Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
DIWANIN WAƘOƘIN
AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA)
Salisu Ahmad
Yakasai
Copyright © Diwanin Waƙoƙin ALA
All rights reserved.
No part of this work may be reproduced in any form, and in any language, without prior written permission from the authors, Salisu Ahmad Yakasai and Abu-Ubaida Sani.
National Library of Nigeria Cataloguing-in-Publication Data
YAKASAI. Salisu Ahmad 1958 –
Dawanin waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)
1. Hausa (African people) - Music
I. Salisu, Abu-Ubaida. II. Tittle
M 1831.H39 Y15 2021 780.96697
ISBN: 978-978-57624-9-0 (pbk) ACCR2
First Published, March 2021
SADAUKARWA
Wannan aiki sadaukarwa ce ga masu tunani nagari da karɓar shawarwari nagari da
kuma aikata aiki nagari.
GODIYA
Da sunan Allah mai rahama da jin ƙai, tsira da amincinsa su
tabbata ga shugaban halittu, wato Annabi Muhammadu (SAW), da alayensa da
sahabbansa da kuma masu bin sa da gaskiya har zuwa ranar ƙarshe.
Aikin haɗaka tsakanin
malami da ɗalibi a
fagen adabi, wani abu ne sabo. Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da ya zamar da
wannan mafarki gaskiya, wato samar da kammalallen aiki game da rayuwa da waƙoƙin
Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa), da ya ƙunshi kusan dukkanin abubuwa da ake buƙata a
wannan ɓangaren,
musamman daga haihuwar ALA zuwa shekara ta 2018.
Muna miƙa godiya ga shi kansa wanda aka yi wannan aiki game da rayuwa
da waƙoƙinsa
mai taken: DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA). Amincewarsa da a gabatar da
wannan aiki ne, ya share fagen samuwar lokacin da ya sadaukar domin bayar da
dukkan bayanan da ake buƙata a yayin wannan bincike.
Mutane daban-daban sun taimaka ta hanyoyi da yawa domin
kammaluwar wannan aiki, wato kama daga kayan aiki da shawarwari zuwa addu’o’i
na fatan alheri. Godiya ta musamman ga Dakta Yakubu Aliyu Gobir na Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo
dangane da irin rawar da ya taka a wannan aiki.
Akwai kuma jerin ɗai-ɗaikun mutane da suka sanya
hannu wajen nemowa da saurare da kuma rubuta waɗannan
waƙoƙi
kamar yadda suke ƙunshe a cikin wannan littafi. Waɗannan
katibai sun haɗa da
Nazif Lamara (Gamawa) da Mujahid Ahmad Mukhtar (Misau) da Hamza Ado (Taura) da
Khalid Sani (Misau) da kuma Anas Suleiman (Darazau). Allah (SWT) ya saka da
alheri bisa ga ɗawainiyoyi
da kuka yi domin ganin wannan aiki ya kammala a cikin nasara.
Muna godiya kuma ga rukunin wasu masana a fannonin rayuwa
mabambanta, waɗanda
kuma suka yi tsokaci da sanya albarka dangane da wannan littafi. Daga cikinsu
akwai Alhaji Aminu Ado Bayero (WAMBAN KANO) da Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
(Tsohon Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa, ANA reshen Kano) da Kabiru Muhammad
Assada (Babban Editan Mujallar Muryar Arewa) da Dakta Aminu Bello (Kwalejin
Ilimi ta Ƙasa
FCE Zariya) da kuma Hajiya Fati Niger (Shahararriyar Mawaƙiyar
Hausa). Yabo da jinjina ta musamman ga masu tunani nagari da ɗaukar shawarwari nagari,
tare da aikata ayyuka nagari.
Salisu Ahmad YAKASAI
Abu-Ubaida SANI
MUƘADDIMA
Godiya ta tabbata ga Allah (Subhanahu Wata’ala) wanda ya
halicci ilimi. Tsira da amincinsa su tabbata ga Annabi Muhammadu (Sallallahu
Alaihi wa Sallam) wanda ya wajabta neman ilimi a kan dukkan Musulmi maza da
mata. Na yi matuƙar farin ciki da aka nemi na yi muƙaddima a wannan littafi
mai suna DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA), littafin da Farfesa Salisu
Ahmad Yakasai da Abu-Ubaida Sani suka rubuta a kan ɗaya daga cikin shahararrun mawaƙan
Hausa na wannan zamani.
