Takabar Maguzawa

    Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2021) “Takabar Maguzawa” in, Yakasai, S. A. et al (eds) A Great Linguist and a Scholar. A Festschrift in Honour of Prof. Ibrahim Ahmad Mukoshy Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. ISBN: 978-978-59094-3-2 Pages 740 -748  

    Takabar Maguzawa

    Daga

    Dr. Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
    Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
    Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
    e-mail: ibrasskg@gmail.com
    Lambar Waya: 0803 6153 050

    1.0 Gabatarwa

    Mutuwa a kowace al’umma ta duniya tana ƙunshe da al’adu iri-iri. Waɗannan al’adu sun shafi kawar da gawar mamaci da zaman makoki da bukukuwa da ladubban da ake gudanarwa waɗanda suka shafi matsayi na abin da mamaci ya mallaka ko ya bari (wato dangin dukiya da ’ya’ya da mata da sauransu). Akasarin waɗannan al’adu suna bin shimfiɗaɗɗun dokoki ne na abin da ake bauta wa. Wasu kuma al’adu ne kawai waɗanda aka gada daga iyaye da kakanni. Idan imanin waɗannan mutanen ya sauya zuwa ga wani abu na daban, to za a ga su ma waɗannan al’adu sun sauya in ban da ɗan abin da ba a rasa ba wanda shi zai ba da hasken inda aka fito. Idan kuma imanin bai sauya ba, to a nan ba za a rasa ganin kutsen zamani ba.

    A wannan maƙalar, za a yi ƙoƙarin duban yadda al’umar Maguzawa suke gudanar da al’adunsu na takaba ba tare da la’akari da sauyawar zamani a rayuwar tasu ba. Wannan zai ba da damar ganin hikimomin da suka tanada a gargajiyance dangane da matsayin matan auren da mamaci ya bari ko kuma namijin da matarsa ta mutu. Haka kuma shi zai ba da damar kwatanta rayuwar tasu da halin da suka sami kansu a ciki a yanzu ko kuma da sauyawar tunanin wasu daga cikin su zuwa ga addinin Musulunci.

       

    2.0 Waiwaye

    Wannan fasali zai yi ƙoƙarin yin bayani ne a taƙaice dangane da muhimman tubalan taken wannan nazari. Waɗannan kalmomi kuwa su ne Takaba da Maguzawa.

    2.1 Takaba

    Dangane da asalin kalmar takaba, babu wata alama ko wani bincike da aka ci karo da shi wanda ya bayyana cewa, aro ta aka yi daga wani harshe. A ƙoƙarin tabbatar da kalmar Bahaushiya ce, wasu suna ganin ta samu ne daga tabarmar kaba. A al’adar shiga takaba a gargajiyance (kamar yadda za a gani a nan gaba), za a tanadar wa mace sabuwar tabarma wadda aka saƙa da kaba. A kan wannan tabarmar mai takaba za ta riƙa kwana har ranar da ta fita. Ganin cewa an keɓe rayuwar wannan mata da amfani da tabarmar kaba na wani lokaci mai tsawo, sai aka danganta al’adar da tabarmar, wato ta-kaba. Ko dai ya kasance matar da ke aiwatar da al’adar ita ce ta kaba ko kuma al’adar ce ta kaba (wacce ake aiwatarwa da kaba).

    Ta fuskar ma’ana kuma, a Ƙamusun Hausa (2006) an nuna cewa, takaba ita ce:

    Zaman alhini da mace take yi na wata huɗu da kwana goma, bayan rasuwar mijinta, kafin ta yi wani aure.

    Wannan ma’ana idan aka lura, ta fi bayar da ƙarfi ne ga tanadin da addini Musulunci ya yi musamman da aka ambaci tsawon lokacin da ake aiwatar da ita. To idan har haka ne, ma’anar ta manta ta kawo tunanin Musulunci na dalilan yin takabar kamar samun tabbacin rashin shigar cikin mamacin. Haka kuma a wajen bayar da wannan ma’anar, ba a yi la’akari da cewa, wannan kalma ce ta Hausa ba wadda tana iya samun wani matsayi ko fasali ko ma’ana ga Hausawan da ba musulmi ba. A taƙaice dai wannan nazari ya gano cewa, Ba Hausawa musulmi kaɗai suke yin takaba ba. Haka kuma ba jinsin mata kaɗai suke yi ba. Wannan tunani ya sa aka mayar da hankali wajen samar da abin da aka kira bakamdamiyar ma’ana.

    A taƙaice ana iya cewe, Takaba zama ne na kaɗaici da juyayi da mace ko namiji kan kasance a ciki a sakamakon mutuwar miji ko mata na wani ƙayyadajjen lokaci da addini ko al’ada ta tanadar tare da bin shimfiɗaɗɗun dokoki masu alaƙa da wannan al’ada ko addinin. Daga cikin tanade-tanaden da aka yi wa wannan zama wanda ya bambanta da zaman yau da kullum shi ne kaɗaita da takumkumin yin wasu aikace-aikace ko mu’amala da mutane kamar yadda aka saba na wani ƙayyadadden lokaci.

    2.2          Maguzawa

    Kalmar Maguzawa tana ɗaukar ma’anar Hausawan da ba musulmi ba, waɗanda al’adunsu da addininsu na gargajiya suke jagorancin rayuwarsu (Krusius 1915, Fletcher 1929, Ibrahim 1982, Yusuf 1986, Kado 1987, Safana 2001, Akodu 2001, Malumfashi 2002, ….) Waɗannan malamai sun tabbatar da Maguzawa su ne Hausawan asali ta gefen uwa da uba. Sun sami wannan suna ne daga ’yan’uwansu musulmi. Kalmar Maguzawa jam’i ne na kalmomin Bamaguje (namiji) da Bamagujiya ko Bamaguza (mace). Duk da yake wannan nazari waiwaye ne na al’adun da Maguzawa suka gudanar a can baya, akwai bukatar a san cewa, har yansu ana samun waɗannan mutane a jihohin Katsina da Kano da Zamfara da kuma Jigawa. Sai dai nazarin ya taƙaita ne ga Maguzawan da aka samu a yankin jihar Katsina ta yanzu.

    3.0  Takabar Matan Maguzawa

    Kamar yadda ma’anar ta nuna, ana yin takaba ne a sakamakon mutuwar mata ko miji. Maguzawa sun tanadi al’adu da yawa dangane da yanayin da matar mamaci za ta kasance idan miji ya mutu. Waɗannan al’adu sun bambanta daga wuri zuwa wuri. A wannan fasalin za a dubi waɗannan al’adu na yanayin takabar matan Maguzawa.

    3.1          Tsawon Lokacin Takabar Matan Maguzawa

    Tsawon lokacin da matan Maguzawa suke ɗauka a cikin takaba bayan mutuwar miji sun bambanta kamar yadda sauran al’adu suka bambanta. Ibrahim (1982:177) ya gano cewa, akwai Maguzawan da suke yin takaba na tsawon wata bakwai da kwana goma sha bakwai. Sun kasa waɗannan kwanaki zuwa kashi uku. Kashi na farko su ne kwanaki bakwai da mace za ta yi na zaman makoki bayan an binne mijinta. Daga nan kuma sai ta shiga rukuni na biyu na kwanaki arba’in a gidan mamaci bayan an share makoki. Idan waɗannan kwanaki suka kammala, danginta da dangin miji za su taru su yi bukin murnar taya ta fita takabar gidan miji. Tun daga wannan rana kuma za ta koma gidan iyayenta ta fara wata sabuwar takabar ta wata shida.

    Maguzawan Kainafara suna yin takaba ne ta tsawon kwanaki ɗari da hamsin, wato wata biyar. Haka su ma Maguzawan Lezumawan Babban kada (Safana) da Maguzawan Ƙwanƙi (ƙasar Bakori) duk wata biyar suke yi. Wannan ya sa idan matar mamaci a Ƙwanƙi za ta shiga takaba, a taƙaice sai a ce ta shiga biyar. In kuma ta fita sai a ce ta wanke biyar. Wato ta yi wankan fita takaba na watanni biyar. Duk waɗannan kwanaki na takaba sun saɓa wa na Maguzawan Gidan Bakwai (Ƙasar Faskari) domin su matansu wata shida suke yi a cikin takaba.

    3.2 Ladubba da Matakan Shiga Takabar Matan Maguzawa

    Akasarin matan da Bamaguje ya mutu ya bari sukan shiga takaba ne a ranar da aka share makoki, wato kwanaki bakwai da mutuwarsa. Sai dai akan sami masu shiga a ranar da mutum ya mutu ko bayan kwana biyar da mutuwa. ’Yan kwanaki kafin ranar shiga takabar, akan tanadi ruwan da za a yi wa matan mamacin wanka a yi jiƙe-jiƙe a ciki. Yawan ruwan ya danganta da yawan matan nasa. Akan tanadi ganyen itaciyar ceɗiya da ganyen yakuwa da farin soɓorodo da wasu saƙesaƙi na itatuwa daban-daban, sai duk a jiƙa su a cikin tukunya ɗaya. Akan nemi sabulun salo a ajiye domin da shi ake yin wankan. Haka kuma kafin ranar da za a yi wankan, za a gayyato tsofaffin mata waɗanda su za su yi wa matan wankan.

    A ranar da za a yi wa matan wanka, in aka buɗe wannan jiƙon da aka yi a cikin tukunya, za a ga yana kumfa. Wannan ke nuna cewa maganin ya haɗu. Matan mamaci za su tsefe kansu. Shi za a fara wankewa da sabulun salo da wannan ruwan. Wai akan fara da wanke kai ne domin ita ma duk wasu iskoki da suke tare da ita waɗanda ke da alaƙa da mamacin a nan suke zaune. Idan an wanke kan da wannan ruwan da sabulun salo, an sallame su ke nan. Daga nan kuma sai a saɓa sabulun salon nan a wanke sauran jikin, ana ɗaurayewa da wannan ruwan maganin. Haka tsofaffin matan nan masu wankan takaba za su yi musu ɗaya bayan ɗaya, ko su nawa ne.

    Daga wannan wankan ba za su sake yin wanka ba sai ranar fita takaban. Za a ba su farin zani wanda za su ɗaura da tabarmar kaba ta kwantawa da kallabi na ɗaurawa da gora na duma. Mace mai takaba za ta kasance a cikin gidan ba ta zuwa ko’ina. Ana ɗaukan waɗannan matakan tsaro ne don a kare ta daga aikata wani abin kunya wanda zai iya shafar mutuncin wannan gida ko zuri’a. Haka kuma mace mai takaba ba za ta yi wasu aikace-aikace ba kamar ɗiban ruwa da zuwa yin itace da noma da faskare da sauransu. Za ta kasance kullum da wannan ɗan goran a hannu. Ba za ta sake yin wata kwalliya ko shafe-shafe na gyara jiki ba, illa ta wanke hannu ko ƙafa ko fuska. Haka ma ba za ta yi kitso ba, duk sai ranar da ta fita takabar. Waɗannan al’adu galibi sun shafi Maguzawan da suke yin takaba a gidan mamaci ne.

    3.3 Fita Takabar Matan Maguzawa

    A ranar da matan mamaci za su fita takaba bayan sun tsaya na waɗannan watanni da aka ambata, za a sa rana a yi wani buki na musamman. Shi ma wannan buki akan sami saɓanin yanayi ko hanyoyin gudanar da shi a tsakanin Maguzawan da ke zaune a wurare daban-daban. Misali, Maguzawan Gidan Gwarzo (ƙasar Matazu) suna fara bukin ne goshin faɗuwar rana har gari ya waye. A duk tsawon wannan dare shagali kawai za a kwana ana yi. Za a sa ƙwarya cikin ruwa a yi ta kaɗawa (kiɗan ruwa). Maza da mata za su haɗu suna ta rawa. Jikoki za su haɗu ana ta ba’a ana rawa. Idan gari ya waye manya-manyan Maguzawan ƙauyen ko unguwar za su haɗu a sha giya tare da matan da za su fita takaba da sauran jama’a. Idan aka ƙare wannan shan giyar, sai su shiga gida su yi wanka, sun fita takaba ke nan. Masu sauran ƙarfi sai su fara zawarci, su yi wani auren. Waɗanda suka tsufa kuma sukan tsaya a nan gidan su kula da ’ya’yansu da matan ’ya’ya da jikoki.

    Maguzawan Kwanƙi idan wata biyar na takaba suka cika, matan za su yi wankan farko. Wannan ruwan da za su yi wankan da shi akan sa masa magunguna iri-iri, gwargwadon gadon gidan ko irin tanade-tanadensu na tsafi da al’ada da camfe-camfen da suka aminta da su. Suna ƙare wannan wanka za su yi kwalliya sai su nufi kasuwa. Wannan ya nuna ke nan ba a fita takaba sai ranar kasuwa. Duk wanda ya gan su a kasuwa ranar ya san sun wanke biyar, sai a yi ta taya su murna. Daga kasuwar nan ba za su dawo gidan mijin ba sai dai duk su koma gidan iyayensu. A can za su kwana ɗaya ko biyu ko uku, wasu ma har mako ɗaya. Idan cikin su akwai masu ’ya’ya kuma ba su da niyyar sake yin wani auren, sai su koma gidan miji su ci gaba da zama da ’ya’yansu. Waɗanda kuma za su yi aure tun daga wannan ranar za su fara zawarci.

    A al’adar Maguzawan Lezumawa, kamar yadda aka yi bayani a baya, suna fita takaba ne bayan wata biyar. Su ma sukan fara nasu bukin ne da almuru. Kafin lokacin, matan mamacin za su soya gyaɗa kamar buhu ɗaya. Wannan gyaɗar ce za a yi ta ba mutane suna ci a wajen bukin. Matan za su ɗaura farin zani da lalle a ƙafa. Za a gayyato makaɗa da sauran jama’a. Akan hura wuta a wani fili inda za a yi bukin. Wasu kuwa bayan gari suke zuwa. Matan da za su fita takaba za su zazzauna suna kallon masu rawar nan. Shi kuma makaɗi ko makaɗa za su yi ta rafsar ganga, samari suna ta rawa suna zagaya wutar da aka hura. Ana kiran wannan rawa, Rawar kadaba. An nuna cewa, rawar kadaba rawa ce ta rashin kunya da batsa da zage-zage da faɗar munanan magangannu. A wajen wannan bukin babu takunkumin faɗin duk wani abin kunya da mamacin ya taɓa yi musamman daga jikokinsa. Haka za a yi ta shagali har wayewan gari.

    Idan gari ya waye, kafin a watse sai kowace daga cikin matan mamacin ta kawo ɗan akuya da zakara ɗaya ta sake su a cikin taron masu rawar. Su kuma za su sa wasoso, wannan ya ja, wannan ya karɓe, kamar ’yan farauta. A wasu lokutan ma akan ɓaɓɓalle ɗan akuyar ko zakaran a yi yaga-yaga da su. Wani ya tsira da kai, wani da ƙafa, wani da karfata. Mai karfi yana iya tsira da ɗan akuya shi kaɗai, maza su gagara fizgewa. Daga nan sai a watse, an sallami taro ke nan. Matan mamacin za su je su yi wanka, su shiga zawarci. Waɗanda kuma suka tsufa su koma gida su zauna da ’ya’ya da jikoki.

    A wani ƙaulin kuma, an nuna cewa daga cikin matan da za su fita takaba idan akwai masu niyyar yin wani auren, in sun kawo wannan zakaran a lokacin da za a watse bukin, za su miƙa wa wanda suke so ya aure su daga cikin ’yan rawar nan. Tana miƙa masa, shi ke nan sai ya ɗauke ta su tafi gidansa, ta zama matarsa. Ba sai an yi ɗaurin aure ko wani buki ba.

