Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Ƙi Yarda Da Mijinta Saboda Tana Azumin Nafila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Yaya hukuncin matar da miji ya bukaceta saboda tana azumin sunna taƙi ta amince masa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Ta yi kuskure, ya kamata ta amsa kiran mijinta, saboda azumin sunna ya halatta a karya shi ko da babu dalili. Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa: "Mai azumin nafila sarkin kansa ne in yaga dama ya cigaba da azumin, in kuma ya so ya karya", kamar yadda Tirmidhi ya rawaito a Sunan.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments