Ticker

6/recent/ticker-posts

Ban San Lokacin Da Jinin Haila Ya Zo Min Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Kasantuwar ana zafi sai ya zama tun daga Azahar ban shiga bayi ba har zuwa yin sallar La’asar. Ina cikin raka’ar ƙarshe a Maghriba ne na ji alama. Da na duba bayan sallah sai na ga ashe jini ne har ya ɗan bushe, alamun ya ɗan daɗe. Shi ne na ke son jin, yaya azumin nawa na yau?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A fili yake cewa azumin wannan yinin dai ya lalace, domin dai tun kafin faɗuwar rana ce hailar ta zubo. Don haka za ki rama wannan yinin a cikin azumman da za ki rama a bayan Idi. Amma sallah ba za a rama ta ba, saboda maganar Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa

«كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ»

Hakan yana samun mu, sai a umurce mu da rama azumi, amma ba a umurtan mu da rama sallah. (Sahih Muslim a Kitaab Al-Hayd, lamba: 69).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments