana iya kasancewa ba haka abin
yake ba. Narambaɗa yana cewa:
Jagora: Ɗan sarkin da yay yi doro,
Har
yay yi ɗan ƙusumbi,
Abu
dan cumui-cumui,
Yara: Faufau ba ka jin an naɗai
sarki,
Jagora: Ɗan Sarkin da yay yi doro,
Har
yay yi ɗan ƙusumbi,
Abu
dai ɗuƙui-duƙui
Yara: Faufau ba ka jin an naɗai
sarki.
Jagora: Ga su can ƙasashenmu,
Irin
su ba su ƙulla komi ba.
(Bunza, 2009, sh.425).
A nan makaɗin
ya yi amfani da nakasar doro da ƙusumbi domin ya muzanta ɗan
sarki.
2.1.6
Ayyukan da ba su dace da ’ya’yan sarki ba
A rayuwa ta zahiri akwai wasu
ayyuka ko yanayin rayuwa na wasu mutane waɗanda ana iya cewa kai
tsaye ba su dace da nasaba ko asalin wasu mutane ba. To duk abin da aka sa ba a
gurbinsa ba sai jama’a sun fahimci haka kuma sun nuna rashin dacewarsa. Narambaɗa
ya muzanta ’ya’yan sarki ta amfani da wasan barkwanci na taubastakar da ya ƙirƙiro a tsakanin su ya
danganta su da wasan tauri ya kuma fito da sakamakon da za a samu idan aka yi
hulɗa da su a irin wannan yanayin. Ga abin da yake cewa:
Jagora: Dut ɗan
Sarkin da kag ga
Ya
shiga wasan tauri
Yara: To! Bari ja nai hwaɗa
Baƙam Magana ɗai
an nan.
Jagora: Dut ɗan
Sarkin da kag ga,
Ya
shiga wasan karma
Yara: Kak ka taɓai
hwaɗa
Baƙam magana ɗai
an nan.
(Bunza, 2009, sh.360).
A nan yana nuna idan har ka ga ɗan
sarki ya shiga wasan tauri to kada ka kusance shi. Babu taurin ma yaya ya ƙare da su ballantana sun
sami dalili.
2.1.7 Takaicin
Rashin Yin Sarauta
Daga cikin abin da makaɗan
sarakuna suke yi domin su ƙara harzuƙa ‘ya’yan sarakuna in ba su sami
nasara atakarar sarauta ba shi ne su yi musu zambo ko habaici. Wannan wani abu
ne mai kama da gwalo ga yaro idan yana cikin takaicin rasa wani abu ko wani
yanayi mara kyau da ya shiga. Narambaɗa yakan yi amfani da
wannan salo na gwalo ga ‘ya’yan sarakuna a cikin waƙoƙinsa ta amfani da wasan
barkwanci na taubastaka da ya ƙirƙiro a tsakaninsu.
Yara: Ba duka ɗan Sarki ba ka samun
Sarki,
Gogarman Tudu jikan Sanda
Maza su yi tsoron ɗan
Maihausa
Jagora: Ɗan sarki duka yag ga
sarauta,
Ga ta kamak kusa tai mashi nisa,
Yara: In
dai bai yi sarautan nan ba,
Sai ya tsufa da mikin zucci
(Bunza, 2009, shf.364-365).
A tunanin Narambaɗa,
gurin kowane ɗan sarki ne ya zama sarki. Rashin
samun wannan damar zai dasa miki a zuciyarsa wadda ita za ta kashe shi idan bai
yi hankali ba. Damar da Narambaɗa ya samu na yin wasa da
‘ya’yan sarakuna ya yi amfani da ita wajen gaya musu hasashen da yake yi na
yanayin da suke shiga idan ba su sami kaiwa ga abin da suke so ba.
3.0 Kammalawa
A wannan nazarin, an yi ƙoƙarin danganta wasannin
barkwancin da ke tsakanin taubasai da abin da Narambaɗa
ya ɗabi’antu da su a cikin waƙokinsa na sarauta.
Wannan shahararren makaɗin yana da al’adar yin raha ta
furta kalamun wasa masu sosa zuciya ga ‘ya’yan sarakuna a cikin waƙoƙinsa na sarauta. Nazarin
ya dubi abin da ake kira taubastaka da kuma abin da ya ƙunsa wanda shi ya bayar
da damar samar da wannan alaƙar a tsakanin makaɗin da ‘ya’yan sarki.
Haka kuma an waiwayi tarihin Narambaɗa a taƙaice. Shi ma ya bayar da
haske a kan wanda ake nazarin a kansa. A rukuni na ƙarshe na nazarin wanda
shi ya tabbatar da hasashen da aka yi tun farko na cewa, akwai wasan taubastaka
a tsakanin ‘ya’yan sarki da Narambaɗa, an dubi fuskokin
wasannin ta la’akari da ɗiyan waƙoƙinsa. Wannan nazari ya
gano cewa, Narambaɗa yana amfani da hanyoyi
daban-daban wajen nuna wannan alaƙa ta wasa a tsakaninsa da ‘ya’yan
sarki. Daga ciki akwai kallon su da munanan ɗabi’u da dabbantar da su
da cusa musu nakasa da dangata su da yin ayyukan da ba su dace da matsayinsu ba
da dai sauran du. Waɗannan su suka kafa hujjar cewa,
Narambaɗa mutum ne mai sha’awar sa raha a
cikin waƙoƙinsa. Kuma ba wanda ya rena wajen yin wannan raha da
ba’a kamar ‘ya’yan sarakuna. Wasan da ke tsakaninsu na alaƙa ce tsakanin ɗan
namiji da ɗan mace watau taubasai.
Manazarta
Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre.
Bunza,
A.M. (1998). “Naƙalin Diddigin Jirwayin Rayuwar Narambaɗa,
Cikin Falsafar Luguden Kalmomin Waƙoƙinsa”. Takardar da aka
gabatar a taron ƙara wa Juna sani, tsangayar Fasaha da Nazarin Musulunci.
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
CNHN (2006). Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero.
Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Gusau,
S.M. (1996). Makaɗa
da Mawaƙan
Hausa.
Kaduna: Fisbas Media Serɓices.
Gusau,
S.M. (2003).
Jagorar Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: Benchmark
Publishers Limited.
Gusau,
S.M. (2001). “Waƙar Gogarman Tudu ta Ibrahim Narambaɗa
a Mazubin Nazari”, Cikin Algaita, Journal
of Current Research in Hausa Studies. Department of Nigerian Languages
Series. Kano: Bayero Uniɓersity.
Gusau,
S.M. (2002). ‘Saƙo a Waƙoƙin Baka’, Tsokaci kan
Turke da Rabe-rabensa’, Cikin Studies in
Hausa Language, Literature and Culture. Kano: CSNC, Jami’ar Bayero.
Ibrahim,
M.S. (1983). Kowa ya Sha Kiɗa. Zaria: Longman Nigeria Plc.
Katuru,
A.M. (1995). “Salon Kinaya a Cikin Waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa”.
Kundin digirin B.A. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Shinkafi,
S.I. (1998). “Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa
Tubali (1975 –1960)”. Kundin digirin B.A. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Tukur, A. (1999). Kowace Ƙwarya da Abokiyar Ɓurminta. Kano: Gidan Dabino
Publishers.
Yahya,
A.B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa.
Kaduna: Fisbas Media Serɓices.
Yahya,
A.B. (2001). Salo Asirin Waƙa.
Kaduna: Fisbas Media Serɓices.
Yahya,
A.B. (2002). “Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo Cikin Nazarin Waƙa”, Cikin Studies in Hausa languages, Literatire and
Culture. Kano: CSNL, Jami’ar Bayero.
Zurmi, M.I. (1981). “Form and Style in Hausa Oral Praise Songs” in Oral Poerty in Nigeria. (leds) by Abalogun and others. Lagos: Nigeria Magazine.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.