     

    3.4 Takabar Mace Mai Ciki

    A cikin tanade-tanaden takabar Hausawa musulmi, idan miji ya rasu ya bar mace da ciki, da zarar ta haihu to takabarta ta ƙare. To a al’umar Maguzawa ba haka abin yake ba. Babu wani bambanci tsakanin mai cikin da take takaba da wadda ba ta da ciki. Duk komai tare za a yi kamar yadda aka ambata a baya. Inda al’adun suka saɓa kawai shi ne idan ya kasance ta fita takaba ba ta haihu ba, to dole sai ta jira ta haihu kafin ta yi wani auren. Ita kuwa wadda ba ta da ciki, tun daga ranar da ta fita takaba za ta fara zawarci.

      

    4.0 Takabar Namiji

    Takaba dai mata aka sani suna yin ta kamar yadda aka gani a fasalin da ya gabata. Amma a wasu al’ummomi na Maguzawa ana samun maza ma suna yin takaba idan matarsu ta mutu. To sai dai irin wannan takaba ta bambanta da wadda aka sani ko aka gani a baya. Ga misali a al’adar mutuwar Maguzawan Kaibaki (ƙasar Fago), a ranar da aka share makoki, wato kwana bakwai da mutuwa, mijin matar da ta mutu zai fara takaba. Sai dai shi ba wankan da zai yi na musamman ba. Haka kuma ba wani buki da ake yi na fita takaba.Wasu ma ba za su lura da ya shiga takaba ba. Alamar kawai da za a gani a gane namiji yana takabar matarsa da ta mutu (musamman ga waɗanda ba su san ya rasa matar ba), shi ne zai juya rigarsa, ya rinƙa sa ta baibai. Zai kasance a haka ne na kwanaki uku. Bayan waɗannan kwanakin kuma sai ya ci gaba da sa rigarsa daidai. Shi ma dai ba a so ya yi wasu aikace-aikace kamar zuwa gona da sauransu na waɗannan kwanakin. Babu wani dalili na tsagaita takabar zuwa kwanaki uku kawai. Wasu na ganin cewa idan aka ce zai yi kwanaki ko watannin da mata ke yi na takaba to duk lamurran gidan da ke buƙatar kulawarsa za su tsaya. Wannan zai sa a shiga cikin wani mawuyacin hali muddin dai zai bi dokokin hani da horo na takaba kamar yadda mata suke yi.

    5.0 Aure Bayan Fita takaba

    Bayan matan mamaci sun ƙare takaba, idan akwai masu sauran ƙarfi ko sha’awar yin aure daga cikinsu, nan take sukan fara zawarci. To sai dai irin wannan zawarci yana da sharuɗɗa. Daga cikin, ’yan’uwan mijinta da ya mutu su ke da alhakin ɗaura wa mace aure. Don haka sai wanda suka ga ya dace. Ko da masoyan suna da yawa, sai wanda suka yi shawara suka ga ya dace ya auri matar ubansu ko ɗan’uwa. Haka ma ko da ta aminta tana son bazawari, idan su ba su amince ta aure shi ba, ba yadda za a yi wannan auren. Dole ta haƙura domin su ne iyayen aurenta. Iyayen mace na ainihi ba su da damar su sa baki. A nasu tunanin, aurenta ba mutuwa ya yi ba. To idan sun bayar da auren ta tare gidan sabon miji, sai ya kasance ta fito daga gidan wannan mijin, to duk wani lamari nata ya koma ga iyayenta. A wannan lokacin ba ruwan dangin mijinta da ya mutu wajen tsoma hannu ko sa baki a auren da za ta ƙara yi.