Haƙiƙa irin wannan aikin haɗin-guiwa
tsakanin malami da ɗalibi,
wata sabuwar hanya ce ta taskacewa da kuma adana waɗannan waƙoƙi domin kada su salwanta. Abin lura a nan
shi ne irin tagomashin da waɗannan
waƙoƙi na
zamani suke da shi, wajen isar da saƙonni ta siga daban-daban domin inganta
rayuwar al’umma. Bugu da ƙari, wannan Diwani ya zo da bayani mai zurfi game da rayuwar
Aminu ALA, wato tarihin ya fito da bayanai dangane da ƙimarsa a cikin al’umma da
yanayin da ya samar da waƙoƙi da kuma mutanen da aka yi waƙoƙin domin su.
Wani ƙari da aka samu kuma a wannan Diwani shi ne na tattara waƙoƙin a
bisa jigogin da suka dace. Wato kama daga jigon ilimantarwa da wa’azantarwa da
faɗakarwa zuwa na
siyasa da soyayya da sarauta da kuma na yabo da jinjina. Sauran sun haɗa da jigogi na ganin dama
da na talla da na aure da na ta’aziyya da ɗaukaka
da kuma na zagin kasuwa. Dukkan waɗannan
abubuwa sun zama shaidar da za a tabbatar da cewa wannan aiki na marubutan haɗaka, wata gudummawa ce ga
ci gaban nazari a fagen adabi, musamman ma fannin waƙoƙin Hausa na zamani.
Farfesa Sa’adiya Omar
Darakta, Cibiyar Nazarin Hausa
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
JINJINA
Muna godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya nuna mana
fitowar wannan muhimmin littafi da aka rubuta a kan waƙoƙin fasihi, gwani, rumbun
hikima wato Alhaji Aminu Ladan Abubakar (ALA). Haƙiƙa ALA wani babban jigo ne kuma jagora a
fagen adabin Hausa na zamani, domin shi ne fitila mafi haske a cikin fitilun da
ke haskaka wannan sabon jigo na waƙoƙin Hausa na zamani.
ALA ya yi amfani da ɗimbin
basirar da Allah ya yi masa wajen ɗabbaƙa
sabon salo a waƙar Hausa ta yadda tilas ya ja hankalin masana da manazarta
adabin Hausa.
Diwani wata taska ce ta adana ayyukan fasaha da suka
danganci waƙa,
da zube, da wasan kwaikwayo, da sauran ayyukan adabi. Muna maraba da wannan
diwani na waƙoƙin
Alhaji Aminu Ladan Abubakar, da fatan littafin zai amfanar a fagen bincike da
nazari ga malamai da kuma ma’abuta
sha’awar waƙoƙin
Hausa.
Marubutan wannan littafi wato Prof. Salisu Ahmad Yakasai da ɗalibinsa Abu-Ubaida Sani,
haƙiƙa sun
yi tsinkaye da hangen nesa wajen yin wannan gagarumin aiki domin ƙara
fito da wannan sabon fanni na adabi da taskace waƙoƙin ALA domin amfaninmu baki ɗaya. Allah Ya albarkaci
wannan littafi, ameen.
Alhaji Aminu Ado Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano
ALLAH SAN BARKA
Samar da littattafai a kan waƙoƙin fasihan mawaƙan Hausa na Arewacin
Nijeriya babban abin jin daɗi
da kuma alfahari ne, saboda ana adanawa da killace ire-iren waɗannan ayyuka domin gudun ɓacewarsu wata rana. Diwanin
waƙoƙin
Aminu Ladan Abubakar (ALA), na tabbata zai zama abin so ga jama’a musamman masu son waƙoƙinsa
da kuma manazarta.
Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
Tsohon Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya, ANA
Reshen Jahar Kano
TSOKACI
Littafin Diwanin Waƙoƙin Amini Ladan Abubakar (ALA), wani kundi
ne da ya zamo ɗaya-tamkar-da-goma
idan ana maganar taskace tarihin mawaƙan Hausa na wannan zamani da kuma
ayyukansu. Mawallafan littafin sun nuna ƙwarewa da naƙaltar sanin ƙabli
da ba'adin wannan fage na adabi, musamman idan aka yi la'akari da tsari da
zubin littafin.
Kabir Assada
Babban Edita, Mujallar Muryar Arewa
GOYON BAYA
Waƙa tana taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka harshe da kuma bunƙasa al'adun al'umma.
Samuwar DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA), tanadi ne na kare wannan aiki
na adabi daga salwanta. Marubuta littafin sun nuna ƙwarewa cikin hikima.
Hajiya Fati Nijar
Mawaƙiyar Hausa
YABAWA
Yau Farfesa Salisu Yakasai,
Sani Ubaida kun yi aiki sosai,
Gun Diwanin nan na ALAN Waƙa.
Wannan aiki Allah sa albarka,
Babbar gona ce ciki ga shuka,
Kwanyar ALA ga ta nan fa ta waƙa.
Don adabi ALA yana raya shi,
Har al’ada ba a bin sa fa bashi,
To haka harshen walwala gun waƙa.
Sulaiman Salisu Muhammad
(Mai Bazazzagiya)
ƘUMSHIYA
SADAUKARWA
GODIYA
MUƘADDIMA
JINJINA
ALLAH SAN BARKA
TSOKACI
GOYON BAYA
YABAWA
GABATARWA
BABI NA ƊAYA
AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAƘA
1.1 Gabatarwa
1.2 Haihuwar Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa)
1.3 Bin Diddigin Laƙabinsa
1.4 Mahaifansa
1.5 Kakanninsa
1.5.1 Kakannin ALA Ta Ɓangaren Mahaifi
1.5.2 Kakannin ALA Ta Ɓangaren Mahaifiya
1.6 Aure Da Iyalensa
1.6.1 Matansa
1.6.2 ‘Ya’yansa
1.7 Iliminsa/Karatunsa
1.7.1 Karatunsa na Addini
1.7.2 Karatunsa na Boko
1.7.2.1 ALA A Duniyar Firamare
1.7.2.2 ALA A Duniyar Sakandare
1.7.2.2 ALA A Duniyar Makarantar Gaba Da Sakandare
1.8 Gwagwarmayar Rayuwa
1.8.1 Ayyukansa
1.8.2 Ayyukan Gwamnati
1.8.3 Sana’a/Kasuwanci
1.8.4 Littattafai
1.8.5 Tafiye-tafiye
1.8.6 Ƙungiyoyi
1.8.6.1 Ra’ayin ALA Game Da Ƙungiya
1.8.7 Ƙwallon Ƙafa
1.9 Kammalawa
BABI NA BIYU
ALA A DUNIYAR WAƘA
2.1 Gabatarwa
2.2 Lokaci Da Dalilin Fara Waƙar Ala
2.3 Waƙar ALA ta Farko
2.4 Ko ALA Yana da Uban Gida A Waƙa?
2.5 Gwagwarmayar ALA A Duniyar Waƙa
2.6 Ɗaukakar ALA A Duniyar Waƙa
2.7 Yadda ALA Ke Shirya Waƙoƙinsa
2.8 Kyaututtukan Da ALA Ya Samu
2.9 Muradin Ala
2.10 Koken Ala
2.11 Lokutan Ƙunci A Rayuwar Ala
2.12 Fargabar Ala
2.13 Wasiyar Ala
2.14 Rubuce-Rubuce Na Ilimi Da Aka Gabatar Game Da Ala
2.15 Kammalawa
BABI NA UKU
WAƘOƘIN ALA MASU JIGON ILIMANTARWA/WA’AZANTARWA/FAƊAKARWA
3.0 Gabatarwa
3.1 Bara a Kufai
3.2 Jami’a Gidan Bankashi
3.3 Yanar Giza-Gizo
3.4 Baba Ina Za Ka Ne?
3.5 Waƙar Ilimi
3.6 Maɗaci
3.7 Marainiya
3.8 Sakarkari
3.9 Rayuwa A Duniya Tana Ban Tsoro
3.10 Murnar Salla Ta Gani
3.11 Waiyo Kaico
3.12 Mutuwa
