Mahaɗin
Miyar Sure
Akwai abubuwan da ake buƙata idan za a gudanar da miyar sure. Waɗannan abubuwa su
ne kamar haka:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Tarugu
viii. Tattasai
ix. Wake
Yadda Ake Miyar Sure
Akan samar da wannan miya daga ɗanyen ganyen sure( yakuwa) ko kuma busasshe. Idan ganyen ɗanye ne, akan wanke shi ne kawai kai tsaye. Amma idan busasshe ne,
akan tafasa shi cikin ruwan zafi. Daga nan sai a wanke shi. A wasu
lokutan kuma, ana iya daka busasshen sure ya yi luƙui tamkar dai garin kuka. A irin wannan yanayi, akan kaɗa shi ne, kamar dai yadda ake kaɗa miyar kuka.
Yayin samar da miyar sure, za a samu wake mai ɗan dama, gwargwadon yawan miyar da ake
son yi. Za a surfa wannan wake sannan a wanke, a kuma cire hanci da ɓawon. A gefe guda kuma, za a tanadi kayan yaji a dake su tsaf. Baya ga
haka, za a yi markaɗe ko jajjagen kayan miya, nau’o’in da aka lissafo a sama.
Yayin da kayan haɗi suka kammala, sai batun ɗora
tukunya bisa wuta. Cikin tukunyar nan za a sanya mai,
tare da albasa. Da zarar ya soyu, sai kuma a sanya
kayan miyan da aka tanada (waɗanda aka gurza a dutse ko aka jajjaga a turmi). Haka za a bar wannan kayan miya har sai sun soyu sarai, sai kuma a sanya kayan
yaji da aka tanada, ciki har da dakakkiyar daddawa. Daga nan sai a ɗan motsa shi na kimanin mintuna uku zuwa sama da haka,
har dai sai daddawar da aka sanya ta haɗe. Daga nan sai batun zuba ruwa,
gwargwadon yawan miyan da ake son samarwa.
Bayan an zuba ruwa, za a sanya
gishiri. Daga nan za a bar wannan tukunya ta yi ta tafasa. Idan miyar da nama za a yi,
to a wannan gaɓa ne za a sanya nama (da ma dai an
riga an tafasa nama an ajiye a gefe). Haka ma idan kifi ne, a wannan gaɓa za a sanya (yayin da za a yi amfani da ɗanyen kifi, to ya kamata a tafasa shi kaɗan tare da gishiri kafin a fara miyar).
Abu na gaba shi ne sanya sure cikin miya. Za a ɗauko
suren da aka yanka aka
wanke tare da kanwa (domin a rage mata tsami) a sanya cikin tukunya. Haka ma idan dakakken sure ne
(busasshen) to za a barbaɗa shi tare da kaɗawa.
Bayan an sanya sure, za a rufe tukunya ta ɗauki kimanin mintuna talatin ko ma
sama da haka. Ana son ta ɗauki lokaci mai tsawo domin ta yi
dahuwa mai kyau. Akwai waɗanda ke barinta bisa wuta har na tsawon awa guda. Da zarar an kammala
wannan, to kuwa an samu miyar sure.
Tsokaci
Mata masu laulayin ciki sukan so miyar
sure sosai, musamman a dalilin ɗan tsami-tsamin da miyar ke ɗauke da shi. Haka ma, akan yi wa marar lafiya wanda ba
ya iya cin abinci sosai saboda rashin jin ɗanɗano sosai a
bakinsa. A ɓangare guda kuma, masu gyambon ciki/ciwon yunwa (olsa) ba su fiye ta’ammuli da miyar sure ba, domin
kuwa ba sa son duk wani nau’in abinci mai tsami. Wannan miyar sananniya ce a
garuruwan ƙasar Hausa, musamman Sakkwato da Zamfara da Kabi da Kano da Katsina da kuma Zazzau.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.