    Dangane da mijin da za ta aura bayan ta ƙare takaba kuma, an haramta duk wani wanda ya haɗa jini da mamacin (tsohon mijinta) ya aure ta. Haka ma ba a yarda maƙwabci ko wani aminin mamacin su aure ta ba. Dole sai bare za ta aura. Hakan na faruwa ne wai saboda kunya da girmamawa ga mamacin. To sai dai an yarda dangin mamacin su nemo wani can wanda suka aminta da shi, su ce ya aure ta musamman don ya kula musu da ƙananan ’ya’yanta idan akwai su. Maguzawa sukan nemi alfarmar wani wanda suka san yana da mutunci ya auri matar ɗan’uwansu da ya mutu don su sami wanda zai kare mutuncinta ba wanda zai wulaƙantar da ita ba a matsayinta na matar ubansu, ko matar ɗan’uwansu.

    Idan matar da ta fita takaba ta sami miji, kuma suka aminta, to za a ɗaura auren ne a ƙofar gidan mijinta da ya mutu. A nan za a yi duk al’adun da auren ya tanada. Haka ma daga nan za a ɗauke ta zuwa gidan sabon miji.

    6.0 Kammalawa

    A wannan nazari, an dubi yadda al’umar Maguzawa musamman na wasu sassa na jihar Katsina suke gudanar da wasu al’adu nasu da suka shafi yanayin da matan aure suke shiga idan sun rasa mazajensu. Kamar yadda nazarin ya nuna, al’adar Maguzawa ta tanadi matar mamaci ta shiga wani kaɗaici na juyayin mutuwar. Wannan zama da za ta yi na mabambantan lokuta yana ƙunshe da hani da horo a kan wasu al’amurra da suka ƙunshi rayuwa na yau da kullum. Haka kuma waɗannan al’adu sun yi tanadi na musamman dangane da sake yin aure ga matar mamaci. Duk da yake ba a ko’ina maza suke yin takaba ba, nazarin ya ci karo da wani sashe na Maguzawan da aka yi nazari a kan su inda maza ma suna yin takaba. To sai dai su nasu takabar kamar yadda binciken ya gano, na wasu ’yan taƙaitattun kwanaki ne. Nazarin ya taimaka wajen ƙara danganta Hausawa da Maguzawa, ya kuma ƙara fayyace bambancin al’adun nasu musamman ta fuskar manufa da madogara.

    7.0  Manazarta

    Abdullahi, I. S. S. (2008). ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan

    Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Sakkwato: Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

    Abdullahi, I. S. S. (2008). “Fitattun Ɗabi’un Maguzawa” Maiduguri Journal of

    Linguistics and Literary Studies (MAJOLLS) Vol. X. Department of Languages and Linguistics. Maiduguri: University of Maiduguri.

    Abdullahi, I. S. S. (2009). “Bukin Hawan Sadaka na Maguzawa” Journal of

    Contemporary Hausa Studies, Vol. 1 No. 1. Department of Nigerian Languages. Katsina: Umaru Musa ’Yar’adua University.

    Abdullahi, I. S. S. (2012). “Falsafar Ɗaurin Auren Maguzawa.” Maƙalar da aka

    gabatar a taron ƙara wa juna sani, Cibiyar Nazarin Hausa. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

    Akodu, A. (2001). Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Zariya: Gaskiya Corporation Limited.

    Fletcher, D. C. (1929). “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment Report on ’Yanɗaka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833. Kaduna: National Archives and Monuments.

    Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Kano: Jami’ar Bayero.

    Ibrahim, M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci. Cyclostyled Edition. Zaria: Hausa Publications Centre.

    Kado, A. A. (1987). “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

    Krusius, P. (1915). “Maguzawa” in: Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

    Maikano, M. M. (2002). “Maguzawan Yari Bori: Tarihinsu Da Al’adunsu”,

    Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

    Malumfashi, A. A. (1987). “Hausa Language Speech Usage Norms: A Case Study

    of Maguzawa Society in Malumfashi Area” (B. A. Hausa Project). Kano: Bayero University.

    Mashi, B. U. (2001). “Maguzanci Da Zamananci: Nazari A Kan Al’adun

    Maguzawan Ɓula A Gundumar Mashi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

    Safana, Y. B. (2001). “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar

    Safana”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa). Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

    Yusuf, A. B. (1986). “Wasannin Maguzawan Ƙasar Katsina”, Kundin Digirin farko. Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.