Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Annabi (SAW) Yake Yin Sallar Daren Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Inaso agayamin haƙiƙanin yadda Annabi yakeyin sallar daren ramadan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace shi Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) baya wuce Raka'a 11 acikin Ramadan ko a wajen Ramadan. Kuma idan kakoma Rubuce Rubucen da Malamai sukayi akan Sallar Daren Ramadan zaka samu su Magabata sunayin Tarawihi iri biyu ne.

Na farko shine abunda suke kiransa Tarawihi, ita kuma yadda suke yinta shine bayan anzo anyi Sallar Isha'i Angama se kowa yatafi gida aje aci Abinci aɗan huta se Asake dawowa Masallaci afara yin Sallar dare, kuma Sallah sukeyi Mekyau sosai ba wai Haya-Haya sukeyiba A'a sallah ce sukeyi me tsawo tayadda kafin Agama Raka'a Biyu kowa ya gaji, se ace toh atsaya aɗan huta masu Buƙatu suje suyi Buƙatunsu se adawo aƙara ɗaurawa asake yin wasu Raka'a Biyun. Toh ahaka akeyi ana hutawa har agama Raka'a 11 wannan shine suke kira Tarawihi, kuma ana cemasa Tarawihi ne saboda wannan Hutawarda akeyi a tsakani.

Watarana kuma sesuce yau ba Tarawihi zamuyiba Tahajjudi zamuyi, shikuma Tahajjudi yadda yake shine bayan angama Sallar Isha'i se ace kowa yaje ya kwanta ayi Bacci a huta, bayan anyi Bacci anhuta se aƙara tasowa adawo Masallaci akama Sallah itama haka zasuyita Raka'o'i masu kyau masu tsawo anayi ana Hutawa. Toh ita kuma suna Kiranta Tahajjudine saboda ansamu wannan Baccin kafin akazo aka fara yinta. Kenan Tarawihi da Tahajjudi dukansu abu ɗayane kawai Bambancinsu shine wancan anyi bacci wannan babu bacci. Kokuma kace wannan a Farkon Dare waccan kuma Tsakiyar Dare Kuma su bawai se a Goman ƙarshe Magabata sukeyin Tahajjudiba A'a koda yaushe suna iya yinta acikin Ramadan.

Amma mu ayau Raunine irin namu da Kasala shiyasa Mukeyin Tarawihi daga Alamtara kaifa zuwa Nasi shikenan angama. Kokuma wasuma sekaji kawai ana Karanta wasu gajerun ayoyi se ayi Ruku'u wannan shima kaga ba daidai bane son zuciyane amma dai Sallar tayi tunda dama Asalinta ba wajibi bane, sedai in kunaso ku samu Cikakkiyar lada to sekuyi koyida irin wacce Magabata sukeyi.

Sannan kuma duk wata Sallarda wani zebaka ko wata Addu'a yace wai ga Addu'arda akeyi kullun a Ramadana wannan Sheɗancine da son rai kuma Bidi'ane. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam beyi wata Sallah ba acikin Dararen Ramadana inbanda Tarawihi.

Allah Yasa mudace

🏼Jameel Alhasan Haruna Kabo (ABU ZULAIKHA)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments