Faten Shinkafa ÆŠanya
i. Attarugu
ii. Barkono (tonka)
iii. Ganyen yakuwa/sure
iv. Gishiri
v. Kori
vi. Magi
vii. Man gyaÉ—a
viii. Nama
ix. Shinkafa
Za a ɗora tukunya a wuta, sai a saka nama da albasa a zabga/tafasa sannan a sauƙe. Daga nan sai a saka mai a wuta tare da albasa da nama da kuma jajjagen tarugu. Za a soya sama-sama, sannan a sanya kayan yaji a ƙara soyawa. Bayan nan za a saka ruwa da magi da gishiri da kori a rufe tukunyar. Za a bar ta sai ta taso, da ma an wanke shinkafa, sai a zuba a jujjuya sai a yanka sure da albasa da dakakken barkono (tonka) na Hausa, a zuba. Idan ya dafu, sai a sauke shi da ruwa-ruwa.
Faten Wake
a. Alayyafu
b. Albasa
c. Gishiri
d. Hanta
e. Kayan Yaji
f. Kifi
g. Magi
h. Mai
i. Ruwa
j. Tarugu
k. Tattasai
l. Wake
Shi kuma wannan nau’in fate, wake za a gyara a cire datti. An fi son yin amfani
da manyan wake ba ƙanana ba. Za a ɗauko alayyafu a wanke a yanka shi manya-manya sannan a dafa shi
sama-sama a aje gefe. Sai a É—auko hanta ko kifi a tafasa su daban
tare da gishiri É—an kaÉ—an.
Daga nan, a jajjaga tattasai da tarugu da albasa tare da kayan yaji a soya da mai. Idan sun
soyu, za a yi sanwa a
saka magi da gishir. Bayan ta jima tana tafasa sai a saka wake tare da kifi da
hanta a juya a rufe tukunyar
zuwa É—an lokaci kaÉ—an. Bayan nan za a buÉ—e
a saka alayyafu a ciki. Akwai buƙatar
a bar shi ya nuna sosai kafin a sauƙe tukunya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.