Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Zubar Da Ciki Saboda Karamin Goyo?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Macen da ta ke da ƙaramin goyo sai kuma ta samu wanin cikin. Ko za ta iya zubar da shi saboda neman lafiyar jaririnta da kuma tsoron kar ta sha irin wahalar da ta sha wurin haihuwar na-baya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Da farko dai, Allaah Maɗaukakin Sarki cewa ya yi

وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ مِنْ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُكُمْ وَإِيَّاهُم

Kuma kar ku kashe ’ya’yanku domin talauci (wanda kuke cikinsa), mu muke azurta ku da su kansu. (Surah Al-An’am: 151).

Sannan kuma ya ce

وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ خَشْيَةَ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُم

Kuma kar ku kashe ’ya’yanku domin tsoron talauci (a gare su), mu muke azurta su da ku kanku. (Surah Al-Israa’: 31).

Don haka, bai halatta a kashe abin da ke cikin ciki ba domin tsoron talaucin da ake fama da shi yanzu, ko wanda ake tsoron aukuwarsa nan gaba.

Haka ma ko ba domin tsoron talauci ba ne bai halatta a kashe jariri ba, matuƙar dai ya kai girman da aka hura masa rai wato watanni huɗu. Dalili kuwa, saboda hadisin Ibn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) wanda ke cikin Sahih Al-Bukhaariy da Sahih Muslim da sauran littaffan As-Haabus Sunani wanda ya nuna cewa: A bayan watanni huɗu ne ake aika masa da Mala’ika ya hura masa rai.

Kuma ko da bai kai watanni huɗun ba ma, malamai ba su yarda a dakatar da tsarin halittar ɗan tayin da ke cikin ciki haka nan siddan, ba tare da wani dalili ƙwaƙƙwara ba. Domin a galibi yin hakan ba ya rasa wata matsala da yake haifarwa. Kuma bai halatta musulmi ya saka kansa a cikin kowane irin hatsari mai cutarwa ga jikinsa ba. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« لاَ تَزُولُ قَدَمَا عَبْدٍ يَوْمَ الْقِيَامَةِ حَتَّى يُسْأَلَ عَنْ عُمْرِهِ فِيمَا أَفْنَاهُ وَعَنْ عِلْمِهِ فِيمَا فَعَلَ وَعَنْ مَالِهِ مِنْ أَيْنَ اكْتَسَبَهُ وَفِيمَا أَنْفَقَهُ وَعَنْ جِسْمِهِ فِيمَا أَبْلاَهُ ».

Ƙafafu biyu na bawa ba za su motsawa a Ranar Ƙiyama har sai an tambaye shi a kan tsawon rayuwarsa: A kan me ya ƙarar da ita? Kuma a kan iliminsa: Me ya aikata da shi? Kuma a kan dukiyarsa: Ta ina ya tattaro ta, kuma akan me ya kashe ta? Sai kuma a kan jikinsa: A kan me ya lalatar da shi? (Sahih At-Tirmiziy: 2417).

Shiyasa malamai suka ƙayyade halaccin zubar da cikin da waɗansu sharuɗɗa kafin a yarda da hakan, kamar waɗannan

1. Lallal ya zama mahaifiyar ba za ta cutu a kusa ko a nesa a jikinta daga wannan aikin ba.

2. Sannan kuma ya zama jaririn da take shayarwa ma ba zai cutu da hakan ba. Domin bai halatta a yi asarar jaririn da yake tabbatacce na-hannu a raye, wurin neman wanda ba a da tabbacin samun sa ko lafiyarsa ko rayuwarsa ba.

Idan kuma akwai tabbacin cutuwar jaririn da ake shayarwa yanzu idan aka bari ya cigaba da shan nonon da ya gurɓace ta dalilin sabon cikin da ta samu, a nan ɗin ma ba za a fara ɗaukar matakin zubar da shi ba.

