Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanayin Halayyar Mutanen Fada a Zubin Diyan Wasu Wakokin Narambada

Citation: Muhammad, A.L. & Kyambo, S.B. (2024). Yanayin Halayyar Mutanen Fada a Zubin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Narambaɗa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 276-281. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.031.

  Yanayin Halayyar Mutanen Fada a Zubin Ɗ iyan Wasu Wa ƙ o ƙ in Naramba ɗ a  

Na

Amin Lukman Muhammad PhD
Federal College of Education , Zaria
08037753401
Lmameen@yahoo.com  

Da

Safiyanu Bayero Kyambo PhD
Federal College of Education , Zaria
08069299860
Kyambohausa2010@gmail.com  

Tsakure

Wannan aiki ne da ya yi nazarin yadda aka yi amfani da harshe wajen fito da wasu ɗ abi’un al’ummar da ke rayuwa a cikin fada. Duk da cewa wa ɗ annan ɗ abi’u ana iya samun su a kusan kowane irin rukunin al’umma, to amma kasancewar maka ɗ a Ibrahim Naramba ɗ a shahararren maka ɗ in fada wanda ya kwashe lokaci mai tsawo na rayuwarsa yana gogayya a fada har ya kasance yakan rattabo wasu halaye da suka yi fice a fada ya-Allah a wajen yin yabo ko zambo ko habaici da sauransu. Wannan ma ƙ ala ta nazarci wasu ɗ iyan wa ƙ o ƙ insa da kuma fito tare da taskace wa ɗ annan ɗ abi’u da suka mamaye rayuwar fada. Wajen ganin an cimma wannan ƙ udiri, binciken ya bi hanyar sauraron wa ƙ o ƙ in Ibrahim Naramba ɗ a da aka na ɗ a a faifan c.d tare da tattaunawa da wasu tsofaffin fadawa na fadar Zazzau wa ɗ anda suka yi mu’amala da Naramba ɗ a lokacin rayuwarsa. Binciken ya ƙ ara tabbatar da cewa , ana iya nazarin ɗ abi’ar al’umma ta hanyar nazarin furucinsu.

1.0 Gabatarwa

Kasancewar harshe ma ƙ unsa al'adu da adabi, wanda da shi ake nazarin kowannensu, wannan ne ya sa aka nazarci walwalar harshe don fito da wasu al'adu na jama'ar Fada. A fizge takardar ta yi kamar da wadda aka nazarci ɓ angaren al'ada to amma ba al'ada ba ce, domin kuwa a ɓ angaren al'ada ana la'akari ne da al'ada ta zahiri da ta ba ɗ ini, wato material and non material. Ita ko wannan, takarda ce da ta kalli walwalar harshe don gwada yadda al'ada take.

Ba ɓ oyayyen abu ne ba a fagen nazarin kimiyyar harshe cewa kowanne rukunin jama'a yana da nasa kalmomi, kamar a fagagen kasuwanci da shari'a da ilimi har ma da rukunin dattijai da samari da malamai da kuma sarakai.

Idan ka ji ana ambaton kalmomi irin su 'ranka ya da ɗ e' ko gyara kintsi ' ko' gyara gaba' da su 'sunkuye masgaye' to ba ko shakka tunanin da zai wa mai sauraro shi ne al'amarin Fada ko na saraki.

Kasancewar Naramba ɗ a maka ɗ in Fada ta sa an fahimci wasu ɗ abi'u daga harshensa da ya yi amfani wajen gina wa ƙ o ƙ insa. Hasali ma, kusan a iya cewa, wa ɗ annan ɗ abi'u su suka mamaye Fada.

Wannan ma ƙ ala, ta nazarci ilimin walwalar harshe ne, ta inda ta fito da wasu ɗ abi’un fada da maka ɗ a Ibrahim Naramba ɗ a ya girke su a cikin wa ƙ o ƙ insa wa ɗ anda da zarar mai karatu ya karanta su zai fahimci yanayin zamantakewarsu. Ibrahim Naramba ɗ a ba ɓ oyayyen maka ɗ i ba ne a ƙ asar Hausa , amma dai zai yi kyau a ɗ an ƙ ara fito da tarihinsa domin a samu kwalliya ta biya ku ɗ in sabulu. Ibrahim Naramba ɗ a shahararren mawa ƙ i ne na sarkin Gobir na Isa da ya yi fice a shekarun gabanin mulkin kai a Nijeria. Bunza , ( 2009 ) ya bayyana cewa abu ne mawuyaci a ce ga shekarar da aka haifi Naramba ɗ a saboda ba a cika kiyaye shekarar da aka haifi mutum ba a wancan lokacin sai dai a yi kirdadon wasu muhimman abububuwa da suka faru a zamanin, har wa yau ba a sami wani abokin ƙ uruciyarsa ba. A sakamakon tattaunawa da Gusau ( 1995 ) ya yi da wani yaron Naramba ɗ a, sun yi kirdadon cewa an haifi Ibrahim Naramba ɗ a a shekarar 1894 a garin Tubali a unguwar Dembo cikin Gundumar Zungeru a ƙ aramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Wannan mawa ƙ i a cikin hikimominsa ya fito da ɗ abi’un fada a cikin wa ƙ o ƙ insa da dama. Wa ɗ annan ɗ abi’u sun ha ɗ a da kyauta da karimci da rowa da guri da gulma da ƙ iyayya da asararu da ri ƙ on addini da ƙ wazo da ragonci da kuma hamayya .

1.1 Fada Da Fadawa

Muhalli ne na rukunin al’umma inda ake gudanar da harkar jan ragamarta. Mutanen da suke zaune a fada, wato hakimai da ‘ya’yan sarki da barorin sarki su ake kira da fadawa. Bunza , ( 2009 ) ya bayyana cewa fadawa ne suke iso ga sarki, su ke ba da lokacin da za a zo a yi hira, su ke zuwa da kyautar da aka yi a ba su tukuici, su ke ba maka ɗ a labarin abubuwan da ba su sani ba, domin su sarrafa su a wa ƙ a.

1.2 Ɗ abi’a

Ƙ amusun Hausa na Jami'ar Bayero ya bayyana ma'anar ɗ abi'a da cewa ita ce halin mutum ko al'adarsa.

1.3 Walwalar Harshe

Yakasai (2012) ya yi sharar fage cewa, harshen Hausa yana da fa ɗ i da yalwa ta yadda har ya kai ga samar da kare-karensa masu daman gaske, ya kuma nuna cewa wannan yalwar tasa ce ta haifar da nau’o’in Hausa daban-daban. Dangane da wannan zance nasa ya yi wa tufka hanci, inda ya nuna kowane rukunin jama’a a Hausa yake da nasa za ɓ a ɓɓ un kalmomi na musamman da yake amfani da su a sadarwarsa ta yau da kullum. Ya ma ƙ ara da cewa kowane rukunin al’umma ba ya yin tarayya da wani dangane da kalmomin fannu a cikin magana. Ya kawo misalai kamar haka:

Hausar kasuwanci ana samun kalmomi irin su: Saye sayarwa tayi .

Hausar malamai: Akwai kalmomi irin su: Ga’i ɗ i da bawali da mawafa ƙ a .

Hausar dattijai: Akwai kalmomi irin su: Mai ɗ akina da makwanci da yaron gidana .

Hausar samari/ ‘yan mata: Akwai kalmomi irin su: Yaya dai? Da ji mana kin ha ɗ u .

Daga cikin rukunan al’umma da Yakasai 2012 ya bayyana akwai rukunin fada, inda ya bayar da misalai kamar haka: Hausar sarakuna: Akwai kalmomi irin su: Ranka ya da ɗ e da mu muka ce da fadawa da fada rangadi da fare da barori da jakadiya da hawan daba.

2. 0 Halayyar Mutanen Fada a Wasu Wa ƙ o ƙ in Naramba ɗ a

2.1   Kyauta

Wata irin ɗ abi’a ce da akan ba ko mallaka wa mutum wani abu kamar sutura ko ku ɗ i ko dabbobi ko kuma kayan gona, domin kyautata masa. Kyauta fitacciyar ɗ abi’a ce da aka san fadawa da ita musamman daga ma ɗ aukaka a cikin al’umma zuwa ga wa ɗ anda ba su kai su ɗ aukaka ba ko kuma daga fadawa zuwa ga maro ƙ a. Ana iya fahimtar haka a harshen maka ɗ a Ibrahim Naramba ɗ a a wurare da dama cikin ɗ iya r wa ƙ o ƙ insa. Misali:

2.1a. Jagora: “Na zaka barka da shan ruwa na zaka don in yi godiya .

‘Yan amshi  Wata kyauta tana ba ni shawa jikan Hassan dut ta yau ta hi .

  Jagora: Ai sai da so anka kyauta .

  ‘Yan amshi In babu so ba a yin komai .

  Jagora: Dokin nan da kab ba ni kyauta jiya .

  ‘Yan amshi Ko da uban mutum as sarki iri nai yakan hau sai .

(Wa ƙ ar Amadun Bubakar)

2.1b. Jagora: “Ya ba ni dawaki na ƙ warai .

  ‘Yan amshi Sa’akka Amadu ɗ an Iro .

  Komai ƙ asarnan, ban rasawa .

(Wa ƙ ar jikan Sanda arna suna shakkar haye ma)

2.1c. Jagora: “Kyautar doki da ba da riga ,

  Du ɗ ɗ ai suke ga ɗ iyab Basharu .

 ‘ Yan amshi Zama shi abu na iskakke .

(Wa ƙ ar ya ri ƙ a ka da girma)

2.1d. Jagora:   Amadu naka lokaci da yawa nai komi ,

  Zamakin na aje kuramen sunag gero ,

  Manyan riguna akwai ƙ arfe nai shanu .

‘Yan amshi Yo bana doki bakwai garan hab barga niy yi ,

  A! dum matan gidanmu sun sai gorat tatsa ,

  Yau kowace na da nagge saura matak kurma .

  (Naramba ɗ a: Bakandamiya)

Sharhi:

A- Doki yana daga cikin manyan kayan ƙ awa a duniya ba ma kawai al’ummar Hausawa ba. Ko a cikin dawaki akwai na musamman wa ɗ anda kyawunsu da nagartarsu sun isa abin nunawa . Irin wa ɗ annan dawaki ba kowa ke iya mallakarsu ba sai wane da wane. Saboda isa wasu har kyauta suke yi da irin wa ɗ annan dawaki kamar yadda aka yi wa Naramba ɗ a.

B- Naramba ɗ a ya ƙ ara fito da yadda ka yi masa kyautar dawaki na ƙ warai kuma ya ƙ ara nuna cewa komai yake so a duniyar nan za a iya ba shi kyautarsa.

C- A nan, Naramba ɗ a yana nuna cewa manyan abubuwan kyauta kamar doki da riga abubuwa ne da yake da tabbas idan ya je wurin ɗ iyan sarki to tabbas zai same su.

D- A wannan diya n wa ƙ a Naramba ɗ a ya lissafo manyan abubuwan da ya mallake su duk ta hanyar kyauta da aka yi masa a fada. Wa ɗ annan abubuwa su ne manyan dami na gero da manyan riguna da tsabar ku ɗ i da kuma shanu da dawakai har guda bakwai. Har wa yau, a sanadiyyar kyauta da aka yi wa Naramba ɗ a a fada, ba shi ka ɗ ai da yaransa ba har da matan gidansa kowacce ta sami kyautar nagge.

2.2 Rowa

Ɗ abi’a ce akasin kyauta wadda akan hana mutum abubuwan da ake mallaka masa a matsayin kyauta. Rowa babbar alama ce da ake fahimtar ɗ abi’ar fadawa a ciki harshen mawa ƙ an fada da dama irin su Ibrahim Naramba ɗ a.

2.2a. Jagora: Ka ga ɗ an sarki da kunnuwa da h wa ɗ i ,

  ‘Yan amshi Ga shi da ƙ arya ga shi da rowa ,

 Ko ka g irmama shi ba ya sarki .

(Naramba ɗ a: Masu gari mazan gabas tsa yayye) .

2.2b. Jagora: “Ai mutanen Ƙ aura suna h wa ɗ in ,

  Samun wane ya zamo samun mujiya ,

  Matanai ba su ci bare danginai su ci…..”

  (Naramba ɗ a: Alhaji Ɗ an Durgu) .

2.2c. Jagora: Abin sarauta abin rabo na ,

  In an sama a ba mutane .

Yan Amshi: Sai ka ga kullun yana shigowa ,

  Amma shi wanda bai sani ba ,

  Sai ya ci shi ɗ ai yana ta gyatsi…..”

(Naramba ɗ a: Tattaki maza ɗ an Shehu na babba) .

Sharhi:

A- Rowa fitacciyar ɗ abi’a ce da ake samu a fada wadda kuma maka ɗ an fada da dama sukan yi amfani da ita su zambaci ko su yi habaici ga masu wannan ɗ abi’a kamar yadda muka gani a wannan ɗ iyan wa ƙ a.

B- An fito da ɗ abi’ar fada ta rowa a wannan ɗ iya n wa ƙ a, ta inda aka nuna saboda tsabar rowar wani ɗ an sarki ko matansa ba sa cin abin hannunsa ballantana mawa ƙ a.

C- Wannan ɗ iya n wa ƙ a ta fito da ɗ abi’ar rowa da ake samu a fada ta inda wani da yake i ƙ irarin cewa shi mai sarauta ne to amma kuma ba ya ba kowa komai sai da i ya ɓ uya shi ka ɗ ai ya ci abinsa.

2.2   Ƙ wazo

Yana daga cikin kyawawan ɗ abi’u na fadawa wanda akan yaba wa mutum idan yana da shi har wa yau yakan zama abin fa ɗ i idan ya kasance mutum bai da shi. Ana iya fahimtar haka a harshen Naramba ɗ a a wurare dama kamar haka:

2.3a Jagora:  An gamu Hausa kullufin jama’a duk sun zo ,

Kowane Kam f wani shina tsaye bakin garka .

Yan Amshi:   Mai duka yat taho da shi da su Gatau ,

  Amadu dum magana wadda kay yi ,

  Anka ji daidai tay yi ,

  Tun rannan Amiru ya ƙ ƙ ara ma girma ,

  Kuma rannan waziri ya ƙ ƙ ara ma girma ,

  Amadu bai hito ga dattijon banza ba.

  (Naramba ɗ a: Bakandamiya)

2.3b Jagora:   In mahaukaci kake duk ɗ ai na ,

  In ɗ an bori kake duk ɗ ai na ,

  In ɗ an tauri kake duk ɗ ai na .

Yan Amshi: In ka ta ɓ a sarki ka gane ya gwada ,

  Maka bai san wargi ga .

(Naramba ɗ a: Bai ɗ au wargi ba na Jekada) .

2.3c Jagora: Ai yanzu ƙ asar Maradun Habu, kai Jallah yab ba .

  Yan Amshi: Zama in ka yi ƙ ulli ina mai walwalewa?

(Naramba ɗ a: Buwayi maza na Jekada) .

2.3d Jagora: Yanzu Amadu ilmi garai na ɗ aure ashararu .

Yan Amshi: Yau ƙ asatai duka babu ko guda sun ce sun tuba .

  Jagora: Amadu mai tawakkali na maji-da ɗ i .

Yan Amshi: Uban malami ka kai duw wurin da Ibrahim shi yak kai ,

  Zamakin an kira shi Sarkin Gobir Hausa ,

  Kai ko an kira ka sarkin Gobir Hausa .

(Naramba ɗ a: Bakandamiya)

Sharhi:

A- An yi gagarumin taro a Sakkwato wanda ya sami halartar ɗ imbin jama’a, a wannan taro kowa sai yabon sarkin Gobir Amadu yake yi saboda tsabar ƙ wazonsa, a sanadiyyar haka har sai da Sarkin Musulmi ya yaba da wannan namijin aiki na sarki. Don haka, ƙ wazo babbar ɗ abi’a ce da ake samu a fada kamar yadda aka gani a wannan ɗ iyar wa ƙ a ta Naramba ɗ a.

B- Mahaukaci da ɗ an bori da ɗ an tauri wasu mutane ne wa ɗ anda aka san su ta ƙ adarai a cikin al’umma, a nan, Naramamba ɗ a yana nuna cewa komai ta ƙ adarancin mutum in ya zo fada ya ha ɗ u da sarki sai ya raina kansa saboda ƙ wazon sarkin. Don haka, ƙ wazo ɗ abi’a ce ta fada da muka gani a wa ƙ ar Naramba ɗ a.

C- A nan kuma an nuna ɗ abi’ar ƙ wazo ta inda ake nuna saboda ƙ wazon sarki idan ya fa ɗ i wani abu babu wanda ya isa ya canza abin da ya fa ɗ a.

D- A ɓ angaren farko na wannan ɗ iyar wa ƙ a, an nuna ɗ abi’ar ƙ wazo ta yanda duk ashararancin ashararai sai da suka sadu da su suka tuba. A ɓ angare na biyu kuwa, an nuna kamar yadda aka kira kakansa Sarkin Gobir na Isa, shi ma yanzu ya yi ƙ wazo an kira shi da sunan Sarkin Gobir.

2.4 Ƙ iyayya

Ɗ abi’a ce mummuna wadda jama’a kan tsani mutum ba tare da wani dalili ba. Irin wannan ɗ abi’a takan sa a sa w a mutum laifi alhali kuma bai yi ba . Haka kuma mutum yakan yi abu mai kyau kuma ƙ iri- ƙ iri ana nuna cewa ba shi ya yi wannan aikin alheri ba. Wannan mummunar ɗ abi’a ta mamaye zaman fada, kuma ana iya fahimtar haka a harshen Naramba ɗ a. Ga misalai kamar haka:

2.4a Jagora: Mai kai dungu ya kai mari ,

  Bai zauna ba safe dut .

Yan Amshi: Mun san ƙ ulle- ƙ ulle ya yi mai yawa ,

  Ba ya samun komai gidan ga sai h warin ƙ wafa .

  (Naramba ɗ a: Garba Ƙ i-gudu ɗ an Mori)

2.4b Jagora: Ya kwance batutuwa na Jekada ya taho gida .

Yan Amshi: Kunya ga ta nan gare ku mutanen banza .

Jagora: Yau mai ashararu ya ka ɗ e duniya ta yi mai h washi .

Yan Amshi:  Babu zama garai zama fitina yat tayas ,

  Ya san ba ya kwarjini ga mutanen Hausa ,

  Kowacce yana iyawa ga hili nan ,

  Sai ya ƙ etare gidanai ba ban kwana .

  (Naramba ɗ a: Ba kandamiya )

SHARHI:

A-   Wannan ɓ alo- ɓ alo ya nuna cewa akwai masu yin ƙ ulle- ƙ ulle a fada wa ɗ anda saboda ƙ iyayya ne suke yi domin su samu su zama sarki ko wani nasu ya zama sarki ko ya sami wata sarauta.

B-    A nan kuwa, Naramba ɗ a ya yi habaici ne ga ma ƙ iyan sarki masu kai tsegumi saboda tsagwaron ƙ iyayya da suke da ita. Don haka, wannan ɗ iyar wa ƙ a tana nuna cewa ana iya fahimtar cewa akwai ƙ iyayayya tsibe a cikin fada.

2.5 Hamayya

Ɗ abi’ar ɗ an adam ce da takan kasance a zukatan mutum biyu ko fiye da haka da suka nemi wani abu guda ɗ aya, a sakamakon haka dole mutum ɗ aya ne zai samu, shi kuma ɗ ayan ko sauran jama’ar dole su ha ƙ ura. Komai yawan ɗ iyan sarki dole mutum ɗ aya ne za a za ɓ a kuma sauran ‘yan takaran su ha ƙ ura. Naramba ɗ a ya fito da wannan ɗ ai’a ta fada a wurare da dama cikin wa ƙ o ƙ insa kuma galibi yakan yi haka ne don muzanta abokan hamayyar sarki ko wani mai sarauta.

2.5a Jagora:  Ai ga fa gidan suna gani sai zago .

Yan Amshi:   Ga mai shi nan kowat taho ya tsai da ƙ a h watai garka .

(Naramba ɗ a: Baban Dodo)

2.5b Jagora: Ku dangana tun ga uwaye .

Yan Amshi: Ba duka ɗ an sarki ba ka samun sarki .

  Jagora:   Ɗ an sarki duka ya ga sarauta ga ta kamar kusa tai ma shi nisa .

  Yan Amshi: In dai bai yi sarautan nan ba sai ya tsufa da mikin zuci .

Jagora: Ɗ an sarki duka ab ba kowa ,

  Ɗ an sarki duka ab ba komi ,

  Sannan ya tsira yawon banza .

  Yan Amshi:   Ya san ba ya sarauta ,

  Sai fa ya kwan nan gobe ya kwan nan jibi ,

  Dangi nai mishi Allah waddai .

  (Naramba ɗ a: Gogarman Tudu) .

2.5c Jagora: Ga Ummaru ɗ an Alu gidanai na Isa .

Yan Amshi: Ya yi sarki kuma ga ɗ iyad da ya hai h wa nan sun yi ,

  Kuma yau ga gadonsa nan jikanai ya hau ,

Dangi sai ku han ƙ ure shi na ham Madi .

(Naramba ɗ a: Baban Dodo) .

2.5d Jagora:  Wa ɗ anga da kak kayar ga shi an h wa ɗ a min .

Yan Amshi: Wai an ce da ni sukaf fushi .

Jagora:   Bamin kokowa kodayaushe shi aka shammata bai iya ba ,

Yan Amshi: Ga wata kokowa an wuce da shi karsanai kakka ɓ e mashi ƙ asa.  (Naramba ɗ a: Ibrahimu na Guraguri).

Sharhi:

A- Wannan yana nuna cewa mutane da yawa ne suka nemi wannan kujerar sarauta ammam mutum ɗ aya ne daga cikinsu ya yi nasara. Don haka Naramba ɗ a ya fito mana da wannan ɗ abi’ar hamayya a cikin ɗ iyar wa ƙ arsa.

B-    Ana iya ganin ɗ abi’ar hamayya daga cikin ɗ abi’un fada a wa ƙ o ƙ in Naramba ɗ a ta inda ya nuna cewa ba duka ɗ an sarki ne kan zamo sarki ba, domin kuwa a wata ɗ iyar wa ƙ ar, Naramba ɗ a cewa ya yi duk ɗ an sarki so yake ya zama sarki. Ashe kenan, masu neman sarkin suna da yawa, don haka ga hamayya ta fito sarari a wannan ɗ iyar wa ƙ a.

C-    A nan, maka ɗ a Naramba ɗ a ya nuna cewa Sarkin Gobir na Isa Amadu ya gaji gadon mahaifinsa wanda shi ma mahaifin nasa ya gada daga nasa mahaifin. Don haka sauran dangi ya zama wajibi su ha ƙ ura domin Sarkin Gobir Amadun shi zai ta ri ƙ e ragamar sarautar har abada.

D-   Naramba ɗ a ya kwatanta neman sarauta da kokuwa inda mai ƙ arfi da dubara da sa’a yakan kayar da abokin kokuwarsa. Don haka, wannan ɗ abi’a ta hamayya tana nan jibge a fada.

2.6 Guri

Ɗ abi’a ce ta ɗ an adam wadda take sa masa matu ƙ ar soyyayyar samun wani abu. Kusan duk wani ɗ an sarki yana da gurin ya ga ya zamo sarki, ko da kuwa ya san sarautar ta fi ƙ arfinsa, wata ƙ ila a sanadiyyar kasancewarsa bai mallaki wasu sifofi da akan gane masu alamun zamowa sarki ba. Tun zamanin da har yanzu akwai wa ɗ ansu alamu a al’adar zamantakewar al’ummar Hausawa da sukan sa a gane wane zai iya zama sarki.

Naramba ɗ a ya fito da wannan ɗ abi’a ta guri a wurare da dama cikin wa ƙ o ƙ insa wa ɗ anda za su sa a fahimci cewa lallai guri yana daga cikin ɗ abi’ar mutanen fada. Misali:

2.6a Jagora: Gurin ɗ an sarki ya yi sarki Allah ya ba ka ƙ asar Isa .

Yan Amshi: Ri ƙ e bayinka ri ƙ e barwanka ka yi addini ka yi alheri ,

  Ka tuna daga sarki sai mutuwa ,

  Mu ka ga muna ro ƙ on Allah ,

 Allah ya cika ma imani kuma yai maka kyakkyawa ƙ ƙ arko.

(Naramba ɗ a: Bai ɗ au wargi ba na Jekada) .

2.6b Jagora: Ko dauri ƙ o ƙ arin ɗ an sarki ya kai gadon tsohonai ,

  Iro ya kai ga gadon magaji Danko ɗ an Garba ga ya ko hannunai .

Jagora: Kai am Muhammadun Badarawa gadanga yau kai a’ Audu .

Yan Amshi: Yun ƙ ura duk ɗ an sarkin dak kag ga bai zam sarki ba bai h washe haushi ba .

  (Naramba ɗ a: Ginshimin gidan Halliru Uban Zagi) .

2.6c Jagora: Duk ɗ an sarki son yake ya zam sarki sai in ba ta samuwa .

Yan Amshi: Ta tabbata ko ban h wa ɗ i ba in gandu ya samu ya fi gamana .

Sharhi:

A- Guri babbar ɗ abi’a ce ta fada wadda Naramba ɗ a ya ƙ ara fitowa da ita sarari a wurare da dama cikin wa ƙ o ƙ insa kamar yadda aka gani ɓ alo- ɓ alo a wannan ɗ iyar wa ƙ a. Haka nan, idan an cimma wannan guri na samun sarauta akan so ta dawwama har ƙ arshen rayuwa.

B- A nan kuwa maka ɗ a Naramba ɗ a ya nuna cewa ɗ abi’ar gurin zama sarki ba ta yau ba ce ko can da ma akwai ta. Kamar yadda ya nuna a wannan ɗ iyar wa ƙ a da ke cewa: “Ko dauri kwarjin ɗ an sarki ya hau gadon tsohonai . ” Sa’annan ya ƙ ara da cewa: “ Ɗ an sarkin da kag ga bai zam sarki bai h washe haushi ba .

C-    Ha ƙ i ƙ a, kamar yadda Ibrahim Naramba ɗ a ya bayyana a wannan ɗ iyar wa ƙ a duk wani ɗ an sarki yana da gurin zama sarki ko da kuwa bai da halin zama sarki, to amma ba a rasa shi da wannan ɗ abi’a.

2.7 Gulma

Ɗ abi’a ce ta ɗ an’adam wanda wani yakan ɗ auki zancen wani ya kai wa wani, wanda kuma aka ɗ auki maganar tasa idan ya ji ba zai ji da ɗ i ba. Kalmomi dangin gulma sun ha ɗ a da munafunci da kissa da kuma makirci. Gulma ɗ abi’a ce marar kyau a zamantakewa kuma dabi’a ce da ta mamamye jama’ar fada.

2.7a Jagora: Ɗ an sarkin da kag ga ya jahilce ya ƙ i batun Allah ,

Yai nan ya yi makirci yai nan da munafunci .

Yan Amshi: Bai sani ba ya lalace ba ya zama komai .

Jagora: Irin su ko cikin dangi ,

Yan Amshi: Su anka mayar baya .

(Naramba ɗ a: Ni ƙ atau Bajimin Macci ɗ o) .

2.7b Jagora: Bari kau yarda da munafiki .

Yan Amshi: Mai ɓ anna ƙ auye da birni kowa ya san shi da ƙ arya .

(Naramba ɗ a: Abu na Namoda Shiryayye) .

2.7c Jagora In ka ga mutum na ‘yan zage-zage sarki bai gyara mai ba ,

Yan Amshi: Ran da yag gyara mai sai bugun gaba .

(Naramba ɗ a: Ya ci maza ya kwan yana shire) .

Sharhi:

A- A wannan ɗ iyar wa ƙ a an nuna yadda ɗ abi’ar gulma ta sami wuri a fada kamar yadda aka ga wannan ɗ an sarki yake zuwa can ya kai wani gutsiri-tsoma, haka kuma ya kwaso abin da aka yi a can ya kawo nan.

B- A nan, Naramba ɗ a ya fito mana da ɗ abi’ar gulma a fada, ta inda ya nuna mana cewa aikinsu kenan munafurci daga birni har ƙ auye kana ya nuna mana cewa wa ɗ annan mutane ba ɓ oyayyu ba ne a cikin al’umma kowa ya san su.

C- Ɗ abi’ar fadawa ce kaiwa gulma wajen abokan hamayya da yin zage-zage kamar yadda Naramba ɗ a ya fito mana da ita a wannan ɗ iyar wa ƙ a inda ya ce: “In ka ga mutum na ‘yan zage-zage.” Bugu da ƙ ari saboda rashin kunyar bafade a duk lokacin da wani zai ba shi wani abu nan da nan zai juyo ya ri ƙ a yabonsa.

3.0 Sakamakon Bincike

Wannan aiki na ilimin walwalar harshe, ya yi nazari kuma ya fito da wasu ɗ abi’un fada a cikin wa ƙ o ƙ in maka ɗ a Ibrahim Naramba ɗ a tare da taskace su. Har wa yau, ma ƙ alar za ta taimaka wa masu son yin bincike da ya shafi halayya da al’adun ɗ an ’a dam (sociologist and anthropologist) wajen fito da irin ɗ abi’un da suke tattare a fadojin Hausawa. Haka kuma, ma ƙ alar za ta da ɗ a haskaka wa masu bincike a kan walwalar harshe, wajen fasalta irin binciken da za su yi, domin kuwa, da na gaba ake gwada zurfin ruwa.

Mana zarta

Bunza, A. M. (2009) . Naramba ɗ a. Lagos: Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.

Fromkin d a Wasu (2007) . An Introduction to Language. U.S.A: Thomson Wadworth.

Haugen, E (1972) . “Dialect Language and Nation ” In Pride J.B & Holmes, J (Ed) England (UK): Cambridge Uni v ersity Press

Jami'ar Bayero (2006) Ƙ amusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero.

McDa v id, R.I (1965) . American Social Dialect. College English. Pride, J.B and Holmes, J (eds) (1972) Sociolinguistics: Selected Readings, Harmondsworth: Pengiun

Post a Comment

0 Comments