3.14 Almuhajura
3.15 Ɗanjarida
3.17 Jami’a Gidan Wuya
3.18 Ɗan Barno
3.19 Hangen Dala
3.20 Uba
3.21 Noma
3.22 Kushewa
3.23 Rama Cuta Ba Laifi Ne Ba
3.24 Gobe Alkiyama
3.25 Kukuma
3.26 Sababin Mutuwar Aure
3.27 Adali
3.28 Cutar Taɓin
Hankali
3.29 Ɗamarar Ko Ta Kwana
3.30 Jami’a Gidan Ban Kashi 2
3.31 Mu Zauna Lafiya
3.32 Kammalawa
BABI NA HUƊU
WAƘOƘIN ALA NA SIYASA
4.0 Gabatarwa
4.1 Allah Kaɗa
Guguwar Sauyi
4.2 Kira ga Gwamnoni
4.3 Dashen Mai Shukan Kainuwa Hawa Mulkin Lamaran Yaro
4.4 Zaɓe
4.5 Tallafi
4.6 Baubawan Burmi
4.7 Kamaye
4.8 Makomar Arewa
4. 9 Allah Ya Maimaita
4.10 Buɗaɗɗiyar Wasiƙa
4.11 Waiwaye
4.12 Walle-Walle
4.13 Raba Gardama
4.14 Your Eɗcellency
Sir
4.15 Mallam Ibrahim Shekarau Allah Ya Maimaita
4.16 Sardaunan Mubi Mai Girma
4.17 Garkuwa Na Matasa Doktoro Yahaya Adoza
4.18 Ɗan Bello Yahaya Gwamna Mai Jihar Kogi
4.19 Gwamnan Jama’a Bindo
4.20 Gwamna Bindo Gwamnan Adamawa
4.21 Farar Aniya Alamin Nasara
4.22 Mu Kaɗe
Kumfar Ruwan Kogi
4.23 Bubukuwa
4.24 Bargon Rufa
4.25 Ɗaurin Gwarmi
4.26 Kammalawa
BABI NA BIYAR
WAƘOƘIN ALA MASU JIGON SOYAYYA
5.0 Gabatarwa
5.1 Angara
5.2 Fuju’a
5.3 So
5.4 Kawalwalniya
5.5 Kibiya
5.6 Kalmar So
5.7 Amina
5.8 Tsohuwa Ta Illaila
5.9 Kammalawa
BABI NA SHIDA
WAƘOƘIN ALA NA SARAUTA
6.0 Gabatarwa
6.1 Sarkin Zazzau Shehu Idirisu
6.2 Ado Mai Kano Mai Martaba
6.3 Jaɓɓama
Marafa Abubakar
6.4 Zazzau
6.5 Tamburan ‘Yan Maza: Nuhu Mamman Sunusi
6.6 Sarkin Bauchi Ka Gama Lafiya
6.7 Santuraki Ali Ado Bayeronmu
6.8 Na Laraba Gogarma
6.9 Sadaukin Lafiya Maigirma
6.10 Abubakar Na Laraba
6.11 Nasiru Ɗan Dano
6.12 Bebejin Zazzau Haji Ahmad
6.13 Usman Kogunan Gamawa
6.14 Attahiru Abdurrazak Bunun Bargu
6.15 Bargu Kingdom
6.16 Chiroma Nasiru Ado Bayero
6.17 Gimbiya Mero Tanko Almakura
6.18 Uban Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar
6.18 Bakan Dabo
6.19 Takawa
6.21 Mai Tagwayen Masu
6.22 Kammalawa
BABI NA BAKWAI
WAƘOƘIN ALA NA YABO/JINJINA
7.0 Gabatarwa
7.1 Farfesa Yakasai
7.2 Taken Maza Buratai
7.3 Kwamishinan ‘Yan Sanda Faruk Usman Ambursa
7.4 Ruhanai
7.5 Galadiman Udubo
7.6 Farfesa Sa’idu Muhammad Na Gusau
7.7 Aminar Mama
7.8 Yahuza Ɗan Sadisu Madobi
7.9 Nana Faɗima
7.10 Janaral Murtala Mazan Jiya
7.12 Manjo Janar Mustafa 1
7.13 Manjo Almusdafa 2
7.14 Ɗiya Maza Ɗaukar Farko Baba
7.15 Mai Nasara Burtai
7.16 Ƙara Haƙƙuri Buratai
7.17 ‘Yan Mazan Gidan Soja
7.18 Mashal Sadiƙu
7.19 Mashal Sadiƙu Dogarin Ƙasata
7.20 Ginshiƙin Adabi
7.21 Hamshaƙin Sadauki
7.22 Hashim Ubale
7.23 Farfesa Ango Abdullahi
7.24 Hindu Ta Bunun Bargu
7.25 Karibu Ɗantata
7.26 Muhammadu Miftahul Futuhati
7.27 Rabbu Yarje
7.28 Ganganko
7.29 Sharu Sulaimanu Jadda
7.30 Nuhu Uba Kura
7.31 Malam Amadu mai Rauhani
7.32 Uwar Iyaye A'isha
7.33 Kammalawa
BABI NA TAKWAS
WAƘOƘIN ALA NA GANIN DAMA
8.0 Gabatarwa
8.1 Momi Ummina
8.2 Al’adun Hausa
8.3 Ala: Basasa
8.4 Zariya Gidan Ilimi
8.5 Kano Tumbin Giwa
8.6 Duniya Tana Ruɗa
Ni
8.7 Dutse Gadawur
8.8 Mahaukaciya
8.9 Zuciya
8.10 Kyauta
8.11 Astagfirullah
8.12 Lafiya
8.13 Sakkwaton Usmanu
8.14 Alan Waƙa Zai Koma Gida
8.15 Nasarun Minallahi Sojojin Nijeriya
8.16 Madina Garin Ma'aiki
8.17 Addu'a Ga Masoyana
8.18 Gidan Soja Ginshiƙin Yaƙi
8.19 Hajji Garin Manzon Allah
8.20 Zuciya Ta Auri Tunanina
8.21 Bazazzagiya
8.22 Baubawa 2
8.23 Mashigan Kano
8.24 Jakadiya
8.25 Makauniya
8.26 Du'a'i
8.27 Bayi
8.28 Astagfurullah
8.29 Kammalawa
BABI NA TARA
WAƘOƘIN ALA NA TALLA
9.0 Gabatarwa
9.1 Amana Rediyo
9.2 AM FM
9.3 CTƁ
9.4 Liɓerty
'Yanci Kaduna
9.5 BBC Hausa
9.6 Inuwar Marubuta Jihar Arewa Da Hausa
9.7 Inuwar Marubuta
9.8 Kammalawa
BABI NA GOMA
WAƘOƘIN ALA MASU JIGON AURE
10.0 Gabatarwa
10.1 Tambarin Masoya
10.2 Ayyuriri Amarya Ango
10.3 Alhaji Surajo Abubakar Ango Na Farida
10.4 Auren Ussuman Lawan da Zainabu Abdullah
10.5 Muhammed Tukur Ango Na Fatima
10.6 Bikin Fadeela
10.7 Alalo-Alalo Masoya
10.8 Tambarin Amarsu Da Ango
10.9 Auren Maryama Da Aminu
10.9 Auren Dakta Abdullahi Da Bara’atu
10.10 Maryama Gimbiyar Mata
10.11 Murnar Aure
10.12 Kammalawa
BABI NA GOMA SHA ƊAYA
WAƘOƘIN ALA MASU ZAGIN KASUWA
11.0 Gabatarwa
11.1 Raƙumi
11.2 Gilashi
11.3 Hasbunallahu wa Ni’imal Wakilu
11.4 Kammalawa
BABI NA GOMA SHA BIYU
WAƘOƘIN ALA NA TA’AZIYYA
12.0 Gabatarwa
12.1 Mutuwa Rigar Kowa
12.2 Ta'ziyyar Maitama
12.3 ‘Ya’yan Sarki Ado Bayero
12.4 Ta’aziyyar Mai Martaba Alh. Dr. Ado Bayero
12.5 Kammalawa
BABI NA GOMA SHA UKU
WAƘOƘIN ALA NA ƊAUKAKA
13.0 Gabatarwa
13.1 Ɗaukaka Abar Gudu Abar Nema
13.2 Hikima Taguwa
13.3 Lu’u-Lu’u
13.4 Shahara
13.4.1 Rukunin Tarihi
13.4.4 Rukunin Ƙalubale
13.4.5 Rukunin Nasara
13.6 Kammalawa
Manazarta
GABATARWA
Martaba da ƙimar mutum su ne suke bayyana wane ne shi
a cikin al’umma.
Martaba ita ke ƙunshe wasu sifofi da suka danganci halayya da tunani da ƙawazuci
da zamantakewa a rayuwar mutum. Hasali ma, batun ƙima da martabar mutum sun wuce yadda ake
ganin su a zahiri. Wato siffofin da suke tattare a cikin ƙima da
martaba, su ne suke kammala cikar mutum.
Na farko daga cikin waɗannan
siffofi shi ne sauƙin kai. Mutumin da ya zama mai sauƙin kai, ba shi da wuyar
mu’amala da sauran
jama’a. Sai dai kuma
sau nawa ka taɓa cin
karo da irin wannan mutum? Mutum ne mai ƙana’a da sanin yakamata. Hasali ma, shi mutum ne wanda ba
shi da saurin fushi ko kasala, kuma murmushi ko fara’arsa na inganta yanayi cikin hulɗa.
Irin wannan mutum yana bayar da goyon baya tare da ƙarfafa
guiwa a rayuwar al’umma.
A kowane lokaci ƙofofinsa a buɗe
suke, wato a shirye yake domin sauraron jama’a da kuma ba su shawara ta gari,
kuma duk inda ya je ba ya ɓuya.
Saboda haka ya kasance aboki ta yadda mutane za su tunkare shi domin ba da
shawara dangane da al’amuransu na rayuwa, musamman ma da yake ba batu ba ne na
kuɗi, face kyawun
hali.
Shin ko halayenmu suna taimakawa wajen yin mu’amala da
zuciya ɗaya, kuma ko
hakan na sa a sami sakamako cikin al’amuran yau da kullum na abokan hulɗa? Ba shakka duk wanda ya
tafiyar da rayuwarsa a cikin sauƙi, to za a ga yadda jama’a suke kewaye shi cikin
aminci da riƙon
amana.
Wata siffar kuma ita ce ta ƙarfin hali. A nan ƙarfin hali da muke magana
shi ne na ɗa’a da
ladabi da biyayya. A zubi da tsarin rayuwa, babu abin da ya dace kuma muke buƙata
face ƙarfin
hali domin faɗin
gaskiya. Muna kuma buƙatar ƙarfin hali musamman a lokacin da muka sami kanmu cikin yanayi
na yin zaɓi tsakanin
abu mai kyau da kuma marar kyau, a lokacin da babu mai kallon mu.
Muna buƙatar ƙarfin hali domin kasancewa masu gaskiya da adalci cikin mu’amala da sauran jama’a. da zarar al’umma ta samu mutum mai ƙarfin
hali a matsayin jagora to rayuwar wannan al’umma za ta kasance cikin dacewa. Irin wannan ƙarfin
hali shi ne ƙololuwar
zama namiji. Akwai kuma ladabi da biyayya cikin aiki ko wajabci. Muna iya
tantancewa tsakanin mutum mai ƙwazo da kuma biyayya. A yayin da imani
yake miƙa
wuya ga aiki ko umurni, ƙwazo kuwa himmatuwa ce ga abin da aka sa a gaba.
Su waɗannan
siffofi guda uku, idan suka samu a lokaci guda, to ba shakka an yi tanadin abin
ƙwarai
ga mutum. Waɗannan
abubuwa su ne jagora wajen tafiyar da rayuwa. Wato ƙwazo da miƙa wuya
su ne sirrin gina kai, kuma cikin ƙwazo ne ake gina mutum. Akwai kuma
tausayi. Da yawa mukan sami kanmu cikin so da ƙaunar mutane masu tausayawa. Babu wata
hanya ta samun jin daɗi
tamkar nuna halin tausayawa. Wato farin ciki yana samuwa nan take amma ba ya ɗorewa. Jin daɗi ko wani abu ne da ke
cikin zuciya. Da yawa manzon rahama yakan hore mu da mu bayar maimakon karɓa, musamman ma da yake
hannun bayarwa ya fi hannun karɓa.
Ba shakka duniya na alfahari da masu tausayi, domin ba a samun nasara sai a
cikin tausayawa. Hasali ma ai masu tausayawar nan su ne masu arziƙi a
duniya da lahira, kuma da yake sun shayar da al’umma baiwa ta tausayawa, to zukatansu na cike da
annuri.
Gaskiya ne cewa fuska ita ce riga, wato ana buƙatar
cikakkiyar shiga ta kamala a kowane lokaci. Da ma dai son tufafi cikin ado ba
sabon abu ba ne ga tsarin mawaƙa. Hasali ma, ai ma’abuta amfani da tufafi na ƙwarai
kan ce jikin da aka kyautata shi yakan tafi tare da halayya, sannan daga baya a
samu tasiri ga mutum gaba ɗaya.
Wato mutumin da ya sanya tufafi masu kyau yana ɗauke
da ƙima
cikin daraja ta musamman. Da haka irin waɗannan
mutane kan ƙara
wa kansu himma da ƙwazo na aiki da armashi, kuma a daɗe ana tunawa da su a cikin al’umma saboda irin
ayyukan alherin da aka san su da su.
A insaniya irin ta ɗan
adam, abin da ya gabata yanayi ne da ya dace da Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa):
Wato shahararren mawaƙin da muke gabatar da tarihin rayuwarsa da waƙoƙinsa a
cikin wannan littafi mai suna DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA).
Domin samun cikakken bayanin rayuwa da waƙoƙin ALA, mun kasa littafin zuwa babi-babi
har guda goma sha uku (13).
Bayan gabatarwa, a babi na farko an yi bayanin haihuwar Alan
waƙa,
wato mahaifa da kakanni da ‘yan
uwa. Akwai kuma batun aure da iyalansa da iliminsa (karatunsa) da kuma uwa-uba
gwagwarmayar rayuwa. Babi na biyu kuma bayani ne a kan matsayin Alan waƙa a
duniyar waƙa.
Wato lokaci da dalilin fara waƙa da batun uban gida da muradi da fargaba
da wasiya da kuma ɗaukakar
ALA a duniyar waƙa.
Daga nan kuma sai batun jigogin waƙoƙin Aminu ALA, wato da
yake jigogin na da yawa, babi na uku yana ɗauke
ne da waƙoƙi na
faɗakarwa. A babi na
huɗu kuma, mun kawo waƙoƙin
Aminu Alan Abubakar (ALAN Waƙa) ne masu jigon siyasa.
Babi na biyar kuwa shi ne ya tattaro waƙoƙin
ALAN waƙa,
masu jigon soyayya. A nan ɗin
ma dai maƙasudin
samar da waɗannan waƙoƙi shi
ne so da ƙauna
duka a cikin soyayya. Daga nan kuma sai batun shugabanci (ko jagoranci), wato
tsari na sarauta, wadda idan ta tunkaro to dole a kauce. Babi na shida ne yake ɗauke da waƙoƙin ALA
masu jigon sarauta. A babi na bakwai kuma, waƙoƙin ALA ne masu jigon yabo da kuma
jinjina.
Sai kuma babi na takwas, inda a nan mun kawo waƙoƙin
Aminu ALA ne masu jigo na ganin dama. Wani jigo kuma da yake da alaƙa da
na waƙoƙin
ganin dama shi ne na waƙoƙi masu jigon talla, a babi na tara. Daga nan kuma sai babi na
goma, wanda yake ɗauke
da waƙoƙi masu
jigon zagin kasuwa. A nan ne msu hikimar magana suke cewa koya ya yi zagi a
kasuwa ya san da wanda yake.
A babi na sha ɗaya,
mun kawo waƙoƙin ALA
ne masu jigon aure, wato batun nan na farko cikin matakan rayuwa. Daga nan kuma
sai babi na sha biyu, wato na waƙoƙi masu jigon ta’aziya. A babi na sha uku kuma, waƙoƙin
Aminu ALA ne masu jigon ɗaukaka.
A nan ne muka bijoro da waƙoƙin tarihi da rukunin gwagwarmaya da na shahara da na ƙalubale
da kuma uwa-uba na rukunin nasara.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.