Maimakon haka sai a ɗauki matakin hanawa ko kawar da wannan cutuwar, kamar ta sauya masa wata madarar da zai riƙa sha, kamar na kanti. Ko kuma a sauya masa mai shayarwa. Wannan kuma abu ne halattacce sananne tun tuni. Allaah ya ce

وَإِنْ تَعَاسَرْتُمْ فَسَتُرْضِعُ لَهُ أُخْرَى

Kuma idan kuka kasa daidaituwa, to wata matar za ta iya shayar masa da jaririn. (Saruh At-Talaaq: 6).

Manufa dai: Wata mace tana iya shayar da jaririn wata idan akwai matsalar da ta hana ita mahaifiyar shayar da shi, kamar idan rabuwa ta auku a tsakaninta da mahaifin jaririn. Ko kuma kamar idan irin wannan matsalar ta tsoron cutuwar jaririn saboda samun sabon ciki a wurin mahaifiyarsa ta auku.

Duk mun san cewa, ko babu wata matsala ma ana iya bayar da jariri ga mai shayarwa, kamar yadda al’adar Larabawa ta gudana tun tuni. Kuma ba mu san wani dalilin Shari’a da ya hana hakan a cikin musulunci ba. Illa dai za a kula da ƙa’idoji da sharuɗɗan shayarwar, kamar: Mai shayarwar ta zama uwa ta shayarwa kenan ga jaririn, da kuma tabbatuwar hukunce-hukuncen da suka shafi hakan a tsakaninsa da ita.

Samun ciki a lokacin da mace take shayarwa ba sharri ba ne. Alkhairi ne kuma baiwa ce daga cikin ni’imomin Ubangiji (Subhaanahu Wa Ta’aala), wadda ya kamata ko ma ya wajaba a karɓa da hannu biyu-biyu tare da godiya a gare shi. Ba mu taɓa gani ko jin labarin wanda yake ƙyama ko nuna ƙin amincewa ba, a lokacin da Allaah Ta’aala ya ƙaddara dabbobinsa suka yawaita haihuwa ba.

Sannan kuma ita ni’imar Allaah ai ba a gajiya da ita, kamar yadda hadisi ya nuna

عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ عَنِ النَّبِىِّ - صلى الله عليه وسلم - قَالَ « بَيْنَمَا أَيُّوبُ يَغْتَسِلُ عُرْيَانًا خَرَّ عَلَيْهِ رِجْلُ جَرَادٍ مِنْ ذَهَبٍ، فَجَعَلَ يَحْثِى فِى ثَوْبِهِ ، فَنَادَى رَبُّهُ يَا أَيُّوبُ أَلَمْ أَكُنْ أَغْنَيْتُكَ عَمَّا تَرَى؟ قَالَ: بَلَى يَا رَبِّ، وَلَكِنْ لاَ غِنَى بِى عَنْ بَرَكَتِكَ » .

Daga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Watarana Annabi Ayyub yana wanka tsirara sai dandazon fara na zinare suka zubo masa, sai kuwa ya kama tattarawa a cikin tufarsa. Sai Ubangijinsa ya kiraye shi: Ya Ayyub! Ashe ban wadata ka daga wannan abin da kake gani ba? Ya ce: Haka ne, ya Ubangijina! Sai dai kuma ba ni iya wadatuwa daga albarkarka ce.’ (Sahih Al-Bukhaariy: 7493).

Amma abin mamaki a yau sai ga musulmi yana ƙyamar kyautar Allaah da baiwarsa gare shi ta hanyar haihuwa?! Ko meyasa?

Wani abu ne da masana suke kira: ‘mental conquest’, wato: ‘al-gazwul fikriy’, ma’ana: Yaƙin tunani. An yaƙi tunanin mutanenmu, an sauya musu tunanin ƙwaƙwalwa har suna ganin yarda da karɓar wannan irin kyauta ko baiwa ta Ubangijin Halittu wata illa ce abar ƙyama!! Laa Haula Wala Quwwata Illaa bil Laah.

Allaah ya faɗakar da mu.

WALLAHU A'ALAM 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments