An yi bayanin bado a ƙarƙashin 17.3 a babi na goma sha bakwai. Tuwon bado nau’i ne na tuwo da ake amfani da bado wajen sarrafa shi. Kayan haɗi da ake amfani da su yayin samar da wannan tuwo na bado su ne:
a. Bado
b. Ruwa
Za a samu bado mai yawa (daidai adadin tuwon da aka ƙudurci samarwa), a ɓare, sannan a shanya shi. Bayan ya bushe za a gyara a cire duk wata ƙura da ke ciki. Daga nan za a ɗora ruwa bisa wuta. Bayan ya tafasa, za a zuba wannan busasshen ‘ya’yan bado a ciki. Haka za a bar shi ya yi ta dafuwa. Bayan ya yi laushi, sai a tuƙe shi tamkar yadda ake tuƙa tuwon gero. Da zarar haka ta samu, to tuwon bado ya kammala.
Tsokaci
Tuwo a ƙasar
Hausa ruwan dare ne mai game duniya. Za a iya cewa shi ne babban nau’in
abincin da Bahaushe ya fi amfani da shi sama da komai. Musamman a
karkara, shi ne nau’in abincin da ake ci da dare sannan a yi ɗumamensa da safe, wato abin da ake kira wuta biyu. Mahaɗin tuwo kuwa shi ne miya, wanda tuwo ba ya cika abinci ba tare
da an haɗa shi da miya ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.